Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

an kure Wanda baida gaskia,kasan kuwa irin sambatun da kakemin har kuka kayi a last da kayi,to yau kace baza kayi ba,
Habawa malam dole sai kayi Sambatu,yarinya ai waccen dan ban shirya bane amma wannan ba wani sambatu,a haka ya rinjayi Iklas ta yarda ita dole sai ta kure karya,da suka fara ma jajurcewa tayi iya fasaharta ta nunawa Omar wai duk dan yayi sambatu ta kureshi,sambatu Omar Ke mata sosai tana ta Kara jajircewa,ai kuwa Omar bai San kadan ba sai wajen asuba ya kyaleta,baya gajia da Iklas Sam,iklas kam yau sai murna takeyi tana na kureka Allah sai sambatu kakeyi wooooo,ai dama na fada ma nice fa Gomnati Ikon Allah

Omar murmushi yayi to naji kin kureni ai zan rama ne kema zakiyi fin nawa watarana,suna samun nutsuwa rungume take jikin Omar yana wasa da dukiyar fulaninta,tace honey Kasan me?sai kin fada cewar Omar,
Hmm Allah kaga na yau da kayi min baka ji ba kamar dadi dadi kuma zafi zafi,sai naji kamar kwakwalwata zata buga,daria ta bawa Omar sosai,Iklas ba ayin 1mnt bata bashi daria ba shi yasa yake matukar kaunarta,tana birgeshi ko yaushe nishadi take sashi,shi yasa ko yaje office baya iya aikin sai tunanin matarsa.shi kadai zakaga yana murmushi.

To next idan munyi dadin zaki ji gaba daya na fada miki,tab ai kuwa za ajini a makwafta kai na yau ma fa jurewa kawai nayi,murmushi Omar yayi yana bubbuga mazaunanta kamar jaririya yace bacci kinji maza muyi bacci.
Haka suka kasance cikin jin dadi da kwanciyar hankali har Iklas ta sha fe 2wks gidan Omar.

Baffa ne ya sauka a gida Nigeria kwanan sa daya yace Omar yazo yana son ganinsa,wankan sukari suka dauka shida Iklas tasa atamfa blue riga da skert, yasa shadda light blue,sai kamshi sukeyi kamar ka sace su ka gudu.wata dalleliyar mota ya zaba cikin jerin sababbin motocin da ya sake dal dal dasu bayan mota suka shiga driver na tukasu,hannunsu sakale dana juna Iklas na kwance a kafadar Omar tana lumshe ido Sanyin A.c na ratsasu,
Minti kadan Omar zai juyo ya hade bakinsu wuri daya yana tsotsa,haka har sukaje gida,
Tun daga nesa Iklas ke kwala sallama sai murna takeyi,su Suhaila suka gani Abdallah zai kaisu Islamiyya,da gudu suka rungume Iklas da Omar,Abdallah kuwa a zuciyarsa Yace bari na tsokani ya Omar Iklas ya mikawa hannu wai su gaisa,Omar bige hannun Abdallah yayi yana zazzaga masa bala'i,Mama ce ta fito kai kuma lfy?daga zuwa zaka cika mana gida da fada,Abdallah yana daria kyaleshi Mama wai daga na tsokaneshi,shinefa yake wannan fadan,Dalla malam get lost naga alama baka San me kakeyi ba cewar Omar,
Da sauri cike da ladabi da kunya Iklas ta duka har kasa ta gaishe da Mama, Mama sai dadi takeji tayi suraka yar mutunci me kula da danta,just 2wks amma Omar har yayi kiba ya kara wani fresh da kyau,

Da gudu Suleim ta kira Ummi ta fito tana a'a amarsu ce da angon nawa,Ummi ai munyi fushi cewar Omar,haba dai kai ka isa har kasa Omar ya gaisar da Ummi tana tsokanarsa ango wannan kiba haka kayi wani ja,me Iklas ke baka ne,tsugunawa yayi kusa da Iklas ya rada mata ki fadawa Ummi irin zumar danake sha,hararar wasa Iklas ta yi masa itama a hankali tace Zafa kasa muji kunya,so what?cewar Omar,
Ummi ce tace halina da yaran nan kenan sai ana abin arziki su fara na tsiya ba kunya ba komai,Mama tace zasu koma inda suka fito yanzu ai idan suka sake.

Iklas harda sunkuyar da kai kasa wai kunyar Mama, Omar zama yayi kusa da Iklas ya dan bigi kafarta da tasa kafar jibarki kamar gaske wai kunya sai gulmar tsiya murmushi tayi ta kalleshi da gefen ido tayi masa signa irin a bari sai mun kebe mu biyu.
Wurin Ummi Iklas ta matsa yar tsohuwa ya kk,shine kika manta dani ko? Ke rufe min baki ja'ira kin samu miji kin manta da kowa sai mu zamu biki,hira sukeyi sai ga Baffa ya fito daga sashensa, shima yaji matukar dadi ganin Omar dinsa ya samu nutsuwa,zama yayi a daya Daga cikin kujerun palon, cike da ladabi suka gaidashi yana ta samusu Albarka.

Babana sabo dakai na dawo kasar nan kayi laifi,cewar Baffa yanzu idan banda abinka Babana da hankalinka kayiwa yar mutane duka haka?wannan wacce mugunta ce,ai gwara da saketa ka kyaleta baka daketa ba,ba girmanka bane, iyayanta sun fada min komai nan Baffa ya basu labarin yanda sukayi da iyayen Sahar.
Ummi da Mama tabe baki sukayi sunji dadin sakin da Omar yayiwa Sahar gwara haka.

Omar a hankali yace Baffa kasan duka ba halina bane, ba ni na daketa ba,abubuwan da takemin ne sunyi yawa shi yasa na saketa,Ku kanku kuna da labarin abinda takeyi,
To Omar wa zai daketa idan ba kai ba?ni dan ka saketa bai dameni ba kayi dai dai,babu me iya zama da Sahar tana wannan lalatar.
Iklas cike da ladabi tace Baffa nicefa na zaneta, salati su Ummi suka saki suna mamaki,Iklas tace Allah Baffa ni bazan iya kishi da wata ba musamman Sahar,Kasan inda ta kamani tayi min duka ta farfasa min jikina ta kalli Omar ko ya Omar?kai ya daga yace ae Baffa Iklas ce ta rama dukanta,
Murmushi Baffa yayi to taya kika iya dukan Sahar haka,daria Iklas tayi tace Allah dan Baffa bakusan muguntata bane,a ruwa na sa mata kwaya tasha jikinta ya koma weak ko yatsa bata iya motsawa na cika mata aiki da wayar wuta ta karfe,nan Iklas ta bada labari kowa dariya yakeyi yanda Iklas har gwadawa tayi yanda tayiwa Sahar.amma bata ce ta yanka mata mazaunai ba.
Ci gaba tayi Dama kuma ya Omar yace zai koreta, Baffa ni kuwa na kara zugashi ya saketa, kowanne na dakin mamakin Iklas sukeyi har Omar dan bai San ta sawa Sahar kwaya ba,dama yayi mamakin ya akayi Iklas ta iya yiwa Sahar duka haka,
Ummi ce ta zubawa Iklas rankwashi rufe mana baki shasha sha marar kunya,wato kai Umaru ina ganinka me hankali shine ka biye wata Iklas ka saki Uwar gidanka,murmushi Baffa yayi a'a Ummi ki kyale min 'yata ni tayi min dai dai,gashi mijinta ya samu kwanciyar hankali.

A shagwabe Iklas ta ce Baffa ita Ummi fa ta daina so na amma fa baka ga abinda wannan Sahar din ke wa ya Omar ba,Mama ce tayi dariyar jin dadi Omar fa yayi dacen me sonsa tace kai kulemin 'yata tayi dai dai,ni bana fatan hada zuria dasu Sahar Allah raka taki Gona.
Dadi Iklas taji tana farin ciki tace Allah barmana Mamanmu.
Baffa yace yana daria wato mu a kashemu ko?kanta kasa tace haba dai Baffa ai bamu isa muce haka ba kai gayya ne ai.kai na daban ne.

Ummi ce ta shige room kyaji dashi ja'irar yarinya,hira sukayi sosai da Baffa sannan ya mike yana na fita ni idan na dawo da wuri shikenan idan kuma ban dawo ba Ku gaida gida,Iklas tace zamu iya jiranka ma Baffa ko kwana zamuyi,da sauri Omar yace kwana fa kikace bada ni ba,to ni sai na kwana cewar Iklas, haba yarinya kafata kafarki da gidanmu zamu kwana gidan wasu,Mama ce ta make Omar rufemin baki marar kunya,ni ban San yaushe ka dawo haka ba wlh,nan gidan ne gidan wasu sabo da kai kayi aure ga me gida ko,ka manta yanda ka dawo ka tare mana anan.
Allah kyauta cewar Baffa Babana ka fitsare kafarka ya fice suna masa a dawo lfy.

Saleem Arziki ya bunkasa yayi wata uwar kiba da kyau,sai fantamawa yakeji ya hadu da wata zukekiya chocolate ce me suna JANNAT har an tsai da ranar bikinsu.Ummi sune kan gaba,
Sahar ta warke sosai inda taci gaba da duniyancinta,kamar kullum wani sabon Alhaji ta samu me kudin gaske Hon.Saminu a wani katafaren hotel dake abuja ta je tayashi kwana,suna room dinsu suna aikata masha'a Hon ya faki idon Sahar ya zuba mata wani grain magani a gabanta sannan yaci gaba da shagalinsa,
Bayan ya nutsu wanka yayi yace mata zaije ya dawo,Ashe guduwa yayi,abinda Sahar bata sani ba Hon Saminu hamshakin matsafine,ta hanyar saduwa da mata yake kudin tsafi,
Bai Dade da tafiya ba ta mike itama tayi wanka ta shirya fes ta kwashi kudin daya bata ta sauka ta hau motarta harda bar masa short note kan bed,na wuce wurin aiki ka kirani a waya.
Tun da Sahar ta fara tuki wani kaikayi ya fara damunta a gabanta tun tana Susa a hankali ta koma yi da karfi,da kyar ta kai kanta gida,da gudu ta fada palonsu tana ihu da Susa.

Dakin Ummi Iklas ta shiga suna ta hirarsu Ummi na kara Jan hankalinta kan ladabi da biyayya,da kula da miji Iklas tace tab Ummi kina bata bakinki wlh,ai duk na wuce nan wajen a karatuna,ina sonfa mijina taya bazan kula da abina ba na bashi jin dadi,nifa ko yanzu ji nakeyi nafi karfin nayi Aikin Gomnati indai Allah ya horewa mijinka kuma shi mijin yasan me yakeyi yana sauke hakkokinsa yana ma komai na rayuwa dai dai iya karfinsa me zanyi da wani aikin Gomnati
Kinga Ummi komai tsadar abu yaya Omar yi min yakeyi jin dadin duniya na sameshi shi yasa na sa masa honey zuma zaki Ummi, salati da sallallami Ummi keyi,Iklas ko ajikinta tanawa Ummi daria tace Ummi ni dama sabo daku nake son aikin Gomnati na taimaka mu samu rufin Asiri sai gashi Allah ya rufa mana asiri,komai mun samu,ga karatun Suhaila jibi irin schl din da suhaila ke zuwa me tsada ji sutura ai mu sai godiyar Allah,Ummi tace aikin ma na mata yana da muhimmanci kwarai ta wani bangaren sai dai kawai na wasu bashi da amfani yanda wasu matan ke kauce hanya sabo da Neman kudi.

Iklas tace kuma Ummi abin haushi wasu idan miji yace su zaba ko aiki ko aure sai suce sun zabi aiki,idan suka kashe auren su fada hanyar banza,wasu mazan kuma suna cikin talauci mace tayi karatunta tana aiki suna rufawa juna asiri sai kiga ya sa mata ido a kudin,ba zaman lfy sai in zata bashi kudi,bayan baya iya sauke mata hakkokinta da Allah yace, matsaloli dai gasu nan Sai Allah kyauta.

Omar ne ya bar wajen Mama ya dawo wajen Iklas dake dakin Ummi, kwanciya Omar yayi kan cinyar Iklas rashe rashe Iklas harda sukuyawa tana shafa sumarsa honey ya akayi ne,me kake so,Yunwa cewar Omar,da wuri haka bari to na tashi kaji dan babyna iklas ta furta,Ummi sakin baki tayi ta ciro dankwalinta ta makawa Iklas ta kara makawa Omar dake kwance jikin Iklas sai daria sukewa Ummi.

Marasa kunyar karshen zamani Ku bar min dakina,Iklas tace ba inda zamu bari ma ki gani,mikewa Iklas tayi bari na kawo mana abinci,sai kuyi ai cewar Ummi,abinci Iklas ta kawo musu ita da Omar,sai lallabashi takeyi tana bashi a baki,shi kuwa sai shagwaba yake mata,Ummi na kallonsu tana mamakin rashin kunyar su Omar.

Mamace ta shigo taga abinda su Iklas keyi Ku kuma meye haka,kema Ummi ki korasu waje mana kika kyalesu,Ummi tace kyalesu wannan yar banzarce Mara kunya fitsararriya tace ba Inda zasu.nazo kiransu ne cin abinci shi ma kamar gidansu har sun ebo suna cin abinsu Mama ta furta,Ummi nuna Iklas tayi da dankwalin hannunta kinga wannan tantiriyarce ta je ta zubo masa jibi abinda Umaru keyi kamar shine macen.
Ficewa Mama tayi dan ita kunya suke bata.

Sunayin Sallar azahar Iklas ta koma dakin Mama time din Omar bai dawo daga masallaciba,Mama na ganinta tace wlh fitar min daga daki yanzu zaku zo Ku addabeni,kai Mama bacci fa nazo yi,Ummi ce ta koro ni,zo ki kwanta to ni dama makwafta zan shiga barka yanzu zan dawo,Mama tayi waje tana saka hijab dinta,
Omar na dawowa dakin Mama ya nufa,Iklas ya gani har tayi nisa a bacci,hawa gadon yayi tare da buga jikin bed firgit ta tashi idonta cike da bacci a shagwabe tace ka dauki hakkina gaskia,bafa zakiyi bacci ba nima haka kike zuwa kina min,mika Iklas tayi me Jan hankali da dare fa baka bari muyi bacci ka barni nayi yanzu dan Allah,
Ni kin manta har ruwa kike zubamin dan kawai kar nayi bacci.murmushi tayi ta wulkita kafafunta ta daurasu gadon bayan Omar,kai bayanka zaiyi dadin duka,cikin sigar wasa a hankali ta dinga yin chanese da bayan Omar da kafafunta,Omar sai kallonta yakeyi kamar ya cinyeta,tana birgeshi akwai son wasan tsiya wajen Iklas kamar yarinya yar 5yrs.

Kafafunta ya hade waje daya ya dagesu ya matsa su da karfi saida ta saki Kara tana bashi hakuri,dankwalin Mama ya dauko ya daure kafafun Iklas tam,
Ya jata jikinsa fitinanniya muyi baccin to gobe zakije schl, yau kuma da dare kin San ba bacci dai.
Murmushi Iklas tayi yawwa honey irin na jiya za muyi style din kwai sweet,daria sosai Omar yayi yace to karfa ki Tara min mutanen unguwa da ihunki,haba wa ya isa ya toshemin baki dole in sakata in wala wlh harda kukan sweet idan ta kama.Omar ya Riga Iklas bacci lallabawa tayi ta dauki gyalenta ta daure kafafun Omar,dankwalin kanta na atamfa ta cire ta kara daure masa hannaye ta koma jikinsa ta makale sai bacci.
4:30 Mama ta dawo ganinsu tayi suna ta bacci kowanne kafa daure da dankwali,shi Omar harda hannu ma.

Dariya suka bawa Mama tana lallai yaran nan naga Alama ciwon hauka ya shigesu,sallah tayi ta wuce kitchen domin shirya abincin dare still su Omar baccinsu sukeyi.
Ummi ce dake taya Mama girki tace bari na yaran nan suje suyi Sallah su leka wajen Haj Rahina su gaisheta. Yayi kyau hakan cewar Mama.






AsmaBaffa


Godiya gareku masu comment. Allah saka muku da alkhairi,ina jin dadi.
[9:18AM, 4/21/2018] ‪+234 903 944 2971‬: ⓂⓂⓂ
MA'AIKACIYAR
GOMNATI
ⓂⓂⓂ

170-175



By
AsmaBaffa.



Tashinsu Ummi ta shiga da niyyar yi amma sai ta saki baki tana kalonsu kowanne daure da dankwali,toilet din Mama ta shiga ta ebo ruwa kadan ta watsa musu da sauri suka bude ido,sai yanzu suka tuno a gidan Baffa suke fa
Ku je kuyi sallah fetsararru ku shiga sashen Umma Rahina ku gaisheta tana fadin haka tayi waje,Omar kallon hannunsa da kafafunsa yayi yasan aikin Iklas ne ,murmushi ya watsa mata sai ki kwance ni yarinya, hannun daya daura ya kwance,wai yaushe ma kika daureni ban sani ba,murmushin dake kara mata kyau saki masa kana ta bacci ta fada tana kwance masa sannan itama ta kwance nata kafar,

Sallah sukayi sannan suka nufi sashen Haj Rahina,dukkansu yan matan Umma suna palonta har Sadiya da Aisha sunzo gaida Ummansu,Iklas sai da ta kara cin Uban kwalliya me kyau,ta kashe dauri tare da kara fesa turaruka,hannunsu sakale da juna sukayi Sallama palon Umma,yuuuuuuu suka zuba musu Ido,Najja ce ta maka uban tsaki tare da Hararar Iklas da Omar,
Suma kannensu su biyu su Amina harara suke kawai aikowa da Iklas,Sadiya da Aisha sun Lula tunanin duniya,a ladafce suka gaishe da Umma ta amsa kadaram kadaham,ba yabo ba fallasa,duk sauran kannen Sadiya iya Omar suka gaisar,Iklas tana kallonsu bata kulasu ba itama,

Kallon Amina Iklas tayi tace yan mata an girma sai aure,haka kika kara girma,kallonta ta mayar kan Sadiya da ta yamushe a gefe daya,tace a'a Ashe kina nan ya kk,ga Maman yan biyu ma,gaskia Aisha kinyi saurin samun ciki,daga kaiki sai ciki.duk wannan maganar da Iklas ke musu Amina karama ta girmi Iklas bare su Sadiya,

Gaba daya su Sadiya ganin yanda Iklas ta kara komawa,ta mirje ta kara yar kiba,ga kyau komai yaji duk sai suka raina kansu,musamman irin tsadajjiyar atamfar dake Jikin Iklas,sai kallon Takalmanta sukeyi,
Komai na jikin Iklas unique ne,abin sai ya birge Sadiya da Aisha da suke jin jiki a dakin miji,shi yasa rainin hankalin ma da Iklas tayi musu basu damu ba Sam,sai su Najja yan mata da Amina su suka dauki zafi,ganin sun girmi Iklas amma tana raina musu hankali dan kawai tana auren yayansu,Haj Rahina kuwa sake sake takeyi Aranta gaba daya jikinta ya mutu taga lallai baza ta iya samun Nasara ba,amma zata nemi shawarar kawarta Haj binta.ko da wani taimako da zatayi mata.
Umma sai mamakin rashin kunyar Iklas takeyi a ranta tace yarinyar nan jaraba ce naga Alama tafi karfinmu.
Umma ce tayiwa Najja Signa da Ido kan ta rama abinda Iklas tayi musu,a masifance cike da rashin tarbiya Najja tace Ya Omar kayiwa matarka kashedin fada mana magana anyhow,duk cikinmu ba sa'anta,dan kina matarsa bazaisa ki samu damar raina mu ba,banza a banza yar matsiyata daga zuwa cin arziki an mallake mutum da tsafi,

Aisha ce ta bige bakin Najja dalla rufe mana baki,Iklas tace nafi karfin na tsaya ja inja dake,ta karkace dauri taci gaba baki isa ki kirani yarinya ba,saboda na fiki sanin duniya,yarinya baki San komai ba tunda baki aure ba,Sadiya ce cike da sanyin jiki tace pls a bar zancen ya isa haka kiyi hakuri Iklas ki kyalesu yara ne basu inda duniya tasa gaba ba.daga har Iklas sunyi mamakin Sadiya da Aisha,sun canja kamanni da hali.

Umma harara ta Dallawa Sadiya,Omar mikewa yayi tare da Jan hannun Iklas ransa bace,Najja ce ta biyosu a baya ta sha gaban Iklas tare da narka wata ashar uban me kika sani a aure, ke karamar yar iska ce,
Kallonta Iklas tayi ta dan saki murmushi yarinya kenan,Najja ce ta kara karfin muryarta mene abunda kika sani Wanda ni ban sani ba,me zaki nuna min?
Iklas a nutse take fadanta silent killer ce,nasan tsayinta nasan kaurinta what of u?oh nasan zaki sani tunda ke taki ba Sadaki kika sani dole kinga da banbanc.....shut up a tsawace Omar ya furta,banza yar Tasha me tallan kwai da Apple cewar Najja,maganar ta konawa Iklas rai,wato Omar ya gama bazawa a danginsa ita tayi talla,ga zahiri kowa idan ya tashi yi Mata gori da yar matsiyata yar talla suke Mata, Sahar ma ta fada mata,a ina sukaji har ta saida Apple da Egg tabbas Omar ne zai fada,wani bakin ciki ne ya lullube Iklas,

Bata San sanda ta cakumo Najja ba,Omar ya fara tafiya ya zata Iklas na bayanshi sai yaga wayam, hangosu yayi rukume da juna suna dambe, dama ga Najja garin jiki ne da ita narkekiyace ga tsayi ga kiba,Iklas kamar biri ta dafalfale Najja,Najja ce ta dage ta ciji Iklas a hannun da ta shaketa, fatar hannun Iklas ta dauke sai jini,Iklas ma bata bari an shata a banza ba,Najja ta gartsawa cizo a kunne sai jini Shar ta Kunnen Sadiya,
Samu tayi iya karfinta ta lankwasa yatsan Najja na tsakiya ji kake rukus, da sauri Najja ta durkushe kasa tana wayyo ta ballamin yatsana wayyo Umma na shiga Uku,

Omar da sauri ya karaso wajen bai wani tsaya bata lokaci ba ya fyallawa Iklas wani lafiyayyen mari,cik Iklas ta tsaya dafe da kunci,Najja na ganin haka tayi luf ta daina kuka sai dariar mugunta ma da takewa Iklas a boye,gwalo tadinga yiwa Iklas,Omar kuwa Najja ya kama ya Mikar ta tsaye,yana antaya mata zagi banza shashasha jaka,dabba wuce ki bani waje kafin na kwadeki,Baku da aiki sai jaye jayen fada da gulma,wlh idan Iklas tazo gidan nan kika kara tararta da fada sai na karyaki haka Omar yayiwa Najja tas,

Ido suka hada da Iklas wacce har yanzu tsaye take kamar gunki,suna kallon juna Iklas ma tayiwa Najja gwalo ta rama itama harda itama dariyar duk abinda Najja tayi Mata sai da ta rama,Kafin Omar ya juyo Iklas ta Nutsu bai San me sukeyi ba,
saida Najja tayi nisa ta juyo tacewa Iklas Apple and egg ta shige gida.Omar yayi Dana sanin Marin wifey dinsa da yayi yaga tabbas Najja yar iskace itama,ashe tuggu ta hadawa Iklas dinsa gashi ya jangwalo tsiya,taya zai lallasheta duk da yasan itama wifey din tasa tsokanar tsiya gareta.

Matsawa yayi wajenta fuskarsa ba rahma yace muje ke kuma ai yana magana Iklas ta rushe masa da kuka ji kake Tim ta fadi kasa tana ta birgima da shure shure,wayyo wayyo wayyo zasu kasheni dangi sunyi min taron dangi,dama ba sona yakeyi ba,yafi son danginsa dani,an zalinceni,zai kasheni,miji me dukan mata aka aura min dama, ni gwara na koma titi talla na,baya tausayina wayyo Allah na tun ina yar mitsilata an fara yi min tabo ajiki akan dangin miji.
Tsakaninta da Allah Iklas ke shure shurenta,Mama da Ummi sunji kamar hayaniya da gudu sukayo waje, su Umma ma dasu Sadiya duk sun fito,Iklas suka gani tana shure shure Omar na tsaye gefe guda yana tintsira dariya danshi dariya abin nata ya bashi.

Ummi ce fara magana ke meye haka lfy?kunamace ta harbeki, Umaru mene haka?da Sauri Iklas ta kalli Omar still kuka takeyi,ido Omar ya mintsina mata wai ta rufa masa Asiri.

Tana sheshekarta tace ba...ba...cinnaka bane ya cijeni,kuma Honey ya kwace min wayata,mene kuma honey inji Ummi, wani farin ciki ne ya lullube Omar shikam abin kunyane ace ya mari Iklas da hannunsa,
Kowanne cikinsu tsaki yaja Mama tace naga ranar da zakuyi hankali, Ita Sadiya birgeta sukayi ita yanzu ta isa tayiwa Alhaji Balarabe haka.ai ranar sai dai gawarta,gata tana aiki tana daukan salary amma jin dadi da zaman lafiya ya gagareta,duk sun tashi a banza.

Kowannensu part dinsu suka wuce,Suna shiga Mama ta kallesu Babana fada min gaskia me ya faru ban yarda daku ba,ganin Basu Umma Rahina Iklas tace Mama Najja ce fa ta zageni tace min yar tallar Apple and egg shine mukayi fada amma saboda Ya Omar yafi kaunar danginsa ya mareni a gabanta kalli inda ta cijeni Mama, su biyu suka rufarmin wai su ga yan uwa,Mama wai mutum ya daga hannu ya doki matarsa ta sunna ai ya fadi ba nauyi,
Omar mukus yayi yace Mama..... rufemin baki shashasha sosai Mama taji haushin Omar,fushi sosai tayi da Omar,Ummi kuwa tasan dole Iklas Nada laifi a zancen nan amma Mama taki yarda,duk suna zaune Palo kowanne tsit kakeji in banda Mama da ta dage tana yiwa Omar fada, ka samu mace me sonka haka ka fara shirme akan Wanda basu da makiyi kamarka etc Iklas sai taji bata son fadan da Mama kewa Omar, sai taji ya bata tausayi gashi Mama na fushi dashi,Ummi sai Hararar Iklas takeyi, Omar ne yayi magana Mama kiyi hakuri haka mana,ai duk ita ta jawo baki San tsokanarta ba,duka Mama ta danawa Omar a bayansa, me makon aji Omar yayi kara Iklas ce ta gantsare ta saki

Please Login or Register in order to submit comment