Crave and Indulge mai gullisuwan en gayuđ Indai magana ake ta gullisuwa, tuwon madara, tsami gaye, kwakumeti, Ridi, da halaka kobo,garin danwake da yaji! toh ba Irin ta a Nigeria. Zaku iya order ma kan ku, yaran ku, loved ones dinku har ma kuyi ma âyan uwa da abokan arziki souvenirđ Ga tsafta ga dadi kumaâ
zaku iya tuntuban su a shafin su na instagrams @crave_n_indulge ko kuma ku musu magana ta WhatsApp https://wa.me/message/SAFXLSMA7TI6L1
33
Duk tafiya akayi yarage daga ita sai Mama afalon dake kallon yanda take kuka, kaman taje ta lallasheta but itama at this point she support Babanta 100 percent, yayi maganin Hadiza, ya gyarata, kuma she trust Baba Hadiza zata ladabtu, kuma zata bada nata gudunmawan ma agayarata, tashi tayi tawuce corridor dakin dake kusada nata tabude daganan tace âtaho ki shiga dakinki kiyi wanka ki chanza kayan jikinki kiyi sallaâ ahankali Hadiza ta tashi ta taho sai kallon fuskan Mama take data hade giran sama da kasa so kawai take Mama ta lallasheta but Mama nosend hatta shige dakin dake da yar katifa yar daidai akasa dawata yar fanka asama babu AC babu POP normal silin ne asama, sai akwatinan kayan ta kakap wanda Nura ya aiko dasu duk suna dakin nan aka ijiye, shiga ciki tayi Mama tasaki labulen ta wuce taje ya debo mata abinci da ruwa da kanta tazo ta kawo dakin, ganinta azaune yasa ta daka mata tsawa. âMy friend stand up kije kiyi wanka nace!â Kallon Mama Hadiza tayi saitaga kaman ba Mama dake nan nan da itaba, jiki asake ta tashi taje bayi tai wanka Mama na tsaye akanta ta shirya tai salla tasa taci abincin dole taci kusan rabin tuwon sanan tawuce tafita da plate din tadawo daki ta kwanta tayi shiru tana kallon fankan dake kadawa asama yana kara dake damun brain dinta sai kawai taji hawaye yafito daga idanunta saita tashi ta zauna ta zubama akwatinan ta ido tana kallonsu sai kawai taji hawaye yakara fito mata a fuzar da iska komi da Zeenah tamata na dawo mata fresh yanzu da gaske Nuri is done with her tunda har yana dawo da komi nata gida wani kuka yazo mata tayishi ta gode Allah tai bacci.
3 dot taji ana kiran sunanta. âKhadija Khadijahâ Adan firgice tabude idanunta jin muryan Baba yana tsaye gaban dakin batare daya shigo cikiba yace âKhadijaâ dasauri tace ânaâam Babaâ strictly yace âdauro alwala kifito falo ina jirankiâ ahankali tace âtomâ tashi tayi tana tangadin bacci tashiga bandaki ta dauro alwala ta dauko hijabi tafito falo Baba kadai tagani ya tsareta da idanu dasauri tasauke kanta kasa dadduma biyu ya shimfida afalon daya agaba daya abaya yace âhau dadduma muyi qiyamun lailiâ Gyadama Baba kai tayi yatada salla yafara karanto Al qurâani kiraâan Baba dadi sai kawai Hadiza taji abun ya tsuma mata zuciya, yaune rana na farko dataji aranta lallai fa tabar Allah for a long time cus bazata iya tuna the last time ta karanta Al Qurâani ba wlh, sai kawai taji hawaye ya gangaro mata feeling fragile, Baba bai wani ja sallan da tsayi ba sabida ita, 5 rakaâa sukayi yajuyo ya kalleta anatse ya daga hannu yace âidan bawa na cikin kunci, damuwa da fitinun jarabawa, bawa dan uwansa bazai iya magance masa matsalolinsa ba Khadija, ni ko mahaifiyar ki bazamu iya magance miki duk abinda ke damunki ba Allah kadaine zai magance miki kome kikeji, shine Ubangiji mai tsarki da daukaka, mai kuma mulki, Al Awwalu, Al Akhiru Al Zahiru Al Badin kuma, duk daren duniya Allah kan sauko dakansa ya amsa bukatun bayinsa, dan haka daga hannunki sama ki gayama Allah bukatun ki kakap, sannan ki rokeshi gafara bisa laifuffukan dakikamai, ki rokeshi haske da dacewa akan rayuwa babu abinda yafi karfin Allah, so kaima Allah kukan ki Khadijaâ Gyadamai Baba kai Hadiza tayi kuka na zuwanmata ta hannunta sama ahankali abin namata kaman ba itaba she canât remember the last time datai salla haka ta roki Allah for anything, sheâs feeling guilty kan tayi neglecting bautama Allah, sai kawai tafashe da kuka tace âAllah na tuba! Allah na tuba!â Sai kuka hakan yasa ahankali Baba ya juya yayi facing gabanshi, Hadiza tai kuka zuciyanta ya sosu sheâs feeling kaman ma she donât deserve rahaman Allah cus tamai laifi da dama, da kyar ta iya controlling kukan tafara adduâa azuciyanta, the first abu daya fito daga zuciyanta is Nura tanson aurenta da Nura tanason ya maidata, tanason mijinta, kawai saita shiga share hawaye, sosai tai adduâa saitaji wani imani da natsuwa na shiganta da tadade bataji ba, anan bacci yayi gaba da ita ta kwanta kan dadduman Baba tajuyo yakalleta yayi shiru idan yace bai damu da damuwa ta ba yayi karya, saisa ya kudirci anniyan zai gyarata yana kuma rokon Allah ya taimakamai yabashi iko dan idan Allah bai nufeta da shirya ba kome zaiyi abanza bazata shiryu ba, adduâoi yacigaba dayı har aka kira asuba sannan yatadata yace âtaje tayo alwala tai sallan asubaâ shikuma yawuce mosque.
Hadiza tadauka Baba wasa yake yana dawowa daga sallan asuba wanda bai dadeba dan normally sai gari yawaye yake dawowa gida but yau ana idar da salla yayi azkar yafito yadawo gida yakirata fitowa tayi ga mamaki ta ganin Baba tayi da bagadadi da gaske saikace yarinya shima Baba yasan duk tsiya ai ta iya alifun, baâun, Al Qurâani suka farayi from fathiha yana karantawa tana repeating after him, suna gamawa sukai alifun har karshe zuwa alifun bil fatha yana koya mata baki dalla dalla, daganan sukai tauhidi Man Rabbuka, Hadiza jitayi zatai kuka abu ya tsayamata awuya ganin yanda Baba ke koyarda ita abubuwan da yasan ta iya, ko su Aman dinta a islamiyyan su sun wuce abubuwan nan amman ya maidata yarinya, lekowa Mama tayi tagansu tadauke kai abinta takoma daki tana samin natsuwa ganin Baba yarike wuta.
7:30 suka gama Baba yace âtashi kije ki daura abincin kari kiyi gyaran gida, tambayo Mamanki me zaâa dafaâ gyadama Baba kai tayi tawuce ciki ahankali tace âMama ina kwanaâ batare da Mama ta kalleta ba tace âlafiya lauâ murya chan kasa tace âme zaâa dafa Mama?â Dan kallonta Mama tayi tace âki surfa wake rabin tiya, saiki debi kadan ayi kosai, ki dama kamu asha dashi, ragowan kiyi alalen rana na gwangwani, injin nikanmu na backyard banason alalen nikan blender, buhun gawayi na kitchen ki hura wutaâ ahankali Hadiza na kallon Mama kirjinta na bugawa tace âba gas Mamaâ? Wani kallo Mama tamata tace âakwai amman jiya Baban ki yasayo gawayi buhu daya yace dashi zaâa dinga girki yanzuâ hawaye Hadiza taji sunciko idanunta tarikesu dasauri tace âMama ban iya hura gawayi ba, shima wake ban iya surfawâŠâŠâ dakuwan da Mama tamata yasa takasa karasa maganan, Mama da haushinta ke cikinta fall sabida yanda takaso auren gidan arziki yaro mai kudi tadawo mata gida tawani zabura tace âwlh kikkipa miki mari zanyi Hadiza kinci kaniyanki, are you stupid dazaki cemin baki iya surfen wake ko iya hura gwayi ba kin dauka nan Abuja ne? Dan mai garinku kafin kiyi aure ba da itace kuke girki agidan nan ba lokacin akwai gas ne? Sau nawa kika dafa alale agidan nan ki surfa waken kiyi komi? Hadiza kalleni nan wake up! Ki gaggauta tashi daga baccin dakike ubanki ba kowa bane haka ma ni uwarki, Babanki Malamin makaranta ne nikuma housewife ahaka muka raineku kuka taso, auren Nura shine ya jiyardake dadin rayuwa kikadan menene rayuwa adukiya, yanzu kuma kin kaso auren gidan ubanki kike look at everywhereâ Mama ta nuna dakin da yatsu tace âbude idanunki da kyau ki kalla nan ba gidan Nura bane gidan mahaifinki ne Hadiza, ki gane banbancin so my dear bace min daga nan kije ki daura abincin safeâ tashi Hadiza tayi ahankali tawuce tafito idanunta har zafi zafi suke mata tsabagen rashin jin dadin rayuwanta, tsakar gidan tafito zuwa kitchen dinsu ta tasaya tana kallon komi ga buhun gawayi ga murhun gawayin, ga tukwane, yanzu itane zatai aiki a kitchen din nan? Tasan tayi aiki aciki da but ta manta? Sheâs not use to old life nata again, ijiyan zuciya tasauke tasa hannunta tadauki kaskon wutan ta ijiye waje daya, tabude buhun gawayin, tadaga fararen soft hannunta dakeshan manicure ta kalla, kuka tafashe da shi ahankali tace âna shiga uku na lalaceâ goge fuskanta tayi da sauri kafin ahankali tasa hannun cikin buhun ta debo gawayin ta zuba a murhun, ledojin datagani da kyallen dinki na hada kasko tadeba ta zuba tana mamakin yanda take tuna yanda ake hura wutan yanzu, bataga kalanzir ba saitadau ashana ta kunna akai makamashin suka kama hakan yasa tafito tawuce flat nasu ta auno wake 8 cup tafito tadeba ruwa ta jika tadauki turmi ta bude tadauki tabarya ta kwashe wajen ta zuba tafara daka ahankali kirjinta namata badadi ko kadan.
Kafin kaceme hannunta sun sassage from surfen sakin tabaryan tayi ta zauna akasan simentin wajen jitake kaman zata sume ta jinginar da kanta a bango tana maida ijiyan zuciya tana yarfe hannunta, hayaki taga yana fitowa sosai daga kitchen din hakan yasa ta dafa bango da kyar ta mike tsaye ta wuce kitchen din, makamashin sun cinye gawayin bai kama ba sai hayaki suke, tari tafara sosai tafito daga kitchen din tawuce takoma daki tasami Mama afalo tana waya tace âMama charcoal din yaki kamawaâ batare da Mama tai magana ba dan waya take ta rarumi throw pillow kan kujera zata jefa mata da sauri Hadiza tafice takoma kitchen din ranta ba dadi.
Mafici tadauka tashiga hurawa but still yaki kamawa fitowa tayi tawuce daki wajen Mama again data bita da kallo ganin tai buzu buzu duk toka toka akanta, ahankali Hadiza ganin Mama tagama wayan tace âMama yaki kamawa wlh nayi nayi, gawayin baida kyau zoki duba dan Allahâ wani matsiyacin kallo Mama tamata tace âBaban ki ya shigo gidan nan baki gama ba wlh zaki gamu dashiâ juyawa Hadiza tayi takoma kitchen ta duka tasake deban makamashi tasa yagamaci still yaki kamawa kawai saita fashe da kuka sheâs so fuatrated kaman taita zuba ihu takeji da kyar akaro na uku yakama tadaura tukunyan ruwa tafito tazo ta kwashe waken data surfa daga turmi taje gaban pampo tazo ta wanke da su attarugu da albasa taje chan backyard ta tsaya tana kallon injin din da ake mishi tadawan generator.
She used the injin before dan su basakai nika waje but yanzu batasan tayaya zatayi ba, ijiye bowl na surfen waken tayi tazo gaban injin din ta tattaba, sannan takama handle na igiyan ijiyan zuciya tasauke sau uku na gathering strength kafin ta fuza da karfinta wani tangal tangal tayi zata fadi ta dafe bango injin din yayi kuka. âTututututututuuuuuuuâ ya mutu bai kunnu ba, sake zuwa Hadiza tayi tasake fizgan igiyan wanan karan saida ta fadi duwawunta ya bugi kasa tace âwayyooo Allah naâ lekowa wajen Mama tayi ganinta akasa tsaki taja kafin taje tajima kanta ciwo bari ta tayata tada injin din just for today, ja daya Mama tayi injin din yatashi takalli Hadiza tace âtashi ki wanke injin din kiyi nikanâ da kyar Hadiza ta tashi Mama tawuce kitchen din dan ganin haukan datake, ganin ta hura wutan harma ruwan na shirin tafasa yasa tai murmushi tawuce takoma daki.
Da kyar tayi nikan ta kashe injin din takoma cikin gida, tana zuwa ruwan ya tafasa ta dama kamu tadaura mai awuta ta debi kullin kosai tana bugawa sai zufa take tasa gishiri da magi guda da albasa data yayyanka albasan shima saida yasata kuka sabida yaji, wlh zaku iya mata kuka kuka ganta a kitchen din nan, hannunta duk bakin gawayi harda fuska nan, tasoya kosen ta kwashe akula tafito daidai Baba da Baffa Amadu na shigowa har ranshi Baba yaji dadin yanda she manage tai girkin dan bai zacima zata iyaba that means yanada hope zata gyaru duk fitowa sukayi zasuyi kari zata tashi takoma kitchen Baba yace âina zakiâ? Ahankali tace âzanje nasa alalen a wuta neâ wuri ya nuna mata yace âzauna kiyi karin kumalo kemaâ zama tayi duk sukai kari ba laifi kosan yayi dadi wlh sosai, tafa iya girki dama kawai iskanci ne ke hanata yi, tass aka cinye ta kwashe komi tafito dashi takai pampo taje kitchen ta dauki buhun gwangwani tabude takai makawarara ta wanko tazo tahada tasa alalen ta zuzzuba a gwangwani ta jera a pot tasa a wuta sannan takoma tai wanke wanke tashiga share tsakar gidan tana gamawa tashigo falon su ta gyara har zuwa dakinta sai nishi take kaman mai asma, komawa kitchen tayi alalen ya nuna tadaura ruwan zafi dazatai wanka dan babu water heather agidan nan, ruwan na tafasa tajuye a bucket ta sirka ta tafi bayinta tadade aciki dan gashi tama jikinta lafiyayye tagaji, tafito tayi shafe shafenta tayi face routine nata ganin har tasoma samin wrinkles from this work datayi tasa kaya ta kwanta agado tana nishi barci kawai takeso tayi, harta runtse idanunta zatai bacci Mama ta kwala mata kira dasauri tabude idanunta daidai Mama na daga labulen dakin ta kalleta hannunta rikeda kayan wanki ta zudda akasa tace âkin wanke bayinka gidanâ? Girgiza matakai Hadiza tayi Mama tace âga kayan nan ki hada da naki da kika cire jiya dan baâa tara wanki agidan nan kije ki wanke kiyi amfani da ruwan kumfan ki wanke bayukan gidanâ duk yanda Hadiza taso tadaure saita kasa danta gaji ainun, fashewa tayyi da kuka tace âMama harda ke baki sona ko yanzu? Mama kasheni zakuyi da aiki? Wlh bayana ciwo, hannuna har bororo yayi sabida surfen danayi kalliâ tanunama Mama hannunta dahar yayi ja yayi bororo tace âMama nagaji, Mama wlh nagajiâ dudda ta balaâin bawa Mama tausayi amman ta daure tace âDan girkin dakikayi na bakinmu kadai bawai girkin tukunya lamba goma ba, da dan sharan tsakar gida da wanke wanke da gyaran falon nan dakikayi shine kika gaji? Bayanki na ciwo? Surfen wake gwangwani takwas bama tiya daya ba shine hannunki har yayi bororo? Lallai Hadiza kin sami duniya, kinsan akwai matan da kullum aduniya sai sun surfa kayan hantsi buhu buhu sabida su sami abin ciyar da bakinsu abinci? Kinsan matan dake zuwa aikatun suna share big big organizations din nan irinsu bank da hospital sannan su wanke bayukan suyi komi sabida su sami kudin ciyarda kansu da iyalansu? Hadiza kinsan menene rayuwa kuwa? Sabida kin dandana dadi? Hadiza kinsan the amount of work people are doing in this life just to survive? Kinsan akwai wayanda yasan kashin damukeyi ne aikinsu? Kinsan akwai wayanda gyaran kwatane aikinsu? Kinsan akwai yan aikin kwadago? Kika har sunyi doro tsabagen aiki? You are complaining sabida kin share falo, kin dafa abinci? To ba ciwo baya ba, ke bayan ya karye ma kinji, tashi ki karasa aikin ki, jeki wanka bayikan gidan nan ki hada kayan nan ki wanke su tass you lazy girl, u might be 33 but mu muka haifeki you must work this work, da kinsan bakison aikin dabaki kaso auren ki kin dawo mana gida ba, da baku nan aini ke komi dakaina da tsufana banda yar aiki, yanzu ko kin kaso aure kin dawo gida ai Alhamdulillah nima nahuta, you donât expect me to be entering kitchen gaki agida, kezaki komi Hadiza yanzu kika fara, bayan ya tsinke ma inyaga dama you will get use to it, tashi kona kira Babanki wlh ai yana wajennanâ tashi Hadiza tayi kawai tafashe da kuka tace âna shiga ukuâ Mama tace âtukunna saikin yabawa aya zakinta Hadiza donât think punishment ne wannan this is normal aikin gidan Babanki which You MUST DOâ cikin kuka sosai Hadiza tace âMama to nayi order washing machine da generator? Na yarda zan dinga wankin a washing machine, koba wuta saimu tada gen, Mama ni gas dinma zan iya sayo wani daban tunda bakuso ina girki da naku, please Mama dan Allah Mama basai Baba yasani ba kurufamin asiri Mama ki yarda wlh zanyi order yanzu nabiya kudi akawoâ wani kallo Mama tamata ganin har yanzu da sauranta Mama tace âHadiza dagani har Babanki are not interested in your money, kudinki is useless agidan nan, abinda Allah ya hore ma Babanki yasaya dashi zamuyi amfani, shikuma zamuci dan haka ko amarfi donât even dream of zaki sayo wani abu ki kawo cikin gidan nan, karki bari nadawo nasameki zaune adakin nanâ.
Kuna ganin idan Baba da Mama suka gyara mana Khadijatul Kubrah bazatama Ummi fincikau ba kuwađ€Ł
Tundaga Alifun Baâun fa aka fara mata.
Akwai wani magana da manya keyi na cewa no matter inda kasami kanka arayuwa always remember where you are from đ
đ«MATAN?? Ko MAZAN??đ«
âđ»M SHAKUR
EPISODE 3ïžâŁ4ïžâŁ
Lokacin sabunta BUDURCI yayiâŠLokacin sake HONEYMOON yayiâŠLokacin dawo da martabar SOYAYYARKI da maigida yayi Shi lokacin AMARCI yafi ko wani lokaci dadi a rayuwar aureâŠshiyasa yau NASARA NERA ke gabatar muku da SABON package dinmu wato VIRGIN AGAIN VIRGIN AGAIN package ne na musamman ga duk wacce kaddara ta gifta ta rasa BUDIRCINTA Wannan package ya kâunshi đ„Powder đ„Steaming herbs đ„Gel đ„liquid Me kike jira??? idan ma aure zai kâara kina da damar kasancewa daidai da amarya, idan kuma haihuwa kikayi zaki iya daidaita kanki kafin resumption, in kuma bazawara ce kin samu damar tashin kan angođ„đ„ Me kuke jira??? Virgin Again wato sabon budurci munyi shi ne don min matan aure dage fama da matse war gaba ,kaman matan da suka haihu,ko kuma matan da Allah ya hada da kaddarar fyade. Bayan matsi da ya keyi yana maganin Infection.
07064487800
https://chat.whatsapp.com/IPh3BxIWPT6D9QsS49DkfB
Our FLAT TUMMY PACKAGE is made with ingredients such as honey, sip and lipton and results is achieved within a maximum of 50days âŠYes its no magic, not 5days âŠ50days of FLAT TUMMY JOURNEYâŠ.would you like to join the flast tummy gang?
Send us a DM NOW!!!
34
Bayan Wata Daya.
Tafiya tai tafiya rayuwa taja, tunda Hadiza tazo gidan Baba wannan routine din nan Baba yake bitamata kullum yaumin, babu randa bazasuyi karatu ba, kowani abu kotanaso kobataso bata isa tace bazataci ba, zaman gidansu yasa taga life from a different angle cus Baba technically shows her kudinta is trash a inda yake dan bai mata amfanin komiba, at the same time itama tai regretting so many things, cus zata iya cewa business dinta da jikinta dasu Amali kawai take kashema kudin, chanza mota, siyoma yaranta designers outfit na yara she neglected gidansu, bawai sabida rowa tai neglecting ba but sabida taga Nuri namusu komi, sai yanzu data shigo gidan tai zaman gidan saitakeji inama ita ta buge gidan gabaki daya an chanza gini, ta zuba air conditions da sauransu dudda tasan ba lallai Baba ya yarda ba, then she remembered ko kafin Baba ya yarda da motan da Nuri yasayomai saida aka kai ruwa rana but dudda haka maybe da Baba yafi zama comfortable da cin kudinta than na mijinta and funny enough ko Mama or Baba basu taba rokonta wani abubu, so taga rayuwa outside abinda tayi and she must say she has not been a good daughter to them wlh nor a good mom to yaranta, abubuwa alot made her to reflect back and ask kanta what is wrong with me?? Inata rayuwane all this while kaman tinkiya, infact I have no right to blame Ummi sabida yarana na sonta wlh wlh nine nasa suka sota sama dani mahaifiyarsu gashi yau wata daya kodan kewanta basuyiba balle suce akirata suyi magana da ita,abun yadameta matuka.
Ko kofar gida bataje ba tun bayan tashigo gidan nan ta iPad nata take monitor business nata da daddare dan bata samu ta zauna kota huta through out da rana, tunanin Nura da yaranta ya addabi zuciyanta takira Nura amman number shi baya shiga, WhatsApp taga yayi blocking nata, IG ma dan business page nashi na real estate business nashi a IG taje ta duba she canât find d page shima yayi blocking, batada any means na ganin yaranta, kowa na gidan ya tauysaya mata but tasasu in a position da kowa kunyan kiran Nura yake sabida abinda ta aikata, but balaâin tausayinta suke barinma ranan data basu labarin abinda Zeenah tamata inda Mama tace yamata daidai it serves her right amman fa sun tausaya mata kuma ba Mama kadaiba hatta Baba duk suna mata adduâa kan Allah yasa Nura ya komar da ita kafin tagama Idda dan Nura mutum ne da kowa zaiyi shaâawan auren shi da diyarsa, gashi tana masifan kewan yaranta, for the first time in her life saitaji tai nadaman yanda yan uwan mijinta da mahaifiyarsu bata shiru dasu da nan nan ko Meena saita kira zata samu tai waya da yaranta abin ya taba mata rai sosai, ta wajigu kuma tagane ta tafka shirme karatun da Baba ke kara mata yakara samata tsoron Allah da tsantsan nadama aranta kullum sallan darenta saitayi adduâa kan Nura yakomar da ita dakinta, aurenta da rufin asirinta dan duk business da kudi is all trash idan ba namiji.
Yauma kaman kullum ta tashi tayi duka abubuwan datakeyi ta daura ruwa awuta taji da kanta da cikinta na ciwo wanda tun jiya da daddare taji hakan amman datai bacci ta tashi bata karaji ba sai kuma yanzu datake kitchen din nan.
Iza ruwan tayi tamike tsaye ahankali saitaji maranta ya rike sosai mamaki tayi period zatayi ne to ko shine ai bata ciwon mara haka, daurewa tayi tana dafa bango ta lallaba tafito daga kitchen din tana fitowa kaman ance oya kara tafiya mugani kawai kafanta ya rike tana ganin jiri d next thing kawai ta zube awajen daidai Baba da Amadu na shigowa gidan tana landing akasa akan idanunsu, Baba yace âSubhanallahi Khadijaâ da gudu yayi wajen ya tallabo kanta tana bude idanunta kadan kadan tana kallon su, Baba Amadu ne yafara ganin jinin dakebin kafanta dasauri yace âYaya kalliâ dasauri Baba yakalli kafanta yace âSubhanallahi, je tada motaâ daidai Mama nafitowa jin hayaniya ganin Hadiza zube akasa ga jini a kafanta yasa dagudu tazo wajen hankalinta tashe abinku da uwa Baba yace âHadiza nada ciki ne?â Arude Mama tace âciki?! Ciki kuma, Wlh bantaba sani ba, ko miyar bata taba tofarwa ba, balle zazzabi ko amai, banganta ma da alaman mai ciki ba kwata kwata, bari na dauko hijabiâ wucewa tayi aguje ta dauko hijabi akasa Hadiza amota Amadu yarufo gidan sai asibiti wani madaidaicin private asibiti Baba yakaita daidai kudinshi ba irin na yan gayun nan ba, karbanta akayi akai ciki chan Dr yafito ya nuna Amadu yace âkaine mijintaâ? Dasauri ya kalli Baba yace âaâa lafiya meya faruâ? Dasauri yace âina mijinta yake?â Anatse Baba yace âlikita meya sami diyata nine mahaifinta? Meya faru take bleedingâ? Cikeda damuwa likita yace âBaba koâina mijinta yake just call him yazo maza maza, bari nakoma ciki, ya iso kwaji ko meneneâ yawuce yakoma ciki, Mama da hankalinta inyay dubu yatashi tace âkira Nuran Malam, Allah ubangiji yasa yana kanoâ dan Jim Baba yayi saiya wuce yafita waje yaciro number Nura yayi dialing.
Cikin wani bacci mai shegen dadi sun gama watsewansu da Ummi yaji wayanshi na ringing hakan yasa da kyar ya iya yabude idanunshi, jaye Ummi yayi daga jikinshi ahankali yasa hannunshi yadauki wayan ganin Father Inlaw saida yayi dan jim har wayan ya katse bai dauka ba sannan yayi dialing number back cikeda girmamawa yace âAssalamu Alaykum Babaâ dan ijiyan zuciya Baba yasauke yace âNura ya gaji?â Ahankali Nura yace âAlhamdulillah Babaâ anatse Baba yace âgamu a asibitin sangu yanzun nan muka shigo, kawai Hadiza ta sume gaban kitchen saiga jini ya balle mataâ dasauri Nura ya yunkura ya tashi daga bakin gadon dayake zaune, anatse Baba yace âsunki gayamana komi Likita yace lallai lallai saina kira mijinta, ana nemanka saisa nakiraka dudda nasan kana Abuja maybe saina yasaka da Likitan awaya koâ?
Anatse Nura yace âina kano Baba gani nan zuwaâ ahankali Baba yasauke ijiyan zuciya feeling calm jin yana kano yace âtohâ ijiye wayan Nura yayi yakalli Ummi dake bacci dukowa yayi yaja bargo ya rufanata yana kallon kirjinta da kullum kara girma suke yarasa dalili maybe
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 28 Chapter of 51