Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya shiga. Allura ya fara masa within few minutes ya fara amai, seda ya gama tas yana sauke numfashi lokace daya yanajin zazzabin jikinsa yana sauka seya kama bangon ya mike yana kallon Master
"Jira nayi wanka please" ya shiga bandakin, minti biyar ya fito ya maida rigar jikinsa yana goge kansa da qaramin towel dinta. Shidai Master binsa kawai yake da ido har ya shiga gyara gadon dayake kaman anyi wasan dambe akai duk pillows din da take tatawa kaman me jinnu sun watse a qasa.

"Fadi maganar bakinka Malam kar ta kashe ka" ya fada batareda ya kalli Mastet din ba. Seda hayi dariya sannan yace "Alhajin Allah wani haske naga ka qara fuskarka har qyalli take shine nace meye sirrin ne" ya qarasa yana masa dariyar shaqiyanci. Murmushine ya subuce masa na tunawa da wani abu, seya zauna a gefen gadon yana shafa kansa at the same time yana ci gaba da murmushin yace
"Gee Ango nake yau".
"Wait is she HAMDAH" ya tambayeshi cike da zaquwa har yana zamowa daga kan couch din da yake zaune.

"Gidan uwar wa zanje to in ba ita ba ko ance maka nima Dan iska ne, ina gaya maka nima yau nabau network na hau jirgi yayi anyi Solo driving dani".

"Kai kace ciwon girma kakeyi tsohon tuzuru yau dai Allah ya yanta ka gaskiya na maka murna kace kawai na tattara drugs dina nayi gaba ga babban magani ka samu" cewar Master yana masa dariyar shaqiyanci, a wani bangare na zuciyarsa kuma yana tausayin Abdul'ahad din. Allah kenan shi kuma se yau tasa wahalar ta yanke. Dibarsa ya ci gaba dayi da tsokana yana hada sauran allura da drip din da ze saka masa dan har lokacin zazzabin be barshi ba ga ciwon Ciki
"Ita fa Amaryar, kona kira Hawwa ta taimaka matane dan nasan bazaka iya ba" ya fada daidai sanda yake maqala masa ruwan bayan ya kwanta akan gadon, naushi ya kai masa da kafarsa yai saurin gocewa yana dariya

"Dan iska ba Hawwa ba Asibiti zaka kira ai wallahi badan larura ba da yanda nayi alqawari nobody will see her har seta haihu amma yanzun ma kai kadai ka sani idan naji a bakin wani nida kaine".
"Haba you know ii got you wannan kuma ai sirrine amma tsaya ta sani kodai kallon e yane take maka har yanzu" ya fada yana dage masa gira da tsokana. Kai kawai ya girziza tareda komawa ya kwanta sosai, a zuciyarsa tunani ne fal na yanda zasu kwasheta da ita. Gajiya yayi da tsokanar da Master yake masa yace ya tashi ya tafi idan ruwan ya qare ze cire da kansa amma yaqi seda ya masa wuta wuta sannan ya samu salama.

Har ruwan ya qare yacire be sake jin motsinta ba, already har shabiyun rana tayi kuma ya fara jin yunwa saboda alluran da aka masa dan haka ya fito palour yana tafiya a hankali kaman mace saboda yanda yake jinsa. He is totally new, kaman wani daban haka yake jinsa kamar an sauke masa wani nauyi daya hanashi walwala. Ko ina neat as usual be kuma ganta a palour ba seya nufi dakin da Master yace masa ta shiga.

Tana zaune ta kifa kanta akan study table tana bacci haiqan, jikin bango ya tsaye tareda harde hannayensa a qirji yana qarewa kyakykywawar fuskarta kallo. Shidai yana son Hamdah irin son da be san iya karsa ba. Zufa ya gani akan goshinta sabida dakin bata kunna Ac ba da alama kuma windows din dukka a rufe suke, seya qarasa ya durqusa a gabanta ya shiga busa mata iskar bakinsa me sanyi akan Fuskarta.

Cikin baccinta take mafarki da Jaan, Abdulmalik da rabonda tayi mafarki dashi har ta manta. Wai ya kaita wani gida me tsananin kyau yace mata sabon gidansa ne harda kukanta akan zata zauna tareda shi a gidan amma yace Aa wai itama taje ta gina nata har yafi nasa kyau. Wai setace masa zafi takeji ya kunna Ac yace Aa ta jira wani ze kunna mata shi yanzu babu komai zakaninsu se zumunchi yanzu wani ne da iko da ita ba shiba. Tana cikin masa kuka ne taji sanyi ya fara ratsata yace mata kin gani ko na gaya miki zezo nasan baze bari kiyi kuka ba. Seta qara gyara kwanciyarta tana shaqar numfashinsa dake chakude da kamshin mouth wash din da yake amfani dashi da kuma qamshin turarensa datake masifar so har wani qara bude hanci take tana shaqar kamshinsa. Se tama bashi dariya ganin yanda take ta juya kai duk cikin bacci, bakinta da take budewa kamar meson yin magana yake bi da kallo abinda baze taba iya resisting ya shiga kissing nata.

Bayan kamshi se kuma taji kaman ana bata madara duk fa acikin baccin lols se kawai ta bude baki sosai tana karba. Seda wasa ya fara nisa sannan ta farga ba ta bude idanunta, a iya saninta a kan kujera ta zauna da Zumbulelen hijab yanzu kuma ta ganta akan Rug da dan guntun towel. Baki ta hangame zata sa ihu ganin mutum a kusa da ita yai saurin rufe mata baki da hannunsa yace
"Shii karki tara mana jama'a" ya janye hannun tareda maye gurbinsa da bakinsa, ba tare da da saurara ba ta sa iya qarfinta ya fizge dare da hankadeshi gafe ya tafi gaba dayansa saboda har lokacin bashida cikakken qarfi ta nufi kofa batareda ta tsaya daukar Hijab dinta ba shima seya bi bayanta amma kafin yaje harta fita ta tsaya a daidai entrance din, Iya qarfin da Allah ya bata ta daddage ta kwalla ihu data san za'a jiyota har main Street sannan tace "Help me some body wants to rape me..." Ai be bari ta qarasa ba ya sunkuceta tareda datse kofar yayi cikin gidan da ita dukda irin ihu da dukan datake kaimasa.




🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*RUBUTACCIYAR QADDARAH*

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*By Maryamah* 💞💞
©2020

*PAGE* 4⃣2⃣


Duk yanda ze mata tayi shiru taqiya kamar wadda yake barbadawa yaji haka ta kware baki tana ihu tuni kuma ta tara masa jama'a a waje daga yanda yakejin ana buga kofar. Wata gigitacciyar tsawa ya daka mata da ta sakata dauke numfashi lokaci daya ta shiga taitayinta.
"Ki min shiru kuma Ki fashi kije ki gayawa mutanen da kika tara min tsorata kikayi babu kowa a gidan nan in ba haka ba na rantse da Allah sena baki mamaki, sena miki abinda baki taba tunani ba I'm going to show you my true colors dan haka tashi my Friend tun ban gama fusata ba" yanda yayi maganar kadai ya nuna mata bacin ran dayake ciki. Seta miqe Hannunta dafe da bakinta a qoqarin hana sabon kukan fitowa ta mike da guntun towel din jikinta se rawa yake abin tausayi dan ta tsorata.

"A haka zaki fita saboda hankali be je miki kafafu ba ko" seta juyo ta rarumumi Hijab dinta har tana tuntube ta tafi ta bude kofar. Already security din Estate din sun cika gurin ana qoqarin yanda za'a bude kofar, suna ganinta sukayi kanta kowa na tambayarta lafiyarta. Duk wata juriya da dauriya ta aro ta dorawa kanta sannan tace musu babu komai she just had a bad night mare (mummunan mafarki) kuma data farka ta ga babu kowa. Basu yarda ba seda suka shiga gidan lungu da saqo basu ga kowa ba abinda ya matuqar bata mamaki, to ta ina ya fita? Sallama suka mata da cewa in taji wani abun ba daidai ba she should alert them kuma ta tabbatar ta rufe kofarta da Key sannan suka tafi.

Kuka ta zauna ta na jerawa na tausayin kanta da rayuwar data fada. Haka ta wuni dakyar ta iya wanka abinci kuwa be samu masauki a cikinta ba gashi daga Zulaiha har Umm Ashrab basa nan bare ta samu dan tayin hira, Zulaiha ta tafi Ghana tun satin daya wuce Mamanta bata da lafiya, Umm Ashrab kuma suna dawowa ita ma ta tafi gidan Uncle dinta dayake anan London Matarsa ta haihu ya roqi taje ta tayata zama bayanan dama Ashrab din tuni yana can gidan. Seda tayi sallar isha taji Yunwa na qoqarin illatata seta miqe ta shiga kitchen ta hada tea da sauran Cake din da take dashi taci.

Batasan meyasa tunaninsa ya dameta ba dukda haushinsa datake ji yafi kewar yawa. Haka ta kwanta bayan data rungume Quilt dinta dayake tashin kamshin turarensa ta rufe ido ta bawai dan tana jin bacci ba sedan kawai tana so ta kawar da tunanin moment din dazu daya addabeta. "He is too Good" zuciyarta ta raya mata. Setayi saurin kawar da tunanin baccin dole ta sa kanta kana kallonta kasan bana dadi take ba.

Cikin baccin ta fara ji yana yinta yana sauyawa, his scent, his soft touches kaman tana mafarki. Seta qara gyara kwanciya sosai tana amsar sakonnin da yake aikata mata anata tunanin duk mafarki ne. Sosai ta saki jiki harda qoqarin maida masa da martani abinda ya qara masa qaimi kenan ya shiga sarrafata son ransa, seda lokaci ya qure mata, yayi nisan da bazeji kira ba sannan ta bude ido sosai jin abin yana nema ya wuce tunaninta. Abdul'ahad ne cikin yanayin da bazata iya fasaltawa ba, bashida buqatar wata magana ko qorafi a lokacin dan haka ya rufe bakinta ruf da nashi yakuma qi bata duk wata dama da zatayi masa gardama.

Seda ya samu cikakkiyar nutsuwa yana kwance a gefenta tana sana'ar tata wato kuka. Idanunsa a lumshe ya dafe kansa da hannu daya ya janyota jikinsa da dayan hannun.
"For God sake Hamdah ke baki gajia da kuka ne? tsabar gulma da munafunchi se da kika gama enjoying sannan zakizo kina min wani kuka na gaya miki in baki qoshi ba feel free to talk ba ki sani gaba kina min kukan tabara ba" ya qarasa yana kwantota akan broad chest dinsa dukda yanda take daddagewa tana jan Quilt dan ta rufe jikinta,
"Allah na tuba wane darene kuma Jemage be gani ba? Malama in zaki saki wannan abun ki kwanta yafi miki dan babu wani abu kuma dayai saura da zaki boyemin anan" yai maganar yana nuna jikinta. Luf tayi akan qirjin sa tanajin yanda zuciyarsa take bugawa da sauri da sauri seta kai hannunta wurin tana feeling heart beat din nasa.

"Kinji yanda zuciyata take bugawa da Sonki ko, haka duk numfashin dana shaqa cike yake da Qaunarki Hamdah" yayi maganar yana pecking goshinta. Bubbuga bayan ta ya shigashi yana busa mata Iska kadan kadan a kunne, duk yanda taso ta botsare masa ko tayi qorafi ya hanata a haka har bacci barawo ya dauke su gaba daya ba tare da sun shirya ba. Da Asuba batasan ya akayi ba ita dai jinta kawai tayi a cikin ruwa me dumi sosai yana ratsata, seta bude ido ta sosai cike da mamaki, Yana tsaye daure da towel iya qugunsa akanta ita kuma tana cikin bath din daya cika da ruwa. Ihu tasa ta shiga kare Qirjinta da hannayenta nan da nan Hawaye ya balle mata.

"Allah ya isa na bakuma zan yafe maka ba, ka cuceni ka zalunceni wallahi se Allah ya saka min" ko a jikinsa sema qoqarin zaunar da ita daya shigayi dan qoqarin mikewa daga ruwan take, ganin zata bata masa lokaci yasa ya daka mata tsawa
"Stand still malama karki batamin lokaci sallah nake so nayi" bata haqura ba takai wa hannunsa daya fara saba ta da soso dashi cizo tana cewa "Ai ba jikinka bane kuma ba kiranka nayi ba kuma Allah ya isa kallan mun jiki da kayi Mugu seka makance senaga da wane idon zaka qara kallon jikin wata matar".
Qaramar dariya yayi, shikam wautar ta tana burgeshi wannan yarinyar bazata girma ba. Wato seya makance to shi yanzu meya rage masa ya kalla kuma? Dan haka yace mata

"Ba komi na makance ai dai narigada naga jikin naki, kinga zan iya bada labarin yanda shape dinki yake, yanda size din......Shower Gel dinta ta wawura ta wurga masa yai saurin gocewa yan dariya, fita yayi yabarta a Bathroom din tana shaqar kuka dakyar ta bawa kanta haquri tayi wankan sallah kadai ta fito idanun nan sun kumbura yaluwar fuskarta ta koma Red. Haka ta tada sallar tana yi tana kuka, ta dade a sujjadarta ta qarshe ya tabbatar da qararsa take kaiwa Allah, se kuma jikinsa yayi sanyi. Yana zaune ta idar akan abin sallar ta kwanata saboda yanda kanta ya fara mata ciwo. Kwana biyu kenan tana kukan da bata san ran da ze qare ba. Duk yanda yaso ya rarrasheta taqi koda kallonsa. Yayi maganar yayi ban bakin har yagaji ya sa mata ido. Ranar dakansa ya shiga kitchen ya hada mata Breakfast ya kawo tana kwance amma ko kallo be isheta ba shida abincin nasa. Tunani take a zuciyarta ita kuma tata kalar qaddarar kenan, Abdulmalik ne kadai na kirki a cikinsu. Shi kadai ya sota tsakani da Allah so na aure ashe shi wannan zaman dadiro ma yake so yayi da ita. A duk lokacin data tuna ya keta gonarta har sau biyu abun na mata matuqar ciwo a zuciya. Ita wa zata gayawa damuwarta a yanzu? maryam ce ta fado mata a rai Aminiyarta ta amana.

Seta miqe dakyar ta bude idonta, baya dakin tun dazu ya fita taji sanda aka kirashi a waya ya fita. Wayarta ta dakko ta shiga kiran Maryam din sedai har tayi ringing ta qarata bata daga ba. Komawa tayi ta kwanta ta ci gaba da kuka wata zuciyar nacewa gara da Maryam din bata daga ba. "Ta daga kice mata Sir AA yana rayuwa dake kamar matarsa ko Yaya?" Wata zuciyar ta raya mata. Wunin wannan ranar ma haka tayi shi ba dadi in banda ruwa babu abinda ya samu masaki a cikinta. Ranar bayan key harda Sakata ta sakawa kofarta, tana kwance akan Rug a palour wurin 11:30pm taji motsin shigowar mutum. Seda Numfashin ta ya dauke tsabar tsoro kaman Aljani kawai ta ganshi a gabanta, to ta ina ya shigo?

Kallo daya tamasa ta hango tarin gajiyar dake tare dashi. Ledojin hannunsa ya ajiye Sannan ya shiga kitchen ya dakko Goran ruwa masu sanyi sosai ya kwankwade sannan ya kalleta duk ta zama wata abar tausayi.
"Stubborn soul" ya fada a fili yana wuceta ya shige dakin kamar na Ammi. Seta bishi da harara kafin ta miqe ta nufi kofar, ga mamakinta sakatar da ta saka tana nan. Se kawai ta dawo ta zauna ta zabga uban tagumin irin na babu mataimaki se Allah. Tana zaune ya fito da alama ma wanka yayi ya saka Three-quarter kalar kakin sojoji da farar Vest. Wani irin yar taji lokacin da idonta ya sauka akan jikinsa me qirar qarfi kaman yana Gyming tayi saurin dauke ido duk yana hankalce da ita.

"Get me plate and cups" ya fada yana chanza channel din data kunna. Setayi banza dashi kawai ta juya kanta ma can wani bangaren daban.
"Kinsan na tsani maimaita magana ko" ya fada ido sa akanta. Seta miqe tana tunzuro baki tayi kitchen din, haka ta dungurar masa da kayan a ranta tana mamaki ko kunya baya ji a fuska me cikakkiyar kamala amma yazo yana iskanci. Kazace data sha kayan hadi se kamshine yake tashi ya juyeta a plate din yana satar kallonta ilai kuwa idonta akai ita ma tayi saurin dauke kai a dole bata san raini.
"Kura kawai" ya fada yanda zata ji shi ta kuwa juyo ta balla masa harara amma fa ranta ya biya da kazar. Yoghurt ya tsiyaya a Cup guda daka kafin ya sauke kayan a qasa ya zauna sosai

"Come here" ya fada yana nuna mata gabansa. Ga yunwa ga kuma Kazar ta biya ranta dole ta tashi ta sauka ta zauna tana hade rai kaman dole aka mata. A baki yaringa feeding dinta with so much love and affection kamar me bawa jariri abinci haka ya ringa kula da ita. Seda ya tabbatar ta qoshi sannan ya fara ci tana kallonsa. Haushi, So da qaunar sa duk suna dukanta a lokaci daya.
"Kiyi haquri karkisa na komawa Ni'ima a rabi irin wannan kallon". Se kawai ta zumburi baki tana qunquni da tattare kafafunta da da tamike su, murmushi yayi kafin ya kai Cup din Yoghurt din bakinsa ya kurba sannan ita ma ya saka mata. Kin karba tayi se ya hade rai, tasan me ze biyo baya dole ta bude baki ya ringa daddaka mata har seda ta shanye. Shi ya tattara komai tana nade akan kujera tana Game a waya. Jira take taga ya tafi itama taje ta kwanta batayi aune ba seji kawai tayi anyi sama da ita ta bude baki as usual ya rufeshi ya shige dakin tareda tura kofar da kafarsa.

3 Month Later

Abubuwa da yawa sun faru ciki kuwa harda tattaro kayan Abdul'ahad da yayi ya dawo dasu cikin gidanta gaba daya. Study room dinta ya mayar dakinsa harda zuba sababbin furnitures. ita kam zuwa yanzu bata da bakin magana se dai ido. Ta riga ta fawwalawa Allah lamuranta kuma. Gashi kamar wadda ya asirce ta kasa fadawa kowa, to wazata gayawa wannan abun kunyar tasan da yawa ma cewa zasuyi da yardarta. Duk ta fige tsabar tunani da fargaba shi kuwa Alhaji Malam Dr Abdul'ahad kallo daya zaka masa kasan ya samu sauyin rayuwa. Yayi kyau ya murje fatarsa ta qara kyau tsabar hutu har wani dan kumatu yayi. Gaba daya ya gama sauke mata duk wata tuzurantakarsa bata da hutu ko kadan, idan taji qarar motarsa gabanta har faduwa yakeyi tsabar tsoronsa da takeyi yanzu kuka kuwa har hawayenta sun qafe sedai tayi na zuciya.

Idan da Allah ya isa na fitowa mutum a jiki kam da yanzu jikinsa babu masaka tsinke saboda yanda take kwarara masa su a Sallah ko haka kawai tana zaune. Gaba daya befi wata biyar ya rage mata ta qarasa Phd dinta ba amma batajin zata iya, Gara ta shirya ta tafi Nigeria ko zata huta da wannan masifar haka musamman tunda satinnan ya kama bata da lafiya. Zazzabi takeyi kuma seda safe ko taje makarantar wuni take a kwance kafin ta dawo gida kuma ya saketa amma ta alaqanta hakan da Jarabar Abdul'ahad da baya barinta isashshen bacci kullum da ciwon jiki take kwana take tashi, tana zaune tunanin yazo mata bayan ta taso daga makaranta. Seta shiga dakinta ta fara binciken passport dinta dan a yau zata fara neman Ticket bazata iya ci gaba da zama a London ba gara ko karatun ne ta haqura dashi haka Allah yaso indai Abdul'ahad ze kyaketa, seda ta bincike dakin tsaf amma passport yace daukeni inda kika ajiye. Kaf dakin seda ta hargitseshi amma babu passport babu alamar sa, se kawai ta zauna ta fasa kukan da yanzu ya zame mata jiki. Bottle water wannan in ta kasa budewa yanzu zakaga ta saka kuka shi abin har mamaki yake abashi. A haka ya shigo ya tarar da ita shima yau tun kafin ta tashima ya fita yana Lab tuni sun fara aikin daya kawoshi London din.

Gefen gadon ya zauna yana qare mata kallo, ba laifi yanzu ta fara warewa, wannan ramar da tayi ta ragu skin dinta har wani kyalli yake ga uban Haske data qara da kyau kamar Aljana shi da daddare in yakalleta wataran har tsoro take bashi sekace yar Aljanu. Idonsa akan fuskarta da tayi shabe shabe da hawaye seya bude mata hannu alamar ta taho, Kaman wadda yaja da Magnet kuwa ta mike cikin sassarfa ta isa jikinsa ya mayar da hannayensa ya rufe.
"Cry cry baby me akayi kuma?" Ya tambayeta yana shaqar kamshin da gashin kanta yakeyi wanda hular ta zame.
"Passport dina ban ganshi ba" ta fada muryarta cike da zallar shagwabar data zame mata jiki. Seya daga ta ya zaunar da ita sosai akan cinyarsa yana goga hancinsa akan nata yace
"Me zakiyi dashi yanzu to da kike kuka nidai dan Allah karki haifar min sangartattun yara irinki". Seta shiga kokarin mikewa daga jikinsa, ita bata san meyasa ba kamar wadda Jinnu ke shafa, yanzu zata manta zaman da suke ta sake dashi lokaci daya kuma abin ya dawo mata. Se ya qara rungumeta yana dariya qasa dan yasan me take tunani, magana ya shiga rada mata a kunne nan danan ta shiga dariya tana zillewa qarshe ta tashi ta fice da gudu. Kallo kawai yabita dashi me cike da So da Kauna. He believes his life is now complete with Hamdah by his side. Ringing din wayar sa ne ya katseshi se yayi saurin dagawa ganin sunan Ammi.

"Ammi barka da Yamma" ya fada cike da ladabi kaman yana gaban Ammin.
"Babana ya aiki ya kuma Amarya gaba daya ta boyeka ta hanamu ganinka ma" seya sunkuyarda kai yana shafa qeyarsa saboda yanda yaji kunya ta kamashi, yaushe rabonsa da Nigeria? Seya fara kame kame ya ma rasa takamaiman uzurin da ze bata. Muryar ta ce ta katse shi tana cewa "To nidai duk ba wannan ba kadai daure kazo dan Jikin Ni'ima yaqi dadi kwana biyun nan ga kuma waccen Gwaigwai din Yar taka ta ishi mutane da Dady kullum".

Seyai saurin miqewa tsaye cikin rudu yake cewa "Ammi meya samu Ni'iman meya sa baku gayamin tun tuni ba shi yasa ko a waya bana samunta kullum tana bacci" dai dai lokacin da Hamdah ta turo kofar ta shigo. Bata san da wa yake waya ba amma Sunan Ni'ima kadai dataji ya taso mata da wani mugun kishi da bata san tana dashi akan Abdul'ahad ba seta juya da baya ta fice daga dakin. Suna gama waya da Ammi ya fito, tana zaune se cin magani take kaman wadda aka daka ya wuceta ya shige sabon Bedroom dinsa. Karamar jaka ya dauka ya shiga zuba duk abubuwan da ze buqata dan gaba daya jinsa yake he is guilty, ya kasa sauke wasu haqqoqi da suka rataya a wuyansa ko ba komai Ni'ima Matarsa ce kuma ta masa abinda har ya mutu baze manta da ita ba, infact itace silar farincikinsa ayanzu abinda yake qara mata qima da daraja a idanunsa kenan. Seda ya tabbatar ya hada duk komatsansa sannan yaja Drawer inda ya boye Passport din nata, a jakar ya jefashi shima karma ya bari tsautsayi ya shigar da ita dakin ta gani.

Anan yayi wanka yai sallar Magriba sannan ya fito har lokacin tana zaune amma ta chanza kayan jikinta daga doguwar rigar Atamfar da ya dawo ya ganta da ita zuwa Wata yar riga me hannun Vest da ko cibiya bata rufe mata ba fara se leggings baqi ta tattare gashinta da tayiwa jerry curles a tsakiya seta zama kaman wata yar budurwar baturiya, da alama yau fitina take ji, haka take tayi shigar data san zata haukatashi kuma ranar be isa ko farcenta ya kama ba. Ta bayan kujerar da take ya salallaba saboda bata ga fitowarsa ba ya shafi wuyanta ai kuwa ta daka uban tsalle kamar wadda taga Miciji ta yi gefe ta bude baki zata yi ihu taga shine, dama me neman nayi se kawai ta fashe masa da kuka tana kai masa duka da pillows din kan kujerar. Palour suka shiga zagayawa tana kuka tana binsa shi kuma yana dariya se haki take dan ta tsorata ba kadan ba seda ta gaji ta zauna tana maida numfashi ga mararta dataji ta fara mata ciwo daga tsallen da tayi.

Shima seya zagaya ya kwanta a qasa kansa akan cinyarta yana leqen fuskarata. "Mugani kai gaskiya kuka yana miki kyau, bari na miki hoto kiga" se ya tashi ya shiga mata Video, lura yayi da yanda ta nutsu hannunta akan Mararta seya dakata ya durqusa akusa da ita tareda dauke hannun ya dora nasa akai yana cewa "sannu tana miki ciwo ne" Seta daga masa kai kawai alamar "Eh".
"Ko period zakiyi" ya qara tambayarta.
Lokaci daya yawun bakinta ya qafe wasu gumi suka shiga keto mata, in ba yanzu ba sam ta manta da zancen wani abu wai shi period a duniya dan dama ba sonsa take ba, idan kuwa bata bata lissafi ba wata biyun baya bataga al'adarta ba. Seta miqe zumbur kaman wadda akayiwa allura ta shige daki ko sauraron kiran da yake mata batayi ba.















🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*RUBUTACCIYAR QADDARAH*

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*By Maryamah* 💞💞
©2020

*PAGE* 4⃣3⃣


Tana shiga dakin taci birki, tama rasa abinyi ta ina zata fara. "Ya ubangiji ka rufamin asiri Allah na tuba" abinda kadai take iya maimaitawa kenan.

Please Login or Register in order to submit comment