sai a zahiri na ganki sannan na gane Kece..... Hannunta duka biyun ya ri'ke yace Zainab nasan had'uwa na dake had'in Allah ne, babu wani abu da wani zaice a kanki yayi tasiri a wajena Indai ba gani nayi da ido naba, so inaso ki daina duk wani tunani akan sonda nake miki
Wani hawaye mai zafi ne ya fito mata daka ido, gaba d'aya jikinta yayi sanyi, tana son Yarima kuma tana son fad'a mishi ko ita wacece gashi ta d'auko hanyar fad'amai ya dakatar da ita, lallai in Yarima yasan wacece ita bazai aureta ba, zan Bari saiya aureni in fad'a mishi koni wacece na tabbata zai fahimce ni S........
Katse mata tunani yayi tare dasa hannunshi yana goge mata hawayen idonta, yace Zainab bana son ganin wannan hawayen naki, kina min asaransu.....
Murmushi tayi tare da fad'in na daina Yarima na daina bazan kara ba.
Hancinta yaja tare da fad'in yauwa my princess
Murmushi ta saki
Yace ya maganan Walima dinki? Mai zamu shirya?
Tace banda wani Abun cewa sai yanda kace.
Yace Nop ina son in San mai kike so..... Yauwa you never tell me what you like nd dislike
Tace Yarima komai kake so shi nake so
Murmushi yayi tare da fad'in toni ke nake so....
Dariya tayi tare da fad'in ni kuma?
Yace eh ke nake so,duk wannan abunda suke hannunshi na ri'ke da nata
Sakin hannunta yayi tare da matsawa ya d'auko wani karamin akwati ya bata yace gashi sai kiyi abunda ya dace, sannan akwai check a ciki nasa iya kudin da za'a cira amma ban sa suna ba Wanda zai cira sai yasa sunanshi, kiba ma islamiyya din, gudun mawarki....
Tace Yarima nagode Allah ya saka maka da gidan Aljanna ban San wani....
Ya dakatar da ita tare da fad'in ya isa haka my princess
Tace Yarima amma kaman hidiman yayi yawa Sosai
Yace komai na miki baiyi yawa ba, u deserve it
Tace ngd
Ido ya kura mata yana kallonta ko kyaftawa bayayi
Ganin irin kallon da yake mata yasa tayi saurin yin k'asa dakai
Hannunshi yasa ya d'ago Mata fuskanta yace my princess d'ago ki kalleni....
Ido ta rufe domin bazata iya kallon idonshi ba, dan yana mata wani irin mugun kwarjini Sosai
Ganin ta rufe ido yasa yayi murmushi tare dakai bakinshi kusa da kunnenta yace I want my kiss now, Bayan ya fad'a mata hakan yayi baya tare da kallon fuskanta yaga har yanzu idonta a rufe, iska ya hura mata a fuska tayi saurin bud'e ido, murmushi ya sakan mata idonsu duka yana kallon na juna, fuskanshi ya fara matsawa kusa da nata kaman zaiyi kissing dinta ganin haka tayi saurin rufe ido, murmushi yayi yakai mata peck a goshi jin a goshi yayi mata yasa ta sauke ajiyan zuciya har yana ji, baya yayi tare da fad'in I don't want the kiss now
Kallonshi tayi suka had'a ido da sauri tai k'asa dakai
Murmushi yayi yace wannan kunyan yayi yawa but very soon zan rage miki shi
Murmushi tayi ba tare da tace komai ba
Yace Zainab very soon you will be mine
Ganin taki magana yasa yace bari inzo mu wuce tunda my princess ta k'osa in tafi
Da sauri tace nifa bance haka ba...
Murmushi yayi yace kina son in zauna?
Murmushi tayi tare da fad'in wannan tambayar..
Sai kuma tayi shuru
Yace Ina ji fad'a min?
Tace Mai zance?
Murmushi yayi yace say you love me
Itama murmushin tayi tare da fad'in yaushe zaka tafi?..
Dariya yayi yace oh saboda karki fad'a kike korana koh?
Tace a'a nifa ba haka nake nufi ba
Yace anyway ya kamata inzo in gudu naga yamma yayi Sosai gashi an kusa kiran sallah magrib...
Tace toh ka Bari in kukai sallah saiku tafi.
Yace OK my princess, yace banga mutumina ba yau?
Tace habib?
Yace eh
Tace baya nan amma zaka iya ganinshi ya fad'o yanzu
Yace OK.... Dan shuru yayi Kafin yace naso inzo saukan ku but I will try in samu inzo
Tace a'a Yarima basai kazo ba, ka Bari kawai duk abunda akayi zan turo maka, ranan fah shine Washe garin auranka kaga karka shiga hakkin amarya
Idonshi na kanta yace Kema ai tawa ce, sannan Idan abun murna ya sameki dole inzo in tayaki
Tace Yarima plz basai kazo ba Wlh na yafe maka, abunda bazan so ya faru akaina ba banso Ayi ma wata akai na
Yace really?
Tace eh
Yace Sai yasa nake sonki, but amma duk da haka Zanzo
Tace shikenan tunda haka kace, but Ina son Yarima na ya zama mai adalci, tunda ni nace na yafe
Murmushi yayi tare da fad'in shikenan Yarima dinki zaiyi adalci insha Allah tare da ja mata hanci
Tace akwai zafi fah
Murmushi yayi yace am so sorry my princess, jin ana kiran sallah yasa ya fita dan yayi sallah
Itama gidan ta shiga tare da ajiye jakan da Yarima ya bata, zama tayi tana tunanin firansu Tana murmushi, Yarima I promise ranan daka aureni zan fad'a maka koni wacece Bazan bari ka aureni ba sai Nayi istabra'i zama tayi tana ta tunani dan tana fashin sallah, karan wayanta yasa ta d'auka ganin Sunan Yarima tayi ta danna tare dakai wa kunnenta
Yace come out in ganki mu kama hanya
Tace OK tare da kashe wayan tana murmushi fita tayi a waje ta ganshi a tsaye
Inda yake taje yana ta murmushi a tsaye suka tsaya yace my princess zan wuce sai yaushe kuma?
Tace sai Bayan bikin ka
Murmushi yayi yace bazan iya ba, Kema kin sani
Tace Yarima daka jibi fah zaku Fara abu
Yace how did you know?
Tace naji Ai kana fad'ama amaryanka
Yace hakane na k'osa ma a kawo ta, yana maganan yana kallon bariki
Ganin ta d'an bata fuska yasa yaci gaba da fad'in bari inje in samu muyi waya ma....
Gaba tayi tana fad'in saida safe tana fad'in haka tayi cikin gidan
Murmushi yayi tare da girgiza kai kiranta yayi amma taki d'auka
Message ya Mata tare da fad'in haka za muyi sallama din?
Ganin batai reply ba kuma bata fito ba yasa ya shiga mota yace suje, kara tura mata message yayi yace ok na tafi kin San hanya zamu kama but kinsa na tafi ba tare da munyi sallama Mai Kyau ba, may be ma wannan ne last maganan mu......
Tana ganin message din ta fito da sauri amma ina motocin sunyi gaba...
Yarima yana kallonta murmushi yayi tare da fad'in I love you my princess
Bariki komawa tayi ta doka ma Yarima kira amma yaki d'auka, message ta tura mishi Tana fad'in plz pick my call I need to talk to you
Yarima yana ganin sa'kon yayi murmushi tare da kashe wayan dan yasan zata kara kira kuma bazai d'auka ba har sai yaje gida, domin bazai iya waya da princess dinshi ba a gaban driver domin sarautar shi bazai Bari driver yaji Kalan kalaman da zaima baby dinshi ba
Bariki kara kira tayi taji wayan a kashe kanta taji ya Sara, jiki a sanyaye ta had'a kayanta tabar gidan dan zuwa d'akinta, tana zuwa d'aki ta ajiye kayan tare da had'a tea tasha, jakar da Yarima ya bata ta bud'e kud'i ta gani makil da yawa dubu d'aya d'aya bandir bandir har guda ishirin million biyu kenan, ido ta d'an zare tana mamaki check din ta d'auka shima taga million uku ya rubuta, a hankali tace Yarima kud'in yayi yawa har 5mil, hawaye ya zuban Mata tace yanzu duk wannan Abun karya nayi maka ka d'auki wannan kud'in kaban, ba tare daka nemi jikina ba lallai Yarima inna Bari na rasaka Nayi babban rashi, duk yanda zanyi dole In boye koni wacece har sai ka aureni zan fad'a maka Nasan zaka fahimce ni, wani hawayen ne ya kuma zubo mata....... Muje zuwa muga ko Asirin bariki zai rufu ko kuma akasin haka
~MARYAM OBAM~
*BARIKI NA FITO*
*BY*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(Maryam Obam)*
*https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/*
*WWW.Maryamobamnovels.com*
*Wattpad @maryam-obam*
*Instagram@maryam_obam*
*MARUBUCIYAR*
*1)FATIMA ZARAH*
*2)DUKIYAR MARAYA*
*3)BA'KIN ALJANI*
*4)BANDA ZABI*
*5)AMINIYA TACE*
*6)KISSA KO MAKIRCI*
*7)SAINA AURESHI*
*8)SUHAILAT*
*9)TAMBARIN TALAKA*
*10)JAWAHEER*
*11)MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*
*AND NOW.... BARIKI NA FITO*
*DEDICATED THIS PAGE TO....*
*HAJIYA NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*
*PAGE 23*
Kuka tayi Sosai lallai Yarima shine mai Sonta na gaskiya, duk namijin da zai maka hidima ba tare daya nemeka ba, shine masoyinka, mazan yanzu basa abu dan Allah sai dai in Sun miki Suma suna so kiyi musu, mata Kwadayi maza kuma shegen sha'awa, daka ya baki abu kin amsa in baice miki wani abuba toh gobe zaice dan ba'a banza yayi miki ba, wannan shi ake kira trade by barter, wani irin son Yarima yake kara shigarta, ido ta lumshe mai yasa na kasa fad'a ma Yarima gaskiya? Saboda ina tsoran in rasa shi, saboda ina sonshi..... D'aukan wayanta tayi da sauri ta kira Layin Yarima amma still switch off, d'an shuru tayi tana tunani kallon lokacin data kirashi tayi dazu taga wajan 39mnt, tace ya isa ace yakai gida yanzu coz daka kaduna zuwa Zaria 30mnt ne, kara kira tayi amma a kashe tayi mugun shiga damuwa, mai yasa Yarima ya kashe waya Bayan yasan zata kira, sannan yasan sa'kon daya tura mata dole hankalinta zai tashi, gashi na kira yaki d'auka daka karshe ya kashe waya..... A hankali ta furta Yarima plz ka kunna waya ina cikin damuwa....
Yarima Aliyu Bayan sun karasa direct masallaci yayi cikin sauri dan yin sallah isha'i, duk da sanda suka isa an idar da sallah din, direct gefenshi yayi toilet ya fad'a yayi wanka sannan ya fito yasa jallabiya, falo ya fita inda yaga an jera Mai abinci zama yayi kuyangi suka zo suka suba Mai sannan suka bar wajan, Fara ci yayi yana cikin cin abinci saiga usman d'an waziri ya shigo
Usman zama yayi kusa da Yarima yana fad'in Wai kwana biyu Ina kake zuwa ne haka?
Yarima baiko Kalli usman ba balle yasa ran samun amsa.
Usman bai damu da hakan da Yarima yayi mishi ba dan dama yasan hali, inda Sabo ya saba, ganin Yarima bazai yi magana ba yasa yaci gaba da fad'in Yarima ya kamata ka rage fita kasan Idan gimbiya tazo jibi maganan fita ya Kare sai kuma Bayan aure....
Yarima ajiye spoon din dake hannunshi yayi tare da fad'in akan wani dalili?
Usman yace domin haka shine al'adan masarautar
Yarima yace thank god al'ada ce ba addini ba, da za'a rufe mutum a hanashi fita like a prison person
Usman murmushi yayi tare da fad'in Yarima kasan wannan masarautar bata wasa da al'ada domin an dauketa da muhimmanci, kuma ina mai baka shawara daka bi wannan al'adan Indai bason ganin fushin Mai martaba kake ba
Yarima Aliyu tashi yayi tare da fad'in nifa ban son takura a Bari inji da wannan auran da ake kokarin cusa min mana haba kodan Anga nayi shuru
Usman yace shurun shine Alheri Yarima, kuma ina mai baka shawara daka girmama zabin da iyayenka suka maka, Indai kana son ganin farin cikin su, kuma kana son Kaga dakyau
Yarima Aliyu yace naji zaka iya tafiya
Usman yace Allah ya huci zuciyar Yarima, dama nazo ne akan kazo muje Kaga gefen ka, domin ance tunda aka fara aikin baka le 'ka ba, ya kamata kazo muje ka gani in yayi maka
Yarima Aliyu yace basai Naje ba, komai akayi yayi dai dai
Usman yace Yarima Mai martaba da kanshi yayi min magana akan muje in kaika ka gani.
Jin umarnin mai martaba ne yasa Yarima fad'in muje
Fita sukayi har zuwa gefen da akama Yarima dan gajeren ginin gidan sama, tsarin ginin ya had'u falo suka fara shiga wanda yana da girma Sosai, kofofin da suka gani a falon suka bude bedroom ne guda biyu a k'asa da kuma kitchen da dinning area, sai sama kuma d'aki uku ne da falo d'aya, ko wani d'aki yana da girma Sosai gidan dai yayi kyau Sosai
Usman yace ya Kaga gidan ina fatan yayi maka kyau
Yarima yace babu laifi
Usman yace gobe za'a zuba kaya domin da mai martaba yaso Asa sarkin katsina yace abarshi domin shi zai saka komai, duk da Mai martaba ya nuna a barshi amma sarkin katsina yace yariga yasai komai, d'azu masu deco suka zo suka duba komai gobe zasu zo su saka kayan
Yarima bai ce komai ba sai waje da yayi...
Ganin haka usman ya bishi yana fad'in Yarima gaba d'aya kayan da zaka saka an kammala su, ranan da gimbiya zata zo nan akwai kayan da zaka sa....
Tsayawa Yarima yayi tare da kallon usman yace akan wani dalili? Kayan da zansa ma sai an zaba min? Ni Mai yasa za'a kawo ta jibi, a Bari sai an d'aura auren mana
Usman yace Indai zaka auri y'ar gidan sarauta toh dole haka za'ayi wacce ba y'ar gidan sarauta bace za'a kawo ta Bayan an d'aura aure
Yarima yace I don't know why kuke d'aukan al'ada kaman addini
Usman yace haba Yarima ai dad'i ya kamata kaji, gimbiya ce fah za'a kawo maka
Yarima bai kulashi ba yayi gaba abunsa
Usman dariya yayi dan yasan Yarima baya son auren kawai dauriya yake
Yarima na shiga d'akinshi wayanshi ya kunna, yana kunna wayan sa'ko ne sukai ta shigowa bud'ewa yayi yaga na mutane ne Kala Kala sai kuma na princess dinshi, nata ya shiga ya fara karantawa.....
Yarima kasan hankali na a tashe yake? Ka d'aga min hankali shine ka kashe waya dan Allah Yarima ka kunna waya bazan iya bacci ba yau har sai...... Bai karasa karanta message din ba kiranta ya shigo
Murmushi yayi tare da kashewa sannan ya kira ta....
Tana ji ya d'auka ta fashe mishi da kuka
Yarima hankalinshi yayi mugun tashi dan jin Zainab dinshi na kuka
Yace my princess what happen? Plz stop it.
Batai magana ba sannan bata daina kukan ba
Ido ya lumshe dan baya son kukanta ko kad'an, yace tunda ba zaki shuru ba gani nan zuwa yanzu
Da sauri tace ni karka zo, kasan zan damu shine ka kashe waya kasan tun yaushe nake cikin damuwa, dan Allah Yarima karka karamin irin haka bazan iya jura ba Ina Sonka Yarima ban son wani abu ya sameka n.... Shuru tayi cikin jin nauyin abunda taita fad'a gashi ance magana zaran bunu
Yarima kam jin kalmanta na karshe yasa shi jin wani irin dad'in da bai taba jiba, ina Sonka Yarima, ban son wani abu ya sameka, murmushi yayi tare da fad'in ina jinki....
Kit ta kashe wayan domin wani irin kunya taji, tana kashe wayan ta Fara dukan kanta kai na kwafsa... Shuru kuma tayi tana mamaki yau itace take jin kunya dan tace Tana son wani, ikon Allah ita da take tubewa tsirara gaban namiji duk bata ji kunya ba sai dan tace Tana son Yarima. Kai gaskiya Yarima kai daban kake Sonka a jini na yake.
Yarima kam jin ta kashe wayan yasa ya saki wani irin murmushi mai cike da farin ciki kara kiranta yayi....
Ido ta bud'e dake lumshe tare da d'auka bata ce mishi komai ba
Yarima yace kara fadamin abunda kika ce d'azu
Tace Mai nace ni na manta
Yace oh I see, bari in tuna miki...
Da sauri tace Yarima saida safe bacci nake ji
Murmushi yayi dan yasan so take ta zille bata son ya tuna mata... Jin ana mishi nocking yasa yace ok baby good night dream about me, nd tell me tomorrow yana fad'in haka ya kashe wayan tare da tashi dan yaga Waye ke mishi nocking
Bariki bayan ya kashe wayan, murmushi tayi tare da fad'in ina Sonka Yarima gaba d'aya kasa na canza daka abunda na fito ina fatan kaima zaka amshi kaddara Kar kaki amsa kaman yanda akaki amsanta a baya hawaye ne ya zubo mata ..... Ganin tunanin da bata son yi yana son tayi shi yasata tashi tayi waje dan bata son tunawa da baya ko kad'an
Yarima bayan ya bud'e kofa sisters dinshi ya gani su duka, wani irin murmushi ya saki cikin jin dad'i tare da fad'in saukan yaushe?
Hafsat tace bros tun dazu suka zo, suna ta jiranka baka dawo ba
Salamatu tace wai ina kaje ne
Yace Kai sis wannan tambayar ai sai ku Bari a gaisa dariya duka suka saki tare da shiga falo din suka zauna
Yarima kallon y'an uwanshi yake yana jin dad'i, yau gasu su duka sun had'u, rukkaya, salamatu, Fatima, nd lil Hafsat dinshi, yarima yace shine kuka zo da wuri haka?
Fatima tace bikin fah saura kwana biyar Aini da naso inzo tun yana sati biyu
Dariya Yarima yayi Sosai kaman ba shiba, yace sai kace Kece maman ango ba
Tace ai yayar ango kaman uwa ce
Yarima murmushi yayi
Zama sukayi suna ta fira cikin so da kauna tare da tsara irin abubuwan da za ayi duk da dama sun shirya komai,
Shidai Yarima jinsu kawai yake dan baya son ana firan bikin kwata kwata
*******
Katsina
Gefen amarya wato gimbiya zinatu Anata shirye shirye Sosai musamman ma ita amaryan inda take ta gyaran jiki
Gimbiya zinatu ce a d'aki daka ita sai wata kawarta kallo d'aya zaka ma kawar ka gane itama suna da sarauta domin yana yin shigarta da kuma yanda takeyi alaman akwai giyan sarauta akanta, y'ar sarkin bauchi ce yarinyar gimbiya Amina
Kallonta gimbiya zinatu tayi tace my love kina ganin duk abunda na tsara zai bada matsala kuwa?
Gimbiya Amina tace bana tunani amma Idan kika wuce gonarki zai iya bada matsala dan haka kiyi taka tsan tsan
Murmushi gimbiya zinatu tayi tace karki damu, baza'a samu matsala ba, tare da d'aga ma gimbiya Amina gira
Gimbiya Amina wacce take magana kaman bata son yi tace ina fatan haka, dan Idan aka sami matsala daka Wajanki toh karki ce ban fad'a miki ba
Murmushi gimbiya zinatu tayi tace, haba haba ai ko d'aya na iya taku na
Gimbiya Amina tace da sauranki dai domin naga kina ta rawan kai nidai ki kiyaye tana fad'in haka ta tashi tayi toilet dan tayi wanka
Ganin ta shiga toilet yasa gimbiya zinatu fad'in my love ko rigima..... Toh fah wannan wani abu ne ake cewa gimbiya tayi taka tsan tsan????
**********
Gaba d'aya masarautar Zazzau ta kidime wajan hidiman bikin tilon d'anta guda d'aya wato yarima Aliyu d'a d'aya namiji a wannan masarautar mai albarka
Yau za'a kawo gimbiya zinatu cikin wannan masarautar ita da y'an uwanta har sai Bayan an d'aura aure zasu wuce abar amarya a nan, an ware musu gefe guda .
Yarima ne zaune akan gadon d'akinshi yana ta faman yin tsaki ga kayan da zaisa an ware Mai, gashi yana ta kiran gimbiyarshi Zainab wato bariki taki d'auka message ya Mata tare da fad'in
Pick my call
Reply ta mishi da fad'in
Sorry I can't pick your call now har sai bayan bikin ka karmu shiga hakkin amarya
Yana karanta message din ya buga hannunshi biyu domin yana bala'in son jin muryanta, gashi daka yau babu inda zashi har sai an d'aura aure, tashi yayi tare da fad'in Indai bazaki d'auki wayana ba dole In Karya wannan al'adan inje in ganki tunda ba addini bane.... Shuru kuma yayi ance gimbiya nan da 30mnt zasu karaso kuma shi zai tarbeta... Dan shuru yayi yana nazari d'aukan key din mota yayi daka gani shi kadai zai fita yace I have to see my princess
~MARYAM OBAM~
*BARIKI NA FITO*
*BY*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(Maryam Obam)*
*https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/*
*WWW.Maryamobamnovels.com*
*Wattpad @maryam-obam*
*Instagram@maryam_obam*
*MARUBUCIYAR*
*1)FATIMA ZARAH*
*2)DUKIYAR MARAYA*
*3)BA'KIN ALJANI*
*4)BANDA ZABI*
*5)AMINIYA TACE*
*6)KISSA KO MAKIRCI*
*7)SAINA AURESHI*
*8)SUHAILAT*
*9)TAMBARIN TALAKA*
*10)JAWAHEER*
*11)MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*
*AND NOW.... BARIKI NA FITO*
*DEDICATED THIS PAGE TO....*
*HAJIYA NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*
*PAGE 24*
Fita yayi ya bud'e kofarshi ganin fadawa a wajan yasa yayi tsaki, domin ya tabbata bazasu Bari ya fita shi d'aya ba and inya fita dasu akwai matsala, dan shuru yayi sannan ya dake tare da fitowa,
nan suka zube suna gyara kimtsa Allah ya taimaki Yarima Mai jiran gado takawarka lafiya.....
Dakatar dasu yayi alaman ya isa, gaba yayi suka tashi suna kokarin binshi ya dakatar dasu tare da fad'in bana bukatar ku bini.
kansu na k'asa suka amsa da fad'in komai Yarima yace dole mubi
Murmushi yayi cikin jin dad'i tare dayin gaba, mota ya shiga kiran VENZA gaba d'aya motar tinted ne baka ganin wanda ke cikin motar saboda tinted din but na motar na ganinka, harya tada motar saiga
Usman nan kaman daka sama bud'e motar yayi ya shiga, tare da fad'in ina zaka? Gimbiya ta karaso kai ake jira
Yarima Aliyu tsaki tayi tare da kashe motar ya fita cikin takaici
Ganin ya fita yasa usman binshi a baya
Direct d'akinshi ya shiga kayan da akace shi zaisa in gimbiya tazo shiya sa, sannan ya fito a falo yaga usman baiko kulashi ba yayi waje abunshi
Ganin haka yasa usman ya bishi a baya yana murmushi.
Koda Yarima ya fito fadawa suka bishi direct wajan motocinshi ya nufa suka bud'e Mai ya shiga, usman shima da sauri ya shige aka ja dan zuwa gidan sarkin katsina dake nan domin suje su tawo dasu.
Koda suka karasa duka mutane suna mota, gimbiya ce ta fito fadawa suka mata Iso har motar da Yarima Aliyu yake ta shiga ta zauna a baya, usman kuma ya koma wata motar
Gimbiya zinatu Bayan ta shiga ta kalli Yarima cikin murmushi tare da fad'in wow my handsome....
Ido ya rufe cikin takaici, jiba yanda take abu a gaban driver
Jan motar akayi suka fara tafiya, hannunta tasa cikin na Yarima
Kallon hannun yayi tare da kallonta ya watsa mata wani irin kallo da sauri ta cire hannunta ganin irin kallon da yayi mata, ganin yanda ya d'aure fuska yasa taji ya bata tsoro yasa ta kame bakinta tayi shuru
Bayan sun karasa masarautar tasu, aka bud'e musu Mota suka fito, su mum ne a tsaye dasu fadawa domin tarban su, gimbiya da Yarima suka fito tafiya suke a tare har inda aka ware musu, wajan babba ne gefen gimbiya da kawayenta babba ne sannan gefen danginta shima daban, Bayan gimbiya zinatu ta shiga ciki zama tayi Yarima fita yazo....
Tayi caraf tace Yarima ba yanzu zaka fita ba sai wani ya shigo
Yace Aiba gadinki aka bani ba yana fad'in haka yasa Kai ya fita a falo yaga su mum suna kokarin shigowa ciki
Mum ganin ya fito tamai wani irin kallo alaman ya koma, ranshi a jagule dole ya koma ciki, tare suka shiga gimbiya zinatu gaida mum tayi cikin girmamawa
Mum amsawa tayi tare da fad'in tubarkallah, su Hafsat zama sukayi suna dan Jan gimbiya da fira duk da tana yi tana d'an jin kunya kaman dagaske, mum ita da Yarima suka fita
Mum d'akin yarima sukayi tace Yarima Wai mai yake damunka ne? A haka kake son in bari ka kara aure jiba yanda kakema wannan ma Anya zakai adalci kuwa?..
Da sauri yace mum kiyi hakuri, yau raina a bace yake amma ai kin San your son zaiyi adalci mum
Murmushi mum tayi tace waya batama Yarima rai?
Dan shuru yayi Kafin yace mum Zainab taki picking calls dina, wai sai Bayan biki na, gashi babu inda zani Har sai an d'aura aure
Murmushi mum tayi danta gane itace wacce d'an nata yake so, tace bani number dinta in kira maka ita..
Kaman yana jira da sauri ya karanto ma mum number din, dialing mum tayi ringing biyu bariki ta d'auka tare dayin sallama dan tunda taga number din take tunani dan taga special number ne sai yasa tayi sallama
Amsawa mum tayi tare da fad'in my daughter, Yarima ya kawo karanki kinki d'aukan waya.
Jin haka yasa ta gane mum dinshi ce, da sauri ta gaida mum cikin girmamawa.
Amsawa mum tayi tare da bama Yarima wayan sannan ta fita
Yarima yace my princess do you know how worry I am right now? Wannan wani irin punishment ne haka? Kin San zan shiga damuwa Sosai na rashin jin muryanki
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 22