Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba da komai zai tafi daidai, abubuwa ba zasu tafi kamar a mafarki tare da mutumin da daga shi har ita basu san juna ba sai bayan aurensu kuma har yanzu bsta san manufarsa akanta ba.
Ma'aruf ba zai taɓa sauko da kansa haka akan ita ɗin da ba kowa ba, don ta sani cewa bayan matar daya aura Allah kadai ya san matan daya sani a a rayuwarsa ko ma wanda yake tare dasu a yanzu, to don me yasa hankalinsa zai tsaya akan ita din da ba kowa ba, ita ɗin da sa baiyane yake cewar ba sa'ar rayuwarsa bace.
Ta girgiza kanta tana kokarin rufe robar ruwan, wannan lokacin kamar zubar ruwa ne kawai kafin zuwan tsawa, kamar iska ce mai daɗi kafin guguwa, sannan kamar kaɗawar ruwan teku ne a hankali kafin ambaliyar sa, akwai wani abu dake jiran ta bayan wannan, kawai dai dan adam baya taba sanin lokacin da ƙaddara ko kuma wata masifar rayuwar ke zuwar masa ne.
Muryar Amma ta cikin mafarkin nan ta gifta a cikin kanta lokacin da take cewa
"Me yasa kika yarda ba zaki iya ba Amina..."
A hankali tayi ajiyar zuciya tana fatan Allah yasa koma meye ke shirin faruwa ta iya tunkararsa da ƙafafunta a tsaye, daidai lokacin da a zahiri ta jiyo muryar Samirah ta shigo tana kiranta.
"A ina kika ajiye sugar?"
Sai kawai tayi sauri ta ƙarasa goge bakinta sannan ta ajiye robar ruwan ta fita.
****
Karfe Bakwai daidai Ishaq ya iso, kuma Amina bata san me ya faru ba, don minti biyar bayan zuwansa sai ga sallamar ɗaya abokin Ma'aruf da shima ta riga ta haddace shi a waya mai suna Faruk.
Su uku kaɗai suka cika falon da surutu kamar su biyar, kuma duk yadda take ganin Ma'aruf na da magana sai a lokacin taji nasa mai sauki ne, don kafin taji muryarsa taji tasu da yawa musamman Faruk ɗin, don shi yafi Ishaq yi mata magana sosai ma, har matarsa da ƴaƴansa yayi alkawarin kawo mata tunda yace yanzun a sama kawai Ma'aruf ya kira shi yace masa yazo.
Kuma har lokacin da suka zo ɗin su Munaya basu tafi ba, Samirah dai taso tafiya amma sai Munayan tayi ta roƙonta akan su ƙara tsayawa tukunna, wani abu da ya ƙara bawa Amina mamaki don ita kanta ta san babu wani dalili Munayan ba zata yi ta cewa su tsaya ba. Ilai kuwa a lokacin da suka je kai musu abincin nan, a lokacin ta samu amsarta, saboda idon Ishaq na kan Munaya tunda suka shiga har ta juya Kitchen don ta ɗauko wani abun, kuma zata rantse ma taga sanda suka yiwa junansu murmushi lokacin da take zuba masa lemo, Allah ya sani yau ta fara ganin Ishaq ɗin amma sai taji zuciyarta na jiyewa Munaya daɗi idan har hasashenta akansu gaskiya ne, don duk inda nutsatsen namiji yake za'a saka Adam a wannan layin, kuma itama Munaya babu ruwanta da wani hargitsi sam.
Sun ji daɗin tarbar da suka samu kwarai, don ba'a kalamansu kaɗai ta fahimci hakan ba, har a fuskar Ma'aruf da kuma yanayin kallon da yake mata tun lokacin da taje ta sako wani dogon hijabi bayan shigowar su, wani abu da ita kanta taji ta kyauta da tayi hakan.
Bayan sallar isha'i ne sannan suka yi musu sallama suka fita, kuma sun daɗe a waje suna magana don har bayan tafiyar Faruk ɗin shi da Ishaq suna nan, har su Munaya suka tafi ta ƙarasa wanke iya kwanukan da aka ɓata kasancewar basu tara wanke-wanken ko ɗaya ba dama a ɗazu.
Kuma tana sallah lokacin da ta jiyo ƙarar fitar motar Ishaq ɗin, sai dai har ta idar ta gama addu'o'in ta da komai bata ji lokacin da Ma'aruf ya shigo ba ko kuma don haka ta ƙudirta a ranta cewa cikin gida ya shiga. Da wannan tunanin ta ninke sallayar tare da hijabin ta ajiye su a gefe, ta ɗauko wayarta don kiran su Amma, sai dai daga layin nata har na Aminu bai shiga ba, kuma bata son kiran Baba a wannan daren, don haka ta bari zuwa gobe, ta nufi wardrobe ɗinta don ta ɗauko kayan bacci, wata sabuwar doguwar riga ta dauko sannan ta dawo gaban gadon don ta canja.
Ɗankwalinta ta fara cirewa ta ajiye shi a kan gadon sannan ta shiga kokawa da zip ɗin rigarta, amma ga mamakinta saiya riƙe ɓam yaki ko motsi, gashi ciwon hannunta ba zai bari ta rike shi da kyau ba, na dama kuma yaki ƙarasawa can saman, dama tunda tazo saka kayan ta kula yana da matsala amma bata yi tunanin ta kai haka ba.
Har sai da hannunta ya ƙage ta tsaya ta tattaro dukkan ƙarfinta sannan ta cigaba da jansa, kafin a lokaci guda kamshin turaren Ma'aruf ya shiga hancinta.
***
A waje bayan Faruk ya tafi, sun dade a tsaye shi da Ishaq suna hirar tarin wasu abubuwan da suka shafe su wanda yawanci duk akan matsalolin dake baibaye da rayuwar Ma'aruf ne, sai kuma zancen Abdurrahim, ƙanin Ma'aruf ɗin dake can New York wata makaranta ta Bebaye irinsa, (Rochester Institute of Technology.) Don Baffa ya gaya musu cewa saura watanni biyu kawai ya kammala ya dawo gida.
Bayan wannan sun tattauna zancen Hamida ma inda Ishaq yayi-yayi da Ma'aruf akan ya ɗauko yarinyar daga inda ya kaita ya dawo ta ita cikinsu, amma ya ɓata bakinsa a banza don ya riga ya rantse cewar Ruƙayya ba zata taɓa sanin inda Hamida take ba sai ya kammala da al'amarinta gaba ɗaya, ko shekaranjiya da Mami taso yi masa zancen itama kai tsaye ya dakatar da ita ta hanyar gaya mata cewa lokacin da zai ɗauko ta bai yi ba, don haka itama taja bakinta tayi shiru, don dukkaninsu sun sani cewar idan har ya furta abu, Baffa ne kawai zai iya sauke shi daga kansa, amma ko da suka yi magana da Baffan shima cewa yayi...
"Wannan zancen naku ne kai da mahaifiyar yarinyar Muhammad, duk abinda kuka yanke idan har ba kuskure bane mu namu addu'a ne tunda kune kuke da iko akanta fiye damu. Kuma kowannen ku yana da ikon da zai riƙe ta, duk da dai a matsayinta na mace an fi so ta zauna a gaban mahaifiyarta, amma idan har za'a samu matsala wajen tarbiyarta ko lafiyarta kamar yadda aka fara yanzu, to zamanta a wajen naka zai fi."
Wannan zancen na Baffa shi ya bashi ƙwarin gwiwar cigaba da shirin da yake da niyya wanda yake jiran lokacin kawai. Daga ƙarshe kuma suka ƙare da zancen ginin su wanda Ishaq ɗin ya gaya masa cewar ya samo wasu sababbin masu ginin da zasu fara aikin tunda Ma'aruf ya sallami waɗancan.
Kuma baiyi mamaki ba da Ishaq ɗin baiyi masa zancen Amina ba, don ya riga ya fahimci cewa ba sai yayi ɗin bane, akwai wasu abubuwa da ba lallai sai sun furta su a tsakaninsu ba, wasu abubuwa ne da ƙarara kowannensu ke ganewa idan ɗayan yana ciki, don haka a yanzu ma Ishaq ya riga ya sani cewar ya riga ya yanke koma wane irin hukunci ne game da zamansu ba sai sun ɓata lokaci wajen biya shi ba.
Da haka suka yi sallama, sabon maigadin da ya samo ya sake budewa Ishaq gate ɗin gidan, shi kuma ya koma ciki.
***
Yayi sakanni biyu tsaye daga bakin kofar yana kallon yadda take kokawa da zip ɗin rigarta kafin ta ankara dashi, watakila jikinta ne kawai ya bata cewar yana daga bakin kofar, don a lokaci guda ta juyo da sauri tana kallonsa, fararen idanunta suka zare akansa yayin da a lokaci guda ta saki hannayenta duka biyun suka sauka a gefenta.
"I'm sorry banyi sallama ba ko?"
Sai ta girgiza kanta.
"Babu komai ban ji lokacin da ka shigo bane."
Ya cije lebbensa tsaye a jingine kofar kafin yace.
"I'm sorry bana so in ɗauki lokaci ne kiyi bacci."
Idanunsa na kallon fuskarta da yaga kamar tana ƙoƙarin kore wani abu wani abu mai kama da mamaki kafin ta tambaya.
"Wani abu kake so?"
Lokaci ne ya tsaya cak a cikin kansa da wannan tambayar yayin da fatar bakinsa ta bude kamar zai ce wani abu yana kallonta, tsakaninta da Allah ta fadi hakan ba tare da ta san tarin ma'anonin da za'a iya fitarwa daga kalaman nata ba, ganin tana cigaba da kallonsa yasa ya sake cije leɓɓensa na ƙasa sannan ya girgiza mata kai.
"I want to treat your hand." (Hannunki zan duba.)
Ya faɗa yana kallon yadda fuskarta ke nuna tarin yanayi kala-kala, ƙafafunsa suka tako cikin ɗakin a hankali zuwa inda take tsaye, kuma kamar a wani shiri sai iska ta buso daga windon da yake fuskantar su daidai lokacin da ya tsaya a gabanta, kuma bai ɓata lokaci ba yasa hannunsa ɗaya ya ɗauko nata mai ciwon nan.
Gabaɗaya tsawonta iya kafadarsa ne, gashin kanta da babu dankwali ya taso sama yana shaida laushinsa, da zai iya a wannan lokacin zai zare ribbon din data ɗaure shi ne don ya sauko kafadunta yaga iya tsawonsa, amma sai ya daurewa wannan tunanin ta hanyar kallon yatsun hannunta da yake riƙe dasu.
Ya san cewa shi mutum ne da yake ƙarbar respect daga ɗimbin mutane, kuma a iya kokarinsa yana kokarin ganin ya kyautatawa duk wanda ya shigo hanyarsa, da kuma kaffa-kaffa musamman a yanzu don ganin bai yi wani abu da zai iya cutar dasu ba, amma Allah ya sani bai taɓa haɗuwa da wanda a lokaci guda yaji zuciyarsa na tsoron ciwonsa akanta ba irin yarinyar nan, yarinyar da a baya bai damu da yadda zaiyi kokarin samun bayanin da yake so daga gare ta ba,
Wani bandeji ne mai haɗe da audugarsa a jiki, don haka magani kawai ya ɗiga a jiki daga cikin wata ƴar kwalba sannan ya rufe ciwon nata dashi, ai kuwa ta runtse idanunta a lokaci guda tana jin zafin na tafiya har tafin ƙafarta.
"Zuwa safe zaki iya cirewa sai a saka wani, insha Allah a kwana biyu zai warke."
Ya faɗa yana sakin hannun nata, kuma duk da zafin da take ji haka ta shiga daga kanta da sauri alamun ta fahimta.
Ya rufe maganin sannan ya wuce ta zuwa wajen da mudubin ɗakin yake, ya ajiye roll ɗin plaster da kuma kwalbar maganin akai sannan ya juyo ya dawo inda take tsaye tana cigaba da danne ciwon.
Kuma bata yi wani tunani ba lokacin da ya tsaya a bayanta, dab da ita sosai, don haka da sauri ta juyo gabadaya ta kalle shi amma sai ya saka hannayensa duka biyu akan kafaɗunta ya juyar da ita.
"Zan taimaka miki da zip ɗin ne..."
Ya faɗa muryarsa na fitowa dab da kunnenta sosai, kuma kafin tayi ƙokarin kamo tunaninta muryar tasa ta cigaba da cewa.
"Akwai abubuwa da yawa game dani a zuciyarki na sani, amma ina so a saman komai kisa a ranki cewar ba zan taba cutar dake ko in takurawa rayuwarki ba insha Allah."
Ya furta hakan yayin da hannunsa ya kai kan zip ɗin, sauran yatsunsa na ɗaya hannun suna taba fatar bayanta, sai kawai ta rufe idanun gabadaya tana ƙoƙarin saita numfashinta, kuma da ja ɗaya kawai hannunsa yayi ya sauke zip ɗin sai dai bai kai shi har ƙasa ba, daga daidai tsakiya ya barshi, taji sanda yatsunsa suka dauke daga saman fatar ta, da kuma sanda yake matsawa, sai ta buɗe idonta lokacin da ya zagayo daidai saitin ta.
"Nagode." Ba zata ba taɓa iya tantance yanayin yadda muryar tata ta fito ba, ya gyaɗa kansa.
"You are welcome, sai da safe."
Da haka ya juya ya nufi kofar ɗakin yana rufo mata ita.
Sakan ɗaya, biyu, uku, suka wuce Amina tana ƙoƙarin saita numfashinta kafin a hankali ta ɗauko rigar baccin nan ta karasa abinda zata yi, wanda har ta gama komai ta kashe fitilar ɗakin kalamansa na yawo a cikin kanta.
...ba zan taba cutar dake ko in takurawa rayuwarki ba insha Allah.
Sai kawai ta rufe idanunta sannan ta dunkule jikinta akan gadon, kuma bata bawa zuciyarta wani damar tunani ba don bata san buhu nawa zata kwance na tambayoyin da bata da amsar su a zahiri dama cikin kanta ba.
Ya rabbi lakaal hamdu kam yanbaghi li jalaali wajhika wa adheemu sulɗaanik.
Bakinta ya furta addu'ar hankali yayin da take jin ma'anar ta na tafiya har ƙasan zuciyarta.
***
Washegari...
Ƙarfe goma na safiyar Litinin, a irin wannan lokacin Amina ta saba da wani irin shiru don ko'ina tsit yake, duk wani mai fitar safe ya daɗe da yin gaba, ƴan makaranta da masu aiki da mafi yawanci sun fi yawa a kowanne gida.
Tana daga kitchen a lokacin tana ƙoƙarin fara aikinta ta tsinkayi ƙarar ƙwanƙwasa kofar, mamaki ya ɗan kamata don ta san babu wanda zata yi tunanin zuwansa a wannan lokacin, ta gyara zaman ɗankwalinta yadda ta yafa shi sannan ta fito daga kitchen ɗin ta iso ƙofar falon kuma ba tare da tunanin komai ba ta buɗe ta,a lokaci guda siffar Hajiya Kilishi dake tsaye ta shiga idonta tun kafin sakon saninta ya ƙarasa ƙwaƙwalwar ta.
Tana sanye da wata haɗaddiyar lafaya ruwan makuba (maroon) da ta nannaɗe ta tsaf a jikinta, fuskarta kamar kullum ɗauke da wannan murmushin nata, murmushin dake haska annurin fuskarta a kodayaushe yana ƙawata kammaninta.
Babu dalili Amina taji gabanta ya faɗi amma tayi saurin kore hakan wajen yin nata murmushin itama.
"Sannu da zuwa Mami, barka da zuwa."
"Barkanmu dai Amarya. Yau dai na ajiye kyuiyata a gefe nazo ganin ɗakin amarya."
Wani murmushin mai haɗe da kunya Amina ta sake yi kafin tayi baya don bata hanya tana kara fadin 'Barka da zuwa', kuma kai tsaye kuwa ta shigo haɗe da sallama yayin da ƙamshin daddaɗan turarenta ke rufo mata baya.
"Wa'alaikum salam."
Ta amsa sallamar tana rufe ƙofar har a lokacin da murmushi a fuskarta, murmushin da a lokaci guda ya ɗauke sakamakon juyowar da Hajiya Kilishi tayi tun kafin ta kai tsakiyar falon tace.
"Idan akwai muƙulli rufe ƙofar dashi Amina, akwai maganar da zamu yi ne."
Zuciyarta ce ta fara bugawa a kirjinta kafin ta juyo ta kalle ta, amma ganin murmushin dake kan fuskarta har yanzu, yasa itama ta dawo da wani dan guntu kan leɓɓenta sannan tace.
"Toh Mami."
Da haka ta rufe kofar tana ƙoƙarin gayawa zuciyarta cewa gabanta ba faɗuwa yake ba sannan ta juyo ta ƙaraso ciki.
A lokacin ta zauna daga tsakiyar kujera mai cin mutum uku a falon don haka ita tameni waje daga ɗaya karshen ƙaton carpet ɗin ta zauna tana fuskantar ta.
"Barka da Asuba Mami, fatan kun tashi lafiya?"
Ba kallonta take ba amma daga yanayin yadda muryarta ta fito wajen amsawa ta fahimci har yanzu murmushin take yi.
"Mun tashi lafiya, Ya bakunta kuma? Ko da yake ai naga su Samirah sun saka kin saba tuni."
Bata ce komai ba illa wasa da karshen skirt dinta da take yi tana cigaba da murmushin da zata kira na dole, don bata san me yasa zuciyarta ta kasa zama waje ɗaya ba.
Hajiya Kilishi ta kalli ƙaton screen din Tvn dake tsakiyar falon dama sauran kayan kallon da aka jera akan hadadden stand ɗin Tvn da dubu tamanin da biyar ta bayar aka siyo shi sannan tace.
"Gidan shiru ke kaɗai baki ko kunna Tv ba?"
Da wani murmushin a fuskarta tace.
"Ai ba'a hada Tvn ba har yanzu Mami."
Muryarta ta fito ƴar ƙarama a cikin shirun dakin, kamar tana son ta shaidawa Hajiya Kilishin ƙanƙanta da kuma rauninta.
"Baku gaya min ba ai, gashi jiya kuwa yaro mai gyaran satelite ya shigo har cikin gida, da ya karaso ya hada muku, amma a bar ki a gida haka shiru, shi ya fice ya tafi hadaniyar gabansa ba zai tuna da wani sha'anin Tv ba.
Sai ta sake girgiza kanta tana cigaba da murmushin.
"Ba komai Mami, duk sanda aka sa baza'a makara ba ai."
Ta fadin hakan lokacin da take kokarin mikewa, amma a lokaci guda Hajiya Kilishin ta tsayar da ita.
"Ina ziki je kuma?"
"Mami, kayan breakfast zan kawo miki."
Ta faɗa taka kallonta, sai ta girgiza kanta.
"Barsu nagode, dawo ki zauna."
Umarnin dake cikin muryar ya kaɗa hantar ta, taji wani abu yana ƙoƙarin ɓallewa daga cikin zuciyarta, amma sai tayi saurin ture hakan ta dawo ta zauna ɗin, hannunta na taɓa hannun kujerar gefenta kamar tana neman taimakon ta.
Kuma zaman nata sai ya zama kamar shine farawar wani shafi na farko a rayuwata, don watakila idan zata bada labari, zata fara ne ta kansa, daga lokacin da kafafunta suka sake komawa kan carpet ɗin nan da kuma lokacin da muryar Hajiya Kilishi ta sake ratsa shirun ɗakin da cewar.
"Amina kunyi waya da mutanen gida kuwa jiya?"
Sai da ta haɗiye wani dunƙulen abu da bata san sunansa ba a kirjinta sannan ta girgiza kai.
"A'a Mami, na kira su dai jiyan amma bai shiga ba."
"Ina wayarki?" Kai tsaye ta sake wata tambayar da ta fito kamar tsawa.
Kan Tv's stand ɗin nan ta nuna inda bayan fitowarta da safen ta saka ta a caji.
"To matso ki kira su."
Wannan karon sai da ta kalle ta tsawon wasu sakanni fuskarta na haskawa da mamaki sannan ta matso a hankali zuwa wajen wayar, lokacin da ta cire ta daga caji taji kamar hannunta na rawa amma tayi saurin fara dannawa ta lalubo nambar Amma.
Sai da ta sake kallon Hajiya Kilishin da murmushin fuskarta ya rage tasiri kafin ta kara wayar a kunnenta, kuma cikin wata iriyar sa'a, bugu ɗaya biyu sai Amman ta dauka, sautin muryarta kadai ya doka wani abu a ƙirjinta tun kafin ta fahimci abinda take faɗa.
"Amina yi haƙuri, tun jiya bamu kira ki ba, muna asibiti ne sai da safen nan muka fara samun nutsuwa..."
"Asibiti? Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!... Me ya faru Amma? Me ya faru?"
A yanzu ta tabbatar hannun nata rawa yake, don tana jin yadda yake tafiya tare da bugun zuciyarta.
Daga cikin wayar Amma tayi ƙokarin gyara muryarta kaɗan sannan tace.
"Aminu ne mai mashin ya taka shi jiya da daddare a wajen aiki, amma sun ce jikin nasa da sauƙi kar ki ɗaga hankalinki, yanzu mu ma zamu shiga mu ganshi..."
Zancen ya katse a lokaci guda da Amina ta nemi wayar a kunnenta ta rasa. Hajiya Kilishin da a yanzu ke tsaye akanta riƙe da wayar tasa hannu ta ɓare bayanta ta fito da batirin ta jefar dashi gefe, sannan ba tare da ɓata wani lokaci ba ta karya wayar gida biyu itama.
Kuma taku biyu kawai ya mayar da ita baya kan kujerar da ta taso, ta cigaba da kallonta har a yanzu da ragowar murmushin nan a fuskarta kafin muryarta ta fito cikin wani irin sauti da yake ainahin halittar ta, sautin da yake manne a kirjinta tare da zuciyarta dake ƙawata mata tarin hanyoyin da kullum suke ɓullewa ga nasararta, sautin da a duniya kaf, mutum huɗu ne kawai suke sanin da kasancewarsa, sai a yau da ta zabi Amina ta zaman cikon ta biyar ɗin, cikon da take fatan zai zama mataki na ƙarshe da take da yaƙinin zai kai ga nasararta.
"Barka da shigowa cikinmu Amina."
Kalamai biyar ɗin data furta kenan wanda ta lissafa cewa adadinsu ya dace da lambar matsayinta, murmushi kan fuskarta cika taf da tarin kalaman da take shirin ɓare mata a yanzu wanda zasu sa ta fahimci wacece Kilishi tun daga tushe da kuma dukkanin abubuwan data aikata a rayuwarta.
***
Wane shiri Ma'aruf ke yi akan ƴarsa Hameeda da kuma Ruƙayya?
Me ya yankewa zuciyarsa akan Amina da har Ishaq ya fahimta?
Ku gaya min ina rayuwar gidan nan ke tafiya?
Munaya and Ishaq, me kuke tunani?
Hajiya Kilishi...
Ina gaya muku har yanzu sunan matar nan kawai kuke ji, next chapter zata buɗe muku abubuwa da yawa game da ita...
Babi na gaba zai nuna muku me ake nufi da ainihin kissa da kisisina irin ta mata kamar Kilishi, wanda suka yarda cewa kowacce mace zata iya samun duniyar da take so a tafin hannunta... Ba boka ba malam!
#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters
#FararWuta.

BABI NA SHA UKU.
~~~~~~~
There's a part of me that likes to beleive everything will be okay, then there's another that breaks down every chance it gets.
- Unknown.
**
Dukkan wata ma'ana ta mamaki da kuma tashin hankali shine yadda fuskar Amina tayi a lokacin da take kallon Hajiya Kilishi.
"Taɓa Aminu dana sa akayi tsaraba ce ga ƙwaƙwalwar ki Amina don ki saurare dukkan abunda zan gaya miki da kyau, ki yarda da dukkan kalamaina sannan kuma zuciyarki ta tabbatar da cewar Kilishin da zaki sani a yanzu da gaske take al'amuranta."
Tayi shiru bayan ta faɗi hakan hannunta na jawo wayarta da ta ajiye a gefe, babu ƙarar kiran dake shigowa alamun a silent ta saka ta.
"Ya akayi Awwalu?"
Muryar tata da ta canja tar ta tambaya cikin wayar bayan ta kara ta a kunnenta... Har a lokacin Amina bata motsa daga yadda take zaune ba, idanunta basu canja daga yadda suke kallonta ba, sannan ƙwaƙwalwar ta bata wartsake daga mamakin dake zagaye da ita ba, Ƙirjinta dake ɗagawa cikin numfashi mai nauyi shine kaɗai abinda zai sa ka san cewa idan ka taɓa ta ba zata tafi ta faɗi ba.
Wataƙila magana guda ɗaya aka fada a cikin wsyar wadda ta gamsar da Hajiya Kilishin, don bata ƙara cewa komai ba ta kashe ta kawai ta sake mayar da ita gefenta, sannan ta sake kallom Aminan, hasken fuskarta na yayewa alokaci guda
"Duk abinda zaki ji a yanzu ya zama tsakani dake ne Amina, idan ba haka ba a ƙarshen zancena zaki gane abinda zai faru idan har kika sako mutum na ukun mu a wannan zancen koda kuwa mahaifiyarki ce.
Da farko mu bar duk wani kewaye-kewaye mu tafi ga abinda yasa kika shigo gidan nan, tunda ni dake dama duk wani mai hankali mun san akwai dalilin aurenki da Ma'aruf..."
Ta gyara zamanta kaɗan sannan ta cigaba...
"... Cire mahaifinki ki ajiye shi a gefe, amma ko mahaifiyarki ta san ruwa baya tsami banza, a muryarta kawai na fahimci cewa irin zurfin tunaninta kika ɗauko Amina, ku duka kun san ba kowacce mace ce zata taka irin matsayin da kika taka a banza ba, zan ƙara tabbatar miki cewa shigowar ki cikin gidan nan dama cikin rayuwar Ma'aruf wani abu ne da ba don taimakona ba, ba zaki taɓa samunsa ba ko zaki mutu sau ɗari ki dawo, saboda a rana guda zamu iya samun mata dubu da zasu yarda da auren Ma'aruf ko da kuwa ciwon da yake dashi yafi haka tasiri, don ba'a wayewar kowacce rana mata ke samun namiji irinsa ba.
Kuma shi kansa Amina, da an bashi zaɓi na sani tsaf zai kawo macen da zata fi ki a komai don irinsu kawai ya sani kuma yake mu'amala dasu, amma sai nayi amfani da ƙarfina da kuma ikona nace ke kaɗai za'a bawa wannan matsayin wanda dole kowa ya yarda da hakan, don haka duk wata soyayya da kika ga kina samu daga mutanen gidan nan dama shi Ma'aruf ɗin da ya fara saurarar ki duka saboda ni suke miki ba don komai ba, ni na ɗora su akan turbar zuciyarsu ta so ki kuma hakan ya zame musu kar dole."
A yanzu Amina tayi ƙoƙarin sunkuyar da kanta tana kallon hannayenta dake faman rawa suna kakkarwa akan cinyarta, zuciyarta na bugawa ne kamar zata faso kirjinta ta fito yayin da kowanne kalaman Hajiya Kilishin ke shiga kunnenta da tsantsar rudani da kuma tashin hankalin da akace ba'a saka masa rana.
Kuma shirun da Hajiya kilishin tayi baiyi tsawon da zata iya fitar da komai ba lokacin da muryarta ta cigaba da cewa.
"Bari in ɗauko miki komai tun daga farko Amina, ta haka ne zaki fahimci zance na.
Lokacin da ina yarinya a wajen kakata na girma, ita ta raine ni tun daga lokacin yaye har girma na, a wajenta na samu tarbiyya da kuma tarin wayo da dabaru irin na zaman duniya, har yasa tun a ƙananun shekaru ina iya kallon rayuwar mutum na bashi shawara mai kyau da zata ɓulle ga matsalolin sa, hakan yasa ƙawayena dama mutanen unguwar a lokacin suka laƙaba min sunan ƴar baiwa.
Bayan wani lokaci sai wannan kakar tawa ta rasu don haka dole na koma gidanmu inda naje na tarar da tarin ƴanuwana, don mahaifinmu matansa uku ne kuma ƙaramar cikinsu wato mahaifiyata ce kawai mai ƴaƴa tara, sauran biyun akwai mai goma sha ɗaya da kuma sha uku.
Rayuwar gidanmu ba dadi sam, saboda a wajen kakata na saba komai namu mu uku ne kawai dani da ita da kuma wani almajirinta Awwalu da take riƙewa, don haka sai rayuwar gidan yawan tazo min a wuya, gashi babu ruwan kowa dani

Please Login or Register in order to submit comment