shi yake nema wasa wasa saiga gashi ya tashi da plate din gaba daya,ya shafa cikinsa take yaji yana buqatar qari bai qoshi ba, ya miqe ya nufi kitchen kasancewar tsarin ginin nasu daya ne shi yasa ya fahimci inda yake,ya daga tukunyar gaba daya ya juye ta ciki ya cinye ya dawo falon dauke da ruwan roba na faro a hannunsa ,sai yaji ya samu nutsuwa ba shakka yunwa bata da hankali inji dan almajiri
Ya miqe a kan three sitter๐saboda yanaji har cikin zuciyarsa yanayin qamshi da tsaftar falon sunyi.masa,idanunsa a lumshe yana tunane tunane har aka fara kiraye kirayen sallar magariba sannan ya miqe ya bar sashen,kafin ya qarasa nasa suka ci karo da samirah na shigowa da motarta,ya tsaya qam yana dakon qarasowarta hannunsa zube cikin aljihun wandonsa,tunda ta hangoshi tace da qawarta sa suka shigo tare "na shiga uku kubra mai gidan nan ya dawo"kubra da hankalinta ke kan waya ta ja tsaki tace"mtswee to sai me?ni wlh samira mamaki kike bani tunda.kika yi auren nan duk kin canza komai adarare duba fa dazu da zamu fita fitted gown fa kawai nace ki saka amma kika qi bayan kinsan gun manyan mutane zamu ji,tsoron mutumin nan kike ji kamar wani Allahn ki ke yadda ma kike tsoronsa baki tsoron Allahn naki ma,nidai gwara ma dai yau naga wanne dan mulkin nan ne wannan da.kike masa biyayya haka kamar shi ya tsuguna ya haifoki
Cike da gadara da rashin kunya kubra ta fito yayin da samira keta.rabe rabe don kuwa riga da skert ne a jikinta na shadda kana kallon shaddar kasan an kashe mata naira mai tsada ce saidai anci mutuncinta ta wajen kacalcalata da yi mata matsatstsen dinki,ga mayafin jiki ta sai kace wadda aka yiwa gorin lullubi
Kallo daya ya yiwa kubra da ta tsareshi da ido duk wata rashin.kunya da ta fito da ita tayi nata gun,hakanan aliyu yake Allah ya bashi baiwar kwarjini masifa,ta sake kallonsa karo na biyu"wow"ta fadi a hankali don gaba daya ya tafi da tunaninta,sai ta mance mission din ta fito da shi,ta zuba masa ido gaba daya,sai a lokacin idonsa ya kai kanta bayan ya dauke kansa daga samira,takaici ya kama Aliyu ganin irin kallon qurillar da take masa ya sake dinke fuska tamau,sai lokacin ta kula da ta bada kanta fa ashe,
Ta dauke kai cike da duniyanci da niyyar bin bayan samira dake ta zuba sauri jiki na rawa,tsawa ya daka mata๏ฟผ๐ ย hadi da nuna mata qofar get sannan yace"get out of my house idiot kada na kuma ganin wadannan lalatattun qafa fun naki a gidana"murmushiย ma ta saki ta juya ta fice cikin karairaya wai ko zata janyo hankalinsa, bata san wani takaicin ne ya sake qumeshi ba yaja wani dogon tsaki ya juya ya nufi sashen samira
Mrs muhammad๐
๐๐๐โ๐ปโ๐ปโ๐ป
3:37 pm 8/11/1437
๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ
*wa yasan gobe?.....*
4โฃ1โฃ~4โฃ2โฃ
Kubra ta tsaya a bakin get din tana jinjina kai ita daya take sumbatu"kut lallai yarinyarnan dole ta matowa gayen nan shi yasa take ta faman rawar qafa?ai kuwa wlh baza'ayi bani ba"tayi qwafa sannan ta ja qafa tayi gaba,
samira ta kasa zaune ta kasa tsaye tasan halinshi sarai yarjejeniya kuma suka qulla tun kan aurensu kan shi baison wadannan kwashen qawayen nata gashi yau ta saba yarjejeniyar,tana shirin guduwa dakin gadonta ya damqota ya maidata kan kujera,ya kalleta sosai sannan ya jefo mata tambaya"ina kika samo waccar shedaniyar?"ta dake duk da tsoro ne fal cikin idanunta tace"qawata ce fa"ya gane mai takeson yi duniyancin nata data saba don haka ya shirya nuna mata nasa salon,don haka sai ya saketa daga riqon da yayi mata,ya saki fuskarsa ya daga kafadarsa hadi da watsa hannayensa na nuna alamun rashin damuwa da abu kana yace"good....verry good tunda qawarki ce kinga abun zai zo min da sauqi kenan ko?,dama gani nayi tamun inason aurenta aikinga zaman naku zai miki dadi tunda kun fuskanci juna, bata san sanda tayi zumbur ta miqe ba tana zazzare idanu ba baki na rawa tace"iyi...mme...me kace"ya daga mata gira sannan yace"abinda kunnen ki suka ji shi nace"ya juya yana niyyar barin dakin,hankalinta a tashe ta riqoshi kasancewar tasan halinshi *fada da cikawa*ya dubeta fuska a turbune yace"meye haka"don Allah ka rufamin asiri wlh bazan qara ba kasan wace kubra kuwa?"ya sake dage kafada hadi da cewa"ni ina ruwana da koma wace ce tunda kin kawo min ita har gida ni kuma na gani kuma ta yimin"ya zare hannunsa yayi ficewarsa,yana jiyo kururuwarta sai ya tuna haukan da tayi masa sanda zai dawo da salima,murmushi๐ ya subuce masa ba tare da yayi niyya ba,yasan cewa shikenan yayi abinda zai rabasu kenan har abada ba tare da ya wahal da bakinsa ba,(samira irin mai rawar kan tara qawayace ko wa qawarta ce kare da doki ga son birga da burgesu ita dole sai an san mijinta wani ne,kaya komai tsadarsa suka gani a gunta tofa take zata basu ko nawa aka siya musu ko na aliyyun ne kuwa,indai zata burge tofa magana ta qare,gata da saurin daukar maganarsu don yadda take jin zancansu nata jin na mahifanta haka ne yayi silar lalacewarta,wannan ne yasa aliyu ya rabata da kowacce qawa amma da yake akwaita da kafiya taurin kai da naci sai ta sake wasu sababbi wadanda aliyyun bai sansu ba)
Kai tsaye ya wuce sashen sa tun daga falin ya ga canji komai fes ya koma hayyacinsa,daddadan qamshin girki ya cika falon nasa,bedroom ya zarce ya daura alwala ya nufi masallaci,kan ta kammala aikin ta gama gajiya tubus don kuwa aikine ya gama taruwa ya cakude ita kanta wani gun cike da qyanqyami ta daure ta gyarashi to ina kuma ga aliyyu
Take tasha alwashin zata yiwa tufkar hanci don badaqalar data tarar a bedroom din tasa ta isa,tuni ta gane cewa fushinta bashi da amfani don yadda komai ya qazance ta sani cewa da duniya zata gani ba iya su samira kawai za'a zaga ba harda ita,don ba wanda yasan mekw gudana tsakaninsu,ta sake gayawa zuciyarta lallai ibada tazo yi ibada kuma mai wahala wadda itace tafarkin shiga aljannarta kuma ta dade da sani aljanna bata samuwa daga zaune ba tare da ka tashi kayi aiki tuquru ba kuma dole ka ninka haqurinka(wannan sune daya daga cikin lafuzan umminsu garesu ko yaushe,uwa ta gari kenan)
Aliyu bai shigo ba har sai da yayi sallar isha'i don haka tuni ta gama komai har ta jere a dining taje tayi wankanta ta shirya tsaf cikin dark blue din shadda doguwar riga wadda aka mata surfani mai kyau tun daga sama har qasanta ,hankalinta dai na kan taliyarta don haka ta nufi table din saidai wayam don ko plate din babu,ta juya ta shiga kitchen acan ma a bude ta tadda tukunyar wayam
Ta san babu wanda ya cinye abincin sai shi don ba wanda ya shigo din,wata dariya๐ ta subuce mata data tuno yadda ya shigo dazun rai a hade yayi wani kicin kicin da shi๐ ashe harda yunwa itama ta taimaka wajen dinkewar fuskar tasa,ta hade kwanunkan ta dauraye ta maida su muhallinsu cikin ranta tana cewa"babu rabona nasha ice cream๐ง
Tana bisa carfet ta bude babbar robar ice cream din tana diba a hankali tana kaiwa bakinta lumshe ido take don babu abinda take jin dadin shansa kamarshi din,wayarta ta duba jin qarar shigowar text _kizo ki bawa mutane abinci_"haka taga an saka,ta duba sunan Aliyyu salim maitama kamar yadda yayi mata serving din ta ranar da bata da lafiya"ta miqe hadi da dauke ragowar ice cream din ta maida cikin fridge ta koma daki ta fesa turarenta na blue lady ta hada da asaal brush perform ta nade kanta da da farin hijabi ta zari wayarta ta fito hadi da kulle gun ta,a hanya suka hadu da salima ta rako baquwa suna tsaye da alama magana suke ganin fitowarta duk sai sukayi shiru suka bita da kallo ganin haka yasa tace musu salamu alaikum sanda zata giftasun,baquwarce kawai ta iya amsawa itama can xiki kamar wadda akayiwa dole,suka ci gaba da kallon nata har ta shige bangaran aliyun
sai a sannan suka dauke idonsu baquwar ta saki ajiyar zuciya tace "tab gaskiya salima tahir na janjanta miki don wannan kam banga ta inda zaki ci nasara akanta ba,saidai ban sani ba ko ta bangaren farar fata"salila ta kai mata duka hadi da cewa"banason iskanci sadiya kota farar fatar ai sai na yi yaqi da itan ,dadin abun ma miskilancin mai gidan bai bari ki gane wa yafi so cikinku ai da tuni inaga na dade da kamuwa da ciwo yanda nake bala'in a son my dear๐ "ta fadi tana dafe qirjinta"(abunda bata sani ba aliyyun irin mazan nan ne wadanda ke nunawa mace qauna wadda kan bawa mutane mamaki har adinga zaton kunya ce basu da ita ko mallakesu akai sunyi sake da damar da ya basu tun farko har ta subuce musu)sadiya ta dafa kafadarta tace"to Allah ya bada sa'a don ko nice a matsayinki gaskiya bazanyi wasa da aliyyu ba"salima ta juya ido tace "ashe kin fara gano gaskiyata๐ "
Mrs muhammad ce
๐๐๐โ๐ปโ๐ปโ๐ป
[10/16, 1:42 PM] ๐๐ฌ๐Salma๐๐ฌ๐: ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ
*wa yasan gobe?....*
๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ
*written by safiyya Abdullahi musa huguma*
๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ
4โฃ3โฃ~4โฃ4โฃ
๏ฟผ๐ณ
''
|๏ฟผ๐ย |
/ \
๏ฟผ๐ ย ๏ฟผ๐
Ku tayani duba jama'a na taho da sauri na ina neman littafina na *wa yasan gobe*zan muku typing na nemeshi na rasa
๏ฟผ๐๏ฟผ๐๏ฟผ๐๏ฟผ๐๐๐๐
Just for fun ga wadanda suka ji haushina
*wa yasan gobe?....*
Loading..........๐๐ผ
*WA YASAN GOBE?....*
*PART 2*
๐บ
1โฃ~2โฃ
Sadiya ta dafa kadar salima tace to Allah ya bada sa'a don ko nice a matsayinki gaskiya bazanyi wasa da aliyyu ba"salima ta juya ido tace ashe dai kin fara gano gaskiya ta๐"
Sanda ta shiga yana zaune gaban na'urar tafi da gidanka yana qarasa aikin sa da dazun yunwa ta hana shi yi,sallama tayi ya amsa kansa na kan allon computer din,kujerar dake gefansa ta samu ta zauna,kusan mintina sama da ashirin bai ce mata kanzil ba don haka itama ta bude wayarta ta soma register din watsapp saboda yanzu as journalists tana buqatar wadannan kafofin sadarwar,
duk da basu dameta ba don ba yadda farida batayi da ita tun a gida ta bude koda watsapp ne kawai ba amma taqi tafi ganewa karance karancen magazines da wasu rubuce rubucen
Cikin yan mintoci qalilan ta kammala da account dinta na watsapp ta soma qoqarin hada na facebook,falon yayi tsit kowa ya sanya na'ura a gaba,lokaci lokaci takan daga ido ta saci kallonsa,qayatacciyyar fuskarsa da hasken screen ya sake hasketa tayi fresh,ta zubawa hannayensa ido yadda yake sarrafa computer din cikin qwarewa da da gwanancewa typing yake cikin sauri tamkar shi ya qera computer din yasan madannin kowanne abu abun sai ya burgeta sosai
Wayarsa ta soma ringing ya dauke kai daga kallon fuskar computer din ya maidaa idonsa kan wayar ba tare da ya daga ba,baquwar numbace kuma bai dagawa,kira aka ci gabaa da yi akai akai har ya gaji ya danna ok ya dora ta bisa computer ya sanya ta a hands free
Muryar mace ce "hello ranka ya dade" "salamu alaikum wake magana?"ya fada hannayensa na saman laptop dinsa yana aikinsa,"daga daya bangaren aka sake maqe.murya"suna na nadiya ina kiranka ne daga unguwar rijiyar zaki kano"bai maida hankalinsa ba kan wannan yace"me kike nema?"aka danyi jim har yana shirin kashewa sannan akace "don Allah ka rufawa zuciyata asiri kada ka kashemin waya domin kashe wayar tamkar kashe ni ne"ya tsayar da abinda yake sannan yace "uhm go on" aka saki ajiyar zuciya sanna tace "maitama Allah ya jarabceni da tsananin qaunarka wadda tasa na kasa jure hakan cikin zuciyata har sai bakina ya furta maka,ina roqonka don Allah ka taimakeni ka so........" "hey!"ya daka.mata tsawa "stop that,rubbish!"tsit tayi,ya ware idonsa kamar tana gabansa yace"ke baki da ajine irin na mata?" Shiru ba amsa don haka ya dora "let me tell you baki da shi,and inason gargadinki wannan ya zama na qarshe da zaki kira numberta,I hope kin fahimta ko"ya katse kiran hadi da jan tsaki,fadila tayi saurin dauke kanta lokacin da ya dago kansa taga tamkar ita zai kalla zuciyarta na wani irin bugu,kishi ya tokare mata qirji,ta lumshe ido bugun zuciyarta na qara sauri.......
Mrs muhammad dinku ce๐
[8/25, 3:44 PM] โช+234 812 673 9684โฌ: 5:55 pm 16/8/2016
๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ
*wa yasan gobe?...*
๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ
๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ
*written by safiyya Abdullahi musa huguma*
๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ
*PART 2*
3โฃ~4โฃ
Kusan kimanin minti biyar idanun nata na lumshe ta kasa budesu saboda wani abu da takeji a jikinta wanda tasan baya rasa nasaba da tsan tsar kishi,ta sauke boyayyar ajiyar zuciya sannan ta bude idonta ta dora su bisa screen din wayarta tana ci gaba da qoqarin kammala bude account nata na Facebook duk da wani bari na zuciyarta na ci gaba da mintsininta,cikin zuciya lallai ta godema Allah da bai qaddara ta zubda ajinta ta bayyana abinda ke zuciyarta ba har ta kai aliyyu ya fuskanta bare ta samu nata kason cin zarafin kwatankwacin wannan wanda it may break her heart
Tabbas ta sake yarda cewa so masifa ne musamman son da hausawa kema laqabi da son maso wani,babu irin baiwar da tabbas bata da ita iya kyau Allah ya mallaka mata shi ilimi hankali da nutsuwa,tasha jin mata yan uwanta da yawa na yaba ta bare tarin maza dake kara kaina a kanta
Ta sake satar kallon nasa wannan karon maimakon ta tadda shi yana aiki kamar dazun yanzun takardun na watse ne a gabansa ya jingina kansa harda bayansa a jikin kujera dukkanin tafin hannunsa ya tallafe bayan kansa da su idanunsa na rufe,gashin idonsa yayi ma idon rumfa tamkar an jera su
"Bani abinci"ya fada idonsa na a rufen,ta miqe ta shirya masa komai still dai idanunsa na arufen har ta gama ta koma ta zauna,a hankali ya bude idonsa ya kalli warmers din"u mean ni zan zuba kenan da kaina?"๐ ta girgiza kai sannan ta taso ta zuba masa white rice ce da miyan kaza sai hadin coleslaw tana kammalawa ta miqe da niyyar fita "ina zaki je?"ya tambayeta cikin izza,ta kawar da kanta sannan tace "sashina zan koma" yaci gaba da cin abincinsa sai da ya mula don kansa sannan yace "ban baki izini ba"cike da haushi da takaicin irin mulkin da yake mata ta koma da baya ta zauna kanta a qas
Cin abincinsa yake with calmness ba abunda ya dameshi ya shanyata abunsa,har ya kammala bai dubi sashenta ba already ta soma gundura da zaman ga bacci ya soma mamayarta ga kuma fita office gobe early,sai da ya kammala duk abinda yake har ayyukan da yake shigarwa cikin laptop dinsa apple sannan ya tattare kayayyakinsa ya maida jakar laptop din yana shirin shiga bedroom dinsa yace da ita"ki hadomin coffee ki kawo min"
Kamar zata fashe da kukaโน ta shiga kitchen cikin mintina biyar ta hada masa ta juye cikin cikin wani set din butar shayi irin na larabawa na silver da cups dinsu yake hade da tray
Hade da sallama ta shiga dakin yana cikin lallausan bargonsa cikin shirin bacci ba haske a dakin sai na fitilar gefan gado,yana receiving call har ta shigo ta isa bed side ta dora plate din daidai lokacin da ya kammala amsa wayar ya kasheta gaba daya ya cillata bayansa tana tsaye har ya kammala addu'o'in bacci sannan ya juya mata baya yana gyara kwanciyarsa hadi da jan bargonsa "kina iya tafiya" dama a gundire take Allah Allah take ta bar masa dakin ta juya ta fice abinta
Tana shiga bedroom dinta nightgown kawai ta sanya ta fada gadonta tana addu'o'in kadan kadan har ta gama,a hankali ta lumshe idonta tana da muradin yin bacci amma ina sai tunanin da akullum yake zame mata na qarshe a rayuwarta shi ya lullube qwaqwalwarta,duk yadda taso bacci yayi awon gaba da ita abun ya faskara har sai da ta dade tana ninqaya a duniyar qaunar aliyyu haidar sanan baccin yayi awon gaba da ita bacci ne mai cike da mafarke mafarken aliyyun
โโโโโโ
Cikin hukuncin ubangiji rayuwar ke tafiya da bawa wani lokaci ta zo maka uadda kake so kake tsammaninta wani lokacin kuma ka samu akasin haka yau fari kenan gobe tsumma jibi nasara gata asara duk cikin hukuncin ubangiji ne da yadda yaso rayuwar bayinsa ta kasance,to bawa mai cike da tauhidi da imani sai ya godewa masa don kamar yadda haka yake ga fadila,shekararta guda kenan cikin igiyar auren aliyyu,shekarar da ta ga abubuwa daban daban ta fuskar qalubale da nasara
Zamu iya cewa babu wani abu da ya sauya dangane da salon mu'amala da alaqa dake gudana tsakaninta da shi baya ga wadda muka riga muka sani,nasara daya ce zata iya daga hannu๐๐ป ta fadeta cike da alfahari shine duk cikin samira ko salima babu wadda take iya sarrafawa aliyyu girki da tsaftar muhallinsa kamar ita
Abunda suka fi qwarewa ciki sune kowacce ta fito tana tunqaho da hura hancin Aliyyu yafi sonta akan sauran 'yan uwanta,takan kau da kai cike da yakanah tayi kamar bata san abinda suke yi ba,wani lokacin kuma sukan bata dariya har ma ta murmusa takan daukesu ne a matsayin wadanda basu san mai ya kamacesu ba duk da kuwa duk sun bata wasu shekaru sun kuma girmemata sosai tana ganin tutiya bata kamacesu ba a irin wannan rayuwa da suke,ta sanu da gayya suke mata wani abun ganin cewa bata taba daga ido ta kallesu ba bare suyi 'yar tankiya
So suke ta zamo daya daga cikinsu domin kuwa fada tsakaninsu sun koma tamkar 'ya'yam tumaki har bangarenta tana jiyo hayaniyarsu,sukan ji kasiririt ne idan aliyu yana gida don ko giyar wake suka sha a yanzun basu fada gabansa tun tuni yayima tufkar hanci ya kuma tauna tsakuwa don aya taji tsoro ta kuma ji din saidai su yita 'yan habaice habaice wadanda shi da yake namiji me bai ma fuskantar me suke
Ta riga tuntuni ta saddaqar da cewa soyayayyar aliyyu wani gine ne daga Allah cikin zuciyarta,tayi imani koda bai sonta ba koma zai sota din ba kamar yadda yayi mata tunqaho Allah bazai taba wofintar da ita darajar biyayyar aure da take hidima a gareshi da kayutata gami da girmama buqatunsa,duk da babu wani sauqi da take ganowa a tattare da aliyyun amma har kulluma tana bawa kanta confidence kan hidimar da take masa especially a duk sanda haduwa ta hadasu da uncle abba momi abbanta ko umminta taga yadda suke nuna jin dadinsu har yau da wannan aure nata sai taga zata iya ci gaba da faranta ransu indai hakane
Saidai abinda bata sani ba shi kansa yakan samu kansa cikin nutsuwa a duk ranakun da suka zamo nata ne ko banza ya san yana sakewa yaci abincinsa cikin nutsuwa da kwanciyar hankali kuma cike da gamsashshen dan dano irin wanda yake so duk da babu ruwanshi da ita,some times ma kafin ya dawo ta hada duka abinda yake so ta bar masa bangaren,mutum ne aliyyu maciyin abinci bao wasa da cikinsa ko kadan hakanan halittarsa take,duk qwaqwar mutum bai isa yayi indication wasu sign da zai nuna yana jin dadin hidimarta ba
Mrs muhammad dinku ce๐๐๐
๐๐๐โ๐ปโ๐ปโ๐ป
[8/25, 3:45 PM] โช+234 812 673 9684โฌ: 5:08 pm 20/08/2016
๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ
*WA YASAN GOBE?..*
๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ
๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ
*written by safiyya Abdullahi musa huguma*
๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ
*PART 2*
5โฃ~6โฃ
Cikin watannin da basu gaza biyar zuwa shida ba fadila ta samu gagarumar nasara ta bangaren aikinta,nasarar da bata taba tsammanin zata sameta in a few months ba,ta soma aikine cikin sa'a,farin jini sosai take da shi,sunanta ya fara fantsama cikin al'umma shirye shiryenta sun samu karbuwa matuqa da gaske,ki ina ka zaga zancan matashiyar 'yar jarida fadila Abbas wakili ake,ita kanta tana mamaki with her few age ta samu daukaka haka,saidai da yake mai hankali ce takan godewa Allah domin tasan babu wanda ya isa yayi mata haka sai Allah,hakan yasa ta sake daura damarar riqo da aikinta cikin qwazo amana da kuma gaskiya da kuma manufa kyakkyawa da zata kawo gyara da ci gaban al'ummarta,bata mantawa da ya ahmad da abbanta wadanda su suka jagoranci samuwar ci gaban nata
Bayan ta kammala duk wasu ayyukanta kamar yadda ta saba,ta shirya masa komai hatta da tissue bata barta ba,sauri take ta yi ta fice daga gun kafin dawowar tasa,saidai kash bata ci nasarar hakan ba don kuwa a bakin qofa suka yi kacibus kadan ne ya rage basu bige juna ba,da sauri taja da baya tana shaqar numfashin ta dake gudu sakamakon tsoratar da tayi,qasa tayi da kanta tana murza tafin hannunta gami da cewa "sannu da zuwa"
Kusan minti biyu taji shiru shi bai wuce ba ba kuma alamun juyawa yayi,ita kuma ya bashi dama ne ya fara wucewa duk da sauri da take ta koma bagarenta ta cire pad din jikinta ta sauya wata,ta dago kanta don taga me yakeyi ne haka yana tsaye hankalinsa kwance kamar bai tsarawa kowa hanya ba don bashi da wani alamu na matsawa hasalima tie dinsa da coart yake cirewa a nutse
Ganin haka yasa ta raba gefansa don ta shige ashe bata sani ba ya sanya mata qafarsa dake saye cikin sau ciki๐sam bata lura ba don hankalinta yayi gaba,luuu tayi baya ya goce sai kuwa ta bugu da qofan falon ,cikin azabar radadi ta dafe gun ta dago a hankali ta kalleshi sai taga tamkar ma baisan mai yayi ba agogon hannunsa na gucci yake cirewa,malolon takaici ya kama mata maqogaro tuni kuka ya kufce mata tasa kai tanashirin bar masa gun tana dafe da goshinta
Ji tayi ya jawota baya ta dawo tayi kamar zata sake faduwa Allah ya taimaketa ta tsaya da qafafunta bayan taga tagar da tayi "sama fa qasa ya kalleta sannan yace "๐ baki da kunya ko?,ni zaki buge ki wuce kenan?"tafin hannunta tasa ta kate fuskarta tana ci gaba fa kukanta shi kuwa ya zuba mata ido ba tare da ya sake cewa komai ba, sai da ya gama ikon nasa don kansa ya kauce tare da wucewa ya bar gurin
Da gudu ta fice tana ci gaba da kukan ta wuce bangarenta,dispenser ta kunna tayi heating gurin sannan ta koma bisa gadonta ta kwanta tana maida ajiyar zuciya,me ta masa?ma ta tsare masa banda tsabar cin zali kawai don ta rabe zata wuce sai ya mata wannan muguntar?" Ta danyi qwafa kadan a ranta tana ayyana zata rama
โโโโโโ
Su biyar ne zaune cikin office din fadilan sai fauziyya fa'iza aisha da halima dukkaninsu abokan aikinta ne matasa ne son saidai duk sun girmemata aqalla zasu bata shekaru uku zuwa hudu,amma nutsuwa da kaifin hankalin fadila yasa ta saje cikinsu suna jin dadin zama da ita sosai duk da miskilace saidai akwai karamci da mutunta mutum
Hira suke gaman da zamantakewar aure irin hirarmi dai mata da aka sani wadda matuqar mayan aure suka wuce biyu aka hadu sai an yita,hira ce ta qaruwa ba banzar hira ba wadda bata kamata ba,duk da haka fadila na gefe don bata da abun fadan saidai jifa jifa takan ce wani abu
Hira tayi nisa fa'iza ke basu labarin wata maqociyar yayarta 'yaf nijar dake saida magungunan mata masu kyau na gargajiya wadanda basu cutarwa,dukkansu suka ce ayi kiran matar suna so fadila kawai ta rage,fa'iza ta kalleta"ke ba ki siya fadila wlh maau kyau ne"murmushi tayi tana neman qaryar da zata gilla musu,don ko ta siya me zata yi da su,ta kalli fa'iza "to a hado da ni ga nawa kudin"ta nude zif din jakarta ta fito da kudin,fa'izan ta kuma cewa idan ma bakiso akwai wani hadin tutare mai tada sha'awar mai gida sai a kawo miki shi"cikin basarwa fadila tace"a hadomin duka kawai"(kaji fa mai karatu kamar gasken tana da buqatarsun ๐๐)
Take fa'iza ta kirata ta sanar mata,ta kaahe wayar tana dubansu tace kun taki sa'a don gata nan ma anan kusa don tana ja'en,cikin minti talatin sai gata kowacce ta karbi nata ta sanya ajaka
Qarfe biyar ta soma hada kayayyakinta tana sallama da su zata wuce gida don ta kammala
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 13 Chapter of 33