jameel ne yayi karfin halin budewa dasauri yabar gaban kofar aikuwa dan malm ghali da garba suka rufto arce suna wuce malm jameel da umma aina u domin kuwa ko ganinsu ma basuyi ba fatansu kawai shine susami gurin tsira. Aikuwa dakin umma suka fada garba ne yadanna sakata yana xubewa jikin ghali ajigace.
Umma da malm jameel suka biyosu umma nakiran
"Aa dan malm wai me kuke yi haka meyafaru.
Shuru bawanda yayi magana malam ne yamatsa jikin kofar yana dannawa
"Dan malm bude min kofar nan nace kuxo kubude min kofar nan naji me nene yafaru ko bakwaji nane garba?
Garba jin ankira sunansa yamike jikinsa narawa yamatsa jikin kofar
"Malam dan Allah kuntabbar babu kowa atare daku?
Umma takalli malm shima ita yake kallo da mamaki yabasa amsa
"Bakomi mukadai ne bude min kofar inji abin dake faruwa daku.
Dan malam ne yamike da sauri yana rike hannun garba
"Kuttt kama isa wlh baka isa kamana sagegeduwa da rayuwa ba akan me uban waye yafada maka malam namu ne wlh itace ta rikide take muryarsa kuma wlh duk kashe mu xatayi baxa tabarmuba dan Allah karka bude.
Garba ya koma kusa da dan malm yaxauna jiki na rawa
Mlm yaji duk maganar dasukeyi donhaka yafahimci komi Ahankali yakalli umma yana murmushi tace.
"Aa malm ya anacikin wannan hali yara sunshigo ba ahayyacinsu kana kallo amma naga kana murmushi.
"Ai sun ban mamaki ne maganar danaji yara kamar su dan malm matasa dasunkai shekaru kamar ashirin da uku uku amma har yanxu yarinta da shiririta batasakesu ba hmmm bari naje masallaci nadawo don naga akwai sauran lokacin xansamu jam'i.
"Toh shikenan malm bari nima nayi alwala ai hankalina atashe yake ne banason abin tashin hankali yara kushigo mana haka abirkice kamar kunyi gamo toh Allah yakyauta.
"Amin aina u, bari naje
"Saika dawo malam Allah yatsare
Koda malm yafuto daga masallaci gida yayo kaitsaye
Umma yasamu cikin kicin tana sauke koko gefe kuma kosai ne acikin kula
"Sannu da aiki aina u yakuwa yaran nan sunfuto?
"Aa ban ga futowar su ba tinda kafuta dai kofar ko motsa ta basu kuma yiba,
"Kai wadannan yara da abin haushi suke amma shikenan yanxu kawo kayan abincin dakina kawai bari naje nacire babbar rigarnan naxo
Sallamar babah ne yadakatar da malm dake kokarin shigewa daki
"Mlm antashi lfy?
"Lfy kalau babah yagida
"Allahamdulillahi
Shuru can ta numfasa lokacin umma tafuto daga kicin shikuma Mlm yashige dakinsa
"Lfy klau babah gida shigo ciki toh
Babah tatsaya tana cewa
"Basai nashiga ba aina u dama akwai abin dake tafe dani banga garba kuma yace mun da asubah ana salla xanga yadawo toh ina xaune shuru shuru har xuwa karfe takwas toh saina futo nace bari naxo nan din ko sunan wajen dan malm.
Umma ta kalli babah tana karasa futo wa daga madafin
"Gaskiya kam gwara ma dakika xo ai domin kuwa wlh babah inafada miki kinga daki can suna ciki tin karfe biyar darabi suka fado gidan nan arikice suka shige dakin nan sika garkama sakata ko motsin kirki bamuji nasu anyi anyi su bude suyimana bayanin menene yafaru sunki saidai shashshe kan kukan su muji.
Babah dasu ta mike tana nufar kofar
"Subhanallahi malm kuma saikuka kyalesu aciki yanxu idan wani abu yasamesu fa haba dan Allah
Takarasa kofar tare dasa kuka
"Garba garba na kabude babah ce haba auta na idan kamutu nika mutar wa garbati
Garba dake jikin kofar dasauri yamike yana kiran
"Wayyo babah wlh ban mutu ba ina nan babah
Kafin dan malm da ghali su ankara garba yaxare sakatar yafuto jikin babah yafada yanasakin wani sabon kukan
Malam ne shiga yariko hannayen dan malm da ghali wadannan suka dassakare malm ne yashiga yimusu addu ah yana tofa musu kafin sudawo hayyacinsu garba baiyadda sun xauna ba yace ma babah sutafi haka taja hannun sa suka tafi sai lallashinsa take
*KING AND QUEEN WRITING CHAMBER*
*(Sarki da Sarauniya Writers)*
" *We Rule the World of Writing* "
https://chat.whatsapp.com/EJyDTUGRuWoCSv2hvGEPB3
https://facebook.com/groups/1756414801245712/
Bismillahir Rahmanir Rahim.
WANI NAMIJI
👉Hot love story 🧡
Na. 🌹Matar Yaya 🌹
page 8️⃣
💧wani bangare💧
Almustapha yakallesa
"Kaga kasan Allah M. Mahmud saika jirani tinda agidan nan ka kwana kuma kace xaka rigani futa tof kaga yanxu xanfuto wlh kajirani
Mufaddal ya kai kaice
"Um um xanje na duba malm jameel ne naji kuma ya aka kaya xandawo Allah saimu wuce kasuwar gori kuma nagode sbda na kwana awannan dakin naka dako cikakkiyar shara baya samu
Musty yayi dariya
"Ahkan dai jiya munsha ri har da yau
Mufaddal yasaki baki yana kallon musty kafin ya nufi waje sbda surutun yafara daminsa baya son aitajan magana gashi baisan wani barkwanci ba gwara ayi wasa kadan yafi.
Musty takyalkyale da dariya lokacin dayaji tashin mashin din mufaddal yana fadin
"Hooo wannan guy anyi muskilin gaske kai ace mutum sam shi bai iya wasa ba Allah yashiryeka M mahmud.
Lokacin da Mufaddal ya isa kofar gidan malm jameel babah kuma suka futo ita da garba mlm jameel naganin kiran Mufaddal yafuto
Dasauri Mufaddal yasauka amashin din yatsuguna
"Barka da futowa Mlm antashi Lfy?
" lfy kalau Mufaddal tashi tashi kaxauna ko.
"Masha Allah mlm angama ko
Mlm jameel ya numfasa sbda har yanxu yaran bawanda yafadi abindaya furgitasu duk wanda aka tambaya saiya ce bakomi anyi anyi sunki maganar komi.
"Mlm lfy kuwa kayi shuru.
Mlm jameel yakuma jin muryar mufaddal yamasa magana key din yadauko a aljihunsa yamika masa
"Allahamdulillah komi ya kammala ba matsala
"Toh mlm gasadaka kuma nagode nagode
Mlm jameel yakarba yana cire wasu yaba mufaddal sauran yana cewa
"Wadannan sun isa yaro amma duka ai yayi yawa ungo wannan ma yayi
Mufaddal yace
"Aa mlm baxan amsa ba kawai kabarsu ni Ne da godiya Allah yakara girma.
Yahaye liform dinsa yaja
Mlm jameel yashige gida yana kirga kudaden daga karshe yaga sunkai dubu talatin cis yasaki dariya sbda dama abincin gidansa yayi kasa ga axumi yataho.
Mufaddal yayi mamakin ganin gidan abude yana kokarin sa key ya bude kawai yaga kofar tai baya mamaki yayi kawai daga karshe yashigar da mashin din yakulle yayi falo.
Hammy kwance tsakiyar falon tana rike da cikinta wanda yake murda mata jitake tamkar mutuwa xatayi sumanta biyu tana farfadowa janciki take sosai akasa tana birgima ga hawaye na xuba a idaninta murya cike da rauni da takaici tafara magana.
"Wannan rayuwa wanne irine yasunan rayuwar danake yi menene matsayi na ni Halima Allah kasassautamin natabbata hakkin mai gidan nan ke bibiyana Allah kaduba yananin dana samu kaina arayuwar nan Allah kafutar dani daga sharrin mugun arnen nan Benuud
Jin wannan maganar cikin jigata da Mufaddal yayi abin yabasa tsoro kenan mutum ce agidan sa ke rayuwa abayan idaninsa bai saniba ashe ba jinni kemasa wannan ta asa takayan abinci ba, tab toh wacece wannan? Kwanan ta nawa agidan nan bansani ba?
Afusace yadanna kofar falon yashiga hammy kara takwalla lokacin da idaninta suka fada kan nasa tabbas mutum ne yakamata kuma afalonsa tabbas asirinta yau yagama tonuwa kafin mufaddal yakuma wani motsi hammy tasuma.
💧💧wani
bangaren 💧💧💧💧
kuka take sosai tana rike da jakar makarantar ta
dasauri mahaifiyarta tafito tana kamata
"fadwa mekikeyiwa kuka kuma keda kikafito makaranta ina direban ne
fadwa na shashshekar kuka tadubi mamanta
"anty umma sun dakeni sunkoreni wai yau baxa akaimu tareba waisai yakaisu sannan yadawo yakaini kuma latti zanyi
anty umma nagirgixa kai takama hannunta
muje nakaiki insha Allahu antynku baxata dake kiba
titi tafita tasamu me nafeef yakaisu saida taga shigarta ciki sannan tadawo daxummar taje anjima tadaukota dontasan tunda suka tsira hka toh masifa suke nema dasu
ummi ce tsaye bakin fat dinsu tana kwalawa anty umma dake shigowa harara tare da haibaici
"hummm tohh ashe dai su ohhh oh anataba abin hhhh karuwanci kai masifa ne Allah karabamu da karuwanci
wasu xafafan hawaye ne suka xubo afuskar anty umma tanagirgixa kai tawuce dasauri wajen ta tanamai addu ah acikin ranta Allah yabayyana mata Farin cikinta.
tsaki ummi tayi tana kokarin komawa fat dinta mustafa yashigo cikin shirin fita office
"aa ummi na wani abu kikesone?
tana girgixa kai tace
"aa mustafa naleko ne kawai jin kamar motsi ashe iskace takada kofar dasu hasiya suka fita sunmanta basu rufe min ba
"ohhh ummi kuntashi lfy ko saurima nake xanfita yau nadan makara wlh
"Allahamdulillahi
kace yauma baxakayi break fast ba ko haka jiyama kayifa toh dai karika tafiya dashi kawai amma banyarda da wannan rashin cin abincin nakaba yanxu kwa nan nanxakaga kanadan wuya
yanasosa kai
"kiba musa yakawomin kawai ummi xanfice tundaxu akemin waya.
"Allah yataimaka Allah yabada sa ah
"Amin ummina
barina duba anty umma
harara tabuga masa
"ficemin dagani kana saurin shine harsai katsaya bata wani lokacin acan svda me ko ance dole ne saika duba sun
yagirgixa kai
"aa ummi amm....
"ya isa kama hanya kafice agidan nan tun muna mu mu biyu wlh
baikuma cewa komiva yasakai inda mashin dinsa yake yaja yabude get yafice yadawo yakulle sannan yatafi sbda basu da megadi.
Allahamdulillahi anan nakawo karshen littafin WANI NAMIJI na daya muhadu alittafi na biyu insha Allahu taku akullum dako yaushe
👇
Shamsiyya Adam
🌹Matar Yaya🌹
😘OUM ARYAN😘
08160375544 WhatsApp only
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels