Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
na karb'e ai kudin na ubana ne. Ko godiya banyi ba na fice. Anan muka shirya,sannan muka nufi inda ake taron,Afficent. Waje ya cika makil da iyayen yara da sauran yan makaranta. Tausayin kaina ya kamani sanin cewa bani da wanda zaizo mini cikin yan uwana gashi ko abun rabo banyiba. Haka na kutsa na zauna,saidai a ranar nayi hotuna da kawayena,Munnira da Jamila, da yan ajinmu maza da mata. Saida akayi kirana domin amsar certificate na mike a nutse naje. Nayi mamakin ganin wanda ban taba zato ba yazo da niyyar daukata a hoto. Yaya Musty(dominka,yaya mustyna..love u forever..miss you:ur bloodsis..rufaida) ne,d'an gidan Gwaggo Hafsatu yayar Mamma dake Kazaure. Na saki fuska sosai,ina karba na nufeshi bakina a washe "Yaya mustyna kai dawa kuke tafe? Ya akayi kukasan da wannan ranar?" Ya harareni "Bayan da kika k'i kiranmu a waya ki sanar damu sai Abdullah dake a wata k'asar ne zai gayamana?" Nayi dariya a shagwabance nace "Afuwan yayana,yanzu kai da waye kuke tafe?" Yana dariya yaja hannuna yana fadin "Muje ki ganewa idonki." Haka mukayita kutsawa taron jama'a bai tsaidani gaban kowa ba sai Mamma da gwaggo Hajara. Ihun murna na saki ban damu da wadanda suka kalloni ba. Na rukunkume Mamma kafin na saketa na rungumi Gwaggo Hajara. Bansan ya akayi ba kawai sai na fashe da kuka sosai,har wani malamin Chemistry dinmu sarkin shishshigi ya matso wai bai taba ganin kukan Headgirl ba(kasancewar mukamin dana rike kenan a makaranta)sai a yau. Su mamma sukayi dariya,nikam na harareshi dariya kawai yayi ya kara gaba bayan yace"Madam,your daughter is one of my best students,very talented." Mamma murmushi tayi kawai. Kirana da aka karayi ne naje nayi speech a matsayina na headgirl na mike na tashi bayan na damkawa Mamma certificate dina. Tiryan tiryan nayi na gama na yiwa manyan bak'i fatan komawa gida lafiya sannan na bada shawara ga juniors dinmu nan aka hau tafi raf raf akarshe na koma gasu Mamma mukayi ta daukar hotuna. Munnira da Jamila suma suka iso suka gaida Mamma. Ina zaune kawai sai naga yaya musty ya shigo da kwalaye,nayi mamakin ganin jakunkunan rabo dauke da memo fa handfan a ciki. Na kalleshi idona taf da kwalla,yace "Zaki soma kuma dai? Muddin kikayi kuka zan fasa baki." Gwaggo Hajara tayi dariya "Wannan hukunci yayi." Nayi azamar share fuskata "Kaga nabar kuka yayana." Mukayi dariya,ashe tun sadda na sanarwa Yaya abdullah ya gayamusu. Shine Mamma ta bayar ayimin memo,anan shima Malam ya k'ara mata kud'i. Don farin ciki na rasa inda zansa raina. "Hamida,hindatu." Hamida ta kalleta ta tabe baki tayi gaba,hindatu ce ta tako ta gaishesu. Mamma ta dafa kanta tana murmushi bayan sun amsa. "Ina maminku? Ku gaisheta." Kusan lokaci daya muka dubi Mamma nida gwaggo Hajara,gwaggo Hajara harararta tayi. Nikam mamakin rashin zuciya irin na Mamma nakeyi,bata fushi. Da hindatu kadai na dauki hotuna,a karshe yaya musty ya amshi camera dita da zummar zaisa a wankemin hotunan harda na tasa wayar. Naji dadi sosai. Har kusan azahar muna tare kafin a watse suma su soma shirin komawa Kazaure. Anan ne idona ya raina fata,gwaggo Hajara ta dafani "Haba 'yata,menene abun kukan? Kiyi hakuri,tunda kunyi hutu saiki tambayi Abbanki idan ya amince sai kizo mana koda sati kiyi kinji? Kukanki sai ya karyar da zuciyoyinmu." Suka lallabani suka tafi. A ranar kuwa nasha zagi wajen Raliya dana koma,saidai batayi gigin taba lafiyata ba. Aikin da acewarta na gudarwa,dole na yishi. A banza kam tunda na samu ranar nan ta tafimin cikin matsanancin farin ciki. Ban kwanta ba sai wajen goman dare. Anan ma banyi baccin ba don hira nayi tayi da hindatu akan makarantarmu kafin bacci ya suremu........! Tun daga wannan ranar kuma sai na soma sakewa Usman kadan kadan,nakan gaisheshi hakanan nakan je dukkan wani aiken da zaiyimin zuwa gidansa ko kicin din Raliya da sauransu. Ban dai sakarmishi sosai ba,amma babu wannan rainin sosai. Har kuwa zuwa lokacin bai rabu da fita yawon dare ba. Nasha ganin Meena tazo wajen Raliya tana bala'i akan ita ta soma gajiya da bin mata irin na Usman,mutum tamkar wanda aka yiwa asiri. Raliya saidai ta bata hakuri don babu laifi iyayen meena akwai naira hakanan takan lasawa Raliya sosai domin ita din macece wacce bata godiya ga Allah. Duk da irin arzikin da ta hau kai tayi zaune na Abba,ga kuma business da takeyi,hakan bai hanata hangen na wasu ba. Bayan watanni uku,lokacin Mamma ta kusa shekara a gidansu,kawai na tsinci wayar Yaya musty yana yimin albishir cewar an daurawa Mammana aure da wani almajirin Malam. Har tsalle nayi don murna. Yara da yawa sukanyi bakin ciki idan uwarsu zatayi wani auren alhalin ubansu na raye, kai koda ace baya raye akwai yaran dake taya ubansu kishi amma nikam baruwana ko a jikina. Daga dariya kuma sai na fashe da kuka. Ina cewa shine ko a gayamin nazo da wuri? Dariya yayi yace kada na damu anan Kazaure Mamma zata zauna duk sanda naga dama na tambayi Abba ya barni toh nazo na ganta. Naji dadi kwarai ya kara tambayata game da Yaya abdullah nace mishi sauran mishi watanni uku kawai ya dawo. Daga haka mukayi sallama tare da alkawarin idan yaje gidan zai kirani mu gaisa da Mamma. Ai kuwa ko awa biyu ba'ayi ba yayi kirana,na hau bud'a karshe na saki dariya. Nayi mamaki dana ji muryar Mamma a sanyaye har na tambayeta ko bata farinciki da auren nan? Bata bani amsa ba ta share da tambayar lafiyata. Nace alhamdulillah,tace zan cigaba da karatune? Na tabe baki "Bansani ba Mamma." "Kamar ya baki sani ba Tasleem? Keda mahaifinki? Kije kiyi mishi magana tun lokaci bai kure maki ba." Na amsa da toh saidai kuma abunda Mamma batasani ba shine,idan har sai naje ga Abba na gwammace nayita zama haka a gidan. Haka mukayi sallama da ita. Bayan kwana biyu,Meena matar Yaya Usman ta haife tsohon cikinta ta samu d'iya mace. Murna a wajen yan gidan ba'a magana. Nikam ko ajikina daman ba wani mutuncinsu nake gani ba. ******* Bayan kwana uku da haihuwar meena,misalin biyar na yamma,ina zaune a bakin firij na Raliya ina gogewa,ita kuwa da yaranta suna falon suna kallon wasan Hausa saidai ko inda suke bana kalla ballantana film din da suke kallo ya dauki hankalina don tun fil'azal fina finan hausa ba burgeni sukeyi ba barni da da kallon Indian series da Korea anan kam ko makiyina ke kallo zan saci kallo. Sallamar Usman ta katsesu,Hamid bai amsa ba saima ya mike ya fice saboda a yanzu haushinsa yakeji akaina. Bayan su hamida sun gaisheshi ya dubi Raliya. "Wa kike ganin ya dace ta zauna wajen Meena ne?" Yayi maganar tamkar da sa'arsa,Raliya bata ko damu ba ta kyabe baki "A'a toh,ko Dijangala ai sai ta zauna. Idan kuwa batason aikinta ga waccan tsiyar saiku kwasa." Sai lokacin na dubeta kafin na watsawa Usman mugun kallo wanda na jima banyi mishi irinsa ba. Murmushi yayi ya dubi Raliya "A'a dijangala shiririta ne da ita,tunda dai ga gwaggon meena zata dunga yi musu wanka sai Tasleem ta dunga gyare gyarem gidan." Raliya bata musa ba domin duk yanda zan kuntata a rayuwa shi tafi kauna. Tace "Hakan ma yayi,ke! Idan kin kammala ki tattaro kayanki ki koma gidan Usman har sai matarsa ta gama wanka sannan zaki dawo." Bance uffan ba don bakin ciki,a matukar fusata ta kammala aikin na mike na shiga daki. Haka na tattaro kayan na fito. Hamida mukayi arba da ita ta tuntsire da dariya gami da yimin gwalo"Haka zaki k'are." Kamar nace mata wani abu saidai na fasa nayi gaba,Raliya har lokacin tana falon banko kalleta ba nayi gaba abina a fusace. Saida nazo daidai garden na zube anan na fashe da kuka,wai haka rayuwata zata k'are? Wane irin uba gareni da bai daukeni komai ba? Ya manta da ya haifeni ne har ya banzatar dani a gidansa ya maidani wofi? Ace yan aiki ma sun fini daraja da kima a gidannan? Na daga kaina nakai duba da d'an lilon da muka saba wasa da Yayana. Haka zaiyita cillani yana goyani muna zagaye garden dinnan muna dariya. Ba zato naji an dafani ta baya,nayi azamar juyowa ganin Usman bansan lokacin da naja tsaki ba nayi kokarin mikewa yayi saurin dawowa ta gabana. "Haba Tasleem,ashe tsanar da kika yimin har takai ace kije ki taimakawa matata ki zauna kina kuka? Duk cikinmu waye mai tausayinki bayan ni? Haba Tasleem,banji dadi ba wallahi." Ganin yanayin fuskarsa sai naga kamar ban kyauta ba,nace "Ni ba gidanka ko matarka na tsana ba ai,irin wannan rainin hankalin da akeyimin a gidan ubana ne na kasa gane dalilinsa. Bansan kuma me na tsarewa mutane ba." Na karashe cikin tsiwa,yayi dariya ya kawo hannu zai dora kan lebbana nayi azamar ja da baya,cikin tsoron yanayin kallon da yakemin "Tasleem komai naki abun sha'awa ne wallahi. Ni bana k'inki,inason ganin kanwata a kusa dani shine ma dalilin da yasa na nemi alfarmar zuwanki. Kiyi hakuri inajin dadin yanda kika kware a gyara muhalli. Meena KAZAMAR GIDA ce, banason ganin gidan nan da kazanta. Don Allah kanwata wallahi tana yin arba'in I promise you zaki komo gida." Bance komai ba na mike na dauki jakata nayi gaba yana magana ko juyowa banyi,menene saukin da nan da can din? **** Baby ta numfasa,hawayenta ya karu wani yana bin wani. Haris ya miko mata (handkerchief) dinsa,tasa hannu ta karb'a saidai bata da niyyar share hawayen. Ta dubi Haris wanda shima ya gaji da waigenta ya karkato gaba daya yana duban fuskarta don jin dadin hirar. "Haris a wannan zuwan nawa ne gidan Usman komai na rayuwata ya soma tabarbarewa. Yanda akayi kuwa shine......." 'YAR BARIKI ©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers) (33) Kwana uku da yin candy dinmu,Abba ya dawo daga tafiya hakanan Hamid shima ya dawo daga makaranta anyi musu hutu. Zuciya irin tawa ta hanani tunkarar Abba da zancen zuwa Kazaure. Sai ince rabona da sanya Abba a ido tun sadda yayi kirana yayimin batun komawa sashen Raliya da zama. Wataranar asabar ina gugar falon Raliya,ina yi ina wake wakena wanda yana daya daga cikin abunda ke konawa Raliya rai ganin bana nuna damuwa a dukkan ayyukan da take sanyani. Saidai batasan cewar kawai dannewa nakeyi amma ji nakeyi kamar na shak'ota don bakin ciki. Hamid ne ya shigo da takalmi ya bi ta inda na taka zuwa bakin firij,na kalli yanda wajen ya b'aci da k'asa bance komai ba na k'ara gogewa,yazo ya kara wuce hannunsa rike da lemon b'awo yana sha yana yarda kwallayen nan ma bance uffan ba don na lura tsokanar fad'a yakeyi. Saida nazo daf da kammalawa ya kara tahowa zai shige. Ai kuwa na sanya mop din na hankad'e kafafuwansa tuni ya zube a wajen,banyi sanya ba na kara dauka na kwala mishi a goshi. Ihun daya fasa yayi daidai da shigowar Hamza da Usman da Nura. Tsayawa nayi ina huci da fada"Wallahi gobe ma ka k'ara gigin b'atamin aikina sai nayi maka abunda yafi wannan haka kawai..." Hannu Hamza ya daga da niyyar kwad'eni ga mamakina Usman ya rikeshi,bani kadai ba dukkansu suma sunyi mamaki hatta da Raliya dasu Hamida da suka fito. "Kana da hankali kuwa? Sakarmin hannu!" Usman shima yace"Meyasa kake da son kaine Hamza?(Kasancewar raini ya shiga tsakaninsu bama kadan ba) Baka ganin laifin na dan banzan yaron nan ne da har zakayi gigin marin Tasleem? Wannan ma ai son kaine." Ya saki hannunsa,ya dubeni "Ke wuce ki tafi." Na dauki mop da robar zan fita,Nura ya dakamin tsawar data firgitani,ya iso ya janyo rigata wannan yasa na fadi na zubda ruwan,ba karamin buguwa k'uguna yayi ba. Kukana ya tsaya sa'ilin da Usman ya daga hannu ya mari Nura. Dakin yayi dif,ya cakumi wuyansa "Wallahi ka kara gangancin taba lafiyarta saika raina kanka! Metayi maka?!" Nura ya fisge hannun Usman daga wuyansa "Nika mara akan wannan yar iskar?" "An mareka!!" Nura yayi kwafa ya fice a fusace. "Hamza bimin bayansa kada ka bari ya dawo nan." Cewar Raliya sanin halin dabancin Nura don ba karamin aikinsa bane ya dawo da wuka ko wani makamin. Hamza ba musu ya fice. Raliya ta dawo gaban Usman "Meke yawo a kwakwalwarka?! Akan wannan yar iskar ka daki kaninka abunda baka tabayi ba shekara da shekaru sai yanzu da girmanku da komai?! Me ta baka kaci?!" Bai saurareta ba ya dawo gabana ya dagani "Sannu Tasleem,tafi zansa a goge." "Uban wa zakasa aikin? Wallahi kaji na rantse maka idan baka fita harkar shegiyar nan ba ranka zai mummunan baci. Dawo ki gogemin waje!" Ta dakamin tsawa,ina hawaye na sunkuya dakyar zan dauki robar saboda zafin buguwar da nayi saidai Usman ya rigani ya dauka ya mikomin. "Kiyi a hankali." Raliya ta sanyashi ficewa na lura baiso hakan ba,haka nayi aikin nan ina mamakin abunda ya faru. Tun daga wannan ranar kuma sai na soma sakewa Usman kadan kadan,nakan gaisheshi hakanan nakan je dukkan wani aiken da zaiyimin zuwa gidansa ko kicin din Raliya da sauransu. Ban dai sakarmishi sosai ba,amma babu wannan rainin sosai. Har kuwa zuwa lokacin bai rabu da fita yawon dare ba. Nasha ganin Meena tazo wajen Raliya tana bala'i akan ita ta soma gajiya da bin mata irin na Usman,mutum tamkar wanda aka yiwa asiri. Raliya saidai ta bata hakuri don babu laifi iyayen meena akwai naira hakanan takan lasawa Raliya sosai domin ita din macece wacce bata godiya ga Allah. Duk da irin arzikin da ta hau kai tayi zaune na Abba,ga kuma business da takeyi,hakan bai hanata hangen na wasu ba. Bayan watanni uku,lokacin Mamma ta kusa shekara a gidansu,kawai na tsinci wayar Yaya musty yana yimin albishir cewar an daurawa Mammana aure da wani almajirin Malam. Har tsalle nayi don murna. Yara da yawa sukanyi bakin ciki idan uwarsu zatayi wani auren alhalin ubansu na raye, kai koda ace baya raye akwai yaran dake taya ubansu kishi amma nikam baruwana ko a jikina. Daga dariya kuma sai na fashe da kuka. Ina cewa shine ko a gayamin nazo da wuri? Dariya yayi yace kada na damu anan Kazaure Mamma zata zauna duk sanda naga dama na tambayi Abba ya barni toh nazo na ganta. Naji dadi kwarai ya kara tambayata game da Yaya abdullah nace mishi sauran mishi watanni uku kawai ya dawo. Daga haka mukayi sallama tare da alkawarin idan yaje gidan zai kirani mu gaisa da Mamma. Ai kuwa ko awa biyu ba'ayi ba yayi kirana,na hau bud'a karshe na saki dariya. Nayi mamaki dana ji muryar Mamma a sanyaye har na tambayeta ko bata farinciki da auren nan? Bata bani amsa ba ta share da tambayar lafiyata. Nace alhamdulillah,tace zan cigaba da karatune? Na tabe baki "Bansani ba Mamma." "Kamar ya baki sani ba Tasleem? Keda mahaifinki? Kije kiyi mishi magana tun lokaci bai kure maki ba." Na amsa da toh saidai kuma abunda Mamma batasani ba shine,idan har sai naje ga Abba na gwammace nayita zama haka a gidan. Haka mukayi sallama da ita. Bayan kwana biyu,Meena matar Yaya Usman ta haife tsohon cikinta ta samu d'iya mace. Murna a wajen yan gidan ba'a magana. Nikam ko ajikina daman ba wani mutuncinsu nake gani ba. ******* Bayan kwana uku da haihuwar meena,misalin biyar na yamma,ina zaune a bakin firij na Raliya ina gogewa,ita kuwa da yaranta suna falon suna kallon wasan Hausa saidai ko inda suke bana kalla ballantana film din da suke kallo ya dauki hankalina don tun fil'azal fina finan hausa ba burgeni sukeyi ba barni da da kallon Indian series da Korea anan kam ko makiyina ke kallo zan saci kallo. Sallamar Usman ta katsesu,Hamid bai amsa ba saima ya mike ya fice saboda a yanzu haushinsa yakeji akaina. Bayan su hamida sun gaisheshi ya dubi Raliya. "Wa kike ganin ya dace ta zauna wajen Meena ne?" Yayi maganar tamkar da sa'arsa,Raliya bata ko damu ba ta kyabe baki "A'a toh,ko Dijangala ai sai ta zauna. Idan kuwa batason aikinta ga waccan tsiyar saiku kwasa." Sai lokacin na dubeta kafin na watsawa Usman mugun kallo wanda na jima banyi mishi irinsa ba. Murmushi yayi ya dubi Raliya "A'a dijangala shiririta ne da ita,tunda dai ga gwaggon meena zata dunga yi musu wanka sai Tasleem ta dunga gyare gyarem gidan." Raliya bata musa ba domin duk yanda zan kuntata a rayuwa shi tafi kauna. Tace "Hakan ma yayi,ke! Idan kin kammala ki tattaro kayanki ki koma gidan Usman har sai matarsa ta gama wanka sannan zaki dawo." Bance uffan ba don bakin ciki,a matukar fusata ta kammala aikin na mike na shiga daki. Haka na tattaro kayan na fito. Hamida mukayi arba da ita ta tuntsire da dariya gami da yimin gwalo"Haka zaki k'are." Kamar nace mata wani abu saidai na fasa nayi gaba,Raliya har lokacin tana falon banko kalleta ba nayi gaba abina a fusace. Saida nazo daidai garden na zube anan na fashe da kuka,wai haka rayuwata zata k'are? Wane irin uba gareni da bai daukeni komai ba? Ya manta da ya haifeni ne har ya banzatar dani a gidansa ya maidani wofi? Ace yan aiki ma sun fini daraja da kima a gidannan? Na daga kaina nakai duba da d'an lilon da muka saba wasa da Yayana. Haka zaiyita cillani yana goyani muna zagaye garden dinnan muna dariya. Ba zato naji an dafani ta baya,nayi azamar juyowa ganin Usman bansan lokacin da naja tsaki ba nayi kokarin mikewa yayi saurin dawowa ta gabana. "Haba Tasleem,ashe tsanar da kika yimin har takai ace kije ki taimakawa matata ki zauna kina kuka? Duk cikinmu waye mai tausayinki bayan ni? Haba Tasleem,banji dadi ba wallahi." Ganin yanayin fuskarsa sai naga kamar ban kyauta ba,nace "Ni ba gidanka ko matarka na tsana ba ai,irin wannan rainin hankalin da akeyimin a gidan ubana ne na kasa gane dalilinsa. Bansan kuma me na tsarewa mutane ba." Na karashe cikin tsiwa,yayi dariya ya kawo hannu zai dora kan lebbana nayi azamar ja da baya,cikin tsoron yanayin kallon da yakemin "Tasleem komai naki abun sha'awa ne wallahi. Ni bana k'inki,inason ganin kanwata a kusa dani shine ma dalilin da yasa na nemi alfarmar zuwanki. Kiyi hakuri inajin dadin yanda kika kware a gyara muhalli. Meena KAZAMAR GIDA ce, banason ganin gidan nan da kazanta. Don Allah kanwata wallahi tana yin arba'in I promise you zaki komo gida." Bance komai ba na mike na dauki jakata nayi gaba yana magana ko juyowa banyi,menene saukin da nan da can din? **** Baby ta numfasa,hawayenta ya karu wani yana bin wani. Haris ya miko mata (handkerchief) dinsa,tasa hannu ta karb'a saidai bata da niyyar share hawayen. Ta dubi Haris wanda shima ya gaji da waigenta ya karkato gaba daya yana duban fuskarta don jin dadin hirar. "Haris a wannan zuwan nawa ne gidan Usman komai na rayuwata ya soma tabarbarewa. Yanda akayi kuwa shine......." 'YAR BARIKI ©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers) (34) "Usman ya dunga jana a jiki da wasa da dariya musamman idan ba idon matarsa a wajen. Tun ina daure masa har dai na hakikance dagaske tausayina yakeji kuma kauna ta don Allah yakemin. Hakan ya zamana na amince cewar bashi da wata manufa akaina. Yaya Abdullah kuwa munfi sati lokacin bamuyi magana dashi ba don bana samun kudin da zan sayi data,hakanan shima bansan meya hanashi kirana ba. Wahala iri iri babu banayi a hannu meena,ni ce kula da jaririyarta da taci sunan uwar meena wato Sadiya suke kiranta da Ummi. A farko Usman so yayi ya sanya sunan mahaifiyarsa saidai ta murje idanunta tace sam bazata amince ba,UWA TAFI UWA don haka saidai a sanya sunan nata uwar. Haka dai Usman ya goyi bayanta,dayake itama Raliyar irin dukiyar da ake kawowa Meena daga gidansu a matsayinta na wacce ta haifi jikar fari ya hargitsa mata kai tace bakomai abi tsarin da Meena da takeso. Wanki kuwa babu ranar da hannuna baya taba ruwa,hakanan daidai da undies din Meena ni nake aikin wanke mata su. Sau daya na taba gigin yi mata musu akan wankin ta jibgeni ba tare da kowa yayi yunkurin cetona ba. Hakanan nayi jinyata na warke domin alokacin Usman baya garin yaje daurin auren abokinsa a Zaria kamar yanda ya shaidamin. Bakar ranar da bazan mance ba itace ranar da babu kowa a sashen usman sai ni. Gwaggo ta raka meena asibiti don allurar da zata kai Ummi,ina zaune a falo zaune kan kujera ina hutawa sanin da nayi matar gidan batanan balle kuma ta gani tunda dai ta rigaya ta sanyamin dokar hawa kujerunta nikam gajiya da aikin dana kammala yasa na shimfide saman kujerar ina kallon tashar Zeeworld da suke hasko series dinnan na Destiny wanda an riga anyimin nisa sakamakon jimawa da nayi ban kalla ba. Yawo naji wani abu kamar hannu yana yimin a kunnena nayi azamar mikewa zaune don ba karamin firgita nayi ba. Ganin Usman yasa nayi murmushi kadan ban kawo komai a raina ba na gaisheshi hade da tambayar "Yaushe ka shigo?" Wani kallo yake watsomin,hakan yasa cike da mamaki na dubi shigar dake jikina naga babu inda na kuskuro da shigar banza. Na kara dubansa "Lafiya dai baban ummi?" Ya basar yana mai mikewa tsaye da dariya "Lafiyar kenan Kanwata,kallonki nakeyi ina tausayawa rayuwarki. Ace ke kam baki da wani hutu sai masu gidan basunan kike da yancin sakewa tamkar ba gidan mahaifinki ba?" Nayi murmushi ina mai jin dadin yanda Usman ke nuna damuwarsa akaina,alokacin na ayyana cewar ko na manta kowa bazan mance kaunar da Usman ya nunamin ba alokacin da dukkan gidan suka juyamin baya. "Ayya,bakomai Baban ummi wataran sai labari fa." Yayi dariya yace "Hakane kanwata,kiyi kallo abinki domin kuwa ina maki albishir cewar matar gidan bazata shigo yanzu ba don zata biya ta gidansu." Naji wani sanyin dadi shi kuwa yayo hanyar dakinsa na maida kaina ga kallo. Jimawa kadan ya fito ya shiga kicin bayan ya chanja suturar jikinsa zuwa doguwar jallabiya. Ban damu da sanin abunda zai aikata a kicin ba,a cewata ma,ai gwara kada ya matsamin ya barni na dan huta kafin hakimar tasa ta dawo. Hankalina ya nutsa sosai ga kallo saidai naji alamar ajiye kwalin a kusa dani. Hakan yasa na juyo na dubeshi,murmushi ya sakarmin yana kurbar lemon kwalin na Chi exotic dake hamnunsa,yayimin nuni da ido ga lemon da yake ajiye akan tebur kusa dani. "Bismillah kina kallona,nasan rowa irin ta Meena bazaisa ta baki damar daukar abun sha ba. Bari na dan kwanta kafin nan da la'asar." Ya mike ya shige daki,nayi murmushi don nasan gaskiya ya fada. Meena rowan tsiya ne da ita,koda bak'i tayi sai sun nemi ruwa sannan ake basu balle akaima ga lemo. Na dubi kwalin lemun ina tunanin yaushe ma rabona dana samu yancin shan lemun kwali duk da a baya katon katon babu irin wanda Abba baya ajiyewa Mamma. Na dauka na bude na sha sosai,inayi ina kallo. Tsayawa nayi cak yayinda kaina yayimin nauyi,na ajiye kwalin lemun na dafe kaina ina mai runtse ido. A hankali na soma fita hayyacina,tun ina jiyo muryoyin dake fitowa a tv har dai na daina ji da ganin komai." ***** Baby ta dakata tana mai sheshshekar kuka sosai,Haris cike da tausayawa ya daure yace "Kiyi hakuri Tasleem." Kamar bazatayi shiru ba,har ta soma rikita mishi tunani don hakikanin gaskiya ya tsani kukan mace. Dakyar ta nutsu ta goge fuskarta da (handkerchief) din daya bata. Kafin ta zubamishi jajayen idanunta wadanda sukayi kusan kwana uku suna zubar da ruwan hawaye.[2/3, 21:29] Rufy: 'YAR BARIKI ©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers) (35) "Haris a wannan ranar Usman ya ketamin haddina. Yayi amfani dani ba a hayyacina ba." Ta numfasa kafin ta cigaba "Baccin nan bai sakeni ba sai wajen magriba. Nayi mamakin irin radadin da naji a gabana. Na yunkura da zummar mikewa daga shimfidar da nake kwana na katifa a karamin dakin yar aikin meena wacce zuwana yasa ta koma sashen raliya da aiki,saidai ko kalilan ban iya motsawa ba. Kawai sai na fashe da matsanancin kuka,a hankali kuma tunanina ya dawo da lemun dana sha hakanan cikin magagin bacci na hango fuskar Usman lokacin daya kwasheni zuwa dakina. Nayi azamar duba pant dina,jinin dana gani ba karamin dagamin hankali yayi ba. Ihu nasa hadi da fashewa da kuka. Yayi daidai da shigowar Meena da Gwaggonta,wuf suka fado dakin. Meena na fadin "Wane irin iskancin banza ne zaki...." Sauran maganarta ta makale ganin halin da nake ciki,gwaggo ta matso tana buga salati "Mun shiga uku,Aminatu kinga abunda nake gani? Yau tsinanniyar nan ta janyo mana abun magana." Meena ta dubi Gwaggo tace"Wa?! Wallahi badai dani ba! Kanta ta janyowa,karuwae banza da wofi. Bazaki janyomin zagin mutane ba." Daga haka ta hau buguna kamar Allah Ya aikota. Ihu nakeyi ina kuka kakkarfa saboda radadin daya hademin biyu. Ta sakeni tayi wuf ta fita ina nan zaune ina jan jikina zan shiga bandaki ta dawo rike da bokiti,kafin na ankara ta gwalemin kafafuna ta watsamin. Ai bansan sadda na saki razananniyar k'ara ba saboda azabar ruwan zafin nan,daga haka na sume. Ban farka ba sai a gadon asibiti. Nayi mamakin ganin har da Abba cikin wadanda ke tsaye a kaina,sai Raliya da kuma Gwaggon Meena. Na dubesu daya daya kafin na maida dubana ga Abba cikin matsanancin tsanarsa. Dukkansu babu masoyina ciki,makiyana ne. Bansan me suka kawoni ayimin ba bayan sun rigaya sun gama da rayuwata,inama ace sun barni na karasa rayuwata anan. Na kauda kaina ina mai jin saukin radadin azabar da nakeji a gabana bansani ba ashe wai har dinki akayimin. "Munafuka,ke juya keyarki mana kin jawo mana zagin mutanen gari. Haba Tasleem,me muka rageki dashi da har sai

Chapter 8 of 16