Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wa na kama, gaskiya a jinjina wa wannan yarinya da tayi nasarar sace min zuciyar ɗan uwa na abinda ban taɓa tunani ba, mutuman da ko kallon mace baiyi bare har a saran zai mata magana, yanda ƴan matan Niamey ke rububun ka amma basuyi nasarar samuka sai ƴar maraɗi, kai gaskiya matan maraɗi sun ciri tuta ya kamata a jinjina masu."


AFREED yace "Kaga nifa ba dan kayimam iskanci bane na faɗa maka idan kana bani shawara da zata anfane ni to ka faɗa man ni banson iskanci, ko faɗawa soyayya haramun ne ko kuwa ni kaɗaine hakan ta fara faruwa da ni ne."


Ali na ganin ransa ya ɓace yace "Haba yi hakuri broh ba wai dan wani abu bane na faɗi haka ba kawai kaban mamaki ne par surprise na ji zancen (a bazata) dole na ce haka, amma ina da wata mafita idan ta maka to matsalar nan ta kau."


AFREED ya wani haɗe fuskar kamar ba yason jin mafitar a dakile yana wani shan magani yace "Ina jinka."


Murmushi Ali yayi yace "To saki fuskar man kana wani yimin yanga kamar baka son jin abinda zance."


Shidai AFREED bai ce masa komai basai fido wayar sa da yayi ya shiga dan nawa kamar bai sauranran shi."


Ali ya ƙara yi wani murmushi dan yasan halin mutum nashi ba tanka masa ba zai yi sannan yace "Mafitar da na samu itace zan shiga in fita in sama maka number ta daga nan sauran ya rage naka sai kasan abin yi."


Ɗan ɗagowa AFREED yayi daga kallon wayar sa ya dubi Ali da yaga Ali shi yake kallon sai yayi saurin maida idon sa ga wayarsa dan kar Ali yaga damar sa, amma a zuciyarsa sai da ya furta "Alhamdulilah."


Ali ya yi murmushi yace "Hum ba ma ko zaka godeman ba to na fasa nemo da number tata sai kayi ai." Ali na faɗar haka ya tashi ya fice daga ɗakin."


AFREED ya bi bayan sa da kallo har sai da ya fita, yana ganin Ali ya rufo masa ƙofar yace "Allah nagode ma nan ba da jimawa ba zan fara waya da farin ciki na, broh ai nasan ka faɗa ne zaka nemo man number ta alhamdulilah."


Shi kuwa Ali ya na fita ya nufi ɗakin sa ya zauna ya na tunani ta ina zai fara neman number AFREEN, can cikin tunanin ya tuna ashe makarantar su ɗaya da Khadijah, kawai ba tare da ɓata lokaci ba ya fido wayar sa da ga aljihu ya nemo number Khadijah yayi lancé appelle (ya turo kira) tare da karawa a kunne, sai da kiran ya kusan tsinkewa a ka ɗaga wayar tare da sallama.


Ali ya amsa sallama sannan yace "Hubby yau ko dai laifi nayi ban sani ba naga ba'a ma son daukan kiran nawa."


Murmushi mai sauti Khadijah tayi sannan tace "Wallahi Hubby ba haka bane bana kusa da wayar ne na shiga wanka ina fitowa na tarda wayar tana ruri da ba ma zan ɗaga ba, kawai idona ya sauka akan sunan da nasaka maka ne ke yawo saman screen ɗin sai nayi saurin ɗaga dan kada ta katse."


Ali yace "Ah kane ya faru to shikenan na maki uzuri ya kike ya gida ya su tanti da tonton injin dai kowa lafiya?"


"Lafiya lau wallahi, ya su momy da yaya AFREED dan yan biyu kuma?"


Yace "Kowa lafiya, ya karatu?"


Tace "Alhamdulilah."


Ali ya ɗan nisa sannan yace "To madala Allah ya taimaka, kina jina Khadijah wani ɗan aiki ne zan sakaki dan Allah in babu damuwa?"


"Lah Hubby dan zaka sakani aiki har sai kace dan Allah mi zaka sakani na ƙasa yi in dai ba saɓon Allah ba ne, ai ko babu komai a tsakanin mu kai ɗin yaya na ne kana da ikon sakani ko wane irin aiki ne kuma nayi ko inaso ko ba naso."


"Hakane hubby amma duk da haka ya kamata na fara tambayar ko kina da dama ko ai sa c'est normal?"


"Hakane kuma to ina jinka miye aikin da zan yi ɗin?"


Saida Ali ya ƙara gyara zaman wayar a kunanan sa sannan yace "Number wata ƴar islamiyyar ku nake so ki samo min a na cema ta AFREEN wata ƴar fara doguwa farin nata dai ba sosai ba wada ta fara karatun a ranar saukar ku."


Fuskar Khadijah da ke ɗauke da murmushi ta koma kamar bata taɓa dariya ba cike da game fuska tace "banga ne taba kuma miye zakayi da number ta, sannan karasa wanda zaka saka wannan aikin sai dan baka ɗauke ni da mahimmanci ba."


Murmushi Ali yayi yana jin daɗi wai saboda shi ne Khadijah ke ta wannan shan maganin alhamdulilah shima an fara kishin sa, daga bisani sai yace "Kwantar da hankali hubby ki yarda dani babu abinda zanyi da number ta ina da ke kuma mi zai kaini kula wata kawai inada buƙatar number ne daga baya zan sanar maki dalilin neman number nata kawai ki taimaka ki nema man idan kikayi hankan kamar kin ceto rayuwa ne."


"To shikenan hubby na gane ta ai dama da gangan nace ban gane ta ba zan nemo number ta insha Allahu sabida ƙanwata ƙawata tace."


"Masha Allah kinga abin ya zo da sauƙi, to sai naji ki gaida su tanti."


"Za su ji insha Allah." Daga nan Ali ya kashe kiran sannan Khadijah ta ajiye wayar ta na murmushi ta nufi wardrobe dan fitar da kayan da zata saka."


Bayan kwana biyun da Ali ya yi kiran Khadijah don ta nema masa number AFREEN, sai gata ran cikon kwana na uku ta kira shi ringing biyu ya ɗaga tare da sallama yace "Hubby barka ki da warhaka da kin yuni lafiya?"


Tace "Lafiya lau ina yuni?"

Yace "alhamdulilah ya gida?"


"Gida lafiyar sa lau."


"To madala ina aikin da na saka ki komai ya daidaita ko kuwa?"


Tace "Komai normal hubby aiki na ƙarasa kiran dana maka kenan na baka résultat ɗin aikin."


Ali ya waro ido kamar tana ganin shi sannan yace "Da sauri haka hubby injin dai baki ce wani ke buƙatar number ba."


Tace "Haba hubby kamar banda hankali, kamar kuma ba mace ba, kawai sai na fito fili na tunawa kai na asiri, to da nayi haka ai da yanzu ban samo lamba ba dan ita da kanta Zeinab ƙanwar ta ɗin bata san na ɗauko number a wayar ta ba."


Ali yace "To ya akayi ki ɗauke ta ba tare da ta saniba."


Murmushi Khadijah tayi sannan tace "Ƙarɓa wayar ta nayi nace ƙawata bari naka sunan da kika saka min a matsayin na ƙawar ki wace baki da kamar ta a islamiyyar nan, sai Zeinab ɗin tace to shikenan bari na baki ƙawata a tunanin ki mi zan saka, kawai sai ta miƙon man wayar na shiga nayi ta duba numbobin mutane banga inda ta saka sunan AFREEN ba, amma sanin yanda ta ke ƙaunar AFREEN ɗin yasa wani suna da nagani ta saka ma deuxième mère (my second Mom) ya ɗaukar man da hankali sosai sai natsa akan sa na tambayeta nace wacce kuma wada kike ji sosai ki ka saka ma wannan sunan, tana murmushi tace man anty AFREEN ce daga nan nayi hamdala sannan nace a lallai yanzu nayar kuna jin juna sosai, tace sosai kuwa ban san ya zan kwatanta yanda nake son ta ba wallahi ni banda kamar ta duk cikin yaye na, ba tare da ta lura ba na hardace number a kaina, sai nayi mata sai anjima nayi tafiya ta harda tambayar naga sunan da ta sakamin ɗin nace mata eh, ina gusawa daga gun ta na saka number a phone ɗin na na saving ɗin ya dan kar na manta."


Ali ya saki murmushi yace "Woow very nice shiyasa nake alfahari dake hubby gaskiya kinyi taimako, ban zan tamɓa mantawa da wannan ba yanzu ki turoman number ta whatsapp yanzu yanzu ina jiranki nagode sosai hubby." Ba tare da ya jiran jin abinda zata ce ba ya katse kiran.


Ba musu Khadijah ta tura masa number daidai ya kuna data saƙon number ya shigo, buɗe saƙon yayi tare yi mata reply kamar haka "Nagode sosai Allah saka da alkairi kinyi ƙoƙarin sosai." sai ya tura sannan ya sake tura mata sticker da aka rubuta i love you sai kawai ya kashe data ya nufi toillet danyin wanka saida ya ɗauki kusan min ashirin kamin yake fito ya shirya cikin wasu haɗaɗun ƙananun kaya masu mugun kyau kuma su ka zauna a jikin sa tsaf kamar dan shi a kayi kayan, sannan ya feshe jikin da daɗaɗan turaruka masu mugun kamshi a take ya fara zuba uban kamshi kamar yayi wanka da tekun turare sannan ya fito daga nashi ɗakin yana ta sakin wani haɗaɗen murmushi kamar wanda akayiwa albishirin shiga aljanna, don yau jin sa yake a cikin wani irin farin cikin mara musultuwa, saboda gani yake ya samo maganin ciwon ɗan uwansa zai warke har abada.


Ɗakin AFREED Ali ya nufa kai tsaye ya buɗe ƙofa ya shiga tare da yin wata ƴar siririyar sallama AFREED dake zaune saman wata haɗaɗiyar kujera dake ɗakin kansa a duƙe da ya dafe a hannuwan sa ya rasa abinda ke masa ɗadi saboda tunanin AFREEN ya amsa masa sallamar ba tare da ya ɗago ba.


Kusan minti biyu Ali ya yi a tsaye ya nazarin ɗan uwan na sa da bisani sai ya ƙarasa kusa AFREED ɗin ya zauna tare da dafa shi, sai a lokacin ya ɗago kansa ya sauke idonsa da suka yi ja kamar gauta cikin na Ali, da sauri Ali ya janye hannunsa da ke saman kafaɗar AFREED tare da ɗan gusawa kaɗan daga kusa dashi a ɗan tsora ce yace "Broh lafiyar ka mi ya sami idon ka kuma komi yake damun ka yanzun, ku ma dan Allah faɗa man kada kasa hankali na tashi."

Ɗan riƙo hannun sa AFREED ya yi sannan ya koma kallon sa yace "Wallahi broh ina cikin matsala nakasa jure rashin yarinya nan, yanda nake ji a cikin zuciyata da yanda son ta ke bin duk sasan jikina yana ratsa jinin jiki na da ilahirin jikina baki ɗaya ya hanani sukuni, gani nake inda banje Maraɗi na nemo ta ba na faɗa mata abinda ke raina zan iya rasa rai na wallahi." kawai sai ga hawaye na gudu a saman fuskar AFREED.


Da mugun mamaki Ali ke kallon AFREED da wani irin tausayin sa da ya ɗarsu a zuciyarsa wai yau AFREED ne ke zubar da kwala sabida wata ɗiya mace, macen wacce bata masan yanayi ba, shida yasan da ko kallon mace baiyi bare har yace yana son ta har soyayyar ta ta kaishi ga haka Allah kenan mai yanda yaso bai taɓa tunanin haka ga AFREED ba.


Bai ƙarasa mamakin saba yaji AFREED na cewa "Ka taimaka min ɗan uwa dan gaskiya nakasa jurewa har ma na yanke shawara zuwa Maraɗi gobe Insha Allahu dan nemo farin cikin rai na."


Da sauri Ali yace "Ai ba se takai ga haka ba ka kwantar da hankalin ka insha Allahu AFREEN taka ce, kai ko yanzu kake so masa zaka iya jin muryar ta dan kuwa har na riga da na nemo maka number ta, saboda ni ma ba jure ganin ka a cikin wannan halin wallahi yanzu komai zai daidaita Insha Allahu."


Wani irin farin cikin ne ya mamaye zuciyar AFREED da har bai san lokacin da ya kama Ali ya rungume ba, ya sakin murmushi tare da hawayen farin ciki yace "ba nida kamar ka ɗan uwa ba zani taɓa samun farin ciki mai ɗaurewa ba in babu kai, ni ban masan wane irin godiya zan maka ba, mi ka keso nayi maka da zai sanya ka farin ciki ka gama min komai a rayuwa Allah ya biyaka da mafificin alkairi ya sada ka da aljannar fidaoussi.


Ali yace "Ni sakeni dan Allah miye na wani yi min godiya ne, ka nagani ina iya farin ciki ne idan kai baka tare da shi, ni kawai ka ɗauki number ta na baka ka samu ka kirata tun kan lokaci ya ƙure maka, ka san ƴan mata ba su zama babu saurayi to idan ka bari wani ya riga ka shiga zuciyata, to fa sunan ka sorry, abinda zaka min naji daɗi kuwa shine kayi gaggawar saka ma yarinyar nan soyayyar ka mai tsananin kamar yanda itama ta yi ƙoƙarin wajen saka tata a zuciyarka, koda kuwa ta nada wanda take so inason kayi ƙoƙarin mayar da soyayyar ta sa a kanka har kazo ka ci nasarar aurenta, idan kayi to ni ka gama yi man komai wallah."


"To shikenan Ali naji saka man number a nan," AFREED ya faɗa ya na mai miƙa masa waya sa cike da farin ciki.


Karɓa Ali yayi ya saka number sannan ya tashi ya fice ya na mai cewa nan da kwana biyu inji dadaɗan labari."


Ali na fita AFREED ya saki wani haɗaɗen murmushi tare da mai da gaba gabas ya yiwa Ubangiji sujada ta nuna godiyar sa a garesa, sannan ya miƙe ya nufi toillet yana farin ciki kamar ba shine ya gama hawaye yanzu ba."


Yana fitowa daga wanka ya tsantsara shiri wanda rabon da da yin sa har ya manta kai kace gun AFREEN ɗin zai je zance ya gama feshe jikin da daɗaɗan turaruka ya fito daga ɓangaren na su gaba ɗaya ya nufi garden inda iskan sanyin maraice ke bugawa, yana ida shiga garden ɗin ya zauna a ɗaya daga cikin kujerun dake gun, tareda fido wayar sa don kiran AFREEN har ya tura kiran kuma da sauri kamin kiran ya shiga sai ya katse kiran, yana tunanin to idan ya kirata mi zai ce mata shi da ba soyayya ya ɓayi ba, hasali ko mace bai taɓa yiwa magana inba secretary ɗin sa in ka fida iyayen sa mata da kuma ƙananan sa, ya na cikin kuma wannan tunanin, saikuma gabansa ya faɗi dalilin tuna cewa ya taɓa ganin AFREED da saurayin ta wajen saukar da su kayi kada a ce ma tayi aure ko da yake da Ali ya samo man labari inda tayi sai kuma yace "Zanyi ko ƙoƙarin saka soyayyata a zuciyarta koda kuwa ta nada wani ai ita allura ce cikin ruwa mai rabo kan samu, kuma in Allah ya yarda malaki na ce shiyasa ma par coïncidence sunayan mu suke shigin na junan mu.


Can AFREED yayi tunanin bari ya fara mata magana ta whatsapp idan tana yi, ai ko take yanke ya shiga whatsapp ɗin sa ya shiga neman sunan da ya sakan mata mai taken ma femme insha Allah (my wife) yana dubawa kam yaga sunanta ya fito a whatsapp kawai ba tare da ɓata lokaci ba ya ɗaga mata hannu tare da rubuta mata salut (hello) sai ya tura cikin sa'a kuma sai a ka yi katarin tana en ligne (online).















*Kashi nayi kokarin wajen ganin na faranta maku har nayi page uku ki da jina kuma sai bayan sallah in da rai da lafiya insha Allahu* 😘😘😘
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*ZAMBA CIKIN AMINCI*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸




Écrit




Par



*QUEEN ZEEFAT*




_Ƴar_
_Mutan_
_Niger_




*Wattpad@nazichou*


💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝
☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/




*_BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM_*





*Page* : 51 & 52

Can AFREED yayi tunanin bari ya fara mata magana ta whatsapp idan tana yi, ai ko take yanke ya shiga whatsapp ɗin sa ya shiga neman sunan da ya sakan mata mai taken ma femme insha Allah (my wife) yana dubawa kam yaga sunanta ya fito a whatsapp kawai ba tare da ɓata lokaci ba ya ɗaga mata hannu tare da rubuta mata salut (hello) sai ya tura cikin sa'a kuma sai a ka yi katarin tana en ligne (online).


AFREEN na cikin chatting da kawayenta a cikin wani group ɗin su da suke tura abubuwan ƙaruwa na Musulunci sai kawai taga alamun saƙo ya shigo da wata bakuwar number da bata sani ba, sai ta fita daga group ɗin ta ƙurawa number ido na kusan minti 3, sai ta sauke ajiyar zuciya tare de cewa can cikin ƙansan zuciyarta "Waye keda wannan number kadai KAMAL ne Idan kuwa shine mi zai ce man kai ba ma shi bane don ba number sa bace, to waye?" AFREEN ta tambayi kanta.


Da har zata huce kuma sai ta buɗe saƙon ta karanta yafi sau uku sannan tayi ta tunanin tashare ko wanene ko kuwa ta mayar danjin ko waye, kawai sai ta yanke shawarar mayar masa da sakon sai ta rubuta masa cewa "salut Xava?"


AFREED nagani ta maido sefa yaji wani farin ciki ya sabko masa a zuciya, bata tare da ɓata lokaci ba ya mayar mata da amsa ta gaisuwa nan dai suka gaisa sannan AFREEN tace "A qui j'ai l'honneur (dawa nake magana)."


Ba tare da wani noke noke ba AFREED ya sanar mata ko shi wanene da kuma inda yasanta sai dai bai faɗa mata matsayin sa ba da kuma aikin da yake.


Nan AFREEN ta sheda shi sannan tayi mamakin inda ya samu number ta, amma bata tambaye shi ba, nan suka ƙara gaisawa, nan dai ya nemi alfarma ta bashi izinin kiranta anjima akwai maganar da yake so zai gayamata, da har taso taki amincewa kawai sai taji ta na so jin abinda zai faɗa ɗin se kawai tace "Allah ya kaimu"


Sannan sukayi sallama AFREEN ta daɗe a zaune ta na tunanin ina ya samu number ta kuma miye abinda yake son faɗa mata, kamin ta tashi ta nufi douche (bathroom) sabida kiraye kirayan sallah magarib da taji an fara ta na shiga ta dauro alwala ta fito ta shimfida darduma ta tayar da sallah.


AFREED na jin AFREEN ta amince da ya kirata hada ɗan tsalle yayi sannan ya nufi ɗakin shi shima ya dauro alwala ya fito a hanya ya haɗu da Ali suka jera suka tafi masallacin a tare.


Wajen ƙarfe goma na dare AFREEN na kwance a saman makeken gadon ta idonta a lumshe kamar mai bacci amma ba bacci take ba saboda bacci ya gagara daukar ta kawai tana kwance tana jiran kiran da AFREED zai mata bata san miyasa ba amma taji tana mugun son ji abinda zai faɗa mata, saboda tana tunowa da kiran nashi kawai sai taji gaban ta ya faɗi shiyasa ta matsu ya kira amma gashi kuma har yanzu bai kira ba, bata ƙarasa tunanin ta ba ƙarar wayar ta ya katse mata tunani da sauri ta tashi zaune ta ɗauki wayar ta riƙe a hannun tare da kurawa number dake yawo akan screen ɗin, wayar har ta katse bata dauka ba, bata ankara ba taji wayar ta sake ɗaukar ruri tana gab da tsinke ta daga kiran tare da kara wayar a kunne, kamin takai ga yin sallama har na cikin wayar ya riga ta da cewa "Amincin Allah ya tabbata a gareki."


Cikin Wata irin sanyayar muryar da batasan tanada ita ba ta buɗe baki cike da faɗuwar gaba da batasan dalilin shi ba tace "Kaima amincin Allah ya tabbata a gare ka," sannan tace "Ina Yuni."


Daga cikin wayar AFREED ya amsa da "Godiya nake cutie da fatan kin yuni cikin ƙoshin lafiya da farin ciki?"


"Alhamdulilah." AFREEN ta faɗa a takaice


AFREED yace "To masha Allah kamar yanda na sanar dake na kiraki ne don muyi wata magana da ta shafe ni kuma ta shafe ki, nasan zaki iya cewa hadake maganar ta shafa saboda ba wani sanin juna muka yi ba hasali maganar da ta taɓa shiga tsakani na dake bata huce biyu ko uku amma kuma Hakan ba abin mamaki dan haka ina buƙatar hankalin ki akan maganar nan."


AFREEN ta sauke wata yar gajeriyar ajiyar zuciya sannan tace "Ba damuwa ina sauraren ka."


Murmushi AFREED ya saki kamar AFREEN na gabansa sannan yace "Ba wani abu bane nakeso sanar dake illa soyayyar ki da ta mani shigar bazata ba tare da na shirya hakan ba ta mamaye ko wane illahirin jijiyoyin da ke cikin jikin na ta ratsa ɓargo da hanta tabi ta kanainaye min zuciya ta na kasa sukuni AFREEN bansan ya zan misulta maki irin ƙaunar da nake maki ba, sonki ya mamaye duk wani jini dake cikin jiki na, dan Allah AFREEN ki taimaka ki karɓi soyayya ta dan Allah wallahi tunda na fara ganin ki na kasa sukuni zuciya ta kasa hutawa kullum ina cikin tunanin ki." AFREED na kai wannan ya sauke wata irin nauyayyar ajiyar zuciya har sai da AFREEN tajiwo hakan a cikin zuciyarsa ya ke cewa, Allah na godema da ka bani courage ɗin bayyana soyayya ta ka wannan baiwa taka saura amincewar ta Allah ka samin hannun ta amince dani."


AFREEN wada tunda AFREED ya fara magana gaban ta ya yawaita faɗuwa da sauri da sauri dan idan a gaban ta maka ke zaka iya jiyo sautin bugawar zuciyar ta, hakan yasa ta kasa koda ƙwaƙwaren motsi haka ta kasa cewa komai don sai juya maganar take a ƙwaƙwalwar ta gashi bakinta yayi mata nauyi ta kasa furta koda kalma ɗaya ce kuma idan ma tace zata buɗe baki tayi magana mi zata ce mashi."


Jin shiru yayi yawa AFREED ya koma cewa "Dan Allah AFREEN ki daure kiyimin magana ko zuciya ta zata samu sallama please ki taimaka min."


Nan shiru AFREEN bata ce komai don tsakanin ta da Allah bakin ta ya mata nauyi ta kasa buɗe shi tayi magana ji take ma bakin ba a jinkin ta yake ba, dan haka ta koma yin shiru saboda idan har ta mayi jarumta buɗe baki tayi magana to tasan da kuka ne zai kubce mata, kawai sai ta koma yin shiru.

Ganin haka yasa AFREED ƙara duba wayar don ganin ko ta katse kiran ne amma mi sai yaga ba ta katse kiran ba da damuwa a fuskar sa ya mayar da wayar a kunnen sa sannan yace "Allo AFREEN kinaji na ki tausaya min kimin magana in har baso kike rayuwa ta ta kare daga yau ba dan Allah kiyi min magana koda ba zata sakani farin ciki ba, dan bansan ko kinada wanda kike so ba idan haka ta kasance ba zan sa dole sai kin so ni ba, amma ki taimaka yanzun kice wani abu s'il te plaît AFREEN."


Ya buɗe baki zai kara cewa wani abun kawai sai yaji ta fashe masa da kuka ai kuwa hankali AFREED in yafi dubu to ya tashi a firgice yace "Inna lilahi wa inna alaihi raji'un AFREEN ki yafe man ban kiraki dan in takura maki ba har nakai ga sakaki kuka nayi ne dan sanar dake sirrin zuciya ta ɗan Allah kiyi hakuri in har abinda na faɗa ya ɓata maki rai, ki taimaki zuciya ta kiyi shuri sai na katse kiran idan har na kashe tare da sanin na barki cikin wannan halin, bazan taɓa iya samun sukuni ba dan ki tausaya man bazan kara takuraki ba idan har bakison magana dani."


Da sanu a hankali ta fara rage kukan har ta ta daina baki ɗaya yanajin tayi shiru ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi sannan yace "To AFREEN Nagode sai da safe yi hakuri da takuraki da nayi hakan ba zai sake faruwa ba , ki kula da kanki." Sai ya katse kiran ba tare da ya jira jin abinda zata ce ba sabida ya ga alamun ba zata ce komi ɗin ba cike da damuwa ya faɗa kan gadon sa ya kwanta tare da lumshe idonsa yanajin yanda zuciyarsa ke harbawa da sauri da sauri, tare da addu'ar neman sassauci wajen Ubangiji game da abinda yake ji a game da ita, ya kai minti biyar a haka kamin ya buɗe ido sa da suka masa jajir don damuwa da radin da zuciyar sa ke masa.


Ƙara lumshe idon sa yayi da niyyar yin bacci amma ina bacci ya ƙasa zuwa haka dai ha kusan ƙarfe ɗayan dare AFREED ya kasa rumtsawa

Please Login or Register in order to submit comment