Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 3
zasu ciro su fado qasa "Shashasha,kamar wani wanda yaga qanin ubansa,sai nayi maganinku" Ta furta cikin fushi. Daga baya baya kadan ya ajiye tray din yana fatan kada hannuwanta yakai kansa,duk da yasan hakan zaiyi wuya,ko don wanzuwar mahaifinsu a wajen "Musaddiq......maza karbi kayan hannunsa ku wuce dakinku dukkanku" Zumbur yaron dake a zaune rakube tsakanin kujerun ya miqe. Bai jira kowa ba a cikinsu yayi hanyar dakinsu,saidai yana tafe yana dan waiwaye. A sanyaye ya sakarwa musaddiq kayan hannun nasa,yana qoqarin maida masa martanin murmushin da yaketa faman yi masa tunda sanda yayi tozali dasu "Muje ko?" Ya sake fadi yana kama hannunsa. Bai musa ba ya soma bin bayansa,don zamansa a falon yayi imanin sam bazai yiwu ba koda abba bai basu umarnin wucewa ciki ba. Zazzafa kuma tozartaccen kallo take binsu dashi,zuciyarta na mata wani irin suya,bacin rai da takeji kamar zata yi aman zuciyarta. Debe idanuwanta tayi daga kansu tana jan qaramar qwafa qasan zuciyarta,ita daidai take dasu,babu wanda ta shirya bari ya takura rayuwarta ko ya quntata ta. Duk wani motsi nata yana karance da ita,har zuwa sanda ya daidaita zamansa saman kujerar sannan ya dubeta yana kiran sunanta "Asama'u" Kallonsa kawai tayi ba tare da tace komai ba "Ga yara nan na kawosu,yara ne kuma da kin sansu bawai baqi bane a wajenki,kin kuma san basu da wata matsala ko aibu ko wani abun fada cikin unguwar nan......alqawari ne da na yiwa kaina tsakanina da ubangijina,na kuma cika alhamdulillah,ina fatan zaki tayani riqesu bisa amana ko don maraicinsu". Wani kallo takeyi masa ranta cike fal da mamaki,ta karkace tana dubanss tare da tattara abinda zata ce masa "Yanzu bayan naka yaran har yaran maqota kakeyimin kalensu?" Ta aje maganar tana jin zafi cikin ranta da zuciyarta. Tana jin ta quna bata tsoron qauri,ta soma gajiya ta kuma soma qosawa tare da debe haso hadi da tsammani na samun shimfidaddiyar rayuwar data jima tana mafarki gami da shimfidawa cewa zata samu cikin gidan..... *SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI* *_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_* *_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_* *_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_* *_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_* *ZAFAFA BIYAR* *_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_* *Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU* _TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_ _QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_ _K'ALBIM Mamuhghee_ _AJIYA A DUHU Billynabdul_ _DUNIYATA Huguma_ _Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_ *hudu 2k* *uku 1500* *Biyu 1k* *Daya 500* _YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_ *09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA* *IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA* *09033181070* *BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK* *ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171* *ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI* *AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*πŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺ 89825722 Nousaiba lawali maradi 1000cf *_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_* *_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*πŸ₯°πŸ₯° *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* *Arewabooks:Huguma* *PAGE 04* A nutse ya daga kai ya watsa mata wani irin kallo. Yau ta fara fadin hakan,amma kuma ya dade yana karantar hakan daga dukka ayyukanta da motsinta. "Nayi tunanin akwai dattako fahimta da kuma qaunar juna a tsakaninmu da har yarana sukafi qarfin kice riqonsu kikeyi,na zaci cewa kina ji a jikinki da zuciyarki kina rainkn 'ya'yan da kika haifa ne a cikinki?" Wani abu ne yazo yayi mata tsaye a wuya,ta juya kanta gefe guda tana tattaunawa da zuciyarta kan "Har abada 'ya'yan riqo ba 'ya'ya na bane,'ya'yan wasu ba zasu taba zama 'ya'yana ba.....banda qaddara me zai hadani da riqon 'ya'yan wasu?" . Idanunsa a zube fes a kanta,ya gyara zamansa sosai yana sake ci gaba da kallonta "Inaso ki cire a ranki riqo kikeyi.....ba 'ya'yana na cikina bama.......hatta yaran dana kawo yanzu,inaso ki ji a ranki Tamkar suna rayuwa ne cikin gidan mahaifinsu a gaban uwa da kuma ubansu". Dukka haqurinta ya qare,ya tuqeta ta kuma kai bango,tana jin ba zata iya ci gaba da zama tana sauraronsa ba,don haka ta miqe tsam,ta kuma gegara ta gabansa tana barin falon. Da ido ya bita har zuwa sanda take shirin bacewa ganinsa. Ya jima yana ganin alamun da suke alamta masa akwai matsaloli masu yawa cikin rayuwar su farouq,amma yayita qaryata hakan gudun kawo damuwa da matsala cikin zaman uwar wani da d'an wani wanda keda wuyar sha'ani,sai gashi a qanqanin lokaci komai yana bayyana kansa daki daki. Numfashi ya zuqa ya fesar yana rufe idanunsa,qoqari yake ya saita kansa yana tunanin hanyar da zai daidaita komai. Tray din da faruqee ya ajjiye yabi da kallo,a dawowarsa daga lagos wannan karon ya fahimci kamar ma suke yiwa kansu girki harma su hada da ita idan ta kama,babu sakewa babu walwala sam tattare dasu. Ya lura da raguwar kuzarinsu kyara da kuma hantara daga gareta,saidai dukka ya kauda kai don bai kamaci a karon farko ya fidda soyayyar yaransa kai tsaye daga zuciyarsa har haka ba,bayaso yabar wani tabo ko targaden da zai kasa gyaruwa tunda wurwuri haka. Da idanu kawai yake bin dakin da kallo sanda Faruqee yaketa masa bayani zuciya da fuskarsa cike da zumudi da farinciki. "Kayi shuru?,ka tsaya a bakin qofa,ko dakin baiyi bane na gayawa abba a qaro wasu abun?" Faruqee ya fada jikinsa yana sanyaya da yadda yaga fuskarshi. Don a yadda ya zata zayaga farinciki sosai a fuskarsa kaman kwatankwacin nasa farincikin na dawowarsa cikin gidansu,farincikin samun aboki me hankali irinsa,farincikin samun aboki da yayi daidai da shekru da hankalinsa,ba aboli irin qaninsa ba da sam.baya gane wsu abubuwan saboda sabanin mizanin hankali da fahimta dake tsakaninsu. Karon farko yayi qoqarin sake fuskarsa da kyau yana kallon faruqee. Dakin gata kuma dakin yaran gata irin wannan da shi din bai taba samun kwatankwacinsa ba ta yaya zaice baiyi masa ba?. Dukka alatu da yayi saura a dakin bashi yake daukarsa ba.......duk da qarancin shekarun daka iya dakusar da tunanin yaro a sannan......amma shi sun bawa qwaqwalwarsa damar budewa da yin tunani me nisan zango akan "Wacce irin rayuwa zasu fuskanta a matsayinsu na agola bayan su kansu tsatson gidan basu tsira ba?,mene ne makomarsu?,meye farko da kuma qarshensu?" Tarin tambayoyin da baisan ta ina zaa fara sauke masa su ba "Nayi murna farouq" Ya furta a sanyaye,sunan da shi daya yake furtashi daidai yadda yake,don har yau bai taba kiransa da faruqee ba. Yadda qanin nashi ya zuba masa idanu ya sanyashi qoqarin sakewa,ya qaraso ainihin cikin dakin kamar yadda sauran suka kai ga shigowar. Qoqarin kauda komai ya dinga yi daga zuciyarsa,yana zaune daga falon yana iya jiyo muryoyinsu sama sama,saidai har yanzun baiji tashi muryar ba. Baiyi mamaki ba,don ya sani,yadda komai nasa ya fita daban daga cikinsu,haka dabi''arsa da halayyarsa ma ta zama daban. Abincin yaja ya soma ci bawai don cin abincin yana masa dadi ko yana burgeshi ba. Tunaninsa yayi zurfin da har ba komai dake wakana cikin falon yake ganewa ba,bai taba zata ba,bai kuma taba kawowa rabuwa da rabi'atu zai iya zame masa qalubale ba sai yanzun da dukkan alamu suka fara bayyana kansu. A karon farko har yaji ya fara tuhumar kansa da kansa,tare da nacin son gano meye ainihin laifin rabi'atu ne har ta cancanci a saketa?. Baici da yawa ba ya ture,ya miqe yana irgen lokaci,sai ya juya ya fara takawa zuwa dakin yaran. Dukkansu sunyi shirin bacci amma bandashi,yana zaune gefe daya na gadon farouq,ya goye hannayensa a qirjinsa tamkar wani babba da yayi nisa cikin nazarin wani abu. Motsin abban ya sanyashi waiwayowa,da sauri ya sauke hannayensa yayi qasa da kansa yana niyyar zamowa daga saman gadon "Yi zamanka me babban suna......tunanin me ka zauna kana yi?,duk 'yan uwanka sunyi shirin kwanciya banda kai?" Farouq dake zaune tsakiyar gadon yayi hanzarin karbar maganar dama tana damunsa tun dazu "Abba yaqi ya canza kaya,na bashi kayan bacci yaqi ya saka tun dazu" Hannu kawai abban ya miqawa farouq din,sai ya saka masa kayan baccin dake gefansa. Kayan abban yabi da kallo yana jujjyasu a hannunsa,sannan ya maida dubansa zuwa jikinsu dukka su ukun dake sanye da wasu kalolin kayan. "Amma faruqee ban gaya muku a bada kayan nan ba dukansu?,ina kayan dana kawo muku wancan tafiyar da nayi?" Ya qarasa tambayar yana maida idanunsa kan saddiq qaninsa. Har wani juyawa saida cikin saddiq din yayi,saboda tunawa da yayi da kakkaifan warning din da suka samu daga wajen matar gidan akan batun. "Abba,dukka mama ta karbesu,ta kuma gargademu kada mu sake mu sanar dakai,idan ba haka ba saita tsoma kawunanmu a ruwan zafi" Ba abba kawai ba,hatta me babban sunan saida maganar ta ratsashi duk da qananun shekarunsa,amma zuwa yanzu ya dade da yiwa kansa karatun qalubalen da suke shirin fuskanta "Ruwan zafi?" Abba ya furta cikin tsananin kaduwa da mamaki,sai faruqee ya gyadawa abban kai. Maganar ta ladabtar d abba ta sanyashi samun waje ya zauna. Yana tsoron ci gaba da wannan tafiyar tasu......yana tsoron garin neman lada ya rufta ya buge d wucewa jahannama,ya debo marayun Allah da nufin basu rayuwa me inganci,muddin Mariya bata goya masa baya ba meye makomar yaran?,ya gobensu zata kasance?. Tambayoyin da suka dinga karafkiya kenan a kansa. Indai haka ne ya zama dole yayi jan ido,ya zama dole yayi wuta wuta akan gidansa da iyalinsa. Ya sauke dukka nauye nauye haqqunan da suka zama wajibi dama wadanda basu zama wajibi bs,ya zama dole to itama ta bishi yadda ya kamata. "Ba komai,tashi me babban suna ka shirya,idan kun kammala ku kashe kayan wuta gaba daya kuyi addua ku kwanta" Yayi maganar ne yana sake nazartar dakin tare da kallon guraben da ga siya ma yaran abubuwa da dama ya ajjiye saboda jin dadin Rayuwarsu a yanzu ba komai a wajen sai gurbinsu. Sai daya kammala komai daga ainihin dakinsa sannan ya zarce dakin mariya. Ta gama shirin kwanciya tsaf tayi rub da ciki tsakiyar gado tana latse latsen waya. Fuska a hade ta daga kai ta kalleshi sau daya saita dauke kan nata ta maida ga wayarta tana sake tsuke fuska. "Tashi zamuyi magana" Ya fada cikin yanayin dake tabbatar mata da gaske yake,da kuma zafinsa ya shigo. Sai da tayi kamar ba zata tashi ba sannan ta miqe ta zauna sosai tana gyara wuyan rigar baccinta tare da tsuke fuska da kyau. *SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI* *_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_* *_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_* *_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_* *_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_* *ZAFAFA BIYAR* *_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_* *Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU* _TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_ _QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_ _K'ALBIM Mamuhghee_ _AJIYA A DUHU Billynabdul_ _DUNIYATA Huguma_ _Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_ *hudu 2k* *uku 1500* *Biyu 1k* *Daya 500* _YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_ *09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA* *IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA* *09033181070* *BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK* *ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171* *ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI* *AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*πŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺ 89825722 Nousaiba lawali maradi 1000cf *_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_* *_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*πŸ₯°πŸ₯° *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* *Arewabooks:Huguma* Page 05 last free page "Asama'u" Ya kirayi sunanta da wani irin yanayi da har cikin zuciyarta ta tabbatar cewa......dukka maganar da zata gita yanzu haka daga bakinsa ,yankakkiyar magana ce wadda babu janyewa a cikinta ko kuma wani sauyi bare sassauci "Ban rabu da mariya ba don na auro wata matar tazo ta azabtar min da 'ya'ya ba,ina tsananin qaunar 'ya'yana fiye da soyayyar da nake yiwa kaina,duk soyayar da zaki gwadamin bata da alfanu rana ko kuma fa'ida a gareni muddin ba zaki so 'ya'yana ba......asama'u,na rantse da Allah,dai dai da rana guda na samu wulaqanci cin amana ko tsanantawa diyoyina bisa ganganci bawai kuskure ko ajizanci irin na dan adam ba bazan raga miki ba"..... Wani dum taji har tsakiyar kabta,batabtaba kawowa dukka maganganunsa zasu kai har wannan iyakar ba,bata tana tsammanin abun yayi zurfi haka haka ba,da ake gaya mata yana da son yara batabtaba kawowa yakai har wannan bigiren ba. Zuwa sanda zatakai qarshen tunaninta shi din ya jima da miqewa yana kallonta "Bazan fasa tafiye tafiye na wajen neman halak da neman abinda zan rufawa kaina da iyalina asiri ba......ba kuma zan kwashe diyoyina na kaisu wanin guri ba,gaki gasu nan asamau,dukkan abinda kika qudirta yi kada ki fasa koki sauya ra'ayi" Ya qarashe fadi yanajin wani irin daci saman harshensa,bai kuma dakata ya saurareta ba ya juya a nutse yana barin dakin nata. Har sanda ya bacewa ganinta bata dauke dubanta daga bakin qofar dakin ba,ta qanqance idanu tana kallon qofar tare da jin dacin kalamansa suna gauraya kowanne sashe na jikinta. A taqaice dukka bayanansa suna auna mizani da kuma adadin iya matsayinta kenan a wajensa?. Bata shigo gidansa don ta fita ba,don muhallin dame muhallin duka sunyi mata,amma kuma bata shigo bautar d'an kowa ba,hakanan bata shigo don a takata ko aci mata zarafi ba bare kuma a hanata sakewa. Shawara take buqata kawai a yanzu hala,don gaba kura ne baya sayaki,ta kula dasu ko ta barsu komai ta fanjama fanjam?,to amma fisabilillahi zai yiwu kuwa ace ta buge da bautar d'iyoyin da ba ita tayi Jigilar daukar ciki da kuma rainonsu ba?. Matsawa tayi kusa da wayar landline dake gefan gadonta,ta latsa lambobi tana fatan sashen kamfanin sadarwar ya sadata da matar data kira take mararin magana da ita. Ba'a dauki dogon lokaci ba sukayi mata hakan,saita qarasa sauke dayar qafar tata qasa tana zama sosai yadda zatafi jin dadin amayar da abinda ke cikinta. Yanayin yadda suka gaisa kadai zai gaya maka akwai shaquwa me zurfi da tsohuwar sanayya a junansu. "Ya nake jinki haka sama sama?" Daga saya bangaren ta tambayeta. Sai data aje dogon tsaki sannan ta fara magana,zuciyarta cike da wannan bacin ran da batasan ranar da zai wanke daga zuciyarta ba "Barni kawai......dukka shirina har yanzun bai tafi a yadda na jima ina tsarawa ba" "Wani abunne kuma?" Kai ta rausayar tana jin kamar ta qifta idanuwanta ta budesu ta tarar babu kowa tsakiya da gefannin rayuwarta da mijinta,daga ita saishi "Yarannan haleema......bayansu ya sake kwasomin riqon marayu,bayan wadannan din har yanzu ban gama da matsalarsu ba......" Daki daki ba tare data rage komai a abinda yake faruwa ba ta shimfida mata,sannan ta dora da fadin "Inajin kamar naje gurinsa ayita ta qare haleema,na meye zaa dinga doramin nauyin da bai zama wajibi a kaina ba?" Ajiyar zuciya haleeman ta sauke "Ashe qarya kikeyi,baki shirya zaman auren ba" Haleema ta katsi numfashinta sanda taji tana shirin sake dorawa da wata mitar "Kamar yaya?,ya zakice haka bayan kinsan komai?" Ta tambayeta tana tsuke gira tare da mamakin amsar data bata "Eh to ai dole nace haka,wani lokaci sam baki da wayo asama'u,yaransa biyu da yake mutuwar so ki gaza riqesu?,bakisan ta hanyar riqon da zaki musu bane zaki samu fiye da abinda kike hange ko hasashe daga jikinsa?" Ta qarashe maganar da sigar tambaya,tambayar data dauki dukka tunanin asama'u ta jefashi wani guri me nisa "Amma haleema,saina zama baiwar yara har hudu?" Ta yiwa haleema tambayar tana jinjina girman abun,tamkar wadda aka dorawa nauyin wanke kashinsu da fitsarinsu gami da ci dasu tsahon kowacce rana da wuni na rayuwarta "Bance haka ba,ban kuma goyi bayan hakan ba,yaransa sune dolensa,su zaki kama ki riqe,saura kuwa wannan baida hurumin tilasta miki zama dasu,idan ma baki riqesu ba bakiyi laifi ba,kedai yaransa su zama makamin zamanki a gidan,yo asama'u kona ganin ido ne ke ba zaki iya ba?.......". Dadewar da sukayi saman waya sa haleema iya adadin karatun data samu daga gareta,ta kwanta ne tana juyawa tare da tauna yadda zata dauki shawarwarin haleema tayi aiki dasu,ta yaya zata danne zuciyarta da dukka wani abu da takeji tayi yadda haleema ta kwatanta mata?. *_W A S H E G A R I_* Dukka su hudun suna zaune a gabanshi,yana jansu da hira cikin yanayin da zakayi tsammanin shi din wani babban yayane a garesu bawai uba ba. Da idanu yake karantarsa,har yanzu dai bai sake ba kamar yadda ragowar 'yan uwansa uku suke a sake. Har yanzu a darare yake,dararewar data sanyashi yaji a ransa akwai abinda ya hanashi sakewar. Har cikin rai da gangar jikinsa a yanzun da suke gabansa yake jin kamar dukka su hudun mallakinsa ne,shine ya haifesu. Inda yana da iko tabbas zai maida agogon rayuwarsu baya ya mantar da al'ummar da suka sanshi dama na unguwar cewa shi din ba shine ya haifesu su biyun ba. Tun daga nesa da take takowa cikin falon idanuwanta yake kansu. Sunyi wanka dukkaninsu sun kuma shirya cikin shaddodinsu masu kyau,wadanda tayi imani cikin sabbin kayan daya saba tahowa da yaranne. Sake maida idonta tayi a kansu,a nutse yake qwarai fiye da dan uwansa,ba wani karsashi a tare dashi ko kuma rawar kai,saidai kuma haka siddan takejin muguwar matsananciyar tsanarsa shi da dan uwansa. Ta yaya tun bata aje nata yaran ba ace wasu yaran sun shigo sun sake cinye gurbi da muhallin mutum biyu bayan gurbin mutum biyun da yaran gidan suka cinye?. A yanzun idan har ta soma aje nata yaran kenan saidai su tashi daga na biyar?,ya za'ayi ta bari haka ta kasance?. Sai data iso dab dasu sannan ta iya controlling kanta tayi sallama. Dukkansu suka daga kai suna dubanta banda abba da ya kauda nasa kan kadan gefe don da haushinta ya kwana. Qoqarin gaidata sukayi,ta amsa tana binsu da kallo daya bayan daya,wannan ya sanya kowa ya sake kama kanshi a cikinsu,bansa me babban suna wanda tun daga kallon farko bai sake daga kansa ba bangaren da take. "Ina kwana abba?" Ta gaidashi cikin matuqar qoqarin daidaita kanta idanunta zube kan kayan breakfast dake gabansu. "Lafiya lau" Ya amsa mata a taqaice yana rufe plate din fried egg din daya gama ci. "Yau nayi bacci me nauyi ban samu tashi na hada abincin safe ba" "Eh laraba tayi.......don dama fita nakeso muyi" Ya amsa mata yana miqewa. "Ina haka da safiyar nan?" Tayi masa tambayar cikin son sanin komai "Makarantarsu Faruqee,inason na yiwa su me babban suna registration,next week idan Allah ya kaimu su koma tare baki daya" maganar tayi mata kama da almara ko kuma ba zata. Tana tantamar akwai hikima ko hankali kuwa cikin maganganun abban?,ta yaya zai dauki yaran maqota ya kaisu makaranta me kudade masu ciwo haka?,makarantar dako yaran cikinsa da taji nawa ne school fees dinsu saida taji kishi da baqincikin abun?,ta kuma bashi shawara a fakaice ya kusa sau biyar akan ya sauya musu da wadda bata kaita ba.... Ko don yadda shima wani lokaci ta lura kaman yawan school fees din yana dan takurasa?. Abinda ya darsu a ranta me girma ne,tana da abubuwan da takeson ta fadi masa amma girman bacin rai da kuma abinda ya tsaya mata a wuya ya hanata cewa komai har suka tarkata suka fice daga falon. Idan nace ta samu nutsuwa tun daga fitarsu har dawowarsu to zance ne kawai. Sanda suka tashi dawowa din kuma sun dawo da dukka tarkacen kayan amfani na buqatar rayuwa na yau da kullum. Komai hurhudu ya siya,amma kaf cikin siyayyar bataga tsinke nata ba "Somin tabi kenan hatsin gara a buta......tun yanzu?" Wani sashe na zuciyarta ya ayyana mata. Ai juma'ar da zatayi kyau tun daga laraba ake ganeta. Tun a rana ta farko ta soma karantar iyakokinta?,dukka kuma akan yaran da suka kasance tamkar wata tsintacciyar mage?. Yaran da basu da GATA ASALI ko wani GALIHU?. Ita kuwa asama'u yaushe?,yaushe zatayi wannan SAKEN?. Muddin bata bazama su ba lallai anyi asarar haihuwarta,muddin bata ganar dasu kuskuren maida UBAN WANI NASU BA bata cika MACE BA.... *_BAN TABA KOMAI BAFA CIKIN LABARIN......BAN FARA KOMAI BA A CIKI_* *_zazzafan labari ne tsakanin SABREEN DA MUHAMMED FU'AD_* *_BANBANCIN RA'AYI TSARI DA AQIDA_* *_MUMMUNAN ZATO DA GURGUWAR FAHIMTA_* *_TA YAYA RUWA DA WUTA ZASU HADU GURI DAYA?_* *_ZALLAR QIYAYYAR MAHAIFIYA HALITTA MAFI SOYUWA A DUNIYA_* *_BAHAGUWAR BIYAYYA BISA TILASHIN ZUCIYA BA DON RAI YANA SO BA_* *_GWANA KUMA QWARARRIYA WAJEN SACE ZUKATA DA ALJIHUN MAZAJE DAMA ASUSUNSU GABA DAYA_* *_KARKI SAKE AYI BABU KE_* *_WANNAN SALON YASHA BANBAN DANA SAURAN_* *DUNIYATA(MUHAMMAD JADDA)* *DUNIYATA(SABREEN)* _GA HANYA MAFI SAUQI DA ZAKI KASANCE DA ZAFAFABIYAR FAMILY IN SHA ALLAH_πŸ‘‡πŸΎπŸ‘‡πŸΎπŸ‘‡πŸΎπŸ‘‡πŸΎ *SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI* *_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_* *_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_* *_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_* *_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_* *ZAFAFA BIYAR* *_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_* *Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU* _TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_ _QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_ _K'ALBIM Mamuhghee_ _AJIYA A DUHU Billynabdul_ _DUNIYATA Huguma_ _Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_ *hudu 2k* *uku 1500* *Biyu 1k* *Daya 500* _YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_ *09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA* *IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA* *09033181070* *BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK* *ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171* *ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI* *AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*πŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺ 89825722 Nousaiba lawali maradi 1000cf *_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_* *_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*πŸ₯°πŸ₯° An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu

Chapter 2 of 3