An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
https://chat.whatsapp.com/DoFR3n8lLtI1RB5Zd2z2IT
💔RAYUWAR UMMAH💔
BY
NARNAH ƘANWAR SOJA
(Sayeedan Addah).
08101235739
💫 ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION 💫
16/11/2024.
Happy birthday sister Najnurr ( Br barkama) Ubangiji Allah ya ƙara year’s masu albarka 💖
Page 1 & 2
"Yaushe zake dawo typing! We miss you! To ga new update!".
Finally Narnah ƙanwar soja is back "Yes am back tare da zazzaffan labari mai ciki da darrusa da tsaƙwarar soyayya duk a cikin RAYUWAR UMMAH......
ADAMAWA YOLA
A dai dai wane siririn lungu motar taxi ke shirrin tsayawa, cikin zafin nama aka bankaɗo ƙofar tamkar daga sama aka jifota cikin sassarffa batare da rufe kofar motar ba taye gaba ..
Burinta kawai ta shiga izuwa cikin mutanen da sukaye cincirindon a ƙaramin kofar gidan duk juyawa sukaye suna kallon ta baki a buɗe bata bi ta kansu ba ta kutsa kai.
Ganin Mubarak da gajeren wando da shabgigiyar bulala a hannun sa inda ya saita ƙarfin sa zai kai wane bugun charaf ta kama bullalar ciki da bakin ciki da takaicin da bai da misali ganin hakan ya joyo cikin tangalili.
" UMMAH" abinda ya furta Kinan da sauri yarinyar da bazata haura shikkara Goma sha shida ba dake durƙushe a gaban sa yana jibgarta da ɗaure hannun ta da ƙafafuwan ta jin an ambaci sunan UMMAH da ko a mafarki bataye tsammanin wannan sunan ba a tsanaki ta kurma uban ihu da cewa “UMMAHHHH“....
Tana ƙoƙarin matsowa bahagun mari UMMAH ta zabga masa wanda yayi sanadiyar zubewar sa ƙasa yana tangalili , bata jira maganganun mutanen gidan ba ta kunce Munira da ke ta zubar hawaye nan ta tallafa ta suka bar cikin gidan ganin Ameera a motar tana sharar hawaye ta rungume ta tsafff UMMAH ta rufe kofar Kinan yayi dai dai da zuwan Farooq " mujee driver ye sauri taka mota mubar unguwar nan " Cewar UMMAH.
Kai tsaye Farooq ya shiga cikin gidan ganin Mubarak tsaye yana tangalili sai huccen masifan da yake ta zubawa dogon tsaki yaja " Aikin banza ka sha giyar ka ka jibga matar ka ko ko kunyar hakan bakaje " .
Sanin cewa baya cikin hayachin sa ya juya tare da shiga motar sa kai tsaye sai Unguwar Runde a ƙarshen kwalta ya tsaya cikin kadarra da ƙasaita ya nufe wane sirririn lungu a dai dai wane zauren gida ya tsaya da aka rufe da mayafin buhu kasancewar babo ƙofa a ruɓaɓen gidan sai wane ya motse fuska yakiye yana ganin gidan up and down......
" Idan ba don yarinyar nan akwai kaya ga daɗin harka da zubin kyau na yarinyar nan ba uban wa zai sa nazo wanan ƙazamin wurin har wata banzan Yarinya tace zata gayyamin magana wai Ummah shegiyar yarinya ko matsayin mai wanke min toilet bata kai ba wanan shine Ƙaddara ta"...............
Karamin yaro ya aika cikin gidan sai dai masifan da zagin da Ummah take ye ne yasa kai tsaye ya kutsa kai domin nuna mata true colour sa.......
WAYE FAROOQ?
To be continued..........
💔RAYUWAR UMMAH💔
BY
NARNAH ƘANWAR SOJA
(Sayeedan Addah).
16/11/2024.
💫 ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION 💫
"Yaushe zake dawo typing! We miss you! Muna son new update!".
Finally Narnah ƙanwar soja is back "Yes am back tare da zazzaffan labari mai ciki da darrusa da tsaƙwarar soyayya duk a cikin RAYUWAR UMMAH.
Page 3&4
WAYE FAROOQ?
Umar Farooq Tambuwal Yaro mai taƙama da kyau da kuɗi ɗaya tilo a gidan Alhaji Farooq Tambuwal ya taso cikin gata da sakalchi daga primary school Nasa har ya kamalla karatu a matakin professor a kasar Amurka kasancewar sa yana son kasar sa Nigeria yasa ya dawo anan kuma ya samu gurbin zama lecturer a makarantar nan ta Abti University Yola jihar Adamawa state, duk da cewa bai cika zama anan ba but yana zuwa a time da yake so ya kuma time da yake so hausawa sukace komai na kuɗi ne .
Umar Farooq yana da shekaru 28 izuwa yanzu da yake kan matakin 29 bashi da wane halli a rayuwar sa sama da neman manta duk inda macce take da zarar ya kai idon sa kanta tofa sai ya lashe zumar jikin ta ko ta wacce hanya ce.
Farooq bashi da wane abokin a rayuwar sa sama da Mubarak ka tsaye yafe karfin sa nisa ba kusa ba sai dai wane babban ƙaddara ya haɗasu guri daya har suka ƙulla abota kasancewar Mubarak yaron talakawa ne sai dai bai taɓa damun Farooq domin bashi da wane banzan hali na ƙyamar talaka a rayuwar sa shi dai babban burin sa ya su macce a lokacin da ya kiso
Mubarak Ali Saurayi mai kyau da nagarta ga basira sai dai kash ya kasance babban tantiri a unguwar su ta Runde inda kowa yasan wanan bak'ar halin nasa na sata da kuma shaye shaye babban abun mamaki a tare dashe a duk lokacin da faɗa ya taso ko i gidan ubanwa to zai shiga domin kare martabar unguwar su hakan yasa duk abinda yace a cikin wannan unguwar ake tsoron sa dole kuma a be wanan umarnin nasa domin a takaice idan ka nuna bazaka biba to iyalan gidan ka sun shiga ukku hatta ƴan sandan unguwar su sun kasa masa komai akai domin dai sun gaji da kama sa har ta kaiga ya kafa wata banzar ƙunƙiya ta masu shaye shaye a bayan makarantar primary na govnatii.
Mubarak na samun kudin kashewa ta hanyar sata ko damfara da yasa ba ye sai kuma wasu ƴan siyasa suka fara ɗaukar nauyin sa izuwa ga aikin dabanci anan Mubarak ya shahara a kasanshi duk abinda yake aikata a zahiri Mubarak hankalin sa baya kan mata burinshi shaye shaye da kuma dabanci mutum ne mai ƙarfe da basira haduwar Farooq da Mubarak ta haifar da babban fitina da matsala kasancewar idan Farooq yazo Nigeria Mubarak she yasan lungu da saƙon nemo ƴan mata she kuma yana bashi manyan kuɗaɗi a hakan suka ƙolla babban abota da ta zama sillar jifa rayuwar UMMAH cikin masifa da fitina wanan itace ƙaddara ta riga fata..
a wannan lokacin ne kuma idon sa yakai ga Ameera ɗiyar Ummah Kinan
Back to story..
Karamin yaro ya aika cikin gidan sai dai masifan da zagin da Ummah take ye ne yasa kai tsaye ya kutsa kai domin nuna mata true colour sa.......
TO BE CONTINUED........
💔RAYUWAR UMMAH💔
BY
NARNAH ƘANWAR SOJA
(Sayeedan Addah).
16/11/2024.
💫 ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION 💫
Barka d ranar juma'a Allah ya amsa mana bukatar mu Share domin Allah da Manzonsa S A W 🥰
"Yaushe zake dawo typing! We miss you! Muna son new update!".
Finally Narnah ƙanwar soja is back "Yes am back tare da zazzaffan labari mai ciki da darrusa da tsaƙwarar soyayya duk a cikin RAYUWAR UMMAH.
Page 3&4
Karamin yaro ya aika cikin gidan sai dai masifan da zagin da Ummah take ye ne yasa kai tsaye ya kutsa kai domin nuna mata true colour sa.
" Na rantse da Allah Mama babo wacce zata kuma gidan mijin ta don uban mutum suzo su sake su don ban haifa ba kuma ban raina wa mazan banza yara ba shegu ƴan isk....."
Katse ta yayi da magana cikin harƙuwa " ƙarya ne na rantse na sake matata akan ke ke har kin isa ke raba ne da matata Ummah ke bine a hankali tun kafin na sa a rufe ke a ƙasar nan har karshen rayuwar ke bazake sake kallon ko idon rana ba "
"A'a Farooq gani kar ka ɓoye ne a duniya kashe ne fitsararre mara kunya kashe ne ka kaine lahira yarinya dai nace bazata kuma ba idan kuma sake ne ka rigi takardar har ƙarshen rayuwar ka ɗan iska mazinaci ne zaka kwaso cuta ka sawa yarinya na mahaukachin banza tsinewar Allah ya tabbata akan ka "
Cigaba da musayar magana sukaye har takaiga ya ɗaga hannu zai tsinka mata mari shigowar mai unguwan su ne yasa duk suka dakata umarni aka bayar nan aka fitar da Farooq sukaye waje mata biyu ne a gidan sai wata tsohuwar mata wacce ake kira da Mama .. kai tsaye Ummah ta shiga cikin dakinta da gudu Amira da Da Munira suka faɗa cikin ta suna taya ta kuka hannu bibbiyu tasa ta ƙara rungume su sai ga wasu zaffafan sirarar hawaye akan kyakkyawar chocolate fuskar ta dake dauke da O face sai dogon hancin ta da yayi dai dai da zabin buɗaɗen bakin ta saurin bude dara daran idon ta taye domin ba ta don yaran ta suga kazawarta har suka hawaye a wanan kyakkyawar fuskar na ta katse su taye da cewa
" Amira ke daura mana ruwan zafi bare nayi sallah daga nan sai muyi mata wanka na sayo mata maganin da zai rage mata zafin dukan nan kuyi hakuri yara na tabads laife na ne da ba aurar da ku ga mazajen da Basu san muhimmancin ku ba ku gafar tamin Amira ce t adube ta da kumburin fuskar ta da cewa " Ummah har kina tunanin wanan laifin na ke ne laife na ne da nace ina son shi Domin a wanan rayuwar duk abinda muke so she kike mana to wanan dalilin yasa kika amince da auren mu kuma wanan shine (AUREN ƘADARRA my next book ).
Kallon su taye cikin so da ƙauna ta nufe kofar fita juyuwa taye ta dube su da cewa " Kuban wayar hannun ku " Ameera ce ta miko mata bata tsaya masa dogon ajiya ba ta ajiye a kan ƙaramar akwatin ta , ta fita waje bayan sallah sunce taliyar da Ameera ta dafa har sun gyara jikin Munira ta samu tasha magani sai Bachin wahala da takiye ..
Kai tsaye Ummah ta shiga dakin Mama ta sameta kwance ganin ta yasa ta miƙe " ƴar albarka kice daren nan"? faɗa wa jikin ta taye ta fashe da matsanancin kuka " A'a Khadijah kice yau da kuka ke tuna wacce ce ke ke tuna jajircewar ke da jarumtar da Allah ya bake, ke tuna karfin guiwar da kike dashi kifa Uwa ce wacce Allah ya bata rayuwar yara biyu alhali bata kai matsayin Uwa ba , ke Uba ne wanda Allah ya bake amanar rayuwar mata biyu cikin hukuncin sa da hikimar sa ya bake ilimi da basira da fasaha wajen ganin tarbiyyar su , shin kin manta duk duniya kicce Allah ya basu matsayin ƴar uwa ,kuma Uwa da Uba duka to me zai raunata tunanin ke har ke zubar da hawayen ke akan mutanen banza tsinannanu m
Maganar tane ya katse lokacin da suka tsinkayo matar gidan na shewa da sauri suka fito abinda ya gani ne yayi mugun bata mamaki yanda numfashi ta ke kokarin ƙwacewa gangar jikin ta idon ta ne ya tsaya chakk akan Ameerah
Mu haɗu a gaba domin jin yanda zata kasance meke faruwa a dai dai wannan lokacin?
Menene asalin labarin Ummah da Ameera tare da Munira ....
Kuna ƙorafi typing yayi kaɗan na ƙara kaɗan yawan comments naku yawan typing.
Barka da Juma'a
https://chat.whatsapp.com/DoFR3n8lLtI1RB5Zd2z2IT
💔RAYUWAR UMMAH💔
BY
NARNAH ƘANWAR SOJA
(Sayeedan Addah).
16/11/2024.
💫 ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION 💫
PAGE 7 @ 8
"Yaushe zake dawo typing! We miss you! Muna son new update!".
Finally Narnah ƙanwar soja is back "Yes am back tare da zazzaffan labari mai ciki da darrusa da tsaƙwarar soyayya duk a cikin RAYUWAR UMMAH.
Maganar tane ya katse lokacin da suka tsinkayo matar gidan na shewa da sauri suka fito abinda ta gani ne yayi mugun bata mamaki yanda numfashi ta ke kokarin ƙwacewa gangar jikin ta idon ta ne ya tsaya chakk akan Ameera dake tsaye da Farooq suna riqe da hannun junan su ɗayan hannun kuma yana cikin himmar nata yana wasa ganin Ummah sai da ta razana matuƙa itama Ummah ganin ikon Allah takiye
"Mata ta zo mu bar gidan nan kin san a hannu nake " yana faɗa yana ƙarawa mannewa a jikin ta ja taye kaɗan ta baya zataye magana Ummah ta katse ta da cewa "A'a Amira basai kin min magana ba Indai akan namiji ne bazan mike mugun baki ba amma ke juya kawai ke fita ido na bana son sake ganin ke a rayuwa ta gaki ga duniya ga kuma mijin ke Farooq a kusa dake ke yafimin na tuba laife na ne da na nuna zan rabaki da masoyin ke kiye hakuri Allah baku zaman lafiya "
Cikin sauri ta juya ta ɗaga idon ta sama nan taga Munira a Kofar ta fito duk abinda ke faruwa akan idon ta wasu sirararan hawaye ne yake biyo kumatun ta Umma ce ta juya kanta " kima ga Mubarak nan tare suka zo bazan hanna ku bin mazajen kuba " saurin dakatar da ita taye a ƙofar shigar ɗakin....
" Babo wane hallita irin na da zai zalunci rayuwa ta ko ya kyautata min kice bake son zama na dashi na juya miki baya a matsayin na na yarinyar ke kuma ƴar uwa ta ke sani rayuwa ta fansa ne a gari ke Umma ke yafe mana Amman bazan iya miki butulci ba Umma". nan ta zube akan guiwar ta dake mata radadin zafi sakamakon duka da Mubarak ya sharara mata ganin haka Umma ta shiga ɗaki tana cewa " Allah ya mike Albarka ".
Maganar Mubarak ne ya dakatar da ita sai dai kuma bata juya ganin su ba " wacce ce za'a ci ta bine Allah ya kiyaye idan ban kashe matsiyaciya ba shima Farooq ai don yana da kuɗi ne itta Umma taki ta gama asirce shi dole tace Ameera ta bishi anga idon Naira "
takarda saki ya watsa mata a inda ta ke durqushe " na sake ke saki Biyu wawiya shegiyar yarinya mara sa uba k ".
Baiye tunanin cewa zai sake kallo a rayuwar sabba sakamakon wane azazzabibin abinda ya sauka a kan fuskar sa yunƙurawa taye zata sake buga masa dutsen hannun ta Umma ce ta janye ta " Kul banson rigima barshi da duniya gidan kashe aho tana jiran wanda ba'a haifa ba balle wanda yake cikin ta yake yawo ".sakamakon mutanen dake zagaye a gidan ne yasa suka kwantar da tarzoma tare da jansa wacce ...
Duk fitta gidan sukaye inda Ameera ta bi mijin ta suka shiga Mota suka ƙara wuta sai a wanan lokacin ne UMMAH ta fashe da wane matsanancin kuka" shikkinan na rasa Ameera meyasa Amira why menene dalilin hakan " Munira da Mama ne suka rarrashi ta cikin dare tagama haɗa akwati biyu nata sai na Munira guda ɗaya dakin Mama ta shiga duk da cikin dare nan suka rungume juna ta fara rarrashi ta sanan ta haɗa da nasiha .
"Ba komai Mama zan ɗauke Munira gobe zan kuma jahar Kano da zama duk da nasan cewa banda kowa kuma banda komai anmman Kano jahar ta ce watakila na haɗu da dangina bazan iya zama a garin nan ba gwada na ja Munira daga wanan shaiɗanin yaron kuma in Sha Allah na mike alƙawarin watarana zan dawo garike idan da nisan kwana , nasan cewa watarana Ameera zata zo gunke watakila ma ta tambaye ke ina muka kuma ke gayyama ta gaskiya cewa muna zama a Kano sai dai babo wane hujja ko dalili da zai sa tasan inda muke da zama domin ne kaina Bansan inda zamuje ba ga wanan takardar duk lokacin da tazo mike da wanan maganar ke bata shi mallakin ta ne na fita daga hakkin ta domin bata dauke ne da wane muhimmanci a cikin rayuwar ta ba......."
Asubar fari Ummah da Munira suka shiga tasha a inda suka shiga motar Kano sai dai mucce Allah ya bada Sa'a tafiya
Shin abunda Amira taye ta kyauta ?
Menene asalin alaƙar dake tsakanin su
Ya zata kaya Umma a Kano
Suwaye dangin Ummah
A hankali zamu kai labarin..
Narnah ƙanwar soja ✔️
https://chat.whatsapp.com/DoFR3n8lLtI1RB5Zd2z2IT
💔RAYUWAR UMMAH💔
BY
NARNAH ƘANWAR SOJA
(Sayeedan Addah).
16/11/2024.
💫 ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION 💫
PAGE 9&10
"Yaushe zake dawo typing! We miss you! Muna son new update!".
Finally Narnah ƙanwar soja is back "Yes am back tare da zazzaffan labari mai ciki da darrusa da tsaƙwarar soyayya duk a cikin RAYUWAR UMMAH.
****************************************
RAYUWAR UMMAH
Tunda suka sauƙa a tasha da mangriba sukaye sallah chan ƙasar wani bishiya addu'a suka shafa nan suka zubawa juna ido cikin tausayawa da ƙaunar juna duk da cewa yau su biyu ne a maimakon su kasance su Ukku sirararan hawaye ne ya biyo takan fuskar Munira Umma ce taye saurin da Katar da ita da cewa " ajiye hawayen nan zai miki amfani wani lokacin yanzu mu fara tunanin ta inda zamu kwana da safe mu shiga gari mu nema gidan haya mu fara sana'a muga abinda Allah zaiye da rayuwar mu " girgiza kai Munira taye kai Umma na bare to yanzu ya zamuyi kwana a tasha nan fa da akwai hatsari" banda abunke yau muka fara kwana a tasha ai tun kuna yara anan nagama kwana daku sai tsoro bayan nan ba'a bunda kika iya " To Ummah zaki fara maganar ke ko ai dai kinsan Ameera " shiru taye tunawa da kar ran mahaifiyar nata ya ɓaci Murmushi Ummah taye ta jawo ta jikin ta suka rungume juna anan suka kwanta asubar fari hayaniyar tasha ne ya fara musu busa akan kunnen su......
Duk inda ya kamata su samu matsakaicin gida a unguwanni talakawa hakan baiye ba har sungaji da neman mafaka gashi yamma ya kawo kai chan kan babban kwalbiti suka zauna duk a gajiye suke ƙafar nan maso buzu buzu kamar an fisgosu daga daji ajiyar zuciya Ummah ta sauke don duk gajiyar ta tafi tausayawa Munira tunda ba wani lafiya gari ta ba jiki duk ciwo chan wani tsoho ya ƙarasu inda suke da sallama amsa wa Sukaye chan ya dube su " Shin da akwai taimakon da kuke nema nan hanyar gida nane tun ɗazon na hange kamar kuna da matsalar muhalli "?!
Charraf Umma ta fisgo zancen kamar damar jira takiye ya kawo karshen zancen " ehh baba gidan hanya muke nema ɗaki ɗaya ne da yarinya na bamu samu ba don Allah ka taimaka mana " murmushi yayi sanan ya dube su da mamaki da maganar ta na cewa Munira yarinyar ta alhali kamar kanwa ce da yayarta " ka taimaka bana " cewar Munira da ta katse masa tunanin sa , ba komai cewar sa ko zo mujee gida na Amman sai kuyi hakuri da yanayin gidan tabbas akwai ɗaki biyu ma Amman dai kuna da kuɗin biya ko dubu ashirin ne a shekara " murmushi Ummah taye " Alhamdullah baba komai mun amince mujee kawai "......
Tsayawa chakk sukaye lokacin da suka tunkaro shiga gidan gaban Umma ne ya yanke ya faɗi ganin gidan kamar gidan karuwai ga ɗakuna daban daban a jire sunkai goma sha biyar ga kuma wasu ɗakunan na matasa maza daga farkon shiga gidan sai madafar girke chan ta hango mata ukku a bakin wane ƙaramin lungu da gidan ko da ta hangu su da buta ta tattabatar da cewa nan nin Bayan gida ne ( toilet kinan).
Kulu ce ta tsaya daga jawo ruwan da takiye daga rijiya ajiye gugar taye ta gyara kallabin ta tana hango Mallam Jauro da ƴan mata kyakkyawa tamkar daga ƙasar larabawa don ma ita Ummah chocolate ce ba kamar Munira da hasken ta yayi fat ba , jin shiru Kulu da a take masifar ta tana jan ruwa taye shiru yasa duk suka zuba mata ido nan suka hango abunda take kallo .....
Gyaran muryar sa Mallam Jauro yayi da cewa " Ga abokiyar zama nan na kawo muku sauran ko koya mata wanan banzan halin naku kinga kawo kuɗin ga ɗakin da zaku zauna yana nuna mata wane ɗakin dake nisa dasu yayi " Nagode sosai Baba Allah ya saka da alheri buɗe jakarta taye nan ta fito da dubu goma ta bashi akan cewa kuɗin rabin shekara ta biya nan ya amsa har yana tuntuɓe, da saure Lantana ta matso bai ankara ba ta bangaje sa tana ƙoƙarin fisqo kuɗin nan suka fara kokuwa abin ba karamin razana Munira da Ummah sukaye ba ganin abinda ke faruwa ........
To be continued…
💔RAYUWAR UMMAH💔
BY
NARNAH ƘANWAR SOJA
(Sayeedan Addah).
08101235739
16/4/2025
💫 ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION 💫
Ga mai bukatar group wattsp kai tsaye kiye magana da Admin ta wanan number na sama ...
Chapter 11 : Gidan Duhu
Ruwan sama yana tsiyaya kamar ana zubar da kukan da zuciya ke ɓoyewa. gidan ba gini ba ne – tamkar mafarki ne da aka yi masa hijira, tsakar gidan cike da laka, bango mai ƙyalli da datti, ƙofar da bata jin murya sai da ƙarfi. a nan ne aka sauke su – ita da diyarta, bazawarar da bata da komai sai tarihin da ba kowa ke son saurare ba.
Bazawara ce amma ba ta rasa komai ba idan ba angayamu ku Munira tayi aure ba bani wanda zai kawo hakan a ransa , domin tana da rauni mai kama da ƙarfi. Zuciyarta na ɓoye ɓarna, amma idanunta na nuna ƙudurinta: zata fara sabuwar rayuwa, ko da kuwa cikin barikanci da cakuɗaɗɗen mafarki."
“Ummah kin ce zaki dawo?” Inji yarinyar