Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kamar takashe lauwali domin bata sonsa, mahaifin lawwali abokin mahaifin ta ne don haka cikin kankanin lokaci akayi bikin. Ranar da a'akai hajara dan madaidaicin gidanta..(domin lawwali yanada sana'arsa) hanashi shiga dakinta tai tarufe kofa sai a soro yakwana ... Auren hajara nada wata hudu tasamu ciki , karkaga bala'i gun hajara "ita bazata haihu da talaka matsiyaciba" ..garaba dai kala2 bawanda bataiba tasha yunkurin zubda cikin amma Allah baiyiba saida ta haifeshi. Ranar suna yaro yaci sunan "Muhammed sani* anace dashi *Arman wanda Haj. Suwaiba ta nada nasa don (kasan abinka da 'yan birni wayayyu) . Haj. Suwaiba shiru2 har shekara biyar ba ciki ba labarinsa, yayinda ta danne zuciyar mijin da asiri don haka ko damuwa bayayi saidai danginsa suma hasukayi suka hakura. Ashekara na shidane Allah yabata ciki karkuga tarairaya da kulawa agun Alh usman dayake bata. Ranar da Hajiya suwaiba tahaihu Alh.usman kamar zai cinyeta don kauna da i'ta da abinda ta haifa, ranar suna jaririya taci suna *Zubaida* anyi shagali kuma anyi barin kudi ranar. *Zubaida* nada shekara hudu aka sata nursery yayinda *fauxiyya* (yarinyar da hajara ta haifa bayan haihuwar arman da shekaru hudu) keda shekaru shidda a duniya shikuma arman nada shekaru goma. Lawwali yana cikin tashin hankali da masifa domin kuwa masifar yau daban tagobe daban da hajara ke masa, ahaka harya kamuda hawan jini da ciwon zuciya kullum yana kwance gida ba lpy gaya bawata kyakkyawar kulawa .. Ana cikin hakane Allah yamai rasuwa saida muce Allah yaji kanshi. Hajara kam abun bai dametaba ko a jikinta don daman kamar kaya yazame mata,, yanzu kwa tayada kwallon mangoro tahuta da kud'a. Bayan tagama takabane tashirya ziyara ta musamman zata kaima kawarta, aminiyar ta *Haj Suwaiba* a kano. Bakaramin mamaki taiba ganin irin daular da kawarta ke ciki. "Uuhm!...rayuwa kenan! Yanzu suwaiba kece cikin wannan daular!?." Farr suwaiba tayi "hmm kedai bari ..duniya kam nasameta." "To sumu kuma haka zamu kare da zani daya kenan." "Aa, kikwantar da hankalin ki, tunda yanzu bakida aure kwai abinyu." Zabura hajara tayi tamatso daf ta i'ta "ayya menene fada min." "Akwai wani abokin Alh., sunanshi *Alh Sulaiman Goni*, yanada mata daya kuma bai taba haihuwaba. Zakije gidan a matayin naiman taimako su taimaka subaki aiki koda share2 ne, idan anyi sa'a sunbaki daganan kuma saimusan abinyi." Wani tsallen farinciki hajara tayi tarungume kawarta hards dan hawayenta "ngde kawata, ngde ngde..Allah yabarman ke." *👄hαвíєвαh luv👄* [3/26, 1:04 PM] 👄hαвєвαh luv👄: *💝KARUWA CE💝.....57/58* _Writing by_ *👄Habieba Luv👄* _Editing by_ *💅Sadnaf💅* 💝💝💝💝💝💝💝💝💝 A gidan haj suwaiba hajara ta kwana, sakamakon mijin bainan yaje Australia wani aiki. Washe gari sassafe suwaiba ta tadata tamata kwatancen gidan alh Sulaiman Goni.. 'Ya'yanta kwa ta d'iba kagansu kamar almajire suka tafi. Dai2 anwangale get din gidan hajara ta karoso tazo shiga . dakatar da i'ta mai gadin yayi yahana shiga, taburewa hajara tace saita shiga. Hayaniyarsu ne yajawo hankalin alh yace mai gadin ya barta . tana isa gaban alh tafashe da kuka tashiga baahi labarin karya da gaskiya. "Alh don Allah katai makamin koda aikin share share ne kabani." Sosea tausayinta yakamashi coz shi mutumne mai tausai. Iso yamata harcikin falon Haj Fatima yanuna maguri tazauna yaran suka zauna gefen ta. Ciki yashiga yakira Haj Fatima suka fito tare. Tunda Haj Fatima suka hada i'do da hajara gabanta yay wani mummunan bugawa, hakanan taji bata mataba. Har kasa hajara tasauka ta gaida Haj Fatima ta amsa adan sake..kamar yadda hajara tafadama alh haka shima tashaidawa Haj Fatima,, ita taji tausayinta sosea ko dan marayun yaran dake gurinta. "To Hajiya shine nayanke shawarar zaabata aiki girki, inyasa sai abata wancan dakin." Yay nuni dawani daki dake gefen store. "Ba laifi hakan yayi..Allah yasa alkhairi zamanmu." "Amin." Hajara harda dan kukanta tana godiya. Fita alh yayi yatafi office. Haka rayuwa taci gaba da tafiya suwaiba sa hajara kullum suna kam magani don suga sunjawo hankalin alh Sulaiman. Wata rana Hajiya Fatima tafita unguwa, alh yadawo da rana cin abinci..kwalliya sosea hajara tayi tabuga dauri tashafa turaren da boka yabata tahada abinci takaima alh. Yana zauna a garden kan wani lallausan rug yayi matashin kai da wani haddaden tropillow .. Tundaga nesa yake kallonta ko kiftawa babu, lokaci daya wani tunani yazo ransa. Dasallama tashiga gurin ta ijeye tryn tayi saving nashi tatashi tafi. Tun daga ranar alh yafata jin yana son aurenta, suma kuwa basu tsayaba cigaba suke da aikinsu. Bayan wata daya, alhaji Sulaiman da kansa yasamu hajara yafada mata abinda ke ranshi, shawara tace zatayi yabata lokaci. Aminiyarta takaima maganar sukayi shawarwarinsu takoma.. Wasa2 hajara da alh soyayya suke a boye cikin gida, maganar aure ya kankama yabata sadakinta ranar jumaa aka daura aure. Sai ranar auren Haj Fatima taji labarin. Tayi kuka harta godema Allah . Washe gari da safe har karfe takwas Haj Fatima taji shiru ba alaman breakfast, dakanta taje dakin hajara amma bata isketaba sai yaranta dasuke bacci.. Fita tayi taje ta daura break. Karfe goma dai2 saiga alh da amarya sun jero suna nufo dining, tsananin mamaki yakama Haj Fatima.. "Wannan wani irin cin amana ne." Alh gabatar da hajara yayi wa Haj Fatima.. Bata i'ya cewa komai ba haka bataci wani abun kirkiba tatashi takoma bedroom nata. Tundaga lokacin komai nagidan ya canza hajara itace tagaban gashi komai i'ta, watanta biyu tasamu ciki karkaga farinciki agun Alh ..lokaci daya Haj Fatima tazama bora..komai sai Hajiya hajara don wata daya da aure suka tafi maka itada mijinta. Su arman kwa sunzama yan gida shida fauxy sai abinda sukaga dama suke. Ranar da hajara ta haihu karkuga murna gurin alh Sulaiman kamar zai cinye jaririyar, ranar suna yarinya taci suna *Farida* su hajara ankara kame gida sai yadda sukayi dashi. *Zubaida*, yarinyar Haj suwaiba, takasance mai harka da kawaye masu rawar kai, gasude yara don awannan lokacin suna js1 amma basuda labari sai na aure.. Tun daga nan aure tashiga ran zubaida batada wani buri daya wuce tana kammala secondary tayi aure. Farida nada shara biyar lokaci daya Allah yabama Haj Fatima ciki..zokafa bakin ciki gun hajara, ba yadda batayi da bokaye da malamai akan cikin yazube amma Allah baiyiba. Ranar wata jumaa Haj Fatima tafara nakuda, alh Sulaiman yana kaita asibiti ta haihu ta haifi yarinyarta mace kyakkyawa mai kama da laraba. Lokaci daya alh Sulaiman yaji kaunar yarinyar yashigesa, yaji duk duniya ba abinda yakeso sama da i'ta. Ranar suna jaririya taci suna *FATIMA ZAHRA* anyi shagali naira tayi kuka. Tun lokacin da hajara ta fahinci akwai so mai tsanani tsakanin alh Sulaiman da zahra ta kudiri niyyar rabasu. Zarah yarinyar tataso da wani kalar da bi'ar bayyan tsaraicinta, batada kunya kwata2 batajin kunya fidda tsaraicin ..shiga irinta yahudawa shine dabiarta ..akwaita da tsiwa bata barin ta kwana ..ba yadda mahaifiyar ta batayi akan ganin ta sanza halayyarta amma abun ya faska , tun abun baya damunta harya fara damunta coz yarinyar girma takeyi abin nakara shiga ranta. Lokacin da zarah tagama primary tashiga secondary tayi wani Abu waishi ruruwan samari..samari kala2 zaka gani tareda zahra, tun daga nan akefara zargidan da bin maza . abin yana matukar kona ran mahaifiyarta, yanzu abbanta baiwani damu da i'taba don hajara ta gama samishi tsanarta . Hantarar da alh Sulaiman yakema Haj Fatima yasa takamu da hawan jini, yauda lpy gobe ba lpy. Wata rana zarah tadawo daga unguwa wani saurayi yasauke a mota carab akan idon mama..wanda haka duk yan gidan suke kiranta. Falon alh tatafi tasanar dashi cewa taga zahra da wani saurayi suna iskanci a mota. Afusace yafito yazo yasamesu zaune falo ruwan masifa yafara saikema Haj Fatima da zahra hakan ya taddasa ciwonta yatashi tafadi, a gigice zahra tayo kanta tana jijjigata tana kuka. Kwananta biyu a asibiti Allah yay mata cikawa, bakaramin kuka zahra tashaba don mamarta kadai ke sonta gidan. Bayadda yan uwan Haj Fatima basuyiba akan abasu zahra amma abbanta yaki haka suka hakura suka barta. Arman tatashi cikin gata a gun alh Sulaiman, don kamar dancikinsa haka yake kallon sa. Arman yatashi da budadden idon akwaisa da son mata suma kuma suna biyemasa coz yaron akwai kudi. Lokacin da zubaida takare secondary school tasamu momynta da maganar aure takeso ita bazata tafi jamia ba sai intayi aure. Koda Momy tasamu daddy zubaida da maganar fir yaki wai dole satagama jamia. Itama taburewa tayi tace sai aure, dagyar da dabara sukaja hankalinta ta hakura tace zatayi..amma ita kadai tasan abinda take shiryawa!. Rayuwat zahra tana cikin kunci bata samun farin ciki, abbanta baya nuna damuwa da i'ta, ga hantarar da ake mata gun yan gidansu, ga maganar duniya da kallon da ake mata Wanda azahirance ba haka yakeba. Agun mutum daya take samun farinciki gurin *Haj Aisha* wato mami..i'ta kadai tarike amana ba yadda batayi da abban zahra akan yabata itaba bayan rasuwar maman ta amma taki. *Yazid* yazama matashin saurayi mai jini a jika, wayayye dan boko.. Maiji da kansa..ga kyau..yagama karatunshi a London yadawo nig. Yayinda yacigaba da kulada kafanonin mahaifinshi..(wanda Allah yay masa rasuwa tunshekaru biyar dasuka wuce) Yazid ba abinda yatsana kamar zahra don ko gidansu taje ranar yini zaiyi a daki kokuma yabar gidan..haka i'tama ba kaunar kallonsa takeba. Haka rayuwa taci gaba da tafiya yayinda zubaida tasa rawuwarta cikin kazanta coz batada wani eaki daya wuce bin maza.... Wannan kenan *Cigaban labari...* *👄Habiebah Luv👄* [3/27, 8:07 PM] 👄hαвєвαh luv👄: *💝KARUWA CE💝....59/60* _wrítíng вч_ *👄hαвíєвαh luv👄* _єdítíng вч_ *💅ѕαdnαf💅* 💝💝💝💝💝💝💝💝💝 *Cigaban labarin.......* *Y* usuf suna fita baizarce da zahra ko i'naba sai *HB SPECIALIS HOSPITAL*, dama already yama frnd dinshi Dr Idriss magana.. Ba b'ata lokaci wata babbar likita *Aunty yagana* ta duba zahra sosea ta tausaya mata don sai anyi mata dinki, cikin 1h aka gama mata dressing tasamu bacci. magunguna aka rubuta Yusuf dakanshi yafita pharmacy yasawo. "Yanzu Dr bazai yiyu muyi tafiyanba kenan? Dole saita kwana?." "Gaskiya saita kwana, coz kasan dinki karamin mistake mutum yayi yakan i'ya warewa..so saita kwana muga yanda abin zaiyi zuwa gaben." Iska mai zafi Yusuf ya furzar,,"OK..alright.. Badanuwa..Allah yakaimu." Abangaren yazid ko ranar bai i'ya tsinana komai ba, hatta masjid bai'ia zuwaba sai agida yarinka salla yana addua yana kuka shabe2 harda majina, i'donsa duk sun kumbura haka fuskarsa daka ganshi kasan yana cikin mawuyacin hali, gashi soyake yaji gidan mami ko zaid'anji sanyi a ransa amma baisan dawani i'do zai kalleta ba. Yana zaune kan praying mat ya gabatar da sallar isha kenan yajiyo buge 2 a dakin da zuby ke ciki, saida yay adduoinsa da tasbihai kafin yatashi cikin bacin rea yabude yashiga. Dakin bakinkirin kamar ba'a hallici haske ciki ba, torchlight din wayarsa ya kunna ya dalle mata ido. Zuby gaba daya tafita hayyacinta..fuskanta dukkya kunbura yay jaa ga fuskan shike da dry tears bakinta a rufe da bandage sai sure2 takeyi. Yazid yana karasawa gurin ya danko gashin kanta yad'ago fuskanta hadi da saukemata wani lafiyayyen mari..saida tashid'e takusa suma. fizge bandage din bakinta yayi yadaka mata tsawa "dan boruobanki menene?." Jiki na bari muryanta na rawa tace "wllh yunwa... nakeji." "Don uwarki ubanki yakawo abinci ne?." Girgiza kai tayi tana hawaye " ni sa'an ubanki ko sa'an uwarki dazakimin nodding, oya open ur mouth n telk...dan kan uwarki." "Don Allah.. Kayi hakuri,,...wllh baikawoba..amma kataimaka min plss..ko kamaidani gidanm.." Wani Marin yakara sauke mata "ke a jakantarki kina tunanin zakici bulus ne?, kinzo kin lalata min rayuwa ,kin rabani da kowa nawa kinrabani da farin ciki na *matata* tareda mahaifiyata ..kin kawomin sauran wasu katin banza... " shiru yayi yahad'e kansa da bango yanajin zuciyarshi kamar zata kone don zafin datake masa. Yafi minta ashirin a haka kafin yafita daga dakin yarufo kofar. Wani kuka maicin rai zuby tafashe dashi tana regretting rayuwanta na baya.. Yazid yana fita yashiga mota yatafi wani can unguwar talakawa. wani almajiri yagani yafito daga wani gida hanunshi rike da roba... Parking yayi gefe yafito yanufi gun yaro. "Almajiri.." Alama yay mishi da hanu yazo, bamusu yaron yazo gurin yazid. "Mene cikin robarnan?." "Abinci ne ciki.." Yafada yana bude robar.. baya yazid yay yana toshe hanci "meye wanna?" Yafada yana pointing robar.. "Tuwone..miyan kuka." "Plss..rufeshi." Rufewa yayi yatsaya yana kollon yazid.. "Kaga , kabani wannan tuwon inbaka dubu daya kasai abinci.." Tunkafin yazid yagama fada yaron yace "eh..wllh nayarda." Yafada yana mika mishi robar. Kin amsa yazid yayi sai yaron yanaimo leda awani provision shop yasa aciki kana yakarba yabashi kudin yatafi. Restaurant yawuce yay takeaway kafin yatafi gida. Afalon ya ijiye dayan ledan dayan kuma yashiga dakin da zuby take ciki. A inda yabarta haka ya sameta, kujera ya jawo yazauna gabanta yaciro abincin ledan ya ijiye gabanta tare budewa .. .wani uban warin daddawane tabugi hanci zuby tai saurin kauda kanta gefe. "Kee maye kakayi hakan?." "Plss don Allah bana i'yacin wannan , indai a nine wllh nakoshi." "Toda kina tunanin a ubanki nakawowa?." Nandai shiru tayi batace komai ba .. "Oya bude baki.." Kin budewa tayi ganin zai zabga mata mari yasa tabude ya turamata loma baki. Da kyar ta'iya hadiyewa tana hawaye.."wllh inbaki hadiye wannan kukanba sainashi uwarki." Yay maganar ba'alamar wasa ..dif tahad'iye kukan tanaci kamar tayi amai. Yazid kwa cikin mugunta yake kara dannamata loma, saida yaga tana kokarin amai sannan ya kyaleta. "Zanyi salla.." Tafada cikin sanyi murya. Mugun kallo ya watsa mata "munafika kawai..zan kunceki kiyi salla, amma kina idawa zan maidaki daure.." "To" Kunceta yayi yafita tareda sama kofar key. Abangaren Hajiya Momy kuwa tana komawa gida tawuce bedroom nata tasaki wani dan marayan kuka.."nashiga ukuna halina yabi 'yata ,yaa Allah kayafemana Allah natuba...kuka tarinkayi tana surutai masu maana da maras, ranar ko ruwa batasa bakintaba lokaci kankani harta fad'a tafita hayya cinta. Damuwanta daya Daddy n zuby batasan how can explain to him ba, meyema zata ce masa 'yarsa *KARUWA CE!* innalillahiwainnailaihirrajiun. Haka shima yazid ko abincin daya siya restaurant bai'ya ciba, kwana yayi yana sallah yana rokon Allah daya sanyaya zuciyar matarshi da mami don su tausaya mai. **** Washe gari... Karfe shida Yusuf yad'auki hanyar Maiduguri bayan sallama da akabasu don yanzu dasauki don ko zafinma kadan takeji. A natse Yusuf ke driven duk wani motsin zahra akan idon sa, motsi kadan ya tambayeta meke damunta.. Daga karshe dai sit ya kwantar mata takwanta bacci yay gaba da i'ta. Ba'ita ta farkaba saida sukayi shigo cikin maiduguri , tafiyan minti arbain takawosu bakin wani babban gida wanda girmansa yakusa cinye layin dukda girmansa. Horn yay maigadi yabude masa get yashiga.... A 1get yay parking natse yafito yabude ma zahra kofa, a hankali ta saukar da beautiful white leg dinta tafito . a hankali suke takawa saboda kafar zahra, dayan get din akabude musu suka shiga . suna zaune cikin wata haddadiyar rumfa akan rug gakuma fruit gefe cikin wani madaidaicin basket... Da sauri aunty tataso ganin Yusuf da zahra don cayayi zashi lag wani aiki. Dukansu suka taso sukayo gurinsu. Cikin mamaki aunty ke kallon zarah gaba dayanta da yadda take tafiya a bude "what's happening Yusuf!?, where did u get her? Kaida kaje lag..kafada min man." "Its long story aunty just take her in.. Kama hanunta aunty tayi suka shiga ciki su twins sukabi bayansu shikuma Yusuf yawuce part dinshi. Ganin condition din da zahra ke ciki yasa aunty direct tawuce da ita toilet ta had'a mata ruwan zafi mai gishiri tashiga gasata, sai ta tabbata tayi sannan tahada mata ruwan wanka tafito. Dakinsu su twins taje ta dauko mata normal wear da panta/ bra taje kitchen tahad'o mata lunch mai lafiya tadawo dakin. Time din zahra tafito daga wanka tana zaune kan dressing chair tana shafa lotion..k'ura mata i'do aunty tayi nakusan mimti goma harsaida tajuyo kana tadauke idonta " ga kaya nan kisa." Tafada tana mika mata .amsa tayi tasa batare da tasa bra dinba don nipple dinta tunda yazid ya tumurmushe su basubar zafiba, fant tasa tadawo gefen aunty tazauna . "ZAHRA!." Dagowa tayi takalleta batare datace komaiba "meyasa bakison bayyana min damuwarki?, ko baki daukeni kamar mahaifiyarki ba?." K'asa tayi da kanta batace komaiba. kama kanta aunty tayi tayi parking dinsa tajanyo wani karamin glass centre table ta daura abincin kai, dakanta tai feeding din zahra saida ta tabbata takoshi sannan ta kyaleta .."ki kwanta kiyi babbici don nasan kingaji, in kin tashi gawaya kikirani sai na had'a maki ruwan zafiko." "To" aje mata wayar tayi kan site drawer tajamata kofa tafito, Batafi minti gomaba bacci ya d'auke ta. Aunty bedroom dinta tatafi tazauna bakin gado tana nazarin Abubuwa dadama. Su twins suna zaune falo shiru kowa da ntunanin dayake ranshisallamar da labaran yayine duk tadawo dasu ,kaya yake shigowa dashi niki2 manyan Leda's sunfi ashirin. Yusuf ne yashigo dayan hannunsa zube cikin aljihun wandon sa dayan kuma makullin mota. "Where is aunty?." Ya tambaye su. "She's in bedroom.." "Oya go and call her." Tashi salima tayi tanufi bedroom din. Ba'adad'e ba saigata da Aunty, zama tayi kan sofa ta zubama Yusuf idonu tanajiran jin more information... "Aunty ga kayan zahra nasawa, sai kujera mata a closet wad'annan atamfofin Kuna sai akai gundinki.Kallonsa Aunty tatsayayi "Yusuf kafad'amin abinda nakeson ji man...." Dan shafa lallausan gashin kanta yayi yashiga bama aunty duk labarin abinda yafaru wanda yaji yazid yafad'a har kwana a hospital din dasukayi bai b'oyeba.. Nodding kai kawai aunty tashiga yi tareda furta " ZARAH! yama haka?, yayi kyau!." *👄hαвíєвαh luv👄* [3/28, 10:40 AM] 👄hαвєвαh luv👄: *💝KARUWA CE💝.....61/62* _Writing by_ *👄habiebah luv👄* _Editing by_ *💅Sadnaf💅* _Dis page goes to u *Official Sa'adatu D/tsafe,* may Allah guide u and Protect u... Together with u *Lainat🐒* hrt u dear ❤😍._ 💝💝💝💝💝💝💝💝💝 Yazid yakasa samun sukuni a rayuwarshi kullum yana cikin tunani, acikin kwana biyu dukya fice hankalinsa yarame yayi baki ga ciwon zuciyar dake dan tab'ashi! . yana zaune kan praying mat yagabatar da sallar asuba yajawo wayarshi yay dailing no. Din mami. Tanakan tadduma tana azkhar wayanta nagefen takawo haske alamun kira yashigo, ganin sunan only son dinnata yasa tak'i dagawa harta katse..sau biyar yana kira amma ko day'a bata dagaba , tanajin tausayin rayuwar da yazid keciki, amma dole take dannen wa don tanuna mishi kuskuren sa. Ganin taki dagawa yasa yakifa kanta da gado yasaki wani kukan huce takaici.. Saida yay mai i'sarsa yatashi yawanko fuskanshi a bathroom yadawo yazauna bakin gado yashiga wani duniyar tunanin. "Yanzu bansan taya zanfara tunkarar mami da maganar zahra ba, inje ince inaso tadayo bayan duk walakancin dana mata..innalillahiwainnailaihirrajiun.. Rire kansa dake saramasa yayi yafada gado. Zubaida tana cikin dakinta wanda dasafiya dadare duk dayane aciki don bala'in duhunsa , tana rakube angle din dakin tahada kai da gwiwa tana sharar hawaye " yaa rabbi kayafemin laifin danayi baya, Allah natuba ubangiji kayafemin kabani ikonyin wata rayuwa mai amfani..." Kukane yaci karfinta tanayi harda shashshek'a. Yazid baizo yabud'e taba yay shirinsa cikin kananan kaya yatafi gidan mami. A Maiduguri kuwa zahra ta warke tafiyanta yadawo dai2 batada wani damuwa yanzu don 'yangidan suna i'ya kokarin su ganin sun kwashe mata dukwani damuwa.. Misalin karfe shad'aya dukkan su suna zaune garden hanun zahra rikeda iPhone din da Yusuf yasai mata sai ganin pix dindasuyi jiya dasuka fita takeyi..sosea duk sunyi kyau, har mamakin kanta take cikin kwana biyu tagyaru tayi wani fresh gadan kiban datayi. "Aunty!" Zahra takira sunanta, "what's happen aunty's daughter?." "aunty nifa yaa yazid yasakeni don bazan k'ara komawa kano ba , har abadah!." Dai2 shigowar Yusuf gurin kenan "yeah kinfadi dai2, nima abinda yasa tun farko banyi wannan maganarba saboda kene, don bansan ko kinason mijinkiba.." Danturo baki gaba tayi "Allah yasauwak'e, damani tun farko bana sonshi..don yanzu kawai yasakeni bankara zama dashi." "Ehh wllh Sis harki koma, irin wannan rashin mutuncinma dayake maki , ea wllh inda nice tunfarko maba zanzauna ba.." Salma tai maganar tana bala'i kamar yanzu abin yake faruwa. Aunty dai tana jinsu batace musu kalaba. "Kinji aunty! Kifadama abba saiyama alwalansa magana!." "Naji Zahra!. " *** Yazid nashiga falon mami yazube kasa gabanta yasaki wani marayan kuka, kamar wani karamin yaro hakayake harda ajiyan zuciya. Mami ko daga kai batayi ta kalleshiba, amma a kasan ranta jitake kamar ta janyoshi jikinta ta rarrashesa. "Mami don Allah ki yafemin nasan nayi kuskure a baya amma wllh arashin sanine mami...mami kikulani kozanji dadi a raina.. Plss mami ubangijima dakansa yana yafiya.." Tashi tayi zata tafi yarike kafarta yana kara fashewa dawani kukan "free my leg yazid inbaso kake inyi mugun sabamaka ba!." "Mami.... Wani dan banzan tsawa tadaka masa bashiri yacikata, yazube gurin yana burgima. Mami shigewa bedroom dinta tayi tanaji itama kamar tarusa ihun kozataji sanyi ranta. Yafi awa biyu yana kwance Gurin yana kuka daga karshe yatashi yafita ko gani maikyau baiyi. Ikon Allah ne kadai yakai yazid gida lpy don idanuwansa rufewa sukeyi zuciyarshi namasa nauyi kamar andaura mata dutsi ga sarawan da kansa kiyi. Yana parking ko rufe motan baiba yashiga ciki kaitsaye yashige dakinsa yakwanta. Abukamar wasa yakejin zuciyarshi kamar ana mata barin wuta, sosea takemasa wani balin ciwo dabata taba yimasaba .. Rike kirjinsa yayi yana kokarin tashi amma yakasa saimawani duhu da jiri daya fara gani. Wani razanan nen ihu yasaki wanda duk gidan yadauka, dai2 nan mortar faruq ta'ida parking yafito a razane jin ihun yashiga ciki. A hankali idonsa ke rufewa harya gama rufewa ruff tareda tsayawar munfashin sa. A hargitse faruq yashigo dakin yanufi inda yahango yazid kwance yashiga kiran sunansa tareda jijjigashi , ganin abun basauki yasashi fitowa yakira maigadi suka sashi a mota sai hospital. Likitoti biyarne kan yazid, faruq dawasu colleagues dinsa..sunfi awa uku kansa suna masa eaki , dagyar suka samu numfashinsa yadawo. Fitowa dashi akayi aka kaishi dakin dabakowa..coz abun baya bukartar hayaniya. Yana kwance idonsa rufe dakaga irin baccin dayake kasan na wahalane, faruq nazaune bakin gadon kan kujera hanunsa rike da waya yana kiran layin mami. Bugu biyu tadaga tare dayin sallama "i nayini mami." "Lpy lau faruq ya aiki? Kwana biyu shiru kamar bakanan.." "Wllh mami inanan eaki yay min yawa." "Ayya to Allah yabada sa'a." "Amin" danjim yayi yarasa ta'inda zaifara fadawa mami , candai yanisa yace "am mami dama yazid ne baida lpy yana hospital dinmu...." Zumbur tamike tsaye "what yazid! Yanzufa yafita daga nan!...OK i'm coming right now." Daga haka takatse kiran. Mayafinta da handbag tadauka tafita driver yakaita. Can gefe da inda sukayi parking ta hango faruq da'alama zuwanta yake jira, yana hangota yataho shiya tama jagora har dakin da yazid yake. Sosea taji wani mogun tausayinsa yadirar mata tana ganin da laifinta ma cikin wannan damuwar daya shiga. "Mami plss have a sit .." Zama tayi still idonta nakanshi. Gyaran murya faruq yayi yafara magana a hankali yanda bazai tada yazid daga baccin dayake . "mami, kinsan abunda kedamun yazid!?." Girgaza maikai tayi batare datace komaiba "Heart attack!. Mami yazid yana dab da kamuwa da ciwon zuciya mai tsananin gaske ..mami kamata yayi kimanta da abinda yariga yafaru kija yazid jikinki hakanne zaibashi confidence na tunkarar sauran yakin dake gabanshi! Mami akwai kalubale dayawa agaban yazid akan ZAHRA! Mami yazid yakamu dason zahra, damuwar rashinta ne ya jefashi cikin wannan hali dayake ciki..plss mami kitausaya nasa, kiyafe mishi..." Mami jitake kamar tai hawaye kozataji saukin zafin da zuciyarta keyi. "Faruq, inama yazid hakane don yagane kuskuren dayayi , faruq kai kanka kasan irin son danake ma yazid, duk duniya banida kowa daya wucesa. Faruq!." Dagokai yayi yakalli mami da i'donta yacika da kwalla "faruq ciwon zuciya shiyayi agalin abban yazid, faruq banaso inrasa yazid kamar yanda narasa mahaifinsa.." Shiru tayi tasanadin hawaye dataji yana zuba mata, dasauri faruq yaciro handkerchief yatare hawayen "mami karki damu, insha Allah ba'abinda zaisameshi ..zai warke da yardar Allah. Adduarki dakuma kulawarki yake bukata." Bayan kwana uku yazid yaji dama2 aka sallamosu suka dawo gida. Kulawa ta musamman mami kebashi kamar wani jariri haka tamaidasa, bata barinshi yazauna shikadai saboda karyayi tunani inkaga mami tabar gun yazid to saidai in bacci yayi. Bayan sati daya.. Suna zaune a falo shida mami yadaura kansa bisa cinyarta tana shafa masa sumar kansa tana bashi labari sai dariya yake. "Ni yazid amaryarka ina takane?." Saida gabansa ya

Chapter 8 of 10