Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuma zai fara neman mata?





Thanks for reading, ayi sharhi filis, sharhi is life ๐Ÿคช๐Ÿคช๐Ÿคช๐Ÿคช๐Ÿคช.






Comment
Like & Share.






~Zeexee ce~ ๐Ÿ–Š๏ธ๐Ÿ–Š๏ธ๐Ÿ–Š๏ธ
[8/30, 1:19 PM] Abokiyar Fight๐Ÿ’œ๐Ÿ’–: ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน
๐ŸŒน
*BANBANCIN KABILA*
_(Short story)_
๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน
๐ŸŒน

*TAMBARI WRTER'S ASSOCIATION*

*_๐Ÿ”ฑ((Home of Expert and Talented writers, da tambarinmu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'umah))_*

*T.W.A*








____________________________________

https://www.facebook.com/Tambari-writers-Association-106058867819812/
____________________________________




*WRITTEN BY ZAYNAB* _(zeexee)_

MARUBUCIYAR

*-RAYUWAR HUSNA*

*-MAHAKURCI MAWADACI (2020)*





```Dedicating this page to Fatima Zarah Eyman aka abokiyar bus๐Ÿคญ๐Ÿคญ๐Ÿคญ๐Ÿคญ๐Ÿคญ. I love you loooodie loooodie```




7๏ธโƒฃ&8๏ธโƒฃ






_Bismillah_






"Babe wake up, it's time". Olamide ta tashi Nafisa.
"Dan Allah habibty ki bari in ankira sallah, wallahi jiya ban yi barci da wuri ba". Nafisa ta fada.
"With all the warnings, kuma kin san bazan tashi ban tashe ki ba ko"?
"Am sorry, bari in tashi kafun kiyi fushi dani".
"Ko ke fa". Olamide ta fada.
Da kyar dai Nafisa ta tashi, tayi alwala, ita kuma Mide, ta riga ta fara sallah.


"Kai habibty, today is going to be stressful fa, ki ci abinci da kyau". Nafisa ta fada.
"Wallahi na koshi haka. Ko so kike inyi loosing din shape dina ne"? Olamide ta tambaye ta tana daga gira.
"Toh! A yau kuma?
Ai ke kam no matter what you eat, ba zaki taba yin kiba ba. Just imagine, ni dake zamu narka abinci, at the end of the day, kiga ciki na ya karu, amma naki na nan flat".
"Kai habibty, banda karya fa?
Kema fa cikin ki ba wani babba bane, sai an lura ake gani".
"Ae, ai still dai ana gani ko"? Nafisa ta tambaya
"Ban sani ba". Olamide ta amsa mata tana yatsina fuska.
Ta kara cewa "ni dai kiyi sauri mu wuce, indai abinci ne, zamu samu a cafeteria"
"Toh naji uwar masifa". Nafisa ta fada
"Yauwa uban masifa".



Suna isa school, suka fara zuwa bursary, suka bada receipt, dan daman sun riga sun biya school fees din su a bank. Daga nan suka fara biyan student unions, sukayi online reg ma. Arannan dai sun dade a school, dan basu bar school ba, sai misalin 5:30pm.
Agajiye suka koma gida. Suna shiga gate din gidan, wasu neighbours dinsu su biyu, suma student ne, suka rungume su. "Oyoyo Olami's" daya daga cikin su mai suna Hafsat ta fada.
"Oyoyo my yar'fara". Olamide ta amsa.
Nafisa kuwa, abun ya kai mata har wuya. Ta tsani taga ana shishige ma habibtyn ta haka.
"Ooh Olami's, ko dan kiban nan baki yi ba. Ni na rasa irin wanan jikin naki, ba ya karuwa, kuma baya raguwa". Halima dayan kenan, ta fada. Halima da Hafsat, dakin su daya suma.
Gidan da suke, one room apartment ne, bedroom, kitchen, and toilet. Kuma apartments hudu ke gidan.
"Nima na rasa roomie. Kuma gata da zubin fulani. Abun dake bata show, shi ne inkaji ance Olamide. Nan ma in baka san ita bace, toh zaka nima Olamide ka rasa". Hafsat ta fadi.
"A'a Hansey, kar muyi haka da ke. Kuma bari mu shiga daga ciki tukun, kunga yanzu agajiye mu ke". Olamide ta fadi.
"Awww, haka ne fa. Fisa baby, ya gajiya, na ma manta kina wajan". Hafsat ta fada.
Nafisa kuwa ta riga ta cika, tayi fam, amma bata son su gane, sai tayi faking din murmushi, ta bar wajan. Olamide ko ta riga ta san abun dake damun kawar ta, sai tayi murmushi, ta ce masu Hafsat "zaku biyo mu dakin mu ne yanzu, ko kuma sai bayan isha ku shigo kaman yanda kuka saba"?
"Hmmmm, zamu zo bayan isha, saboda alokacin hira ke yin pepper ko Hafsah"? Halima ta tambaye ta.
"Ae hakan ma yayi. Amma Olamis, baki kyauta ba, ko kiyi tambayan su Khausar da su iklima".
"Awww sorry, na ma manta da su wallahi". Olamide ta fada
"Sun ce sai next week zasu dawo. Kinsan Khausar da Hafiza cousin's ne, kuma rana daya suke zuwa. Su Iklima da Mufida ma, suma sunce sai next week".
"Gaskiya ne, zamuyi complete kenan next week. Allah ya dawo dasu lafiya".
"Amin". Halima da Hafsah suka amsa.
"Yauwa, kunga bari in shiga ciki, na gaji sosai". Tana fadan haka, ta bar wajan, bata ma tsaya jin amsan su ba.


Data shiga ciki, ta samu Nafisa ta jingina da pillow, tayi lamo kaman bata jin dadi. Ta cire hijabin ta, tayi hanging din jakar ta, ta sa takalmin ta amazunin shi, sannan taje kusa da Nafisa, ta taba ta, tace "ya akayi ne habibty, tun awaje naga mood din ki ya chanza".
Sanda tayi wani nishi, ta ce "babu, me kika gani"?
"Don't ask me that, na san akwai abun da ke damun ki, ki fada mun mana please, kar ki bari hankali na ya tashi".
"Babu komai fa, am just resting ne kawai".
"Please stop telling me that, kin san bana taba kaunan in gan ki ahaka, hankali na na tashi". Olamide ta fada helplessly.
"Ba komai my habibty, let just say ina missing din gida ne".
"Ban yarda ba Nafisa, ban yarda ba. I thought am like a sister to you, then what is my role as a sister"? Mide ta tambaya.
"To always be there for me in any situation, and vice versa".
"Then why are you not letting me play my role". Alokacin, har idanuwan ta sun kada.
"Bakomai, kawai dai, kawai dai". Bata iya completing din statement din ta ba, ta fashe da kuka.
Abun so ya samu, Olamide ma ta fara kuka. Sai suka rungumi juna suna kuka, Olamide na rarrashi Nafisa. Cikin kuka Nafisa ta ce "na sani inga ana miki shishigi, yana kona mun rai, na tsani inga mutum na nuna maki so agaba na, sai in dinga jin wani iri. Wallahi na dauke ki tamkar yar'uwa ta ta jini, shi yasa kika ga nake kishi akan ki. Kina nuna mun son da maybe in ma ina da yaya ko kanwa, da kyar sununa mun. Kuma soyayya bai tsaya akan ki ba, harda Mummy da kannan ki, kuna nuna mun so sosai. Shi yasa in naga wata na kokarin shige maki, sai inji kaman za'a kwace mun ke". Ta fada tana kara volume din kukan ta.
"Shiiiiii, ya isa haka habibty, bana son kukan nan, kar ciwon kai ya kama ki". Ita ma ta fada tana kuka.
"Zan daina, amma sai kinyi promising dina ba zaki bar ni ba, zaki tsaya da ni kaman yanda true sisters ke tsayawa da juna". Nafisa ta fada.
"Am not perfect, and I don't know what tomorrow holds, amma ina son ki sani I will always be there for you ore mi( kawa ta)".
"Shikenan, na daina kuka, kema ki daina. Kuma nima na maki alkawari, I will always stand by you".
"Yauwa, ki daina kishi, Fai'za ta Nafisa ne, itama Nafisa ta Fai'za ce".
"Ae". Nafisa ta amsa, tana goge hawaye.
"Kinga tashi muyi alwala, ana kiran sallah".
"Okay toh. Amma me zamu ci ne da daddaren nan, wallahi yunwa nake ji".
"Toh mu ci talliya mana". Olamide ta fada.
"Gaskiya kam, tunda muna da stewssssss".
"Hahhhh, gaskiya kam muna da su".



Da suka idar da sallan magrib, suka sa talliya awuta, kafun isha, har ya dahu sun ci, kafun suyi isha. Suna idarwa, kaman su Halima na ganin su, suka shigo.
"Ooooh yes Olamis, mun zo shan hira. Kinsan jiya da kika dawo, bamu nan, munje gidan aunt dina, nan muka kwana". Hafsah ta fada.
"Hmmm haka ne. Ko dai anje hmmm....". Olamide ta fada tana murmushi.
"Kefa mun chanza, mun daina".
"Allah yasa". Nafisa ta fada.
"Ke zan mazge ki fa". Halima ta fada.
"Ki mazge ta, adalilin me"? Olamide ta fada.
"A'a aunty, kar kiyi fushi. Mun san baki son ana tsokanan habibtyn ki"
"Gaskiya kam bana so, ko kadan". Halima ta amsa.
"Ku manta da wannan, mu sha hiran mu kawai". Hafsah ta fada.
"Ae ku sha hiran ku. Ba shekaran jiya na dawo ba, me ya hana ku zuwa shan hira"? Nafisa ta fada.
"Babu, kema fa kin san mun fita, kuma ai da muka dawo mun dan shigo ai". Halima ta amsa.
"Ya isa. Kun san me"? Hafsat ta tambaya.
"Ya zamu sani"? Olamide ta fada.
"Kai habibty, you always have answers to every question". Nafisa ta fada, tana dariya.
"Kuyi shuru mana". Hafsat ta fada.
"Mun yi". Suka fada a tare.
"Aha, Nabila fa ta kusan aure".
"Wace Nabilan"? Olamide ta tambaya.
"Nabila kawar ku mana, bata fada maku ba ko?
Actually nima dai ba ita ta fada mun ba, naji ne, kin san gidan su ba nisa da gidan aunty na". Hafsat ta fada.
"Ai ko in bata fada mana ba, baza mu je ba ko habibty"? Olamide ta tambayi Nafisa.
"Ae, mu bamu gayyan sodi". Nafisa ta amsa.
"Kai! Why is your blood rushing, ai bata fada ma kowa bako, kuma dai kun san zata fada maku". Hafsat ta fada.
Olamide tayi wani dariya, sai ta ce "abun ya yuwu da dan gombe kenan". Tana fada, suka tafa da Nafisah.
"Toh ku ma yaushe za'ayi naku"? Halima ta tambaya.
"Randa Allah yaso. Kuma kema kin yi ne"? Nafisa ta tambaya.
"Toh ai na kusa, next year In Sha Allahu, maybe june'.
"Allah ya kai mu, amma still you have no right to ask us, tunda ba'a gwanjo ake samo mazan ba". Olamide ta fada.
Duk suka fashe da dariya.
"Gwanjo kuma habibty?
Kin san gwanjo ma akwai grade ko"? Nafisa ta tambaya.
"Ae da anan ake samun su, da zamu dinga zuwa da wuri, dan mu samu grade, ba zamu ba in 9:am yayi , sai dai ya same mu acan". Olamide ta fada.
Duk suka kara fashewa da dariya.
"Kai Olamis, baki da dama. Shiyasa nake son hira da ke. Although kin iya shunning din mutum, amma still kina da ba mutum dariya, but banda angry part din ki, lokacin da kike mantawa kinba mutum nickname, sai ki kira sa da sunan sa". Hafsat ta fada.
"Bari kawai yar'faran habibty, ai in habibty tayi fushi, ta na mantawa da soyayyan da take nuna ma mutum. Kinga in tayi fushi, alokacin zaki ji tana NAFISA SULAIMAN".
Duk suka fashe da dariya.
"Bari kawai ba zaku gane ba. Ai alokacin, nickname baya mun dadin fada, sai dai sunan mutum".
"Toh Allah ya shirye ki. Ya zaki yi da mijin ki, ko shima da sunan sa za'a na kiran sa, in ya kai ki neck"? Hafsat ta tambaya.
"Ke abu kadan miji, baki gajiya ne. Toh ko shima, zan kira sa da sunan sa, so he will know am serious".
"Toh ai it's not my fault, at this stage of life, abun da ya kamata mu damu da shi kenan. In mu kayi aure kuma, mu fara maganan yara". Hafsat ta fa.
"Toh sannu marriage consultant. Kai yar'fara, wanan aikin zai miki kyau fa". Olamide ta fadi.
"Sosai ma". Halima da Nafisa suka amsa.


Su Halima basu bar dakin su Olamide ba, sai 9:39pm. Nan ma, saboda Olamide ta masu complain cewan suna jin barci ne. Inba haka ba, basu ki aita hira ba har cikin dare. Wani hiran ma sai sauran hudun sun dawo.






ใ€ฐ๏ธใ€ฐ๏ธใ€ฐ๏ธใ€ฐ๏ธใ€ฐ๏ธใ€ฐ๏ธใ€ฐ๏ธใ€ฐ๏ธใ€ฐ๏ธใ€ฐ๏ธใ€ฐ๏ธ



Da kyar Abdallah yake cin abinci, saboda tunani ya mai yawa. Of course shi ya san yana son aure, amma da wanda za'ayi shi ne matsalar sa. Ina zai fara. Kuma ko su Umma basu fada ba, shi bazai iya auren cousins din sa ba. Hamma Sudais din daya yi, yaga zai iya ne, kuma ma ai yayi hitting din jackpot, saboda matar shi akwai hankali. Ko adda Wasilan da take cewa ya zaba daga cikin su, ta manta da abubuwan da duka fada akan ta ne, ita da suke cewa zata auri mijin ta ne saboda kudin sa. Amma data yi aure, ta fara fita, tana daukan wanka, suka soya hali, ko wannan su ta zama yar dakin ta, iyayen su ma suka zama abokiyar ta. Ita kuma Adda Bilkisu, tana da kudin kan ta, kar ma ayi maganan na mijin ta, yasa suke ribibi akanta, ita da ma ba'a nan take zama ba, tunda Allah ya buda ma mijin ta, ya samu aiki a dubai, suka fara son ta, harda yayan ta. Basu ki yayan suce masu suzo su taka kan su ba, saboda tsabaragen son abun duniya. Ita kuma Adda Fadila, mijin ta akwai rufin asiri, ba laifi. Dan itama ba zaka ganta ka raina ta ba. Amma abun mamaki, sun raina iyayen su, amma suna son yayan su saboda abun duniya. In shima ya auri daya daga cikin su, shi ma zai zama dan so. But to hell, bazai bi abun da kawu Dajjo ke so ba. In sauran nayi, shi bazai yi ba. Shi zai bi umarnin iyayen sa ne.
"Abdallah! Abdallah!! Abdallah!!! Sanda Abba ya kira sunan sa sau uku, kafun ya amsa.
"Na'am Abba na".
"Naga baka cin abincin ka ne"? Abba ya tambaye shi.
"Bakomai Abba, ai ina ci".
"A'a, Abdallah bamu saba ganin ka haka ba, kai da you are always there to make us laugh". Umma ta fada.
"Toh ai shi ne". Abba ya fada.
"Bakomai. Bana ma jin yunwa, sai da safen ku". Ya tashi zai tafi dakin sa, Abba yace ya dawo.
"Gani Abba na".
"Zauna".
Ya zauna.
"Nasan abun dake damun ka, kar ka damu da abun da tsohon nan ya fada, na shi kawai yake fada. Ni yanzu zan bari ne ya maka auran dole ne?
Kuma in aure ne, lokacin ka ne baiyi ba auta, in lokaci yayi, ba mai iya stooping din shi. Saboda haka, ka saki jiki ka ci abinci".
"Ai kuwa. Ka daina damuwa da bad energy. In yaga sauran na dancing to his tones, toh ai ya kamata ya san mu kam bamu cikin su. Kuma ka auri koma waye, but make sure she will be a good wife and mother to your kids". Umma ta fada.
"Am in support of what your Umma said. Ba dole bane ka auri bafulatana ba, ko bahushiya ka samu kuma ta zauna maka, ko shi bazai daura auren ba, ni zan daura agidan nan. Nine uban ka ba shi ba". Daga yanda yake magana kasan ran Abba ya baci sosai.
"In Sha Allahu, nagode sosai Abba na da Umma ta, Allah yasa ku dade mana, Allah ya saka maku da aljannah, thanks for the support".
"Bakomai, ai responsibility din mu ne as iyayen ka ko Hajaju"? Abba ya tambayi Umma.
"Kwarai kuwa".
"Barci nake ji, gobe ina da morning duty". Abdallah ya fada yana hamma.
"Toh, kuma kar adawo gobe ayi mana complain, dan naga yau da wuri za'a yi barci". Umma ya fada.
"Toh ai ina huta gajiyan yau ne, gobe ma ai zan yi nashi gajiyan ko Abba na". Abdallah ya tambaye shi".
"Haka ne auta na., ko wani rana nada gajiyar sa".
"Wannan kuma ku kukasani" .
"Manta da ita Abba na, kishi take" Abdallah ya fada. Yana magana, Umma ta dau pillow, ta jefa masa, amma yayi sauri ya bar wajan.




Da yaje office, yayi attending to patients, lokacin komawa gida yayi, ya dauki briefcase din sa, ya cire coat din sa, ya rike a hannu. Yana kan tafiya, wani ya kira sunan sa "Dr Abdallah!".
Yana jin sunan sa, ya juya, yana juyawa, yaga abokin shi ne Dr Farouk.
"Bana ce maka akwai magana ba"? Farouk ya tambaye shi.
"Am sorry, na manta ne. Kasan stress din patients dinnan".
"Gaskiya attending to patients ba karamin aiki ba ne". Farouk ya fada.
"Wallahi. So what up"? Abdallah ya tambaye shi.
"Muje mu zauna akan bench dinan dake karkashin bishi yan nan".
Suka je suka zauna, Farouk ya fara magana " Guy kasan ansa aure na da Nabila bayan sungama wanan semestern, amma yanzu sun chanza, wai inba damuwa, ayi shi nan da two weeks, twoo weeks fa". Ya fada yana nuna yatsun sa biyu.
"Congrats man, Allah ya sanya alheri". Abdallah ya fada.
"Am serious fa, kuma kasan worst part din, su Abba sun yarda, wai hakan ya fi". Farouq ya fada.
"Toh me ke ciki, ayi abun da za'ayi kawai ka huta. Yours is even good, mufa yanzu muka fara hunting".
"Toh kai aganin ka hakan ya fi kenan"? Farouk ya tambaya.
"Ae, wallahi, na maka murna fa sosai. Ka ce dai mu fara shirin zuwa kano, ko muma zamu samo wata acan". Abdallah ya fada.
"Toh mashaAllah, tunda abun ya zauna cif, nima nayi relaxing. Amma da'a I was so worried".
"Kar ka damu, your brother in islam is here". Abdallah ya fada.
"Yeah thanks for za support. Sai yanzu ma maganan ka ke flashing. So ba ma raka ni zakayi ba, kaima zaka je neman mata ne"?
"Ae mana, ai yanzu na fara wife hunting, kuma I want it soon, bana son ana raina mu iyaye". Abdallah ya fada.
"Ban gane ba, wake son raina Su Abba"? Farouq ya tambaya.
Nan ya fada mai komai, sai Farouq ya ce "aiko, ko ni am in support. Allah yasa ka samu. Dama ka samu bahaushiya, muga expression din wanan kawun na ku".
"Amin aboki na, muga iya gudun ruwan sa, muga ko zai kashe ni ne, ko kuma me. Shi din daya ke magana, ai second wife din sa bajara ce. Amma ya bi ya takura mana, wai sai bafulatana dole". Abdallah ya fada.
"Kyale shi, dan yaga shi ne babba ai, shi yasa yake mulki akan ku yanda yake so. Aboki na, Allah ya baka bahaushiya, muga karke Kawu". Farouk ya fada.
"Amin ya rab aboki na. Shi yasa neke ji da kai".











```Thanks for reading, sharhi is bea, kaman yanda kuka sani.
```





~Zeexee ce~ ๐Ÿ–Š๏ธ๐Ÿ–Š๏ธ๐Ÿ–Š๏ธ
[8/30, 1:21 PM] Abokiyar Fight๐Ÿ’œ๐Ÿ’–: ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน
๐ŸŒน
*BANBANCIN KABILA*
_(Short story)_
๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน
๐ŸŒน

*TAMBARI WRTER'S ASSOCIATION*

*_๐Ÿ”ฑ((Home of Expert and Talented writers, da tambarinmu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'umah))_*

*T.W.A*

*WRITTEN BY ZAYNAB* _(zeexee)_

MARUBUCIYAR

*-RAYUWAR HUSNA*

*-MAHAKURCI MAWADACI (2020)*






```Dedicating this page to my Kawallie (Hansey)๐Ÿคญ๐Ÿคญ๐Ÿคญ๐Ÿคญ and my kanwas(boddi'am). I love you guys soooo much, long live the three musketeers๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ .```







9๏ธโƒฃ&๐Ÿ”Ÿ






_Bismillah_






Da suka gama hira, Abdallah ya je gidan adda Wasila.
Saboda yanayin sa, ko mai gadin gidan ma bai mai wasan da suka saba.
Da ya shiga ciki, yaran ta na ganin shi, suka san yau kam uncle auta ba lafiya. So they just greeted him, su ka bar wajan. Adda Wasila ma tasan ba kanta.
"Uncle auta! Lafiya kuwa yau"? Adda Wasila ta tambaye shi.
"Ba lafiya, dan na zo ne na miki magana tsakanin kani da yaya".
"Toh Allah yasa dai inji alheri". Adda Wasila ta fada.
"Amin. Gaskiya adda, da zaki ji nawa, ki daina wani kula wannan tsohon familyn mu. Bashi da respect for our parents, even an atom. He talks to Abba anyhow, but you always think his decisions are right, duk da kema ya maki rashin mutunci alokacin da zaki auri Uncle Hussain, ba irin wulakanci da ba'a miki ba, amma yanzu kam na kasa gane direction din da kike". Abdallah ya fada yana huci.
"Toh Abdallah ya kake son inyi, shi ne fa babba fa a familyn mu, so kake inyi disrespecting din sa"?
"Bance kiyi disrespecting din sa ba, amma ki daina sake masu, dan shi ne abokin shawaran ki. Ni ban sani ba ko neman gidin zama kike oho maki. Adda fa duk wanda baya son iyayen ka, baya son ka ne. Kullum fa cikin raina Abba mu yake". Yana magana duk jijiyoyin wuyan sa na fita.
"Gaskiya Abdallah, bazan bari ka zo gida na ba, ka dinga mu maganan banza ba. Ni yayar ka ce, shekaru kusan hudu ke tsakani na da kai, kasan yanda zaka mun magana. Kuma kana cewa neman gidin zama nake, toh na neman. Idan ka shirya yi mun magana cikin hankalin da natsuwa, ka mun, in kuma baka shirya ba, here is the door, you can leave". Ta fada tana nuna mai bakin kofa da hannun ta.
"Wow! Wow! Adda, nagode sosai. Wallahi kina bani mamaki, amma dai tunda kin nuna mun kofa, bari in wuce. Amma karki manta, wallahi in baki guje shi ba, wata rana, sai ya wulakanta iyayen mu agaban ki, kuma ki kasa cewa komai. Amma ki sani, duk randa na samu labari, toh za'a yi ta." Yana gama magana, ya duki wayar sa da ya ajiye akan center table, ya parlor, ya je wajan da suke parking din motoci, ya shiga motar sa. Yanda Lawali yaga yake driving, yasa ya hanzarta, ya bude masa gate. Daya bude masa ma, kaman zai buje shi, sanda ya matsa da gudu.
Idanuwan sa duk sun bi sun kada sunyi jazur, gashi jikin sa sai bari yake. Last time ma saboda maganan kawu Dajjo, su ka samu sabani da ita, kuma fa duk akan wulakancin da yake ma iyayen su ne. Shi bai san wata iri ce ita ba. Wai mutum ka dinga ganin anama iyayen ka nonsense, amma ka dinga jurewa, saboda kana son a dinga yabon ka, toh sun dade basu yabe shi ba.
Driving yake da gudu, ya iso wani green gate, ya fita a motar, ya buga gate, wata farar mace ta fito, mai kama da Abdallah sak, da yaron ta da bazai wuci 2 years ba yana biye da ita.
"Waye ne"?
"Ni ne, ki bude mun". Abdallah ya fada.
"Aww yau kam an tuna da ni kenan". Ta fada tana bude gate din.
Data bude, sai ya shigo, ya bude duka gate din, ya shigo da motar sa, ita kuma tana gafe, dan ta na manne da ita.
Da ya gyara parking, ya fito. Yana fita ya ce "chewing gum din Mummy, baza'a gaishe ni bane"?
Yaron ya ki motsawa, instead, ya kara manne ma Mumnyn sa.
"Mu shiga daga ciki, Afran ka na can, ka bar mun da na".
"Ko baki fada ba, me zanyi da wannan mai kiwan".

Da duka shiga ciki, ya zauna a parlor, Afra na jin muryar sa, ta fito tana "oyoyo Uncle". Ta zo da gudu ta rungume shi. Bata wuci shekara hudu ba, tana kama da Umma takwaran ta. Dan asalin sunan ta Rukayya ne, amma suna kiran ta da Afra. Abdallah na mugun son Afra tamkar shi ya haife ta, although niece din sa ce, but he has a fatherly love for her.
"Oyoyo my Afra. Ya kike"? Ya tambaye ta.
"Lafiya kalau Uncle. Baka tambaye ni ya school ba". Ta fada tana tura baki.
"A'a afuwan Afran Uncle. Ya school"?
"Fine, an bamu homework". Ta fada.
"Toh mashaAllah, adage da karatu ko my Afra?
Kuma fa a dinga zuwa islamiyya, a daina karyan ciwon ciki".
"Ina zuwa, ko Mummy"? Ta tambaya, tana kallon wanda ta kira da Mummy.
"Bawani, sai na hada da bulala kike zuwa". Matar ta fada.


Please Login or Register in order to submit comment