Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya feshe illah hirin ikinshi dashi gaba d'aya d'akin ya d'ebi wani irin k'amshin mai dad'in shak'a.

ita kuwa Meenal har yanzu zaune take tana kuka k'asa-k'asa ga hawaye cur-cur suna zuba daga dukkan alama bacci take ji amman kukan ya hanata tayi baccin ,
ta cikin mirror ya tsura mata ido tare da tsuke fuska a ranshi ko yana Mamaki yadda kuka baya mata wuya yanzu inta ga dama sai ta hanashi bacci da wannan kukan,
tsaki ya d'an ja tare da sa hannu ya tatsi maganin ta na shafawa a goshin,
cikin kauda kai yaje bakin gado ya tsaya a gaban ta,
a hankali yasa hannu ya d'an d'ago fuskar ta sannan ya d'an matso maganin tare da sunkuyowa yana murza yatsun sa biyu kan goshin nata,
kan nata ta janye tare da komawa tsakiyar gadon tana yarfa hannu tare da cewa.
"Shiihhhi wallahi zafi."

Bai kula taba sai haurawa kan gadon yayi tare dasa hannu ya jawo nata da nufin ta matso ya shafa mata,
ita kuwa cikin jin d'an zogin maganin ta zame ta konta tare dasa hannu ta kare goshin nata.

Shi kuwa yunk'ura yayi da niyar ya sauk'a ya barta da ciwon ta dai-dai sanda yasa guiwar sa zai tsalla kata ya sauk'e k'afafun shi,
a dai-dai lokacin a take yaji wani irin sanyi ya ratsa shi wanda gaba d'aya tsikar jikin shi ta mimmik'e wata iriyar muguwar kasala ta rufe shi ta yadda hatta lips d'in shi yaji sun mishi nauyi a take jikinshi ya fara wani irin rawa da tsuma cikin kasala mai tarin yawa,
ya zame kan gadon ya konta jiki na rawa konciyar yayi a hargitse k'irjin shi zuwa cikin shi ya kifa kan pillow sannan yasa hannushi d'aya ya zagayo k'irjin ta k'afafun shi kuwa suna kan nata k'afafun,
ido ya lumshe cikin kasalan da sanyi tare da jin tsinkewar zuciya ,
hannushi yake son janyewa ya kasa kuma sai kawai rawan sanyin daya fara yana ta duk'unk'u newa.

Ita kuwa Meenal jin yadda ya matseta yasa ta tattaro k'arfin ta zata yunk'ura hakan yasa ta zame kan pillow sai gashi shima ya mirgino tare da had'e k'irjin su wurin d'aya,
tsoro ne ya rufeta jin yadda yake numfashin da fizga kai ta d'an d'ago ta kalleshi cikin tsoro tace.
"Me haka Hamma haiydar?."

Cikin sanyin murya ya fara magana.
"shhhhh Meenarl sanyi nakeji rufeni rufemin jikina."

Ido ta zaro cikin Mamaki ganin yanzu yanzu lafiyar sa lau sai gashi yanzu kuma sai rawan sanyin yake yi.

Yunk'uri tayi zata zare jikin ta daga gareshi ,
sai kuma taji ya k'ara shigewa jikin ta yana.
"Shhhhhhhihhh sanyi nake ji Meenarl zazzab'i shhhihh kija blanket ki rufe ni."

Cikin tausayi tasa hannu ta janyo blanket d'in ta rufe shi ,
shiko sai k'ara shigewa jikin ta yake yi yana murza k'afafun shi a jikin ta cikin kasalan ya rink'a tura hannayen shi yana mik'a da had'e su cikin blanket d'in.

Ita kam Meenal ba abinda take yi sai cewai .
"(Isa ) sannu" .

Lokaci d'aya zazzab'i mai zafi ya rufeshi gaba d'aya jikin shi sai wani irin tiriri yakeyi jikin yayi zafi tamkar wuta.

A haka yayi ta rawan sanyi da dunk'u lewa cikin jikin ta.

Haka ya kwana cikin wahala da kasala da zazzab'i da tsinke war zuciya,
shine bai samu sa'ida ba sai da iskar asuba ta fara kad'awa tana ratsa ko ina.

A hankali ya fara jin sauk'i sai kuma kasalan dake damun shi,
ido ya bud'e tare da kallon yadda suke konce cikin jikin juna ita kam Meenal baccin take cikin mak'aleshi,
ido ya tsura mata ganin yadda ta d'aura kanta kan k'irjin shi ta mirgina k'afafun ta kuma tsakiyar cinyoyin shi yayin da gaba d'aya rigarta ta tartare ta dawo har kan cikin ta sai d'an gajeren wonddon dake jikin ta hatta cibiyarta a fili take daga sama kuma ta matse mai k'irjin sa da nata,
shi ma en duk jallabiyarsa ta nad'e cinyoyin shi kab a woje fatarta na gogarta sa sai hannunta d'aya akan cikin shi.
Shiru yayi yana mai jin sauran kasalan a jikin shi so yake ya mirgina ta k'asa ya kasa sai murza k'afafun shi yakeyi,
ita kuwa motsin shine ya sata ta d'ago kanta cikin bacci ta kife kanta kan nashi kan bakin ta dai-dai kan nashi ta woni tsuke bakin ta tura shi ,
bakin shi ya bud'e cikin sanyi da nufin ya tasheta,
aiko sai ga lips d'in ta cikin bakin shi
ido ya lumshe cikin janye numfashi ya d'an kamo lips d'anta na k'asa ya d'an ciza,
cikin tsoro da firgita tasa hannu ta tallabe kanshi tareda janye bakin ta,
ido ta tsura mishi cikin tura baki tace.
" wallahi ba kyau yin mugunta."

Ido kawai ya tsura mata a ranshi ta bashi dariya amman sai kawai ya d'an kamo lips d'inshi ya fara tsotsa,
ita kuwa cikin kiciniyar tashi takeyi daga kanshi,
shi kuwa ya matseta da hannu d'aya sai ya kuma tura d'aya hannu tsaka nin cinyoyin su yana lalubo jallabiyar sa a nufin shi ya jawo ya rufe cinyoyin shi karta ganshi a hakan
ita kuwa ido ta zaro jin yanata tura hannushi a tsaka ninsu,
shiko ya samu ya jawo ya rufe jikin shi sannan ya d'auke hannushi a kanta,
jin ya sake tan yasa ta mirgina ta konta ta bashi baya tare da tura mishi k'ugunta,
Robar gajeren wonddon dake jikin ta ya tsurawa ido ganin yadda hips d'anta ya ciki a ciki har wonddon ya matseta,
Ido ya lumshe tare da sa hannushi kan k'ugunta yatsun shi biyu yasa ya kamo roban sanna ya sake,
pet ya fetta mata shi tare da jawo duguwar rigarta yana rufe mata cinyoyin ta,
Ita kam tsalle tayi tare da dirowa kasa tana shafa inda ya fetta mata roban,
shi kuwa cikin kauda kai ya mik'e yaje yayi al'wala sannan ya fito ya nufi masallaci,
itama alwalan tayi tana ta mota sannan tazo tayi sallan.

Sune basu bar masallacin ba sai 7 dai-dai ya shigo cikin gidan shida Abban shi a parlour suka same ta ta shirya musu abin shan tea ,
Abba ta gaida tare da bashi tea d'in,
shi kuwa General sai ta kalleshi sai tayi saurin sunkuyar da kanta,
a haka har suka gama shan tea d'in Abba ya mik'e ya nufi parlour shi,
itama Abban na tafiya ta mik'e tayi cikin bedroom ensure,
Shima mik'ewa yayi cikin zafin nama yabi bayan ta,
suna shiga yayi kanta tare da matse....


Ramadan kuwa shida Rayhana tun jiya suna dawowa gida cikin tsere suka nufi part din Ammin suna shiga suka sameta da bak'in hakan yasa dole suka koma part din Ramadan suka rink'a magana kan wannan mutumin da suka gani,
jira sauk'e bak'in su tafi suko bak'in sai tara harda rebi suka tafi,
Wanda tuni su Rayhana anyi bacci,
haka yasa Ramadan yana fitowa masallaci sallan Asuba,
kai tsaye d'akin Ammi ya wuce,
bayan ya gaida ta cikin kad'uwa yace.
"Ammi....

By
*Garkuwar Fulani*
πŸ“πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
*BANDIRAWO* page 3⃣1⃣ to3⃣2⃣
Na
*Aysha Ali Garkuwa*
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡


*Wannan shafi sadaukar wane gareki k'anwata ta gari har kullum kina raina Ummee Garkuwa 😍😘*



Pml
yace.
"Ammi kin san abin da muka gani kuwa jiya da hantsi?."

Murmushi tayi cikin kula tare da maida hankalin ta kan d'an nata gudan jinin ta mai sata farin cikin mai share mata k'ollah a duk sanda suka koranyo a fuskar ta mai cike da tunani da bagen wani abun da ta rasa.

Kai ta jinjina tare da cewa.
"Me kuka gani Ramadan har ya rud'aku haka?."

Ido ya tsura mata tare da yana yin mamaki yace.
"Ammi jiya ba munje gidan uncle Ibrahim duba jikin shiba?."

kai ta gyad'a mishi tare da cewa.
"Ehh."

Matsota ya kuma yi tare da rik'o hannun ta cikin shak'uwa da mahaifiyar tasu yace.
"Ammi jiya a gidan uncle ni da Rayhana mun had'u da wani Soja a dai-dai k'ofar shiga part d'in uncle Ammi kin ga yadda Sojan nan yake kuwa?."

Ido ta tsura mashi tare da girgiza kai cikin son jin k'arshen maganar.

Cikin muryar mamaki yace.
"Ammi dana ganshi zuciya ta tayi ta bugawa tsikar jikina gaba d'aya ya rink'a tashi idona sai rawa suke a kan kaman nin fuskar sa hankali na kuwa ya tashi Ammi."

Rik'o hannunshi tayi cikin tsoro kar d'an nata yayi gamo ne tace.
"Ramadan me ka gani a fuskar sa? shi mutun ne ko aljan?."

Kai ya jinjina tare da sauk'e ajiyar zuciya a hankali yace.
"Ammi ina da tabbacin mutun ne shi,
Ammi kamannin fuskar Sojan nan ya bani mamaki da tsoro,
Ammi komai fa na fuskarsa da halittarsa irin nawa ne,
Ammi hatta farin mu irin d'aya ni dashi Ammi hatta k'wayar ida nunshi irin nawa ne,
Ammi hatta sajen dake fuskar sa irin nawa ne ,
Ammi wallahi ko yatsun hannushi irin nawa ne,
Ammi kamata da wancan Sojan yayi yawa har takai kamar da nakeyi dashi wallahi ko Rayhana da muke tagwaye bamuyi irin wannan kamar ba,
Ammi tsawo kawai da d'an k'iba ya fini alamun ya d'an girma ni a haife,
Ammi wallahi kwana nayi ina mafarkin shi yana kuka yana k'iran sunan ki yadda muke kiran ki Ammi shima haka yayi ta k'iran cikin mafar kina,
Ammi shi kad'ai na gani a mafarkin yana rayuwar kad'aici ba wanda ke kusa dashi dake nuna mai k'auna ko kulawa sai wata budurwa ita kuma tayi nesa dashi sai wani haske da yake tsaka ninsu sai kuma na haggo wani duhu a hannun wata mata tana turawa cikin hasken daga gefen shi kuma Hamma Jabeer ne yana jan hannun wannan budurwa."

Sai hawaye cur-cur a fuskar sa murya na rawa ya kifa kanshi jikin gadon ,
wanda Rayhana ke konce tana jin duk abinda suke fad'a tuni itama sai kuka take yi sun had'a kai wuri d'aya suna kuka a hankalin.

Ita kuwa Ammi bugawar zuciyar tane ta tsananta,
lokaci d'aya hankalin ta da tunanin ta suka koma kan d'anta Aliyu Haiydar wanda ta rebu dashi tun yana d'an shekara bud'u,
a badiri kullum Ammi Aliyu na cikin ranta dashi take kwana dashi take tashi tana son d'anta tana son ta kasance dashi ta bashi kulawa da tarbiya wacce ko wanne d'an yake samu gun mahaifiyarsa,
amman ina haka bata samuba dan fushin da iyayen ta sukayi.


a lokacin da Abban Aliyu ya saketa,
ya kuma karb'e d'anshi haka yasa Babban yayan ta mahaifin Captain Sani da Dr Jabeer ya d'auke ta daga garin Kaduna ya koma da ita Adamawa Yola inda yake aikin sa cikin gidan shi ya ware mata part nata ita da mahaifiyarsu,
ya rink'a kula dasu da duk wani dawaini yarsu,
Karin konciyar hankali linsu matar sa Hajia Asma'u mahaifiyar su Dr Jabeer da Captain wacce suke kiranta Nenne ,
macece mai mutunci da sanin ya kamata ta d'auki dangin mijinta kamar denggin ta ,
ta taimakawa mijinta wurin kula da y'ar uwarshi da mahaifiyarsu du-du yaran Nenne 2 ne Dr Jabeer sai Captain Sani ,
amman ganin d'an uwanshi bai tab'a haihuba wato (Alhaji Ibrahim mai dala),
sai ya d'auki d'anshi na biyu Captain Sani kenan ya bawa k'anin shi,
daga nanne Captain Sani ya koma Kaduna da zama.

Ita kuwa Ammi bayan fitan ta gidan Abba da wata d'aya ciki ya bayyana inda take laulayi kamar zata rasa ranta,
cikin kulawa d'an uwanta Barrister Lawan mai dala ya kaita Asibiti gojin forko aka gano tana d'auke da cikin wata 3 a jikin ta,
Ammi tayi farin ciki dan ita a zaton ta ko dan albarka cikin yayunta da mijinta zasu gyara auren ta koma kan d'an ta gudan jininta,
haka kuwa sukayi Alhaji Ibrahim yaje ya samu Abba da batun cikin,
amman da yake a wancan lokacin asirin da Mama tayi ya kama shi yana aiki a kanshi shiyasa,
fir Abba yak'i yace shi wannan cikin ba nashi bane can suje su nemi uban cikin dake jikin ta,
shi ba ruwan shi ,
wannan kalma ta cewa ciki ba nashiba yasa Barrister Lawa fushi mai tsanani Wanda daga nan ya yanke duk wata alak'a da zata had'a Ammi da gidan Abba hatta kadunan Barrister ya hana Ammi zuwa kota-kota,
Ammi kam da tajin maganar tayi kuka kamar ranta zai fita sana din wannan abin ta samu hawan jin,
inda mahaifi yarta da Jabeer suka zama abokan zaman ta Jabeer yana son Ammi a ranshi fiye da zaton d'an adam Jabeer jin Ammi yake tamkar ita ta haifeshi domin komai a part nasu yake yi Ammi kemai duk abinda Uwa keyiwa d'anta Ammi ce abokiyar shawaran sa itama shine abokin shawaranta tasha zama ta bashi labarin Haiydar shima Jabeer sai yayi ta kuka yana son d'an uwan shi kuma shine kad'ai yasan yadda Ammi ke shiga damuwar rashin d'an nata, yayin da Kaka ke basu kulawa gaba d'ayan su,
bayan watanni 6 Ammi ta haifi yan tagwayen ta inda Ramadan ya fito mai kama da Aliyu sak da sak ,
ita kuwa y'a macen sun rasa dawa take kama ba abin da ta dauko na kowa a zuriyarsu sai muryar tace kad'ai irin ta Ammi da zaran ta bud'u baki tayi magana toh sautin muryar Ammi sak.

Haka yara suka tashi cikin gata da kulawa da tattalinsu da ake a cewar Alhaji Ibrahim su yaran basuma ishesu ba bare a wulak'an ta musu y'ar uwa a banza su zasu rik'esu har iya rai da mutuwa,
ita kuwa Ammi tun daga nan bata kuma yin aure ba aceqarta zata kula da yaranta,
Dr Jabeer da Ramadan da Rayhana sun tashi gida d'aya d'aki d'aya gaban Ammi ta musu tarbiya mai kyau sun tashi cikin k'aunar juna da shak'uwa.

Alhaji Ibrahim kuwa duk sanda zaije Taraba Gembu Duba yarshi Amina yakan biya cikin Yola ya d'auki d'an yayan nashi wato Jabeer suke tare,
toh shi Jabeer daga nan yasan Meenal haka kuwa yasa kullum k'arshen sati sai ya shirya yaje Yola to Membila yaje ya duba k'anwar shi Ammi ma da su Ramadan da Barrister da Nenne tare da Kaka duk suna zuwa su kaiwa Meenal ziyara,
a haka shak'uwa mai tarin yawa ta shiga tsaka ninsu ,
shiko Captain Sani kasan cewarsa a makaran tar sojoji yake da yanayin karatu shi da aikin shi yasa bai tab'a zuwa canba ko sau d'aya,
Sannan Abba kuwa yana sakin Ammi Mama ta kuma mishi asirin da dole zaman Kaduna yafi k'arfin shi saida ya k'aura ya koma Katsina yana Katsina ya karisa ginin gidan da suke ciki a yanzu suka k'aura suka koma can yayin da Aliyu ya tare a part d'in Abba shi yana rayuwa shi d'aya a haka ya girma komai na karatu Abban na mishi,
toh sana din k'auran nasu yasa Alhaji Ibrahim bai kuma ganin Aliyu ba bare da ya girma Alhaji Ibrahim bazai gane shi ba kuma shi Alhaji bai tab'a zuwa gidan su Aliyun ba dan in yaje kam zai had'u da Daddy toh dole zai gane Aliyu .....


Toh yanzu sanadin B'atan Meenal yasa Alhaji Ibrahim ciwon zuciya da hawan jini,
shine fa Barrister Lawan ya shirya da iyalanshi kab da Kaka mahaifiyar su da Ammi dasu Rayhana da Nenne duk suka zo Kadunan duba Alhaji Ibrahim d'in da jikin yayin da suka sauk'a a gidan Barrister Lawan d'in dake nan cikin kaduna,
toh su Ramadan sun zo sun gaida Uncle Ibrahim d'inne sun fito zasu koma suka had'u da General...


*Mu koma kan labarin*

ajiyar zuciya Ammi ta sauk'e tare da zubar k'ollah tana mai kama hannun Ramadan da Rayhana da
Ramadan kuka kawai suke yi cikin kukan Ramadan yace.
"Ammi nasan fa akwai abinda kuke b'oye mana nida Rayhana Ammi na fara zargin mahaifimu na raye,
Ammi wannan sojan d'an uwanmu ne duk yadda akayi mun had'a jini dashi."

Cikin kuka sosai Ammi ta basu labarin abin da ya faru shekaru 26 da suka wuce ta kuma d'ora da cewa.
"Ramadan ina ji a jikina Sojan nan d'an uwanku ne yayan ku Haiydar ne shine yayanku Uwa d'aya uba d'aya,
Amman ko kunce zakuje yan uwana zasu ha naku dan sun rik'e mahaifin ku a ransu."

Hannu Ramadan yasa ya rik'o nata cikin share k'ollan fuskarsa yace.
"Ammi mu dai Abba mahaifin mune bamu da wani uba daya fishi kuma mu ya watsar da mugun furucin ,
mu kuwa nida Rayhana mun yafewa mahaifin mu muna kuma son uban mu zamu kuma nemoshi muna son d'an uwanmu zamu je gareshi zamu raba shi da zaman kad'aici zamu sashi happy a rayuwar sa dan haka karki gayawa su Uncle komai akan zamu nemi Abban mu,
bamuga laifin su Uncle ba dan dole suji zafin abin da akayi miki a matsayi su na yayunki."

Kai Ammi ta jinjina cikin zubda k'ollah tace .
"Rayhana kinji abinda Ramadan yace kuma kema kina bayan shi?."

Kai Rayhana ta jinjina cikin kuka sosai tace.
"Ammi inason Abba na in ason in ganshi ina son Hamma Haiydar naji tausayin Hamma Haiydar ya rayuwa tamkar maraya alhalin iyayenshi na raye,
haba ashe shiyasa fuskar Hamma Haiydar ba fara'a baida sakewa ashe cikin kuncin rashin Uwa da uba yake rayuwa ba d'an Uwa ba y'ar Uwa a kusa dashi ina son d'an uwana Ammi."

Cikin kuka Ammi ta dafa Kansu tare da cewa.
" Allah ya muku albarka rabbi ya kaddara saduwar ku da mahaifin Ku na amince kuje gareshi."

Murmushi Ramadan yayi tare da mik'awa Rayhana hannu,
ta d'ora nata hannun kan nashi,
cikin yana yin jinjina ni yarsu,
itama Ammi murmushi tayi a ranta koba komai farin cikin ta zai dawowa gareta d'anta abin al'fahari ta Aliyu Haiydar..


Shi kuwa Aliyu yana shiga bedroom d'in lokacin daya bi bayan Meenal jikin durowa ya tsare ta cikin had'e fuska yace.
"Ke me kike ta min kallon munafurci kina wani zaro ido kamar mayya."

Shiru tayi cikin kallon shi a tsorace tana mai girgiza mishi kai tare da cewa.
"Mayyahh."

Fuska ya kuma tsukewa tare dasa hannu kan....

By
*Garkuwar Fulani*
πŸ“πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
BANDIRAWO pg3⃣4⃣to3⃣5⃣
Na
Aisha Ali Garkuwa
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡

MI YETTI ALLAH MI YETTI LILADO ALLAH, BANDIRABE AM ONON MA MIYETTI ON I IRI YIDDE DE KOLLOTO DO YAM MIMMA I MIDI ON FU DONTO GONDON 😘😘😘




General Aliyu ba qaramin wahala ya ke sha ba in har dare yayi, sannu a hankali ciwon ke qara ba Meenaal tsoro, yau kam ciwon ya fi na kullum, gashi ya hana ta sanar ma Abba, dabara ce ta fado mata a sukwane ta nufi falon shi ta dauko dodilo zamzam a Kofi ta dawo kusa da shi addu'a ta rinqa tofa mishi irin su Ayatulkursiyu, Qulhuwa, Falaqi da Nasi, da Amanarrasulu, ta tofa mishi, don Baffan ta hk ya ke mt in in ba ta da lfy kuma cikin hukuncin Ubangiji sai ta samu sauqi shi ne ya fado mata ta ce bari ta gwada mai kilan shi ma ya samu sukuni, haka ta tallabo kan shi ya ta ce hamman Haydar tashi ga zamzam ka sha zk ji sauqi in sha Allah, bai musa ba yai Bismillah ya sha ta shafe mai sauran a duk jikin shi, tun yn rawar sanyi a hankali ya dena zafin jikin ma yn sauka sosai ya ji dadin wannan taimakon da Meenaal ta ba shi tare da mamakin yadda shi sam tunanin shi bai bashi ya rinqa addu'a yn sha ba, ko da ya ke in zazzabin ya tashi ko bakin sa ba ya iya motsawa, cikin jin dadin jikin sa ya jawo ta jikin shi ya rungume ta a hk bacci ya kwashe su,


Ramada sun karbi no captain Sani a gun Dr Jabeer,.ya tabbatar musu za su gan shi da zaran ya samu lokaci, Captain Sani bai samu zuwa ba sai bayan kwana biyu, fara tambayan shi sunan ogan shi da sk gan su tare a gidan uncle Ibrahim suka fara haba yan qanne na ba ko gaisuwa sorry bross ina wuni hankalin mu ne yai gaba, lfy lau ina Ammin sun fita da mummy ok, don Allah ka gaya mana sunan shi mn cewar Rayhana to sis sunan General Aliyu Wani ihu ta buga tare da rungume Ramadan tana fadin Wallahi shi ne Ramadan shi ne, Ramadan ko Alhamdulillah kawai yke jerowa captain Sani kuwa baki a hankade yake bin su da ido ban gane ba me kuke nufi, Ramadan ne ya fara mgn ka bari Ammi ta dawo ita za tai mk bayani da kan ta, wannan kenan


Can gurin General Aliyu kuwa Alhamdulillah jiki ya yi sauqi sosai zazzabin ma yayi sauqi sosai don suna ganin alamun shi za su debo zamzam su tofe shi da addu'o'i ya sha sai ya mai da shi wajibin sa zai sha da sassafe da yamma ma hk in ya manta ma ko yana sauri Meenaal zt sa mishi a gora ya tafi da shi yn qoqarin ganin da shi yake karyawa, Meenaal ce ta roqi anuty Aysha ta na son gayen magarya murmushi aunty Aysha ta yi ta ce ai ni bana rasa shi saboda amfanin shi gurin mu mata, ita dai Meenaal ba abun da ta gane da ta dauko mt karba tayi tai godiya, kan ya dawo duk tayi addu'o'in da ake yi saboda Baffan ta ya dade da koya mt da ganye magarya 7 ta tofa ta ajiye ms, yau bai shigo da wuri ba sai bayan isha yn wanka ya fito ta dauko mai mgn a cikin jug ta ba shi, yn ganin magarya a ciki ya gane nufin ta amma sai ya bita da ido yn da kallon tambaya, tce mgn ne in kai amfani da shi zk ji dadin jikin ka Baffa na ne ya gaya min bai musu ba don shima da yn yi duk bayan wata 3 ynz ne da aiki yai mai yawa ya dena tana ganin yana shirin shafawa ta ware falo, gaskiya ba qaramin dadi da mamaki yarinya ta ba shi ba tare da birge shi ya fahimci ta samu tarbiya mai kyau, da dare yayi ne fa kida ya so ya canza don suna kwance sai ya ji lakwanin shi na mikewa in yai kokarin mai da ta sai byn yan mintoci sai ta qara mikewa abin da bai taba yi ba Meenaal na kwance sai ta ji kmar an zungure ta tofa sunan wani turare wai shi Zandariya πŸ˜œπŸ™ˆ

SORRY FANS DIN AISHA GARKUWA KU YI HAQURI TA DAWO JIBI TAYI MN NA GASKIYA, DON NG WASU HAR SUN SAKI IDO DA BAKI 😜😜😜😜😜😜😜 KU YI HAQURI TA DAWO WANNAN JUST FOR FUNNY,
Ruqayya Aliyu
Maman Khalil
πŸ“πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
*BANDIRAWO* page 3⃣3⃣
Na
*Aysha Ali Garkuwa*
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡



*JOGU ALLAH BE ANNABIJO BE DEFTERE ALLAH LELDI ANNBIJO MEN BE MAI , TO ALLAH JAB'I TA JOGI D'ONI A HISAI DUNIYA BE LAHIRA*




Kan gashin ta saitin idanun nata cikin tsuke fuska yace.
"Inafa gaya maki ki daina yimin irin wannan kallon munafurcin inba haka ba sai na k'wak'wulo k'attin idanun naki masu kama dana jinnu- jinnu."

Shiru tayi cikin zubda k'ollah tare da zamewa k'asa ta tsuguna ta kifa kanta kan guiwowin ta,
ta saki kuka mai sanyin sauti.

Shiru yayi a tsaye a kanta ya kafeta da ido,
yana jin yadda take fidda sautin kukan nata,
tsaki ya ja cikin lumshe ido ya juya ya koma kan gadon jiki a mace cikin jin bacci,
dan deren jiya bai samu yayi bacci ba,
hakan yasa konciyar yayi tare da jan blanket ya rufe jikin shi,
yana kallon ta kamar wasa amman sai kukan take shi kuwa harga Allah ranshi na b'aci en yaji sautin kukan nata idon ya kuma bud'ewa tare da tsura mata su a kanta ,
kokaci d'aya kuma sai tausayin ta ya rufeshi tunda ya tabbata shine ya rebota da kowa nata shine sana din zuwan ta garin shine aka bawa amanar ta,
sannan a kanshi take kuka da zubda k'ollah,
jiki a mace ya mik'a mata hannu tare da bud'e baki a hankali yace.
"Meenarl "
shiru bata kulashi ba sai sautin kukan nata ido ya kuma lumshewa yace.
"Meenarl kina ji ina kiranki kinyi shiru bazaki amsa ba."

kai ta d'ago tare da zuba mai ido cikin zubda k'ollah,
shi kuwa hannu ya kuma mik'a mata tare da cewa.
"Taso ki taso kizo nan kinji ko?."
ya fad'a yana nuna bakin gadon cikin tsare ta da ido,
kai ta sunkuyar tare da mik'ewa a hankali ta matso bakin gadon murya na rawa tace.
"Gani."
Idon a lumshe yasa hannu ya kamo nata sannan ya jawota kan gadon ta zauna a bakin gadon,
shi kuwa ya mirgino ya juyo gareta yana kallon bayan ta jiki ba k'arfi ya k'ara matsota yana kallon fuskarta murya can k'asa yace,
"Juyo nan ki gani."
juyo wan tayi tare da kallon shi cikin tsoro tana

Please Login or Register in order to submit comment