Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zamo filin yaƙi na wannan daula gaba ɗaya.
Wannan abu da sarki Samudul Ansari yayi ya dauwamar da zaman lafiya a wannan daula, babu wani tashin hankali ko ta'addanci.
Sarki Samudul Ansari bai raba wanna daula izuwa birni-birni ba, a dunƙule take gaba ɗaya saboda yaji daɗin tafiyar da mulki.
Saboda taimakon Tau'rin, duk wani abu dake faruwa a wannan daula sarki Samudul Ansari yana saninsa.
Sarki Samudul Ansari ya samar da mayaƙa kamar ma'abota Bankai guda dubu goma.
Ya basu horon yaƙi mai tsananin wahalar gaske, sannan tau'rin da kansa ya saka musu albarka.
Samudul Ansari ya samar musu da takubba daga 'Jeeish' sannan ya baiwa kowacce takobi kyautar aljani guda uku-uku.
Saboda haka su ma zasu iya kai hari mai tafiya sannan zasu iya kare wannan daula gaba ɗaya.
Waɗannan dakaru guda dubu goma, su Samudul Ansari ya zaɓa a matsayin waɗanda zasu taimaka masa a yaƙi da ma'abota Bankai.
Saboda albarkar tau'rin dake tattare dasu Samudul Ansari baya shakkar tunkarar daular Gorgon dasu, sannan baya tunanin zasu bashi kunya.
Zaka iya cewa shima Samudul Ansari a wannan lokaci ya shirya...
*******
Yau *16/03/2023*
Babi na gaba zaizo **18/03/2023* da yaddar ALLAH.RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 99: *Babba ma, da babbansa*
*
***TARIHIN SAMUDUL ANSARI***
*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga Zahra.
*
UMS
*
Sarki Samudul Ansari, sarauniya Arya, Zarifa da sauran fadawa suna zazzaune a cikin ƙawatacciyar fadar ƙasar wadda Samudul Ansari yasa hadiman aljanu suka gina masa ita.
Sarkin na zaune kan ƙasaitacciyar karagar mulkinsa, Arya tana zaune a hannun damansa, Zarifa kuma a hagu.
Ana tafiyar da harkokin mulki kamar yadda aka saba.
Ba zato yaji wata takarda da take cikin aljihunsa ta soma ɗaukar zafi kamar ana hura mata wuta, cikin gaggawa ya zaro takardar sannan ya dubata.
Abin mamaki taswirar wannan daula ce akan takardar.
An ƙawata taswirar sosai sannan anyi mata wani sihiri wanda ke nuna dukkan abinda ke faruwa a daular.
Gaba ɗaya taswirar koriya ce, da zarar wani yanki ya fara fuskantar barazana ko kuma ana yaƙi a wannan yanki, daidai wajen da abin ya shafa zai fara nuna alamun ja.
A wannan lokaci wajaje guda biyu ne, suka nuna alamun ja, wato wajajen babu zaman lafiya kenan.
Waje na farko wannan kogi ne wanda yake gefen waɗannan ƙauyuka guda uku waɗanda sarki Samudul Ansari ya taso a cikin ɗaya daga cikin su.
Waje na biyu wani gari ne wai shi Kaliyrus wanda ke gefen filin yaƙin Ajalin-Abokan-Gaba a farkon shiga wannan daula.
Sarki Samudul Ansari na ganin haka, yayi amfani da wadannan idanuwa na tau'rin ya hanga izuwa wannan kogi dake gefen ƙauyen Salwaza.
Ma'abota Bankai ya gani guda ɗari, sun shiga cikin ruwan kogin, suna ta zuba masa wani irin baƙin dafi wanda bai taɓa kallon mai kama da shi ba.
Sarki Samudul Ansari na ganin haka ransa ya soma ɓaci, ya sake hangawa izuwa garin Kaliyrus dake kusa da Ajalin-Abokan-Gaba.
Nan ma ya sake yin arba da ma'abota Bankai kimanin guda ɗari biyu, suna shirin afkawa cikin filin Ajalin-Abokan-Gaba.
Sarki Samudul Ansari ya gyaɗa kai ya dubi Zarifa ya ce, "Ki je ki ɗauki sabbin dakarun mu guda ɗari, ku je kogin Saisal dake kusa da ƙauyen Salwaza akwai abokan gaba a wajen."
Zarifa ita ce shugabar waɗannan dakaru da Samudul Ansari ya samar a wannan daula, waɗanda zasu taya shi yaƙi da ma'abota Bankai.
Saboda haka kula da baiwa wadannan dakaru umarni yana hannunta.
"Idan kun gama dasu, ku wuce kai tsaye izuwa filin Ajalin-Abokan-Gaba inda zamu fafata da ɗaya rundunar tasu!"
Zarifa tana jin wannan umarni ta zube a gaban Samudul Ansari cikin biyayya ta ce, "Zamu yi kamar yadda ka ce sarki!"
Idan aka zo fada, kwata-kwata Zarifa bata nuna ita matar Samudul Ansari ce, ɗaukarsa take a matsayin sarkinta. Shi kansa yana jin daɗin hakan.
Zarifa ta wuce izuwa sansanin waɗannan mayaƙa, ta zaɓo gwarazan cikinsu mutum ɗari, suka yi hawa gaba ɗayansu suka tunkari kogin Saisal.
Gaba ɗaya waɗannan mayaƙa suna ɗauke da irin wadannan maɗaukakan takubba da tau'rin da kansa ya samar musu.
Takubbansu suna bayar da baƙin sheƙi sannan suna ɓulɓular da baƙin hayaƙi daga cikinsu.
Wannan shi ne ƙarfin ikon tau'rin - Baƙin hayaƙi mai kama da tasowar ƙonannen nakiya.
A can fadar sarki Samudul Ansari kuwa, miƙewa yayi daga kan karagar mulkinsa ya dubi sarauniya Arya ya ce, "Aiki na gaggawa ya taso min. Ki je wajen da muka tanadi ruwan sha a cikin waɗannan gangunan, ki baiwa hadiman mu umarnin fitowa da ruwan su rabawa dukkan ƙasar nan.
"Sannan ki bayar da umarnin kada wanda ya kuskura ya sake mu'amala da ruwan dake fitowa daga cikin kogi ko kuma tekunan daular nan. Kai, indai ruwa ba daga wannan ma'ajiya tamu ya fito ba, a duk faɗin daular nan na haramta shan sa."
Sarki Samudul Ansari na gama faɗin haka, ya fice daga cikin wannan fada ya nufi wani ƙaton ɗaki inda yake ajiye kayan yaƙinsa.
Sarauniya Arya ta ɗauki wani bawa matuƙin keken doki, suka nufi wannan ma'ajiya wadda Samudul Ansari yayi tanadin ruwa a cikinta domin gudun kada wannan cuta ta sake dawowa.
Ɓangaren su Zarifa basu ɓata lokaci mai tsaho ba, suka iso ƙauyen Zumur wanda daga shi sai ƙauyen Salwaza inda ma'abota Bankai suke.
Zarifa ta ɗaga hannunta dukkan mayaƙan suka tsaitsaya a bayanta, ta juyo ta dube su ta ce.
"Abinda ya rage mu isa ƙauyen Salwaza inda kogin Saisal yake, baida yawa. Saboda haka na tsayar da wannan runduna tamu domin na baku umarni akan yadda zamu ɓullowa wannan yaƙi!
"Abu na farko shi ne, ina so wannan runduna tamu ta rabu izuwa kaso huɗu sannan mu kewaye ƙauyen Salwaza gaba ɗaya.
"Yana da kyau a yayin yaƙinmu da waɗannan halittu mayar da hankali sosai, kada mu ɗinga kashe waɗanda basu ji ba basu gani ba!
"Sarki ya baiwa kowa damar amfani da dukkan ƙarfinsa domin gamawa da waɗannan halittu. "
Zarifa tana zuwa nan a zancenta, ta rarraba wannan runduna izuwa mutane ashirin da biyar-biyar sannan ta basu umarnin kewaye wannan ƙauye na Salwaza.
Dukkan mayaƙan suka rarrabu sannan suka fara kewaye ƙauyen cikin sanɗa ba tare da sun bari an gano su ba.
Sannu-a-hankali suka gama kewaye daidai inda kogin Saisal yake.
Abinda Zarifa da waɗannan dakaru basu sani ba shi ne, ɓuyan banza kawai suke.
Waɗannan ma'abota Bankai dake wannan waje babu wanda a cikinsa bai mallaki takobin Bankai mai mataki sama da na arba'in, don haka suna da idanuwan Renin-Yilan.
Idanuwan Renin-Yilan suna iya ganin abu nisan zango biyu, saboda haka duk sun ga tahowar su Zarifa da kuma yadda suka kewaye su.
Shugabar dakarun guda ɗari ta baiwa mayaƙanta umarnin fiddo makaman yaƙinsu, sannan suka jejjeru a sahu guda.
"Ku daina wannan ɓuya da kuke, mun riga da mun gan ku!" inji shugabar ma'abota Bankai ɗin.
Abin mamaki a hankali tayi maganar, amma Zarifa da dukkan dakarunta saida suka jiwo.
Zarifa tana jin abinda suka ce, tayi murmushi dama tasan irin haka zata iya faruwa ta fito daga inda take ɓoye ta kwarara ihu.
Waɗannan dakaru guda ɗari dake ƙarƙashinta suna muryarta suka fito daga inda suke.
Rundunonin guda biyu suka fuskanci juna a bakin kogin Saisal.
Shugabar ma'abota Bankai ta fito gaban rundunarta tayi ihu, ta zaro takobin Bankai mai mataki na arba'in da tara, ta kaiwa iska sara.
Wani irin faifai na ƙanƙara ya fice daga tsinin takobin nata yayi kan rundunar su Zarifa.
Faifan yana tafe yana daskarar da iskar dake gilmawa ta gabansa saboda tsananin sanyi.
Wani hadari na ƙanƙara ya bayyana a saman su Zarifa, sanyi mai ratsa kashi ya kusan fasa ƙashi ya fara bugan su.
Zarifa tana ganin haka tayi murmushi, ta zaro takobinta daga cikin kufe.
Wani baƙin hayaƙi ya fito daga cikin takobin ya tashi sama.
Kafun wannan fai-fai da ma'abociya Bankai ta aiko ya iso inda suke, Zarifa ma ta sari iska da wannan takobi nata.
Wani mutum-mutumi wanda aka halicci da irin wannan hayaƙi ya bayyana, ya ruga da gudu kan wannnan fai-fai na ƙanƙara.
Mutum-mutumin ya sa hannaye ya fara ƙoƙarin hana wannan fai-fai ƙarasawa inda su Zarifa suke.
Shi kuma fai-fai ya ci gaba da dannawa yana so ya ƙwace ya wuce, amma mutum-mutumin ya hana shi.
Nan fa suka fara kokawa wadda ta ja hankalin dukkan mayaƙan dake wajen, suka ƙurawa abin idanu suna al'ajabi.
Wannan mutum-mutumi jikinsa babu tsoka da jini, zallar baƙin hayaƙi ne kawai ya cure a waje guda.
Koda aka ɗauki lokaci ana wannan fafatawa sai shugabar ma'abota Bankai ta fusata ta sake kai wani wani saran kan iska.
Zarifa ta sake yin murmushi ta caka wannan takobi nata a cikin ƙasa, take wajen da suke gaba ɗaya yayi girgiza, tamkar ƙasa zata rufta ta haɗiye dukkan waɗanda suke kanta.
Gagarumar ƙura ta turnuƙe wannan waje gaba ɗaya, su Zarifa basa ganin komai har wannan ƙura ta lafa.
Ai kuwa sai suka nemi waɗannan ma'abota Bankai ɗin sama da ƙasa suka rasa.
Dama abinda ya kawo su wannan waje shi ne, gurɓata ruwan sha kuma sun gama hakan, saboda haka suka gudu suka tunkari Ajalin-Abokan-Gaba inda ɗaya rundunarsu take.
Zarifa da waɗannan mayaƙa suka yi amfani da takun sawayen mayaƙan, suka take musu baya da gudu.
Duk tsananin gudu da naci irin na dawakan su Zarifa sai ya zamo na banza domin ko hango ƙurar ma'abota Bankai ba sa yi.
Saida suka shafe sa'a ɗaya da rabi suna gudu. sannan suka iso filin Ajalin-Abokan-Gaba inda suka iske tuni gagarumar rundunar sarki Samudul Ansari ta daɗe da hallara.
A gefe guda kuma, ga rundunar ma'abota Bankai guda ɗari da shugabar su guda daya.
Sarki Samudul Ansari dakaru guda ɗari uku kacal ya ɗebo ya fito wannan yaƙi da su.
Ya san karo da ma'abota Bankai sai cikakken shiryayye, shiyasa bai cika fitowa da runduna mai yawa ba.
Sarki Samudul Ansari ya taka da ƙafafuwansa ya fita gaban wannan runduna ya tsaya, Aiyni Gorgon tana ganin haka itama ta saki linzamin dokinta ta nufi inda yake.
Tana zuwa suka yi kallon-kallo sannan ta ce.
"Zan yi maka adalci guda ɗaya - ka miƙa wuya!" inji Aiyni Gorgon.
Sarki Samudul Ansari yayi murmushi ya ce, "Ina matsayin sarki, zan miƙa kaina ga azzalumai? Sannan a cikin ƙasata?"
Aiyni tayi murmushin mugunta dama tasan cewa, sarki Samudul Ansari ba zai taɓa miƙa wuya ba, amma tayi masa tayin ne kawai.
"Adalci na biyu - mu gwabza yaƙi ni da kai, duk wanda aka kashe rundunarsa ta faɗi..." ta ce.
Sarki Samudul Ansari yayi guntun tunani ya ce, "Na amince da wannan..."
Aiyni tayi murmushin jin daɗi ta juya wajen rundunarta domin sanar dasu wannan hukunci da ta yanke, shima Samudul Ansari saiya koma ya sanar da su Zarifa.
Duk cikin rundunar Samudul Ansari babu wanda zuciyarsa tayi rawa bisa wannan abu da sarki Samudul Ansari yazo ya sanar da su.
Sarki Samudul Ansari ya sauƙo daga dokinsa sannan ya koma tsakiyar filin ya tsaya.
"Ina da magana..." inji tau'rin.
Samudul Ansari yayi guntun tunani ya ce, "Ina jin ka..."
"Yau zamu kawo ƙarshen gardamar dake tsakanin mu da ma'abota Bankai, yau zasu tabbatar da ƙarfin mu..."
Samudul Ansari ya ce, "Wannan ba wani abin damuwa bane, tau'rin..."
"Kayi amfani da kaso talatin na ƙarfinka, saboda na raina ƙarfin wannan yarinyar..."
Samudul Ansari yayi murmushi a lokacin da Aiyni ta iso gabansa.
Aiyni ta zaro takobinta Bankai mai mataki na saba'in da takwas.
Gagarumar walƙiya wadda ta haska dukkan wannan daula gaba ɗaya ta bayyana.
Farar walƙiya mai ratsi-ratsin shuɗi ta sauƙo daga cikin wani baƙon gajimare ta shiga cikin wannan takobi ta Aiyni.
Idanuwanta suka sauya launi suka koma tamkar na maciji, harshen bakinta ya koma dafin maciji.
Wannan ita ce ƙarfin Aiyni Gorgon - ɗaya daga cikin BES.
Kowanne ɗaya daga cikin BES yana da ƙarfi na musamman wanda duk faɗin daular Gorgon babu mai rabinsa.
Walƙiya ita ce iko da ƙarfin Aiyni.
Samudul Ansari na ganin haka ya gyara tsayuwa, ya zaro takobinsa ta Saif-Al-Barzaƙ.
Babu wani canji da Saif-Al-Barzaƙ ta haifar a wannan waje. Kai kace ƙarfinta bai kai ya tsaya a gaban ikon Aiyni ba.
Sannu-a-hankali sararin samaniya ta soma cika da irin wannan hadiri wanda walƙiyar Aiynin take fitowa daga cikinsa.
Babu abinda ke tashi a wannan filin yaƙin idan ba walƙiyar Aiyni ba, idanuwanta suna fitar da irin launin walkiyar, haka ma takobinta.
"Ka shirya?" ta tambayi sarki Samudul Ansari. Muryarta tana fita tamkar ƙarar aradu na zubowa ƙasa.
Sarki Samudul Ansari yayi murmushi sannan ya buɗe hannayensa, alamun ya shirya.
Aiyni Gorgon tayi murmushi sannan ta kaiwa sarki Samudul Ansari sara, takobinta ta tunkaro shi, tana tafe tana ƙugi, tana tartsatsin walƙiya.
Tabbas babu abinda za'a sara da wannan takobi, wannan walƙiya bata narkar da shi ba.
Sarki Samudul Ansari ya haɗe fuska ya harari takobin, baƙin hayaƙi ya fita daga idanunsa ya juye izuwa siffar takobi ya tare takobin Aiyni.
Wata gagarumar ƙara ta cika wannan fili gaba ɗaya, bisa dole kowa ya sunkuya sannan suka toshe kunnuwansu.
Baƙin hayaƙin ya tarwatsa takobin Aiyni, sannan ya juyo ya shafi a jikinta.
Abin mamaki, a hankali wannan hayaƙi ya shafi jikinta amma ji tayi wani dunƙulallen hannu a cikin hayaƙin ya gabza mata naushi.
Saboda ƙarfin naushin saida tayi tsalle sannan ta faɗo a can baya.
Cikin gaggawa ta miƙe tsaye fuskarta cike da tsananin mamaki.
Wai ana nufin harin Bankai mai mataki na ashirin bai kai ya illata sarki Samudul Ansari ba?
Ya ya aka yi sarki Samudul Ansari ya ɓoye naushi a cikin wannan baƙin hayaƙi har ya samu nasarar gabza mata?
Aiyni ta ɗaga takobinta sama ta kwarara uban ihu.
Walƙiya ta fara feshi daga cikin bakinta, gajimare suka lulluɓe daidai inda take.
Ta tashi ta tsaya a cikin iska, ta dakawa sarki Samudul Ansari wani irin harara da idanuwanta na Renin-Yilan.
Farin haske wanda ba'a taɓa kallon irinsa ba, ya fice daga cikin idanun nata yayi kan Samudul Ansari gadan-gadan.
Wannan farin haske shi ne sirrin dake cikin idanunsu, duk abinda ya gilma ta cikinsa daskarar dashi yake ya mayar da shi gunki.
Samudul Ansari shima ya kalli wannan farin haske da idanuwan tau'rin, take baƙin haske ya fito daga cikinsu sannan ya tari farin hasken.
Suna haɗuwa a waje guda, suka tarwatse suka bi iska gaba ɗaya.
Ga dukkan alamu ƙarfin Renin-Yilan yazo daidai da ƙarfin baƙin haske na tau'rin.
Aiyni ta haɗe fuska ta ƙara ƙarfin takobin izuwa mataki na arba'in, ta kaiwa Samudul Ansari.
Faifan walƙiya ya fita daga cikin takobin, saboda ƙarfin gudunsa da kuma yadda yake rangaji saida ya firgita dukkan jama'ar dake filin yaƙin.
Aiyni Gorgon bata san yadda aka yi ba, amma cikin sauri wanda yafi gaban wannan walƙiya nata Samudul Ansari ya ɓace ya bayyana a kusa da ita.
Kafun ta gama ankara tuni ya kai mata sara a wuya, takobin Saif-Al-Barzaƙ tana tafe tana fitar da baƙin hayaƙi wanda ya tare mata gaba.
Aiyni tayi amfani da idanuwan Renin-Yilan ta kaucewa saran, amma dukda haka saida daidai inda saran zai samu yayi alamun baƙi.
Wani irin ƙaiƙayi ya cika wajen wanda yasa Aiyni gaggawar sosawa, tabbas inda ace takobin Saif-Al-Barzaƙ ta sameta a wuya, da ƙarshenta yazo.
Aiyni ta daka tsalle gefe, ta kawowa Samudul Ansari sara ita ma a wani salo na mayar da martani.
Cikin kwanciyar hankali Samudul Ansari ya juyo ya dubeta, baƙin haske ya sake ɓulɓulowa daga cikin idanunsa, ya tarwatsa takobin sannan yayi jifa da ita.
A fusace Aiyni ta sake miƙewa tsaye ta kwarara uban ihu wanda ya cika wannan fili gaba ɗaya.
Ta yi jifa da takobin da ke hannunta, gashin kanta ya juye izuwa macizai, idanuwanta suka fara fitar da farin haske mai sanya firgici, harshen bakinta ya sauya izuwa na maciji.
Ta fizgo maciji guda ɗaya daga cikin gashin kanta, yana fitowa daga kanta ya juye izuwa takobin Bankai wadda ke ɗauke da lamba na 78 a yaren daular su.
Bayyanar takobin yasa gajimare masu cike da walƙiya suka cika sararin samaniya, ƙarar aradu ta soma ƙwararowa ƙasa ta addabi sauran dakaru.
Jikin Aiyni ya juye izuwa kore-kore, tayi ihu ta ɗaga wannan takobi, ta ruga da gudu kan Samudul Ansari.
Sawayenta na dira bisa turba suna haifar da gagarumar girgizar ƙasa wadda take watsi da dakarun dake can gefe.
Samudul Ansari ya gyara tsayuwarsa ya riƙe takobinsa da kyau.
Aiyni Gorgon tana isowa inda Samudul Ansari yake suka ruguntsume da azababben yaƙi mai matuƙar ban tsoro da sanya tsoro a zuƙatan masu kallo.
Aiyni ta wanzu tana kawowa Samudul Ansari sara da suka da zabgegiyar takobin dake hannunta ta walƙiya.
Shi kuma yaci gaba da kare kansa cikin kwanciyar hankali, ba tare da ya mayar da martani ba.
A duk sa'adda takobin Aiyni ta tunkaro Samudul Ansari sai kaga hadiri masu yawan gaske sun bayyana a saman kansa.
Suna feso masa wuta daga cikinsu.
Amma dukda haka tsahon lokaci basu yi masa komai ba, shi kuma ko sau ɗaya bai mayar da martani ba.
Lokaci mai ɗan tsaho suna ta wannan fafatawa, amma Aiyni bata sami nasarar komai akan Samudul Ansari ba.
Lamarin da yayi matuƙar fusata ta kenan, domin a wannan lokaci ta gama ƙure ƙarfin takobinta.
Mataki na saba'in da takwas ace bai yiwa Samudul Ansari komai ba?
Ko ba komai Aiyni tana daga cikin BES waɗanda suke da tsananin ƙarfi fiye da tunanin mutum.
Cikin tsananin fusata ta juyo wajen Samudul Ansari, a wannan lokaci jikinta ya gama juyewa zuwa kore, irin wannan walƙiya na feshi daga cikin bakinta da takobinta.
Ta danƙarawa Samudul Ansari sara a kafaɗa cikin wani irin azababben sauri wanda yafi gaban gudun walƙiya.
Takobin nata ta fasa jikin Samudul Ansari amma raunin baiyi zurfi sosai ba.
Sinadarin walƙiya ya shiga cikin jikin Samudul Ansari, ya soma yawo a cikin jikinsa.
Sinadarin ya soma kumbura a cikin jikin Samudul Ansari, lamarin da yasa shima ya soma kumbura kenan.
Saida Samudul Ansari ya kumbura ya ninka girmansa da tsahonsa na da sau uku, sannan yayi bindiga ya tarwatse.
Wannan shi ne babban harin takobin Bankai mataki na saba'in da takwas da Aiyni tayi amfani dashi akan Samudul Ansari.
Gangar jikin Samudul Ansari ta ɓace ɓat! daga cikin wannan fili aka nemeta aka rasa.
Aiyni ta sumbaci wannan takobi nata ta kwarara uban ihu, ta nuna sauran rundunar Samudul Ansari.
Gagarumin hadiri mai ambaliyar walƙiya ya bayyana a saman kansu. Sassanyar iska ta fara kaɗawa a ƙasan su, wadda ta yi matuƙar addabar su.
Aiyni ta sake tashi sama cikin iska, tazo saman wannan hadiri ta zauna.
Ta haɗe tafukan hannayenta guda biyu a waje guda sannan ta rufe idanunta ta fara kiran ɗalasimai.
Hadirin ya soma sauya launi izuwa kore-mai-duhu, tsahon lokaci kafun a fara wani irin koren ruwa.
Wannan ruwa na da ban al'ajabi, baya isowa ƙasa yake taruwa akan iska sannan ya koma koren hayaƙi ya zube ƙasa.
Lokaci mai tsaho ana ta abu ɗaya, kafun Aiyni ta ɓace daga kan gajimaren.
Aiyni ta koma gaban rundunarta ta sanar dasu su ja baya kawai, wannan yaƙi yazo ƙarshe.
Gagarumar rundunarta suka ja da baya amma ba haka suka so ba, sun so a basu dama su more takubban su akan wannan runduna.
Amma babu yadda suka iya, dole ne su bi umarnin shugabar su.
Wannan koren hayaƙi da ya zuzzube a ƙasa, ya fara tashi sama yana tsiri.
Sannu-a-hankali ya soma rikiɗewa yana juyewa izuwa macizai ƙananu.
Macizan zasu iya kai guda ɗari, suka tunkari inda su Zarifa suke.
Suna ƙara gaba suna daɗa girma.
Kafun su iso inda su Zarifa tuni sun juye izuwa gabza-gabza kamar bishiyar dabino.
Zarifa ta baiwa rundunarta umarnin fiddo takubbansu, cikin gaggawa suka yi hakan sannan suka afkawa waɗannan macizai da sara da suka.
Nan fa aka sake buɗe sabon gumurzu tsakanin manyan macizai da su Zarifa.
Takubban hannun su Zarifa suna ɓulɓular da baƙin hayaƙi wanda yake hana waɗannan macizai kallon su sosai.
Zarifa ta shiga sare kan waɗannan macizai da takobin dake hannunta cikin zafin nama.
A wannan lokaci a fusace take, bisa ganin cewa sarki baya nan.
Tabbas ta san cewa, babu wani abu da zai faru da sarki Samudul Ansari kawai ya tafi ne domin aiwatar da wani shiri.
Aiyni da sauran dakarunta kuwa, gefe guda suka koma suka sakawa wannan gumurzu idanu.
Ba'a ɗauki lokaci mai tsaho ana wannan gumurzu ba, wadannan macizai suka soma illata dakarun Zarifa.
Babban abinda yake taimaka musu shi ne waɗannan takubba da sarki Samudul Ansari ya samar musu.
Da zarar sun sari jikin macizan da waɗannan takubba sai wajen yayi baƙi sannan ya ƙone ƙurmus.
Dukda haka saida wajen dakaru ashirin suka rasa rayukansu saboda ƙarfin dafin macizan.
Ana cikin wannan hali ne, wani baƙin hayaƙi ya soma fitowa daga ƙarƙashin ƙasa, ya fara baibaye jikin waɗannan macizai.
Kafun a jima gagarumar baƙar wuta ta fara kama jikinsu tana ƙone su ƙurmus.
Cikin ƙanƙanin lokaci dukkan macizan da Aiyni ta samar suka ƙone suka zamo toka.
Ba wai ma'abota Bankai ɗin da suka zo wannan fili kaɗai ba, hatta ita kanta saida ta sake cika da tsananin mamaki.
Idan aka ce ma ƙololuwar mataki na saba'in da takwas to wadannan macizai guda ɗari kenan.
Komai girman daula idan aka turo su, suna iya ruguje ta a cikin abinda bai wuce kwana guda ba.
Ba don komai sarauniya Yilan ta turo Aiyni ba, sai domin amfani da wadannan macizai ta hallaka daular gaba ɗaya. Ba wai iya Samudul Ansari ba.
Abinda yasa Aiyni da kanta ta koma wajen dakarunta ta basu umarnin komawa gefe shi ne, ta san sun gama da wannan daula.
Bata taɓa tsammanin takubban hannun waɗannan dakaru zasu illata macizan ba balle har su kashe wasu.
A yanzu gashi an

Please Login or Register in order to submit comment