An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
[5/20, 7:29 PM] El Yaqoub: 💘MATAR ABBANA💘
(Luv Story)
Writing By Amnah El Yaqoub
Kuyi following Channel dina domin samun zafafan labarai💃🏻👇🏻
https://whatsapp.com/channel/0029VbBR7naJ93wTuOypQV45
1
Duk yanda yaso motar tatashi, abun yaci tura, badon yaso ba, haka yajuyo cikin ladabi da girmamawa yadubi Hajiya Kaka yace"Hajiya inaga saide natare muku abun hawa ku qarasa gida,zan kira me gyara yaduba motar,bansan meyasa ta tsaya ba"
Hajiya Kaka tasaki ajiyar zuciya sannan ta dubi kyakykywar jikarta, wadda hankalinta kacokam yake kan wayar hannunta qirar IPhone,tace"to hamshaqiya muje, kin hard'e kina danna waya kamar 'yar sarki,mota ta lalace mu sauka munemi abun hawa"
Yarinyar da batafi shekara goma Sha takwas ba,daga ganinta kasan surutu bai dameta ba, batace uffan ba, sai baki data ta6e tafara qoqarin bude motar, saide kafin takaiga budewa direban ya zagayo da sauri yabude musu, sannan yazaro wayarsa daga cikin aljihun wandon sa yafara kiran me gyara, yayinda hannunsa na hagu yake d'agashi sama yana qoqarin tare musu Keke napep.
Ba'a bar Hajiya Kaka abaya ba, itama hannu tasa tana qoqarin tare musu abun hawan har Allah yakawo wani ya dakata,kafin direban yayi magana Hajiya Kaka tace"tsaya,tsaya,d'an sahu,tsaya ka kwashemu "
Dan adede ta ya kalli motar dake gefensu fara tas,qirar Lexus Rs 350 motar sai shining take tana daukar ido,da alama sabuwa ce,nan take yasan cewa yayi babban kamu.
Hajiya Kaka tashige, sannan itama jikarta tashiga, direban ya d'an rissina dede wajan da d'an sahu yake zaune sannan yace"G.R.A zaka kaisu"
Dan sahu ya kalli Hajiya Kaka yace"Hajiya kudinku dubu uku"
Hajiya Kaka tace"muje Allah ya saukemu lafiya"
Direban nasu yafara qoqarin dauko kudin zai bayar, Hajiya Kaka tace" 'Dan Ladi barshi zan bashi kudin"
'Dan Ladi ya maida kudinsa cikin aljihunsa sannan yace"to Hajiya Kaka saina qaraso,Allah Yakiyaye hanya"
Hajiya Kaka tace"A a 'Dan Ladi, zoka kar6i dubu daya kasayi ruwa kasha"
'Dan Ladi direba yayi murmushi yace"A a Hajiya Kaka ki barshi"
Hajiya Kaka tace"to kanaji ko 'Dan Ladi?,idan angama gyara motar, kana shigowa layin farko kafin kaje gidan Alhaji Biniya,anayin qosai awajan kasiyo min kataho min dashi"
Kafin 'Dan Ladi yayi magana d'an sahu yace"Hajiya baku gama bane?"
Hajiya Kaka tace"mungama, sarkin azalzala muje,ni Allahn dayayi ni banason kad'ar hankali a rayuwata,ita rayuwa dakake bahaka ake tafiyar da'itaba "
Jikarta dake gefe ta dafe kanta da hannunta sannan ta kalli Hajiya Kaka tace" yanzu de tunda yaja mun tafi Kaka kiyi shiru mana,sai mita kike tun dazu haba!"
Hajiya Kaka tayi shiru,saide bakin nan nata ta cuno shi gaba alamun fad'an da jikar tata tayi mata baiyi mata dad'i ba.
Sun d'auki lokaci suna tafiya wani mutum daga gefen titi yataresu yace"Kabuga"
'Dan sahu yace"Drop suka dauka"
Sannan yafara qoqarin cigaba da tafiya, Hajiya Kaka tace"ai kasan drop d'in muka dauka amma daya tareka ka tsaya, tunda ka tsaya Yaya na'iya dakai? daukeshi kawai,shi musulmi ai d'an uwan musulmi ne"
Dan sahu yace"to nagode"
Ya kalli fasinjan dake tsaye yanajin duk abinda yake faruwa, sannan yace"nawane dakai?"
Fasinja yace" d'ari biyar ce"
Dan sahu yace"gaskiya banida canji yanzu nafuto"
Yana fad'ar haka yafara qoqarin tada napep dinsa, cikin sauri Hajiya Kaka tace"dakata d'an sahu,bari in duba muku canji, banaso naga abokin kasuwanci na yana Neman canji"
Cikin sauri jikarta dake gefe ta kalleta tace"Abokin kasuwancinki?, Kaka yaushe kika fara Jan adedeta bamu sani ba?"
Kota kanta bata biba, tabude hand back din dake kan cinyarta tabasu canjin, sannan ta matsa masa shima yashigo cikin adeden,basu dade da daukan hanya ba, sukasha kwana cikin wani gidan mai, Hajiya Kaka tana ganin haka tace"uhm za'a bata abinci"
Babu wanda ya tanka mata acikin adedetan har suka tsaya aka fara zuba musu mai, daga gefe guda akwai wasu samari su uku kowa yana kan Abun hawa suna jira layi yazo kansu,zancen Sojojin qasar suke,d'aya daga cikin matasan yace"ainaji dad'in yanda shugaban Sojojin nan ya tunkari kidnappers d'in nan yayi futo nafuto dasu "
Kafin wani daga cikinsu yabashi amsa Hajiya Kaka ta leqo kanta daga cikin adede tace"shi kwamandon Sojojin ne ya tunkari masu Garkuwa da mutane? Kuma baya jin tsoro?"
Wani daga cikinsu yayi murmushi yace"Haba Mama, wanne tsoro kuma? ai bayajin tsoro"
Hajiya Kaka ta jinjina kanta sannan tace" wataran zaici gidansu kuwa"
Babu wanda bata bawa dariya ba,ciki harda jikarta wadda hankalinta yake kan wayarta tana shafawa.
Suna barin gidan man gaba kad'an sukaga dalibai masu yawa 'yan makarantar secondary suna tsaye agefen titi kasancewar safiyace kowa yana fafutukar neman abun hawa domin tafiya makaranta. Hajiya Kaka ta kalli wannan uban dalibai wanda dayawa daga cikinsu duk Yan mata ne,kuma dukkaninsu babu me aure, ahakan burin ko wacce uwa shine ta aurar da diyarta, tasaki ajiyar zuciya ta kalli jikarta tanayi mata nuni da wannan daliban tace"kinga duk jiran abun hawa suke"
Jikar tata ta kalli daliban sannan ta maida hankalin ta kan waya batare data tanka ba,basu dade da barin wajanba suka sake ganin wasu tarin daliban, nanma Hajiya Kaka ta gagara yin shiru saida ta tanka, tasake kallon Jikar tata akaro na biyu tace"suma wannan jiran motar suke,uhm...,Allah de yabaku nagari"
Wannan Karon ma Jikar bata tanka mata ba, haushi yakama Hajiya Kaka,cikin 6acin rai tace"nifa arayuwata natsani baqin miskilancin nan naki Husna,shiyasa banason tafiya dake nafiso nayi tafiya da Hassana, muna tafe munata zancen mu,amma ke sai kiyi gum da baki kamar Yayanku HAFEEZU, gaba daya kin kwaso baqin miskilancin sa kin dorawa kanki"
Husna ta girgiza kanta tace"yanzu Kaka me kikeso nace miki? ni wallahi surutun naki ma ya isheni,qiris yarage kaina yafashe,shiyasa nayi miki shiru amma ke ban hanaki ba kiyi abunki ke kadai"
Hajiya Kaka ta jinjina kanta sannan tace"gaskiya ne,ga Rabi'atu uwar ta6a66u ai dole nayi surutu ni kadai,ato duk wanda yake surutu shi kad'ai kam menene marabar sa da ta6a66e?"(🤭)
Dan sahu yana jinsu yana dariya shi kadai,Shima d'aya matashin dayake zaune agefen Hajiya Kaka saida ya murmusa, yayinda Husna tayi shiru bata tankaba kamar bada ita ake maganar ba.
Hajiya Kaka kuwa ta cuno baki gaba tace"Gaskiya ne"
Da'aka sake jimawa ita kadai de tasake cewa "Gaskiya ne"
Itade Husna batace komai ba, har Allah yakawo su gida lafiya,d'an sahu ya ajiyesu a bakin get din wani danqararen gida,kallo d'aya zaka yiwa hadaddan gidan ka tabbatar nera tayi kuka.
Me gadi ya bude masu qaramar qofa yana sake gaida Hajiya Kaka cikin girmamawa, suna shiga compound din gidan Hajiya Kaka tacire Mayafin jikinta tad'aga qafa tayi gaba tabar Husna abaya,yayinda wayar Husna tayi qara alamar kira yashigo, ta amsa kiran tana magana yayinda idonta yake kan parking lot din gidan wanda wasu manya-mayan motoci guda hudu suke adane aciki sai daukan ido motocin suke, saide akwai yar qura ajikinsu kad'an kasancewar ba'a cika hawansu ba.
Hajiya Kaka tana shiga falonsu wani sanyin esi ya daketa, tayi wulli da Mayafin hannunta akan kujera sannan ta zauna tana fad'in "banda zuwa ta'aziyyar nan tazamemin dole, da babu abinda zaisa nafita daga gida sassafen nan"
Hassana dake jera abun break fast akan dining taqaraso falon tana fad'in "Kaka kun dawo?, ina kika bar Husna?"
Hajiya Kaka ta kalleta, 'yanbiyun jikokin nata basu da banbanci ta 6angaren kamanni,idan baka sansu ba babu yanda za'ai ka'iya banbance su saboda yanda suke tsananin kama da juna,saide halaiyar su ta banbanta data juna, Husna miskila ce taqin qarawa kamar Babban Yayansu HAFEEZ ,yayinda Hassana take faram-faram kowa nata ne.
Saida tagama tunanin sannan tace"naje na siyar da'ita nadawo, kudin kuma qarfi ya cinye"
Hassana tanajin haka tayi murmushi, lokaci daya tagano cewa da alama sunyi abunda suka saba, wato fada.
Kafin tayi magana Husna tashigo falon, suna ganin juna itada Hassana suka saki murmushi, daga nan Hassana tawuce tahado tea, ta kunna Kallo takamo musu tashar Bollywood, tana shan tea suna kallo, yayinda Husna take danna wayarta gefe guda kuma tana kallon itama, basu dade da fara kallon ba suka fara musu da juna, inda Husna take ganin Tauraruwa Rashmika tafi Dipika, Hajiya Kaka ta kallesu ta girgiza kai sannan ta miqe tawuce Dining domin cin abinci, dan kwata-kwata bata fahimci akan me suke musun ba.
*** *** ***
Sassafe tatashi daga baccin datake me mutuqar dad'i,kasancewar ta kwanta jikinta cike da gajiya hakan yasa baccin yayi mata mugun dadi sosai,daqyar tatashi ta zauna tayi wata irin miqa tana banqaro qirji,hakan yasa fararen nashanunta suka banqaro kamar zasu futo daga saman rigar jikinta, wadda kallo d'aya zaka yiwa doguwar rigar jikin nata ka tabbatar cewa rigar taji jiki, hamma tasaki wadda tayi sanadiyar lo6awar kumatun ta duka biyun (dimples), tajuya manyan idanuwanta wadda qwayar cikinsu ta kasance ruwan toka,ta kalli inda INNA TA RASULU datake kwance tana baccin ta cikin kwanciyar hankali,ta rafka wani irin tagumi hannu bibbiyu tana alhinin rayuwarta, Koda yaushe aikinta Kenan tashi sassafe tatafi wajan sana'ah,kuma Koda wasa Inna bata taimaka mata da aiki ko tsinke bazata dauke mata acikin ayyukan datake ba.
Tasaki ajiyar zuciya tana girgiza kanta cikin alhinin MATAR ABBAN NATA,yanda ta girgiza kan nata ne yayi sanadiyar kuncewar dogon gashinta harya sauko yazubo mata zuwa gadon bayanta, ahankali tasaka hannu ta tattare dogon gashin nata me mutuqar santsi, sannan tajuya ta nemi d'an kwalin rigar tata wanda yayi gefensa saboda dad'in bacci, ta daure kanta tafuto daga cikin gidan sauron datake ciki, kai tsaye bandaki ta shiga ta tsaftace jikinta kasancewar tana hutun sallah.
Tsakar gidan su ta futo wanda yake cikeda rairayin qasa ta zubawa dan qaramin tsakar gidan nasu ido tana kallo tana tunanin da wanne aiki zata fara?
Fara ce tas! cikakkiyar bafulatar qasar Mali, farar fuskar ta tana d'aukeda manyan idanuwa,qwayar idonta ruwan toka ne,tanada d'an qaramin baki siriri,ko kad'an batada qiba, Siririya ce kamar ka hureta tafad'i,abinda yakeda auki ajikinta shine hips,tanada bajajjan hips Allah yabata daidai gwargwado,yayinda nashanunta suka kasance madedeta kuma a tsaye car kamar zasu tsonewa mutum ido.
Allah yayi mata baiwar zaqin murya mai daukar hankali,muryarta tanada zaqi sosai musanman idan tana rera karatun Alqur'ani, abinda take mutuqar so arayuwa shine karatun Alqur'ani, ta qulla qawance dashi kullum tana karanta shi a fili ko a zuci,bata wasa da hadda akoda yaushe.
Wanke-wanke tafara yi, sannan tayi sauri ta share gidan nasu tas,ta dauki niqan wake tafice tabar gidan,kai tsaye gidan da'ake musu niqa tawuce,matar ta niqa mata waken sannan tadawo gida tasake shiryawa ta dauki abinda zata dauka tayi shirin ficewa qofar gida inda suke sana'ar soya qosai, har zuwa wannan lokacin Inna tana bacci bata tashi ba.
Idan akwai mutanan da ake kira expert to wannan yarinyar tana cikinsu,domin kuwa yanda take soya qosan kadai zai tabbatar Maka da cewa 'yar na gada ce ba 'yar na koya ba,kan kace me, samari da yara da masu abun hawa suka yanyameta suna siya, saide dayawa daga cikin samarin ba qosan ne yakawo su ba,yarinyar datake qosan ce takawo su wajan.(🤫)
Cikin qanqanin lokaci tagama saida wa ta kashe wutar ta tattaro kayanta tayi gida,tana zuwa gida taga Inna a zaune cikin 'yar qaramar rumfar dake tsakar gidan nasu, kai tsaye wajanda suke wanke-wanke ta wuce ta wanke kwanukan data dawo dasu,tasake diban ruwa mai yawa taje ta zubawa shukar na'a na'arta, kasancewar kullum cikin karatun Alqur'ani take hakan yasa ta nemi na'a na'a ta shuka,kullum zata siyo shayi ruwan bunu tasaka aciki tasha,kokuma ta dafa shayin da Na'a-Na'ar,duk lokacin datasha tana ganin amfanin ta sosai wajan daidaita mata fitar da makarujul huruf.
Saida tagama jiqe na'a na'ar da ruwa sannan ta qarasa wajanda Inna take tace" Inna ga kud'in"
Wadda aka kira da Inna tasa hannu ta kar6i kudin ta qirga ko sannu batayi mataba. Daga nata 6angaren itama bokiti ta dauka ta wuce ta debo ruwa tanaso tasake watsa ruwa kasancewar tanajin zafi,uwa uba kuma dama daga gaban wuta take,jikinta banda gumi babu abinda yake.
Inna ta kalleta tana daga cikin rumfa sannan tace "HAFEEZA zoki dauki wayata ki kamomin lambar Mariya ki kiramin ita"
Abinda take tabari, tazo ta dauki wayar tata,takira taji ba Kati, ta kalleta cikin zazzaqar muryar ta tace"Inna bakida kati yaqare"
"Flashing zaki mata" cewar Inna.
Sake gwada kiran tayi akaro na biyu sannan tace"bazai fita ba, nima kuma wayata ba Kati dana kira miki ita"
"saurayin naki be saka miki Kati ba?"
Cikin sanyin hali Hafeeza tace"besan banida kati ba Inna"
Wadda aka kira da Inna ta numfasa tareda girgiza kanta sannan tace"oh ni Aminatu,narasa wacce irin sokuwar yarinya ce ke Hafeeza,kwata-kwata baki iya dabarar kar6ar kud'in samari ba,irin haka ai saiki masa flashing idan yakiraki sai kice karkaji shiru yau ban kiraka ba banida kati ne shiyasa"(😲)
Kafin Hafeeza tayi magana Mariya tashigo gidan, mace me kimanin shekaru arba'in da wani abu,ganin mariya ta shigo gidan hakan yasa Hafeeza tayi hamdala aranta tayi wuf tashige bandaki domin watsa ruwa. Tana shiga cikin bandakin nasu ta zare kayan jikinta gaba daya, lokaci d'aya farar fatar jikinta ta bayyana,cikin nutsuwa tafara wankan ta harta gama wanke jikinta gaba d'aya,tazo wanke fuskarta tasaka sabulu a fuskar tana wanke wa kamar wasa taji qaran abu asama, cikin sauri tafara qoqarin wanke idonta da farin ruwa,saide kafin tagama wanke fuskar wata uwar gafiya tafad'o jikin Hafeeza kasancewar langa langan da'aka rufe saman bandakin dashi duka yamutu, rana ta riga ta kashe shi, hakan yasa gafiyar tasamu damar fadowa jikinta, Hafeeza tana had'a ido da wannan gafiya tasaki wani uban ihu tana Salati, aguje ta fizgi zanin wankan ta tafuto daga bandakin fuskarta duk kumfa, yayinda rabin nonuwan ta suke awaje kasancewar daurin zanin bana nutsuwa bane.
A tsakar gida tayi turus tana maida numfashi, yayinda fatar jikinta inda gafiyar ta fad'o wajan ya qwarzane yafara jini kad'an saboda 'yan yatsun gafiyar ya karceta awajan.
Mariya ta kalleta tace"Hafeeza lafiya kike ihu ke kadai?"
Hafeeza bata iya bata amsa ba,sai numfashi datake maidawa jikinta banda rawar tsoro babu abinda yake.
Inna Aminatu ta kalleta taga yanda tabar nonuwan nata awaje, kuma ana tambayarta tayi shiru,baqin ciki ya kamata, tasaki ajiyar zuciya tace"wannan Nono de angama nunawa duniya,saura za'a kai gidan miji"
Hafeeza tanajin wannan furucin ta runtse idonta, tadawo cikin hayyacinta tasaka hannu ta gyara daurin zaninta,tasan cewa dede gwargwado tana yiwa Inna biyaiya,batasan meyake damunta ba tsufa ne kokuma haka nan take mata wasu abubuwan?tarasa meyasa wani lokacin furucin arziqi baya futowa daga bakin innar tata kuma MATAR ABBANTA.
(Fan's ya kwana biyu zance ko shekara da watanni🤔🫣)
littafin kudine, Complete document 1k
8621296018
Amina Muhammad
Fcmb
Amnah El Yaqoub✍🏻
[5/21, 12:38 PM] El Yaqoub: 💘MATAR ABBANA💘
(Luv Story)
Writing By Amnah El Yaqoub
Kuyi following WhatsApp Channel dina domin samun sababbin update👇🏻
https://whatsapp.com/channel/0029VbBR7naJ93wTuOypQV45
2
Mariya tayi murmushi tana duban Inna sannan tace"haba Ta Rasulu, wanne irin saura kuma? gani aiba ta6awa bane"(🙈)
Bata saurari amsar Inna ba tajuya ta kalli Hafeeza sannan tace"Hafeeza meyafaru haka?"
Saida tagama maida numfashi sannan tace"Inna Mariya Gafiya ce tafad'o jikina ina wanka"
Mariya tace"Subhanallah, Allah Yakiyaye gaba,qarasa Randa ki wanke fuskarki ki kawomin ruwa abuta"
Kanta da gyada babu musu ta wuce ta Debi ruwa abuta ta wanke kyakykywar fuskarta kasancewar dama tagama wankan,sannan ta debowa Inna Mariya wani ruwan takawo mata.
Inna Mariya ta kar6a tace"nagode,Allah yabaki miji nagari, mijin kirki muje gidanki musha kunun tsamiya"
Ta Rasulu kalli Mariya tace"kunun tsamiya kuma ina kanta? kiyi mata fatan wani kunun de"
Inna Mariya tayi murmushi taqarasa alwala tatada kabbarar sallar Walaha, kasancewar tsohon ciki gareta hakan yasa da qyar take iya yin sallar,bayan ta idar Ta Rasulu takalleta tace"Mariya Kirage wannan haihuwar wallahi,inba hakaba mahaifarki fashewa zatayi"
Inna Mariya ta cire Mayafin jikinta tana firfita dashi sannan tace"shikkenan ma idan ta fashe nahuta,Innar Hafeeza bazaki gane Jarabar Baban Mas'uda ba,bashida aiki sai Jaraba kullum ana abu d'aya, har so nake yaqara aure nima inhuta Amarya kuma saitaci gaba da haifa"
Ta Rasulu ta jinjina kanta sannan tasaki numfashi tace"gani yayi kina haifar su lafiya-lafiya shiyasa baya d'aga miki qafa,kekuma dakika fishi Jaraba Mariya kin kai shekara Arba'in da biyar amma kullum idan ya debo jiki yazo saiki bud'e masa qafa"(🙊)
Mariya tayi murmushi tana d'an leqen cikin daki inda Hafeeza take tana fatan ace Allah yasa de yarinyar bata fahimci akan me suke magana ba.(🙈)
Ta Rasulu kuwa ko akanta, saboda tariga tasan halin Hafeeza bazata kasa kunne tanajin zancen su ba, ta kalli Mariya tace"Haka wasu mata suke fama anan layin mu,duk shekara saisun haihu itada kishiyar ta, mijin baya daga musu qafa saboda tsabar tsohuwar jaraba,acikin su biyun d'aya mata take haifa duk shekara, d'ayar kuma maza take haifa, kusan kullum sai sunyi fada suna yiwa juna gori, ita me haifar mata so take ta haifi namiji Koda sau daya ne,itama me haifar maza so take ta haifi yar budurwa, ita me haifar mazan tsabar yanda takeso ta haifi mace tana haihuwa tun kafin mabiyya ta futo take leqawa tace mena haifa? Amma kullum amsar itace namiji ne ba mace ba"
Mariya tasaki wata irin ajiyar zuciya tace"tabdi kaji jaruma,ni ai bana tambaya kuma bana dubawa kodan mix nake maza da mata? wahala ma bata bari na induba"
Ta Rasulu ta d'aga murya tace"Hafeeza futo kici abinci,banason mutum ya zauna da yunwa"
Hafeeza datake zaune adaki idonta a lumshe tana tulawar karatun Alqur'ani ko zuciyar ta zatayi sanyi akan furucin Inna na cewa tagama nunawa duniya nononta, saura zata kai gidan miji,maganar har yanzu taqi barin zuciyar ta, hakan yasa ta nutsu take tulawar karatun Alqur'ani har saida takai ayar datake karantawa sannan tace"Bazanci ba Azumi nake"(😂)
Cikin d'aga murya Ta Rasulu tace"kina al'ada ni zaki cewa azumi kike? kar Allah yasa kici, ni har a fadamin azumi? acikin tsakiyar azumi aka haifi mahaifina,Asalin Sunana shine Aminatu d'an Azumi,kara ce tasa ake kirana Aminatu Mamman"
Mariya tace"Ta Rasulu ai kina qoqari ma,tunda kishiyarki ta mutu tabar miki Hafeeza kike fama,Shima mijin naku rai yazo yayi halinsa, inda take birgeni de yanda ta dage take muku sana'ah, gashi kamar tana fita da sunan Allah tana fara suyar qosai sai kiga ansiye kodan mahaddaciyar Al-Qur'ani ce inajin akwai karatun datake na kiran kasuwa kafin tafice daga gida"(😂)
Inna tace"yo in bamuyi sana'ah ba me zamuci Mariya? sana'ah ai tazame mana dole"
*** *** ***
Hajiya Kaka tayi shiru ta zubawa abincin dake gabanta ido ta gagaraci,ko kad'an hankalinta baya jikinta,tariga tayi nisa wajan tunani,idan bata manta ba yau Babban jikanta mafi soyuwa acikin zuciyar ta yacika shekaru ashirin da takwas,babu abinda ya rasa na rayuwa, amma koda wasa babu tunanin aure agabansa,abun yana mutuqar damunta musanman idan tatuno shekarun baya kafin yazama cikakken saurayi yanda yake fama da matsala ta tsananin sha'awa.
Husna ta kalleta tace"Kaka bakici abinci ba"
Cikin damuwa Hajiya Kaka tasaki ajiyar zuciya,fuskarta cikeda tsantsar damuwa tace"qyaleni Husna bata abinci nake ba, ta rashin auren yayanku nake"
Hassana dake zaune agefe ta kalleta tace"Kaka da kinyi haquri da batun auren nan, shi Yaya miskiline, ko yanmatan layin nan baya kulawa, bare su sasanta da wata ayi maganar aure"
Kaka ta kalli Hassana tace"ke rabu dashi da Allah, miskilancin banza, to ai irinsu sune 'yan'iskan"(😂)
Husna dake kusa da Kaka tasaki murmushi.
Hajiya Kaka tabawa Hassana wayarta tace"ungo kiramin shi awaya"
Hassana taduba number Yayansu ta doka masa kira, saida ya dauka sannan tabawa Kaka wayar.
Hajiya Kaka ta kara waya a kunnanta tace"Hafeezu ya aiki?"
Cikin damuwa ya runtse idonsa,bayason wannan Hafeezun datake fada,gaba daya lalata masa suna take,saida ya saita kansa kafin Ataqaice yace"Alhamdulillah"
Hajiya Kaka tace"Hafeezu ita Rayuwa dakake gani,bahaka ake tafiyar da'ita ba,tsakani da Allah shekara da shekaru Hafeezu kana zaune babu aure,ka girma harka riqa kana zaune a tuzuru,shine nace Hassana ta kiramin kai nace konaje nayi magana ne a had'a ka da yarinyar nan Hafsa 'yar wajan Alhaji Qani nakan layin mu?"
Ajiya zuciya yasaki daga cikin wayar,tsawon lokaci ya dauka batare dayayi magana ba harta cire rai zaiyi magana sannan yabude baki cikin tsantsar aji da tsananin miskilanci yafara magana a rarrabe kamar bayaso "Koda yaushe Kaka...,bakida aiki sai zancen had'a aure....,kina daga zaune,kin zama me dalilin aure" (😂)
Cikin sauri Hajiya Kaka tace"yaushe nata6a had'a aure Hafeezu? yaushe akai haka? banta6a jiba"
Tana fada masa haka ta dauke wayar daga kan kunnanta ta miqawa Hassana tace"ungo kashemin wayata"
Hassana ta kalli wayar sannan ta kalli Hajiya Kaka tace"Kaka yana magana fa"
Cikin 6acin rai Hajiya Kaka tace"Kashemin waya nace!!"
Babu yanda ta'iya dan dole ta kashe wayar.
Kaka ta saki tsaki tace" abinda yasa kukaga na damu da aurensa bafa komai bane, sonake muma mu dinga ganin qananun yara acikin gidanmu, bamuda kowa, 'yar'uwa ta qwalli d'aya data ragemin ta mutu,Zaman lafiya suke itada kishiyarta na innaa-naha, da kishiyar tata ta mutu damuwa tasa ta susuce daga baya itama ta mutu, zamansu lafiya kalau duk inda zasuje suna tare, ko girki daya zatayi to tare sukeyi kokuma d'aya tayiwa d'aya,komai nasu tare sukeyi, to yanzu shi ban'isa nayi masa maganar aure ba saiya fututtuke fuska dama shi fuska kullum a d'aure, kuma tausayi yake bani wallahi, wannan rashin auren nasa yasa duk ya sauya, gaba d'aya a firgice yake"(😂)
*** *** ***
Kamar kullum yauma sassafe tatashi takama aikin da tariga tasan cewa nata ne,kasancewar bata kwanta da wuri ba sakamakon hadda datayi daren jiya, hakan yasa idonta yake cikeda bacci, aikin take amma tanayi tana Hamma tana murza idonta dake cikeda jin bacci,yau Inna Ta Rasulu idonta biyu, tana ganin duk yanda Hafeeza take ayyukan ta cikin sanyin jiki saboda rashin samun isasshan bacci yasa gaba daya kasala ta lullu6eta, ganin gari yana sake wayewa ko niqan wake bata kai musu ba hakan yasa Inna ta miqe da azama ta nufi Hafeeza tana fad'in "ke da Allah bani wankin waken nan na qarasa, kina abu kamar sauna"
Tafadi hakan tana qoqarin meqa hannu zata kar6i robar da waken yake ciki, tana sako qafarta santsin ruwan da Hafeeza ta zubar awajan ya kwashe ta saiji kake timm....,Inna Ta