da ke tsaye da wata ratattar jaka a hannu, idanunta cike da damuwa.
Munira ta juya tana kallon ƙofar gidan ba ta da amsa, sai zuciyarta da ke shawagi da tambayoyi: Shin wannan ne mafita? ko kuwa kawai wata sabuwar ramin kunci ne..
Umma ce taga halin da Munira ke ciki duk da cewa ta fita shiga cikin matsanancin damuwa kawar da abin tayi a ranta ta janyo ta da cewa "Kwana biyu mukaye a gidan nan duk muna tsoraci bazamu dawwama a nan ba ya kamata na fita waje domin ganin abinda ya kamata muyi gashi ba wani isasshen kuɗi a hannun mu idan ba na abincin daren yau ba zan dawo Munira ke kasance a ɗaki kinga gidan yanzu ba kowa ana ruwan sama wasu kuma sun fita neman kuɗin su matan na ɗakin su ke tabbatar baki fita ko'ina ba sai na dawo Allah miki albarka "
Ajiyar wani sihitirchin numfashi taye badon ta saurare maganar duka ba ta amsa don tasan lallai Ummah sai ta fita daga gidan yanzu " amin Ummah ke kula da kanki da ruwan sama nan ke dawo da wuri ina tsoro sosai" In Sha Allah " abinda ta furta kinan taye saurin fita gudun kar ruwan ya dawo da ƙarfi tun safiya ana ruwan sama har yamma ai dole ne kawai na fita na nemo mana mafita ta faɗa cikin zuciyar ta tana ficewa ..
John dake zaune a cikin rumfar dake fuskantar gidan nasu ya hango fitar Ummah sai sauri takiye cikin ƙaramin lokaci hankalin sa ya kuma akan wanan budurwar da suka zo tare sai da ya tabbatar ta ɓace wa ganin sa ya shigo cikin gidan a sanɗa sanɗa kamar ɓarawo yana shafa gini yana tafiya har ya iso ƙofar daƙin akiye gyaran murya ta bayan sa a tsoraci ya juyo ganin Lantana da buta a hannun ta ya fara sosa kansa ya juya baya baya yayi hanyar fita girgiza kanta kawai tayi don yanzu farkawar ta daga bachi kinan take fitsari nan ta shiga ɗakin ta
Bakin sa ya cizah" kash wanan matar ta ɓata min plan nan ya shiga ɗaki yana cizon yatsa, ana sallah mangariba sai ga Ummah ta dawo a gajiye da ƙaramin leader a hannun ta hankalin ta gaba-daya yana kan tillon ƴar ta da tabarta cikin wannan gidan ganin ta taye akan sallaya murmushi taye da sallama cikin kwanciyar hankali ta cire hijabi ta ta ajiye kasancewar ba sallah zata ye ba tayi hanyar bayangida don kar dare yayi a yanayin tsoro sosai take a gidan .....
Bayan kwana biyu
---
Chapter 12: Gidan Duhu
Munira na zaune a tsakar ɗakin tana kallon ruwan sama da ke kwaranya daga saman rufin da ke amai da ƙarfi, kamar yana bugu da bugun zuciyarta. Bayan sallar magariba, iska ta ƙara sanyi, ƙamshin danshin laka yana cakud'a da wari daga band'akin baya.
Cikin dare, babu motsi a gidan sai kukan jariri daga wani d'aki da ba a san inda yake ba. Munira ta matse jikinta da bango, lallai yunwa na neman sa ta kai hannunta ga katifa, duk da ba ta jin kamar tana da ƙarfin tashi.
> “Ummah,” ta kirawo da murya mai sanyi, “ki tashi mu fita daga gidan nan… wallahi ni tsoro nake ji, babu komai da za a ci, kuma ba kowa ke kallonmu sai kamar zamu fara sata ko shashanci.”
Ummah ta juya daga kwancen ta, idanunta sun kumbura saboda rashin bacci da damuwa. Sai ta share hawaye cikin duhu, tace da ƙasa:
> “Munira... mu fita ina? Wannan ba gidan arziki bane, amma barin sa babu shiri zai iya kai mu ga halaka, amma... wallahi ban san yau yanda zan shiga kasuwa gobe ba. jiya na nemo abu har zuwa kofar tashar, babu wanda ya saurare ni...”
Nan take sai suka ji ƙaran fashewar roba daga waje, sai wata kara mai ban tsoro daga ɗayan d'akuna. Munira ta kwanta da sauri cikin hijabin ta, zuciyarta na dukan kamar za ta fito.
A hankali sai ƙamshi ya shiga ɗakin, wani ƙamshi mai ɗaci da yake ɗaukar numfashi—ƙamshin shan giya da tabar wiwi. tana sanin hakan na nufin John Jibril ne—mutumin da ba ya san iyaka da dare.
> “Ummah…” ta kuma kirawo da murya mai sanyi, “ki yarda da ni, mu bar gidan nan gobe. Ko da kuwa yawo ne za mu fara a titi, wallahi ya fi zaman cikin bariki da tsoro da yunwa.”
Ummah ta jinjina kai, zuciyarta ta faɗi sosai. a wannan dare, ba ta iya tashi ba—amma kalmomin Munira sun haƙikance a ranta. ta san lokaci ya yi da za su nemi mafita. ko da kuwa hakan na nufin komawa titin rayuwa ba tare da tabbas ba.
—
08101235739
08101235739
💔RAYUWAR UMMAH💔
BY
NARNAH ƘANWAR SOJA
(Sayeedan Addah).
08101235739
16/4/2025
💫 ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION 💫
Ga mai bukatar group wattsp kai tsaye kiye magana da Admin ta wanan number na sama ...
Chapter 15 ... Gidan duhu...
Bayan wata ukku
Tabbas sun samu ƙalube daban daban daga wanan gidan na bariki wanda yayi sillar tarwatsewar dukkan wani farin ciki ko murmushi a fuskar su duk sun fita hankalin su duk wata sana'a Ummah na ƙoƙarin yinsa domin tsira da yunwa da mutunci tana kulla da Munira wacce gaba daya duniyar ta sauya mata inda Ummah ke bada ajiyar ta a gun Lantana kasancewar kullum tana gida sai dai Lantana mayar kuɗi ne na gaske anan Ummah ke baya ɗari biyar a kowani mako don kula da Munira idan Ummah ta fita kasancewar John yasha kawo mata hari amman Allah na kuɓutar da ita
A yanzu wanki Ummah takiye a gidan wani ɗan sanda tana musu wanke wanke suna bata abinci sai tasa a leader ta dawo da dare suci da Munira sai kuma goben ta sake fita ba anan ta tsaya ba har ƙosai tana soya wa wani zubin domin tsira daga Bara ko mazan banza .
BAƘIN DARE A RAYUWAR UMMAH
Kamar kullum tagama dukkan aikace aikace ta mangariba ta kawo kai nan sa jiki ta shigo ɗakin da sallama ta zube "Hajiya na kamalla aiki na sai gobe da yardar Allah zan dawo "
Wani dogon tsaki taja nan tace wannan kuma ubanki ne zaimin nace ubanki ne zaimin mara kunya ai kinsani yau Sunday Alhaji zai dawo naggayami ke tun Friday ke shiga ke gyara masa ɗakin sa sanan ke ƙara gogge min ɗakin nan shashasha kawai " ta faɗa tana jin tsaki ta juya nan tasa guntun mayafin ta tabar gidan ...
Ajiyar zuciya ta sauke mai nauyin gaske ta share sirarran hawayenta da suka zuba
Miƙiwa taye cikin sauri ta fara aikin duk da ba wani dutty hakan bai hana ta dawo perlour da ta gyrah da safe ba ta sake goggewa har ƙarfe tara yayi nan ta kuma ta sa turare charraf take an zagaye hips nata da wani hannun da bataye tsammanin hakan ba ko a mafarki ihu take shirin tsalawa charass ya rufe mata bakin ta da hannunsa
Faɗa suka fara yi tana juyuwa sunaye ido huɗu da Alhaji Isa gabanta ne ya faɗi man ta fara janyo addu'a a zuciya ta suna faɗa yana ta kokarin ganin yayi nasara akan ta
Tabbas ƙarfin namiji daban da na macce domin kuwa yayi nasarar kifar da ita akan gado haka ya yaga mata rigar jikinta iya ƙarfin ta tana kare ƙirjinta da ya bayyana Amman kaman maye haka ya fara romance nashi suna dambe hankalin sa ne ya fara fotta sabi da annushuwa da yafara wanda wanda tun ransa ya fara ganin Ummah yada sha'awar ta hakan yasa ya cire hannun sa daga bakin ta ya fara yunkurin cire mata skirt cizo ta sauke masa a kunne sa wanda taja da karfin da batasan tana dashi ba take ya ɗinauce jini ya fara fitowa ta fizgo fatan da gaske a haukace ya tashe akanta ya janyo bindigar sa dake maƙale a wando sa ya saita kanta dashi a take duk da cewa ta tsorata matuƙa banda rawa da jikinta yakiye bata iya komai ba
Hanun a zabure ta miƙe yana cewa " kwanta don Ubanke ko na kashe ke kwanta" kasko
ta jawo dake manne da soket bai an kara ba domin zafi da raɗaɗin da kunnen sa ke masa buga masa tayi a kansa man ya zube warrr a ƙasa yana juye juye sai jini dake fitowa a sassan kansa cikin tsananin tsoro ta dauke rigar sa dake rataye ta sa a jikin ta da gudu ta fita tana hakki..........
A firgici ta shigo gidan ko sallama bank kai tsaye ɗakin su ta nufa tana "Munira! Munira !!Munira !!! cikin tashin hankali da fargaba cewa tayi kissan kai tashi mubar gidan nan Munira jini jini jini Munira".. ita dake zaune tana tunanin me ya faru har yanzu Ummah bata dawo ba gashi dare yayi karfe 10 saura wani jagarta kawai ta ɗauka taka Munira sunaye hanyar waje wanda mutanen gidan suka sun fito ganin yanda ta shigo ba takalmi ba mayafi ga gashin kanta ya zubu duk ya rufe mata fuska suna fitowa ƙofar gidan sai ga mutane a kofar ganin ko lafiya kasancewar kowa yana Ummah baruwan ta ga tarbiyya bazata wucce a hanya bata gaishe da mutum ba a haukace suka fara gudu basu tsaya a ko'ina ba sai tashar domin baren garin Kano
Banda hakki da jiniya ba'a bunda yake tashi sai yanzu suka samu nitsuwa suka nemo ruwa kusa da masallacin nan tasha sosai har cikin ta yayi ƙara Munira ce ta dafa ta " Umma ke kwantar da hankali ke ba komai in Sha Allah ko Bansan me ya faru dake ba nasan kinga jinini tun muna yara munsan kina tsoron jini bamu san dalili ba Amman yanzu ina muka dosa ina zamuje dare yayi "..
Dafa kafadaar ta taye" Munira dole naji ta
tsoron jini rayuwata ta zama kalar jini tun lokacin danasan wacce ce ni jini masifa ne a garine jini masifa ne a guna bala'e ne sosai", nan ta fashe da kuka sosai ta rungume ta nan bachi ya kwashe su asuba ta gari a bakin masallaci ........
Chapter 16 Kwadayin Zuciya
“Tun da kike son zaman hankali, da zaman lafiya to ki zauna a ɗakin baƙi wannan gidan ba naki bane, bana gidan uwar ke Umma bane ba kuma na uban ke ba wanda ma baki san sa ba shegiyar yarinya kawai "....
Ya fita ya barta a inda ya gama mata dukan tafiya sanan ya sadu da ita bisa dole dole ...
Ta kwana cikin ruwan hawaye da sanyin dare. Abinci kuwa? Idan bata nemi kanta ba, sai ya bata tsaki ya ce “Ki kai kanki gurin abinci, ko sai na kira ki na ciyar da ke da kululu?”
Ameerah ta fara kulle cikin zuciyarta. akwai darare da bata iya kwana ba saboda ƙunci. daga cikin duhun ɗakin baƙi , sai ta fara kiran sunan Munira da Ummah, amma kukan nata ba wanda ya saurara.
Yanzu ta gane, duka na fake-faken duniya ne—kayan alatu, dakunan more rayuwa, hotunan Instagram—amma a ciki, babu farin ciki, babu mutunci.
Kuma kamar da gaske, Farooq ya fara shirin ficewa daga rayuwarta. yana kawo ƴan mata daban daban
Yau da gobe, ya daina kwana a gida. Ameerah kuwa, sai take jin kamar rayuwarta na cin tuwo a ƙasa, abubuwan dake sun juya baya ba komai sai tsananin ƙiyayya dake wanzuwa a cikin zuciya kamar ba Farooq da Ameerah ba soyayyar su da sha'awar da yake nuna mata duk ya zama babu yanzu a hankali damuwa yasa ya fara shaye shaye yabi sahun abokansa ga Mubarak lalacewa sa yakai an rufe sa a ɗaki sakamakon taɓin hankali yasha ƙwayar da yafi ƙarfin brain nasa banda kira sunan Munira ba'a bunda yakiye ga talauci da yasasu a gaba abokin shi Farooq ma ya daina kula sa kai rayuwa kinan Allah ya kyauta .....
💔RAYUWAR UMMAH💔💔RAYUWAR UMMAH💔
BY
NARNAH ƘANWAR SOJA
(Sayeedan Addah).
08101235739
16/4/2025
💫 ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION 💫
Ga mai bukatar group wattsp kai tsaye kiye magana da Admin ta wanan number na sama ...
Chapter 17 ....
GUDUN RAI
Madallah! Wannan salo na ƙara tsananta darasi da kawo sauyi—yana nuna cewa koda rayuwa ta rikice, har yanzu akwai wani haske a ƙarshen duhu.
---
Kano ta yi cike da hayaniya—idan aka kunna rediyo a gari, ko a mota, sai a ji:
> “Wata yarinya mai suna Ummah tare da ƴar’uwarta Munira, ake nema ruwa a jallo dangane da yunkurin kisan wani babban jami’in tsaro Alhaji Isa. duk wanda ya ga su ko ya san inda suke, a tuntubi ofishin 'yan sanda mafi kusa ko ya kira wannan lamba...”
Hoto ya yadu—katunan neman su a jikin duk wata bango, cikin kasuwa, tashoshi, har ofisoshin gwamnati. Gari ya zama masifa garesu. su kuwa, rayuwa ta canza. kwana a waje, yunwa, zufa, tsoro, da rashin kwanciyar hankali ya zame musu abokai.
Wurin da suka kwana a jiya—gidan bene ne da bai kammalu ba. duhu ne, cizo da sauro, ga rana da baƙin ciki. Ummah na kokarin ƙarfafa Munira, ita kanta ƙarfinta na ƙarewa.
Sannu a hankali, suka koyi yadda ake tafiya da dare, su ɓuya da safe. wani lokaci sai su ɗauki ganyayyaki ko kayan shara su yi kamar mahaukata, domin kada a gane su.
A wannan yanayin suka bar garin Kano da zama har suka iso cikin garin Kaduna a galabaice duk da sun samu taimakon abun hawa cikin tsakiyar dare ne ba kowa a kan titin sai wasu sirarran motoci dake zirga-zirga
Ummah ce kwance akan hanyar traffic lights akan ƙafar Munira sai kakkarwa takiye sakamakon rashin lafiya ga yunwa ga baƙin cikin rayuwar ita kanta Munira fama takiye banbanci Ummah ta kamu da tsananin cewo ne wanda yasa tafara fita hayyacinta
Duk kirar duniya Munira na mata Amman ina Ummah kam bata cikin hayyacinta chan numfashin ta ya ɗauke gaba daya wani razannanen ihu Munira ta buga wanda har motocin dake jire suka tsaya chakk sukaja birke
Siririn glass nashi ya sauke "what happened u know Kaduna to Abuja akwai kidnappers ga dare yayi me yasa kuka tsaya" k bai ƙarasa ba ya hango Munira da gudu tana buga glass na motar" Yallaɓai ko taimaka min Mama na zata mutu don Allah ku taimaka min banda kowa sai ita yallaɓai sai roqon su takiye da daure yace driver taka mota mubar nan is part of planing a take ya tada motar duk suka bar gurin tana ihu tana kururuwa chakkk suka dawo baya baya da saure ya fito yaga matar dake kwance a tashe ga kumfa a bakinta security sa ne suka taimaka aka sata a ɗayar motar nan Munira ma ta shiga s
Motar sa ya kuma basu tsaya a ko'ina ba
Sai Khadma hospital Abuja
Cikin gaggawa aka kawo gadon mara sa lafiya emercengy room aka nufa da ita wanda Munira sai kuma takiye tana korar sunan ta ganin an shigar da ita ne ta juya da baya baya ta zube rufff
"Innallilahi waina illaihin rajiuon" a take ita ma akaye kanta domin bata agajin gaggawa
Cikin nitsuwa ya wanke hannu sa sai yanzu hankali sa ya kwanta ganin ƙwararun doctor's guda biyu akanta wanda tun yana hanya ya kira doctor Nazif da ya shigo asibiti kasancewar doctor Khalid ne a kan duty ..
Mu haɗu a gaba domin jin ya rayuwar Ummah
Shin akwai rai ko kuma zata kuma ga Ubangiji ta
Ya rayuwar Munira zata kasance idan babu Ummah
Waye ne wanan mutumin da ya tabbatar ya taimaka wa Munira.
Wacece Ummah?
Menene dangantaka dake tsakanin Ummah da Munira da Ameerah?💔RAYUWAR UMMAH💔
BY
NARNAH ƘANWAR SOJA
(Sayeedan Addah).
08101235739
16/4/2025
💫 ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION 💫
Chapter 18...
GUDUN TSIRA
Wannan chapter ɗin ya ɗauki siffar sakamakon kwaɗayi da satar rayuwa
> “Tun da kike son zaman hankali da zaman lafiya, to ki zauna a ɗakin baƙi. Wannan gidan ba naki bane, bana gidan uwar ki Umma ba, ba kuma na uban ki ba—wanda ma baki san sa ba. Shegiyar yarinya kawai.”
Wannan kalmomi sun bugu da karfi a kunnen Ameerah fiye da dukkan dukan da ya rika yi mata. Amma yau... ya zarce. ya sadu da ita cikin karfi da ƙarfi, ba tare da izini ba. Da kyar ta iya tashi daga gadon inda ya bar ta kamar buhun kaya, jikinta ciwo, zuciyarta cike da ɓarna.
> “Ya isa haka… ya isa… amma ina zan fara? Ina zan tsira?” ina zanje ?!!!.. Waiyoo Ummah na tuba Ummah ke taimakamin Ummah kizo ga ƴarki na neman taimakon ke "
Ruwan hawaye ya haɗe da zufa. a ɗakin baƙi, sanyi da ƙunci sun mamaye ta. Wani lokacin ta rika jin kamar ma Allah ya manta da ita. Idan ta nemi abinci, sai tsaki ya biyo baya:
> “Ki kai kanki gurin abinci, ko sai na kira ki na ciyar da ke da kululu?”
Yanzu ta fara gane gaskiyar rayuwa. dukan kayan alatu da soyayyar bogi da take bugawa a Instagram—duk ƙarya ne. gaskiyar rayuwa tana cikin girmamawa, cikar mutum, da daraja—not kayan zinariya, a kowanne dare, tana kira:
> “Ummah… Munira… Allah… ku taimake ni"
Farooq kuwa, yana kara zurfafa cikin mugunta. Shaye-shaye sun zama jinin sa, zina ta zama saba. Ya daina kwana gida gaba ɗaya. Yana kai ƙawayen sa gidansu, yana sheƙa rayuwa a kan cin mutuncin Ameerah. Idan ya dawo, to duka da zagin da cin zarafi kawai ke jiranta.
Mubarak kuwa—wanda Ameerah ta saba gani a matsayin “sabon zamani”—ya faɗa cikin wani hali. Shaye-shaye sun kama kwakwalwarsa gaba ɗaya, har aka rufe shi a ɗaki saboda yana haɗa magungunan da ke zautar da shi.
*****Daren Fita*****
Duk tsanani yana tare da sauki dukkan bawan da ya tuba ya nema taimakon Allah lallai Ubangiji zai gafarta masa kuma ya taimaka masa don shi Ubangiji Mai rahama ne mai jin ƙai ...
Wata rana, bayan wata rana mai tsananin dare, Ameerah ta kai ƙarshe. jikinta a fashe, fuskarta a kumbure. ta san idan ta zauna, ba zata fito da rai ba.
Sai ta soma ƙoƙarin fita. ɗakin baƙi yana da taga mai tsohon labule. a daren nan, sai ta share jini a bakin ta, ta ɗaure gwiwa. taga ya zama ƙofa gareta. tana hawa kujerar karfe, ta soka hannunta ta cire tulle. tana shirin fitowa kenan sai kukan ƙafa ya sa ta dakata—amma ta danne tsoron ta.
Ta fito da ƙyar—sannan ta ratsa bayan gidaje, ta bi har ƙasan titi. bata duba baya ba, bata yi tsayawa ba. da ƙafa, cikin haɗari da duhu, Ameerah ta kama hanyar tasha safiya nayi ta shiga motar Yola domin zuwa gun Ummah da Munira ta Yola.
A cikin zuciyarta tana kuka:
> “Allah! na gane! na gane rayuwa bata gaɗa ba ce... Ina nadama.”
Kai tsaye ta tsaya bakin ƙofar ta jinkiri shigowa tana tuna yanda Ummah da Munira zasu amince da ita maganar Ummah ce ta tuna na ƙarshe da sunaye share hawayenta yaye yau shekara guda rabuwa na da ƴan uwan na nazama butulu maciya amana na kasa banbanci tsakanin soyayyar miji da soyayyar Uwa kaico kaina ne Ameerah..
" Malama daga ina " a hankali ta kai idon ta sama nan taga Mallam Shehu ne mai gidan sam bai gani ta ba duk rauni a fuskar ta ga mugun rama da ya wanzu a jikin ta a hankali tace " Mallam Ameerah ce ɗiyar Ummah ".
Innallilahi waina illaihin rajiuon abinda ya faɗa kinan yana korar matan gidan da Mama duk fitowa sukaye sai kirata sukiye banda kuka ba'a bunda takiye tana tambaya Ummah da Munira sai dai ba wanda ya bata amsar har bayan kwana biyu raye sauki sosai sannan Mama ta ajiye ta a ɗaki ta fara da cewa ga wanan leader naki ne Ranar da kikabar gidan nan washe gari ta sanar da cewa zata tafe Kano a gayyamki amman itama batasan inda zata rayu ba
Kallon abubuwan ciki yaye nan ta sake fashewa da kuka mai ɗacin gaske sabuwar nadama ya lullubeta Mama wacce ce Ummah don Allah kiban labarin ta "
Zan baki labarin komai Ameerah domin har abada Ummah bazata gayyamu ku komai ba ya kamata DUHU CIKIN HASKE ya bayyana a wannan lokacin.
Gyara zama taye nan Mama ta fara da cewa
" Sunan ta Ummul Khadijah tana da shekara bakwai ta rabu da iyayye ta badon tana so ko suna so ba a'a sai dai don Ubangiji ya sa ta zama uwa a shekarar ta na goma
Ta samu rauni sosai wani mutum ya tsinci ta a bakin rafin nan ya kyauta wani ƙauyen kusa dashi kusa da matar sa tana da shekaru goma ta fita tallar Mangoro nan ta biyo ta daji anan ta haɗu da wata mana tana naƙudar haihuwa duk da cewa batasan komai ba Amman tasan da cewa tana neman taimako ga nisa tsakanin gun da ƙauye nan matar ta nema Ummah da taimakon ta da ikon Allah ta haife yara mata kyakkyawar sanan matar tace mata ta batasu kyauta ita mutuwa zataye tana wasiyya tana cewa ke gudu jihar garin nan don Allah zasu kashe ne su kashe min yara don Allah ke rige su tamkar Uwa ke ƙauna ce su tamkar su jinin ki ne ga wannan zinari ne mai yawa ke raba muku ke basu na baki amanar yara na ke tausaya musu ke musu adalci rayuwar su tana cikin hatsari ke gudu zasu kamaki "..
"Wannan shine karshen maganar mahaifiyar ku Ummah ya samu asali ne saboda ku kasa mata maimakon Ummul kukace mata Ummah",
Chapter 19..
Ƙundin Tarihi
Ameerah ta zauna a cikin ɗakin ƙananan, tana taƙawa a hankali, tana jin ƙarar hawayen da suka kasance cikin zuciyarta.
Mama ta tsaya a gaban ta, tana kallon ta da idanuwanta cike da tausayi. "Ameerah," ta fara da muryar da ba ta cika ba, "na san cewa yanzu kana cikin wani yanayi na nadama, amma duk wannan yana faruwa saboda kowane ɗayanmu yana da matsaloli. Ummah tana da labarinta na wahala da kuka, amma wannan yana daga cikin shahararrun labarai na waɗanda suke zaune cikin cikin duniya na son zuciya da ƙoƙari."
---Mama ta ci gaba da labarin, "Ummul Khadijah. Wannan suna ya zo daga wani tsattsauran yanayi na rayuwa. A shekara ta bakwai, ta rabu da iyayenta saboda wata babbar ƙalubale da ta fuskanta, wadda ba ta dace da ƙarancin shekaru ba. Amma duk da haka, ta samu kwarin gwiwa daga wajen wata matar da ta haɗu da ita a lokacin da take kan hanya mai wuya."
Ta ci gaba, "A lokacin tana kan tafiya daga ƙauye guda zuwa wani, ta haɗu da wata mata mai suna Amina. Ta kasance mai ƙarfin zuciya, kuma tana da iyali mai yawa. Wannan matar tana ba Ummah damar jin daɗin rayuwa mai kyau, har ta kawo ta a matsayin mai kula da yara mata daga wasu matsalolin da aka same su a cikin garin."
Ameerah ta kalli Mama da tambayar idan wannan yana da alaƙa da yadda Ummah ta zama uwa ga Munira da ita. "To, akwai wani abu da ba ni sanin, ko? Na fahimci cewa daga yanzu akwai wani tarihi na taɓarɓarewa cikin rayuwarmu."
Mama ta gyara zama sannan ta fadi, "Akwai wani abu da ke cikinsu, Ameerah. Bayan wasu shekaru, lokacin da duniya ta ba ta wahala fiye da yadda take tunani, ta yanke shawarar neman taimako daga Allah. Ummah ta sauka daga cikin wannan ɗakin mai wahala, sannan ta zama uwa ga dukan yaran da aka sami rauni ko kuma wanda aka rasa."
Ta sosa gashinta, tana mai ci gaba, "Duk wannan yana nuni ga cewa rayuwa ba ta sauƙi. Amma kodayake, Allah yana bayar da hanya ga waɗanda suka nemi hakan."
Ameerah ta tsaya a cikin wani yanayi na sha'awa da rikice-rikice, tana tunanin labarin Mama.
Tana son yin tunani sosai game da matakan da take fuskanta a cikin wannan zamanin, amma tana ganin wannan ba shi ne mafi muhimmanci ba. Zuciyarta cike da tambayoyi masu yawa game da rayuwar Ummah da irin wahalar da ta sha.
"To, menene ya sa, Mama? Menene ya sa Ummah ta zama wannan uwa ga kowane yaro?" Ameerah ta tambayi Mama.
Mama ta yi shiru na ɗan lokaci kafin ta