Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kiran layin amma a kashe, but bata taɓa tunanin itama ta tura masa text ba Burin ta a yanzu tasan masoyin nata, sabida a yanzu zuciyar ta ta yarda dashi; soyayyar sa ne tsantsa a cikin ran ta. *___________________________* Yau ta kasance Sunday, kuma yau ne taron Familyn su kasancewar duk ƙarshen wata suna taruwa a General parlour aci abinci tare, masu matsaloli su faɗa a magance musu Breakfast ne kawai kowa ke yi a part ɗin sa, Lunch kuma da dinner sai su haɗu aci tare, haka za su zauna ayi ta hira tunda babu me zuwa aiki a ranan Wani lokacin ma har su Aunty Zainab suna zuwa, Aunty Zulaiha CE kawai bata cika zuwa ɗin ba sabida tana nesa sosai, amma idan ta sami lokaci tana ziyartan taron Gaba ɗaya matan gidan suke haɗuwa ayi girki kala-kala da soye-soye, a babban kichen ɗin gidan suke haɗuwa tare da masu aiki su taya su Yau ma hakan ta kasance duk sun haɗu suna ta girke-girke Sauran yaran gidan kuma duk suna General parlour suna ta hiran su Su Big Dady kuma suna ƙaramin parlour'n dake kusa da General parlour, anan suka zauna suna hira da nishaɗi A cikin yaran in ka cire Fadila dake part ɗin su babu wanda ba shi ciki, ita dama bata cika son zuwa hiran ba, iyakan da an gama abinci zata zo taci ta tafi abun ta Kaka shima na ɗakin sa yana karatun Jarida be fito ba, be son su ishe sa da surutu that's why ya zauna cikin ɗakin sa Ɗahira na zaune gefen Baffa suna hira suna kallo cikin waya sai dariya suke yi Gefe can kuma Yusra da Shakira ne su ma suka buɗe tasu shaftan, Fadil ya zauna tsakiyan su sai zuba musu surutu yake yi, su kuma idan ya'ishe su wannan ta mangare shi ta nan, wancan ta mangaro shi ta nan, kuma yaƙi tashi a wajen shi a dole sai dasu zai yi hira Yau dai su Aunty Zainab babu wacce tazo cikin su. .......... .......... .......... ......... Babu jima wa aka soma shigo wa da abincin ana jera wa a dainning table ɗin cikin parlour'n dake can gefe, babba ne me cin a ƙalla mutane ashirin Bayan an gama an hallara a lokacin ne itama Fadila ta shigo ta zauna cikin su, kowa ya zuba abinda yake so Ɗahira kuwa tana can cikin Parlour tare da Kaka dake zaune kan Wheel chair ɗin sa, dama haka take yi idan har ba ya son zuwa kan dainning ita take zama kusa dashi tana taya sa hira, idan ta ɗibo masa abinci sai su zauna tana taya sa hira suna ci har su gama Yau dai shima Baffa ɗauko nashi abincin yayi ya dawo kusa dasu yana ci yana saka musu baki Haka Familyn suka kasance yau cike da nishaɗi Bayan kowa yaci ya sha aka dawo parlour aka zauna, nan su Big Dady sukai ta tambayan matsalolin mutane, daga nan kuma Kaka ya soma yabon Ɗahira da ƙoƙarin ta kan aiki, haka su ma su Big Dady sai yaba mata suke yi suna saka mata albarka Abbu da Aunty Amarya hakan ya saka su farin ciki matuƙa Hajja Fatu kuwa baƙin ciki kamar ya karta, haka ma Shakira sai dai ko kaɗan basu nuna a fuska ba Hajiya kam babu ruwan ta duk da itama ba wai yabon yayi mata daɗi bane, Umma ma dai na ciki na ciki Fuskar Yusra kamar zai fashe saboda baƙin cikin yanda iyayen nasu suke yabon Ɗahira, ko kaɗan ta kasa ɓoye abin da ke zuciyar ta, sai cika take yi tana batse wa babu wanda ya kula da ita Anan Big Dady yake faɗa musu Usman zai dawo gaba ɗaya gobe, iyayen sun yi farin ciki amma ban da yaran don sun san halin sa ba ya da mutunci bare ɗaukar raini, yanzu zai zo duk ya takura musu Daga nan aka ci gaba da hira, masu abun yi sun tashi sauran kuma sun zauna Fadila ce farkon tashi ta koma part ɗin su. *__________________________* Ɗahira ce ta shigo cikin ɗakin nasu Fadila dake waya tabi ta da kallo, sai kuma tayi dariya tana faɗin, "ga ta nan yanzu ta shigo ai". Cire wayan tayi a kunne tana kallon Ɗahiran da ta nufi wajen gadon ta tace, "Ga shi za ku gaisa da Yaya K.b". Murmushi Ɗahira tayi ta'iso wajen ta'amshi wayan tana kangawa a kunne kafin ta zauna gefen gadon Fadilan "Yaya na". Tafaɗa tana dariya Shima daga can dariyan yayi yana faɗin, "ƴan mata kin ɓuya da yawa fa". "Haba ko dai ka ɓuya? Kaji min wannan mutumin". Dariya yayi sosai yana faɗin, "Allah Ni ina nan ke ce dai kika ɓuya". "Ai dama kai ba ka son laifin ka, so how are you, how everyone?" "Alhmadulillah. how about you?" Ɗahira murmushi tayi tace, "lafiya sumul kamar yanda kuke, ina Shamsiyya?" "Ai kam yanzu ta tashi anan ta gama min daɗin baki". K.b yafaɗa yana murmushi "Hmm kai dai ka faɗa gaskiya ko dai kai ne ka gama mata daɗin bakin? Ai nasan hali". K.B said, " Let me call her and u ask her," "A'a Ni bance ba, ka barta nariga dai nasan Shamsiyya baza tayi maka haka ba, ya Ɗan kinibibi ina fatan yana lafiya? Duk da nasan kai dashi baku da zumunci, wai ace anyi Waliman mu amma kuka ƙi zuwa". K.b dariya yayi yace, "sorry Madam wlh kin san Ni aiki ne yayi min yawa, idan ma wani zai ƙi zuwa ai Ni bazan ƙi ba tunda har da my dear, amma insha Allahu kwanan nan zan zo Garin ma". Taɓe baki Ɗahira tayi tana kallon Fadila da ta shiga Toilet tace, "Mu dai muna zuba idanu; and Kar ka manta da saƙo na don Allah idan zaka zo". "Ok insha Allah, ga fa Mutumin naki nan ya shigo in ba shi wayan ne sai ki faɗa masa sunan da kika kira sa dashi?" Rufe baki Ɗahira tayi cikin waro idanu tace, "don Allah rufa min asiri kar ka haɗa ni dashi". K.b me zai yi in ba dariya ba Ita kuwa Ɗahira wayan ta miƙa ma Fadila da ta dawo ta zauna kan gadon tana faɗin "Riƙe wayan ki naga Yaya K.B yana son yaja min salalan tsiya". Fadila amsar wayan tayi tana maida wa a kunne, sai kuma tayi dariya tana faɗin, "ai har ta fice ma a ɗakin". Dariya ta sake yi tana gyara zaman ta, daga nan hiran su suka ci gaba da yi. Kabir K.B shi ne ɗa na uku wajen Hajiya IKRAM, ɗiyar ta na farko Sunan ta Nafisa, suna kiran ta Aunty Mimi, tayi aure har da yara, sai Isma'il, suna ce masa Dady, sannan K.B ɗin, sai kuma Jalil sannan Shamsiyya, sai ƙannin Shamsiyyan guda uku K.b ke son Fadila har kowa ya rigada ya san da zancen, yanzu kawai lokaci ake jira sanda Kaka zai ce su fito da mazajen aure ayi musu. [01/09, 5:04 pm] OumƊahira نفيسة: 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎              *DOCTOR'S FAMILY*                          🩺 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎 🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱   *NAFEESAT RETURN* 🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱 *MALLAKAR:*                  _NAFISAT ISMA'IL LAWAL_ *بسم الله الرحمن الرحيم* *SADAUKARWA* _Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY*_ _Wannan shafin naku ne masoyana, kuji daɗin ku._❤️ .         *EPISODE Fifteen*       Fitan Ɗahira ɗakin sai ta wuce ɗakin Maman ta kai tsaye, babu ita ciki tana can General parlour Kan gadon ta tanufa ta soma kwashe mata kayan wankin ta dake ajiye an ninke, kwashewa tayi ta kai mata sif ta dawo ta soma gyara ɗakin, ba wani datti yayi ba amma haka ta sake gyarawa har da wanke mata Toilet, ta dawo Kan kujera ta zauna ta soma duba wayan ta, message ɗin da Masoyin ta ya turo mata yanzu babu jimawa ta buɗe _"Kyakykyawa ta Barka da hantsi da fatan kina lafiya? Ya Weekend Ina fata kina enjoying?"_ Murmushi ta saki, a karo na farko yau tayi tunanin tura masa amsa, sai ta soma typing cikin ƙware wa _"Alhmadulillah ina fata kaima haka? Please I want to know who?" Sai tayi sending ɗin shi, tana nan zaune tana jiran ko za'a dawo mata da amsa but babu, sai ta gyara kwanciyar ta tasoma chatting da friends ɗin ta waɗanda sukai school tare Can kuma sai saƙo ya shigo, da sauri ta buɗe tana murmushi duk farin ciki ya cika ta _"Hmm kyakykyawa ta Kar ki damu da sannu zaki san ko Ni wane ne, Ni dai fata na in samu soyyayyar ki, don Allah ki so ni ko da kaɗan da yanda nake miki"._ Wani irin farin ciki ne yake mamaye da Ɗahira, sai dai bata mayar mishi da amsa ba tunda bata san me zata ce ɗin ba, sai taci gaba da chatting ɗin ta cike da nishaɗi.               ⚫⚫⚫        Buɗo ƙofan Hajiya tayi ta shiga parlour'n da sallama Yusra dake kwance cikin 3 Sitter tana kallo ta'amsa mata Zuwa tayi ta zauna tana faɗin, "Yusra, get me some water." Tashi Yusran tayi ta nufi Fridge tana faɗin, "Hajiya wai don Allah da gaske gobe Yaya zai dawo?" Hajiya bata amsa mata ba har sanda ta kawo mata ruwan, ta'amsa tasha sannan ta'ajiye sauran kan Centre table tana maida hankalin ta kan t.v Turo baki Yusra tayi ta zauna gefen ta tana cewa, "Hajiya I am talking to you." Sai Hajiya ta kalle ta tana hararan ta tace, "dan ƙaniyar ki Dadyn naki ƙarya zai miki? Ina ce a gaban ki ya faɗa?" Sake bunso baki gaba tayi tace, "to Ni Hajiya gaskiya bazan zauna ba zan koma gidan Aunty Zainab da zama, don wlh bazan zauna anan kullum ina cikin takura ba". Hajiya tace, "to Ni ban aike ki ba, idan kin tambayi Dadyn ki ya yarda sai ki fi ruwa gudu ma". "Don Allah Hajiya kiyi masa magana mana wlh bazai yarda ba in Ni ce". Hajiya bata sake mata magana ba Ita kuma sai magiya take mata har da ƴar ƙwallan ta Ko kaɗan ba ta farin ciki da dawowar Yayan nata, tunda sai tafi kowa takura kasancewar Part ɗin su ɗaya, ko kaɗan idan yana nan ba ya ƙaunar kayi ƙwaƙƙwaran motsi a gidan, yanzu sai ya zama laifi a wajen sa Daga ƙarshe ma Hajiya tashi tayi ta nufi cikin ɗakin ta tabar Yusra nan tana kumbura fuska kamar Flower, ba don ranta ya so ba itama ta tashi ta fice a part ɗin ma gaba ɗaya, duk zuciyarta babu daɗi.    ⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫    *TOMORROW MORNING*       Monday tushen aiki ko Bature na tsoron Monday Gaba ɗaya ahalin gidan sun tafi aikin su, sai su Umma da aka bari su uku a gidan sai kuma masu aiki, sannan Kaka dake Part ɗin sa Hajiya itama tunda ta tashi ta soma soye-soyen ta wanda zata tarbi Babban ɗanta dashi, yau gaba ɗaya farin ciki ya cika ta Allah-Allah take yi anjima yayi ta ga dawowar sa, dama sun yi waya jirgin ƙarfe 02:00pm. Yace mata zai biyo; don haka komi take yin sa a tsanake, ita da kanta ta shiga ɗakin sa ta gyara masa tayi masa duk abin da ya dace, bayan ta saka airfreshna sannan ta ƙara masa da turaren tsinke ta rufo ɗakin ta koma kichen taci gaba da harkokin ta.            ⚫⚫⚫          Ɗahira tunda ta fara duba Patiens ɗin ta take jin kanta na sara mata, amma dayake ita ɗin jajirtacciya ce bata bi takai ba taci gaba da harkokin ta Bayan ta gama ta nufi Ward ta duba sauran mara su lafiyan ta sannan ta dawo Office ɗin ta Tana son yau ta koma gida kamar lokacin tashin ta but ko kaɗan ba ta ƙaunar taje ta haɗu da maƙiyin ta (sunan da ta saka masa kenan) Tunda Baffa ya shigo ɗazu ya sanar mata da lokacin da zai je ɗauko sa a airport take ta jin ta babu daɗi, sosai kan nata yake ƙara ciwon Agogon dake ɗaure a tsintsiyan hannun ta takalla taga ƙarfe 01:20pm. Ne yanzu Tsaki taja ta tashi ta nufi drower ta ciri magani tasha da ruwan Robber dake ajiye saman table ɗin ta, Labcoat ɗin ta tacire ta rataye akan Hanger sannan ta cire Eyeglasess ɗin ta ta'ajiye saman table ɗin ta nufi Toilet Alwala ta ɗauro ta fito ta tada sallah, har ta'idar tana zaune nan tana lazimi, barci ne ya soma fisgarta don haka ta tashi ta ninke sallayan ta'ajiye ta nufi gaban table ɗin ta taɗau Glasses ɗin tamayar a idanun ta Hanyan ƙofa ta nufa don zuwa Office ɗin Abbu ta kwanta acan, amma me ta tuna sai ta dawo tana jan tsaki Ta san idan taje can zai tilasta mata ta koma gida ne, kuma a yau dai ba ta buƙatar ganin ta a gida, shiyasa ta dawo ta zauna kan kujeran ta ta ɗaura kanta a Deks ta rufe idanun ta, dayike barcin ne sosai yake cin ta don haka babu daɗewa ya ɗauke ta. Koda ta farka babu ciwon kan a yanzu, sallan Asar tayi sannan ta saka Labcoat ɗin ta, tana shirin fita ne Beeper ɗin ta ya soma ruri, don haka ta fita da sauri tayi hanyan emargency ward.               ⚫⚫⚫         At home, everyone was celebrating Usman's return        Gaba ɗaya matan gidan suna part ɗin Hajiya sun je taya sa murnan dawowa Sai da kowa ya watse sannan Shakira da Yusra da take Part ɗin su Shakiran yanzu suka nufi sashen Hajiyan don su gaishe sa Yana zaune a dainning yana cin abincin da Hajiya ta girka masa da kanta Yayi wanka har ya sauya shigan sa cikin ƙananan kaya kamar yanda ya saba Koda suka shiga gaishe sa suka yi, ya'amsa musu cikin Izza da taƙama Basu sake cewa komi ba suka miƙe suka fice don ba shi wuri, Part ɗin su Shakiran suka koma suka dasa hira.            Shi kuma bayan ya gama ɗakin sa ya koma, kwanciya yayi kan Three sitter ya lumshe idanun sa, shi ba barci yake yi ba kawai kwanciyar yayi, sai da aka kira sallan la'asar kafin ya tashi yayi alwala ya fita A waje suka haɗu da Baffa suka jera har masallacin dake nesa kaɗan da gidan su Bayan sun dawo a haraban gidan suka haɗu da Abba da Abbu da dawowar su kenan daga aiki Gaishe su yayi cikin girmamawa, su kuma sai tambayan shi hanya suke yi cike da fara'a, haka ya'amsa musu sannan ya wuce ya nufi babban Parlour Fadil na zaune a kan kujera yana kallo shi kaɗai ya shigo Da sauri Fadil ɗin ya gaishe shi Da kai ya'amsa masa ya nufi hanyan da zai sada shi da ɗakin Kaka Da idanu Fadil ya bi shi dashi, sai da ya shige sannan ya taɓe baki a ransa yana mitan "miskilin banza! kai da Fadila wlh ban san wanda yafi mugun hali ba". Sai kuma ya kwaɓe fuska yaci gaba da kallon sa.        Tura ƙofan yayi ya shiga yana motsa bakin sa Kaka dake zaune kan Wheel chair ɗin sa kamar ko yaushe yana karatun Jarida ya ɗago yana kallon sa, sai kuma ya yalwata fuskar sa da fara'a yace, "Maraba da Jikalle na". Takowa yayi ya zauna saman kujeran ɗakin yana kallon Kaka, kaɗan ya saki fuskar sa yace, "Old man are you still alive?" Sai Kaka ya saki dariya me sauti yace, "ja'iri ka ƙosa na mutu ko? To ina nan babu inda zan je sai na ga auren ka". Kyakykyawar murmushin sa yayi yana shafa gashin kansa yace, "uhmm Kaka kace da sauran ka kenan tunda Ni dai ba yanzu ba". "Koma dai me zaka ce sai naga auren ka tukun zan bar duniyar nan, dama tunda nayi muku maganar kai da takwara babu wanda ya haɓɓa sa, kun fi so dai a haɗa da ƙannin ku ko?". Usman taɓe baki yayi sai dai be ce komi ba Kakan changed the conversation and asked, "Ya hanya?" Shi kuma ya'amsa masa a taƙaice Kaka sai zuba masa hira yake yi, shi kuma daga ya'amsa da Eh sai A'a, daga ƙarshe wayan sa ya ciro yana latsawa yana sauraron Kakan, a haka yaja dogon lokaci a ɗakin kafin ya miƙe yayi masa sallama ya fice. [01/09, 5:05 pm] OumƊahira نفيسة: 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎              *DOCTORS FAMILY*                          🩺 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎 🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱   *NAFEESAT RETURN* 🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱 *MALLAKAR:*                  _NAFISAT ISMA'IL LAWAL_ *بسم الله الرحمن الرحيم* *SADAUKARWA* _Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY*_ .         *EPISODE Sixteen*            Sai ƙarfe 05:45pm. Ɗahira ta koma Office ɗin ta, Jakarta ta ɗauka da abinda zata buƙata ta fito ta rufe Office ɗin ta nufi Lifter Tana sauka ta fita ta nufi inda motan ta yake ta buɗe ta shiga, rufewa tayi ta'ajiye jakar ta kan Kujeran me zaman banza sannan tayi ma motan keey, sai dai yaƙi tashi, ta daɗe tana gwadawa amma yaƙi ya tashi, guntun tsaki taja tana dafe goshin ta, lumshe idanuwan ta tayi na kusan minti 2 kafin ta buɗe ta sake gwadawa amma ina har yanzu be tashi ba, fitowa tayi tana ɗan waige-waige, sai kuma ta nufi gaban motan ta buɗe Garage ɗin ta soma tattaɓa wa, duk ta duba ko da akwai matsala ne amma ita a fahimtan ta bata ga komi ba Tana nan tsaye a wajen tana ɗan sake duba wa taji sallama, sai ta ɗago kyawawan idanuwan ta wanda ƙwayan ciki suke ƙyalli sakamakon Hasken fitillun haraban wajen, amsa mishi tayi tana kau da kanta ganin kallon da yake mata tamkar zai haɗiye ta "Are you all right? I've seen you here before. Are you still gone? What's going on?" Ɗahira kamar baza tayi magana ba, sai kuma ta ga hakan be dace ba tunda taimakon ta zai yi, bata ɗago ba ta bashi amsa, "Wlh nima ban sani ba, kawai ta ƙi tashi ne". Dr. Sa'id yace, "ok bari in duba miki mu gani ko?" Babu musu ta matsa mishi yazo ya soma duba mata, shima ya daɗe yana taɓe-taɓen sa kafin yace mata, "wake up the car". Shiga tayi tayi ma motar keey amma har yanzu ya ƙi tashi "Ina ga dai motar ki sai ta ga bakanike coz myb wani matsalan ne babba wanda baza mu iya gane wa ba". Yayi maganar bayan ya rufe mata garejin "To Nagode". Tace dashi tana ciro jakarta kafin ta rufe motan da keey "In ba damuwa muje in rage miki hanya mana". Ta tsinkayi muryan sa da har ta juya baya zata tafi Jimmm tayi tana tunani domin ita mutumin ko kaɗan be mata ba, coz ta kula kallon tsiya ne dashi tun ganin sa na farko Murmushi yayi yana takowa wajen ta yace, "don't worry. Ni ba siyar da kanki zanyi ba, ai kin san a nan nake aiki balle kice Ni ɗin baƙo ne, so ni ba baƙo bane babu wanda be San ni ba, My name is Dr. Sa'id Khan". Kallon sa ta ɗan yi sai kuma tayi guntun murmushi tace, "ba damuwa mu je". "Yauwa ko ke fa". Yafaɗa yana yin gaba wajen motar sa Shi ya buɗe mata murfin motan da zumman ta shiga Sai kawai ta ga abun yayi mata wani iri domin ita idan har ba Baffa ba basu taɓa hakan da wani ba, hakan ko kaɗan be burge ta ba, amma babu yanda zata yi ta shige ta zauna ya rufe mata Shiga shima yayi yaja motar suka bar asibitin A cikin motan ma babu wanda yayi magana cikin su, sai da suka ɗan yi tafiya kafin ya soma jan ta da Surutu duk a kan aikin nasu Ko kaɗan ba ta jindaɗin surutun nasa Shi kansa ya gane ba ta ƙaunar hiran sa; yanda take amsa masa maganar kamar baza tayi ba, don haka yaja bakin sa yayi shiru yana mamakin yarinyan, shi tunda ya ganta yaji ta burge sa matuƙa kuma yana son ƙulla alaƙa da ita, sai dai ya ga alamun hakan ba me yiwuwa bane duba da yanda take ɗin, da alamun tana da girman kai kuma zata yi wuyan sha'ani, a yanda ya fahimce ta kenan Har suka kai ƙofar gidan su kafin ya tsai da motan Kallon sa Ɗahira tayi cikin siririyan muryanta me kamar tana yanga tace,"Thank you, Dr." He smiled and looked at her and said, "It's all right." Buɗe motan tayi ta fito Dai-dai lokacin su Baffa da Usman suka ƙariso wajen sun dawo sallan magriba Gaba ɗaya kallon ta suke yi, yayinda Usman ya ɗauke kansa time ɗin da ta juyo zata sauke idanun ta a kansu, cikin gidan ya wuce batare da yayi wa Baffa magana ba Shi kuma Baffan sai ya nufo ta fuskarsa duk babu walwala yana bin motan Dr. Sa'id da kallo da har ya ja ya tafi Itama ganin ya taho ɗin ne yasa ta tsaya tana masa murmushi Yana ƙari so wa idanun sa a kanta yace, "wannan kuma wane ne? ina Motar taki?" Sai da ta kalli hanyar da Dr. Sa'id yabi kafin ta dawo da ganin ta kanshi tace, "Yaya Motata taƙi tashi ne wlh ban san kuma me ya faru ba, shi ne yace in zo ya rage min hanya". Gaba ɗaya zuciyar Baffa ba ta mishi daɗi, tsananin kishi ne yake nuƙurƙusan sa a ransa, daƙyar ya"iya saisaita kansa ya sake jeho mata tambaya "Aina Motar taki ta tsaya da har kuka haɗu dashi?". "A cikin Hospital ɗin ne fa, kuma shima Dr. Ne cikin asibitin shiyasa ma na yarda na hau, but da farko ban yi ninyan hawa ba". Murmushi Baffa ya kirƙiro yace, "let's go then". Babu musu tayi gaba yana bin ta a baya duk da ita bata fahimci musabbabin tambayan nasa ba, amma ta san cewa shi ɗin Yayanta ne yana da right ɗin tambayar ta Sai da suka shiga ciki kafin suka jera cikin gidan, Part ɗin su Ɗahira suka wuce Suna shiga da sallama, Aunty Amarya dake zaune ita da Fadil suka amsa musu "Aaah maraba da Mijina". Aunty Amarya tafaɗa tana yalwata fuskarta da fara'a Baffa na faman shafa kansa yana murmushi ya ƙariso ya zauna a kan kujeran kafin ya gaishe ta Ta'amsa masa cike da fara'a tana tambayar sa aiki Itama Ɗahira sannu da gida tayi mata ta wuce ɗakin su ba tare da ta zauna ba Su kuma suka ci gaba da hira suna kallo Daga baya itama Umma ta fito aka ci gaba da hiran da ita Baffa duk ya ƙosa Ɗahira ta fito amma tunda ta shiga bata sake fitowa ba, shi kuma ya zauna ne don ita amma tunda ta fito ta zuba abinci ta sake shige wa ɗaki, aiki take yi a ciki shiyasaka ta zauna nan ɗin tunda ba ta son hayaniya Sai da aka kira sallan isha'i kafin Baffa ya miƙe tare da Fadil suka fito Anan suka ci karo da Fadila itama dawowar ta kenan, gaishe da Baffa tayi Ya'amsa yana faɗin, "Sarkin miskilanci sai yanzu aka dawo?" Murmushi tayi tace, "Yaya kana son dai tsokana ta ko?" Murmusawa yayi shima yana cewa, "ai gaskiya ne, kwana biyu ma gaba ɗaya kamar ba kya nan a gidan, rabon da in ganki na jima sai jiya a wajen meeting". Fadil dake tsaye yana sauraron su yace, "ai Yaya wlh duk wanda ya auri Aunty Fadila ya bani, shiyasa ma zan ba ma Yaya K.B shawara tun wuri ya sauya ta don baza tayi daɗin zama ba idan ya aure ta, yana ji yana gani zata mayar da waya abokin rayuwanta ta ƙyale shi yay ta surutun sa.." Kawo masa duka tayi dole yayi shiru yana matsawa gefe da sauri "Wlh zan ɓalla ka a nan wajen; Ni sa'ar wasan ka ne Fadil?" Tafaɗa tana hararan sa cike da haushi Baffa dariya yayi yace, "mai da wuƙan don Allah wasa yake miki". Ƙwafa kawai tayi ta juya ta buɗe ƙofan Part ɗin nasu ta shige, tana jin Baffa yana faɗin "Babu sallama kuma zaki tafi?" Amma bata jiyo ta kalle sa ba bare ta tanka masa Su ma wuce wa suka yi suka tafi, Baffa na shan dariyan Fadil da yaci gaba da maganar Fadilan.              ⚫⚫⚫              *08:45pm.*          Suna zaune su huɗu a kan dainning suna cin abinci, babu me magana cikin su sai ƙaran cokula da Plate da ake ji Kansa na ƙasa yana cakalan abincin kamar bazai ci ba, rabi kuma hankalin sa naga wayan sa yana kallon wani abu da aka tura masa, har kowa ya miƙe suka bar sa nan zaune be ma san sun tashi ɗin ba Parlour suka koma sukai zaman su, Big Dady da Hajiya suna taɓa hira while Yusra kuma ta mayar da hankalin ta kacokan kan Film ɗin da ake yi a Bollywood, Film ɗin زوجة زوجي searese A hankali ya miƙe ya taho cikin parlour'n yana shirin wuce wa ɗakin sa Dady ya tsayar dashi yana faɗin,

Chapter 7 of 22