Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
aka fara ruwa Kamar da bakin kwarya Yan matanka suka nemi wurin buya domin kada ruwa ya musu duka, amma sanda aka sami matsala domin ya ca'be musu ado Abangaren yazeed kuwa parking yayi domin ruwan ya tsagaita ganin zakky baby ta 'bata masa lokaci gashi ko kulashi batayi Ba balle yasa ran zata bashi hakuri abin sai ya bata masa rai Yace Zakky what's all of this ? Tace Meaning? Yace first you wasted my time,also came out walking like a snail and you can't even apologize? Tace What wrong have I done that I will apologise? Is it wrong to walk majestically? Look that's fashion She said that Prolonging the fashion Yace Fashion my foot,the hell with it Alokacin ruwan ya tsaya kunna motan yayi Ayayinda zakky ke Cewa Look idan ka fito dani just to disgrace me ne am not in the mood please hurry up ma ni am starving gushhh Wani wawan acceleration ya kwasa ya kure speed din motan shi dama ba mutane akan titin Alokacin dadai su zaliha sun fito daga Inda suka labe domin su tsallaka titi takalmin minal ya Tsinke tsallakawa zaliha tayi koda ta juya ta hango minal bata tsallako Ba tace Ki tsallako kamin abawa motocin Hannu . Minal tace ke aradu sai na gyara takalmi na. Zaliha tace wallahi ko ki tsallako ko in tafi in tafiyata minal tace da nace ki jiranine? Tsugunawa tayi ta cire takalmin ta fara kokarin gyarawa yayinda zaliha tayi tafiyatta tana mai jin haushin minal din. Neman kara minal ta farayi bata zamu Ba aiko tana Daga kanta taga wani a tsakiyar titi Dan haka Ba tare da nazari Ba ta hay kan titin domin burinta kawai ta gara takalmin ta. Alokacin kuwa aka bada Hannu kuma daidai lokacin fada ya kaure tsakanin zakiyya da yazeed CeCe kuce suke tayi yana hankalinsa kenan daga titi yana Cewa zakky don't try me this evening Minal kuwa ta dauko karanta tana kokarin gyara takalmin tare da tafiya a hankali akan titin domin itama ta tsallaka taga mota a guje yana iyowa kanta Duk kayan cikinta sanda suka kada. Daidai lokacin yazeed ya lura da ita kokarin kaucewa yayi ya fada cikin wani Dan rami Wanda ruwa ya taru kuma ya daki motan wani Tun daga sama har kasa yawatsawa minal ruwa ta sule ta fadi kasa yayinda mai dayan motan ya fito...................... Hahhhh finally This is my sallah gift to u guys hope you like this chapter NOTE: All pictures of characters shown here are not related to the story. Kindly share, and comment thank you Much love 4th June 2019 Mzz untichlobanty💕 [1/11, 1:33 AM] Mzz_Untichlobanty💞: 🏆🏆KURUCIYAR MINAL🏆🏆 By miss untichlobanty *🍀🌹CHAPTER 9🌹🍀* Juyowa yazeed yayi ya kalli zakiyya yace oh gush,look at the mess you cause! Minal ko lokacin da ta d'aga idonta taga Wanda ya watsa mata ruwa ya juya yana magana da wata(saboda motar Ba ita yake using ba babu tinted)abin ya mugu bata haushi Minal ta fara magana a hankali lallai ma mutuminnan ya watsa mini ruwa sannan ya tsaya magana da budurwarsa? Mikewa tayi zata zazzaga masa rashin mutunci daidai lokacin me motan nan ya fito yazeed dake shirin fitowa shima yace bawan Allah kayi hakuri.... Mutumin ne yayi saurin katseshi ta hanyar Cewa  wa make gaji Kamar captain yazeed murmushi yazeed yayi yace nine Dan Allah a Duba ma asarar da Nayi sai inbiya ga card dina ya fadi hakan yana kokarin bawa katinsa mutumin yace ka barshi kawai yallabai ai paint nema ya Dan kurje Gaskiya Muna alfari dakai a ka sannan Allah ya kara yi maka jagora yazeed yace ameen amma dan Allah ko wannan ne ka karba mutumin yace waneni ranka shi Dade kuda kuka bamu rayuwarku Dan kukaremu shine har sai na karbi kudinka Dan ka gurjemin mota?ai kake wallahi Ba Komai sai alolacin ya lura da zakiyya cikin fara'a yace ina wuni madam ? Ya tsine tayi kamin kasa kasa tace lafiya tana mai kauda kai. Dariya mutuminne ya dauke yace ranka shi Dade zamu iya yin selfie? Murmushi yazeed yayi yace Ba matsala. Quick selfie mutumin ya musu sannan ya Shiga motarsa yana mamakin abinda zakiyya tamai dukda ko bai Santa Ba amma da alamu tanada alaja da yazeed din. Yazeed ko da ya mance da ya watsawa minal ruwa dukda ko laifinta ne tana tafiya ahankali akan titi amma shima harda laifinsa daya biyewa zakiyya ya kunna motarsa zai wuce minal tayi saurin riko hannun kofar sauke glass yace baiwar Allah dan Allah Kiyi hakuri ban lura bane wallahi hankalina ne ya sauke Daga titin amma kema hada laifinki kina tsallaka titi bakya kallo ki kula Dan Allah ya fadi haka yayinda ya zabgawa zakiyya harara yana kokarin Ciro kudin a aljihunsa. ganin zakiyya ta fashe da dariya, abin ya kara bawa minal haushi Su watsa mata ruwa amma ko su kallo Inda take yarda wani tsayawa Suna surutu da photo da wani mutumi sai kace Yan film bayan sun gama Iskancin nasu zasu ta fita rikosu shine ya wani kwame a mota yana bata hakuri Sannan budurwarsa tana mata dariya kwafa minal tayi kamin ta kama kwankwaso ta fara jijjiga tayi kicin kicin da ido Tace wallahi Allah ya isa na ya za'ayi Ku watsan ruwa kuma kunai mini dariya Babu abinda yazeed ya tsana Kamar ayi masa Allah ya isa Hakan yasa shi mugun mamaki amma ganin fiskanta kwalliyar ta cabe bakinnan sai yalki yake Kamar tasha man gyada Abin ya basa dariya amma ya shanye,50k ya miko mata yace gashi ki siya sabulu  kije a Duba ki kiji kanwata ? Minal tace me kuddin zai min kuma babu wani batun Kanwarka ni karkayi min zakin baki Dan bazaiyi aiki Anan Ba. Ta fadi hakan sannan ta murkutsa baki The girl is now getting on his nerves He just pressed his car accelerator trying to leave Not yet Mr.yazeed abdulmajeed Wani tsalle minal ta daka ta sake rike hannun kofarsa Zakiyya babu abinda take sai dariya Dan ita ganin clown takeyiwa minal,fadan nasu yana kayatar da ita hakan yasa ta dauko wayarta ta fara video. Malam ya zaka watsamin ruwa ka kusa bigeni har na fadi kasa amma ka hakimce a mota kana miko mini kudi me zanyi da kudinka?ai fitowa zakayi ka Duba Lpy ta. Fitowa yayi a harzuke Kusa da ita yazo ta daga kanta Wai Wai Wai wannan dakyar in takai kafadansa ma tabdi Ai bata lura gardi bane wannan sai sai basamude ma ai da batayi masa rashin kunya ba ta wuce abinta salin alin babu wata hayaniya yanzu wannan Idan ya mata naushi daya ai har lahira. Gaskiya dukda tana jibgar maza bazatayi koda kuskuren tunanin dukan shi Ba balle ta aikata Yazeed yace ke wa kikeyiwa fitsara? idonta ya ciko da hawaye a take tsoro take kar ya daketa Dan taga ya dunkule Hannu jikinta na rawa ta girgiza kai Yace Nayi kama da sa'anki? Tace a'a Yace shine kike min rashin kunya Tace ai kai ka jawowa kanka kana Abu Kamar baksan darajar dan Adam ba Ya dalle mata baki da yatsansa Tace Allah ya isa na wallahi bazan yafe makaba kuma bullukutut bakar mutuwa. Yace ke zan canja miki halitta fatace Bismillahi Daga hannu yayi Kamar zai mareta dashi bata dukan mata  tace wallahi kana marina zan kira Yan sanda kaga wayata? Yazeed yace to sai me dankin kirasu? Tace sai en sandan su kama ka Yace idan ni kakansu nefa? Tace sai sojoji su kamaka Yace idan ni ubansu ne fa? Tace da gaske nake fah zan kirasu inka tabani Ya matso kusa da ita yace Bismillah Tace a ah fa Ya kara matsowa yace ki kira mana! Ya fadi hakan da kakkausar murya cire dayan takalminta tayi ta rike a hannun dan ta lura zaliha da haske ta tafi tun dazun ta tafi tun dazu Tace mai zubin samudawa da ido kulya kawa sannan ta Diba aguj Bata tsaya a ko Ina ba sai gidan aunty fauziyya zata fada a guje taji gate a kulle ga wani mota shigen na yazeed ya shigo Latin take fitsari ya cika mata Mara take gumi ya fara karyo mata. Bubbuga gara din ta farayi aiko zaliha na bude mata ta nufi ban daki tana mai cillo da takalmanta. Bayan ta fito aunty fauziyya tace ina kika tsaya tun dazu muMun dauka kin Koma gidane ma kuma ya akayi kika bari fitsari ya matseki? Labarta musu abinda ya faru tayi aiko sukayita dariya zaliha tace ai in kinsan wata bakisan wata Ba 😂 Nandai zaliha ke fadamata irin haushin data bata har ta tafi ta barta Nan aka dago da zancen auren zaliha har minal take basu labarin baba nason ya mata aure amma yace sai mai Dan ilimi Minal tace nidai indai gidan da abinci Toh shikenan banida damuwa kai amma fa banda mai warin hammata. Aunty fauziyya tace har kura zatace da kare maye ? Keda bakyayin minti uku kingama wanka? Harvwani bakison mai wari? Zaliha tace ai ta gyara yau bakiga har kwalliya na mata Ba aunty Fa'iza tace dallah dubi wani gira Kamar Anyi bakin fenti dukkanku Ba abinda kuka iya Haka dai suka dinga hira suna kwasar dariya Kamar Ba gobe Minal shaf ta manta dacewa Ba kwana zatayi Ba Aunty fauziyya kuwa ganin a holiday suke kuma taga minal da katan jaka sai ta dauka kayanta ne aciki Zaliha kuwa dama sati zatayi mata Aunty fauziyya Ba laifi mijinta yanada rufin asiri mijinta Dan kasuwa yanada shago akasuwa Itakuwa tana gyaran jiki,dasu makeup,da turaren wuta Wanda inna ce ta koya mata makeup kuwa Training class tayi Kuma Ba laifi tana samun alheri. Da daddare suka dafa Dan malele  suna cikin sha Minal tace Innalillahi wa inna ilaihi raji'un Aunty da zaliha sukace menene? minal ta side manjan dake bin mata hannunta kamintace na manta baba yace karnayi dare Atare sukace dama Ba kwana zakiyi Ba ? tace eh Aunty fauzy ta kalli agogo pass 9 tace dare kuma yayi Tara ya wuce Wayar baba tanananko? Minal tace eh Aunty fauxy tace yauwa bara na kirasa na fada masa Nan ta kira baba tace minal zata kwana a wajenta Yace to Ba Komai daganan ma ta kara mata fada akan tsafta Dan yau yaji dadin yanda ya ganta tace Ba Komai Insha Allah zata musu fada dukkansu biyu ma Nan sukayi sallama Anan suka tattara suka kwanta dama mijin aunty fauziyyan bayanan. Yazeed's POV Yazeed kuwa koda minal ta falfala a guje tsaki yayi yace idan na kama yarinyannan sai Nayi mugun saba mata sai ta gwammaci ba'a haifeta ba Komawa mota yayi zakiyya nata dariya tace swthrt kaga bakinta kuwa itafa gani take ta kure kwalliya Yazeed yace gaba zakky ke wato duk rashin kunyar da tamun Ba dameki bako? Tace wannan tsakaninku ne ai Dear pls let's go ! Yace my zakky you will never change Sannan ya kunna mota suka tafi yanata gungunin abinda minal tamai zakiyya sai dariya take Kamar tababbiya Abin mamaki take basa zakky wace iriyar mutum ce?kawai yayi smiling. At night After sun dawo daga dinner dinsu Suna hira a parlour mom tana fada masa Cewa she is planning on visiting her family Wayan YAZEED yayi ringing it was his aboki,a brother as well Jamal Jamal yace Hello captain. Yazeed yace Dude how far? Jamal:guy I have a surprise for you? Yazeed: and what's that? Jamal:gobe zan shigo garinku Yazeed: are you serious? Jamal: of course yes! Yazeed:okay I will send habu(personal)driver to pick you up Jamal: guy pls kazo da kanka Yazeed: no need to plead with me I will come,by what time would u land? Jamal:that's why I like you,emm we will land by 12:30pm Insha Allah Yazeed: okay see yah Jamal: bye Yazeed: bye............ Hope you love this chapter? Juma'at Mubarak 7 June,2019 Mzz untichlobanty💕 [1/11, 1:40 AM] Mzz_Untichlobanty💞: 🏆🏆KURUCIYAR MINAL🏆🏆 🌹by miss untichlobanty🌹 🍀CHAPTER 10🍀 *Morning* Koda su minal suka tashi akayiwa yara wanka sukayi  karyawa suka ci Suma sukayi wanka suka danyi hira Anan  aunty fauziyya tayiwa minal fada sosai akan tsafta sannan ta bata wasu yan turare tace tanayin aiki dasu ta bata wasu sako ma ta kaiwa inna(nima bansani me acikiba) Waje ta fice domin nemo almajiri ya kai mata gyaran takalmi aiko taci karo da kandala mai gyada wanka mata mari tayi tace ke kandala da ub*nki me kikazo yi nan unguwar iye? Kuka kandalar ta fara tana kokarin kwashe gyadatta daya bare tace wallahi saina hadaki da aunty salma minal tace inkin fasa kinki Allah ita kanta salmar tayi kadan balle ke banzar bazara kunun bayan ludayi. Dama itama Daga haka ta fara Daga talla ta fara bin maza unguwa unguwa yanzu ta zama magajiya adai juri zuwa rafi. Bankadeta minal tayi tace sh*giya jaka. Gyaro mata takalmin akayi sannan ta kama hanyan  gida domin Azahar ya kusa pass 11:00am........... Yazeed's POV Yana tashi da safe after yayi all necessary things needed ya gaida mom sannan yadan fita.  motanshi fara tare da guards 2 kamin 12:00pm yayi ya dauko Jamal . After yaje wani cafe yanashan favorite cappuccino dinshi phone dinshi yayi ringing. Zakiyya:swthrt awhile naga fita ko?pls if you don't mind kabiya restaurant da mukaje jiya ka siyo mana pizzan naga akwai a menu dinsu kaga sai ka daina siyowa a dayan wajen kasan yaufa Thursday She said all of that in not more than 2 breath Yazeed: haba dear!can't you atleast say good morning, u didn't ask about my well being or anything all you care about is the pizza which we will eat later at night ? Zakiyya: sorry good morning Hope zaka siyo pizzan ? Yazeed: naji Zakiyya: and also kafin ku dawo kudan biya ta boutique dina Ku karbo min wani sako( legendaries), bye love you tiiit Yazeed:love yo..... Oh god,bukatanta ya biya she can't even wait for me to say bye He called the waiter,paid for  cappuccino dinshi And went out security men dinshi guda biyu na biye dashi Kofa suka bude mai ya Shiga motan sannan suka rufe daya ya Shiga drivers seat dayan kuma front passenger seat Na driver's seat ne ya kunna motan ya kama hanyan airport yazeed yace we are going to zakby unique boutique  before going to the airport Drivern ya karya kwana sukayi hanyan boutique Minal POV Tana cikin tafiyarta tana er wakenta akan babban titi wasu en shaye shaye suka hangota Thug 1:boss kaga wata er shila kuwa Thug 2:kunama yarinyannan tayi Thug 3:boss kawai mu sankacota mana Thug 4:boss nifa inason sidin kwano Thug 2:goje(thug1) Ku kai min ita Mansion amma kuyi ahankali Dan yarinyar ta Shiga raina Thug 1:lallai yarinyannan ta Shiga ranka boss tunda har sai an kaita mansion baza'ayi Anan Ba Boss:banason maganan banza ni har kishinta ma fa ya kama ni (Kaji min rashin kunya irin na Dan tasha Wai kishinta ya kamashi ni yama bani haushi) All thugs:hahahahaha boss kenan mude in an gama a aiko mana Boss:zundum me kuke jirane Ku dauko min amaryata Minal tana tafiya taga en shaye shaye sunyo kanta fuska tayi taci gaba da tafiya Goje ne yace amaryar mu ji mana Bata kulasu Ba amma tana fake dasu Scorpion ne yayiwa Goje alama da ido akan su kamata basu ankare Ashe Amaryar su ta Dade da arar kafar kare acan nesa suka hangota ta auna a guje suma da gudu suka bita Gudu take batasan inda take wulla kafarta ba wulan keluwa (kwana)tasha inda ta hango booth din wani mota a bude da gudu ta daga kayan ciki ta Shiga kasan kayan yazeed yaji  jijjigar motan kuma baiga fitowan su ezikel Ba a karo na biyu hakan yasa ya leko Alokacin su scorpion Suna arean motan minal ta bace musu ganin yazeed ya fito daga motan gashi wandon sojojinshi yasa da farin T-shirt Ba shiri suka bar wajen shikuma da baiga kowa Ba kawai sai ya koma Su ezikel ne suka fito da guntun kayan suka saka a booth din kamin suka rufe minal tana hangosu suka daura mata kaya gashi ta gansu da kaki atake wani mugun fitsari ya matseta   Yazeed ya Duba agogo yaga 11:45 sai yace kawai su kaiwa zakiyya kayan sai su wuce airport Dan ko su Jamal din sun iso kamin su sauko, kayansu ya taho, ya fito zai bata lokaci shi kuma bayason jira Sai yace muje gida mu sauke kayan Driver ya kunna mota suka nufi gida Minal tanajin an kunna motan tace shikenan za'a kaini barikin sojoji na Shiga uku na lalace. AT JEEDMAR Suna shigowa yazeed ko fita daga motan baiyiba yace su sauke kayan daga motan su shigar gida Sukace yes sir Booth suka bude fara Ciro kayan lukman na daga Leda taga Kamar kafan mutum Ahankali ya radawa ezikel "be ready something no dey right here Ezikel ya Ciro AK47 dinshi ya saita daidai minal Lukman ya ajiye ledan hannunshi ya daga daidai na kanta Wata yar kyakkyawa ya gani mai cute pinky lips tana bacci babu Komai a fiskanta sai uban man baki Kamar zai digo Suka furta wow a tare Kallon juna sukayi Suna magana da ido akan yanda zasu fadawa boss Lukman ya gyada kai alamun zaije ya fada Kewayowa yayi murya kasa-kasa yace boss an sami matsala Yazeed: meaning? Lukman: dama...em da Muka..mukaje Ciro kayan....shin........ Yazeed: hope Ba Barin kaya kukayiba ? ya fadi haka adan tsawace Lukman: a a dama acikin booth..... Ezikel ne ya tsindumo baki Ezikel: boss lukman dey shy for u ooo,wani Yaro ne beauuuuutiful Muka ganshi asikin booth yana bassi Yazeed: ezikel what nonsense are you talking about ? Ezikel: boss if adey lie,thunder fire me Yazeed: let me go and see Futowa yayi yazo wurin booth din minal ya gani tana bacci hankali kwance Tabbas bazai manta wannan fiskarba Wannan yarinyarce Wanda tamai fitsara jiya dole ya shaidata kodan man bakinnan lebensa na kasa ya gatsa Sannan ya dakarkare ya daka mata duka a gadon baya yaga ko motsawa batayi Ba Aranshi yace lallai wannan yarinyar ni zata nunawa jarumta Kwata kwata bekawowa kansa Cewa zai iya yuwuwa suma tayi saboda babu ninfashi ba Wanda haka abin yake suma tayi Saboda rashin ninfashi inba hakaba minal ko cinnaka ya cije ta an Shiga uku balle soja ya watsa mata tafi. Ciki ya Shiga babu kowa sai mai shara yace ta kawo masa chilled ruwa gora biyu Jiki na bari ta dauko ta basa ya karba ya fita Zuwa yayi ya kalli minal tana kwance yanda ya barta su lukuman a tsaye Gora daya ya mikawa ezikel Sannan ya bude dayan Ezikel yace boss ruwan akwai sanyi sosai fa Yazeed yace na fika sanin haka Kamin ezikel ya kara magana Yazeed ya juyewa minal ruwan sanyi.............. Ina sonku irin sosai dinnan 9 June,2019 Mzz untichlobanty💕 2 - CHAPTER 11-20 🏆🏆KURUCIYAR MINAL🏆🏆 By miss untichlobanty *🍀🌹CHAPTER 11🌹🍀* A zabure ta wantsalo daga cikin booth din tana salati ta fado a gaban lukman ta kurje hannunta Bude idon da zatayi taga takalmin soja sai alokacin ta tuna mai ya faru kawai sai idonta ya ciko da hawaye Fitsarin da takeji dazu ya dawo ya cika mata Mara taf Yau tasan ta Shiga uku kashinta ya bushe ta Shiga hannun soja Tsawa yazeed ya daga mata ke mike tsaye ? Allurar ta motsa Ba ita kadai Ba har su lukman Saida suka tsorata fitsarin da takeji  atake yabi jikin skirt dinta tana zazzare ido tace kuyi hakuri walla..... Bata karashe Ba yazeed yace shut up my friend, kalleni! Sai alokacin ta kalleshi babu shakka wannan basamuden datayiwa rashin kunya ne jiya itakam ta shi uku Ashe soja ta tsokalo Duka kam yau zata shashi harda na sadaka Tace Dan Allah kayi hakuri ka yafe mini wallahi bazan kar.... Yace shhhhh yimin shiru Yazeed yace Samuel inasu doggy suke ne? Samuel:Suna cage ne fah Yazeed: bring them out Samuel: yes sir Minal taji ance su doggy kuma ance cage sai ta dauka Cage din da yake kai masu laifi nan zai kaita Tafara Cewa oga sir kayi hakuri karka hadani da arna a caji office dinka wallahi na dena Gashi idonta ya ciko da hawaye amma sunki su zubo tayi tayi sunki su zubo Shi kuma yazeed abinda ke kara bashi haushi kenan takiyin kuka ita a dole jaruma Haushin karnuka ta faraji a take ta kara tsula wani fitsarin Wasu kosassun police dog ne guda biyu Tsalle tafara tana ihu innalillahi wayyo inna na Shiga uku na lalace amma still babu hawaye Alokacin duka masu aikin gidan sun taru tsabagen muryarta shiyasa inna batason minal tana kuka ta kwammaci dije tayi sau goma akan minal tayi sau daya kowa na tsoran bada hakuri kar a hada dashi wasu kuma na mamakin mai ya hada oga da wannan yar kyakkyawar innocent yarinya Dan basu taba ganinsa a wannan yanayi Ba dukda sunsan Cewa bayada sakin fiska ayanzu Gashi mom batanan taje gidan friend dinta balle tasa baki Madam zakiyya ma batanan ta tafi wani get together da sukeyi ita da business partners dinta Wanda yazeed bai Masan dashi Ba Da minal tayi hawaye yazeed zaisa amayarda karnukan ganin takiyin hawaye tana ihu kawai yasa yake ganin pretending takeyi besan tsananin tashin hankali yasa ta kasa hawaye ba Kallonta yayi yace ke al'amarinnaki bayan tsiwa harda taurin kai ko ? Tace wallahi oga sir Ba taurin kai bane Yazeed yace release them! Atake Samuel ya sakesu sukayo kanta babu shiri ta antaya a guje fitsari nabin skirt dinta domin ahalin yanxu ta tsula yakai sau biyar  Gudu take Suna binta har suka iso wurin swimming pools. Toh anzo wurin minal nason wasan ruwa amma bata taba Shiga mai yawa Ba gashi Ba tashin kauye tayi ba balle ta iya nitso da linkaya amma kuma ga karnika nan Suna tunkarota kuma wa dannan bazasuyi mata da kyau ba Dan ga bakinsu har yawu yake zubarwa Kawai sai ta yanke shawara gwara ta fada ruwan koba Komai gawanta zatayi mutunci Finndumm!! ta fada swimming pool din Samuel kuma da gudu ya riko karnikan Dan karsu bita cikin ruwan Yazeed Wanda ke tafiyan kasaita har ya iso wajen Alokacin lukman na shirin fadawa ruwan Dan ya cetota Yazeed ya dakatar dashi Rigarsa ya cire sannan ya fada ruwan alokacin har tasha ruwa nimfashinta ya kusa daukewa ya daukota Akunnenta ya rada mata bashi  sannan ya fito da ita yacewa masu aiki su hada mata shayi mai zafi tasha sai su nuna mata side dinshi Tasameshi acan sannan su lukman suje su dauko jamal kuma karkowa ya sake ya fadawa mamy ko Jamal abinda ya faru Ya wuce side dinshi Wet trouser dinshi ya cire sannan Ya saka wani tare da farin T-shirt kamar Wanda ya cire sannan ya fada gadonsa yana tunanin abinda zaiyiwa minal Idan ta farfado batayi kuka ba Domin yaga sanda ta suma a hannunshi........ Am feeling so sleepy yet typed coz of the love I have for u guys Show me some love as well 11 June 2019 Mzz untichlobanty💕 [1/11, 1:44 AM] Mzz_Untichlobanty💞: 🏆🏆KURUCIYAR MINAL🏆🏆 By miss untichlobanty *CHAPTER 12* minal kuwa shayin dazai taimaka mata da condition din da take aka hada mata Kamin suka samo bowl da ruwan dumi da tsumma Sannan suka dauko first aid box domin ciwon dake hannunta har yanxu yana zubda jini duk ya bata mata hijab dinta Tabawa dukkan maids da securities din gidan tausayi hatta sojojin domin duk rashin imanin wasu daga cikinsu sunsan Cewa minal ta horu What so ever her fault is? They all look at her pitifully, how young she is,yet going through all these sort of troubles First was her hiding inside the Booth, Then passing out due to lack of oxygen, Then woken up by a chilled bottle water ! Then fear of being in an army's house as an offender! Then the blood cascading from her hand making her clothes look like......... Then the looks and presence of those horrible and terrifying,wicked dogs The dogs chasing her is the biggest fear of her life Her falling into the pool. That one is called helplessness.................... Wata maid me suna tala (mai shara)ce ta sa'a tsumman a ruwan zafin ta matse sannan ta fara goge ma fiskanta Wani nifashi taja kan ta sauke hawayen wahala suka fara zarya a idonta yadda kasan ruwan sama Cikin 2 min harta jika hijabinta ta fara jika pillow da hawaye Maid uku ne Dama a dakin da take daya da first aid,daya bowl din warm water,daya kuma tea and toasted bread Dukkansu idonsu ya ciko da kwalla musamman da suka ga yadda minal take kuka Wani mahaukacin atishawan data watsa ne ya dawo dasu saga duniyar da suka fada na halin da take ciki Katrina wacce take baturiya itace first aider na gidan First aid box din ta bude sannan ta ciro su cotton,dettol,spirit,iodine,and Bandage. Treating ciwon ta fara aiko ana fara goge jinin minal tafara yarfa hannu (nace tabdi tun ba'a saka alhaji dettol da oga iodine) Yamutsa fiska take yadda kasan mai nakuda Dettol aka saka domin ayi disinfecting aiko wani kara ta sake ta mike a take tana Cewa Dan Allah Kiyi hakuri,wallahi ni Ba mai lafi nace karki min mugunta Itadai Katrina ganin bats gane Ba sai ta kalli sauran with a questioning look Fassara mata sukayi kamin tace oh sai tacewa minal din No no my dear am gonna harm you,impact am being gentle with you Minal dai anzo gurin domin bata gane ko Abu daya data ce Ba Hasali

Chapter 3 of 19