Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kamar bazata yi maganaba sannan tace patients sufara shigowa, nan suka fara shigowa daya bayan daya, Ta dauki tsawon lokaci tana duba yara marassa lafiya har ta kammala sannan ta tashi ta fita zuwa dakin yara wato (round) nan dinma ta dan dade domin har kusan karfe 1 saura sannan tafito ta koma office dinta, Dr Naz tagani zaune acikin office din da laptop dinshi dore akan cinyarshi yana daddannawa,zama tayi akusa dashi tana yatsina fuska, "Wash..." Tafada ahankali tana mai jingina kanta ajikin kujera, "Meya faru?" Ya tambayeta yana faman kashe mata ido, "Kafata tagaji ne" tabashi amsa, sunkuyawa yayi yafara cire mata cover shoe din dake sanye cikin kafarta, idan da sabo yasaba ganin wannan sarkar datake daurawa a kafarta da zoben da take sakawa sai dai shi sam bai taba damuwa da sai yasan dalilin da yasata take sakawa ba, "Dole kafarki tayi ciwo irin wannan dogon takalmi haka anty maryama.." Yafada cikin tsokana yana dagowa daga sunkuyon da yayi bayan ya kammala cire mata takalman, Murmushi tayi tana kallonsa saboda duk lokacin da yaso zolayarta to da anty yake kiranta, "Taimaka ka danna min bell Joseph yazo" tafada tana gyara zamanta akan doguwar kujerar, "Angama ranki ya dade" Kan tabur dinta yaje ya danna kararrawa ko zama baiyiba Joseph ya shigo, "Dauko min lunch box dina da flat shoe dina" tace da Joseph, Daukowa yayi ya dora akan center table din dake gabanta ya ajiye ya fita, Bude flask din tayi ta dauki fork tafara cin chips da kwai din da kuku ya soya mata, "Dr ga abinci.." Karbar spoon din hannunta dr naz yayi suka fara ci tare suna kama kama,cup ta dauka ta tsiyayo masa tea ta mika masa ya karba yafara sha ita kuma tana kurbar na cikin dan karamin tea flask din ta yar karamar kofar dake jikin murfin, "Yau naso in turo miki wata mata ki duba min ita saboda ni taki yarda in dubata wai kunya takeji" Dr naz yafada yana kallonta, tabe baki tayi ta mike domin dama lokaci zuwa lokaci yana turo mata patients dinsa ta duba masa su musamman ma yanmata kasancewar shi likitan mata ne, Fridge ta nufa ta dauko coke roba daya mai sanyi ta dawo ta zauna, Rike robar coke din dr naz yayi yana kallonta, "Haba dr kamar baki san ba aso ahada ruwan sanyi da na zafi a lokaci guda ba? Kefa dr ce" Yamutsa fuska tayi ta kalleshi, "Dan Allah kabarni nasha idan bansha ba ai jina zanyi kamar marar lafiya" "Kindai saba ne kawai" Yace da ita tareda sakin robar yana kallonta, Laptop dinshi ta dauka ta fara neman film din da zata kunna daga karshe ta kunna wani mai suna _behind enemies line_,tareda dr naz suka zauna suna kallon film din har yamma tayi, tanata zaune tana jiran shaddad yazo taji shiru tsaki taja ta duba agogon dake daure a tsintsiyar hannunta, har karfe 5:30 bai zoba sai 6 saura sannan yazo, shikuwa shaddad yama manta da maganar wai zai dauko maryama daga office har sai da ya dawo daga headquarter dinsu sannan ya tuna,garage din gidansu maryaman yaje ya fito da motarta kirar KIA new model,kalarta ash colour, Tana cikin office azaune ta cika tayi fam sai ga Joseph yashigo yace ta fito anzo daukarta, hada mata kayanta yayi ya fita, sai da ta gama bata lokacin ta son ranta sannan tafita ta na aikin yatsina fuska, Yana zaune da farar riga mai gajeren hannu da wandon sojoji ya kunna radio yana sauraren wani programme na ban dariya,tafito kenan sai ga dr naz shima yana fitowa zai wuce zuwa theatre, kallonta yayi yana karasawa kusa da ita, "Sai yanzu?" Yafada cikin tsokana, "Wallahi tun dazu nake jiran driver amma wai bai zoba sai yanzu" "Hakuri zakiyi maryama sarauniya.." Yafada yana kokarin gyara mata barimar gold din dake kan hancinta saboda yaga ta dan zamo kamar zata fadi, duk abinda ke faruwa akan idon shaddad ne dama tuni zuciyarsa tafara zargin cewar maryama tana bin maza ko kuma tana lesbian,wucewa tayi bayan dr naz ya gama gyara mata barimar wacce ta kasance mai kirar star sai walwali take, Bude gaban motar tayi ta shiga ta zauna batare data kalleshi ba, shima tun kallon farko da yayi mata lokacin da zata shigo bai sake kallonta ba, Shi Kadai yake murmushi yana driving saboda abin dariyar da yakeji, hannu maryama tasa ta kashe radion saboda har kanta yafara ciwo, sam bata son radio domin bata kaunar hayaniya a lamuranta, Sake kunnawa yayi ta sake kashewa domin aganinta wannan ma ai rainin wayone, ita da motarta har ya tsaya yana yimata abinda yake so, "Kai Malam bafa motarka bace tawace so baka da hujjar da zaka takura min..." Tafada akufule domin dama can ranta abace yake sai gashi kuma yasake kunnota, "Tabbas nasan ba mota ta bace amma ya zama tilas nayi abinda nakeso da ita ahalin yanzu tunda a hannuna take.." Tsaki taja ta juyar da kanta tana jin haushin sa saboda ya takurawa rayuwarta da yawa, "Karki sake yimin tsaki dan ba ayimin tsaki kin gane? So respect your self..." Rabuwa tayi dashi ta zaro iPhone dinta daga cikin hanbag dinta ta jona earpiece tasaka acikin kunnuwanta ta toshe, tana jinsa yasake kunna radion, Sai da tabari sun kusa zuwa barikinsu sannan ta sake bata fuska tace, "Namanta ina son shiga kasuwa zan yi siyayya.." K'uluwa shaddad yayi saboda wannan rainin hankalin nata yayi yawa, yarinyar da batafi sa'ar kanwarshi ba itace zata rinka kokarin dole sai ta juyashi kamar wani waina acikin tanda, "Hello father, ina son zuwa kasuwa, ka fadawa driver ya kaini" Yajiyota tana magana da alama mahaifinta ta kira, Tun kafin Dada ya kirashi yayi ribos ya juya ya nufi yoroba market domin itace tafi kusa dasu,kiran mahaifinta ne ya shigo cikin wayar shaddad, Yana dauka yaji yafara rokonsa akan ya yi hakuri yakai maryama kasuwa,amsawa yayi da cewar ai sunma kusa zuwa kasuwar, katse wayar yayi ya mayar da ita cikin aljihun wandonshi, "Bana zuwa wannan kasuwar domin abinda nake nema ba asayarwa anan.." Tafada fuskarta atamke ranta ahade, "Ke ni ba sa'anki bane kuma ba drivern ki bane, kar ki rainamin hankali" yace da ita cikin zafin rai, Fusgar motar yayi suka koma baya ya nufi wata kasuwar daban ransa abace, Handbag dinta ta balle ta ciro wani chewing gum kato ta bare ta jefa cikin bakinta tafara tauna ahankali babu abinda kakeji sai k'as k'as, Agefen titi yaja yayi packing saboda babu hanyar da mota zata shiga, bude motar tayi ta fita tana rike da handbag dinta earpiece makale a kunnenta, farin medical glass dinta ta ciro tasaka duk yana kallonta ta glass, sai taunar chewing gum take tana yin k'wai sai kuma ta fasashi tush taci gaba da taunar chewing gum din, titi ta tsallaka tana rike da high waist dinta data dage gudun kada ta kwashi datti dan haka duk k'waurinta awaje suke ga wani dogon takalmi dake kafarta amma kasancewar tasaba tafiya dashi takunta take yanda take so.... *_Ummi Shatu_*👌🏻 *_MARYAMA SARAUNIYA..!!_* *_NA_* *_UMMI A'ISHA_* _Dedicated to Maryam Qaumi_💕 _*9*_ aishaummi.blogspot.com ~~~~D'an karamin tsaki shaddad yayi lokacin da yaga shigewarta cikin kasuwar, "Yarinya kamar karuwa, komai nata irin na yan tasha, in banda tsabar duniyanci menene nata na shiga kasuwa tana taunar chewing gum?" Yayi wannan maganar acikin zuciyarshi, Tunda ta shiga kasuwar bata fitoba sai da ta shafe fiyeda mintuna 20,duk yagama kosawa da jiranta sai faman tsaki yake yana bin hanyar da kallo domin ganin kota taho sai yaga shiru, yana nan zaune ya hangota ta fito tana ta faman taunar chewing gum dinta tana yin k'wai amma taunar chewing gum dinma cikin yanga da kinibibi take yi,k'ura mata ido yayi yanda take tafiya tamkar bazata taka k'asa ba saboda tsananin yanga, gashin kanta duk awaje kasancewar mayafin data yafa akanta bai gama isarshi ba, D'auke idonshi yayi daga kanta aranshi yana jaddada tabbas mace mai kyau fitinace a duniya, yanzu kamar maryama yanda take da wannan tsananin kyau din da rashin kamun kai ai Allah ne kadai yasan yawan adadin mazan dake kwadayin kasancewa da ita, Bude gaban motar tayi ta shiga ta zauna ta rufe tana mai cigaba da taunar chewing gum dinta, kallon ledar dake hannunta shaddad yayi saboda yana son ganin abinda ta siyo wanda har ta dade haka, sugar cane yagani acikin ledar an daddatsashi, mamakine da haushi suka kamashi saboda ganin yanda ta b'ata masa lokaci ta zaunar dashi gashi har lokaci ya kure yasan bazai samu salla a jam'i ba domin kafin su koma har an idar, Cikin bacin rai ya yiwa motar key yahau titi, ita kuwa sarauniyar sai aikin latsa iPhone dinta take tana taunar chewing gum, chaten take da dr naz wanda har yanzu yana asibiti bai tasoba amma yace yau zai zo hira wurinta, Har suka shiga barek din shaddad bai ko kalleta ba domin haushi take bashi tunda yazo garin nan bai taba rasa salla a jam'i ba sai yau ta dalilinta, Bude murfin motar tayi zata fita, juyowa tayi ta kalleshi, "Kajira blessing tazo ta daukar min kayana sai kaje kasaka motar cikin garage.." Sake harzuka yayi ya kashe motar ya fito ya rufeta yace da ita, "Ungo key dinki.." Bai jira amsarta ba ya wulla mata mukullin yayi gaba ranshi abace,kallo tabishi dashi ganin komai nasa yana yinsane cikin zafi zafi da zafin nama, Bata damuba tawuce ciki tana yatsina fuska, Blessing ce ta sauko da sauri tana rikeda duster a hannunta wacce ta kammala goge glasses din dake jikin window din dakin maryaman, "Karbi key dinnan kije cikin motata ki dauko min kayana, akwai sugar cane idan kin kawo kisa minshi cikin fridge" abinda tafada kenan ta wuce sama, tana zuwa ta shiga wanka duk ranta abace yake saboda gadarar da shaddad yake nuna mata gamida wulakancin da yake son rinka yimata ako yaushe, Ruwa ta sakarwa kanta tayi wanka mai kyau tafito, wasu kananan kaya ta tarar blessing tafito mata dashi,farar riga yar karama body hug da farin wando three quarter, pant kadai tasaka ta zira kayan tafesa turare ta fita bayan ta saka silifas dinta, Fridge taje ta buda ta ciro robar coke guda daya ta nufi bedroom dinta, drewar din jikin gadonta ta bude ta ciro takardar wasu kwayoyi ta debi guda biyu ta jefa cikin coke din sannan ta sauka kasa da robar coke din a hannunta tana sha, kan dining taje ta zauna domin ganin abinda kuku ya girka musu yau, white rice & stew tagani sai ko hadadden salad da aka hada agefe sannan ga dafaffen kwai nan agefe, shinkafar ta dan diba spoon uku tasaka miya amma ta zuba salad din da yawa sai dafaffen kwai data saka guda biyu, fara ci tayi sai dai kuma dakyar ta iya cinyewa abincin data hada, Coke dinta ta shanye ta tashi takoma sama ta kwanta sai a lokacin ma ta tuna da cewar ashefa batayi sallar azahar ba bare la'asar kuma gashi yanzu har ankusa yin isha, kwanciyarta tayi ta mike ta lumshe idanunta. Tunda ta kwanta ta dan samu bacci ba ita ta tashiba sai karfe 8,dan siririn gyale ta dauka irin wanda tasaba yafawa tafita zuwa falon Dada, Zaune ta sameshi kafarshi dore kan wani tumtum saboda ciwon kafar dake damunshi, "Sannu dada, ciwon kafarne?" Tafada tana karasawa inda yake, "Yawwa sannu mai sunan mama..." Dada ya amsa mata yana kallonta, Agigice ta zauna akusa dashi tana kallonsa saboda yanada ciwon sugar sannan wannan ciwon kafar ma yadade yana fama dashi, itama kusan tayi gadon ciwon saboda tana fama dashi lokaci zuwa lokaci, "Dada kodai sugar dinka ya hau ne?" "A'a daughter lafiya lau fa nake" Tashi tayi ta nufi dakinsa domin dauko na'urar gwaji wadda ta tanada musamman domin gwada mahaifin nata, Tana fitowa taganshi zaune shida shaddad yana duba wasu takardu, Agaban dada taje ta zauna ta ciro na'urar ta fara gwadashi, ajiyar zuciya ta sauke ganin sugar din bai hauba hakama jininsa shima bai hauba kawai dai ciwon kafarne ya tashi, Mikewa tayi taje ta mayar da na'urar sannan ta dauko masa maganin da yake shafawa a kafarshi ta dawo falon ta zauna ta bude maganin tafara shafa masa a kafafunshi, shaddad yana kallonta ko kunyar fitowa ahaka bata ji, Cigaba da Shafa maganin tayi tana ma mahaifinta magana ahankali, "Father tunda kafar nan ta matsa kawai kaje saudiyya this time kar kaje chairo" Murmushi Dada yayi yasake gyara zamansa, "To daughter yanda kikace ai haka za ayi, insha Allah nanda 3 weeks zan nemi visa sai intafi" Ahankali take murza masa maganin akan yan yatsunshi tana jijjiga kai cikin kulawa, "Dada dan Allah ka rage cin tuwon semo dinnan, kaga yanzu sugar dinka normal yake Bai hau ba bai sauka ba" "To mai sunan mama insha Allah za arage" Mikewa tsaye tayi tana cewa, "yawwa father, ni shiyasa kullum cikin exercise nake saboda ban son nayi gadon wannan ciwon sugar din naka..." Fita tayi daga cikin falon taje bedroom dinta ta dauko key din motar ta, falon ta koma ta mikawa shaddad key din, "Am gashi ka saka min motar acikin garage.." Kamar bazai karba ba sai kuma ya karba saboda nauyin idon mahaifinta da yakeji domin yajashi ajiki koda yaushe nunawa yake shi danshi ne ba bare ba, Juyawa tayi ta fita aranta tana cewa "kai din dai kaine zaka dauke motar daga inda ka ajiyeta" Bedroom dinta ta koma ta sake gyara fuskarta ta feshe jikinta da turare saboda dr naz yazo, ayanda take dinnan ahaka ta fito zata fita wurinshi babu abinda ta kara, daga ita sai body hug din jikinta da wando three quarter iya gwiwarta sai dan siririn karamin gyalen data warware ta dora akanta sabanin da dayake adaure akanta ga wani sanyayyen kamshi dake fita daga jikinta, Afalon kasa suka hadu da shaddad shima da alamar fitar zaiyi, batare da ya kalleta ba yawuce abinshi bin bayanshi tayi tana latsa wayarta amma kafin taje waje har ya dade awurin shi, Ya bude kofar motar kenan yaganta ta fito ahaka ta nufi wata mota dake fake a gaba kadan da wurinda ya ajiye mata motarta, mamaki ne yaketa dawainiya dashi tun lokacin da yafara ganinta saboda dabi'unta mabanbanta ne da sauran matan da ya saba gani, in banda rashin tarbiya yaushe mace zata iya fita ahaka? Motar ya shiga ya tadata ahankali ya nufi cikin garage din domin adanata lokacin tuni har maryama ta bude gaban motar dr naz ta shiga ta rufe ruf...... _Gaisuwa mai tarin yawa ga baby Lilmeerahcute..!!_ *_Ummi A'isha_*👌🏻 *_MARYAMA SARAUNIYA..!!_* *_NA_* *_UMMI A'ISHA_* _Dedicated to Maryam Qaumi_ 💕 *_10_* aishaummi.blogspot.com ~~~Ahankali ya fito daga cikin motar ya rufeta zuciyarsa na tir da halaye irin na maryama domin tun lokacin da yafara ganinta babu wani abu guda daya da zai iya tunawa wanda ya kasance mai kyau data aikata sai dai sabanin haka, Motar dr naz ya nufa yana zuwa yafara knocking din glass din saitin da take amma shiru sai da yayi kusan sau biyar sannan ahankali yaga glass din yana yin kasa, Hangota yayi jingine jikin kujera tana kallonshi amma ta kasa magana, cilla mata key din yayi cikin motar ya juya ya tafi batare da yace komai ba saboda ko ba afada masa ba yasan yanayin da ta shiga wanda har yasa ta kasa yimasa magana, Tsaki yayi ya waiwaya domin yajiyo karar tashin motar dr naz din, su dinne shida ita suka fita a mota da alama wani wurin zasuje, Wani dogon tsaki yaja yana mai kara jin tsanarta acikin ranshi, "To yanzu ina zasuje acikin wannan daren?" Ya tambayi kanshi, "Yawon shedancinsu mana" wata zuciyar tasake bashi amsa, Hannayenshi duka ya zira cikin aljihunshi ya nufi gida yanata faman tunanin irin rayuwar da maryama ta zabarwa kanta indai kuwa hakane to tayi kyan banza, tayi kyan dan maciji, da wannan tunanin yaje gida ya bude ya shiga. *** K'arfe 11:30 daidai maryama ta sauko cikin shirinta na fita office, wata kyakkyawar hadaddiyar doguwar riga Arabian gown ce ajikinta, coffee colour mai adon stones ajiki ta dan dora dan siririn mayafinta akanta, wani cover shoe mai mutukar tsini ta saka coffee colour, babu abinda kakeji sai kamshin tuarukan data bulbulawa jikinta wanda ya gauraya yabada wani daddadan kamshi na musamman, Tana tafe tana gyara barimar kan hancinta harta ida saukowa, shaddad yana tsaye shida kukunta wanda yake rike da lunch box dinda ya hada mata abincinta kamar yadda ya saba, Fuska ta dan yamutsa ta dubi kuku, "Me ka dafa min yau?" "Tea na dafa miki sannan kuma na soya miki chips.." Girgiza kai tayi, "yau bazan ci chips ba, plantain nake son ci dan haka kasan yanda zakayi da wannan chips din ka koma kitchen ka soya min plantain anjima driver zai dawo ya karba after yayi dropping nawa..." Daga ido tayi ta kalli shaddad bayan kukun yabar wurin, fuskar nan tashi ko alamun murmushi babu tana nan awani murtuke ahade kamar wanda aka aikowa da sakon mutuwa, "Idan kafito da motar muje ko.." Tace dashi bayan tafara tafiya, "Idan natafi to kisani bawani dawowa da zanyi na karbar miki abinci kwara ma ki tsaya ki tafi da abinki saboda ni ba bawanki bane" Tsayawa tayi cak saboda jin abinda shaddad yafada, juyawa tayi da niyyar ta mayar masa da martani amma sai ta kasa saboda kwarjininsa da ya cika mata ido, dole ta koma falon ta nemi kujera ta zauna ta dauki wayarta tana latsawa tana jan dan siririn tsaki, Tana nan azaune shikuma yana can tsaye har kukun ya fito da alamu ya kammala, tashi tayi ta fara tafiya batare da ta jira abinda kukun zaice ba, Kusa da motar taje tana jiran karasowar shaddad, tun daga nesa ya kamata ya bude mata amma baiyi hakan ba har saida ya zo gaban motar, lokacin ne ya bude ya shiga, itama shigar tayi fuskarta babu walwala ko kadan saboda wannan guy din ya gama rainata tarasa dalili, Fisgar motar taji yayi bayan kuku yagama zuba mata kayanta abaya, babu shiri taja belt ta daura domin ta fahimci zata iya buguwa da gaban motar mutukar bata daura belt ba, Yauma radio ya kunna yana sauraro yayinda ita kuma taji ta takura, kai alla alla ma take yaje ya sauketa yakama gabansa domin yagama takurata, Wurin wasu sojoji suka tsaya wanda ke tsaye agefen titi suna dan yin checking, I d card dinshi ya ciro ya nuna musu ya ajiye agefenshi bai mayar aljihu ba, bude motar yayi ya fita bayan yayi packing agefen titi, Haushine yakama ta saboda ganin sai bata mata lokaci yake yi alhalin ita kuma tanada abinyi, tsaki taja ta juyar da kanta tana tunanin to ina yaje yabarta acikin wannan zafin haka? A.c ta kunna sai kuma idonta ya sauka akan id card dinshi, dauka tayi tafara dubawa, SHADDAD A SADIQ shine cikakken sunansa, Date of birth dinshi ta kalla bakinta abude saboda tsananin mamaki, "28 years? Dama duk wannan rainin wayon nasa 28 years yake shine zai rinka yin abu kamar wani ubana, mtswwww ashema age mate dinane, to daga yanzu nadaina jin tsoronka wallahi.." Ta mirror ta hangoshi yana tahowa dan haka tayi gaggawar ajiye I d card din tasake daure fuska taci magani ta ciro medical glass dinta ta sa tadauki phone dinta tasoma latsawa, Bude kofar mortar yayi ya shiga ya zauna ya figeta, ko dagowa batayi ta kalleshi ba wayarta kawai take latsawa jin ya kunna radio yasata kashewa, Bai ko bita kanta ba yaci gaba da driving dinshi har suka shiga asibitin, yana packing ta sake bata fuska, "Ka tabbatar kadawo daukana da wuri saboda akwai inda zanje da yamma bayan natashi daga aiki" Ko kulata ma yayi balle tasa ran samun amsa daga gareshi, hakan da yayi yasake sata jin haushi, "Kai dakai fa nake magana", Mamaki abin yabashi jin ta kirashi da kai sai kace wata uwarsa lallai yarinyar nan bata da kunya, Da karfi ta rufe kofar ji kake gummm ta nufi office dinta bayan Joseph ya taho dibar mata kayanta, "Na hadu da shu'umin driver ni maryama" tafadi hakan acikin zuciyarta, Ranta abace fuskarta babu walwala ahaka ta kammala duba patients ta nufi round, kasancewar ma yau bata samu patients da yawaba da wuri tagama, Tana fitowa sukayi kicibus da dr Sameer dama wurinta ya doso, "Maryama sarauniya azo atayani aiki mana..!" Yafada tareda langabar da kansa, Dan murmushi tayi ta kalli fuskarshi, "Baka gama ganin patients din bane?" "Ai maimakon raguwa karuwa ma suke yi wallahi gashi yau dinnan natashi da ciwon jiki" "Ayya sorry, to muje" Jerawa suka yi zuwa office dinshi suka shiga kowannensu yaja kujera ya zauna patients suka fara shigowa suna dubasu, suna yi suna hirarsu har patients din suka kare, Agogon hannunta ta kalla karfe 1:30,mikewa tayi tana kallon dr sameer, "Dr bari naje office saboda yau ina son komawa gida da wuri akwai wurinda zanje" "To shikenan dr, amma ki sani idanuwana basu gaji da kallon kyakkyawar fuskar maryama sarauniya ba.." Murmushi tayi ta juya tafita batare data sake yin magana ba, Office dinta ta shiga ta zauna ta dauki tea dinta tafara kurba tareda kiran dada awaya, "Father dan Allah ka turo min wannan yaron yazo ya daukeni saboda nagama abinda zanyi kuma ina son zuwa gidan gona ta idan nadawo.." Cikeda mamaki taji Dada yace, "mai sunan mama shaddad dinne yaro? Ai yayanki ne saboda ya girmeki" Shagwabe fuska tayi tace, "wallahi Dada yarone bai girmeni ba the same age muke dashi, yau naga date of birth dinshi 28 years yake..." "Kina da son girma daughter, shikenan zan turo miki shi" taji Dada yafada yana murmushi, Katse wayar tayi tana magana ahankali, "Ai ni yanzu nadaina jin tsoronshi tunda na fahimci shi yarone ba girmata yayi ba wallahi" Tashi tayi taje kan doguwar kujera ta kwanta tana jiran zuwan shaddad, shiru bai zoba har 3 tayi, tana nan akwance dr naz yashigo ya zauna, tana daga kwance shikuma yana zaune suna hira, 3:30 Joseph yazo ya shaida mata driver yazo, kayan tabashi ya fita dasu ita kuma ta zauna jan aji, sai da yafi minti 15 yana jiranta bata fitoba, Motar ya rufe ya fita ya shiga masallacci domin yin sallar la'asar saboda yaji anata kokarin tada salla, Ita da dr naz suka fito har zuwa wurin motar, ganin baya ciki yasa tasake kuluwa, wato duk lokacin data bata tana zaman jiransa shine zai rufe mortar yatafi? "Dr muje ka ajiyeni agida" tace da dr naz, "Ok babu damuwa dama dan baki bani wannan damar bane" Murmushi tayi tabi bayanshi zuwa motarshi, shiga tayi yaja suka tafi, basu jima da fitaba shaddad yafito, ya dade atsaye yana jiran fitowarta yaji shiru, Ganin karfe biyar saura amma bata fitoba yasashi niyyar binta office dinta, karo nafarko da yanufi office din domin yagane hanyar da take bi, Dr maryama shine abinda yaga an rubuta asaman office din wannan ya tabbatar masa da cewar office dinta ne, ahankali ya buda ya shiga, wani sanyine ya ratsashi gamida daddadan kamshin turaren wuta wanda take kunnawa, Ciki ya shiga yana bin office din da kallo wanda ya tsaru iya tsaruwa tamkar office din shugaban kasa, Kan table dinta wani hadadden dan abune a ajiye da hoton butterfly ajiki, ga hoton wasu kyawawan yara, gefe kuma wata karamar drewar ce ta glass dauke da kayan tea su gwangwanin madara, Ovaltine, Milo, cornflakes, golden morn,da sauransu, "Lallai yarinyar nan yar gayuce, a office dinma dadi takeji kenan" yafada acikin zuciyarsa yana girgiza kai, Joseph ne ya bude kofa ya shigo ganin shaddad yasashi mamaki, "Ko dr tayi mantuwane?" Kallonsa shaddad yayi, "a'a nashigo ne naduba ko tana nan" "Ai tajima da tafiya itada dr nazir.." Juyawa shaddad yayi ya fita bayan yayiwa Joseph sai anjima, ranshi abace yabar asibitin yana tunanin wannan ai wulakancine tasa yazo kuma shine zata tafi. Ita kuwa maryama har taje gida tayi wanka ta shirya tasaka pink din t shirt da bakin trouser wanda ya kamata sosai, wata hula tasaka irin wacce yan fulani kesawa sai dai ita tata ta robace ba ta kaba ba, wani takalmi ta daura sau ciki pink colour tasha turare ta fito taje ta dauko bike dinta tafita saboda gidan gonarta take son zuwa wanda ke can titin zuwa kiri kiri, Kamar kullum kure wuta tayi tana shara gudu atiti, Shaddad shima akan hanyarsa ta dawowa gida yashawo kwana kenan ya hangota tana tahowa zata wuce..... _Gaisuwa marar adadi gareki ummu mukhtar nagode Allah yabarmu tare..._ *_Ummi A'isha_* *_MARYAMA SARAUNIYA..!!_* *_NA_* _*UMMI A'ISHA*_ _Dedicated to Maryam Qaumi_💕 *_11_* aishaummi.blogspot.com ~~~Wuta ya k'ara bawa motar ya nufi kanta gadan gadan amma cikin kwarewa ta kauce masa tawuce babu alamun razana ko tsoro atare da ita, mamakine ya kamashi saboda ganin yanda take yin abubuwa kamar wata namiji komai nata cikin rashin tsoro take aiwatar dashi, Ita kuwa maryama dama ta rigada tasan cewar shaddad ne domin tunda motar tace ai dole ta gane, murmushi tayi ta jijjiga kai tana cewa, "Yaron nan dan rainin hankaline wato da so yake ya razanani in fadi ko? Neva wallahi" tafada tana kokarin shiga kwanar da zata sadata da gidan gonarta, Wani katon kangone wanda aka zagayeshi da waya ga wani tsoho zaune yana daddasa wasu tsirrai acikin kaskon kasa yan madaidaita, yana ganinta ya washe baki yana murmushi, "Sannu da zuwa ranki ya dade.." "Yawwa baba dan azumi, bude min nashiga" Cikin azama ya tashi yaje ya bude mata kofar shiga ta shige tana bisa kan bike dinta, Daga gate din zuwa cikin wurin tafiyace mai dan karen nisa domin kangon yanada mutukar girma in banda sanyi babu abinda wurin yake yi domin harda dan kwarya kwaryar rafi aciki, sannan ga wani karamin lambu agefe wanda ke dauke da kayan itatuwa shuke acikinsa, Sauka tayi daga kan bike din ta nufi wani wuri dake kewaye da waya wanda ke dauke da kaji lukuta lukuta aciki da alama wurin kiwon kajine, bi tayi tana duddubawa, wasu sunyiyyi kwai yayinda wasu kuma sai a lokacin suke yi, Wurin da ake kiwata kifi ta karasa nanma ta dudduba ta fito ta shiga lambu wanda abubuwan dake cikinsa sai Wanda yagani kawai domin abubuwane masu tarin yawa shuke acikinsa ga kuma tsuntsaye abisa bishiyoyin dake wurin sunata faman rera kuka mai dadi, Duk lokacin da ta shiga lambun nan bata son fitowa domin yana sanyata nishadi mutuka, yauna kamar kullum kan wani rishen bishiyar goba tasamu ta zauna wanda ya dan sauko sosai sannan ya kanannade kamar kujera, Zama tayi tana faman bin wurin da kallo musamman ma wurinda aka dasa flowers masu

Chapter 3 of 15