Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 4
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels BUSA A MUTU!!!! Littafi Na Hudu (4) Part A Na Abdulaziz Sani M Gini AA Misau ke magana Ayi Hakuri Munyi Iya Kokarinmu Amma bamu samu littafi na 3 ba. KODA HUSNAILA TA GA YADDA MURAISU YA KASANCE sai ta kamu da tsananin farin cíki. Ta shiga kodashi tana mai cewa. "Gaisheka Magajin MAZAN JIYA. Tabbas na yarda da jarumtakarka da kuma horon da na baka, don haka bana shakkar ka tari mayaka komai yawansu. Ka sani cewa yanzu ne fa zan ga amfanin horon da na baka na tsawon shekaru anan dajin Kirzufa. Yanzu ne zan gani idan baka sha nonona a banza ba. Idan har ka bani kunya ba ni ba kai har abada!" Koda jin wannan batu sai zuciyar Muraisu ta buga da karfi bar kwalla ta cika masa idanu, ya dubi Husnaila ya ce, "Ya ke Ummina ya za a yi kuwa na baki kunya alhalin wannan ita ce ranar da na dade ina jiran zuwanta? Lallai kuwa yanzu ne za ki san cewa baki yi baibuwar banza ba. Yanzu ne za ki san cewa ba ki yi haihuwar banza ba. Yanzu ne za ki san cewa kin haifi jarumi dan jarumai, kuma jikan JARMAI." Koda Husnaila taji haka sai ta rungume Muraisu cikin tsananin farin ciki tana mai sa masa albarka. Daga can kuma sai ta janye jikinta daga cikin nasa suka fuskanci juna ta ce, "Abu na biyu da nake son na sanar maka shi ne mu kasance a cikin shiri koda yaushe. Da zarar ka ji wani motsi a cikin dajin nan wanda bamu saba jinsa ba, kawai ka fiddo wannan kah0 na farautarka ka bu: busashi domin sauran abokan gaba tare. Da zarar mun yi arba da abokan gaba kada ka rigani afka musu. Ka tsaya ka ga yadda ake yin yaki tukunna, lallai za ka ga yadda zan ragargaji maza, sannan sai kaima ka sa hannu. " Muraisu ya gyada kai yana mai nuna gamsuwarsa. Nan take Husnaila ta kama hannun Muraisu ta ja shi izuwa cikin gidan nasu, Jairul da Hairul na biye da su a baya tana mai cewa, "Yana da kyau, mu je mu zauna mu huta tunda tun safe muke ta aiki". Haka dai Muraisu da Husnaila da sauran dabbobii. dajin Kirzufa suka kasance kullum a cikin shiri da jiran zuwan abokan gaba kuma, a kullum din idan lokacin busa Kahon BUSA A MUTU ya yi sai Muraisu yaje ya busashi. Shi kansa Muraisu duk sa'adda zai busa kahon sai yaji bankalinsa ya dugunzuma domin ya san cewa lokaci ne na tashin hankalin komai da kowa da ke nahiyar gaba daya. A ranar kwana na ashirin da daya ne da fara busa kahon da rana tsaka su Muraisu suka jiyo sukuwar dawakai barkatai da ihun mazaje ya cika dajin Kirzufa gaba daya. A wannan lokaci Muraisu da Husnaila na zaune cikin gidansu suna cin abincin rana. Koda suka jiyo wannan hayaniya sai suka mike tsaye zurmbur! Husnaila tayia wuf ta dauki mashinta, shi kuma Muraisu sai ya dauki kuttun kwarinsa guda uku gami da bakansa na gado ya ratayasu a kafadarsa, kuma ya ruga izuwa Kofar gida. Yana fita ya fiddo kahonsa na farauta ya busa. Nan take karar kabon ta danne hargowar Dakarun da suka shigo dajin gaba daya har suka yi turjiya gaba dayansu da dawakansu a lokaci guda suka yi cirko-cirko domin dukkaninsu sun razana, kuma sun zata ma kahon BUSA A MUTU ne aka busa. Wadannan Dakarun yaki dai da suka shigo cikin dajin Kirzufa su dubu saba'in ne, kuma suna da nmatukar kwarjinı da ban tsoro, suna dauke da mugayen makamai na yakı iri- iri, har da ma kalar da mutum bai taba gani ba. Ba wani bane ke jagorantar wadannan mayaka ba face Sarki Zaidur, kuma shi ne akan gaba ya yi gagarumar shigar yaki mai matukar kwarjini da ban tsoro, fuskarsa a murtuke take ko kadan babu annuri a tattare da ita. Nan da nan dabbobin dajin Kirzufa gaba dayansu suka taru a gaban Muraisu da Husn aila, kuma sai ga Jairul da Hairul sun jawo tawagar birirrikan dajin gaba daya. Suna isowa suka zube kasa a gaban su Muraisu suna kwasar gaisuwa. Husnaila ta dubi gaba dayan dabbobin ta ce, "Ya ku abokan zama, kun sani cewa shekara da shekaru muna zaune a cikin wannan daji duk mahalukin da ya shigo cikin wannan daji baya fita a raye, kuma baya iya cutar da mu. To fa ku sani wannan karon al'amura za su sauya, domin abokan gabar da suka shigo mana yanzu za su iya cutar da mu, amma fa dayansu ba zai fita ba a raye. Abinda nake so da ku shi ne, ku tsaya mu yi yaki da ranmu da jikinmu, domin mu kare rayuwarmu da mahallinmu" Koda gama wannan jawabi sai Husnaila ta wuce kan gaba tana rike da mashita, ai kuwa sai dabbobin daiin suka bita a baya duuu! Shi kuwa Muraisu sai yai sauri ya hau kan Zaki Jandal, suka bi bayan su Husnaila. Al'amarin su Sarki Zaidur kuwa, lokacin a tawagar tasu gaba daya suka ja linzamin dawakansu suka yi tirjiya sakamakon jin sautin kahon farautar Muraisu sai suka tsaya suna raba idanuwa suna kallon gabas da yamma, kudu da arewa suna jiran su ga ta inda mai kahon BUSA A MUTU zai fito su afka masa gaba daya. Idan mutum ya dubi fuskokin Dakarun gaba daya sai ya ga alamun tsoro a tare da su, Sarki Zaidur ne kadai zuciyarsa a kekashe, sai muzurai yake kamar zai ci babu. Sarki Zaidur ya cika katon mutum mai kirar samudawa, domin girman halittar jikinsa ta yi kusan biyun ta Muraisu. Ya kasance dogo, kakkaura kuma shima duk jikinsa a murde yake tamkar curin nakiya. Kallo daya mutum zai yi masa ya san cewa ya cika barde mai dakawa maza gumba a hannu. Gaba dayan jikin nasa a cike yake da layu da gurave na tsafi, wanda ya gada tun iyaye da kakanni kuma bava amfani da su face a yaki. Kwatsam! Ba zato ba tsammani sai su Sarki Zaidur suka bango Husnaila a guje a durlafosu rike da mashi. dabbobin dajin na biye da ita. Har Dakarun yakin sun fara dariya bisa ganin mace ce ke tunkarosu, sai kuma suka ga wadannan dabbobin daji biye da ita duu! a baya, sai suka fara razana. Koda ganin haka sai Sarki Zaidur ya dakawa Dakarun nasa tsawa ya ce, "Me ku ke jira ne da su! Ma za ku afka musu ku zo mn da kan wannan hatsabibiyar mace wadda ta haifo mana alakakai a cikin wannan daji". Kafin Sarki Zaidur ya gama rufe bakinsa tuni Dakarun su dubu saba'in sun sakarwa dawakansu linzami sun sukwanesu a guje sun yi kan Husnaila da dabbobin. A wannan lokaci ne kasa ta kama girgiza saboda karar sawayen dawakai da na dabbobi. Inda ace mutum yana nan a lokacin da za ayi wannan mugun gamo yana kallo sai ya yi tsammanin cewa yakin duniya ne ya barke. Ai kuwa runduna biyun na haduwa aka kacame da azababben yaki, ya zamana cewa karar karafa, ihun mazaje da rurin dabbobi ya cika dodon kunne. Ana haduwa aka cakude, aka ruguntsume da azababben zazzafan yaki mai matukar muni. Babban abinda ya tayarwa da Dakarun Sarki Zaidur hankali shi ne, dabbobin tsalle suke suna dira akansu suna jehosu kasa daga kan dawakai, kafin su yi wani yunkuri tuni sun turmushesu sun yagalgalasu. Kalilan ne daga cikin Dakarun suke da matukar zafin naman da suke iva kaiwa dabbobin sara da suka suna yi musu lahani. Amma saboda naci da taurin rai irin na dabbobin sai ka ga sun mike sun ci gaba da yakin duk da cewa jini na zuba a jikinsu. Duk wannan bakin artabu da ake yi Sarki Zaidur na Asaye akan dokinsa yana kallo kawai, AA Misau ke magana domin ya fahimci bangaren da ke samun nasara, amma ya kasa, domin yakin ya zamo KARE JINI, BIRI JINI. Shi kansa yadda yaji bokansa ya bashi labarin masifar dabbobin dajin Kirzufa sai ya ga ma ashe ya fi haka. Yana cikin kallon abinda ke fdaruwa ne jarumi Muraisu ya durfafo wajen bisa Zaki Jandal. Jandal na yin wata irin tafiya a hankali cikin takama da kasaita ya ratayo kwari da bakansa. Tun daga nesa Sarki Zaidur ya kurawa Muraisu idanu cikin tsananin mamaki. oms Ba wai kwarjininsa ne ko Zakin da yake kansa bane suka bashi mamaki, kamanninsa ne da suka zo iri daya sak da na ubansa marigayi Sarki Muraisu. Nan fa Sarki Zaidur ya fara aiyanawa a ransa yana mai cewa, "Anya kuwa Wannan ba Sarki Muraisu bane ya yi fatalwa?" Wata zuCiyar kuma sai ta ce da shi, "Ai kuwa inda Sarki Muraisu ne ko dai fatalwa ya yi ya kamata ace fuskarsa ta nuna manyanta tunda kusan shekaru goma sha takwas ke nan da mutuwarsa" Koda Muraisu ya kara matsowa kusa, sai ya raba idanunsa A waje biyu, ya zamana cewa yana kallon gumurzun da mahaifiyarsa Husnaila take ya ga yadda ta zama tamkar shaidaniya a tsakiyar wadannan Dakaru, sai sokesu take da mashinta suna faduwa kasa oatattu, kuma da mashin nata take kare sara da sukansu. Kai har tashi sama takea ansu tarmkar tsuntsuwa mai fuka-fukai. Sannan kuma sai yc dubi Sarki Zaidur wanda ke tsaye bisa dokinsa a gefe daya suna kallo-kallo. Sa'adda Sarki Zaidur ya ga irin 6arnar da Husnaila take yiwa Dakarunsa da kuma barnar da dabbobin dajin ke yiwa Dakarun nasa sai ya fusata ainun, ya dirgo kasa daga kan dokinsa yana mai zare takobinsa ya falfala da gudun tsiya izuwa inda ake wannan gunurzu. Yana isa cikin turmutsitsin taron ya tarwatsa dabbobin dajin, loakci guda ya soki wadansu Damisoshi guda uku, ya sari giwaye biyu ya bazar da su kasa sannan yasa kafarsa ya make wani Zaki da wata Kura duk suka baje a kasa wanwar ko shurawa basu yi ba, saboda tsananin karfin dukan nasa. Al'amarin da ya firgita gaba dayan dabbobin dajin ke nan suka ja da baya suka koma can bayan Husnaila. A lokacin ne suma Dakarun yakin na Sarki Zaidur suka koma bayan Sarkinsu, aka fara kallon-kallo tsakanin Sarki Zaidur da Husnaila.AA misau ke magana Kawai sai Sarki Zaidur ya juyo ya dubi Dakarun nasa ya ce, "Ina masu kwari? Ku harba kibiyoyin wuta". Kafin Sarki Zaidur ya gama rufe bakinsa tuni Dakarun sun kunna wuta a kasa sun fara dodana kibiyoyinsu akan wutar. Koda Husnaila ta ga abinda ke shirin faruwa, sai ta falfalo da matsanaicin gudu ta daka wawan tsalle sama izuwa kan wadannan Dakaru masu kwari ta hau sokesu da mashinta. Koda Sarki Zaidur a ga haka sai ya ruga da gudu izuwa ga Husnaila domin ya kawar da ita, ai kuwa sai jarumi Muraisu ya zaburi Zaki Jandal da gudu. Kafin Sarki Zaidur ya iso inda Husnaila take tuni Muraisu ya sha gabansa ya daka tsalle daga kan Zaki Jandal ya doki kirjin Sarki Zaidur da kafa funsa biyu. Duk da irin azababben karfi na Muraisu sai karfin dukan nasa ya kasa kai Zaidur kasa, amma sai da ya ja da baya taga-taga har taku uku, sannan ya tsaya cak yana mai kallon Muraisu cikin murmushi. Al'amarin da ya matukar baiwa Muraisu mamaki ke nan domin komai girman bishiya mna idan yai tsalle ya doketa da kafafunsa sai ya kaita kas, amma yau gashi ya kasa kai mutum kas. Nan fa ya sha jinin jikinsa ya tabbatar da cewa ya gamu da gamonsa. Sarki Zaidur ya kwarara uban ihu wanda ya firgita komai da kowa da ke cikin dajin gaba daya har aka daina yakin aka ja da baya aka zuba musu idanu shi da Muraisu, Nan take kwalla ta cika idanun Sarki Zaidur, ya dubi Muraisu a fusace ya ce, "Ya kai wannan dan marigayi Sarki Muraisu, kayi sani cewa ka yanke min farin cikin rayuwata tunda ka kashe mini dana sakamakon kabon da ka busa don baka ne naji tsoron wannan daji na Kirzufa ya fita daga raina, shi yasa na fito da dukkan shirina domin na kashe duk wata halitta da ke cikin wannan daji kuma na koneshi kurmus yadda za a manta da fargabarsa har abada, " Kafin Sarki Zaidur ya gama rufe bakinsa tuni Husnaila ta tari numfashinsa ta ce, "Kafin kasa a manta da fargabar wannan daji na Kirzufa ni da dana sai mun sa an manta da duk irin zaluncin da kuke yi a wannan nahiya. Shin ka manta ne cewa shekara da shekaru babu Zaman lafiya a kowanne birni cikin wannan nahiya? Sace-sace da kisan rayuka ya yawaita a ko ina amma saboda abin bai taba shafarku ba ko wani naku shi yasa kuka bar talakawa a cikin masifa, sai yanzu da ka rasa danka wanda ka fi so fiye da komai shi ne za ka yi kokarin shafe dajin Kirzufa da abinda ke cikinsa? To ka sani cewa dajin Kirzufa da mu masu mallakinsa mun fi karfinka. Da sannu zamu karkade duk azzaluman da ke wannan nabiya". Koda jin wannan batu sai Sarki Zaidur ya kara fusata ainun ya kwarara uban ihu a karo na biyu ya ruga izuwa kan Husnaila da Muraisu suka ruguntsume da sabon azababben yaki, suma Dakarun yakin nasa sai suka fara fadawa dabbobin dajin aka dada rincabewa. Wannan karon sai masu kwari da baka suka sami damar harba kibiyovin wuta, nan fa wuta ta rinka kama Sassan wurare a cikin dajin, ai kuwa sai giwaye suka fara aikinsu na kashe wutar suna zuko ruwa da bakunansu a cikin koramu da koguna suna watsawa akan wutar. Da zarar sun kashe wutar sai su ga an sake kunna wata. Jairul da Jairul kuwa, sai suka jagoranci sauran 'yan uwansu biririka suka rinka debo manyan duwatsu suna jefawa abokan gaba, sai dai ka ga an fasawa Badakare kai ko goshi jini yai tsartuwa ya sulale kasa daga kan dokinsa, kafin ya mike tsaye dabbobin sun turmusheshi sun yagalgalashi. Kamar yadda dabbobin ke wannan 6arna haka suma zakwakuran mayakan Sarki Zaidur ke ragargazar wasu daga cikin dabbobin suna saransu da sukarsu da takubba da masu gami da kibiyoyi. Haka dai yaki ya kara tsamari ainun ya zamana cewa komai kallon kurillar mutum bai isa ya gano bangaren da ke samun nasara ba sai dai ya ce KARE JINI, BIRI JINI ake yi. A bangaren Sarki Zaidur da su Muraisu kuwa, labari ya sha bamban, domin idan suka sareshi ko suka sokeshi AA Misau ke magana sai dai su ji kamnar dutse suka sara, shima kuma idan ya sare su sai dai yaji kamar karfe yake sara, domin KAIFI DA TSINI baya tasiri a jikinsu su duka, amma kuma sai ya zamana cewa ya fi su karfin dantse da zafin nama don haka sai ya zame musu alakakai suka rasa yadda za su yi su sami nasara akansa. Hatta takobin da ke hannun Muraisu wacce ya kar6a 8 hannun wani Badakare da ya make tuni ta dakushe saboda saran Sarki Zaidur. Lokacin da Sarki Zaidur ya fahimci cewar KAIFI DA TSINI ba zai yi tasiri a jikin Muraisu da mahaifiyarsa ba sai ya yi wurgi da takobin bannunsa ya shigesu da dukkan karfinsu ya fara kai musu naushi da bugu da hannayensa da kafafunsa. Duk da cewa suna kokarin karewa da mai da martani sai ya fara kuntatasu har ma ta kai cewa ya doki tsakiyar mashin Husnaila da hannunsa. Nan take mashin ya 6alle, ya raba gida biyu, sannan ya fisge takobin da ke hannun Muraisu ya mutsittsiketa da bannu daya tamkar takarda ya dukunkune, ya ja da baya yana mai gyara isayuwa gami da dunkule hannayensa biyu. Al'amarin da ya firgita Muraisu da Husnaila ke nan suka Rara tabbatar da cewa lallai sun gamu da uban sadaukai. Kawai sai Muraisu da Husnaila suka dubu can inda ake ta fafata yaki da dabbobinsu, suka ga lallai kare jini biri jini ake yi, sai hankalinsu ya dugunzuma ainun suka kamu da tsananin bakin ciki. Muraisu ya dubi Husnaila ya yi ma ta inkiyar ta koma gefe daya ta kyaleshi da Sarki Zaidur. Cikin alamun firgita tayi masa nuni da cewar ba za ta iya ba, sai dai su hada karfi su yakeshi. Kamar hadin baki kuwa sai Muraisu da Husnaila suka ruga da gudu izuwa kan Sarki Zaidur suna masu kurma ibu cikin mugun nufi. Sarki Zaidur ya tsaya cak a inda yake ko motsawa bai yi ba. Koda suka iso daf da shi suka kawo masa naushi da bugu sai ya goce cikin zafin nama suka naushi iska. Kafin su ankara tuni Zaidur ya gabzawa Husnaila wawan naushi a fuska. Saboda karfin naushin sai da tayi katantanwa a tsaye uku sannan ta sulale kasa sumammiya. Shi kuwa Muraisu tuni Zaidur ya shake masa wuya da hannu đaya, wani irin mugun shaku ya yi masa wanda nan take idanun Muraisu suka yi bulu-6ulu kamar za su fado kasa, yaji kamar numfashinsa na neman daukewa, kuma ya shiga kokarin banbare hannun Sarki Zaidur daga wuyan nasa da hannaye biyu, amma sai ya kasa. A dai-dai lokacin ne Muraisu ya bango su an barbi biri Jairul da kibiyoyi guda hudu ya kife kasa rub da ciki ko shurawa bai yi ba. Cikin tsananin fusata Muraisu ya daga kafarsa ta gaba ya doki fuskar Sarki Zaidur da ita. Nan take hancin Zaidur ya fashe, jini ya fantsama akan fuskar tasa ya ga taurarin wuya har idanunsa na lumshewa. Ba shiri ya saki wuyan Muraisu ya kama layi. A wannan lokaci ne Muraisu ya ga mabaifiyarsa kwance a kas jini na yoyo a hancinta da bakinta, kuma babu alamun rai a tare da ita. Koda ganin wannan al'amari sai jarumi Muraisu ya kurma uban ibu mai tsananin firgitarwa fiye da wanda Sarki Zaidur ya yi a baya. Cikin bakin zafin nama wanda ba zai misaltu ba ya daka tsalle samna ya sake dukan fuskar Sarki Zaidur da guiwar kafarsa ta dama. Nan take hakori guda ya yi fitar burgu daga cikin bakin Sarki Zaidur. Kafin ya sulale kasa cikin matukar galabaita tuni Muraisu ya kamo kansa ya karya masa Wuya, ji kake kaka kass...! Kawai sai ya yi jifa da gawar Sarki Zaidur a kas ya ruga izuwa inda mahaifiyarsa Husnaila ke kwance ya shiga girgizata yana mai kwala kiran sunanta, kuma ya fashe da matsanaicin kuka. Koda Dakarun Sarki Zaidur suka ga Sarkinsu yaje kas sai zuciyoyinsu suka karaya suka firgita ainun suka fara zaburar dawakansu suna juyawa da baya a guje domin su fice daga cikin dajin na Kirzufa, amma sai dabbobin suka rinka kure musu gudu suna rafkesu. Kai idan ma Badakare ya samu ya kai bakin iyakar dajin sai ya ga dokinsa ya kasa haura iyakar dajin da shi ya kama tutsu sai dai ya yar da shi kasa kuma Kafin ya mike tsaye wata dabbar tazo ta turmushe shi ta hallakashi..... Anan zan dakata sai wani lokaci kuma idan Allah ya kaimu Ku ci gabaa da bamu kwarin gwuiwa domin samun cigaban wannan littafin Admin AA Misau ke magana Domin shiga group dinmu ta WhatsApp danna blue din rubutunnan Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/E0GMznXcaxwC0avNVdF30QBUSA A MUTU!!! Littafi Na Hudu (4) Part B. Na Abdulaziz Sani M Gini AA Misau ke magana Likes Comments Domin Bamu Kwarin gwuiwA. Labari Ya Isowa AA Misau Cewa.. KUMA KAFIN YA TSAYE WATA DABBAR TAZO TA TURMUSHESHI TA HALLAKASHI. Daya bayan daya sai da dabbobin suka kashe gaba dayan wadannan Dakarun yaki guda dubu saba'in ya Zamana cewa dayansu bai tsira da rayuwarsa ba. Al'amarin jarumi Muraisu kuwa, sai da ya dan jima yana jijjiga Husnaila yana kuka amma bai ga tayi molsi ba don baka sai ya kankameta a kiriinta ya dada fashewa da matsanaicin kuka. Yana cikin wannan hali ne uwar giwayen dajin tazo ta watsa musu ruwa shi da Husnaila. Faruwar hakan ke da wuya sai Husnaila ta farfado daga dogon suman da tayi tana mai jan numfashi. Al'amarin da ya jefa Muraisu cikin tsananin farin ciki ke nan ya kama kyalky ala dariyar murna, amma koda idanunsa suka kai kan gawar biri Jairul sai ya fara sabon kuka. A sannan ne Husnaila ta dawo cikin haiyacinta. Koda itama tayi arba da gawar biri Jairul da sauran dabbobin dajin wadđanda adadinsu ya kai đari uku da doriya sai ta kamu da tsananin bakin ciki, itama ta fashe da matsanaicin kuka. Babu abinda zai baiwa mutum tausayi face ganin yadda Hairul yaje kan gawar dan uwansa Jairul ya kwanta akanta ya kankameta hawaye na sartu daga cikin idanunsa. Al'amarin da ya kara karya zuciyar Husnaila da da Muraisu ke nan suka dada fashewa da kuka. Sai da lusnaila da Muraisu suka yini suna kuka da bakin ciki a cikin daiin Kirzufa sannan suka tattaro gawarwakin dabbobin da aka kashe su da sauran dabbobin suka haka Raton rami guda daya suka binnesu. Gawarwakin su Sarki Zaidur kuwa da suka tarasu him a Waje daya sai suka lullubesu da busassun itatuwa suka bunka musu wuta suka kone kurmus. Husnaila da jaumi Muraisu basu dawo cikin haiyacinsu ba da nutsuwa sai bayan kwana uku kuma duk sa'adda suka tuno rashin da suka yi na abokan zamansu su Jairul sai su fashe da kuka. Hakika sabo da sha kuwa mugun abu ne. Tabbas Muraisu da Husnaila ba karamar shakuwa suka yi ba da biri Jairul domin mutuwar Jairul ta jefasu cikin nugun hali, kai ka ce wani dan uwansu na jini ginshiki suka rasa. A ranar kwana na uku ne suna zaune sun yi jugum! a cikin daki kamar masu zaman makoki sai lokacin busa kaho ya yi amma sai Husnaila ta ga Muraisu bashi da niyar tashi ya dauki kahon ya fita don haka sai ta dubeshi ta ce, "Ya kai dana me kake jira ne baka tashi ka fita ba har yanzu ko kuwa ka manta ne da batun busa kabo?" Koda jin wannan tambaya sai Muraisu ya girgiza kai sannan ya dubeta ya ce, "Ya ke Ummina kiyi sani cewa tun daga ranar da muka yi yaki da su Sarki Zaidur na ga an kashe mnana abokan zamanmu da yawa har da Jairul sai naji ina tsananin tsoron busa wannan kaho domin ina tsoron kada a sake kawo mana wani farmakin a kashe mana abokan zama. Ina mai labbatar miki da cewa idan aka ci gaba a haka Amu iya wayar gari mu ga babu dabba ko guda daya a cikin dabbobin nan namu, mu kanmu ba lallai bane mu tsira da rayuwarmu." Lokacin da Muraisu yazo nan a bayaninsa sai Husnaila ta murtuke fuskarta ta daka masa tsawa tana mai cewa, "Ai koda komai da ke cikin dajin nan zai kare ba za ka daina busa wannan kaho ba har sai izuwa ranar da ka cika iya adadin bushin da ake bukata. Ina so ka sani cewa duk irin bala'in yakin da za a yi kai ba za ka mutu ba har sai ka dauki fansar ran mahaifinka a birnin Lairuf. Kuma duk mai tsautsayin da ya kuskura ya shigoa cikin wannan daji bai isa ya fita a raye ba. Lallai abin da ya faru ga Sarki Zaidur da Dakarunsa ya isheka abin misali. Ka gani da idanunka dayansu bai tsira ba da rayuwarsa. Yanzu ka fafata yaki a karon farko a rayuwarka, to ka sani cewa wannan yaki da kayi tamkar share fage kayi domin ban ga iyakar jarumtakarka ba tunda da mutum daya ka fafata, wato Sarki Zaidur. Ina son na ga iya kokarin da za ka yi ya yin da ka tsinci kanka a tsakiyar dubunnan mayaka. Ya kai dana, wai shin ya ya aka yi ka sami nasarar hallaka Sarki Zaidur? Tabbas ban san abinda ya faru ba domin abinda zan iya tunawa kawai shi ne, mun ruga da gudu izuwa kansa a tare'" Sa'adda jarumi Muraisu yaji wannan tambaya sai ya yi murmushi. Nan take ya kwashe labarin duk abinda ya faru ya zaiyane ma ta tun daga lokacin da Sarki Zaidur ya gabza mna ta naushi ta sulale kasa sumammiya, shi kuma ya shakeshi,

Chapter 1 of 4