Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

(oh kajini da shirme dama ai surukai ne).





"Allah yau nasha bazaka zo ba" ya kama hannunta yace "tunda inanan ai Babu abunda ze hanani zuwa" Khaleesat tayi dariya tace "Kai yayana wallahi shiyyasa nake matuk'ar k'aunar ka, kuma kasan mine, anjima ka biyomin mu koma gida tare Sam banajin dad'in rayuwa Anan" Shureim yace "ai shikenan driver zezo ya kaiki" tad'an had'e rai tace "to kaifa" Kai kurum ya girgiza Mata, tasan bazeyi d'in ba shysa kawai ta rabu dashi suka cigaba da firar harya tafi.





"amma kaje gurin su ko" Shuwaiba tayi tambayar tana d'an kwab'e fuska, shima ya had'e rai yace "wannan tambayar taki batada amfani kidena kawai suma Mata nane kamar dai ked'in nan" tace "Uhmm amma nace wane mataki ka d'auka Akan waccan Mara imanin matar taka" ya had'e gira yace "kamar ya kenan" tace "amata hukunci daidai da abunda tayi mana" Shureim ya mik'e Yana d'aukar wayar shi yace "let me remind you something, itad'in Mata tace, kuma auren soyayya mukayi ba auren had'i ba dan haka ki kama min kanki ki tsaya a matsayin ki Idan ba haka ba zan iya aikata komai akanta *SHE'S MY EVERYTHING*" daga Haka ya fice, had'a Kai tayi da gwiwa ta cigaba da rizgar kukan ta, waime yasa yafi son waccan shegiyar Akaina, kuka tayi sosai kamar ranta ze fita.





Tsabar yanda ta b'ata Mai raine yasa ko gurin Juwaira be biya ba ya wuce banki, Yana Kan hanyar shine, diamond ta kirashi, duk yanda ranshi ke Mai ciwo be hana farin ciki kwanciya Akan fuskar Shiba, d'auka yayi tare da cewa "aduk Sanda Naga kiranki bak'in ciki na yayemin duhu na mayemin haske, amma aduk Sanda Naji muryar ki nakanji nine me nasarar sake had'a wannan alak'ar, Iname farin cikin dawowar farin cikina cikin rayuwata, abaya nad'auka kin manta nine kuma kin gujeni amma se yanzu na fahimci dalilin ki na aikata hakan diamond ked'in...." dasauri ta katse shi da "Ohh my golden boy Naji dan Allah ya'isa haka, jiya kace Sarauta batada lafiya yajikin nata" yad'an yi shuru yace "jikin nata da sauk'i amma yau ban duba taba sena koma anjima" diamond tayi ajiyar zuciya tace "my golden ka kula da'ita sosai har zuwa lokacin da k'udirin mu akanta ze cika" Shureim yace "baki da matsala da hakan kulawa ma kuma da'ita zan yaudare ta amma diamond" ta katseshi dacewa "karka ce komai dole mu aikata hakan dole na nuna Mata kuskuren ta dole tabiya harda kud'in ruwa ma kuwa" Shureim yace "Aidai Haka kike so ko" diamond tace "kwarai" yace "angama ki kwantar da hankalin ki" daga Haka ya yanke wayar ya ajiye.





Se around 6 yagama abunda yake, yabiya gidan shi yayi wanka, sannan ya wuce gidansu.




"Wayyoh Allahna" yakalleta yace "to uwar raki miye kuma" ta kwab'a baki tace "k'afata fa kemin ciwo" Shureim yakama k'afar ya dudduba yace "amma ai angyara miki" ta amshe k'afar tace "dama ai Haka zakace tunda ba k'afar ka bace" yayi murmushi yace "kwantar da hankalin ki miye na d'aukar xafi Haka" Juwaira tayi murmushi tace "yaya Idan Naji sauk'i zamuje ka kaini Al jamea plaza da Al baik muyi dinner acan, Aidai zakaje ko" yayi shuru kafin yace "ya ummata safiyatu" ta tab'e baki tace "suna gaida Kai" Haka suka cigaba da firar na d'an lokaci kafin ya tashi ya nufi gurin uwar house.





Tsaye yake a bakin falon nashi Yana lek'e, dan tsoron shi k'arya had'u da Ummee, "to shikuma yaya wayake lek'e" Shubai'a tayi maganar a zuciyarta tana lek'en falon, tab'o shi tayi, cak ya tsaya Yana fad'in "Wayyoh" duk a tunanin shi Ummee ce, Yana juyowa yaga Shubai'a ce yayi ajiyar zuciya, tayi mishi nuni da "wayake lek'e" Kai ya girgiza Mata Yana shiga falon, ita kuma ta d'aga kafad'a tawuce.





A hankali ya bud'e k'ofar d'akin ya shiga, cak ya tsaya Yana Kallonta, juyowa tayi ta kalleshi dasauri ya duk'ar dakai, ciki ya k'araso Yana zama a k'asa gefen ta, itama ta ajiye ninkin da take ta zauna gefen gadon, a hankali yace "Ummee Ina wuni" Banza tayi dashi, se zuwa can tace "kasan kanada patient Anan Ina kaje baka zoba da safe" ya kuma yin k'asa dakai yace "Ummee naje banki ne" Ummee tace "zuwan yafita mahimmancine" ya girgiza Kai, tace "to Akan yarinyar nan zan sab'a maka Prince, kuma ka jirata ta fito wanka ka sauya Mata dressing d'in kanta" daga Haka ta mik'e ta d'auki kayan data ninke tayi hanyar fita, Shureim yace "Tasha maganin ta" Ummee ta tsaya tace "she's fasting" Shureim ya mik'e with full surprise 😲 yace "azumi kuma Ummee, in her condition" Ummee tace "ai ita daban Kai daban" Shureim yace "amma Ummee Sam azumi..." Ummee ta d'aga mishi hannu tace "please ka adana tambayar ka Idan ta fito daga wankan ka tambayeta" daga Haka Ummee ta fice, ajiyar zuciya yayi ya koma gefen gadon ya zauna.




Zuwa can tafi to toilet d'in, d'aure da towel fatar ta har glowing take, d'an k'aramin towel d'in hannun ta take tsane ruwan jikinta dashi, tana d'aga Kai taganshi taji gabanta ya fad'i "Innalillahi" kurum ta iya fad'a ta juya ta da niyyar komawa toilet d'in, ruff taji ya rufe k'ofar toilet d'in, d'agowa tayi ta kalleshi tace "Wai duk hakan miye ne, Aikin kud'i fa ka d'auke ni amma kake yin irin haka ni wallahi b....." kasa k'arasawa tayi sakamakon Jin ya kama Mata hannu, har bakin gado ya kaita ya zaunar da'ita, takuma yunk'urin yin magana ya d'ora hannunshi Saman lips d'inta ya girgiza Mata Kai, lotion d'in dayake amfani dashi ya d'auko tare da zubawa a hannun shi sannan ya d'ora hannun Saman lallausar fatar bayanta, lokaci d'aya suka lumshe ido, a hankali yasoma shafa Mata man, almost 10mins Yana Abu d'aya, kamar an tsunkuleta Haka ta zabura tayi baya tana k'ara Jan towel d'in jikinta nanda nan idonta yakawo kwalla, gefe ta juyar da kanta ta goge hawayen kafin ta juyo cike da fad'a tace "wallahiΒ³ bazan d'auka ba, AKAN KUDI na aure ka kuma bayan hakan baka gayamin zanyi maka aiki irin wannan ba please Mr man kozaka iya fita if not ni zan iya" ta k'arashe tana mik'ewa domin barin d'akin, hannun ta ya rik'e yace "zan canza miki dressing" fisge hannunta tayi tace "Bana buk'ata" daga Haka ta d'au abayar ta ta fice daga d'akin, zama yayi tare da dafe kanshi, yafi Minti 20 ahakan kafin ya tashi ya fita, "ita meyasa batasan rayuwar ta nacikin had'ari ba, meyasa batasan ana farautar rayuwar ta ba, Idan wani Abu ya sameta kuma fa, Kai Ina yakamata nagaya Mata gaskiya kozata je tanemin gafara, WAI meyasa meyasa kika zab'ar ma rayuwar ki Haka" ya k'arashe maganar zucin Nashi Yana bugun sitiyarin motar.





Direct d'akin Shubai'a taje, ranar acan ma ta Kwana, Sunyi magana da Ummee Akan zata bata mukullin d'aya daga cikin part d'in cikin wancan ganin dake nesa dasu wanda wani zubin ma se anhau mota kanan ake zuwa nan, gaskiya kuma Sarauta taji dad'in hakan sosai saboda tana buk'atar kad'aici.




*HISHAM*


Baridai muji wanene Hisham Yusuf, Hisham d'ane a gurin Yusuf bn Raqiz yayan Ummee kenan yaran shi uku, JAMEELERH, HISHAM, KHAIRY, sune yaran shi, Jameelerh na aure a k'asar Cairo, inda ita kuma Khairy take zaune tare da iyayenta a birnin mekkah, shikuma Hisham kasuwanci, Hisham da Shureim abokan wasa ne, shysa tsakanin Shureim da Jameelerh ba arzik'i Idan suka had'u gaddamar bala'i kamar y'an kwallo, amma kuma khairy Kallon yaya take mishi ba abokin wasa ba shysa shima yake Mata Kallon k'anwa, yanason yarinyar saboda tarbiyyar ta da hankalin ta sannan uwa uba ilimin boko Dana addini, yanzu ta kusa kammala karatun ta under engineering, wannan dalilin ne yasa Hisham ke yawan tsokanan Shubai'a saboda abokiyar wasan sa ce. To mundai ji wanene Hisham.





Zaune suke a falon suna fira, Sarauta ta kalli Ummee tace "Ummee nikad'ai ce a building d'in dazan zauna ko kuwa" Ummee tad'anyi shuru kamar me tunanin wani Abu, zuwa can kuma ta girgiza Kai tace "ah ah kamar ke kad'ai ce aciki amma akwai hadimai biyu a ciki" ta k'arashe tana tunanin Anya gaskiya ta fad'a kuwa, Sarauta tace "Ummee lafiya dai" Ummee tace "Uhm kawai nad'an ji kaina namin ciwo ne Bari naje na kwanta" Sarauta ta mik'e tace "Bari na rakaki" Ummee tace "ah ah kizauna kawai zanje da kaina" Haka ta wuce ciki jikinta duk a sanyaye.





"bazan gaji da Gaya muku ba wannan yarinyar itace mukullin bud'e duk wata k'ofar sirrin ku, gashi tana son bud'e muku k'ofar farko, a yau taso ta tunama Maryama abunda muka dad'e da goge matashi a kwakwalwarta, Idan kuma hakan ta faru kuma kunsan abubuwa sun fara warwarewa" Mama Unana ta k'arashe tana Kallon su duk su biyun, Hajja jumaima ta goge zufar dake tsaftsaf Mata tace "yanzu Mama Babu abunda zaku iya Akan wannan shegiyar yarinyar kenan" Mama tace "bawai bazamu iya bane, munan dakika ganmu munsan Allah kuma munsan dama tsarin shine Abu ze faru da mutum kawai dai mune sila, amma ita Allah be kaddaro Mata akwai Aikin daze cita nan kusa ba sedai Ina da shawara" dasauri Hajja Mubeena tace "kitemaka mana ki sanar mana miye shawarar" Mama tace "Ina zargin akwai shigar ciki a jikinta wanda bamu fatan a haife shi aduniyar nan, sannan kuma kusa jikokin ku suyi Mata sharrin kisan Kai wanda itama sedai a kashe ta" lokaci d'aya suka kalli juna kafin Hajja Mubeena tace "zamubi duk hanyar data Dace domin ganin mun rabata da cikin amma maganar kisan dai dakyar yaran xasu amince" Hajja jumaima tace "gaskiya Kam Adai canza shawara" Mama Unana tace "wannan sharrin kurum shine mafita akai, amma ku kawo min jikokin Naku nan zanyi musu bayani ta yanda zasu fahimta" suka amsa Mata da Tohm, amma zuciyar su cike da bak'in cikin samun cikin Sarauta Taya ma akayi Hakan ta faru.



*BAYAN SATI D'AYA*




"Hisham kenan Haka Dai kace" Shureim dakeni zaune Saman kujera 3seater yafad'a Yana Kallon Hisham dake kwance Saman gadon, Hisham yace "Humm yanzu ka barsu sun dawo batare da d'aukar wani mataki Akan abunda suka aikata ba, ba dole next su k'ara ba" Shureim yace "Kai Ina ruwanka ne Wai Malam mind your own business" Hisham yace "oh really, dama ai hakan zakace tunda uwar gidanka ta guma maka tak'i dawowa, ai wallahi ma gwara karta dawo" Shureim ya d'ago ya kalleshi yace "to Wai tsaya koma Kaine kaje ka zugeta ne" Hisham yace "ni, wane ni, ni yaushe rabon ma Dana ganta tunda naje na gaisheta ban kuma ganin ta ba" Shureim yace "ai yayi Mata daidai, Idan bazata dawo nan ba aikuma kaga dole ta koma bakin aikinta ko" Hisham ya tab'e bakin shi yace "ikon Allah ni Ina ruwana da lamarin iyalinka, I suppose to mind my own business" ya k'arashe Yana kwanciya, Shureim yayi murmushi dan Sarai ya gane inda maganar ta dosa.





"wash Allah Ummee na gaji wallahi" Ummee tace "to Sannu harkun gama Kai kayan" Sarauta tace "Uhm anjima ma zanje gida na kwaso kayana kinsan on Monday zan koma bakin aikina, Ummee tace" Ohk ba matsala Allah ya kaimu "Sarauta ta amsa da" Ameen".






Zaune suke Akan dining d'in sunayin lunch, kowa cikin su waya take dannawa kamar Dai Koda yaushe, ji sukayi an banko k'ofar anshiga, duk lokaci d'aya suka juya suka kalleta, se wannan harareΒ² take harta shigo falon, suma duk mik'ewa sukayi, tayi musu Kallon Marasa AJI sannan ta Haye upstairs d'in, Khaleesat tace "ita kuma wannan shegiyar miye ya dawo da'ita" Juwaira tace "Uhm ai wannan Karon Kodai mu ko ita" Shuwaiba tace "banzar, kurabu da'ita muga da wacce tazo" k'arar saukowarta ne yasasu yin shuru, se fama take da akwati harta sauko, harta wuce su sekuma ta dawo baya kad'an tace "kudai k'ara shiri dan wannan Karan ba irin wancan bane, shiri yakamata kuyi sosai kafin na dawo shysa zan Bar muku gidan domin kuyi gagarumin shiri domin daga yanzu zuwa Koda yaushe Zaku iyayin out daga gidannan saboda umarnine uwar gidan za'a koma bi" Juwaira tace "ke Dallah Mara zuciya kawai" Sarauta tayi dariya tace "akwai ma wanda yafiku rashin zuciya ne, daga cewa ku dawo kun wanko k'afa kun dawo, mukuwa mu mukai laifi Amma dan dole se'anzo bikonmu, inason na sanar muku da kishi da y'ar NIGERIA ba riba gwara kowa ta nema ma kanta mafita" daga Haka ta wuce abunta tabarsu da tunanin Banza da Wofi....




*ikon Allah, Humm nama rasa Abun fad'a aradu*




*Karku manta AKAN KUDI k'irk'irarren labari ne Danayi shi domin fad'akarwa, nishad'antarwa tare kuma da tunatarwa, nice taku me nishad'antar daku akullum da ko yaushe*





@ *sherntee Ghayu* 😍 😍






@07064706167


πŸ’΅ πŸ’΄ *AKAN KUDI* πŸ’΄ πŸ’΅

(A poor lady story)


....... 27th May, 2023




*Story & writing*
*By*



@ *sherntee Ghayu* 😍 😍





πŸ””πŸ“š *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATIONS* πŸ“š





πŸ‘‘ J. W. A πŸ‘‘





πŸ…Ώ...... *035 & 036*





"ah ah harkin dawo" tana zama gefen Ummee tace "nadawo ai dama bazama zanyi ba" Ummee ta juya ta kalli Shureim dake cin abinci sannan ta kalli Sarauta tace "yanzu Kije ki huta" Sarauta ta gane Ummee batason Shureim yasan inda zata koma ne, shysa tayi hakan itama mik'ewa tayi ta wuce d'akin Shubai'a.





"amma Ummee ke kina ganin abunda yarinyar nan keyi daidai ne" Ummee ta kalleshi tace "name fa" Shureim yataso yadawo kusa da'ita ya zauna yace "Ummee kiduba ki gani gaba d'aya sauran sun koma amma ita ko maganar ma bataso, bafa dani tayi fad'an ba dasu tayi" Ummee tace "toni yanzu my boo yakake son Nayi maka" Ya kama hannunta yace "kice Mata ta koma gida Anjima" Ummee ta amshe hannun ta, tace "kaga Nidai Babu ruwana bataimin maganar ba, kuma Nima ba uwar Banza bace dazanje nasameta Nayi Mata magana akai ba rashin kunyar ma kuwa takai, waikai tsaya yaushe ma ka fara sonta ne" yad'an had'e rai yace "Babu wani sonta danike Yama za'ayi naso wannan yarinyar ya maganar tarbiyya yarana kuma Ina abunma da baze yiyubane ba sofa kika ce Ummee tab" Ummee tace "to kagani karka kuma damu na Akan maganar nan" Shureim yace "dama Nayi ne domin kawai hakkina ne hakan" Ummee ta d'age kafad'a kafin ta sauya firar suka cigaba dayi.





"Su madam Shubai'a kuma dawa ake chat ne" Shubai'a ta nuna Mata number taga anyi saving da brother Jameel, Sarauta tace "Jameel waye shid'in kuma ko surukin nawa ne" Shubai'a ta rufe bakin ta, kafin tayi Mata nuni da "yaron ummah Ni'imatu nefa yayan jabeer da Shuwaiba" Sarauta ta tab'e baki tace "to yayi kyau ni Bari na kwanta" daga Haka tad'an juya Mata baya ta kwanta, idonta alumshe duk da ba barci take ba tunanin abunda ya dameta take, harga Allah Ummahnta take son gani akwai abubuwa da yawa daya Dace ace tasani zuwa yanzu, ajiyar zuciya tayi ta cigaba da tunanin ta abunta.





"My har cikin gidannan fa tashigo tayi mana warning yanda kikasan gidan ubanta har cewa take Wai bamu da class wallahi Idan Ina ganin y'ar iskar yarinyar zuciyata rad'ad'i takeyi kamar na mutu" Khaleesat dake waya da Sirayya take fad'a Mata haka, Sirayya tayi ajiyar zuciya tace "tabbas yarinyar nan akwai abunda ta shigo dashi gidannan amma karki damu zanyi maganin ta wallahi dani take magana ki kwantar da hankalin ki kinji My one and only daughter" Khaleesat tace "kullum Haka kike cewa amma kink'i kiyi komai akai fa" Sirayya tace "Aidai ninace miki xanyi ko to zanyi and kuma anjima Nabil Yana nan zuwa ai kinjini" Khaleesat tace "wallahi My yaron nan ya rainani kwanaki fa har cemin yake Duka shekara 2 nabashi dan haka nadena mulka shi yaron bashi da tarbiyya" Sirayya tace "shi Nabil d'inne yayi miki hakan, Aiko Kibarni dashi sena mishi wulaqanci Kibarni dashi" Haka suka cigaba da fira Akan rashin tarbiyyar Nabil. (Uhm Niko Naga ikon Allah Wai na cikin masai ke cema na waje ka taka Kashi).





"hello Ina jinka fa" Juwaira ta fad'a tana kanga wayar a kunnen ta, ta cikin wayar wata husky voice tace "Kindai yadani Kwana biyu ko kamar ma Lamar masoyin kiba, Haba my Juwy kinsan irin yanda Nayi missing d'inki kuwa gaba d'aya kin watsar dani, kinga yanda na rame kuwa a dalilin sonki" Juwaira tayi ajiyar zuciya tace "bawani dad'in baki zakayimin bayan Ance ka Jone da Larry girl ai agayamin komai" yad'anyi shuru kafin yace "wannan maganar ba gaskiya bace masoyiya ta ke kad'ai ce a zuciyata Larry girl d'in Banza yarinyar dako magana bata had'amu nifa Kece duniya ta" ya k'arashe Yana marairaice murya, Juwaira tayi dariya tace "Uhmm dama nasan sharri kurum ankaima domin a had'amu amma karkaji komai my boos Nima Nayi missing d'inka" yayi dariya yace "that's my Juwy, shikenan to kinsan Dai Nayi missing d'inki yaushe zamu had'u" kafin ta bashi amsa taga Kiran ummmahnnnta ya shigo, dasauri tace mishi "zan kiraka my boos ummmahnnna nakirana zan kiraka" daga haka ta yanke wayar ta d'aga ta Safiyatu, "hello ummmahnnna" Safiyatu tace "komai Dai lafiya ko" Juwaira tace "Uhm, Au d'azu waccan Mara mutuncin tazo d'azu tad'au kayanta Wai har cemana tayi mu shirya ma dawowarta, keni wallahi kashe shegiya kurum xanyi abunta yayi yawa" Safiyatu tace "karki damu zamuyi magana da hajjata Inji yanda zamuyi, amma dole mu d'auki mataki akanta Abun is too over" Juwaira tace "ai gwara Kam, Amm ummahhna zan kiraki yanzu Ina wata wayane me mahimmancin gaske se anjima" daga Haka ta yanke wayar, takira masoyinta suka cigaba da fira abunsu.





"waike wace irin Banza ce ne, shysa wani lokacin ko miye akayi miki Bana Jin haushi saboda Kece kika jama kanki, yanzun nan fa kike cemin Wai tazo harda yi muku warning amma shine kike wani cemin Waike ko ajikin ki harkike cemin na kwantar da hankali na Shuwaiba ke Kad'aice d'iya mace d'aya danike da dole na yak'i koma waye domin samun farin cikin ki" Ni'imatu ta k'arashe maganar a sanyaye, Shuwaiba data kauda wayar da kunnen ta, se sannan ta maida wayar tace "Uhm karki damu kanki, ai maganar fad'a ce tajimin ciwo Naji Mata, nifa damuwata mijina, kuma nasamu to Ina ruwana da'ita ita tasani, Nidai yanzu ki aikomin da chocolate" Ni'imatu ta daure ta danne ma zuciyarta tace "ke dad'ina dake ana maganar serious kina kawo wata maganar chocolate, karki damu za'a kawo miki amma yanxu yazamuyi da wannan banzar yarinyar nifa ko Sunan ta banason ji" Shuwaiba tace "Uhmm kinga kishiyata ce fa, bataki ba kuma ma ai dani take zaune ko to mijina nasonta Nima ina sonta, amma duk tamin iskanci Nima zan Rama, amma kinwani bi kin d'aga hankalin ki abanza nikawai akawo min chocolate d'in zanje in ci abinci se anjima" daga Haka ta yanke wayar ta sauka k'asa domin cin abinci.

Ni'imatu kuwa Kallon wayar kurum take abunma ita mamaki yake bata Anya ba asiri akayi ma d'iyarta ta ba tab akwai Jan aiki a gabana dole sena dage, haka ta cigaba da tunani ita kad'ai.





*5Days later*




Zaune take a office d'in, yau tun asuba ta iso office d'in domin tana da aiki sosai agaban ta. Around 8 ya shigo office d'in beyi mamakin ganinta ba saboda yasan AKAN KUDI takeyin komai, dasauri ta mik'e cike da girmamawa tace "morning Sir" shima ba yabo ba fallasa yace "morning" daga haka ya wuce mazaunin shi ya zauna.




Bayan gurin Minti 10 ta mik'e ta k'arasa gurin shi d'auke da iPad d'inta, d'agowa yayi ya kalleta, mik'a mishi iPad d'in tayi tace "ranka shidad'e ga wannan bayanan ka duba, kamfanin coal na Nigeria ibadan, k'asar Russia na fama da Matsalar coal, yayin da sukuma k'asar 9ja suke da yawaltar shi sakamakon yawan daji dasuke da, Ina ganin Idan da zamu had'a hark'alla dasu inaga mu zamu samu riba, suma su samu sannan k'asar Russia ta samu cigaba "ta k'arashe tana tana k'ara nuna mishi videon irin yanda ake sarrafa gawayi, yad'au almost 5 minutes Yana Kallon videon kafin ya mik'a Mata iPad d'in yace" Nagani, zanyi tunani akai" ta amsa iPad d'in, amma sedai ta tsaya ita bata tafi ba kuma ita ba tace wani abuba, ganin tsayuwar ta ta tayi yawa yasa, ya kalleta yace "anmm Lpy dai ko" kujerar gaban shi taja ta zauna, tana fuskarta shi tace "ammm ranka shi dad'e dama.. Kawai.... Uhmm" Shureim yayi murmushi yace "ki gayamin kawai Kai tsaye" ta d'ago Kai ta kalleshi tace "ranka shidad'e dama Akan maganar contract d'innan ne na k'asar Syria, shine Naga ya dace Nayi maganar saboda sunata takura mana da Aike komun amince shine nakeson Naji yanda zamu sanar musu" yad'anyi Jim Yana kallonta kafin ya d'aga wata laptop ya fiddo file d'in ya mik'a Mata yace "gashi, wannan ne file d'in, ki sanar musu da contract granted" ta zaro ido ta kalleshi tace "Dagaske ka amince y'allabaina" yayi murmushi yace "since last week Nayi signing Akan file d'in kuje ku fara shirin zuwan mu Syria daga can zamu wuce Nigeria domin yin magana Akan coal d'in" ji takeyi kamar tayi tsalle ta rungumeshi, kai kawai ta d'aga ta wuce mazaunin ta.




Tunda ta zauna take murmushi tana satar Kallon shi, a hankali ta d'ago ta kalli fuskar shi, aiki yake cike da nutsuwa dakuma iyawa, iskar dake shigowa ta window nad'anyin baya da gashin kanshi daya rufe almost rabin fuskar shi, murmushi take tana k'are mishi Kallo, "tabbas shid'in mutum ne me sauk'in Kai da fahimta Idan ka bishi a yanda yakeso zeyi maka duk abunda kake buk'ata, Yarima mutumin kirkine ga hak'uri gashi Allah ya azurta shi da kyau da dukiya" itakad'ai take wannan tunanin a zuciyarta, huuuuu taji an hura Mata iska Akan fuskar ta, firgigit tayi ta dawo hayyacin ta takalleshi, ya d'aga Mata gira yace "why the look" Kai ta kama girgiza Mai tama rud'e, murmushi yayi yace "Zaki cinye ni" daga Haka ya kama hannunta ya mik'ar da'ita yace "let go to the bank" Kai kurum ta d'aga Mai ta had'o kayanta ta fito.





"madam beauty" taji sautin murya, tsayawa tayi tare da juyowa, "Ali khan" shine abunda ta fad'a tana Kallon Shureim dayayi gaba, Ali khan yayi murmushi ya k'araso tare da cewa "surprise" tayi dariya tace "and you surprise me" Yana k'arasowa yace "kin Dena d'aukar wayana, and contract dinmu daku ya k'are ba lallai in ganki ba, to yau dai gani a HAUWA JIDDA naxo ganin ki" tana yak'e tace "to sannunka da zuwa, amma wane aiki kazo yi Anan" yad'an

Please Login or Register in order to submit comment