Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

rungumeshi Yana fadin daina kuka Yarima Addu'a ya kamata kayiwa Bintu adai adai wnn lokacin Addu'arka take buk'ata, in har kacika masoyinta,
Kasani ko wanne Mai Rai zai mutu muyiwa kanmu fatan cikawa da imani Bintu lokacinta ne yayi."
Hakan sarki yayi ta kwantarwa Abdullah da hankali har yayi shuru ya daina kuka ya koma Kukan zuci wanda yafi komai zafi,
Hakan aka d'auki Bintu akayi Mata sallah snn aka kaita gidanta na gaskiya."

Sai da aka Kai Bintu aka dawo snn Jamila tafito daga b'angarenta tana kukan munafurci tana fad'in bintu da Sauban Allah ya jik'anku hak'ik'a munyi Rashi babba a gidan nan"

Kyara kalamanki Sauban Yana raye bai mutuba,
Sautin muryar Hajjah taji ya dura a kan dodon kunnenta,
Wanda yasa tayi saurin d'aga Kai a zabure ta kalli Hajjah da Anna sai Kuma Sauban dake kusa da Anna Yayi shuru Yana kallon kowa d'aya bayan d'aya bini bini sai ajiyar zuciya Yake saukewa
jama'a duk sun zagayesu ana amsar gaisuwa."

Kallon da Jamila tabi Sauban dashi cikin firgita yasa Hajjah ta d'ora a alamar tambya a kanta, hakan Anna wacce ta anyana a ranta tabbas mutuwar Bintu lokaci d'aya akwai wata sarka'nkiya a cikinta Amma insha Allah komai zai bayyana gaskiya zatayi halinta."

Saitin muryar Hajjah ta kumaji tana fad'in " Sauban ba zai mutu a yanzun ba sai ya hau kujerar mulkin mahaifinsa bayan yayi murabus, kalaman Hajjah kenan karo na biyu."

Zaro Ido Jamila tayi cikin sarkewar murya tace "tuba nakeyi ranki ya dad'e nayi kuskure abinda akacemun kenan."

Ta Kuma kallon Sauban tace "zo Nan yarona hak''ika nayi farin ciki da ganinka Cikin k'oshin lafiya Allah ya jik'an mahaifiyarka."

Ko kallon inda take Sauban baiyiba domin ko can dama baya yarda da ita, basa Zama inuwa d'aya da ita,
Sabida duk suka had'a wuri d'aya daga ita sai shi sai tayi Masa mugunta
Musamman idan Abdullah ya d'aukoshi ya shigo dashi sashenta bazai fitaba sai ta fakaici idon Abdullah tayi Masa muguntar da zata sakashi kuka har ya daukeshi ya mayar dashi wurin mahaifiyarsa."

Ganin ko kallon inda take Abdullah baiyiba, taji haushi ta mik'e tsaye tana fad'in Allah ya bamu hakurin rashin bintu."
Bayi suka amsa da Amin gimbiya Allah ya biya ya k'are Mana lafiyarki."

Muryar Hajjah taji tana fad'in Allah yasa da gaske akeyi komai zai fito fili asiri zai tonu za'ayi hukunci marar dad'in ji da sauraro idan gaskiya tayi halinta, daga Abdullah sai Sauban a fagen sarauta domin sune suka cancanta, ko bayan ran kowa a wurin nan."

Murmushin da yafi kuka ciwo Jamila tayi Bata tankawa Hajjah ba illah ma tayi kamar bada ita takeba ta wuce ta fita."

Tana shiga sashenta tashiga cire Alk'yabbar jikinta tayi jifa da ita tashiga Kiran jakadiya, cikin hanzari jakadiya ta zube gabanta,
Jamila ta dubi jakadiya tace "asirinmu Yana shirin tonuwa domin Hajjah ta sakarmun magagganu masu Kama da gugar zana,
Babban tashin hankalinmu d'aya ne Ashe Sauban bai mutuba."

"Bai mutuba ranki ya dad'e to ya akayi hakan ta faru?"

"Abinda nakeso nasani kenan, lallai ansare macijine ba'ayar da kansa ba,
Dole ne mubi ta wata hanya wacce zamu salwantar da rayuwar yaron can,
Domin tin yanzun anfara yimun gorin sarauta cewa daga Abdullah sai.Sauban,
Dafe k'irji jakadiya tayi tace waye yace maki hakan,

Cikin d'aga murya Mai cike da tashin hankali da damuwa tace "waye ya Isa ya furtamun hakan bayan hajjah."

Ta Kuma sakin wata irin dariya tace "ki kwantar da hankalinki Hajjah dake da Sauban duk a lokaci d'aya zan aikaku lahira domin kune damuwata a gidan Nan."

"Kinyi tunani Mai kyau ya uwargijiyata Amma shawarata a Nan a d'an jira har mutuwar Bintu ta lafa sai a aiwatar da wnn aikin,
Wnn karon aikin bokanya ne domin Bintu kad'ai ta gagari bokanya, tinda ankawar da ita komai zai zo cikin sauki, ta Kuma sunkuyar da Kai tace ya uwargijiyata ki natsu ki dinga saita kanki kada a gane wani abin dangane dake,
Ina ganin ko Hajjah wani abin ta hango a idonki shiyasa tayi maki wnn kalamin."

Shuru Jamila tayi tana nazari,
Ganin tayi shuru yasa jakadiya tashi tayi Mata sallama tafita."

Bayan mutuwar Bintu Sauban ya koma hannun Hajjah da Anna Wanda suke bashi kulawa suke taka tsantsan dashi a duk inda zai tafi da Kuma duk abinda zai Sha ko Kuya ci."

Bayan wata bakwai da mutuwar Bintu a lokacin Sauban Yana da shekara hud'u har ya Fara zuwa makaranta Wanda Yardajen direban sarki Yake kaishi ya Kuma tsaya har a tashi ya d'aukoshi ya dawo dashi gida cike da kulawa, Wanda Sauban yarone Mai kaifin basira malamansa suke tsananin sonshi da Alfahari dashi a makarantar."

Babban burin Jamila a Koda yaushe tayaya zata salwantar da rayuwar Sauban takeyi,
Bokanya ta Bata maganin da zata zuba Masa a abinci da zarar yaci to sai dai wani ba shi ba,
Abinda yafi d'aga Mata hankali shine,
Taga Sauban a idonta wuya Yake Mata sai dai daga nesa baya zuwa wurinta Sam, snn ga wasu bayi da kuyangi manya manya majiya k'arfi da aka zuba a b'angaren Hajjah Wad'anda duk Wanda yazo shiga basa barinsa, Daga ciki Kuwa har da ita, duk da dai Bata tab'a yunkurin zuwa wurinba labari ne yazo mata a kunnenta cewa har ita idan taje bazasu barta tashigaba wnn umurnin Hajjah ne"

Ana hakan wani dare ta tashi da amai da zawo sai shekashi takeyi ba sauki,
Hankalin Abdullah ya tashi yashiga kula da ita Yana tausayinta domin duk a tinaninsa itama mutuwa zatayi ta barsa kamar yanda bintunsa ta mutu ta barshi."
Cikin sauri ya d'auki wayarsa yakira family doctor dinsu,
Minti ashirin saiga doctor yazo d'auke da Kayan aiki, yashiga Bata kulawar gaggawa awon farko ya tabbatar masu da tana d'auke da ciki na tsawon wata hud'u Bata saniba."

A zabure Jamila ta mik'e zaune tana zarar Ido tana fad'in "ciki likita nice keda ciki har na tsawon wata hud'u?"

"Kwarai Kuwa ranki ya dad'e cikine dake d'an wata hud'u,

"Alhamdulillah Tashiga furtawa tare da Abdullah Wanda sai murmushi yakeyi Yana dariya tare da yiwa likita babbar kyauta."

Washe gari gidan ya d'auka Jamila ciki ne da ita d'an wata hud'u,
Masu murna sunayi wad'anda ko ajinsu sunfi masu murnar yawa, bayinta da kuyanginta basuji dad'in samun cikin nataba domin sunsan da zarar ta haihu wata sabuwar azabace zata kuma lunkuwa a kan wacce take basu a yanzun,
Domin sun san Akan abinda ta haifa komai zata iya aikata masu, don wani sabon mulkine zata shinfid'a tare da abinda ta haifa d'in."

Labari yakai har cikin fada cewar Jamila tana d'auke da ciki,
Sarki yayi murna sosai sai da yabawa Dan Aiken kyauta Mai tsoka,
Hakan da labari ya Sami Hajjah mere Baki kawai tayi domin ita da haihuwar Jamila da rashinta duk d'aya ne a wurinta."

Samun cikin Jamila shine ya janye Mata hankali wurin salwantar da rayuwar Sauban domin tana ganin da zarar ta haihu idan namiji ta haifa Dole ne ya gaji sarauta."

Anan hakan cikinta ya girma ya shiga watannin haihuwarsa,
Wani dare ta tashi da nak'uda ta haifi d'anta namiji,
Sak ita komai nata da d'an iri d'aya ne."

Murna a wurinta da danginta abin ba'a magana,
Ranar suna yaro yaci suna SADEEQ."

Anyi bikin suna na kece raini,
Amma Sam ko k'adan bai Kama k'afar bikin sunan Sauban da akayiba,
Hakan akayi aka watse lafiya, taci gaba da renon d'anta Wanda ta d'auki burin duniya ta d'ora a kansa,
Bata Bari kowa ya d'aukar Mata yaro, hatta jakadiyarta Bata Bata Sadeeq a cewarta za'a iya Bawa jakadiya kud'i masu yawa Dan ta salwantar da SADEEQ Dan ta lura da jakadiya bak'in kwad'ayine da ita da Kuma son abin duniya,
duk a tunaninta abinda takeyi shi kowa keyi." Hatta da sarki idan ya aiko a d'aukar Masa shi, Bata bayarwa sai dai tace acewa sarki bacci yakeyi idan ya tashi zata aiko dashi,
Har sarki ya daina aikowa a d'aukar Masa sadeeq
Wanda Hajjah ko da Wasa Bata tab'a aikowa a d'aukar Mata Shiba indai Abdullah ya d'aukoshi yashiga dashi wurinta zata amshesa tayi Masa Wasa har tabawa Sauban shima yayi Masa Wasa idan zai fita ya daukeshi ya fita dashi."

Ana hakan Sadeeq Yana cika shekara biyu a duniya a lokacin Sauban Yana da shekara shidda, Jamila ta Kuma samun wani cikin ta Kuma haihuwar d'a namiji aka sanya Masa SAGEER, Kuma haihuwar d'a namiji da tayi ta dingajin kanta tafi kowa a gidan daga ciki kuwa har da hajjah jitakeyi tafita
Sai wani sabon salon iyayi ya tashi a gidan ganin d'iyanta biyu duk mazane gado nata ne." Dan hakan. In har tana raye ba Wanda ya Isa yayi mulkin masarautar nan bayan Abdullah sai yaranta domin ko a lissafi Bata Sanya Sauban domin ta San wurin da ta ajiyeshi kallon matance take Masa."


*Hmmmmm d'an hakin da karaina......ku iyar Mata friends*






*Mrs Ana's Bawa*โœ





*Hmmmmm muje zuwa friends da fatan kuna biye Dani Kuma Kuna fahimtata*





*Mrs Ana's Bawa*



*Mrs Ana's Bawa gusau*๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜




Yawan comment yawan typing idan naga ba'a comment to zai koma na kud'i KO a jikina๐Ÿคท๐Ÿปโ€โ™€



One luve my friends



Mrs Anas bawa ce,
Muje zuwa wnn karon naxo mku da wani sabon salon labari a kyauta๐Ÿ‘Œ๐Ÿป




*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*โœ



๐Ÿคด *D'AN SARKI SAUBAN*๐Ÿคด



Writing by
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Basheer_)




*DIDECTED TO Fateemah M Uthman*





*Page 9*



Hakan Jamila taci gaba da kula da yaranta Bata yarda kowa ya rab'e inda suke, bare a Kai ga d'aukarsu,
A kullum tunaninta za'a iya zuba masu wani mugun Abu a cikin abinci suci su mutu."

Kuyanginta ma tare da bayi, kullum cikin sabuwar wahala suke tare da Azabtarwa musamman idan taji kukan d'aya daga cikin 'ya'yanta to tabbas duk Wanda Yake kusa da d'akin da suke sai ya gane kurensa Dan yinin ranar a tsakar Rana zai k'are yininsa baci basha."

A kwana a tashi ba wuya Wanda a yanzun Sauban Yana da shekara 12 a duniya Sadeeq Yana da shekara 6 Sageer Yana da shekara hud'u, makaranta d'aya suke karatu tare da Sauban Wanda a yanzun Sauban yake mataki na k'arshe a primary school d'insa jarabawar fita sukeyi."

Sauban Yana tsananin son Yan uwansa Sadeeq da Sageer domin duk abinda yasamu a makaranta bashida wani buri illah ya Bawa Yan uwansa,
Snn duk Wanda ya Dakar Masa Yan uwa a lokacin za'aga b'acin ran sa, don komai girmansa sai ya Rama masu,
Hakan yasa soyayya tashiga tsakaninsa da Sageer a duk inda kaga sauban a makaranta Yana tare da Sageer, a tare suke cin abinci Wanda Sauban yake zuwa dashi,
Domin shi bayacin abincinsu, wnn umurni ne daga Hajjah tin Yana k'aramunsa take lurar dashi,
wnn dalili yasa ba komai yakeci ba, kwata kwata bayacin wani abin idan ba a hannun Hajjah yafito ba, ko a makaranta baya sayen komai sai dai ya sayawa 'yan uwansa musamman Sageer da jininsu yafi had'uwa, Wanda shine k'arami a cikinsu,
Sadeeq Kuma sak halin mahaifiyarsa ya d'auko, baya k'aunar Sauban ko kad'an,
Ko a makaranta Yana yawan had'a Masa tarko cikin ikon Allah Sauban Yake k'etarewa kasan cewar yaro ne shi mai tsananin wayo, Yana kallon kowa tsaf yasan Wanda Yake sonshi yasan Wanda baya sonshi."

A na hakan Sauban suka kammala jarabawarsu ta primary aka had'a masu biki na musamman,
Wanda harda sarki da Abdullah tare da Hajjah suka halarci bikin yayewarsu makarantar primary."

Hakan Jamila itama tazo domin tana da labarin cewa harda Sauran classic za'a Bawa d'alibai kyauta wad'anda sukayi na d'aya Dan tana da yak'i nin har da yaranta a ciki saboda tana kiran malaman a bayan fage tana basu kud'i Dan su rik'a Bawa yaranta na d'aya ako WANNE k'arshen zango kamar yanda taga Sauban Yana d'aukar na d'aya,
Domin ta fahimci Sageer da SADEEQ ba wani k'ok'ari ne dasuba musamman Sadeeq, Dan har k'ara Sageer Wani lokacin Sauban yakan zaunar dashi ya koya Masa karatu idan suna makaranta." Sab'anin Sadeeq da ba abinda yasani sai mungunta dason nuna mulki da Isa tin Yana k'aramunsa sak halin uwarsa๐Ÿ‘Œ๐Ÿป"

Biki akeyi kowa sai murna yakeyi musamman Maimartaba da Abdullah da sukaga Ankira Sauban ya bud'e taro da Addu'a cikin harshen larabci, cikin natsuwarsa da kamalarsa tare da k'asaitarsa Mai fitar da kwarjininsa na jinin sarauta,
Bayan ya gama Addu'ar bud'e taro cikin harshen larabci snn ya koma magana cikin harshen turanci irin turancin Nan Mai kyau irin na mutanan England, tamkar ba'a bakinsa harafin turanci yake fitowaba,
Dad'i tamkar ya kashe duk wani masoynki sauban dake wurin
,
Amma Banda Jamila da takeji Ina wuta ta jefashi Dan bak'in ciki sai fad'i take a ranta tsinanne Mai halin uwarsa kaima ka kusan zuwa Ina tsinanniyar uwarka tatafi"

Bayan ankammala komai aka Fara bada kyaututtuka, inda Sauban ya samu kyauta ta musamman. Domin duk wani Mai fad'a aji Wanda ya halarci taron sai da yabawa Sauban kyautar ban girma tare da burgewa."

A nan aka zo Sauran classic duk d'alibin da yayi na d'aya, a ka shiga Kiran sunansa d'aya bayan d'aya ana basu kyauta, Jamila sai murmushi takeyi tana gyara hannu tana jiran Akira yaranta taje da kanta ta k'arb'ar masu Dan Bata buk'atar wani yaje ya amso masu." _halinki ba kyau jamila_ ๐Ÿค”
Sai da aka kammala Bawa ko wanne class taga ba'a Kira yarantaba haushi da takaici ya k'umeta,
Wayyo Allah kuxo kuga fuskar Jamila ganin ba'a Kira yarantaba bak'in ciki kamar ya kasheta ganin ko wanne yaro sai d'aga kyautarsa Yakeyi Yana Bawa mahaifiyarsa Amma Banda yaranta,
Lura da hakan da Sauban yayi yasa yasaki murmushi ya tako yazo wurin k'annensa ya janyo hannunsu zuwa jikinsa ya rungumesu Yana lallashinsu tare da cewa kuyi hakurin kunji k'annena,
Wani time d'in kuyi k'ok'ari, ku daina Wasa a karatu ,
Kuma za'a baku kamar hakan kunji."

Sadeeq ya fisge jikinsa daga jikin Sauban ya nufi wurin mahaifiyarsa Yana sharar hawaye,

Sunan Sauban akaji ana Kira cikin abar magana Wanda tasaka kowa natsuwa,
Cikin takunsa yanufi wurin da ake kiransa a gaban governor yaje ya tsugunna Wanda shine yasaka akirashi,
Governor yana murmushi Yana kallon Sauban ya d'auki wata kyauta Mai girman gaske Wacce aka lullub'eta a cikin wata Leda Mai haske da kyalli,ya mik'awa Sauban."

Hannu biyu Sauban yasaka ya amsa cike da girmamawa Yana godiya, ai Kuwa aka shiga yi masu hotona,

_wayyo mutuwa kozo kuga idon jamila_๐Ÿ˜‚

Idon kowa Akan Sauban ya mik'e a gaban governor Yana tafiyarsa cikin natsuwa yana d'auke da kyautarsa a hannu kowa sai kallonsa yakeyi Kai tsaye wurin Jamila yanufa ya durk'usa gabanta ya mik'a Mata kyautar
don ta Sanya Masa Albarka,
Ido kansu kowa sai kallonsu yakeyi cike da burgewa
Wad'anda suka San komai sun zuba Ido domin ganin yanda zata karb'eshi,
Ganin Ido kanta snn ga Abdullah da sarki Suma kallonta sukeyi suna murmushi,
yasa tasaki dariya ta k'arb'i kyautar tana murmushin Yak'e Wanda yafi kuka ciwo ta dafa kansa tana fad'in, d'ana kayi k'ok'ari sosai Allah ya taimaka."

ai Kuwa aka shiga d'aukarsu hotona sai murmushin takeyi tana k'ara rungumo Sauban zuwa jikinta, a can cikin zuciyarta kuma jitakeyi kamar ta kurma ihu akan bak'in ciki,

Ganin idanu sun janye kansu Sauban ya koma wurin maimartaba ana hotona yasa tana ganin hakan tayi saurin mik'ewa tsaye tabar wurin tare da Jan yaranta suka shiga mota tanufi gida."

Murmushi manyan Hajjah tasaki domin Sauban ya matuk'ar burgeta da yayiwa Jamila hakan,
Don ko yanzun zata gane idan Rana tafito tafin hannu baya rufeta."

Ana hakan taro ya watse sarki ya dawo gida cike da farin ciki da annashawa, hakan Abdullah sai dai Jin zafinsa d'aya Banda Sadeeq da Sageer Wurin bada kyauta kamar yanda yaga ana Bawa Sauran d'aliban da sukazo na d'aya, yashiga tinanin
Kodai basa karatun ne?"

Hakan yasa suna sauka a mota ya nufi b'angaren Jamila,

Sageer da SADEEQ kwance a kan jikinta tana lallashinsu Sadeeq Yana fad'in Muguntace Sauban ya masu shine ya Hana a basu kyauta a makaranta Wanda Sageer yake cewa ba laifin Yaya Sauban bane laifin uncle ne,
Jamila ta dakawa sageer tsawa tare da zare masa Ido tana fad'in wnn yaron da a asibity na haifeka da nace anyi mun canjenka domin na lura gaba d'aya baka biyo halina ba,
Da zarar anfad'i laifin Sauban yi kakeyi kamar kafashe da kuka, ko ka dakemu,
To bara kaji ka bud'e kunnenka da kyau kaji Sauban ba masoyinku bane Dan ba d'ana bane banice na nahaifeshe ba, kaga ku biyun Nan ku kad'ai na haifa,
Sauban d'an ubane abokin gabarku ne, ko kashesa kukayi ba abinda zai faru, domin idan Baku kashesa ba kunaji Kuna gani zai hau kujerar sarauta,
ku Kuna gefe kuna kallo sai yanda yayi daku kun Zama 'yan kallon kenan."

Sallamar Abdullah yasa taja bakinta tayi shuru illah ta had'e fuska domin Bata ga alamar Wasa a tare dashi ba."

Wuri ya samu ya zauna cikin d'aure fuska tace "barka da shigowa,

"Yawwa yace snn kuyangi suka zagayeshi da kayan motsa baki."

Kallonsa Sadeeq da Sageer sukeyi domin ba'a koya masu gaisuwa ba, shima bai damuba domin yasan irin tasu tarbiyar kenan,
Wanda yayi fad'a har ya gaji ba wani sauyi a tare dasu,
Kallonsu yayi snn ya d'aga masu hannu alamar su zo wurinsa, cikin sauri Sageer ya riga Sadeeq zuwa suka zauna a gefensa."

Kallonsa Jamila tayi ta d'anyi murmushin tace yarona Sauban yayi k'ok'ari sosai."

Shima murmushi yayi ya Kuma had'e fuska ya kalli sadig da sagir yace "meyasa bakuzo na d'aya aka Baku kyauta ba Kuma makaranta kamar yanda aka Bawa kowa?"
Ashe dama ba karatu kukeyi ba?"
Baza kuyi koyi da yayanku Sauban ba?"

Sageer yace munaso Abba,
Sadeeq yace "Ni nafison nafishi ta ko Ina."

Murmushin Abdullah yasaki domin ya dad'e da fahimtar duk halin mahaifiyarsa sadeeq ya d'auko,
Yace "tayaya zakafishi bayan baka mayar da hankali a karatu ba,
Gargad'i na k'arshe da zan Kuma yimaku shine duk kuka kuskura hakan ta Kuma kasancewa sai na d'aukar maku mataki."

Jamila tayi karaf tace "tayaya?"
A'a nifa bana son hakan, duk abinda ya faru da akwai wata a k'asa,
Kai kutashi kushiga daga ciki Allah ya rayamunku domin Ni ka d'ai ke sonku a cikin gidan Nan."

Suka tashi cikin sauri suka nufi d'akinsu,
Ido kawai Abdullah ya zuba Mata baice da ita komai ba ya tashi ya fita Yana tir da Hali irin nata."

Fitarsa b'angaren Hajjah yanufa ya d'auki Sauban ya fita dashi yanufi Gidan gonar mahaifiyarsa, Wanda ya lura da Sauban Yana matuk'ar son zuwa wurin Yana Jin dad'in KASANCEWARsa a cikin gidan gonar Koda yaushe tamkar mahaifiyarsa bintu

Sai kusan k'arfe bakwai suka dawo gida,
BaYan ya Kai Sauban b'angaren Hajjah snn yawuce masallaci sukayi sallar magariba tare da maimartaba suna cikin masallacin akayi Isha'i kamar yanda suka Saba a kullum,
bayan sun kammala yin sallar ne suka fito a tare suna tafiya dogarai na biye dasu a baya
Sarki yake cewa "Abdullah ya kamata kayi aure ka maye gurbin Bintu Wacce ta mutu,

Murmushi kawai Abdullah yayi bai tankawa mahaifin nasaba,
Sarki yaci gaba da cewa idan ka shirya ko a gobe zan d'aura maka aure, sai dai wnn karon mata biyu zaka aura a lokaci d'aya domin inason lokacin da zan sauka a kan kujerar mulki idan za'a d'oraka akai ya zamana kana da Mata hud'u kamar yanda aka San ko wanne sarki,
idan ka cireni daga ciki koni akwai dalilina nayin Mata d'aya."

Murmushi Abdullah yasaki baiyi magana ba domin koshi Yana da buk'atar k'arin auren koba komai ya dinga samun kulawa ya Kuma dinga samun natsuwa idan buk'atarsa ta motsa domin Jamila yanzun Bata da lokacin komai sai mulki dasaka a gaba da hidimar yaranta."

Sarki yace Kai nake saurare meye ra'ayinka ko baka buk'ata ne?"

Girgiza Kai Abdullah yayi cike da girmamawa yace "duk abinda kace shine dai dai,
Bana da zab'i sai naka a kullum burina nayi maka biyayya na faranta maka nasaka ka farin ciki, ko yanzun ka shirya Nima a shirye nake za'a iya d'auramun auren da ko wacce macce kake so zan karb'eta hannu biyu."

Sarki yaji dad'in furucin Abdullah Wanda sai murmushi yakeyi Yana girgiza kai,
Ba Wanda ya sake yin magana a cikinsu har Abdullah ya Kai maimartaba d'akinsa kamar yanda yasaba idan suka dawo sallar, sai ya kaisa har d'akinsa snn yayi Masa sallama yafito yanufi d'akin Hajjah itama yayi Mata sallama snn yanufi nashi d'akin domin ya kwanta,
Wnn karon bayan ya Kai maimartaba d'akin nasa wuri yasamu a gefensa ya zauna tare da sunkuyar da Kai Yana jiran ya Sanya Masa Albarka kamar yanda yasaba snn yatashi yafita."

Sarki ya juyo ya dafa kansa kamar yanda yasaba yashiga "fad'in Abdullah Allah yayi maka Albarka Allah ya sanyawa rayuwarka hak''ika wnn biyayya da kakeyimun Allah yabaka d'anda zai lunka maka fiye da hakan , snn kazama cikin shiri gobe za'a d'aura maka aure da wasu tsala tsalan bayi wad'an da Aka 'yanta Naga sun dace da Kai Allah yabaku zuri'a Mai Albarka."

'Ameen Abdullah yace Yana murmushi Mai cike da jin dad'i."
Wayarsa tayi ringing yayi kamar bazai d'aukaba sarki yayi murmushi yace ka d'auki wayar Mana."

Cikin sauri ya Sanya hannu a Aljihu ya d'auko wayar,
Ganin sunan Abokinsa ne Wanda suka tashi a tare wato sarkin Bauchi Wanda mahaifinsa ya rasu aka d'orashi a kan kujerar mulkin,
Yana murmushin ya d'aga wayar tare da karawa a kunnensa da sallama a bakinsa, cike da tsokana Yake fad'in ranka ya dad'e sarki Allah ya k'ara maka lafiya ya kake?"

Murmushi Abdulrahaman yayi yace "yau Kuma 'yar zolayace "to kiranka nayi domin nayi maka Albishir Sarauniya ta haihu ansami 'ya macce."

Masha Allah Abdullah yashiga fad'i tare da cewa Ina kusa da Abba gashi ku gaisa sai ka fad'a Masa."

Jin hakan sarki yasan Abdulrahaman ne sarkin Bauchi yakira Abdullah domin shi kad'ai ne Yake kiransa Abdullah idan suna tare wani lokacin ya kan k'arb'i wayar su gaisa tare da lurar dashi akan abinda ya shege Masa duhu akan lamarin sarauta, kasan cewar mahaifin Abdulrahaman Amine ne a wurin sarki mahaifin Abdullah."

Sarki ya amshi wayar ya kara a kunnensa Yana murmushi bayan sun gaisa,
Abdulrahaman Yake fad'awa sarki anyi Masa haihuwa ansami 'ya macce,
Kasancewar matansa hud'u ba Wacce ta tab'a haihuwa sai yanzun."

Masha Allah sarki yace tare da fad'ad'a fara'arsa yashiga fad'in "Allah ya raya SAUDAT yasanya Mata Albarka."

Murmushi sarki Abdulrahaman yasaki domin yaji dad'in sunan da sarki yasaka ma 'yarsa, yashiga fad'in Masha Allah sunan yayi dad'i Abba Allah yak'ara girma da d'aukaka, tabbas ada nayi rashin mahaifi Amma a yanzun samunka duk ya kawar mun da Kashi hamsin a cikin d'ari na Rashin mahaifi da nayi, nagode Abba,
yashiga godiya sarki Yana amsawa Yana murmushi snn ya mik'awa Abdullah wayar."

Abdullah ya k'arb'a Yana fad'in sunan 'yarmu Saudat lallai Abba ya it's zab'en suna Mai dad'i, Allah ya raya Mana ita sai munshigo bikin suna gaba d'ayanmu."

Hakan sukayi sallama ya kashe wayar,
Snn yayiwa maimartaba sallama ya tashi ya fita cike da farin cikin gobe ne d'aurin Aurensa snn Babban Amininsa ya samu k'aruwar 'ya macce wacce sarki ya SAKAWA suna "SAUDAT."

Washe gari ya Kama ranar juma'a kenan a babban masallacin k'ofar gidan sarki bayan an kammala sallar juma'a aka d'aurawa Abdullah Aure da bayinsa Khadija da Aishat, d'aurin auren da kowa ya shaida."

Wanda Jamila sai dai ta tsinci maganar daga sama bayan anyi komai angama,
Anan take sarki yasaka aka gyarawa kowa part d'inta kasancewar part 4 a b'angaren Abdullah,
Wnn aure ya ba k'anwata Jamila rai musamman da taji duk bayine aka 'yanta Kuma aka aurawa mijinta."

Jikinta baiyi sanyiba sai da safiya ta waye suka shigo gaida ita, anan taga zallar kyau da kwarji, batasan lokacin da idonta ya rufeba tashiga surfa masu ashar tare da korarsu daga b'angarenta."

Kasan cewar sun san halinta Sarai yasa ko wacce daga cikinsu hankalinta bai tashiba illah ma suka sakar mata murmushi suna fad'in Allah ya hushi zuciyarki, dama Yarima ne yace muzo mugasheki ba Wai yin kanmu bane,
suna fad'in hakan suka tashi suka bar Mata sashen nata."

Tabd'i jam Ashe tsugunne Bata k'are kenan tinda Abdullah ya auro wad'an Nan tsala tsalan Yan Mata tabbas tasan ko kallon banza a yanzun Bata ishesaba yo Mai zaiyi da ita Yana ganin wad'an Nan Yan Mata wad'anda bata inda Allah ya ragesu,

Ga wani sabon rainin wayo

Please Login or Register in order to submit comment