Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Sai kawai yace "eh Baffai bata da lafiya tana gidan baabaa Mero"
Baffai yace "to Allah ya sauwaqa ya bata lafiya, sai kaci tuwo muje muyi sallahn isha'i mu biya naga yaya jikin nata"
"To Baffai" ya faɗa a taqaice ya tashi ya shige ɗakin da yake mallakin sa.
Ɗaki 1 na Magaji
Ɗaki 1 nasu Hassu
Ɗaki 1 na Inna A'i
Ɗaki 1 na Mama Lami

Shigewa yayi yana qara ganin qoqari irin na mama lami wajan iya zagewa ta laftowa Baffai qarya duk da bai san mene asalin abunda ya faru ba amma dai yasan shigowan sa bata tsakar gidan ma kuma ba ita takai Innai gidan baba mero ba sannan ba ita taje da kanta ba tunda dai shine ya kaita, Inna dake nuna halin ko inkula akan ƴar tata tana basa mamaki ba ɗan kaɗan ba, Shima dai gashinan shine ɗan fari agidansu amma ba ruwan gwoggonsu da wannan abun al'ada-al'adan.
Zaunawa yayi yaci tuwonsa bayan yag ama ya fito da kwanukan.
Alwala yayi yace "Baffai mu tafi masallacin ko"
Fita suka yi a gidan suka wuce masallaci suka yi sallah sannan suka wuce gidan baabaa. Da sallama suka shiga gidan, samunta suka yi itama ta idar da sallahn kenan tana jan carbi.
Innai ce ta fito a ɗaki tana cewa "sannu da zuwa Baffai na" ta shumfiɗa masu tabarma.
"Sannu maman baffanta ya jikin? A taqaice tace "da sauqi baffai" .

Suna zaune sai suka ji sallaman Baba. Duk suka amsa masa ya shigo ya samu waje ya zauna.
Magaji ne ya gaishe sa ya amsa sai Baffai da yace masa "sannu da shigowa yaya" suka gaisa.
"Baba sannu da zuwa" cewar Innai da kanta ke qasa.
"yauwa maman Baba da Baffai sannunki ko, yau kuma a gidan takwara ake hirane" faɗin Baba cikin kulawa.
Langwaɓar da kai tayi tace "a'a fa Baba banda lafiya ne shiyasa"
Ashshaa! sannu maman Baba Allah baki lafiya ko
"Ameen" cewar baabaa Mero da ta shafa addu'a.
Kallon su tayi duka, gaisheta Baba yayi ta amsa Magaji ma ya gaidata ta amsa sannan Baffai ya gaidata amma tayi kaman bata kallesa ba ma.
Kansa aqasa yace "baabaata me nayi amun afuwa"
Cikin karaji tace "Au tambaya kake mevkayi bayan ka tara marassa tausayi da imanini a gidanka wai matanka"
"Ayi haquri baabaa Inshà Allahu ba zasu qara ba" cewar baba cikin sigar rarrashi.
"Bawani ba zasu qara ba Musa ka qyaleni da me sunan mallam na zaure, wato shi dai ba zai wa Indo nasiha da faɗa ta gyara halinta ba, ace mata suna gani suna ji yarinya ta kusa mutuwa amma ba mai temaka mata dan tsabar jaraban mugunta ai ba amfanin zaman su a gidan, Ita kuma wannan gulmammiyar Lami sanda ta ganni wai ta fito duba yarinyan wai duk wannan lokutan da yarinya ta kwasa a zube a qasa wanwar a sume duka walha take yi dan ta maida waye sha-sha-sha, Walha a gidan wa inba ganin arahan gabas da kuma renamun hankali da tayi ba yaushe ta tsaida sallah biyar 5 a rana ma bare ta qara da nafila, ni dai waɗannan marassa imani da ka tara a gida basu da amfani a wajena" baabaa ke maganan kaman zata rufe Baffai da duka.
Haquri suke ta bata dukan su, ita dai Innai ba tace komai ba saima tashuwan da tayi ta wuce ɗakin tsohuwar.
Da qyar suka lallaɓa stohuwar tasu sannan tabar faɗan da take yin, Baba yace "Insha Allah za'a gyara baabaa sannan kai kuma baffan Magaji ka musu faɗa sosai dan nima abun nan da Innar su keyi bayamun daɗi"
Baabaa tace "Ka qyaleshi dai tunda shi sha-sha-sha ne sha-giri girbau sun maida shi mijin tace, yana zaune zasu kashe masa ɗiyar sa da Allah ya basa, tom ni dai bazan bari haka ta faru ba daga shi ɗin har su zan yi dai-dai dasu"
Haquri Baffai ya bada akan za'a gyara zai musu faɗa.
Magaji yana zaune gefe be ce komi ba a zanceb iyayen nasa.
Baabaa Kallon magajin tayi tace "to kaima zan dawo kanka, wai kana boko kana nan ka gama girme mana a gida sai ka rasa wacce zata auri tsoho irinka ai"
Haɗe fuska yayi yasan dama tijaran stohuwar nan da yawa bata qyale kowa.
"Yauwa baabaarmu a faɗa masa ya nemo mata" cewar Baba.
Baffai yace "a dena takura wa yarona bai gama girma ba tukun"
taɓe baki baabaa Mero tayi tace "wannan zindiqin baligun yaron ne bai girma ba? Shikkenan zan kuwa bada shi sadaka wa wata baiwar Allah ba da jimawa ba"
Qwalawa Innai qira baabaa Mero tayi "takwara, takwaraa, takwaraaa zo nan"
Zuwa tayi ta zauna gefen baabaa Meron.
Baabaa tace "niifa banson zaman ɗakin nan kaman munafuka"
Baba ya kallesu yayi murmushi, cewa yayi "baabaarmu kar dae mu jiki da takwararki"
Baabaa tace "Allah sauwaqa a jimu"
Baba ya maida kallonsa kan Innai yace "mamar baba meke damunki?
take idonta ya kawo ruwa, cikin shagwaɓa tace "Kai na ke ciwo sai ciki na"
Salati baabaa Mero tayi tace "kunga ja'irar ƴarku ko tun da rana nake binta ta faɗa mun amma taqi faɗin meke damunta sai yanzu dan taga iyayenta shikkenan zaki tashi ki bisu dama ba za'a bar Hassu ita kaɗai ba tun da dai ke ma munafurcin kike son koya yarinya kaman narkakken tuwo, nan yanzu ma daga tambaya sai kuka, ooh ni Mero Allah nagode maka shikkenan ai kema ɗin tattara ki zamu yi mu aurarki".
Suka ci-gaba da hiransu da baabaar tasu cikin raha, ita kuma Innai ta kwantar da kanta a qafan baabaa mero.
Magaji ya tashi ya fice yace da iyayen nasa in sun gama yana waje.
Baabaa Mero ta bisa da harara tana cewa "mutun sai jarababben baqin hali ai zaka ji dashi dan ni dai ba kayo halin miji na ba".
Can su Baffai suka wa baabaar tasu sai da safe suka fice a gidan.
Magaji bayan ya fito wucewa yayi dandalin dake qauyen direct abunsa, Baffai da suka fito basu gansa ba sunsan za'ayi haka daman dan haka tafiyansu suka yi suna hira na yan uwa.
Baba ya qara jan kunnen Baffai akan abinda matansa keyi, lallai ya musu faɗa su gyara hakan bai kamata ba inba dai basu son zaman lafiya da baabaa Mero ba.
Bayan ya gama jaddada wa ganin nasa sai suka yi sallama Baffai ya shige gidansa kasancewan basu da nisa da baabaa Mero, Baba ma ya wuce nasa gidan dake gaba da na Baffai ba sosai ba.
Ya shigo gidan ya samu duk basu tsakar gidan, ɗakin Innar su Hassu ya wuce da sallama ya shiga, samun ta yayi ita da Hassu suna taɗi tana haska mata tana homework nata( kasancewansu fulani kuma waɗanda ke qauye bai hanasu karatun boko ba tunda yanzu duniya a waye take).
Ganin Baffai ya shigo ta tashi ta tattara littatafan nata dan dama da gama ta masu seda safe, albarka Baffai ya sanya mata. Ɗakin mama Lami ta wuce dan ba zata iya kwana a ɗakinsu ita ɗaya ba tsoro take ji in ƴar uwanta batanan.

Dasallama ta shiga,amsa mata mama Lami tayi.
Bata dai ce mata komi ba ta haura gado qarami dake ɗakin bayan ta kakkaɓe ta kwanta ta lulluɓu abunta, mama lami ba tace mata qala ba kawai ita ma lulluɓuwan ta tayi sai bacci kuma.

Baabaa Mero ta lallaɓa Innai taci tuwo ta qara shan magani, suna hiransu baabaa mero na mata ta-tsuniya, har suka kwanta zuciyan ta cike da tunanin ƴar uwanta zata kwana ita ɗaya a ɗakin nasu gaba-ɗaya sai taji ba daɗi, a haka suma har baccin ya ɗauke su.

Baffai tunda ya zauna nasiha yake mata akan inba zata daina wannan halin ba to ta rage don kuwa bai kamata ba, Allah zai mata hisabi tsakaninta da ƴar da ya bata.
"Aishatu su yara da kike gani da Allah ya bamu amana ne ya bamu ba wayonmu ko dabarar mu ba, amana kuwa kinsan ko ɗan adam ne ya baka to dubi abunda sakaci da amanansa keja maka balle wanda ya haliccemu da kansa ya bamu amana muyi sakaci dashi me kike tunani a kai? Tabbas wannan ba al'ada bane A'ishatu dan naki ya wuce a qira sa da hakan, dan girman Allah ki aje wannan abu a gefe ki rungumi abunda Allah ya azurtaki dashi, dan su 'ya'ya arziqi ne babba ma kuwa, ko kina ga a wannan duniya tamu in uwa ba taja ɗan ta a jiki ta soshi ba wani zai so mata shi ne? Ko ɗaya dan wannan alhaqi ne dake kan uwa kuma duk abinda wani zai nuna wa ɗan ki na soyayya ko tsangwama(hantara/qiyayya) to kece sila dan kece malamar da kika nuna hakan a koyarwanki. Dan girmam Allah ki gyara A'ishatu kamun lokacin hakan ya qure miki".
Inna kanta a qasa bata ce komi ba illa iyaka "ayi haquri malam"
Tashuwa tayi ta haye gado ta kwanta
Shima baffan hawa yayi dan ya lallashi matar aljannan sa, tunda yaga abun sai a juya ɗayan sigan dagann sai.......




𝐓𝐀𝐋𝐋𝐀!! 𝐓𝐀𝐋𝐋𝐀!! 𝐓𝐀𝐋𝐋𝐀!!

𝐎𝐔𝐌 𝐀𝐋'𝐀𝐌𝐄𝐄𝐍 𝐃𝐀𝐓𝐀 𝐒𝐄𝐑𝐕𝐈𝐂𝐄
𝐲𝐨𝐮𝐫 𝐬𝐚𝐭𝐢𝐬𝐟𝐚𝐜𝐭𝐢𝐨𝐧 𝐢𝐬 𝐨𝐮𝐫 𝐜𝐨𝐧𝐜𝐞𝐫𝐧.

𝐊𝐮𝐳𝐨 𝐤𝐮 𝐬𝐚𝐲𝐢 𝐝𝐚𝐭𝐚 𝐦𝐚𝐢 𝐬𝐚𝐮𝐪𝐢 𝐦𝐚𝐢 𝐢𝐧𝐠𝐚𝐧𝐜𝐢 𝐝𝐨𝐦𝐢𝐧 𝐠𝐚𝐛𝐚𝐭𝐚𝐫 𝐝𝐚 𝐡𝐢𝐝𝐢𝐦𝐨𝐦𝐢𝐧 𝐤𝐮 𝐚 𝐨𝐧𝐥𝐢𝐧𝐞 𝐤𝐨 𝐤𝐮𝐰𝐚 𝐤𝐚𝐥𝐥𝐚𝐜𝐞-𝐤𝐚𝐥𝐥𝐚𝐜𝐞 𝐚 𝐘𝐎𝐔𝐓𝐔𝐁𝐄 𝐛𝐚 𝐭𝐚𝐫𝐞 𝐝𝐚 𝐝𝐚𝐭𝐚𝐧𝐤𝐢/𝐝𝐚𝐭𝐚𝐧𝐤𝐚 𝐲𝐚𝐲𝐢 𝐬𝐚𝐮𝐫𝐢𝐧 𝐳𝐮𝐪𝐞𝐰𝐚 𝐛𝐚. 𝐈𝐧𝐚 𝐦𝐚'𝐚𝐛𝐨𝐭𝐚 𝐚𝐦𝐟𝐚𝐧𝐢 𝐝𝐚 𝐤𝐚𝐟𝐚𝐫 𝐬𝐚𝐝𝐚𝐰𝐚 𝐭𝐚 𝐓𝐈𝐊𝐓𝐎𝐊 𝐦𝐚𝐬𝐮 𝐤𝐮𝐤𝐚𝐧 𝐬𝐚𝐮𝐫𝐢𝐧 𝐪𝐚𝐫𝐞𝐰𝐚𝐧 𝐃𝐀𝐓𝐀 𝐭𝐨 𝐟𝐚 𝐰𝐚𝐧𝐧𝐚𝐧 𝐛𝐚 𝐤𝐚𝐦𝐚𝐧 𝐤𝐨 𝐰𝐚𝐧𝐧𝐞 𝐛𝐚𝐧𝐞 𝐬𝐚𝐢 𝐚𝐧 𝐠𝐰𝐚𝐝𝐚 𝐚𝐤𝐚𝐧𝐬𝐚𝐧 𝐧𝐚 𝐪𝐰𝐚𝐫𝐚𝐢 𝐝𝐚𝐧 𝐢𝐧𝐠𝐚𝐧𝐜𝐢 𝐝𝐚 𝐤𝐮𝐦𝐚 𝐪𝐚𝐫𝐠𝐨 𝐠𝐚 𝐃𝐀𝐓𝐀𝐧 𝐤𝐚 𝐭𝐨 𝐤𝐪 𝐳𝐢𝐲𝐚𝐫𝐜𝐢

𝐎𝐔𝐌 𝐀𝐋'𝐀𝐌𝐄𝐄𝐍 𝐃𝐀𝐓𝐀 𝐒𝐄𝐑𝐕𝐈𝐂𝐄

𝐌𝐓𝐍 𝐀𝐈𝐑𝐓𝐄𝐋

𝟏𝐆𝐁 - 250 𝟏𝐆𝐁 - 2𝟓𝟎
𝟐𝐆𝐁 - 5𝟎𝟎 𝟐𝐆𝐁 - 500
𝟑𝐆𝐁 - 75𝟎 𝟑𝐆𝐁 - 750

𝐆𝐋𝐎 𝟗𝐌𝐎𝐁𝐈𝐋𝐄

𝟏𝐆𝐁 - 25𝟎 𝟏𝐆𝐁 - 25𝟎
𝟐𝐆𝐁 - 50𝟎 𝟐𝐆𝐁 - 5𝟎𝟎
𝟑𝐆𝐁 - 75𝟎 𝟑𝐆𝐁 - 75𝟎

𝐌𝐮𝐧𝐚 𝐚𝐫𝐚𝐡𝐚 𝐦𝐮𝐧𝐚 𝐡𝐚𝐧𝐚 bashi😊 𝐬𝐚𝐲𝐚𝐧 𝐧𝐚 𝐠𝐚𝐫𝐢 𝐦𝐚𝐢𝐝𝐚 𝐤𝐮𝐝𝐢 𝐠𝐢𝐝𝐚(𝐢𝐧𝐣𝐢 𝐡𝐚𝐮𝐬𝐚𝐰𝐚)
𝐙𝐚𝐤𝐮 𝐢𝐲𝐚 𝐭𝐮𝐧𝐭𝐮𝐛𝐚𝐧 𝐦𝐮 𝐚𝐤𝐚𝐧 𝐰𝐚𝐧𝐧𝐚𝐧 𝐥𝐚𝐲𝐢 𝐝𝐚𝐧 𝐛𝐢𝐲𝐚 𝐤𝐨 𝐭𝐚𝐛𝐛𝐚𝐭𝐚𝐫 𝐝𝐚 𝐬𝐡𝐚𝐢𝐝𝐚𝐧 𝐛𝐢𝐲𝐚
𝟎𝟕𝟎𝟐𝟓𝟐𝟑𝟐𝟎𝟐𝟗
𝐂𝐀𝐋𝐋/𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏

𝐀𝐜𝐜𝐨𝐮𝐧𝐭 𝐧𝐮𝐦𝐛𝐞𝐫
𝟕𝟎𝟐𝟓𝟐𝟑𝟐𝟎𝟐𝟗
𝐀𝐈𝐒𝐇𝐀 𝐀𝐋𝐈𝐘𝐔
𝐎𝐏𝐀𝐘 𝐁𝐀𝐍𝐊.

𝐒𝐀𝐈 𝐊𝐔𝐍𝐙𝐎𝐎𝐎


***
RUGAN HAMMAN
Shine sunan rugar tasu, ruga ce da takenan kaman gari ba ruga ba sakamakon cikan da tayi da kuma cigaba da ake samu a rugar ta hanyan asibiti da makarantu etc...
fulanine mafiya yawa a rugan sai ɗaɗɗaya-ɗaɗɗaya dags wasu yaruka kaman bolawa, terawa, wajawa har da hausawa.
Rugan ya xama kaman garine sakamakon fulanin rugan mazaunane ba matafiyaba, suna gudanar da rayuwansu cikin nasarorin cigaba Alhamdulillahi.
Suna karatun muhammadiya sosai da boko duk da basu da na gaba da primary, rugan nasu na qarqashin qaramar hukumar 𝘼𝙨𝙝𝙖𝙠𝙖 dake garin 𝙜𝙤𝙢𝙗𝙚 state.
In mutum ya gama yaqi da jahilci da primary a rugan sukan fito cikin qaramar hukumar ashaka dan ci-gaba da secondary....


ZANCI GABA DA POSTING NE KAWAI IN NAGA YAWAN COMMENTS NAKU

09161720046
Mrs big barbieyh ✍️




💋💋 امى بتولة💋


𝘿𝙤𝙢𝙞𝙣 𝙩𝙖𝙡𝙡𝙖𝙩𝙖 𝙝𝙖𝙟𝙖𝙧𝙠𝙪, 𝙠𝙪 𝙩𝙪𝙣𝙩𝙪𝙗𝙚𝙣𝙞 𝙖 𝙬𝙖𝙣𝙣𝙖𝙣 𝙡𝙖𝙮uka:-
09161720046
𝘾𝙝𝙖𝙩 𝙤𝙣𝙡𝙮.
07015870735
𝙔𝙤𝙪 𝙘𝙖𝙣 𝙘𝙖𝙡𝙡 𝙙𝙞𝙨 𝙤𝙣𝙚, 𝙭𝙖𝙢𝙪 𝙢𝙖𝙠𝙪 𝙩𝙖𝙡𝙡𝙖𝙣𝙠𝙪 𝙖 𝙧𝙖𝙝𝙪𝙨𝙖 𝙢𝙖𝙞 𝙨𝙖𝙪𝙦𝙞, wai hausawa sukace sai an gwada akan san na qwarai. Ni Hareeyh ina maraba da ku masoya, har da alakoron talla inayi😁

NOTED : karku nemeni a wannan layi 08146292652 domin yanzu baya aiki both whatsapp and call.

# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚




𝗝𝗔𝗛𝗜𝗟𝗖𝗜 𝗞𝗢 𝗔𝗟'𝗔𝗗𝗔𝗛? 🥺

Al'qalamin

Uwar batoorl 🕊️


Na sadaukar da wannan shafi sukutum gare ki TATTAƁA KUNNE NA fatan farinciki a rayuwanki da na iyalanki har abada.

Masoya na ababen qaunata ba zaku irgu ba♥️ fatan alkairi gare ku

Adama Umar marubuciyar - halak ɗina (inayin wannan littafi naki Allah qara basira da ɗauka ka)

𝗙𝗮𝗻'𝘀 𝗸𝘂𝗺𝗮 𝗸𝘂𝗻𝘀𝗮𝗻 𝗸𝘂 𝗻𝗮 𝗱𝗮𝗯𝗮𝗻 𝗻𝗲 🤙 𝘀𝗮𝗶 𝗱𝗮 𝗸𝘂𝘂𝘂𝘂
𝗨𝘄𝗮𝗿 𝗯𝗮𝘁𝗼𝗼𝗿𝗹 𝘁𝗮𝗸𝘂 𝗻𝗮 𝘆𝗶𝗻𝗸𝘂𝘂𝘂𝘂 𝗼𝘃𝗲𝗿! 𝗢𝘃𝗲𝗿! 𝗢𝘃𝗲𝗿

𝗠𝗮𝘀𝘂 𝗰𝗼𝗺𝗺𝗲𝗻𝘁'𝘀 𝗱𝘂𝗸 𝗔𝗹𝗹𝗮𝗵 𝘆𝗮 𝗯𝗮𝗿𝗺𝗶𝗻𝗶 𝗸𝘂 😘
𝗠𝗮𝘀𝘂 𝗯𝗶𝗻𝗮 𝗽𝗿𝗶𝘃𝗮𝘁𝗲 𝗱𝗮 𝗮𝗱𝗱𝘂'𝗼𝗲 𝗱𝗮 𝘆𝗮𝗯𝗼 𝗱𝘂𝗸𝗮 𝗶𝗻𝗮 𝗺𝗮𝘁𝘂𝗾𝗮𝗿 𝗴𝗼𝗱𝗶𝘆𝗮 𝘄𝗮'𝗱𝗮𝗻𝗱𝗮 𝗯𝗮𝗻𝘀𝗮𝗺𝘂 𝗻𝗮 𝗱𝘂𝗯𝗮 𝗺𝗲𝘀𝘀𝗮𝗴𝗲'𝘀 𝗻𝗮𝘀𝘂 𝗯𝗮, 𝗶𝗻𝗮 𝗺𝗮𝘁𝘂𝗾𝗮𝗿 𝗯𝗮𝗸𝘂 𝗵𝗮𝗾𝘂𝗿𝗶 𝗮𝗯𝘂𝗯𝘂𝘄𝗮𝗻 𝗻𝗲 𝘀𝘂𝗸𝗮 𝘆𝗶 𝘆𝗮𝘄𝗮 𝗮𝗺𝗺𝗮 𝗸𝘂 𝘀𝗮𝗻𝗶 𝗸𝗼 𝗱𝗮 𝗯𝗮𝗻𝗴𝗮𝗻𝗶 𝗯𝗮 𝗸𝘂𝗻𝗮 𝗿𝗮𝗶𝗻𝗮 🥺💯

𝗜𝗡𝗔𝗬𝗜𝗡𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗦𝗢𝗡𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗜 𝗗𝗔 𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗤𝗔𝗠𝗡𝗔𝗥𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗠𝗨𝗞U 𝗙𝗔𝗧𝗔𝗡 𝗔𝗟𝗞𝗔𝗜𝗥𝗜 𝗗𝗨𝗞 𝗜𝗡𝗗𝗔 𝗞𝗨𝗞𝗘 𝗔 𝗙𝗔'𝗗𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔𝗥 𝗡𝗔𝗡.
𝘂𝘄𝗮𝗿 𝗯𝗮𝘁𝗼𝗼𝗿𝗹 𝘁𝗮𝗸𝘂 𝗺𝗮𝗶 𝘀𝗼𝗻 𝗳𝗮𝗿𝗶𝗻 𝗰𝗜𝗸𝗶𝗻𝗸𝘂.

اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله saw🖤🤍








💋💋 امى بتولة💋

𝗙𝗿𝗲𝗲 𝗯𝗼𝗼𝗸 🅿️ 5_6




Tana tashuwa da safe bayan sunyi sallah sun idar ta ɗau stinstiya ta share ɗakin ta gyara musu sannan ta fito tana share tsakar gidan.
Baabaa Mero da fitowan ta kenan daga banɗaki ajiye butan hannunta tayi tace "ke dai takwara Allah kawo miki sauqi ko kaɗan bakya gajiya da wahala shiyasa gakinan ba auki kaman taliyar murji dan nemawa mutane wata jarabar ba ki da lafiya kin kama aiki, yarinya sai son manyance kaman wata babbar mata"
Innai tanajin stohuwar amma ko a jikinta sharan ta gama ta tattara kwanuka tace "baabaata bari nakai kwanukan gida na dawo"
Baabaa Mero taɓe baki tayi ta karyi goronta sannan tace "in kinga dama karki dawo sai bayan shekara 100, wahalalliya kawai ai so kike kije ki aikatu da jikin da ba kiji sauqi ba, yarinya sai shegen jarabar rashin ji, ni dai Allah ya gani ba haka halina yake ba wai ance mutum yakan iyo halin takwaransa to aradu baki biyo halina ba dan ni nan bana barin ko ta kwana sannan bana ɗaga qafa ba ruwa na da jarabar haukan stiya amma ke a masu suna Maryam ɗin ma kamata yayi ace maki damo(sarkin haquri) yarinya zuciya kaman kare ya lashe, ni ɓacemun daga gani kamun na qarisa ki da kaina" ficewa Innai tayi tana murmushi bata tsaya sauraran baabaa Mero ba dan tasan duk da sonda take mata yanzu zata iya kwaɗa mata abu.
Baabaa Mero ta ci-gaba da mitan ta kaman zata daki babu sannan ta ɗauko kwanon madaran da ta ajiye dan ta bawa takwarar tata tasha da magani sai kuma ta bostare ta tafi gidan nasu da zata mutu bamai kallonta, zama tayi ta shanye abunta tass sannan tace "Allah ganar da ke mai qaunanki takwara".
Fitowa tayi daga gidan baabaa Mero tana murmushi, tafiya take cikin nustuwa wanda wasu sukan ɗau tafiyan nata akan rigima ta keyi.
Yarinyace yar kimanin shekara 14 da haihuwa amma in ka ganta sai kace takai 16 year's, domin halittan da Allah ya mata. Fara ce sol kuma Siririya ce ba mai jiki ba(qiba) abunka da bafulatana, amma rashin jikinta da qarancin shekarunta bai hana halittar da Allah yayi mata bayyana ba dan tun bata gama girman ba maqerin budurci ya bayyana gare ta.
Tana da qugu(mazaunai), kuma duba da gashin dake kwance gaban goshinta da kuma sajen fuskanta hakan ya isar da cewan Allah ya mata baiwan gashi Masha Allah! Round face take dashi mai ɗauke da dara-daran idanunta (golden eyes) farare ne tass kaman madara kai kace idon jinjirine haka baqinma baqi wuluk, tana da yalwan cikan gashin gira wanda har ya haɗe hakan kuwa sai ya bada wani sirri a kyau nata, Tanada dogon hanci wanda shi da biro banbancinsu kawai rubutu ne, ɗan madedecin bakinta wanda inka gani za kayi mamakin anya tana ma cin abinci kuwa tsabar qanqantarsa, tabarakhallah Masha Allah don kyakkyawace ta ajin qarshe wanda qarancin shekatunta basu ɓoye ni'imomi da baiwan da Allah ya azurta ta dasu ba, duk da bawai girman ya gama bayyana a gareta ba.
Innai kenan wacce asalin sunanta shine Maryam takwara ga mahaifiyar Baffanta wato baabaa Mero.

A nuste tayi sallama ta shiga gidan nasu ta kuma yi sa'a baffanta na nan, ta samu Innar su na aikin ɗumame qanwarta Hassu kuma na shara.
Kallon Innar tasu sai jikinta yayi sanyi amma a haka ta qarisa wajanta, durqusawa tayi har qasa tace "jamɓanduna Inna"
Inna A'i kanta a gefe tana ayyukan ta ko juyowa ta kalli yarinyar nata ba tayi ba kawai ta girgiza kai alaman ta amsa gaisuwan.
Daman in da sabo ta saba da hakan tasan iya abunda Innan tasu za tayi kenan, kanta a qasa haryanzun jiki a sanyaye kaman kullum in hakan ya faru ta wuce ɗakin mama lami.
"Jam ɓanduna mama"
(Antashi lafiya mama)
"Jam innai noi ɓandu ma"
(Lafiya innai ya jikin ki)
"Ɓandu waɗu dama"
( jiki dasauqi)
"To Allah hokke en jam"
(Allah qara sauqi) Mama Lami ta faɗa tana jera kwanukan ta.
Da "Ameen" Innai ta amsa sannan ta miqe ta fito a ɗakin.
Hassu ta gaishe ta cikin fillanci tana tambayan ta jikin nata "Adda Innai noi ɓanduma?" "Ɓandu waɗu dama Hassu am".
Mawanki ta wuce dan tayi wanke-wanken, Hassu tace "Adda zanyi wanke-wanken ki bari ki huta abunki kinga baki da lafiya"
Murmushi kawai tawa qanwar nata ba tace komai ba. Haɗa kwanukan wanke-wanken tayi da wanda ta shigo dasu daga gidan baabaa duk ta wanke su, bayan ta kammala ɗakinsu ta wuce ta gyara musu.
Tana kammala ayyukan ta Hassu ma ta gama sharan da take yi dai-dai Baffan su ya fito a ɗakin Innar su sai dukansu suka nufe sa, suna zuwa suka stugunna suka gaishe sa cikin fillanci.
Amsawa yayi yana sanya musu albarka sannan ya tambayi Innai jikinta, da sauqi ta amsa masa, duk gaisuwan da suke yi da fullanci suke magana.

Magaji ya fito a ɗakin sa shima ya tsugunna ya gaida Baffan nasu, Baffai ya amsa cikin fara'a. Gaishe da shi Innai da Hassu suka yi ya amsa masu sannan shima ya tambayi ya jikin Innai ɗin, da sauqi ta amsa masa.

Albarka baffa ya sanya musu duka yace kowa yaje ya karya.
Inna ke madafi tana raba musu abun karyawan, Innai zuwa tayi tace "Innan mu bari in qarisa miki"
Ba tare da Inna tace komai ba ta tashi ta fice a madafin.
Qarisa wa Innan ta aikin tayi ta raba komi har da madaran da Hamman su magaji ya kawo ta raba ta sawa kowa nasa, ta kaiwa Hamman su nasa har ɗakinsa sannan ta qira Hassu kuma takai na Baffai, ita kuma ta miqawa su Inna nasu, Hassu ta ɗauka musu nasu suka yi ɗakinsu da shi.
Ɗumamen tuwon surfaffen masara da aka wanke yayi haske sosai da miyar ɓaskoje bushashshe(bushashshen kuɓewa) da yaji nama da man shanu, sai naman zabbi da kuma madaransu mai ɗumi.
Karyawa suka yi sannan suka haɗa kwanukan Hassu ta wanke masu bayan ta dawo kai wa baabaa Mero nata.

Ɗakinsu suka shige ko waccen su ta kwanta dan hutawa amma kowa da abunda take tunawa a ranta.
Innai da ta faɗa duniyar tunani hawaye ne ya gangaro a idonta wanda ke nuni da damuwan da take ciki, sai tace "Duk da kasancewana yarinya amma abun na damuna anya Inna ce ta haifeni anya ba tsintata suka yi ba suke ɓoye mun" sai kawai ta fashe da kukan da bata san ma ya qwace mata ba.
Hassu ta tashi tana cewa "Adda Innai ɗume?"
Innai cikin hawaye tace "Hassu jam, wala ko ɗume"
Itama hawayen ta fara tana magana cikin harshen fillanci "Adda Innai ki faɗamun bana son ganinki cikin damuwa in baki faɗa wa ƴar uwanki abinda ke damunki ba wa zaki faɗa wa?"
Cikin Kukan tace "Hassu ba zaki fahimta ba ko na faɗa miki, Hassu inajin kaman zan mutu bansan me nawa Inna ba bansan me yasa Inna bata qauna ta Inna bata sona kaman ba ita ta haifeni ba" ta faɗa tana hawaye
Haquri take bata itama tana kukan "Adda kiyi haquri Allah Inna na sonmu kinji" cewar Hassu tana rungume ƴar uwanta
Haka suka rungumi juna tana taya Addan nata kuka kai kace marayu ne ko kuwa mutuwa aka musu.

Baffai ne a ɗakin Inna bayan ya gama karyawa yace "tom A'ishatu yanzu ke me shawaranki akan makarantan Innai da nake son tayi gaba, dan gaskiya wannan al'ada ta aurar da yara da wuri ba ruwa na, ni ba wani al'adan da zan gwada wanda yake kaman jahilci ya sanya na cuci rayuwan yara na"
Shiru Inna tayi ba tace komai ba, Baffai cikin hasala da quresa da halin ta ke yi yace "wai ke A'ishatu me yasa kika zaɓi haka ne? Ko kaɗan baki son gaskiya na jima da fahimtan ki, wannan ƴar taki baki tunanin da qanqantan ta ciwon zuciya zai iya kashe miki ita، wannan kalan banzan al'adan naki zai sanya ki tafka babban asara tunda kina uwa amma zai sanya uwa ta gagara ceton rayuwar ɗiyarta sannan ta kasa mata abunda zai zama ci-gaba a gare ta har da ita uwar kanta tunda komi ɗa ya samu a rayuwa ba mai amfanuwa ko morar sa irin uwarsa barin ma dai ɗiya mace, A'ishatu yanzu ke baki tunanin Innai zata fara tunanin ba kece kika haifeta ba shiyasa kike mata haka? Yarinyar nan ki godewa Allah da yayo ta da haquri sannan ki kiyayi ranar qarewan haqurin ta ɗan aje-aje zata daina kallonki matsayin mahaifiya irin halayen da kike nuna matan nan" ita dai Inna kanta na gefe bata ce komai ba har yanzun.
tsaki Baffai yaja a hasale ya miqe ya fice a ɗakin dan in ya cigaba da zama zasu iya samun mastala.
Ɗakin magaji ya wuce, ganin Baffai sai Magaji ya tashi ya zauna yana cewa "Baffai da kanka ba ka qirani ba"
Baffai cikin murmushi yace "bakomi baban baffa, yanzu dai shawara nazo muyi game da yar uwanka, yanzu kaga sunyi wannan jarabawa wai na gama firamare(primary) to kana ga ya za'ayi ta wuce gaba ina tunanin zai fi ba"
Magaji yace "Baffai gaskiya ya kamata kam ta wuce gaban inya so sai a lallaɓa baabaa ta ajiye batun aure a gefe tunda ko saurayi bata da shi, kuma sai dai a nemi na zuwa a dawo dan makarantan kwanan nan sai a hankali".

Baffai yace"amma Magaji samun abun hawan da zai ke kai ta ya dawo da ita ba matsala ba"
Magaji yace "babu matsalan komai Inshà Allah Baffai, kawai a nema mata wanda zai ke kai ta yana dawo da ita nasan za'a samu ko

Please Login or Register in order to submit comment