Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

su mazauninsu inda babu wanda ze iya ganinsu. A hankali ya shiga takawa zuwa kan gado dan ya baje ya yi baccinsa. Se dai me? Sam be saba jin komai ba bayan ya sha. Be saba jinsa kamar ba shi ba. Se dai yau ɗin gaba ɗaya se yake ji kamar ba shi ba. Idanunsa har wani ƙanƙancewa suke yi. Cikin lokaci ƙanƙani ya ji kansa ya wani irin sara masa. Ya kai hannunsa da sauri ya dafe kan nasa idanunsa a lumshe. Idanunsa na a rufen ya shiga takawa dan ƙarasawa kan gadon, se sai yanda yake ji kamar ana daƙire shi ne. Kamar ba tafiya yake yi ba. Hannunsa ya sake dafewa saboda yanda ya cigaba da sara masa. Zuwa yanzu ma ji ya yi ya masa wani gingirin kamar wanda ya ɗora wani ƙaton gini a kan nasa. Tilas ya dakata daga inda yake dan hatta ɗakin ya soma juya masa. Daidai lokacin Didi ta turo ƙofar ɗakin kamar yanda ta saba dan zuwa ta ajje abin da ke hannunta. Kanta na ƙasa Allah Allah take ta ajje ta fice daga ɗakin. Se dai me? Tana cigaba da takawa zuwa wajen ta ɗan ɗaga kanta da niyyar kallan gabanta. Se ta hange shi tsaye hannunsa riƙe da kansa idanunsa a kulle. Kamar wadda aka dakatar, se ta dakata a inda take tsaye. Ta cigaba da kallansa cike da mamakin yanda ta gan shi a tsayen nan haka kamar ba shi ba. Kafin ta ida tunanin Bad Man ya yi iya ƙoƙarinsa, cike da dauriya ya shiga takawa. Se kuwa ya yi taga taga kamar ze faɗi, alamar dai mutumin da ke cikin maye. Ba ta san lokacin da ta watsar da abin da ke hannunta ba. Ƙirjinta na bugawa ta yi inda yake. Motsin da ya ji ne ya sanya shi soma buɗe idanunsa da zuwa yanzu sun yi jaa kamar ba na shi ba. Da ƙyar ya iya buɗe su shi ma ba duka ba. Kamar ma wanda be buɗe idanun ba saboda yanda suke wani irin lumshewa. Be taɓa tsammanin ganinta ba. Be taɓa zaton buɗe idanunsa ya ganta ba. Se ga ta tsaye a nesa kaɗan da shi.

"Fita!" Ya yi maganar cikin ƙarfin hali a kuma dake daidai lokacin da ya runtse idanunsa yana ɗan girgiza kai saboda tsananin yanda yake sara masa. Girgiza kai ta yi na tare da ta motsa a inda take ɗin ba. Dan kuwa haka nan kawai ta ji ta tsorata da yanda ta gan shi. Be daddara ba ya sake ɗaga ƙafarsa ya cigaba da takawa. Na en sakanni kan ya sakar masa, dan haka ya ƙarasa ya zube kan gadon a wata irin kwanciya ta rigingine. Kansa na kusan ƙasa zan iya cewa dan kuwa har hannuwansa duk sun zubo ƙasa ne.

"Fi..ta!" Ya sake faɗa yanzun ma a ɗan rarrabe se dai a daken dai. Hannuwansa da ba sa kan gadon ya ɗaga ya maida su kansa da yanzun ma ya sara masa yana mamakin abin da yake faruwa da kan nasa haka. Da sauri Didi ta matsa wajen gadon ba tare da ta lura da abin da yace mata ba har lokacin tana jin wata muguwar faɗuwar gaba. Duk kuma da kasancewar daga gajeren wandon nan babu wani abu a jikinsa ita ba ma ta lura ba dan hankalinta na kan yanda yake cigaba da riƙe kansa ne kamar wanda wani abin ya same shi a kan nasa. Ji take kamar ta kai hannunta ta riƙe masa kan ta karanto masa addu'a ko ze ji sauƙi. Don kuwa yanzun har jijjiga kan yake cikin matuƙar azabar da shi kaɗai ya san abin da yake ji. Cigaba ta yi da kallansa zuwa lokacin narkakkiyar zuciyarta ta daɗe da karyewa har ta hawaye sun fara zubo mata. Ganin dai tsayawar da take yi ɗin ba mafita ba ce. Ya sanyata yin shahada a hankali ta soma matsar da hannunta da ke rawa. Cike da fata da addu'ar Allah ya sa kar ya ci mata mutunci ta kai hannun nata kan goshinsa. Ta runtse idanunta bugun zuciyarta na ƙaruwa. Babu ɓata lokaci ta shiga yi masa addu'a a zuciyarta. A nutse ya shiga buɗe idanunsa yana sauke numfashi da mugun sauri. Ya fahimci me ye a kan goshinsa. Dan haka da yake lokacin kan ya ɗan sakar masa se ya yi amfani da ƙarfin sa ya rage masa ya saka hannunsa ya riƙo nata hannun. Be yi wata wata ba se jan hannun da ya yi da niyyar ya turata ta bar kusa da shi, ta ma fice daga ɗakin gaba ɗaya. Se dai yana ƙoƙarin turatan wani irin jiri ya kwashe shi. Be san lokacin da ya saketa ba bayan ya koma baya. Cikin ƙankanin lokaci se ga ta a kan gadon kamar wadda aka jefo, yayin da shi kuma ya yi baya se ga kansa a kan cinyarta...



MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO50*


___ Cikin sauri zuciyarta na wani harbawa ta zo dan miƙewa. Se dai gaba ɗaya ƙarfinsu ba ɗaya ba. Maida dubanta ta yi kan fuskarsa da ya cigaba da runtse idanunsa. Gaba ɗaya se ta manta da batun tashin. Ta sake kama kan nasa duk da yanda hannunta ke rawa ta cigaba da yi masa addu'a. Kusan mintuna 10 ya ɗauka yana cigaba da murƙususun, se kuma cikin lokaci ƙanƙani wani wahalallen nannauyan bacci ya kwashe shi. Wata ƙatuwar ajiyar zuciya ce ta suɓuce mata ba tare da ta sani ba. Ta lumshe idanunta tana jin wani sanyi har cikin ranta. A hankali kuma se ta soma ƙoƙarin zame ƙafafunta dan ficewa daga ɗakin tun da ya yi bacci. Se dai saboda yanda ya yi bacci, ga kuma yanayin ƙarfinsu ya sanya sam ta kasa motsa cinyar tata, ko da nan da can ne. Ba tare da sarewa ba ta cigaba da ƙoƙarin zamewa. Se dai duk iya ƙoƙarinta se ta kasa. Ta yi ta yi ta kasa janyewa. Idanunta da suka ciko da ƙwalla ta kai hannu ta ɗauke ƙwallar sannan ta dawo da dubanta kan kyakkyawar fuskarsa da cikin ƙanƙanin lokaci ta yi fayau kamar ta mara lafiya. Cigaba da zama Didi ta yi na tsawon mintuna masu yawa. Har kuma lokacin ba ta haƙura ba, ta cigaba da ƙoƙarin janye cinyar tata. Sam bata sani ba, ba kuma ta ankara ba wani bacci ya yi awon gaba da ita.

Bayan shuɗewar wasu awanni.. A hankali ya shiga buɗe iidanunsa da suka yi mugun nauyi kamar wanda suka gama masa ciwo, ko kuma wani abu mara daɗi ya same su. Daidai lokacin da Didi ma ta buɗe nata idanun. Se kuwa ya yi daidai da lokacin da ya ida buɗe nasa kuma a kan Didin. A take idanunsu suka sarƙe cikin na juna. Didi ta yi ƙarfin halin yin baya da sauri dan sauka daga kan gadon se dai i zuwa lokacin ma se ya zamana kusan rabin jikinsa gaba ɗaya yana kanta ne. Hakan ne ya sanya kamar jiyan yanzu ma ta kaasa. Da sauri ya tashi daga inda yake kwancen, ita kuma ta yi maza ta yi amfani da wannan damar tana ƙoƙarin dira daga kan gadon. Ya yi saurin sanya hannunsa ya riƙo nata hannun ya dawo da ita baya. Da yake shi kansa be gama tashi zaune ba se ya yi baya kan gadon ya yin da ita kuma ta biyo bayansu se ga shi a kan gadon ita kuma Didi ta faɗa kansa. Ba tare da ta ɓata lokaci ba ta miƙe jikinta na wani irin karkarwa. Kafin ta ida miƙewa ya sanya hannunsa ya sake riƙo tsintsiyar hannunta ya dawo da ita tana kallansa se dai bata hau kan jikinsa ba. Amma fa dab take da shi dan kuwa hatta yanda numfashinta ke fita da bugun gaske yana iya ji.

"Kee!!" Ya yi maganar lokacin da ya aza mata shu'umar ƙwayar idanunsa. Yanayin yanda ya riƙetan ne ya sanya ita ma kallan fuskarsa take yi. Hakan ne ya sa cikin ƙanƙanin lokaci idanunsu suka shige cikin na juna. Kusan a lokaci ɗaya kowannensu ya ji wani bugun zuciya. Be taɓa tsayawa ya kalli yanda idanunta suke ba se a yau. Dan kuwa se ya ji tamkar kar ya janye idanun nasa saboda yanda idanun nata suka ƙawata shi. Wannan brown ɗin ƙwayar idanun nata su yake kalla. Idanuntan da suka fi kama da na mage. Be taɓa ganin irin idon ba, be sani ba kuma ko akwai masu irinsa. Shi dai amma be taɓa gani ba se a yanzu. Yanda ta ga ya shagala kamar me tunani ya sanyata sake ƙoƙarin tashi. Sarai yana sane da ita, hakan ne ya sanya shi sake riƙo hannunta ta sake yin kusa da shi.

"Keee!! Ki nutsu ki faɗa min me ya zaunar da ke cikin ɗakin?" Shiru ta yi tana ɗan janye hannunta ko za ta samu ya saketa.

"Taurin kai koh? Ba na miki gargaɗi ba?" Ya dakata a nan yana cigaba da kallanta kamar ba shi ba. Nan ma ba tace komai ba se kawar da kanta take yi tana cigaba da ƙiƙƙifta narkakkun idanunta da ke cike da ƙwalla. Gaba ɗaya ta rasa yanda za ta yi. So take ya saketa amma ya ƙi, so take ta bar ɗakin amma ya ƙi barinta.

"Ki ka sake ki ka min kuka za ki ga abin da zan miki." Ya faɗa yana damƙe hannunta da ɗan ƙarfi saboda yanda ya ga yanayin fitar numfashinta ya ƙara gudu alamar kuka za ta yi. Ƙaramar ƙara ta saki saboda yanda ta ji zafi. A hankali ta buɗe baki cikin rashin sanin mafita idan ba wannan ba tace

"Don Allah ka yi haƙuri.. Ba ma zan sake shigowa cikin ɗakin ba. Ka yi haƙuri don Allah.."

"Better.." ya ƙare maganar yana sakar mata hannu. Cikin matuƙar sauri ta sauka daga kan gadon a gaggauce ta fice daga ɗakin tana sauke wasu taggwan ajiyar zuciya.



... Ta kai fiye da mintuna 20 tana daga cikin ɗakin tana kallansa. Se dai ta kasa fitowa dan ko magana ma ba ta son yi masa ballantana a kai ga ta karɓi wani abun a wajensa. Minti 1 ta ƙara zuwa lokacin ta haƙura, kawai ta soma takawa dan fitowa daga cikin ɗakin saboda kar ta je ya tashi ya bar ɗakin kuma a yi biyu babu. A ɗan nesa kaɗan da shi ta tsaya, se dai inda ta tabbatar ze jita. Nan ma cigaba ta yi da tsayuwar ba tare da tace komai ba. Se cuno baki da ta soma yi kamar wadda aka tilastawa yin maganar. Duk da rubutu yake yi cikin wata farar fullscap amma sarai ya san da wanzuwarta a wajen. Se dai be nuna alamun hakan ba. Ya cigaba da rubutunsa a nutse. Se da ta wula sannan dan kanta ta buɗe baki da ƙyar tace

"Ka ara min wayarka zan kira Didi.." ta ƙare har lokacin tana tura baki tana kuma kallan gefe. A kaikaice ya ɗaga ido ya saci kallanta. Sosai ta yi kyau da yanda take yin maganar. Se ya sauke kansa yana cigaba da rubutunsa, ya nuna kamar be ji ba. Ba ƙaramin haushi ta ji ba jin shirun da ta yi. Ta ɗauka ko yana jinta ne amma ya yi mata shiru. Se da ta ɗago kanta ta kalli inda yake zaunen yana rubutunsa cikin kwanciyar hankali sannan ta fahimci be jita ba. Ta gyara tsayuwarta tana fatan yanzu idan ta yi maganar ya jita.

"Ka ba ni wayarka in kira Didi.." ta sake faɗa se dai yanzun tana kallansa.

"Wai da ni kike magana?" Gwani ya faɗa cikin basarwa bayan ya ɗaga kai shi ma ya kalleta. Shiru kawai ta yi tana ji kamar ta rusa ihu dan takaici. Musamman da ta fahimci kamar yana sane ya yi maganar nan. Kamar ba za tace komai ba, se dai kuma da yake ita take nema ya sanyata maimaita abin da ta faɗa a karo na biyu. Yamutsa fuska ya yi bayan ya ɗago da kansa daga kan rubutun da yake kafin yace

"Ohh.. ban ji ba.. me ne..?" Ya ƙare yana karkatar da kansa, shi wai a lallai da gaske so yake ya ji abin da ta faɗa ɗin. Se dai yau ɗin burinsa ta ƙara cewa wani abun ya saurara a yanda ta yi maganar tun farko, dan idan ba dan ya san halinta ba se yace shagwaɓa take yi ba tsiwa ba. Zuwa lokacin fa Lulu ta gama shaƙa da yawa. Se dai ta fahimci da gasken yana sane yake yi mata wulaƙanci dan ya ga ta zo neman abu a wajensa...



A yi manage da wannan. Za mu haɗe gobe idan Allah ya kai mu.


MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO51*


___Ba ta ƙara ko minti 1 a wajen ba ta juya dan barin wajen. A ranta tana sake mamakin yanda ya ƙi chanja hali har yanzun bayan ta san waye shi. Ita ta ɗauka waɗanda ba su san shi ba yake nunawa izza kamar yanda yake musu kafin su san shi. Se dai ta fahimci sam ba haka ba ne. Abin da ta kasa fahimta kenan har yanzun.
Fahimtar abin da za ta yi ya sanya shi yin murmushin da ya ƙawata kyakkyawar fuskarsa. Se ya samu kansa da binta da kallo kamar wanda ake ja. Se da ta ɓacewa ganinsa sannan ya dawo da dubansa kan abin da yake yi. Ɗan lumshe idanunsa ya yi yana maida kansa ya jingina da bangon da ke bayansa. Be san dalilin da ya sa a kwanakin nan yake yawan son kallanta ba. Yake kuma yawan son ya ji ta yi magana ba, ko da kuwa tsiwar nan tata za ta yi. Yanzun ma abin da ya sa ya ƙi nuna ya fahimci abin da take faɗa ne dan ta cigaba da tsayawa ko ya samu ya dinga kallanta ko da a fuzge ne. Se dai da alama ta fusata. A hankali ya ɗan buɗe idanunsa daidai lokacin da ya furzar da iska daga bakinsa ya sake bin ɗakin da ta shiga da kallo. Ɗakin da duk da kasancewar kayan kitchen a cikinsa hakan be hanata zama a cikinsa ba duk lokacin da yake nan. Se kace wanda ze yi mata wani abu. Abin da zuciyarsa ta raya masa ne ya sanya shi yin murmushi lokacin da ya tuna da abin da ya faru. Wanda shi ne kusan sanadiyyar da ya sa ta dena haɗa ɗaki ɗaya da shi. Kawai se ya girgiza kai lokacin da yake miƙewa ya fice daga ɗakin.


... A hankali ta cigaba da takawa zuwa cikin ɗakin tana bin ko ina da kallo a wani yatsine kamar wadda ta ga mutum a wajen. A haka har ta ƙarasa ɗakin Bad Man. Kai tsaye ta tura ƙofar ɗakin ta shige. Yana zaune kan gadon sanye cikin wasu ƙananan kaya masu shegen kyau. Waɗanda suka mugun amsar shi, kamar da ma dan shi a ka yi su. Sake kallan agogon dake ɗaure a kan tsintsiyar hannunsa ya yi, har lokacin ya kaasa dena mamakin tsawon awannin da ya ɗauka cikin ɗakin nan yarinyar nan na ciki. Be taɓa zaton har gari ya waye ba. Ya ɗauka dai dukka cikin dare ne. Se bayan da ta fita daga ɗakin ya duba lokaci sannan ya fahimta. A daidai lokacin Mom ta shigo cikin ɗakin. Ya ɗaga kai ya kalleta da sauri dan ya ɗauka Didi ce ta sake dawowa.

"Mom.." ya faɗa da ɗan mamaki, saboda daɗewa da ya yi be ga ƙafar Mom ɗin cikin ɗakin nan ba. Ba ta amsa ba se da ta gama ƙarewa cikin ɗakin kallo sannan ta nemi waje gefensa ta zauna.

"Good morning my dear.." ta faɗa lokacin da ta gama gyara zamanta a kan gadon.

"Morning Mom.. How you dey?" Maimakon ta amsa shi se ta jefa masa tambayar da ta sanya shi ɗaga kai ya kalleta.

"Ka fara shiri ne?" A mamakance ya kalleta ɗin dan shi har ga Allah gaba ɗaya ya manta sun yi wata magana makamancin wannan.

"Shirin me fa?" Ya tambaya yana kallanta.

"Ban gane ba Areef.. me kake nufi da ni ne? Ba mun yi maganar duk ranar da zan bar ƙasar nan za mu bari tare ba? Ko ka manta ne?" Ta ƙare a raunane dan ta soma shanshano abin da yake nufi. Sauke numfashi ya yi, se kuma ya shiga girgiza kai sannan yace

"Sorry Mom.. Na manta ɗin da gaske.. But In Sha Allah zan biyo ki bayan tafiyarki." Hannu Mom ta kai ta dafe goshinta da shi. Ita kam wannan yaro, wannan yaro na neman saka mata ciwon kai. Jin ba tace komai ba ya sanya shi ɗorawa da faɗin

"Ban shiryawa zuwa ko ina ba. So dole se na shirya kin sani Mom. Ba ze yiwu yau kawai na tafi wata ƙasar ba. Na san dole za ki ce se kin fara zuwa Abuja ki kwana biyu kafin ki wuce.. toh idan dai na gama shirye shiryen da zan yi may be mu sauka tare." Ba dan wannan maganar da ya yi ba ba za ta yarda da barin nasa ba. Amma jin abin da ya faɗa ya sanyata yin amanna. Se ta sauke ajiyar zuciya sannan tace

"Shi kenan.. Zuwa anjima zan wuce Abuja.. And kai nake so ka kai ni." Daidai lokacin da ya miƙe tsaye yace

"Babu damuwa.." Daga haka se ita ma Mom ɗin ta miƙe dan ficewa daga ɗakin da tun lokacin da Aunt Makiyy tace ta dena shiga ba ta sake shiga ba. Se yau ɗin da ta manta da ita kawai ta shige.

"Za ka fita ne?"

"Ehh.." ya amsa mata lokacin da shi ma ya fara tafiyar dan ficewa daga ɗakin. Tare suka fito daga cikin ɗakin. Mom ta zuba ido ta ga ko ze yi hanyar ɗakin da ta tabbatar Didi na ciki. Se ta ga ko kallan wajen ma be yi ba. Ta yi murmushi tana tuna irin macen da za ta zaɓawa Areef ɗin. Er gidan manyan mutane, masu arziƙi. Kai abubuwa da dama dai duk ta ci burinsu a kan Bad Man ɗin, musamman lokacin aurensa.



... A bakin layin da ze sadaka da gidan Bad Man ya yi parking na motarsa. Kusan a tare shi da Gwani suka kalli layin. Daga inda suke suna iya hangen fita da kuma shigar mata da maza yawanci kowannensu sanye cikin kayan mutunci, kai se ka rantse gidan arziƙi suke shiga.

"Ya za a yi?" Bad Man ya faɗa bayan ya kalli Gwani. Sauke ajiyar zuciya Gwani ya yi kafin yace

"Ina ganin mu sauka.. mu saka a kira mana ita. Ga wani waje can za mu iya yin magana a can." Ya ƙare maganar yana nuna wani waje da ke gefen gidan.

"Ohk." Bad Man ya faɗa yana ficewa daga cikin motar. Kusan a tare suka fita daga motar. Babu ɓata lokaci suka soma takawa zuwa ƙofar gida. Cikin ƙanƙanin lokaci idanun mutane da dama suka dawo kansu. Musamman waɗanda suka san Areef Matawalle. Tuni mutane suka zuba na mujiya dan ganin abin da ze faru su je su yaɗa.

A yanda suke tafiya kai ba za ka taɓa cewa wannan ne ɗan gidan me kuɗi wannan kuma akasinsa ba. A haka har suka ƙarasa wannan wajen da Gwani ya nuna musu. A nan suka nemi waje suka tsaya. Ba tare da wani yace da ɗan uwansa uffan ba. Har zuwa lokacin da wani ɗan saurayi ya zo wucewa ze shige cikin gidan. Da sauri Gwani ya ƙarasa ya miƙa masa hannu suka gaisa. Kallansa kawai saurayin yake yi kamar wanda ya ga baƙon halitta.

"Gidan nan za ka shiga?" Gwani ya tambaya. Jinjina kai saurayin ya yi da sauri yana jira ya ji amsar da za ta fito daga bakin Gwanin. Cikin nutsuwa Gwani yace

"Idan ka shiga ka ce mu na son magana da Ladi.. mu na tsaye a can.." Ko a yanayin maganar Gwanin ya isa a fahimci hankalinsa. Se dai shi mamakinsa ɗaya a ce duk wannan kamalar tasa, da zubin muminai. Da kamanni da Allah ya masa irin na larabawa a ce ya zo wajen karuwa. Wannan wace irin lalacewa ce? Ya tambayi kansa duk da cewa shi ɗin ba mutumin kirki ba ne. Amma Gwanin ya ba shi mamaki. Kawai se ya sauke numfashi yace

"Toh.." Daga haka ya juya ya wuce cikin gidan. Komawa Gwani ya yi inda ya bar Bad Man tsaye yana waya da Lucky abokin nan nasa. Bayan wajen minti 10 se ga Jakadiya Ladi ta fito sanye cikin abaya da mayafinta. Fuskar nan ta sake yin ɗau saboda uban mai da ya sake ratsata. Hango mutanen da ke tsaye da ta yi ne waɗanda aka ce su ke sallama da ita ya sanyata jin wani irin daɗi. Ko ba komai ta san yau ɗin ta yi babban kamu, dan kuwa tun kafin ta ƙaraso idanunta sun gama nuna mata tsananin kyawunsu. Har wani chanja tafiya ta yi lokacin da ta kusa ƙarasowa inda suke. Ta shiga ɗan karkaɗa jikinta saboda su yaba. Duk da ba ta san me ya kawo su ba.

"Ka bar ni da ita.." Bad Man ya yi maganar ciki ciki. Wanda idan ba Gwani dake kusa da shi ba babu wanda ze iya jin abin da ya faɗa ɗin. Jin abin da ya faɗa ɗin ne ya sanya Gwani cigaba da tsayawa yayin da Bad Man ya dawo gefensa. Se ta yi murmushi tana faɗin

"Sannun ku da zuwa." Ji ya yi kamar ya share saboda yanda wani takaici ya rufe shi. Musamman yanda wani chanjin iskar da yake shaƙa ta sauya lokacin da suka ɗan samu kusanci. Se dai tuna abin da suke da buƙata ya sanya shi faɗin

"Yawwah.."

"Memakon ku shigo ciki.. Ai ba kwa tsaya a nan ba. Ka san mutane da sa ido, yanzu se ka ji ana yi da mu." Gyara tsayuwarsa Bad Man ya yi yana iya ƙoƙarinsa wajen daurewa ya yi maganar da ita. Ban da haka da ko kallan inda take ba ze yi ba ballantana ya mata magana.

"Babu damuwa.. Ki na ji?" Ya faɗa yana karɓar wayar hannun Gwani.

"Ehh ina ji." Ta yi maganar tana sake gyara tsayuwa.

"Akwai wani hoto da na gani na kuma san aikinki ne. So ni ma ina da buƙatar ai min irin aikin a kan wata yarinya.. shi ya sa na neme ki." Ya ƙare yana miƙa mata wayar. Hannu ta saka ta karɓa, tana jin kanta na wani irin tiriri. Tun da har irin mutanen nan kan zo domin ta saka ai musu aiki ai ita kam shau shau da mai. Ba tare da ta damu ta san a inda ya san ita ce ta saka aka yi aikin ba tace bayan ta gama kallan hoton.

"Ohh wannan ƙaramin aikin..?" Ta faɗa dan ya sake sanin fiye da wannan ɗin ma fa za ta iya. Ta san ze sake mata kallan babban kai. Gwani dake gefe ya ji abin da ta faɗa se ya sake bayar da duk wani hankalinsa kanta dan jin abin da za ta faɗa.

"Oh ƙarami ne ma wannan? Ki ce in saki jiki za a min wanda yafi wannan" Bad Man ya faɗa yana murmushin da iyakacinsa kan fuskarsa. Tana cigaba da kallan hoton tace

"Ehh ƙarami ne mana.. Yarinyar ce kawai na sota kamar me.. se dai ita ta ƙi yadda da ni ita wai er gidan masu mutunci. Shi ya sa na sa aka mata haka kowa ma ya rasa har iyayen nata." Ta ƙare maganar tana kallansa

"Gaskiya ne.." Bad Man ya faɗa se dai lokacin fuskarsa ta soma komawa ainahin tasa ba wadda ya aro ba.

"Ina so a min makamancinsa.. se dai yanzu ana jirana dan haka zan dawo mu ƙarasa magana."

"Toh ba damuwa, duk lokacin da kake so kawai ka zo."

"Yanzu da mutane a ciki ne?" Ya sake tambaya yana karɓar wayar, dan yau ɗin so yake ya gama bugar cikinta kafin su bar ƙofar gidan nan.

"Ehh ehh.. Amma idan ɗaki kake so ai akwai nawa da nake saukar baƙina na musamman." Ta ƙare tana wanshare baki. Saboda takaici shiru ya yi yana jin zuciyarsa na masa zafi. Kamar ya tafi ya bar wajen tun da ya gama jin abin da yake son ji. Se dai gudun kar ta fahimci wani abun ya sanya shi daurewa. Se dai muryarsa a cunkushe yace

"Babu damuwa.. Ai

Please Login or Register in order to submit comment