Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hali.


idanunta ta dan juya, kafin tace "barci!", ta faɗa tana lumshe ido, "na hana ki ne ?", ya fada yana zama gefen bed, turo baki tayi kafin tace "to ba ka tashe ni ba", ta fada tana komawa ta kwanta, "ke ni bazaki kwanta min anan kina min tsamin dauɗa ba, tashi in kina son kiyi barci" ya fada yana gyara Agogon hannunshi,"karfe nawa ne ?",bai ko kalleta ba ya nuna mata Agogon da take manne a bango, hamma ta dan yi kafin tace "lokaci har ya zarta da yawa haka ?, Yaaah Shehi bari na watsa ruwa na bika Masallaci" ta fada tana miƙewa,bai ce mata koma ba har ta shige.


bata jima ba ta fito , tana goge jikinta, a gabanshi ta gama shirinta tsaf, gabanshi tazo ta tsaya , idanunshi ya watsa mata yana kallon yarda fuskarta tayi wani irin haske, sai haskawa take kamar fitila, miƙewa yy, gaba tayi da sauri bata bari ya shiga gaba ba, tana gabanshi yana bayanta har suka fita daga cikin main palo suka doshi waje,"aikin kenan abun da kuka iya kenan,kullum.kullum kuna liƙe amma har yau bb wani ɗan labari, Mtswww madamar da raina na koma Nigeria Wlh sai na raba Auren nan", har Sadiyerh ta ɗaga ƙafa zata taka ta kasa saukewa.



har bata san lokacin da tayi revers ta dawo baya ba, "Allah ya fiki Mushirika" tana faɗar haka tayi waje cike da tashin hankalin irin maganganun da Jadda take faɗa, to yanzu ita maye laifinta dan ta Auri Yaa Shehi ?, shin laifi ne dan ta Auri jininsu da zata mata wannan tsanar ?,.


bin bayan Yaaa Shehi tayi wanda dama shi bai ko tsaya ba, wucewarshi yy abunshi, wannan halin na Yaa Shehi ya yanzu ya fara ɓatawa Sadiyyerh rai, abubuwanshi yanzu haushi suke bata.
a matsayinta na matarshi bai kamata ace yana mata ko in kulaba, kan wani dalili nashi, so da dama a gaban idanunshi ana son ci mata mutunci amma baya kulawa,baya nuna damuwarshi, ta fara ƙoƙanto akan Alaqarsu shi ko dai baya sonta ne yasa yake mata wannan halin na ko in kula, tun abun baya damunta har ya fara damunta a wannan lokacin .


motarshi da take bude ta shiga,gefenshi ta zauna, rufewa aka yi suka fara tafiya,shiru tayi tana tunanin wannan halin nashi, mutum ace ko maganar kirki bata haɗaka dashi a matsayinsa na mijinka, tana iya ƙoƙarinta aka taga ta gyara halayen Yaa Shehi na rashin magana da ko in kula amma har yanzu ya kasa dainawa, wannan abu na mugun ci mata tuwo a ƙwarya.


har suka ƙarasa Masallacin da ya cika da mutane suna ta nafilfili da sauran nau'ikan Ibadu kala-kala, suna tsayawa ta fice daga cikin motar tana tafiya a hankali, har ta isa ƙofar mata, shiga tayi, chan ta dan zauna gefe da babu yawan mutane sosai .


Ajiyar zuciya mai karfi ta sauke, lokacin da taji zazzaƙar muryarshi ta daki dodon kunnenta, a hankali wata siririyae ƙwalla mai zafi sosai da ta rasa ta mace ce ta silalo mata kan kumatunta, bata damu da ta goge ba, ta ci gaba da abun da take.


"Sannu!" taji an furta daga saman kanta, a hankali ta ɗaga idanunta kalli mai maganar , Matashiya ce da bata wuce sa'arta ba , tana sanye da fararen kaya tass, tun daga kanta har ƙafarta duka nannaɗe suke ,in ka cire fuskarta bb abun da ake iya gani a jikinta, dan rigarte da rufe mata ƙafarta sosai har jaan ƙasa take, hannunta kuma na cikin kyakywar hijab dinta, wadda itama ta kasance fara, shiru Sadiyyerh tayi dan ba kasafai ta ci ka sakin jikinta da mutane ba,koma wanda ta sani balle wanda bata sani ba.


Hannunta mai sanye da safar hannu fara ta fiddo ta miƙa mata, cikin sanyin murya tace "Am Mrs Arman-Maleeq Lamiɗo Abdul-Azeez Arman-Maleeq," kara kallonta Sadiyyerh tayi tare da cewa "Mrs Arman-Maleeq Lamiɗo Abdul-Azeez Arman-Maleeq", ta fada tana haɗiyar wani yawu, wanda dakyar ta sameshi ta hanyar kalatoshi cikin bakinta, jinjina mata kanta tayi, tare da nuna mata Wata kyakyawar yarinya da bazata wuce 2 to 3 years ba, tana tsaye gefenta , itama sanye da fararwn kaya, kyakyace Yarinyar sosai, tana da zagayayyar fuska, idanunta dara dara blue dasu, hancinta siriri sosai, tana da ɗan karamin baki wanda bama zaka yi zaton tea spoon zai shiga ciki ba.


"Hafiza Arman-Maleeq Lamiɗo Abdul-Azeez Arman-Maleeq", ta fada tana kallon fuskar Sadiyyerh , "ke fa ya sunanki ?", inaaa Sadiyyerh bata san tana ma magana ba, tun bayan maganar farko wadda ta tarwatsa mata tunaninta.


taɓota tayi tare da cewa "kina lafiya kuwa", da sauri ta ɗago da idannunta da suka kaɗa tana kallonta, dauke hannunta da yake kan ƙafaɗarta tayi, cikin sanyi tace "Sunana Sadiyyerh", tana fada ta, kallon fuskawar wayar matar wanda kamar da gayya ta kunna power wayar haske tare da photon Yaa Shehi da ita suka bayyana, yana sanye da Shadda Blue black da Alƙyabbar shi fara tass , yana riƙe da hannunta, fuskarshi washe da murmushi , itama tana sanye da kaya kalar nata, har Alƙyabbar jikinsu Iri daya ce, tana gefenshi jikinsu na manne da juna.



Finger print ta sanya , tuni wani photon nasu ya bayyana akan Home Screen din wayar, suna tsaye bakin wani ruwa wanda da akama gurin shaƙatawa ne, suna sanye da kaya iri daya shi T-shirt Omo Blue da ratsin fari fari, sai wando fari, itama tana sanye da Gown Omo Blue da ratsin fari tun daga sama har ƙasa, kanta yane da farin gyale, hannunshi daya ya kama hannunta daya kuma ya dafa cikinta wanda ya bayyana ƙarara.



fuskarsu dauke da murmushin farin ciki, zallar tashin hankalin da take ciki ne yasa bata ma san lokacin da ta miƙawa Yarinyar da take tsaye hannunta rike da Chocolate tana sha ba hannu , hannunta Yarinyar ta kama tana kallonta, zaunar da ita tayi kusa da ita tana kallonta.


tsananin kamarta da Yaaa Shehi take haskowa kan fuskar Yarinyar, "Innalillahi wa'inna'ilaihi raju'un , Allahumma Ajrni fi Museebati", ta furta , tana jin wani abu na tokare kirjinta, har wani ji take kamar zata amayo wani abu mai nauyi, kamar butunbutumi haka ta zubawa Yarinyar nan idanu, tana kallonta, har lokacin da aka yi Sallah Asuba tana zaune a gurin.



A hankali ta fito daga cikin Masallacin tana tafiya ba tare da sanin in da take jefa ƙafarta ba, tsananin damuwa da tashin hankali ne kan fuskarta, sai yanzu ta fara tunanin abun da yasa baya kulata, ashe dan yasan yana da wata matar, baya bata kulawa, taya ma zai bata kulawa, alhalin achan wani side din yana bawa Yarshi da Matarshi, yaushe Yaa Shehinta ya koyi irin wannan cin Amanar, shi ya raineta tun tana ƙarama, bata taɓa hango rashin gaskiya cikin idanunshi ko a aiyukanshi ba, amma yanzu gani take gaba daya gaskiyar nan karya ce, ya ɓarar da gaba daya yardarta gareshi.



Sai a wannan lokacin ne ta gane cewa lallai kuka ma rahma ne, abun da take ji ya wuce gaban kuka, gashi tana son yin kukan amma ta kasa sakamakon tashin hankalin da take ciki, tayi tafiya mai nisan gaske a ƙafa, amma bata san tana yi ba, har sai da ta bar masallaci da nisa sosai, ta shiga wasu lungunan ma da batasan ko ta ina ta shiga ba,bata jin zata kuma iya mayar da kanta in da ta fito, sai a lokacin kuma idanunta suka tara ruwan hawaye.


zubewa tayi a ƙasa gaban get din wani gida, kuka mai karfin gaske ta sake, tana ɗurkusawa guiyayunta ƙasa, ta kifa kanta a kan cinyoyinta tana wani irin kuka wanda yake bayyanar da zallar ciwon da yake ƙasan zuciya, kukan take sosai babu mai lallashinta har bata san iya Adadin lokacin da ta dauka tana kukan ba.


miƙewa tayi tsaye tana goge idanunta da tsabar kuka har bata gani sosai, a hankali take tafiya tana kallon hanya dishi dishi, har ta fito titi, Taxis ta tara, sai ma da ta tare Taxis din ta rasa inda zata ce a kaita, tunda ita ba fita take ba, im ma ta fita da motar gida ne, duk inda zata ta dawo a ciki, laluɓen Wayarta ta shiga yi, amma abun haushi bb Wayar bata fito da ita ba.takaici duk ya ƙara mata yawa a zuciyarta, hkr ta bawa Mai Taxis din ta koma gefe ta zauna tana kallon yarda motoci suke wucewa, ga yunwar da take ji, wasa-wasa har rana ta fara yi tana gurin, duk wsnda zai wuce sai ya tsaya, yaji ko mai take so sai dai ko magana bata iyawa,dan da ta bude baki sai kuka ya taho mata, hakan yasa tayi gum.


Gently yake tafiya cikin dukkan natsuwarsa da kamalarsa, kyakyawan numfashi yake saukewa, yana ƙara baza babbar Alƙyabbar jikinshi, Zayn -Maleeq da su Yayah Muhammad suna bayanshi suna binshi a baya,ka rantse shine Yayan , Yayah Muhammad, saboda yarda ya fishi cika da kwarji.


da Sallama suka shiga cikim palon gidan, Amsa musu Sallamar na cikin palon suka yi, kafin su ci gaba da firarsu, sama Yaa Shehi yy , ba tare da ya tsaya ba, su kuwa sauran zamansu suka yi aka ci gaba da firar da su.


sun dade sosai suna fira, kafin Rayhana ta an kare da basu dawo da Sadiyyerh ba, kallon Mijinta tayi tace "Abbu ina Sadiyyerh ban ga shigewarta ciki ba ?", "Sadiyyerh kuma ?", ya fada yana duna bayanshi dan shi yama manta da ita kwata-kwata, "ai ba tare da ita muke ba ko ?", ya fada yana kallon su Zayn, jinjina kanshi yy yana kallon Rayhanar.


"Tun dare fa da suka fita da Yaaah Shehi bata dawo ba, duk mun dauka kuna tare har yanzu", Yaah Shehi ne ya ƙara fitowa cikin wani shirin fitar, kallon Rayhana yy yace "Sadiyyerh fa ?", ya fada yana dan shafa gashin girarshi mai yawa .


kallon-kallo aka shiga yi tsakanin Rayhana da Ayyana da Yaah Shehi, "Kamar ya Sadiyyerh fa ?, Sadiyyerh ba tare kuka fita ba ,yanzu ka dawo kace ina take, mai kake nufi ?", Ayyana ta faɗa tana kallonshi cikin ruɗu, gyara tsayuwarshi yy yana kallonta, sai dai ya kasa cewa komai , "kamin magana ma, ya zaka yi shiru ?, kar fa kayi musu sakaci da rayuwar Ƴa", ta fada tana kallonshi.


Ciki Ayyana ta yi ta shiga bincika gidan ko tana wani guri, gaba daya gidan ta bincike bata ganta ba, dawowa palon tayi gaba daya fuskarta ta bayyana zallar tashin hankali, "Sadiyyerh fa bata cikin gidan nan", kalmar da ta daki dodon kunnen Yaa Shehu kenan, da sauri ya ware manyan idanunshi da ya lumshe, gaba daya yan cikin palon suka miƙe suma hankalinsu ya fara tashi, gaba daya waya suka fara bubbugawa, Amma Yaah Shehi na zaune kamar butunbutumi bb wani alamu da ya bayyana akan fuskarsa wanda zai nuna maka cewar yana cikin damuwsa ko ya damu da abun da yake faruwa.



Idanun Ayyana da suka yi Jaazir ra watsawa Yaah Shehi, suna haɗa ido yy maza ya dauke idanunshi daga cikin nata, dan yy bala'in jin fargaba da bugun zuciya lokacin da ya kalli cikiin idanunta, "baka damu ba ko ?", ta fada tana kallo shi, bai ce mata komai ba, haka zalika bai kalleta ba, "Wallahi tallahi Maleeq wani abu ya faru da Sadiyyerh sai ka raina kanka, tunda kai taƙamarka Isgilanci da Wulaƙanci tare da rashin nuna damuwa , ace matarka ta Sunnah ka fita da ita amma ba zaka yi tunanin dawowarta ba, har kana ma da kwamciyar hankalin da zaka saki jikinka gar irin wannan lokacin amma bata gida baka san yarda take ba ?, Wlh tirrr da wannan halin naka, in haka Malunta da Sarauta take Tirrr da ita, bb kulawa ?, babu tausayawa ?, bb jin ƙai ?, bb nuna soyayya ?, damuwa bb , sauke haƙƙi ma babu, to me ne ne amfanin Auren tunda dukkan wani haƙƙi nata haka ƙoƙarin saukewa, dole zaka rabu da ita tunda kai baka da Ɗabi'ar Arziki", tana fadar haka ta fice idanunta sun ƙara mugun kaɗawa.


sanyayyan numfashi ya fesar yana mai lumshe idanunshi, tare da cusa yatsun hannunshi cikin kanshi, yana shafawa a hankali, akan fuskarshi ba zaka taɓa hango wani abu mai kama da tashin hankali ba, ko kuma wani alamu mai nuni da cewar akwai wani abu da yake damunsa ba", duk ficewa suka yi daga cikin Palom zuwa waje, kai tsaye gidahen TV .Radio . da Jaridar Saudia suka nufa domin bada sanarwa, cikin abun da bazai wuce 1 hour ba gaba daya Garin Saudia da makwabtansu suka dauki labarin Ɓatar matar Yaah Shehi Arman Maleeq , ko ina ka shiga cikin Social media zancen ake.


Yan sanda ma sun fara aikinsu na nemanta, bayan gama sun gama bada dukkan wani rahoto suka dawo gida, in da suka bar Yaah Shehi nan suka dawo suka sameshi, ko motsawa bai yi ba, "Anya kuwa kai mutum ne ?, anya kana da zuciya a jikinka ? kai gaba daya baka san damuwa ba ?, bakasan raɗaɗi ba ?, Wlh ka chanja halayenka dan basa sa kyau kwata-kwata ", tana gama fada ta wuce sama.


sosai Yan sanda suka shiga yawon nemanta, amma dakyar suka sameta, a Anguwar da take kusa da tasu, dan ko a ƙafa sai a gangare daga Anguwarsu zuwa chan din.
kai tsaye suka nufo gidan da ita, Zayn-maleeq da su Sayyid sun fito zasu fita, suka yi kiciɓis da Yan sanda , Sadiyyerh ya bayansu ,suna tafiya "A ina kuka samota ?", Zayn ya fada cikin karajin murna, da gudu suka fito daga cikin palo , sakamakon muryar Zayn da suka ji cikin munar yana furta cewa "Ina kuka samota", da sauri Ayyana ta rungumeta tana furta "Alhamdulillah. Sadiyyerh ina kika shiga haka ?", ta fada tana kallonta da dukkan farin cikin kan fuskarta "Anguwar da take bayanku", kai tsaye Dan sanda ya basu Amsa, "kai Amma fa mun gode sosai, Allah ya saka da Alkhairi", ta fada cikin murna, godiya suka shiga musu, Zayn ne ya fiddo kuɗi ya basu ya musu godiya, Jan hannunta Ayyana tayi tana tambayarta, sai dai bb Amsa sai idanunta wanda suka jeme suka koɗe saboda kukan da ta ci take juyawa,lokacin da zasu shigo palo Yaah Shehi ya shigewarshi Abunshi.


"Yanzu Yaron nan dagaske bai damu ba, ya shige ciki ko murna bb ?", Ayyana ta faɗa cike da jin haushn Yaah Shehi, "shiga ciki ki watsa ruwa ", Ayyana ta fada tana sakin hannunta, jujjuya kanta tayi tana cewa "Ayyana bana s......



Kumin Afwa don Allah🙏.


Ya hutun Weekend hope dai kowa yy Enjoy Weekend dinshi Qlau ?
[4/27, 9:07 PM] salmeertsanisalman: *P. 20*




Jujjuya kanta tayi hawaye na cika idanunta, miƙewa tayi tana laluɓe ta hau sama, ɗakinta ta bude ta shiga, kan bed ta faɗa ta ci gaba da kukanta, kamshin turarenshi ha Huge Boss ne ya fara cika mata hanci alamar yana very cloth da ita, bata ɗago kanta ba, sannan bata daina kukan da take yi ba.


A hankali ya fara takawa zuwa cikin ɗakin idanunshi na kanta, har ya ƙaraso gurin da take bata ma san ya matso sosai ba, zama yy gefenta, tare da birkitoto ya zamana tana kallom sama daga riginginan da tayi.


tallafo fuskarta yy yana kallonta, kallon fuskarta yake, yana kallon yarda hawaye suke zuba daga cikin idanunta,fisge fuskarta tayi daga riƙon da yy mata, hannunshi ya ƙara kai wa da niyyar taɓata, jajayen idanunta ta bude tare da watsasu akan fuskarta, shi dai bada ban kar ya faɗa ba dai-dai ba da sai yace har wata wuta-wuta ya hango tana ci cikin idanunta, cikin tsanar da ya gani miraran cikin idanunta tace "Kar ka sake hannunka ya taɓa jikina", ta fada tana juya ba, hannunshi ya daura kan kafadarta, janye hannunshi tayi ta wancakalar dashi, miƙewa tayi da niyyar barin ɗakin.


da sauri ya riƙe waist dinta, wata kalar juyowa tayi, zai yi mgm ta ɗaga mishi hannu, ido rufe ta fara cewa "bana son ka ƙara taɓani , kaje chan karuwar da ka ajiye ka ringa taɓata Mtswww", ta fada tana juyawa, wani irin fisgota yy, yana kallon cikin idanunta.


da sauri ta dauke idanunta , ta fice daga cikin ɗakin, kai tsaye ɗakin Ayyana ta nufa, jij karar takowarshi zuwa cikin ɗakin yasa ta rufe tare da sanya key, jikin ƙofar ta tsays tana wani irin kuka sosai, numfashinta har sarkewa yake.


Haka aka ringa yi tsakanin Yaah Shehi da Sadiyyerh , da yazo guri take tash, yanzu bata sonshi bata son ganinshi, tun bb wanda ya fuskanci hakan har kowa ya riga ya gane, amma kuma bb wanda yy musu magana, a cewarsu in ta ishesu sun faɗa. Gently ya shigo Palon yana samye da Alƙyabba Baƙa irin ta manyan Mallumma, kanshi na sanye da hirami da makawuya, idanunshi liƙe da wani siririn glasses irin na Mallumma, yana tafiya a hankali kafarshi sanye da Cover shoes , yana tafiya yana baza kamshin turaren Huge boss mai masifar kamshi da sanyaya zuciya.


da Sallama a bakinshi ya shigo palon, a zaune ya tarar da Umma Jakadiya, Ayyana, Zayn-Maleeq, Sayyid-Maleeq, Abdul-Maleeq, Anty Rayhana, Yaah Muhammad , Yarsu Amnah , Amaturrahman, Amatul-Azeez , Sadiyyerh, gaba dayansu suna cikin palon suna hira , yana shigowa Sadiyyerh da rake sanye da wata Abaya Blue black , gashin kanta da yake gyare wanda Ayyana ce ta gyara mata shi, ta sanya mishi hula ,Tsumewa tayi , tayi shiru tana kaɗa kafafunta.



tana ɗaga idanubta suka yi ido biyu sai ta dauke kanta, a hankali ya shiga takawa zuwa inda take, zama yy yana tattare Alƙyabbar jikinshi, yana zama ita kuma ta miƙe tare da yin sama, gaba daya binta da kallon suka yi, banda Yaah Shehin da yasan dama hakan ce zata faru, izuwa yanzu kowa ya fara ganin laifin Sadiyyerh kuma, sun san yanzu Yaah Shehi Sulhu yake nema tsakaninsu, amma taƙi , kuma daɓa ba tun yau suka san taurin kanta da kaffiyarta ba, bata da saurin fushi, amma tana da wahalar saukowa gata da muguwar ƙafiya da riƙo .



zaka iya mata abu ka manta amma ita bazata manta ba, sai tace *in maye ya ci ya manta, Uwar Ɗa bata manta ba*, sai dai kafin suga irin wannan fushin nata ana dadewa, dan ko tana fushi da kowa bata yi da Yaah Shehi, kuma da yazo yace mata abar wannan fushin da faɗa shi kenan ta barshi, amma gashi yau ita take yi dashi.



bb wanda yace da ita ko shi komai, yana kallonta ta ƙasan ido har ta haye sama .

ruf ya rufe idanunshi , hannunshi na kan gemunshi a hankali yake dan jaa kamar mai cire wani abu, haka yake zaune gurin daya, Ayyana ma da ke fushi take da shi sai ta tashi tayi tafiyarta, Yah Muhammad ne ya matso kusa da Yaah Shehi, cikin yin ƙasa da murya yace "Shalelen wai mai kawa Kanwata da Ayyana ?, naga muna fira suna ganinka suka shige ciki", ya fada yana kallonshi, shiru yy baice komai ba, "Matsalata da kai faɗin rai ", ya fada yana harararshi.


bayan gama jin duk abubuwan da suke faɗa ya miƙewarsa, tare da hayewa sama.


11pm ya shigo cikin gidan hannunshi riƙe da wasu manya-manyan Ledoji masu dauke da Tambarin *Al-Ihsan Fashion Design* .
A hankali yake taka steps din benan har ya isa sama, kai tsaye bedroom din Sadiyyerh ya nufa, a hankali ya fara kwankwasawa, daga ciki yaji sautin maganarta tana cewa "Waye ?", chan ciki yace "Uhmmm",wani dogon tsuka ta jaa kafin ta ƙara gyara kwanciyarta.
ba kaɗan ba Yaah Shehi yaji zafin wannan tsuka da ta mishi dan har cikin ransa yaji, yasan dan tasan ya tsani wannan tsukar shi yasa tayi, yanzu duk wani abin da tasan baya so shi take ƙoƙarin aikatawa, saɓanin da da duk abun da baya so bata yi.



Har ya juya suja haɗu da Umma Jakadiya, murmushi ta sakar mishi, a hankali ya dan loma bakinshi, yana kallon ledar hannunshi, "gashi!" ya miƙa mata yana barin gurin, numfashi ta sauke tana jaddada zuciyar Sadiyyerh, koma mai ya mata yanzu ai ya isa ace ta huce sa boda yarda yake bin kanta, amma taki, "Yarinyar nan nason yin Amfani da damar da Allah ya bata", ta fada tana nufar cikin ɗakin,bugawa ta shiga yi, amma babu amsa, daga chan ciki , cikin tsuka Sadiyyerh tace "wai waye ?", ta faɗa cikin faɗa-faɗa "Uwarki ce sai ki buɗe ki bugeni", ta fada cikin kufuluwa dan yanzu ta fara bata haushi da irin Iskancin da take yi.


Da sauri ta bude tana jaa baya, tare da yin ƙasa da kanta, a hankali ta furta "Sannu Ummuna !", kallonta tayi daga sama har ƙasa kafin tace "ai ke za'awa sannu.
nace kece mai Sannu Sadiyyerh, ke yanzu wannan halin naki ashe har yau baki daina ba ?, Wlh ki ci gaba da dukkan abun da kike, kina ganin Mijinki Salihi Bawan Allah, amma kina gasa mishi aya a hannu, wlh kar kiyi fatan ganin ranar da zai goge ya fara rama abun da kike masa, dan yanzu zamaninan da muke, irin Yaah Shehi wlh tsada suke da wuya samunsu ko an tona, amma ke kina wasa da Damar da Allah ya Ara miki,duk kuwa da kinsan cewar *SO DAYA TAK DAMA

3 Comments On ARMAN MALEEK
avatar
batula-yahaya

1 year ago

Reply

08139693951

avatar
daiy

1 year ago

Reply

Replying to batula-yahaya

Me yasa kika ajjiye nambarki kuma

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to daiy

Thanks for tuni

Please Login or Register in order to submit comment