Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 8
° Wasa-wasa sai da Adamu yayi sati yana ~ jinyar dukan da ya sha wajen aljanninsa ba tare – da ya leKa gidansu ba, yana kwance Salmanu na jinyarsa, yana yi masa famfon Kin zuwa gidansu ko sanar da su halin da yake ciki, wayarsa na hannun Salmanun shi yake zuwa ya . ce Hajiya na gaishe shi wai Kafarta ke ciwo shiyasa bata zo duba shi ba kasancewar Alh. yayi tafiya zuwa Enugu: . . Ba wannan ne kadai aikin da yake da wayar ba, yayi blocking din hanyar shigowar ko wane kira, duk sanda ya bushi iska kuma ya kan tafa maganganun cin mutunci da cin fuska hadi da nuna Kiyayya ya tura wa Salma a zuwan shi ne Adamu. Salmanu ya dauki wannan matakin ne dalilin abubuwa uku, na farko jin haushin yadda Alh, ya runtse ido ya ce ya raba shi da Salmianu, shiyasa a tasa iyawar yayi niyyar nuna musu tasu iyakar. ; Sannan abu na biyu ya san tabbas idan Adamu na gida sai an yi yadda aka yi ya ga Salma, abinda kuma Salmanu yafi tsana kenan yanzu a filin duniyarsa, Salma ta shiga jerin _ mutanen da ya tsana, saboda haka yake iyakar _ yin sa ya hana ta rayuwa da Adamu. . Sai dalili na karshe, ya sami wani Alaramma ya sanar da‘shi matsalar Adamu ta zargin da yake na an masa Sihiri, saboda haka kullum yake bada rubutu ana kawo wa Adamu, Salmanu na yi masa Karyar ai maganin bibikon aljanin da ya make shi ne Adamu bai taba shakkar abinda Salmanu_ke fada masa ba don Salmanu ya iya hila, saboda haka hankalinsa kwance yayi zamansa a gidan gonar nan, kuma gidan sana’ar bokancinsu da cutarsa ta dakatar dasu farawa. A can gida hankalin Hajiyarsa ne kadai yayi Kololuwan tashi saboda rashin ganin . Adamu, amma Alh. ya rantse ya kuma wallahi _ Adamu yana sane ya buya, kawai so yake ya nuna musu iyakarsu, don haka babu inda zai je nemansa. Hajiya ta so ta musa, amma kasancewar Alh. na iyakar KoKarinsa akan Adamu, kuma_ yawancin abinda ke hado su ma Adamun ne _bashi da gaskiya, sai kawai ta daure ta cije domin kar ta kware wa Alh. baya, musamman _ da yake yana ta kumfar bakin don shi Adamu_, ya buya, sai da ya sanya shi karade dangida maganar aurensa da Salma: sannan zai juya baya ya zo masa da rainin wayo, ya bace kowa in ya buga lambarsa ba zai same shi ba, sai shi , idan ya ga dama ya bude ya dinga aikawa da Salma baKaKen maganganu da nuna Kiyayya. “Na rantse da Allah, sati daya na cika in — ma bai dawo ba sai na daura aurensa da Salma sai dai idan ya ga dama yace ni ba jininsa bane mu raba hanya”. – ’ Wannan ne alwashin da Alh. ya dinga ci. cikin tsananta fishin da ke Kara tashin hankalin Hajiya mai son ta kare Adamu ko tayi umarnin a yi cigiyarsa. . Amma dai dole haka ta hadiye ta cigaba da kawaici, shi kuma Alh. ya cigaba da shirye shiryen aurar da Adamu cikin sati dayan da ya Kudurta, kuma ya himmatu cikawa, ya kuma cika a ranar da Adamu ya cika kwanaki bakwai . da Bacewa, ba tare da an yi gangamin tara mutane ba, hasalima su isu danginsu suka hadu da makwabta aka daura auren. A wannan sati dayan duk. zirga-zirgar da – su Salma zasu yi gidan bokansu sun yi abinsu, . Shi ya tabbatar musu aure an yi an gama, shi ya ingiza Alh. rasa kwnciyar hankali har sai da ya daura auren, sannan ya tabbatar musu Adamu idan ya dawo ba shi da wani katabus na – yunKurin bijirewa. ; . Ranar da Adamu ya cika sati dayan, da kansa ya ji hankalinsa yayi mugun tashi na buKatar zuwa gida. Tun da sanyin asuba ya gallabi Salmanu _ tafiya zai yi. Ba tare da son rai.ba Salmanu ya dinga Karfafa masa gwiwa, amma cikin siyasa ya . dinga ribatarsa har ya kai azahar sannan ya.bar shi ya tafi gida bayan sun ajiye ajandar.cewa – gobe da sanyin safiya zai fito aiki. cikin Karfin gwiwa sosai ya tunkari gidansu kai tsaye zai shiga yana dab da shiga soro suka yi kacibis da Alh. ya fito daga ’ gidan shi kuma zai fita. . Adamu ya ji wata irin mummunar faduwar gaba ta daki Kolin zuciyarsa. Gaskiya ba haka __ ya so ba, ba Alh. ya so fara gani ba, Hajiya yaso fara gani yadda duk yadda ya tsara ta zata tsaru, ashe yau Allah ya hukunto masa haduwa da abinda ba ya so. . “ Kawai sai rudewa ta sanya Adamu zubewa Kasa yana gaishe shi saboda tsabar rudewa, musamman da ya gan shi cikin fishi. Alh. yayi masifar cin magani, maimakon ya amsa gaisuwar kawai sai ya yafice shi yace . masa, “Zo mu je” . Tsoro ya Kara kashe Adamu da ya ga ba cikin gidan Alh. ya dosa ba, hanyar gidansa ya . dosa. : . Wani Karfin gwiwa ya shigi Adamu da ‘ wani tunani ya zo masa Kahon zuci, don me ma zai dami kansa da tsoron Alh. sai ka ce wani – Ubangiji? Bakinsa na rawa ya tambayi Alh. wanda ya riga yayi gaba, “Alh. ina za mu?” ‘ “in mun je sai ka gani~ Ya amsa masa ba cikin dadin murya ba. . ° Adamu ya Kara dakewa, “To ba zan iya shiga na gaisa da Hajiya ba – ~ tukunna? Gara na shiga ta gan ni hankalinta ya kwanta..”. . Cikin juyawa ya kalle shi fuskaatamke ~ Alh. ya amsa,, “In kwanakin sati da kayi baka gidabata fadi ta mutu saboda bata ga fuskarka ba ai, rabin awa ko awa daya da zaka yi yanzu ba zai sa ka dawo ka tarar ta mutu ba” . Adamu na jin haka ya san Alh. ya hadiyo, don haka sai ya ja bakinsa ya rufe, a ransa_, kuma ya Kudurta rashin kirkin da zai yi in an nemi raina masa wayo. Ya tarar da gidan da hayaniya, amma dai suna shiga aka hau kallonsa saroro yana bin. Alh. a baya yana ta faman yake yana gaisawa da mutane har suka shige dakin Alh. — Alh. ya shige bandaki shi kuma ya nemi kujera ya zauna ya ci magani yana ta faman muzurai da saKe-sake har Alh. ya fito daga bandakin ya hakimce a kujera cikin kalar nasa « nuna bacin rai “Ba na so in ce daga ina kake Adamu, don kar in ji amsar rainin hankali ta janyo in tashi in kashe ka da mari” Adamu yayi fuska iyakar fuska, : “Ni dai namiji ne, bare a ce yawon duniya _ na tafi” . Mamaki ya cika Alh. wannan fa shi ake kira Karfin hali wai barawo da sallama, daga bisani kuma sai ransa ya baci ya Kura wa ido Adamu cikin bacin rai. Adamu ya muskuta ya sake muskutawa yana wani basarwa, – . “Wallahi fashina aka yi” – .Alh. ya jima bai tanka ba saboda tsabar haushi ya ma rasa me zai cewa Adamu, dama abinda ya guda kenan, ya san Adamu zai iya * zuwa masa da rainin hankalin da zai tunzura. shi, ilai kuwa. Sai faman kokawar hadiye fishinsa -yake, har ya samu ya hadiyu, ya sassauta fuska ya dubi Adamu, Fashi wane iri, su waye suka yi. fashin . naka?” . Adamu ya sake kawar da kai yana cin magani, _ * “Masu fashin mutane mana, sun ga ba zan yi musu amfani ba suka dawo da ni” Wannan tatsuniyar ta gajiyar da Alh. sosai, —ya ga kawai mafi a’ala ya rife babinta ya dauko babi na gaba. – Ya girgiza kai cikin halin ko in kula, . “Allah sarki, to Allah kiyaye gaba” Amin”? Adamu yayi fuska ya amsa. . Alh. ya sake gyara zama sannan ya gyara murya, “Na zaci lafiyarka lau ka guje mu shiyasa har na yi maka wani karambani” HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NGMUN TSAYA Alh. ya shige bandaki shi kuma ya nemi kujera ya zauna ya ci magani yana ta faman muzurai da saKe-sake har Alh. ya fito daga bandakin ya hakimce a kujera cikin kalar nasa « nuna bacin rai “Ba na so in ce daga ina kake Adamu, don kar in ji amsar rainin hankali ta janyo in tashi in kashe ka da mari” Adamu yayi fuska iyakar fuska, : “Ni dai namiji ne, bare a ce yawon duniya _ na tafi” . Mamaki ya cika Alh. wannan fa shi ake kira Karfin hali wai barawo da sallama, daga bisani kuma sai ransa ya baci ya Kura wa ido Adamu cikin bacin rai. Adamu ya muskuta ya sake muskutawa yana wani basarwa, – . “Wallahi fashina aka yi” – .Alh. ya jima bai tanka ba saboda tsabar haushi ya ma rasa me zai cewa Adamu, dama abinda ya guda kenan, ya san Adamu zai iya * zuwa masa da rainin hankalin da zai tunzura. shi, ilai kuwa. Sai faman kokawar hadiye fishinsa -yake, har ya samu ya hadiyu, ya sassauta fuska ya dubi Adamu, Fashi wane iri, su waye suka yi. fashin . naka?” . Adamu ya sake kawar da kai yana cin magani, _ * “Masu fashin mutane mana, sun ga ba zan yi musu amfani ba suka dawo da ni” Wannan tatsuniyar ta gajiyar da Alh. sosai, —ya ga kawai mafi a’ala ya rife babinta ya dauko babi na gaba. – Ya girgiza kai cikin halin ko in kula, . “Allah sarki, to Allah kiyaye gaba” Amin”? Adamu yayi fuska ya amsa. . Alh. ya sake gyara zama sannan ya gyara murya, “Na zaci lafiyarka lau ka guje mu shiyasa har na yi maka wani karambani” ZAMU TASHI Adamu ya dube shi cikin rashin fahimta, amma bai tanka ba. Alh. bai damu da shirunsa ba ya cigaba da Magana.. ~ “Kodayake ba za’a kira shi da karambani ba illa son in faranta maka ko kuma in cika maka wani burinka da _ Kodayake kafin yayi masa zancen aurensa da Salma ya zo da bakinsa da cin maganinsa har ya dan sassaki rashin kunyarsa da rainin hankalinsa. Kenan Karamin tabin kwanyar da ya same shi na nan take ne bayan jin an aura masa Salma. To bakin alKalami dai ya riga ya bushe, aure ne an riga an daura, yayi haukansa ya warke. Don haka Alh. ya share shi ya cigaba da yi masa bayani, “Ta bangaren Salma kuma kar ka damu, — na bawa Sa’a ‘yan wasu kudi ta y mata siyayya, babu abinda na ke nema a Bangarenka ~ sai halarci ta hanyar yi‘wa Salma adalci da riKe ta bisa amana, ka ga marainiya ce bata da kowa sai mu wanda ko ba kai ka aure ta ba kai mai tsayawa ne ciki-ba-hatsi ba ka Kwatar mata ‘yancinta idan mijin da ta aura ya danne”’ Da wannan nasihar Alh. ya sallami Adamu ya fito yana layi ya doshi gidansu. Zuciyarsa fanko ce baya tuna komai ko saKa komai, amma dai wani radadi-radadi daga can Kasa yana fuzgarta, sai dai ba ya nisa yake cin tuntube ya nuna ba komai. ” . Kafin ya je gida ya dinga jin kansa yana wata irin Kara tamkar yana shirin bindiga ko kamawa da wuta, kawai sai ya tsaya wani kanti a unguwarsu ya sai fuyo wata mai dankaren sanyi har leda hudu ya shiga da shi gida. . Hajiya na kakabin murnar zuwansa da Kokarin fashewa da kuka saboda ganinsa a hargitse, shi kuma yana mika mata ruwan ya tsuguna a gabanta cikin raunin. murya yana cewa, – “Hajiya zuba min ruwan nan a tsakar kaina kar ya kama da wuta” * Jikin Hajiya na bari ta karbi ruwan ta dinga fashe masa su a aka har leda hudu ba tare da ta damu da jika falonta da take yi ba ta dago kansa cikin fuskar alhini da jimami tana kallonsa, sannnan cikin raunin murya ta ce, “Adamu ina ka shiga ka bace?” _ Maganar da tayi cikin rauni ta Karasa raunata tasa zuciyar, ya ja jiki da Kyar ya isa kan tabarma ya zube yana shassheKar kuka. Hankalin Hajiya ya kai Kololuwan tashi, da sauri ta durKushe a gabansa tana tambayarsa cikin rudewa, “Adamu me ya same ka?” , Ya ji tausayin kansa da na Hajiyarsa wadda ta damu da shi ya ‘mamaye ransa, ya saki kuka mai nuna tsanantar Kunan rai, “Hajiya Alh. yayi min auren da ba zan taba farin ciki da shi ba har abada” : Kafar Hajiya na rawa ta silale ta nemi gurin zama tana sauke nishi cikin sauri, “Dama ba kai ka bashi damar ya aura maka Salma ba? Dama baka sonta Adamu?” Ta tambaya a rikice, . Ya amsa mata da rauninsa da kumaiyakar gaskiyarsa, “Nine, amma ban san abinda ya shiga cikin kaina na fadi hakan ba, wallahi ba Salma ce zabina ba, ban taba zabarta ba, ban taba mafarkin aurenta ba, kuma ban taba fatan ko a mafarkin in aureta ba” . Kan Hajiya ya so ya shiga dubu duk da a iyakar imaninta ta san iyakar gaskiyr Adamu kenan tunda yake furucinsa cikin kuka, sai ta rasa da Kalmar da zata yi amfani wajen karbar wannan Kalubalen nasa. Ta cigaba da zura masa ido galala shi kuma ya cigaba da. shassheKar kuka kafin ya zarce da cewa, “Na kasa cewa Alh. ba zan iya rike auren da yayi min ba, amma duk lokacin da kika sami sarari ki sanar da shi, ni dai ya tauye rayuwata ya kuma cutar da ni, ba Salma nake © so ba, wadda nake so ina yi mata son da ko wane hali aka rataye zuciyata ba za’a iya raba ni da son ba… kuma in na sami sarari zan iya ko ma menene da zai iya samar min da ita” . Bai jira cewar Hajiya ba ya mike yana . niyyar barin dakin. Gabadayan kan Hajiya ya kulle, a gigice , take kwarai, amma dai maganganunsa na Karshe sun zabure ta Karfin halin miKewa ta riko rigarsa kafin ya fice, cikin rawar murya ta ce, . . “Adamu zo ka fada min, wa kake so?” Ya dakata ba tare da ya juyo ba yace _… mata,“Husna nake so” . “Wacece haka?” _ Ta tambaya cikin nuna rashin fahimta. Ya kada kai idanuwansa na cigaba da zubar da hawaye, zuciyarsa na wani irin Kuna, . ya koma ya zauna yana kallon Hajiya da ta tsaya kansa hankalinta a tashe, “ita ce wadda tun tuni nake maganar ina so, akanta na ki karatun boko don in sami kudin d azan riKe ta…. Kai Hajiya ko me na zama akanta na zama, ko kuma nake shirin zama… ina fada miki wannan ne dan ki gane ban fara sonta don in daina ba…” ‘Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un” Kawai Hayjiya ke Ambato cikin tafa hannu = mai nuna alhini da nadama, tamkar ita ta yi wa Adamu auren dole take ji cikin ranta, ta kasa = yafewa kanta sakacin da tayi aka aura masa. abinda ba ya so. Ta matsa can jikin bango ta jingina da shi, “Adamu ni ban san abinda zan ce maka ba, hakuri zan baka ko kuma sakacinka zan nuna maka?” Ya sake miKewa tamkar kunama ta dalle shi yana girgiza mata hannu, “Kar ki ba ni komai Hajiya, ko Husna kika ba ni a yanzu ba zaki birge ni ba, don na san . Husna zata rage darajar son da ta ba ni in ta. tarar da wadda Kaddara ta aura min wato Salma, duk ku riqe abinda zaku fada min don ban ki karbar abinda aka ba niba wato Salma, amma dai ba zan kasa sanar da ku an cuce ni ba, ba zan kasa fadar ba a yi min daidai ba….” Ya sake ficewa daga dakin cikin fishi. Wannan karon Hajiya bata iya riKo shi ba, duk da ta fahimci ba cikin hayyacinsa yake ba, yakamata ita ma ta bar shi ya huce, yadda zasu fi fahimtar juna. . i ; ” Haka dai ta zauna tana ta kakabin alhini da fargabarta har lokacin da ta yanke shawarar * daukar waya ta kira Alh. su tattauna. . ********* Adamu bai damu da goge hawayen fuskarsa ba ma bare ya kintsa tafiyarsa ta Boye rashin nutsuwarsa ko tashin hankalinsa A dazu ya gama Kaddara kwanyarsa ta tashidaga aiki, amma a yanzu da ya gan shia. hanyar gidansu Husna ya tabbatar ko kwanyarsa zata manta komai ba zata taba manta Husna da abinda ya shafe ta ba. , . Har ya-isa Kofar gidan bai san abinda ya kawo shi gurinta ba, amma yayi imanin tunda zuciyarsa ta kawo shi ta san abinda zata fada. A hargitsensa ya sami yaro ya tura shi gidan yayi masa sallama da ita. Husna na kan kekenta da ta fito da shi tsakar gida tana ta faman dikin, yaron ya shiga da sallamarsa, ta toshe kunnuwanta da head phone tana sauraron wakoKin da ba su fice na soyayya ba, zuciyarta a rude take da tunanin ‘* Adamu har kwalla na tsattsafo mata tana goge abarta a saye. Kuma da yake tana hadawa da_= ~dan rausaya alamun tana jin dadin wakar da take sauraro babu wanda ya damu da gane cewa wuya take sha. “Wai Husna ta zo” Yaron ya sake, maimaitawa bayan yayi Sallama duk Husna bata ji ba, sai da Hajara ta fito daga kicin ta tambayi yaron, “Wanene yake kiranta?” ~ Yaron da yake irin fadi ba a tambayeka bane ya ce, “Wani saurayi ne, baKi mai dan kauri da tarin gashi, kuma na ga ma kamar kuka yake?” ~ _Kukan da aka ce yana yi ne yayi mugun jan hankalin Hajara ta yafito Husna cikin firgita, . #Ke shashasha, ki saurari yaron nan ya zo da maganar a kasa kunne a saurara” Husna ta ji haushin kiranta shashashan da Hajara ta yi, ta debo mita zata sauke Hajara ta tare ta, . , “Yanzu haka shi ma me neman naki rashin _ kunyar kika yi masa, na san yanzu sai ki zage ni… Sai kawai Husna ta saki baki tana kallonta – . cike da Kunan zuciya. . Hajara ta juya tana cewa yaron, “Ga ta nan ka sanar da ita saKon” Tana rufe baki yaron ya furta, , ’ “Wai Husna tazo in ji wani:..” Shi ma Umma ta tare shi, “Shi wai wa? Ka sanar da ita waye” ‘ Yaro kuwa ya gyara murya ya kwatanta mata Adamu. . ” Tunda ya ambaci’ mai tarin gashi ta ji numfashinta na neman daukewa, -zuciyarta ta dinga bugawa da sauri da sauri tamkar tana ambatar mata, Adamu ne! Adamu ne! Hajara ta zuba idon ta ga Husna ta kora mai kiran sai ta ga nan da nan ta saki dinki ta hau janyo ruwa tana wanke Kafa, a gurguje ta dauki hijabi ta yi waje. Kamar yadda ta zata, Adamu ta tarar wujiga-wujiga da shi tamkar an finciko shi daga bakin kura ba, ga shi ba, ba ga zuciyarsa ba wadda fuskarsa ta nuna alama, sannan itama kanta bata sha wahalar gane cewa kuka yake ba. ; . Ai jikinta na bari tamkar ta riKo hannun Adamu ta yafito shi, “Shigo shigo nan Adamu” Ba ta yi gaba ya biyo ta a baya ba sai ita ta sanya shi gaba suka shiga soron. Da sauri kuma ta shige cikin gida tanace masa, “Bari na kawo maka kujera” Adamu ya kasa Magana ne saboda yadda kuka ya Kara cika kansa. Ya tabbatar barin jikin da Husna ke yi da shi na so ne, to yaya zata ji idan ta ji cewa an aura masa kunduba – Salma? Duk yadda yayi Kokarin ya dake wa wannan tausayin sai da ya ci Karfinsa, hawayensa suka Kara araha a fuskarsa dan ma yayi namijin KoKarin hana sautin kukan fitowa. A haka Husna ta fito ta same shi, tana dauke da kujerar zaman dinkinta da kuma pure water mai dan Karen sanyi hade da tambulan din roba. Ta kula da Karuwar damuwarsa kuma . Zuciyarta ta Kara rauni, sai dai bata nuna hakan ba. Ta dire masa kujerar cikin kuzari ta nace. masa, ; “Zauna Adamu” Ba musu ya zauna. Ta huda pure water ta tsiyaye shi a tambulan din ta miKa masa, ‘Ungo sha ruwan sanyi hankalinka ya dan kwanta sai na ji me ke akwai” . Adamu ya kasa Magana, kirkin Husna ya sanya shi jin lallai an tafka masa asarar masoyiya, asarar da ba zai taba fanshewa ba. Sai da ya shaye ruwan tas, bata bar shi ya ajiye kofin a Kasa ba ta miKa hannu ta karba idanunta akansa tamkar in ta rufe ido zata bude ta ga ya Bace, . “Adamu

Chapter 5 of 8