Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 3
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels *A D U N I Y A T A* 🌎 *_H U G U M A_* *Arewabook:Huguma* __________________________ *_Amintaccen guri kuma muhalli na siyayyar ingantattun suturu na alfarma,siyayya cikin aminci,farashi na musamman da babu irinsa_* *lace* *kowanne nau'in shaddodi* *yadika na maza da mata* *mayafai* *lafaya* *takalma da jakankuna na kece raini,masu babban farashi da qanana* *sarqoqi da agoguna* *under wears* *abayoyi na manya da yara da jallabiyoyi domin maza* *_Akwai group na musamnan saboda nasu buqatar kayan kitchen HUGUMA UTENSILS UNIVERSE_* https://chat.whatsapp.com/EzM8Qst8A2XAevw3akx5ub *_Duniyar kwatalle kitchen din amarya da uwargida_* *_me kikeyi tuntuni bakiyi joining group dinnan ba?,sallah tana matsowa,azumi na tunkarowa?_* https://chat.whatsapp.com/DT97XBDyEfyEwniN0a09Cz __________________________ Page 01 *_The gateway_* "Maaaam.......don Allah maama,abbee bashi da lafiya sosai kin sani maama......idan kika tafi waye zai kula damu?,idan kika tafi maama waye zai kula da abbeee?" Muryar yaron da gaba daya bazai haura shekara goma sha uku ba kenan take fita cikin wani irin sanyi da matsanancin rauni wanda koda ba'a gaya maka ba.....koda kuma baka kalli fuskarsan nan dake jiqe da hawaye ba.....koda baka kalli hannuwansa dake rawa ba wanda ke tallafe da mujinyacin dake zaune tsakanin cinyoyinsa ba zaka fahimci yana cikin matuqar kaduwa razani tare da zallar firgici. Idanunshi qur bisa kanta yana fatan jin qididdigaggun kalmomin "Na fasa tafiya" daga bakinta,duk kuwa da cewa ba wani abu guda daya tal da ya bashi alama komai qanqantarta da take nuni da zata iya janyewar. A maimakon haka ma,sai sake gyara yafen mayafinta dake saman kanta tayi,ta duqa tana cusa ragowar kayanta da basu samu gurbi ba cikin baqar jakar gabanta. "Don Allah mariya.......ba don ni ba......ko don yaran nan,kiyi haquri......ki zauna ki rungumesu,ni tawa me sauqi ce,ina da tabbacin kwanaki qalilan ne suka ragemin,su din dai sune abun dubawar......" Mutumin da rashin lafiya da kuma talauci sukayi gamayya da matsin rayuwa suka yiwa kowanne sashe na halittar jikinsa illa. Yayi maganar da qyar yana fidda numfarfashi kaman numfashin nasa zaya qwace daga tsakanin qirjinsa zuwa hunhunsa. Dauke dubansa yayi daga kan fuskar mutumin da yake MAHAIFI a gareshi ya maida kanta zuciyarsa na narkewa da wani irin tausayin kansu gaba daya idan ka debe ITA!. Bugun zuciyarsa na sake daduwa da tsananin tashin hankali da tausayin na daban kamar zai fasa zuciyarsa ta tsage. Ya jima yana begen jin fitar wasu kalmomi daga bakin mahaifinsu wanda a qalla yau kusan kwanaki goma cif kenan baya um baya um um. Ya kashe darare masu yawa yana kasa kunnen yaji wani abu daga bakinsa.....sai gashi a yau bakin ya budu,amma kuma sun budu ne saboda tsananin bala'i da firgici da take shirin jefa rayuwarsu,bawai ya budu bane da zummar musu magana da kyawawan kalmomin nan da baya rabo dasu a kansu. Idanunsa cike da fatan zuciyarta zata rusuna daga kalaman mahaifinsu.....kodon kalmar mutuwa daya ambatarwa kansa wadda ta zama daya daga cikin dalilan da ya sanya yaji inama baiyi maganar ba,inama shuru yayi da bakinsa duk da tarin buri da begen yaji yayi maganar wanda ya cika zuciyarsa. Yana tsaka da wannan shawagin cikin zuciyar zato da fata ya sake jin busashiyar muryar mahaifin nasa mara amon sauti yana sake tattara dukka juriyarsa yana fadin "Mariya......idan kika tafi waye zai kula dasu?" A fusace ta waiwayo ta watsa masa wani irin kallo tana rataya jakarta bisa kafadarta "Dasu nazo?,ai dama a nan na samesu kuma a nan din zan barsu,dan da uwarsa ke mutuwa ma randa ta haifeshi yanzu haka suna rayuwa sunfi miliyan bare wadanda suka kai shekara sha uku da takwas" tana kaiwa nan ta soma daga qafafunta tana baiwa dakin takun bankwana,abinda ya bashi tabbacin da gaske fa take! Ba zata rusuna ba!. Da alama kuma ba abinda zai sanyata rusuna din!. Baisan wanne tunani ya kamata yayi ba,don a sannan qwaqwalwarsa tayi qanqanta da daukan dukka wadannan abubuwan bare har ya rarrabe hukuncin daya dace da wanda bai dace ba,sai ya tsinceshi a gabanta,riqe da qafafunta yana qaramin kuka da iya dukka qarfinsa a shekarunsa. Dubansa tayi kaman zata qwace qafar,sai kuma ta saka hannu ya dagoshi ta maidashi ta zaunar tana cewa "Nan din shine dolenku,a nan zaku zauna da dadi ba dadi,da wuya ko babu,idan nace nima zanci gaba da zama,dukkanmu ni daku za'a yi haihuwar guzuma ne ni kwance ku kwance babankun ma haka,gwara na matsa kadan,wataqila rabon yana a gaba". Cak maganar ta yiwa zuciyarsa tsaiwar mashi. Idanuwansa suna iya hangen mahaifinsa yana runtse idanunsa. Sai ya zare nasa idanun yana maidawa kan yaron daya yunqura zaibi bayanta bayan fitarta qofar dakin. Wata gigitacciyar tsawar data girmi shekarunsa ya daka masa "Dawo ka zauna!......zamu rayu.....zamu rayu da mahaifinmu!.......zamu rayu da wuya ko da dadi!.......zamu rayu da farinciki ko babu!.......mu din dolen junanmu ne yanzu!......bamu da kowa sai kawunanmu sai mahifinmu!" Ya qarashe maganar yana numfarfashi qirjinsa yana dagawa sama da qasa. Cak ta tsaya,ta kuma waiwayo,idanunsu suka sarqafe guri guda. Ba sanin shekara daya ko biyu tayi masa......ba kuma sanin shanu tayi masa ba.......tasan dabi'unsa dake zubi da dabi'un mutumin daya dauki wani dogon xango xamani ko kuma qarni cikin sararin duniya...... dabi'un da sukan jefata duniyar mamaki a wasu lokutan..... Amma ko a shifcin qwaqwale bata taba tunanin fitar wadannan kalamai masu tsananin zafi daga harshensa ba. Kalaman da suka jeru da kyau!. Suka kuma isar da saqo tamkar dai ya jima yana ajiyarsu......kamar kuma rubuta masa su akayi ya dauki dogon lokaci yana gwajin yadda zai furtasu. Yadda ta zare idanunta daga kanshi haka ya zare nasa. Sai ya maida dukka yunqurinsa wajen qoqarin kwantar da mahaifinsa yadda zayaji dadin kwanciyar. Jikinsa ya qara nauyi ya kuma sake sosai. Saidai duk da haka numfashi na fita ta qofofin hancinsa,abinda ya sanya sam tunaninsa bai kai kan komai ba. Bashi da wani sauran FATA a kanta......amma kuma hankalinsa ya gaza daukewa daga kanta,yana lissafe da takun takalminta sanda take ficewa daga cikin gidan nasu. Fitar da har yanxu ta kasa barin qwaqwalwarsa. Fitar da har yanxu take masa matsanancin ciwo......fitar daya alaqantata da sila kuma MABUDIN afkuwar kowanne irin tsanani da matsin rayuwa. *SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI* *_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_* *_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_* *_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_* *_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_* *ZAFAFA BIYAR* *_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_* *Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU* _TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_ _QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_ _K'ALBIM Mamuhghee_ _AJIYA A DUHU Billynabdul_ _DUNIYATA Huguma_ _Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_ *hudu 2k* *uku 1500* *Biyu 1k* *Daya 500* _YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_ *09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA* *IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA* *09033181070* *BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK* *ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171* *ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI* *AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪 89825722 Nousaiba lawali maradi 1000cf *_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_* *_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰 *D U N I Y A T A*🌍 *_H U G U M A_* *Arewabooks:Huguma* Page 02 Idanunsa da suka qanqance suka kuma sake shigewa ciki saboda tsananin kuka tashin hankali da firgici ya bude. Ya jefa idanunsa gefansa hannun hagunsa,ya kuma aza idanunsa saman shimfidaddiyar lamusashiyar shimfidar. Shimfidar da kwanaki uku kenan da matuwar mamallakiyarta, shimfidar da kwanaki uku da suka gabata iwar haka suna tare da me shimfidar. Kaka a garesu,mahaifiya ga mahaifinsu wadda ta zame musu bango jigo kuma majingina a garesu bayan rasuwar mahaifinsu. Har yau ya kasa sanya hannu ya tattare shimfidar,hakanan babu wanda ya damu ya dauke ta. Yo ina aka damu dasu ma ballantana abinda ke cikin gidan?. Su din ba wasu bane,basu da abinda zasu bawa jama'ar zaman makoki,basu da gata basu da wani tsayayye da zai tsaya ya tayasu jimamin rasa kakar tasu da suka zauna da ita shekaru uku cikin tsanani da kuma zazzafar gwagwarmaya irin wadda ke xamantoww tsere ne tsakanin tsanani da kuma sassauci cikin tsananin. Hawayen nan daya kasa yankewa daga idanunsa ne suka sake bullowa. Har yau gani yakeyi wasa ne,har yanxun gani yake JADDA zata dawo. Shudewarta ya dawo masa da mikin rasuwar mahaifinsa,sai yakejin kamar yau ne ya rasu,kamar a yau ne yayi bankwana da duniyar,kamar a yaune MAAMA ta sanya qafafu ta fice ta barsu,tafiyar data xama wani yanki na tunzura yanayin rashin lafiyar abbee......tafiyar kuma data zaman kamar ta tafi da ruhi da kuma rayuwarsa. Hannunsa daya ya sanya ya riqe wuyansa da kyau kamar yana shirin shaqe kansa. Wasu murtuka murtukan jijiyoyi suka fito bisa saman kansa da goshinsa sukayi layi rad'a rad'a. Kalar da idanunsa yayi ya sake ninkuwa da kalar jaa ainun,kuka da hawaye me zafi ya sake yanke masa,matuqar maqurar qiyayyar jinin mahaifiyarsa yana tsartuwa cikin kowanne sashe da lungu na gangar jiki da zuciyarsa. "Hamma.....ham" yaron daya fado dakin ya dakata da kiran da yake jera masa. Cikin wannan yanayin ya waiwayo yana kallonsa,sai yaron ya dan ja da baya,don ya tsorata ainun da yadda yaga fuskarshi ta sauya. Yanayi ne dake sanya masa tsoron hamman nasa sosai da sosai,duk sanda ya ganshi a irin haka sai ya dinga ganin kamar ba hamma dinsa ba. Ya lura da hakan shima,wannan ya sakashi zare hannunsa daga wuyansa yana tattaro wani irin yawu me tauri da kauri yana hadiyewa da qyar kamar me hadiyar duwatsu. Yakai zuciyarsa cen nesa,ya kuma gyara harshensa sannan ya jefa masa tambaya "Menene?" Murya da jikinsa suna danyin rawa ya soma fadin "Abba ne......abbansu farouq ne yace kazo yana soro" idanunsa ya sauke yana jin wani kaso na rahama da sassauci suna sauka a zuciyarsa. Mutum qwaya daya tak a duniya da ganinsa ko jin kiransa yake shaida masa zuwan alkhairi sauqi sassauci ko rangwame daga dukkan wani hali da suke ciki. Yana tafe amma yana jin kaman ba'a kan qafafunsa yake tafiya ba,yana tafe yana jin kamar tsakanin sama da qasa yake,saboda tashin hankali yunwa harma da qishi. Ko sau daya bayan rasuwar ya gaza kai qwayar abinci bakinsa daga abincin da maqota ke saka musu jifa jifa. Yana daddafe da bango yana wulga idanunsa ga sararin tsakar gidan nasu daya zama kamar filin sukuwa......ya zama fetal ya sake fadi,abinda ke alamta masa cewa lallai sun sake rasa wani bangon kuma madaafa. ******Dattijo me cikar kamala wanda duka duka shekarun haihuwarsa a duniya ba zasu haura arba'in da biyar ba. Amma alamu sun nuna muraran shi din me ginanne kuma lafiyayyen jiki ne dake iya cinye shekaru. Yana sanye da yadin kufta da yasha aikin hannu wanda ya qara masa cikar kamala. Ya tura hularsa baya,qafarsa sanye da slipper dan madina,wanda ke zamantowa daya daga cikin dabi'unsa a lokuta da dama idan zaya fito guraren da bai wuce masallacin cikin unguwa ba ko wata unguwata kurkusa a cikin abun hawansa ko a qafa. A raunane suke kallon juna shi da shi,ganinsa sai ya sake sakawa zuciyarsa wani raunin,yana shirin duqawa ya gaidashi ya tallabeshi "Tashi tashi......sannu da qoqari,sannu da haquri......akwai wai abu da kuke buqatar dauka ta cikin gidan?" Ya tambayeshi yana dubansa. Bai gane komai abban yakeson fada ba,don haka ya dubeshi sosai. "Gida na zan wuce daku,ba za'a barku ku dinga kwana kuna tashi gidan da ba kowa a cikinsa ba saiku kadai" Muryar nan data nuqu qwarai cikin wahala da gararanba ya bude "Sai kayan sawarmu" "Dauko abinda ya sawwaqa a kulle gidan" yayi maganar yana kama hannun qaramin qanin nasa dake kusa dashi. Sanda yake hada kayan kudu da yamma gabas da arewa na zuciyarsa a cakude yake da tunani. Zasu koma gidan abba?. Gidansu farouq?. Tabbas su farouq 'yan gata ne gaba da baya,saidai wani irin gata suke samu dake da wani wawakeken gibi da kuma naqasu. Gatan daya rasa wani bango kuma jigo a cikinsa,gatan da wani lokacin yakan juya musu da wani irin launi mara armashi. Wani gata da bai amsa sunansa ba a lokuta masu yawa,su din sukan zama har sun darasu samun wani abu guda daya,duk da tarin nasu naqasun rashin wadata da sukunin rayuwa. Sun darasu samun 'YANCI SAKEWA DA KUMA WALWALA. kenan zasu rayu tare da momy?,zasu zama qarqashin inuwa da mulkinta kamar sauran yaran?. Sakin ragowar kayan hannunsa yayi ya sulale ya zauna a qasa. Iya wannan tunanin kadai ya karya duka sauran guntun karsashinsa. Tunaninsa ya dinga rarrabuwa,a haka dai gatane suka sameshi saboda abban wani irin dattijo ne me fafutukar taimakawa da tallafawa sukkan me rauni. Tun zamanin da mahaifi da mahaifiyarsu ke rayuwa tare hannuwansa da aljihunsa harma da lokacin cikin hidimta musu suke. Shudewar uba a garesu ya sanyashi sake ninka alkhairinsa. Ya sanya hannu bibbiyu ya tallafi rayuwarsu data jadda,a yanzun kuma yana shirin maida nauyin kacokam bisa wuyansa. "Idan ba zaka iya shirya kayan ba fito hakanan a barsu zuwa gobe ko?" Muryar abban ta baqunci kunnensa,wanda dole ta sanyashi miqewa ya debi iyakar abinda zai iya. Ya janyo qafafunsa yana fita daga dakin,idanunsa na rarrabuwa a sassannin da suka qaraci dabdalar rayuwarsu suda jadda bayan shekaru uku da rasuwar mahaifinsu. Abinda ya dunqule waje guda ya bashi adadin shekaru SHA BIYAR a duniya. *SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI* *_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_* *_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_* *_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_* *_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_* *ZAFAFA BIYAR* *_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_* *Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU* _TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_ _QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_ _K'ALBIM Mamuhghee_ _AJIYA A DUHU Billynabdul_ _DUNIYATA Huguma_ _Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_ *hudu 2k* *uku 1500* *Biyu 1k* *Daya 500* _YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_ *09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA* *IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA* *09033181070* *BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK* *ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171* *ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI* *AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪 89825722 Nousaiba lawali maradi 1000cf *_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_* *_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰 *D U N I Y A T A*🌍 *_H U G U M A_* *Arewabooks:Huguma* Page 03 https://chat.whatsapp.com/CKY0xZDtpby6MTkGrPkXLr ______________________________ Yana riqe da hannunsa tsam cikin nasa cikin tausayi da nuna kulawa. Yayin da yake biye dasu a baya,rungume da kayansu jikin qirjinsa, wanda ke dauri a wani yalolon mayafi. Duk taku daya yana yinsa ne tare da bugawar zuciyarsa,wani irin shakkun shigarsu gidan yana mamayar zuciyarsa,dukkan sarewa da kuma rauni tare da rashin tabbas suna cikashi. Daidai sanda abban ya waiwayo a nutse,lokacin da suka kawo bakin gate din gidan. Murmushi ya sakar masa a hankali da mufin kwantar masa da hankali,ya fahimci akwai anunuwa da yawa dake kai komo a zuciyar yarin game da shigarsa gidan. Shigarsa gida wani tsohon labari ne daya jima da shudewa,a qalla shekaru kusan biyu cur kenan yanzu ake magana. "Ka saki jikinka,hakan shine zai sanya dan uwanka shima ya saki jikinsa,ka dauka a ranka tamkar mahaifinku ne ya dawo,zan zame muku uba bango kuma majingina muddin numfashi yana yawo a gangar jikina,kasa a ranka a yanzun baku da sauran matsala ko maraici kaji?" Abba ya furta yana dora hannunsa saman kanshi,qauna da tausayinsa yana ratsashi. Ya jima yana kallon yaron a mabanbantan ranaku lokutta da kuma gurare cikin unguwar. Ya jima da sanin cewa yaron ya fita daban cikin sauran yara,komai nasa na dabanne,nutsuwa da hangen nesansa kawao zai sanya kayi tunanin ya girmewa shekarunsa. Bai taba ji ba,bazai kuma taba iya tuna wani lokaci da yaji wani yayi kusa dashi cikin unguwar bisa rashin gaskiyarsa ba,muddin kaji wani koke a kansa to lallai ba shakka taboshi akayi,an shiga gona ko huruminsa. Duk sanda ake irin wannan case din a mafi yawan lokuta yana tare da mahaifinsa,yakance "Ka barni nayi masa hukunci koda shine da gaskiya,ya cika zafin rai,ya fiya taurin kai da kafiya,wannan duka ba dabi'u bane masu kyau,ya kamata ya sauya saboda rayuwa". Murmushi abban yakan saki,ya kuma maida dubansa ga fuskar yaron kafin ya bawa mahaifinsa amsa "Ka godewa Allah,ba'a taba kawo maka qararsa akan rashin gaskiyarsa ba,koda kuwa an kawo qarar zaka sameshi ne ame gaskiya,shin me kake nema ko fata sama da haka?". Mahaifinsu mutum ne me tsananin kawaici,kanshi kawai yake kawarwa yana murmushi. Abban ya wuce komai a wajensa,maqoci ne me nagartar da samun irinsa yake wahala,don haka ne yake bashi dukkan girma,ba kuma wai don arziqi ko dukiyan daya mallaka ba,a'ah,don kawai ya cancanci hakan. "Kana jina?" Abba ya sake fada don maido hankalinsa kansa,sai ya gyada kansa a nutse shima yana duban abban "Yauwa,muje ciki,dukka su saddiq ma suna ciki na tabbatar yanxu" Bai musa ba yayi gaban abban yana biye dashi yana tsokanar dan uwan nasa daya sake sosai,farinciki ne ma kwance akan fuskarsa,da alama quruciya da rashin sanin cikakken ciwon kai ya sanya ko kusa ko alama baya hasashe ko hangen abinda kan iya faruwa,ko a kusa ko a nesa,me kyau ko akasinsa a kansu da rayuwarsu dama DUNUYARSU gaba daya. Ci gaba sukayi da tattaki cikin harabar gidan,yalwatacciyar haraba dake shimfide da interlock. Kana ma gidan kallo daya zakasan akwai sukunin rayuwa a cikinsu,duk da ba zaka kirayeshi da wani MAHAUKACIN ME KUDI BA amma tabbas yana cikin jerin MASU KUDI ARZIQI DA WADATAr daya tserema neman komai na biyan buqatar rayuwa,kamar yadda ya tserema RASHI ya masa tazara irinta HAIHATA HAIHATA. "Bude mana" Abban ya furta sanda yaga yaja ya tsaya ba tare daya buda qofar falon da zata sadaka da ainihin cikin gidan gaba daya ba. Matsawa yayi gaba kadan,ya murda qofar ya kuma tura,sannan ya saka qafafunsa cikin falon dake gauraye da sanyin Ac. Ita dince dai,itace mace ta farko da idanunsa suka fara tozali da ita. Bai sani ba,tsabar yadda ya washeta ne,yake kuma qyamatar shiga cikin dukkan lamuranta ne kamar yadda take nuna qyamata da qin jininsu qarara a fili?,wannan shi ya sanya ta zama mutum na farko daya fara gani?. "Kai dakata!,ina zaka je?,wajen wa kazo?,wai ban hanaku shigowa gidan nan haka gaba gadi ba kamar gidan tsohonku?,me ma ya kawowa da wasu tsummokara a hannu?" "Nine na kawoshi" Abba dake bayansa ransa na quna da jin kalamanta ya furta. Sak ta danyi,duk da bawai ta razana bane da jinsa,sai tsabar baqinciki da kuma zato daya soma zuwa ranta "Lallai kawai bala'i cikin gidan nan" Ta raya a ranta tana sake tattara dukka girarta waje daya ta hade,babu rahama ko qanqani saman fuskarta. Yaron dake zaune a rakube daga qasan carfet din ya sake tattare jikinsa waje daya,alamu dake bayyana lallai ya shiga taitayinsa da sauyawar yanayin nata. "Laaaaa......kaine kuma yau?ashe zaka sake shigo mana?" Yaron dake fitowa daga kitchen din gidan ya furta,fuskarsa na juna tsantsar farinciki,kamar yadda ya bada dukka hankalinsa akan wanda ya jefawa tambayar,hannunsa dauke da tray,daga hannun nasa har zuwa qafafunsa ya tattare bakin wando da kima rigar tasa. "Kai me yasa baka da hamkali ne?,zaka zo ka ajjiyemin ko kuwa?" Hamshaqiyar matar dake zaune saman kujerun falon ta sake ma yaron tsawa,wanda tamkar ma ya manta da abinda ya fito dashi daga kitchen din,kaf hankalinsa ya tafi ga baqon yaron daya shigo din,wanda a idanu shekarunsu tamkar daya suke. Juyawa yayi xuwa gareta don aje mata tray din,hakan bai isheta ba ta bishi da wani mummunan kallo,idanunta kamar

Chapter 1 of 3