Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 5
ce da Bintu ‘’yo to ki ka cize nan Gimbiya kya iya wad’uwa ba ki sani ba, gide rufa mana asiri mu tai, ke kawai ki ta salati, hallo ka da ki kuskura ki kai kallan ki ga jama’a, hakan ka iya rud’a ki, maza soma ambaton Allah’’ Nan da nan Bintu ta tsinci kan ta ta na mai ambaton Ubangiji. Tsakiyar Uwanlenze da Gwaggo Munari, Jakadiya daga baya, biye da ita bayi goma shabiyu ne, su ka kutsa ta hanyar da aka tanada na musammam domin wucewar Gimbiya. Ba su zame koina ba sai cikin fadar Fabarusa. Kansencewar Masarautar Fabarusa ta yi biyun ta Sa’ayrasa a girma da tsari, ba su Ladiyo ba, hatta Gwaggo Munari sai da ta yi da gaske wajan 6oye shawa’an ta ga Masarautar domin kuwa lokacin da su saka k'afar su a katafariyar fadar Fabarusa, sun ga abin mamakin gaske, wato bayan girman fadar na da ban al’ajabi, kuma yadda aka fasalta ko tsara ginin ta shi ma abin mamaki ne. A tak’aice sai da su ka zamo tankamar k’auyawan da su ka shigo birni. Gini ne irin na gargajiya wanda aka kafa harsashin ginin da manyan duwatsu ma su tsada, wad'an su kamu takwas wasu goma. Tsakanin kowace katanga akwai duwatsu masu tsada wad’anda aka yanka su bisa ga ma’auni san’annan aka dasa itacen al’ul daga gefan su. Tsuntsayen fada iri iri ke shawagi, musammam d’awisu da jin su ne su ka fi yawa. Sai da su kusta sauro gomasha biyu kan su kai ga shiga cikin gidan Sarki, kowanne da na sa irin adon da kayan k’awa, wanda idan su ka shiga wannan su ka shiga na gaban sa sai su ka ashe na baya ba komai ba ne idan aka had’a sa da na gaban sa. 'Bangarn uwar gidan Sarki Abdulrahman, wacce ake kira Goggon nan aka sauke su. In da aka zaunar da Bintu bisa shimfid’a na musammam da aka ta na dar mata daga tsakiyar falo, yayinda su Ladiyo, Hansai, Lanta da Maman Cangwai su ka yi zaune daga gefe matsayin su na bayin Gimbiya. Tuni Barori da Bayi su ka shiga kai kawo da hidima domin tarbar baki cikin aminci ta hanyar tabbatar da ba su bawa Masarautar su kunya ba. Kayan marmari na daga ‘ya’yan itace ne, nama na k’arama da babban dabba kai har da ma na d’awisu, su dubulan ne, caccabe, alkaki da nakiya komai bajau sai wanda jama'ar Sa’ayrasa su ka za6a. Gwaggo Munari na mai jinjina kai cikin ran ta take fad’in ‘’ma su abu da abun sa, gaskiya dukiya cikin wanga masarauta ba a cewa komai! D’iyar bayi ke kuwa Allah ya yankewa kakar saka, amre cikin wanga Masarauta shi an baiwa’’ Ciki su ka bud'e su ka ci su ka yi nak. Amma ita ko Bintu ruwa ma kasa sha ta yi bare ta kai ga cin abinci duk da kuwa azababban yunwa ne ya addabi cikin ta. Bayan an tabbatar su huta ne wata baiwa ta zo ta ce da su idan sun shirya za ta kai su ga masauk’in su domin Gimbiya Fatima ta shirya ta sami fitowa zuwa taron wankan amarya wanda za a yi nan ba da jimawa ba. 🐫🐪🐫🐪🐫🐫 Bintu ɗiyar bayi ce (book 2) Chapter 8 Admin 001SAYYADI SADIQ @Whatsapp 08146934644 8⃣ Sidiya ce.....✍🏼 Shiryayyan d’aki mai had’e da 6and'aki aka aje su Ladiyo, su Bintu kuwa d’aya daga cikin d’akunan Goggon nan a matsayin ta na uwar gida aka sauke su kan a gama wankan amarya a mik’a ta ga na ta 6angaran. Su na shiga masaukin na su ba da jimawa ba, wata baiwa ta sake dawowa d’auke da kaya, gaban Bintu wacce ke zaune bisa gado har lokacin ba ta bud’e fuskarta ba baiwa ta zu6e, ta na mai aje kayan gaban ta, ta ce ‘’ an gaida Gimbiya Fatima, wagga kaya tsaraba ne da ga Goggo nan, ta ce a shedawa Gimbiya Fatima ta sanya su yayinda za ta hito wajan wankan amarya nan ba da jimawa ba’’ ‘’Gimbiya Fatima ta amsa, ta na godiya’’ Cewar Gwaggo Munari. Bayan fitar baiwar Gwaggo Munari ta yaye alkyabbar Bintu, sai ga ta ta yi wuri wuri da ido. ‘’Gimbiya yanzun ga ba lokacin tuntuntuni ba ne, kin dai san dalilin da ya sa ki wanga Masarauta da kuma a gurbin wacce ki ka zo, gwara dai ki sake shawara ki nutsu in har ba so ki ke ki rasa ran ki sa’annan ki haddasa yaki da gaba wanda ka iya halaka ta mu Masarauta gaba d’aya’’ Fad’in Gwaggo Munari cikin gazawa da halayyar Bintu dan kuwa idan ba ta yi da gaske ba ko shakka babu asirin su mai tonuwa ne. A sanyaye Bintu ta ce ‘’ina tuba....’’ ‘’ba tuban ki mu ke buk’ata ba!’’ Gwaggo Munari ta katse Bintu, kana ta k’ara da ‘’ Aikin ki mu ke buk’ata Gimbiya! Wanda za ki fara yanzu ta hanyar zama Gimbiya ba d’iyar bayi ba. Allah ya mi ki zubi irin na jinin mulki, kowa ya gan ki ya san hakan nan Allah ya yo ki, ba ki gada ba amma Allah ya baki su a halittar ki, Dan haka tak’ama da isa shi na ke so daga gare ki, ki saka a ran ki wannan dama ne da Allah ya baki dan jin dad'in rayuwa da kuma taimako ga Masarautar mu, idan asirin mu ya tonu gaba d’aya farin cik’in masarautar mu ne zai koma ga zubar jini, ina fatan kin fahimce ni?’’ Bintu ta gyad’a kai. Kana Gwaggo Munari ta dafa kafad’ar Bintu ta ce ‘’madallah da d’iya ta gari. Sai ki yi shiri yanzu su Ladiyo za su zo su had'a mi ki ruwan wanka. Hakuri za ki yi na san kin saba yiwa kan ki komai amma daga yau komai yi mi ki za ake yi, ki jure Bintu wata rana sai alkhairi’’ Bintu ta dad’a jinjina kai. Ana hakan kuwa su ka ji an sake turo kofa an shigo. Maimakon Ladiyo da Gwaggo Munari ta ce, Lantana ce baiwar da Yarima Nuhu ya za6a ta musammam domin kular masa da al’amran Bintu ta shigo ta zube gaban su. Gwaggo Munari na mai duban ta tace ‘’Lantana gide ke ce mai shirya ruwan wankan ne? yo to ina sauran? Kar dai sun tsaya kallan kauye mu ka biya ku fa sai mu makara!’’ Lantana waccen ita dama da ka gan ta ka ga zubin munafunci, dan ko magana ka ke da ita haka za ka ga ta na sinsin da idanu sam ba ta bari a ga kwayar idanun ta. Ta kada baki ta ce ‘’ai ga su nan tafe, sauri na yo dama na shirya ruwan wankan kada a makara’’ Jin haka Gwaggo Munari na mai mata nuni da bayan gidan da ke cikin d’akin ta ce ‘’yauwa madalla da ke, maza je ki ga bayan gidan can shirya mata gide’’ Sim sim ta shige bayan gida. Sai da ta fara taran ruwa sannan ta shiga had’a ruwan da turaruka iri iri kamar yanda su ka saba had’a ruwan wankan Gimbiyoyi. Ko da ta zo kan turaren karshe, sai ta faki idanun Gwaggo Munari ta tabbatar hankalin ta na kan su Ladiyo da shigowar su ke nan, ta na mu su bayanin yanda ta ke so su kasance wajan taro. Sannan ta jawo kofar bayi ta rufe. Gefan zanin ta ta kwance, ta dauko wani kullin magani, cikin sauri da azanci ta bud’e maganin ta na mai zazzage shi cikin ruwan wankan Bintu. Tuni wani irin bakin hayaki mai wari ya taso daga ruwan yayi sama, ita kan ta Lantana sai da ja baya ta na mai toshe hancin ta cikin tsoran kada fa su Bintu su ji duk da dai Yarima Nuhu ya tabbatar mata babu wanda zai ji warin bayan ita da ta zuba. Sai da ruwan ya dena kumfa da hayaki sannan ta mayar da sauran kullin maganin cikin zanin ta ta kulle, ta fito hankali kwance kamar ba ta aikata komai ba. 🐫🐪🐫🐪🐫🐪 Bintu Diyar bayi.....book 2 chapter 9 to 11 sSayyadi Sadiq ......08146934644 +234 808 323 2323: 9⃣ Sidiya ce......✍🏼 Fitowar ta ba da dad’ewa ba Gwaggo Munari ta sanya Bintu wankan dole dan kuwa ba da san ran ta ba. Da taimakon su ladiyo da Hansai Bintu ta fito fes cikin doguwar riga ruwan d'orawa, rigar da Goggon nan ta aiko mata. Material ne mai tsada ke, sai kuma mayafi kore mai turawa da ratsin ruwan d'orawa. Gwaggo Munari ruke da hannun ta domin kuwa ita ta ke gane mata hanya su ka fito, Su Ladiyo biye da su yayinda aka mu su iso zuwa babban zaure in da mata da iyalan Sarki ke jiran isowar su. Babban zaure ne wanda ya fi k’arfin a k’ira sa da zure sai dai ko d’akin taro, tsawon sa kamu d’ari, fad’in sa kamu hamsin. Haka kuma ko wacce kusurwa na zauren an masa ado da itacen al’ul a bisa ginshishik’an sa. Bayan ga dadduma mai kulliyar jikin damisa da ke shimfid’e tun daga fari har zuwa k’arshen zauren da kuma tintin masu adon jikin damisa da ke baje bisa daddumar, akwai duwatsu wanda aka auna sa’an nan aka yanka su da zarto ciki da baya daidai da juna, aka jera su zagaye cikin zauren tamakar kujerun zama irin na zamani. Haka kuma bangon zauren zane ya ke da tambarin Masarautar Fabarusa. Cikin zauren su ka tadda dukkanin iyalan Sarki Abdulrahman tare da y'anuwa da abokan arziki wanda su ka zo domin ta ya su murna. Matan Sarki Abdulrahman uku wanda su ka had’a da Goggon nan (uwar fada), sai ta biyu wacce su ke kira da Goggo ta dole(uwar dole) sai ta ukun wacce ake kira Uwar Soro, wacce itace mai k’arancin shekaru cikin matan sarki. Kowacce hakimce, k’ishingid’e bisa tuntin. Gaban su kuma wani tulu ne wanda aka masa ado da azurfa cike da ruwa mai d’auke da turare da garin lallel. Haka kuma ‘ya’ya da jikokin sarki da na su wajen daga gefe wanda d’irga su ba k’aramin aiki ba ne kasancewar ‘yay’an sa mata ma su aure da ‘ya’ya sun kai su goma sha takwas, kuma dukkanin su ba su yi k'asa a gwaiwa ba haka su ka zo da sassa da yankunan Jamhuriyar Nijar domin tarbar amaryar d’an uwan na su. Duk da dai ciki akwai mu su bakin cikin lamarin kasancewar ciki d’aya su ke da Yaremi Sadauki. Musammam Yaya Mai Soron Baki, babbar d’iyar Sarki Abdurahman da mai bin mata wato Yaya Jidda wanda su 'ya'yan Goggon nan. Wajan da aka tanadarwa Bintu gaban su Goggon nan aka zunar da ita. Tun da ta yi wanka da ruwan nan na Lantana hankalin ta ya ke a tashe, gashi gaban ta sai fad’uwa ya ke, ta na son fad’awa Gwaggo Munari amma ta tsoran za ta yi zatan fad’an da aka mata ne be shige ta ba, dan haka a dole ta hakura da ikon Allah. Maimakon Gwaggo Munari ta zauna gaban ta, sai gani ta yi ta ja gefe daga wajan su Gwaggon nan. Cikin girmamawa ta mik’a gaisuwar ta tare da damk’a amanar Bintu gare su bisa ga al’ada. Goggon nan wacce a ran ta ta yi farin cikin fasa auren d'iyar Sarkin Sa'ayrasa da Sarki Abdulraman yayi, ta kuma yi bakin cikin aurar da aka aurawa Barde a maimakon d'an ta Sadauki, ta fara kar6ar amana ta hanyar saka hannu ta bud’e mayafin Bintu da ke gaban su, tuni Bintu ta yi k’asa da idanun ta cikin fad’uwar gaba. Sai da ta kalli fuskar Bintu na d’an wani lokaci ta na mai yamutsa fuska ta saki mayafin ba tare da ta rufe fuskar gaba d’aya ba. Kana ta ce ‘’ni Munzaratu jikar Sarki Abdulrahman na difa, d’iyar Sarki Abdulmuminu iii na Agadez, matar Sarki Abdulraman ii na Fabarusa, na bud’e fuskar amaryar dan mu, d’iyar Sarkin S’ayrasa, Sarki Sule Inuwa Magaji da zannuwa hamsin, kallabi hansin tare da bayi guda uku’’ Jakadiya ta rangwad’a gud’a, yayinda waje ya d’au sowa. Ita Bintu ta yi k’asa da idanun ta, ji ta ke kamar ta dan ta k’arasa rufe fuskar ta gaba d’aya. Amma me za ta ji? Goggo ta dole ce ta sa hannu ta k’ara yin baya da mayafin Bintu yanda za ta ga fuskar Bintu da kyau, kafin ita ma ta jero sunan ta da nasabobin iyayen ta, ta bud’e fuskar Bintu da silallan gwal. Ita kuwa Uwar Soro da tashi na ta bajintar da dawakai tare da rak’uma ta bud’e fuskar Bintu. Tuni Bintu ta zama mai arziki da kadarori, su Ladiyo cikin ran su sai mamakin baiwa da Allah yayiwa Bintu, su na jin ina ma dai su ne. Bayan da matan Sarki suka gama budar ka, sai kuma sauran 'yan uwa da abokan arziki, yayye da k'Annan Barde su ma su ka nuna ta su bajimtar. Bayan an gama ne Jakadiya ta mik’a wa matan Sarki tulu. Matan sarki su ukun nan su ka tsaya bisa kan Bintu su na mai tsiyayo mata ruwan cikin tulun kad’an kad’an bisa kan ta, yayinda Jakadiya ke bada wak’a jama’ar wajan na amsa mata "Ayyare daure jure ayyaraye daure jure! zaman gidan wani tilas ne! ba kan ki ne aka fara ba da kan ki ne aka fara ne da kin ci kuka kin k'oshi ke yar tsohuwa mai 'yar tulu Allah ya kar ki watan gobe Mu ci gumba’’ [10/08, 11:59 AM] +234 808 323 2323: Bintu ɗiyar bayi ce (book 2) Chapter 10&11 Admin 001 Mukhtar Adam Nation Tareda Naja'atu Lawal Rijau @Whatsapp 08083232323 09060202323 1⃣0⃣ Sidiya ce....✍🏼 Ana gama wankan amarya Bintu ta ja jik’akken mayafin ta ta rufe fuskar ta tana mai shar6ar kuka. Ba tare da 6ata lokaci ba d’aya bayan d’aya sauran iyalan Sarki su ka dinga zuwa Jakadiya na gabatar da su, har su ka k’are sannan aka rufe taro da addu’a. Da aka gama maimakon a kai Bintu d'akin auren ta, 6angare ne na musammam cikin gidan Sarki, sai wani 6angare aka sake kai ta na daban daga cikin 6angaran Goggon nan wanda ya kunshi d’aki biyu kowanne da bayi sai kuma falo. Nan za ta zauna har sai sanda ta kai budurcin ta d’akin mijin ta. Za6in bawai d’aya daga cikin bayin ta wanda za su na kwana 6angaran ta aka bata. Gwaggo Munari ce ta za6a mata Ladiyo dan kuwa ta fi yabawa da hankalin ta, sauran kuma wuni za su na yi, idan lokacin bacci yayi ko kuwa Bintu ta sallame su sai su koma 6angaran da aka tanadarwa bayi. Yarima Barde kuwa duk wannan bikin da ake masa ya na daga na sa 6angaran. Su Yarima Jafar da Khalil tun suna iya jure shirun da ya mu su har su ma su ka gaji su ka yi na su gurin. Da ya gaji da zaman ne ya watsa ruwa yayinda ya sanya jallabiya, kai tsaye in da ya saba zuwa duk sanda ran sa ya ke 6ace ya nufa, wato lumbun da yake k’yatare da 6angaran matan Sarki. Nan bisa dutse ya kusa raba dare, sai da ya ji idanun sa sun masa nauyi sosai sannan ya tashi a hankali ya nufi 6angaran sa. Ko da ya zo giftawa ta 6angaran da ya san babu shakka nan aka sauki amaryar da aka aura ma sa, sai ya tsinci kan sa ya na mai mummunar fad’uwar gaba. Hakan ya sa shi wucewa da sauri ya na mai ambaton ubangiji. Bakin kofar sa ya tadda dogarai da bayin sa sun yi jugum jugum kasancewar ya mu su hani da biyo shi, ganin sa su ka fara masa kiran lafiya su na mai fad’in ‘’takawa sannu Yarima Barde, lafiyarka dama da hauni, dama da hauni lafiya, salamun salamun’’ Ganin ya zo daf da shiga kofar da za ta sada shi da 6angaran sa, su ka taka masa baya, har ila yau fad’i su ke ‘’gicciye dama Yarima, gicciye salamun’’ Tsayawa Yarima Barde ya yi, ya d'aga mu su hannun alamar baya buk’ata su biyo shi kafin ya sa kai ya shige ciki. Ya bar su waje su na kallan kallo, dan kuwa sun san lamarin auren Yarima Barde kan su zai k’are duk da dai ba su suka kar zuman ba, rataya aka ba su. Washagari da sassafe jama’ar Fabarusa, Samari da ‘Yan mata har da tsuffin cikin adon su na burgewa su ka yi dandazo kofar fada domin kallan hawan angonci bisa al’ada. Amma Yarima Barde ya yi k’yememe ya ki fitowa ko da kuwa kofar 6angaran sa ne bare a sa ran zai hau. Ko da su Khalil su ka je da numin bashi baki, a bakin k’ofa dogarawa ma su tsaran kofar Yarima Barde su ka fad’a mu su buk’atar Barde na kada a bawa kowa damar isa gare shi. Dan haka sai hakura su ka yi, Magatakarda ne yayi shela ga jama’a cewar Yarima Barde be shirya yin hawan angoncin shi a ranar ba, su yi hakuri sai zuwa ran da ya shirya za a sheda mu su. Da kyar kamar ba su hakura ba su ka watse, dan ba k'aramin cin burin hawan angoncin Yarima Barde su ka yi ba, kasancewa akwai k’auna tsakanin sa da Talakawa, musammam ‘yan mata da samari, Yarima Barde na su. "Bayan hayaniyar kofar fada ta lafa, jama’a sun watse su Gwaggo Munari da sauran tawagar Sa’ayrasa su ka yiwa iyalan Sarkin Fabarusa sallama, an had’a mu su koma ta arziki sannan su ka d’auki hanyar komawar su gida S’ayrasa, in da su ka bar Bintu tare da bayin ta, wato Ladiyo, Hansai, lantana da Maman Cangwai a sabon Masarauta. Gwaggo Munari ce ta shedawa Iyalan Sarkin Sa'ayrasa irin tarbar da aka mu su da tarin dukiyar da Bintu ta samu. Gimbiya K’amariyya kuwa sai da ta had’a da kwanciyar asibiti. D’aya daga cikin bayin da su ka juyo ne ta isar da sak’on Lantana ga Yarima Nuhu. Sakon na cewa ta aikata komai yanda ya umarce ta, kuma komai ya tafi daidai. Tsabagen dad’in sak’on na ta har kyautar zani da kallabi ya bawa baiwar domin kuwa in har maganar hakan ta ke babu shakka hakin sa ya cimma ruwa. Kwanci tashi. Bintu ta cika sati guda Masarautar Fabarusa, amma ko da wasa Yarima Barde be ta6a takowa in da ta ke ba bare ma ta san kalar fuskar sa. Gata kuwa ta na sha gurin matan Sarki, musammam Goggon dole da Uwarsoro ,domin kuwannan su burin su ace amaryar Barde daga ta ta ce, Maman Cangwai ce ke saka Bintu a hanya kasancewar ita ta gane manufar su ba lalle alk’airi ba ne. Ita dai ta bi kowa sannu a hankali. Goggon nan kuwa mulki da jin kan ta kad’ai ya fi k’arfin ta, shi Yarima Barde ba gaban ta ya ke ba, bare uwa uba matar sa. 1⃣1⃣ Sidiya ce.....✍🏼 Da hantsi Sarki Abdulrahman zaune bisa kujerar mulkin sa, ana zaman fadanci sai ga Yarima Barde. Ganin sa Sarki be san sanda ya murmusa ba, dan kuwa ya lura wasan 6uya Yarima Barde ya ke da shi, idan har ba zaman fadanci ba ba ya ta6a yarda su had’u da Sarki duk dan gudun duk wate magana da ya shafi Bintu wanda tun da aka d’aura auren ba su sami kye6ewa da Sarki ba bare su tattauna batun. Sanye ya ke cikin fararan kaya an masa d’inkin hannu irin na sarauta. Ya sha rawani irin na buzaye kai da ka gan shi ka ce daga sahara ya ke. da shigowar sa dogarai su shiga yiwa Sarki kiran lafiya su na mai sanar ma sa da isowar Barde ‘’ kimtsi gyara daidai alher, gyara kimtsi ga kyau’’ Gaban Sarki Yarima ya zube, hannun sa na dama dunk’ule ya kai jinjina ga Sarki, dogarai fad’i su ke ‘’jinjine dama lafiya alher, an gaishe ka Yarima Barde’’ Da ga gefe kusa da Yarima Sadauki ya ja ya zauna. Nan fa aka ci gaba da fadanci ana tattaunawa akan abin da ya shafi cigaban al’umma da ma kuma matsalolin al’umma da yanda za a magance su. Har aka yi aka k'are idanun Sarki na kan Yarima Barde. Ko da Sarki zai tashi sai cewa yayi da Barde su na san ya riske su a turakan su. Yayinda Sarki zai tashi dogarai su ka rufe sarki ta hanyar baza babban rigunan su yanda ba wanda zai iya ganin motsin sa bare tashin sa. Fad’i su ke ‘’ rangwame Tafsawa, sannu rangwame alher, lafiya Adali, lafiya Mataimakin Musulunci, gyara kyamtsi ga kyau’’ Haka su na masa kiran lafiya har ya kai ga ficewa daga fada. Bayan fitar sa ne Yarima ya kai gaisuwar sa ga sauran Hakiman, ciki har da wanda ke masa Allah ya sanya alkhairi. Ya zo fita kenan Yarima Sadauki ya shagaban sa, ganin sa Yarima Barde ya Murmusa ya na mai dunkule hannun sa na dama ya jinjinawa Sadauki sa’annan ya furta ‘’Sadauki ne kai’’ Cike da tak’ama, shi lalle Yarima mai jiran gado, Sadauki ya maida masa da martani yanda ya saba ta hanyar fad’in ‘’kai ma Barde ne, musammam sa’in da na hau kujerar mulki’’ Barde be fasa murmushin da ya ke ga d’an uwan na sa ba duk da kuwa ya san magana ya ke fad’a ma sa. Kana ya ce ‘’barka da hantsi, da fatan mu na lahiya’’ ‘’lahiya lumi fa, ya kwanan amaryar dole? Ko da shike har yau ba mu ji labarin budurcin ta ba bare mu ce ango ya sha k’amshi, d’iyar abokan gaba ce duk da kuwa abun ba dambe ba ne ba, kada Barde ya ba mu kunya!’’ Ya na gama fad’in haka ya yi gaba. D'if Yarima Barde ya d’auke wuta, Khalil da ke tsaye daga bayan su, ya kuma ji dukkannin maganan da Sadauki ya fad’a ne yayi saurin ta6a kafad’ar Yarima Barde, kana ya ce ‘’ba kai an babba ba, amma babba gare ka Barden mahadi maida garin wani kongo’’ Jin haka ya san hakuri Khalil ya ke ba shi. Ya ko yi na’am da Khalil ta hanyar murmusawa ya na mai fad’in ‘’ina da muradin zuwa wucan gadi mutumi na, ko za mu sami dama tafiya kafin na sami saduwa da Sukuku Bakaka(Sarki)’’ Cikin jin dad’i Yarima Barde ya fara sakewa Khalil ya nemo Yarima Jafar domin su tafi wucan gadi. Da yamma likis bayan Yarima Barde ya dawo daga wucan gadi ya isa ga Sarki. Turakar Sarki su ka d’an ta6a hira sama sama, kafin Sarki ya kawo batun Bintu ta hanyar tambayar ‘’ya amanar da mu ka ba ka? Shin an duba kuwa?’’ Barde na mai durk’usar da kai k’asa ya kasa magana. Ganin haka Sarki ya fahimci in da ya dosa, kana ya ce ‘’kar ka damu d’an mu, ka bi sannu a hankali ba laifi ba ne, amma dai mu na ruk’on ka da kar da mu zamo daga cikin azzalumai ta hanyar d'auka lokaci mai tsayi, wannan gona ta ka ce, kada ka manta akwai idanu dayawa bisa kan ta, da fatan za ka kula a wadata ta, san samu ma a ziyarce ta ko da kuwa daga yau zuwa kwana uku ne’’ Maganar Sarki ba k’aramin nauyi ta yiwa Barde ba, dan kuwa ji ya ke ina ma zai iya masa musu ko da kuwa na sakan d’aya ne, amma ina tsaintar kan sa yayi ya na mai fad’in ‘’an gama Sarkin yakin musulmi, bango madafan bayi’’ Sarki kuwa ba k’aramin jin dad’in yanda Barde ke masa biyayya ya ke ba, cikin ran sa ya na mai jin ina ma shi ne babban d’an sa ba Sadauki ba. Sai bayan da su ka idda salar isha’i sannan Barde ya baro wajan Sarki. Kai tsaye lambun nan da ya saba zama duk dare ya nufa, zuciyar sa na sak’a masa yanda zai yi ya gujewa had’uwa da amaryar da aka d’aura masa, wato kanwar budurwar sa. 🐫🐪🐫🐪🐫 Bintu ɗiyar bayi ce (book 2) Chapter 12 Admin 001 Sayyadi Sasiq @Whatsapp 08146934644 1⃣2⃣ Sidiya ce.....✍🏼 6angarn Bintu kuwa kamar yanda ta saba, yau ma ta sallami dukkanin bayin ta, ya rage daga ita sai Ladiyo, wacce ita dama d’aki d'aya su ke kwana idan ta tabbatar kowa ya d’auke k’afa, tsabagen tsoro da rashin sabon kwana ita kadai. Bintu na kwance bisa gadon ta, tunanin Innar ta ta take da rayuwar ta na da wanda shi ya fi mata dad’i akan wannan daula da ta tsinci kan ta a ciki. Ladiyo da ke tsaye bisa taga idanun ta kan hanyar lambun da ke kyetare da 6angaran Bintu, sai ajiyar zuciya ta ke ba tare da ta san ta na yi ba saboda tsabagen muradin sake zuwa lambum da ya addabi zuciyar ta, ba dan komai ba ko dan ta ga wannan buzun da ta gani ciki mai irin sifar aljanu tsabagen kyauwu. Gashi ran da ta fara shiga lambun satar hanya ta yi bayan Bintu ta yi bacci ta ga wucewar sa, kasancewar shi kad’ai ne ya sa ta yi tunanin kila talakan Sarki ne, wanda su ke da daurin gindi wajan fadawan Sarki ko kuwa d’aya daga cikin ‘ya’yan hakiman masarautar nan. Nan ta gan shi zaune bisa kan dutse ya na sakar zuci, har ta k’are masa kallo be san ta na yi ba tajuya tana tasbihi ga Allah bisa tsarin halitta da yayiwa bawan Allah nan. A hankali ta kai kallan ta ga Bintu, kana ta ce ‘’gide Gimbiya ba ki da muradin ganin farin wata ne? aradu zaman cikin kurya ya ishe ni’’ Jin haka Bintu ta yi farat ta tashi zaune ta na fad’in ‘’yo to Ladiyo mu tai mana, ba tun yau na ke da muradin mik’e k’afa, kwankwatsi ni ma na gaji da zaman nan, hallo ki na ga babu matsala aka gan ni a rariya?’’ Abun da Ladiyo ke so ta samu duk da kuwa ba ta yi tsammanin haka daga wajan Bintu, ko da shike dama ai d’iyar bayi ce Ladiyo din ce ke sha’afa. Ta yi saurin dawowa gaban Bintu jiki na rawa ta ce da ita ‘’gide ai da yawa ba su san fuskar ki ba, ba na jin za su waye ki, kai in ki na son badda kama ma zai fi na ara mi ki d’aya daga cikin kaya na na bayi......idan fa Gimbiya za ta iya sanyawa’’ Ta k’arasa ne cikin d’ard’ar kada Bintu ta ce ta raina ta, duk dai ita kan ta ta san babu laifi Bintu ba ta canza mata ba, in har ba wai akwai mutane gun ba yanda ta saba mata tun tana baiwar ta hakan ta ke ma ta. Ga mamakin Ladiyo sai gani ta yi Bintu ta tashi cikin hanzari ta na mai fad’in ‘’kayya

Chapter 3 of 5