Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tana sheƙi da ɗaukar hankalin duk mai kallo. Sun cika tsaleliyar rigar jikinta tamkar za su fito waje, Gashin kanta baƙi sidik mai ƙyalli da sheƙi ya zuba har izuwa kan kafaɗunta.

Haƙiƙa duk inda kyawu yake wannan budurwa ta kai maƙura domin duk irin tsantsar kyawu na Sulairat da ta yi arba da wannan kyakkyawar halitta sai da ta raina kanta ta tabbatar da cewa gaba da gabanta aljani ya taka wuta.”
Ba wata ba ce wannan kyakkyawar budurwa da ke kishingiɗe a cikin keken dokin ba face Sarauniya Abidat.
Sulairat ta ƙurawa budurwar idanu ta sa kare mata kallo, a sannan ne ta fahimci cewa wannan budurwa ba wata ba ce face Sarauniya Abidat wacce take neman ta ruwa a jallo.
Nan fa zuciyarta ta kama tafarfasa tamkar za ta ƙone kuma ta ji ƙiyayyar Abidat ta daɗu ainun a zuciyarta.
Ya yin da ya zamana cewa sarauniya Abidat da dakarunta sun matso daf da inda Sulairat take tsaye, sai Sulairat ta hango wani zabgegen kyakkyawan saurayi jikinshi ko riga babu face bante da ya rufe cibiyarshi zuwa cinyarshi, gashin kanshi ya zubo izuwa kan fuskarshi, hannayenshi da kafafuwanshi sanye suke cikin da sasari na baƙin ƙarfe yana jan keken dokin da Sarauniya Abidat ke ciki a maimakon ace dawakai ne ke janye da keken.
Nan fa Sulairat taji ta kamu da matuƙar tausayin saurayin, kuma ta tabbatarwa da kanta cewa, tabbas duk inda mutum ke tsammanin zaluncin Sarauniya Abidat ya wuce nan.
Ana cikin wannan hali ne wannan kyakkyawan sarauyi da ke janye da keken dokin ya dago da kanshi sama, ya kalli inda Sulairat ke tsaye sadda suka yi arba da fuskokin juna sai nan take a karo na farko a rayuwarsu suka ji sun kamu da matuƙar ƙaunar junansu, Sulairat ba ta san sa’adda ta sakarwa sarauyin wani tattausan murmushi ba mai tattare da tsantsar so da ƙauna.
Bisa mamaki sai Sulairat ta ga saurayin ya mayar mata da martanin murmushin, kuma ya tsaya cak daga jan keken dokin yana ci gaba da sakar mata lallausan murmushi.
Al’amarin da ya yi matuƙar ɗaurewa Abidat kai kenan, kuma ya fusata ainun ta dakawa badakaren dake kula da keken dokin tsawa.
Abin da ya ɗaure mata kai kuma ya bata mamakin shi ne ita dai ta duba ba ta ga komai ba amma mene ne ya sanya bawa Himlas kw kallon wajen
yana murmushi, abin da ya fusatat a kuwa shi ne ta ya Himlas zai daina tuka keken dokin.

Kafin sarauniya Abidat ta gama rufe bakinta badakaren dake kula da keken dokin ya daga bulalarshi sama ya zabgawa bawa Himlas, take inda ya dake shin ya dare jini ya yi tsartuwa ya zuba a ƙasa, amma har sai da badakaren nan ya yi mashi bulalar fiye da talatin amma Himlas bai daina kallon wajen da Sulairat take ba yana yi mata murmushin.
A ɓangaren Himlas kuwa, babban abin da ya ɗaure mashi kai kuma ya ba shi mamaki shi ne gashi dai kuru-kuru dakarun sarauniya Abidat na kallon na Sulairat amma ba su yi yunƙurin cutar da ita ba.
Koda Sulairat ta fahimci cewa matsawar wannan saurayi bai daina kallonta ba to wannan badakare ba zai daina dukanshi da bulala ba.
Sai kawai ta juya ta nufi hanyar da za ta fitar da ita daga birnin tana mai waigen saurayin suna jifan junansu da ƙayataccen murmushi mai tattare da tsantsar soyayya.
Sai da Sulairat ta ɓace ɓat! Sannan bawa Himlas ya yunƙura cikin juriya da jarumtaka ya ci gaba da jan keken dokin, a lokacin da raunukan da badakaren ya yi mashi suka shiga yi mashi zugi da raɗaɗi, ga zafin rana na ƙona tafin kafarshi.
Komai rashin imanin mutum babu yadda za a yi ya ga bawa Himlas a cikin wannan hali face ya kamu da matukar tausayinsa.

Mu haɗu a babi na hudu domin cigaban wannan ƙayataccen littafi.
Daga mai ɗebe maku kewa a kullum da koyaushe.
MANSUR USMAN SUFI
Sarkin Marubutan Yaƙi
08137237071
KARSHEN ZALUNCI book 2 end
Babi na hudu
Rubuta labari
MANSUR USMAN SUFI
Wthapp number
08137237071
A can dajin Baitul-Shazwas al’amarin Sulairat kuwa tun sa’adda ta fice daga birnin Sin zuciyarta cike da matuƙar ƙaunar bawa Himlas, sai ta ci gaba da saƙe-saƙe a zuciyarta har ta isa dajin Baitul Shazwas, da zuwanta sai suhaimata da zakanya Juraima suka tare ta cikin tsananin farin ciki suna yi mata sannu da dawowa.
Da yake a wannan lokaci duhun magariba ya kawo kai Suhaimat ta shiga haɗa masu abin kalaci, bayan da ta kammala ne sai ta zauna tare da ‘yarta Sulairat domin su fara cin abincin.
Suna fara cin abincin ne Suhaimata ta lura cewa Sulairat na cikin damuwa, domin har sai ta yi loma biyar ba ta yi guda ɗaya ba, don haka sai kawai ta dube ta ta ce “Ya ‘yata abar alfaharina shin ina dalilin wannan damuwa ta ki?”
Koda jin wannan tambaya sai Sulairat ta yi murmushi ga mahaifiyarta sannan ta ce “Babu wani abu da yake damuna ya immi kawai sai ina tuna irin zaluncin Sarauniya Abidat ne.”
Suhaimat ta yi murmushi da yake nuna fahimtar wani abu game da furucin ‘yarta ta dube ta a karo na biyu ta ce.
“Ya ‘yata bai kamata ace kin ɓoye mani gaskiyar abin da yake damunki ba, domin kar ki manta cewa baki da kowa a duniya face ni kaɗai, bisa ga yadda fuskarki ta nuna alamu ba komai ne ya haddasa miki damuwa ba face tarkon soyayya ko ba haka ba ne?.”
Koda jin wannan batun sai kunya ta kama Sulairat ta sunkuiyar da kanta ƙasa tana mai cewa, “ki gafarce ni ya ummina, haƙiƙa na yi kuskure da na ɓoye maki gaskiyar abin da yake damuna.”
Suhaimat ta dafa kafaɗun ‘yarta Sulairat da hannayenta biyu ta ce, “Ya ‘yata ki yi sani cewa ba wai zan hana ki ki yi soyayya ba ne, sai dai ina gargaɗin ki da ki kiyayi so, domin babu komai a cikinsa face tsantsar wahala da takaici.”
Cikin alamun matuƙar mamaki Sulairat ta dubi mahafiyarta ta ce, “Ya Ummina shin ta ya ya so zai zama tsantsar wahala da takaici, bayan cewa rayuwar ɗan adam tana tabbata ne idan akwai so.”
Suhaimat ta yi lallausan murmushi mai taushi a gareta ta ce, “Kwarai kuwa maganarki gaskiya ce amma da a ce kin karanta hikayar manyan sarakunan duniya uku dake cikin KUNDIN HIKAYA haƙiƙa da kin gasgata abin da na faɗa miki.”
Da jin hakan sai mamaki ya kama Sulairat ta tambayi kanta a cikin zuciyarta tana cewa, “Shin me ya faru da manyan sarakai uku me so ya zamo masu a rayuwa?”
Amsar tambayoyin da Sulairat ta kasa bawa kanta kenan kawai sai ta ɗauraye hannunta da ruwa a cikin wani ɗan ƙaramin akushi, sannan ta je inda shimfiɗarta take ta kwanta, domin ta huce gajiyar da ke tattare a jikinta, amma sai ta kasa rintsawa, ba komai ne ya haddasa hakan ba face tsananin bege da tunanin bawa Himlas, domin duk abin da ta kalla a kogon dutsen sai ta ga fuskar bawa Himlas take gani yana yi mata murmushi mai taushi, haƙiƙa Sulairat ta yi zurfi a kaunar bawa Himlas wacce ba za ta taɓa jin kira ba, haka ta kasance a cikin wannan hali har barci ya yi awon gaba da ita. Wannan shi ne abin da ya faru da Sulairat bayan ta dawo daga ziyara izuwa birnin Sin.

A can brinin Sin kuwa, washegari tunda duku-dukun safiya fadar Sarauniya Abidat ta cika ta batse da jama’a maza da mata yara da manya, duk inda mutum ya kalla kawunan bil’adama ne rututu babu masaka tsinke tamkar dandazon kiyasai.
Abin tambaya anan shi ne ko me ya sanya jama’ar barin gidajensu suka halarci wannan fada tunda duku-dukun safiya haka?.


Ba komai ne ya sanya hakan ba sai domin a yau ne sarauniya Abidat za ta yankewa baiwa Sunaifa da bawa Himlas hukuncin kisa ta hanyar sare masu wuya.
Bisa wani BOYAYYEN AL’AMARI da ta gano a cikin halarar tsafinta a daren jiya, abinda ta gano din kuwa shi ne.
Ba wani abu bane ya sanya bawa Himlas yake wannan murmushi a jiya a lokacin da suke tafiya a cikin kasuwa ba har ya dai na jan keken dokin da take kai ba face arba da ya yi da Sulairat, har suka kamu da soyayyar junansu.


Abin da zai ƙara tabbatar maka da hakan shi ne idan ka yi duba izuwa ga waɗansu manyan diraku da ke tsakiyar fadar, za ka yi arba da bawa Himlas da baiwa Sunaila ɗaure cikin sasari na baƙin ƙarfe hannu da ƙafa.
Fiye da tsawon rabin sa’a jama’a na cece-kuce kowa na faɗin albarkacin bakinshi bisa jinkirin fitowar Sarauniya Abidat.
Ana cikin wannan hali ne sai aka jiyo bushin algaita haɗe da bugun tambura daga cikin gidan sarauta alamar ga Sarauniya Abidat nan tana gab da bayyana.


Jim kaɗan sai ga Sarauniya Abidat tare da muƙarrabanta sun kunno kai izuwa cikin fadar waɗansu gabza-gabzan samudawa dakaru ma’abota baƙaƙen tufafi na take masu baya, a wannan lokaci sarauniya Abidat tana sanye da shuɗiyar alkyabba mai ratsin ruwan zinare da ta kama jikinta, surorinta suka bayyana ainun kanta sanye da kambu na sarauta fuskarta a murtuke babu annuri.
Kai tsaye ta huce izuwa inda karagar mulkinta take ta taka matattakalar fadar ta juya tana mai fuskantar jama’a, nan take fadar ta yi tsit tamkar mutuwa ta gifta.



Sarauniya Abidat ta sake murtuke fuska tamkar an aiko mata da SAƘON MUTUWA ta buɗi baki cikin kakkausar murya sannan ta ce, “Ya ku jama’ar wannan fada tawa mai albarka ku yi sani cewa, ba komai ne ya sanya na taraku anan ba sai domin ku ganewa idanuwanku irin hukuncin da zan yankewa bawa Himlas da baiwa Sunaila bisa mummunan laifin da Himlas ya aikata mani na kin bayyana min abokiyar gaba ta Sulairat ‘yar marigayi sarki Urwat na birnin Nurul-Kusuf a lokacin da yake jan keken doki na a cikin kasuwa.”
Sa’adda sarauniya Abidat ta zo dai-dai nan a jawabinta sai fadar ta kaure da cece-kuce kowa na faɗin albarkacin bakinshi.
Zukatansu cike da matuƙar takaici gami da baƙin ciki bisa hukuncin da Abidat za ta zartarwar bawa Hilmas da Sunaifa.
Ya yin da Sarauniya Abidat ta ga fadar ta kaure da hayaniya sai kawai ta daga hannunta sama, jama’a suka yi shiru, sannan ta ci gaba da cewa.
“Sanin kanku ne cewa a iya tsawon rayuwata ba a taɓa aikata mani laifi mafi muni da ya huce wanda Himlas ya aikata min ba, saboda haka a yanzu zan zartar masu da hukuncin kisa ta hanyar sare masu wuya.”

Koda gama faɗin hakan sai sarauniya Abidat ta koma kan karagarta ta hakimce, kawai sai wani basamuden ƙato ya zare wata sharɓeɓiyar takobi a gadon bayanshi mai tsawo da kaifin tsiya, ya durfafi inda Himlas da Sunaifa ke ɗaure, yana huci tamkar zai ci babu ya yin da ya isa daf da inda suke sai kawai ya daga takobin domin ya datse wuyan bawa Himlas, a dai-dai lokacin da baiwa Sunila tare da wasu daga cikin jama’ar fadar suka fara zubar da hawaye saboda tausayi.

SHIN WANNAN BASAMUDEN ƘATON YANA SARE WUYAN BAWA HIMLAS DA BAIWA SUNAILA?

SHIN YAUSHE NE SULAIRAT ZA TA ƊAUKO TAKOBIN SAIFUL-IMFAL DAKE CIKIN DAJIN BAITUL SHAZWAS?

YAUSHE NE ZA TA SHIGO HAR CIKIN BIRNIN SIN DOMIN TA ƊAUKI FANSA AKAN SARAUNIYA ABIDAT?

A WANE HALI ZA TA KASANCE NA KAMUWA DA MATUKAR SOYAYYAR BAWA HIMLAS?

Mu haɗu a ƘARSHEN ZAMUNCI littafi na uku domin jin cigaban wannan ƙayataccen labari.
Daga mai ɗebe maku kewa a kullum da koyaushe.
Mansur Usman Sufi
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2

Please Login or Register in order to submit comment