Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"

Dariya ya shiga yi sannan yace "kinyi sallar isha Kuwa"?

"A'a Zan daiyi"
"Okay ki idar tukunna sai mu cigaba da wayar ko"?

"Toh Shikenan"
Ya katse wayar, Khalfana Tashi tayi ta shiga ban d'aki tayi alwala tana fitowa , zee da Zeemah kallon ta kawaii suke , ganin kallon yayi yawa Tace "Malamai yadai bashi ko Tara"?

Zee Tace "Ko d'aya, Khalfana Kun shirya da Maan ne"?

"Toh da ance Miki munyi fad'a ne"?

"A a bafa Ya Maan nake nufi ba shikam nasan Kuna tare ai,Alhj Maan nake nufi"

"Oh Suleiman Zaki ce min sai na fi ganewa, Yana kirana ai baki Sani bane"?

"Ina Zan sani baki fad'a min ba"

"Toh Uwata, muna waya da Suleiman Shikenan"?
"Ba Shikenan ba waye Kuma Mr Unknown"?
"Gashi kin fad'a he is unknown ban San shi ba"?

Zeemah tace "ji karya tun d'azu fa kuke waya kice baki San shi ba"

"Wallahi wallahi ban San shi ba" Nan ta Sanar dasu tun ranar da ya Fara tura Mata sako har I zuwa yanzu.

Fatan Alhairi suka Mata, Khalfana Tace "kunga muyi sallah sai mu cigaba da hiran"

Bayan sun idar da sallah, Khalfana Tace "muyi kallo anan ko mu Koma parlor"

Zeemah Tace "a'a parlor dai yafi"
"Okay muje to"

Zee Tace "Khalfana wallahi ke muguwa ce, yanzu kimanin watanni bakwai Kenan kin maida Mata miskiniya"

Zeemah dariya ta shiga yi Tace "Khalfana yanzu fa da d'azun Nan Idon ta biyu da Shikenan asirin mu ya tonu"

"Eh wallahi,ai duk sharrin zee ne, kalen dangi"

Zee Tace "Dakata Malama, abokin Mijina ne fa, kinga ta zama qawata"

Zeemah tace "Mtwws wallahi kinyi asara zee"

Zama sukayi a parlor Khalfana ta kunna musu kayan kallo suna kallo suna Hira Khalfana chat take a WhatsApp da Mr Unknown d'inta.

*Washe gari*

Kamar kullum sakon Mr Unknown ne ya shigo wayar ta, a karo na farko ta Masa reply da amsa Mai dad'i ganin message d'inta yasa ya ji dad'i sosai.

Yau asabar Khalfana sai 4 suke da lectures, aikin gida kawai Suka shiga yi bayan sun gama Suka shiga aikin Hira, suna xaune a garden na gidan,horn na mota Suka ji, duk suka maida kallon su zuwa gate , motar na shiga Khalfana tsalle tayi ta nufi motar da gudu tana fad'in "Zee, Zeemah mummy ce fa"

Suma bin bayan ta sukayi, tana Isa ta rungumi Mummy, Mummy Tace "Kaii Khalfana baki girma da shirme ko"?

Har kasa zee da Zeemah suka gaida mummy ta amsa.
Khalfana Tace "Mummy shine baki Sanar damu kina zuwa ba"

Mummy Tace "Eh haka na gadama,zuwan ba zata, ko na Koma ne"?

"A'a mummy you are highly welcome" jakar hannunta ta karb'a suna Hira har suka shiga cikin gida, sannan Suka dawo Suka kwashi kayayyakin da Mummy ta kawo, aunty Fatee da uncle sunyi Farin ciki sosai da ganin mummy.

Yau ake suna gidan ya cika makil dangin nesa da kusa duk sun Zo, Alhamdulillah yan 2 sunci sunan Mummy da Daddy, Mujaheed da Mujeedah, Amma ana Kiran Mujaheed da Aayan mufeedat Kuma Ayyan.

*Bayan shekara d'aya*

Khaleel so da kaunar Khalfana karuwa takea zuciyar sa, a yayin da Soyayya Mai karfi ta shiga tsakanin Mr Unknown da Khalfana, Aayan da Ayyan sun taso gwanin sha'awa, Aunty Fatee ta aje aikinta, uncle babban boutique ya bud'e Mata.

Zee da Adam Soyayya Masha Allah, Haka ma Azeemah da Dr, Yusrah ta warke, Amma duk da hakan Bata daina tsula tsiyan ta ba, Amma duk iyayinta Bata tab'a Haneefah da Haneef.

Khaleel in dai Yana gari Yana yawan zuwa gaida Mummy.
Wasa wasa yau Khalfana suna aji 3 saura musu 1 year.

Khalfana ta matsa wa Mr Unknown ya bayyana mata kansa in ba haka zata daina kulashi , ya Mata alkawarin zai bayyana Mata kansa Amma bazai fad'a Mata ranar ba.

Khalfana, zee da Zeemah ne zaune a Love Garden suna karatu, wayar Khalfana ne ya Fara ringing hannu tasa a Jaka ta zaro wayan murmushi tayi sanan ta amsa Tace
"Assalam"

"wa alaikissalam Masoyiya, ya zafi"?
"Alhamdulillah Amma ai ba zafi sosai"

"Kaaai a hakan Zaki ce ba zafi,bayan zafin Gombe yafi na Abuja"?

"Toh Kai ko ya akayi kasan zafin Gombe yafi na Abuja bayan baka Gombe"?

"Ina Gombe Mana"

"Hmm yau Kuma da zolaya ka Tashi ko"?

"Wallahi Ina Gombe"

Zaro ido tayi tana kallon su zee, zee ta d'aga Mata hannu alamun "Lafiya"?

Sa wayan tayi a handsfree

Tace "Dan Allah Ka daina zolayata Mana"

Murmushi yayi yace "dama nasan baza ki yadda ba, Amma fad'a min kina Ina ne yanzu"?

"Ina makaranta"
"Makarantan ta Ina,kinsan Nima GSU nayi"

"Allah sarki Ina Love Garden"

"Okay bani Nan da 20mints Zan karaso"

"Okay to"
Zee Tace "Khalfana finally yau zamuga Aljanin ki" ta karasa maganar tana dariya

Khalfana Tace "Zee tsorana d'aya Kar Kuma bai min ba"

Zeemah Tace "Khalfana don't worry as far as Yana kaunar ki kamar yadda yake nuna Miki an wuce wurin"

Khalfana Tace "I hope so, Zeemah wallahi am anxious"

Zee Tace "don't worry everything will be okay"

Karatu suka cigaba da yi, zee na d'aga kanta daga wasu motoci guda 5 a jere sai kyalli suke, tab'a Khalfana zee tayi tana nuna Mata inda motocin suke, Khalfana d'aga kanta tayi sai ta jaa tsaki "zee to yau kika Fara ganin motoci Mtwws"

Wayan Khalfana ya Fara ringing picking tayi yace "gani nazo Amma ban ganki ba" Khalfana mikewa tayi tana dubawa ko zata ganshi Tace "zaka ga mu uku , muna zaune nasa Hijab purple, su Kuma gyalle ne a jikin su"

Yace "okay na ganku, Kece kika sa Nikab ko"?

"Eh nice"
"Okay gani Nan karasowa"

Ya katse wayar , sojoji ne suka fito a wannan Motocin da suka shigo su uku suka nufu inda su Khalfana suke ,d'aya ne a gaba 2 na binsa a baya, sauran Kuma suna tsaye a jikin Motocin.

Zee Kam hankalinta duk na gun su ta ce "Khalfana kiga ni" Khalfana ko kallon zee batayi ba, Khalfana Jin inuwar mutum a kanta yasa tayi saurin d'ago kanta.

Ganin Wanda yake tsaye a kanta yasa tayi saurin mikewa tana nuna shi da hannu murya na rawa Tace "dama k..kk kkkai ne?

Murmushi yace "eh nine Kinyi mamaki ko"?
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️

A gafarce ni na rashin typing d'in da banyi ba kwana 2, ciwon idone ya sani a gaba, Amma yanzu Alhamdulillah.

mu had'u a page na gaba don Jin waye ne Mr Unknown d'in Nan da alama Khalfana ta San shi, Fans a ganin ku wane ne Mr Unknown?

Sai naji daga gare Ku

💞 *MILHAAT CE*💞

Please Share and Comments🙏🏻🙏🏻🙏🏻
💜💜💜💜💜💜💜💜
*MATAR AURE NAH*
💜💜💜💜💜💜💜💜

_*(A love and sympetic story)_*

```Story and written by Fadeelah Yakubu (Milhaat)```🖊️

*Matar Aure Nah, labarine Wanda ya kunshi soyayya tausayi fad'akarwa Nishad'antar wa gami da ilmantar*

*Note_* ```bamu yarda Wani ko wata su juya mana labariba ba tare da izininmu ba```


*Daga Alkalamin*
*Fadeelah* *(Milhaat)*✍️✍️


🌎 *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da aikida da ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da masoyan ta.```🥰
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*PAGE* 1️⃣5️⃣5️⃣↔️1️⃣6️⃣5️⃣
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️

Wannan page d'in nakune @⁨Meenah⁩ da @⁨Mom Arpat⁩ Ina jin dad'in comments d'inku Allah ya bar kauna.

"Eh nine Kinyi mamakin gani na ko Khalfana"?

Kallon sa Khalfana ke yi Sai hawaye take wiwiwiwi, Khalfana a ranta Tace "Kamar shine sojan da na Mara, tabbas shine don ban Manta kamannin sa ba,to me yake yi anan Kar dai shine Mr Unknown"?

"Eh nine" kallon sa ta sake yi cikin rashin fahimta, matsawa yayi dab da ita ya sa hannu ya d'aga Nikab d'in Dake fuskar ta, murmushi yayi Wanda yasa Dimple d'in Dake fuskar ya nuna sosai, sannan yace "Alhamdulillah rabo na da ganin wannan kyakkyawar fuskar tun shekaru uku da suka wuce"

"Dama Kai ne?kaine Wanda muke waya? Kai ne Mr Unknown, Kuma kamar Kai ne Wanda na ma......"

"Shhhhhshh Khalfana Kar ki ce komai ni d'in ne" sauke Mata Nikab d'in yayi sanan ya durkusa a gaban ta wani d'an karamin akwati ya Ciro daga aljihun sa , ya bud'e, wani zobe ya Ciro ruwan toka ne ansa Masa stones Jaa sai sheki yake, har ya Kai hannu zai riko hanunta sai ya fasa yace "Mi Amor, can I"? Yana nuna Mata zoben.

Khalfana kuka ta Fara yi Mai sauti, Nan da Nan mutane suka cika gun daga masu d'aukan hoto sai masu tafi, zee da Zeemah suka karaso inda Khalfana take, zee Tace "Khalfana kukan me kike yi ko baki son sa ne Kuma"?

Khalfana kukanta ta cigaba da yi, zee da Zeemah suka rungume ta suna rarrashinta ta, share hawayen ta tayi sannan ta Mika Masa hannun ta, ya sa Mata zoben, ihu aka Fara yi ana tafi, hannun ta ya riko suka nufi mota, zee da Zeemah na biye da su, da kansa ya bud'e Mata motar ta shiga ta zauna, ya nuna wa su zee d'ayar motar Suma aka bud'e musu suka shiga , Khalfana har yanxu kuka take, har suka fita d'aga cikin makarantar Bata daina kuka ba, shiru yayi Yana kallon ta sai ganin kukan yaki ci yaki cinyewa yace "Khalfana kukan me kike yi ne"?
Cikin kuka Tace "Kai ne fa Wanda na Mara ko"?
"Eh nine Khalfana it's not a big deal after all laifina ne da na rike Miki hijab hakan ne ya nuna min kina da tarbiya, tun daga ranar na kamu da sonki Khalfana, tun daga ranar na Fara bibiyan ki, har gidan ku naje"

Kai ta d'ago ta kalle shi Tace Masa "Gidan mu, yaushe kaje gidan mu Kuma yin me"?

"A ranar da kika mare ni washe gari mukaje Dani da Idris, in baki Manta ba akwai ranar da kika shigo d'akin Sufyan kika tarar da wasu"?
Tace "Eh na tuna"

"Toh nine d'ayan, Khalfana ki daina kukan Nan, you have cried enough Dan Allah"

Sai Tace "naga mun fito ina zamu je"?
"Restaurant zamu je, yunwa nake ji kinsan yanxu na shigo"
"Yanzu from Abuja Kenan, Amma ba da mota bako"?
"Eh jirgin sama na bi"
"Okay shiyasa"
"Khalfana suna na Mujaheed, Amma ana kirana da Khaleel, ni Soja ne Amma sojan sama ma'ana Air Force, ni Air Marshall ne sannan Nima d'an Gombe ne"

A ranta Tace "Alhamdulillah wannan had'in yayi min"
"Kinyi shiru sai kace ba ke bace wannan talkative d'in ba"
Murmushi tayi ta sunkuyar da kai, Jin motar ya tsaya yasa ta d'aga kanta ta duba taga har sun iso, Zata bud'e kofar motar sai taga har an bud'e Mata, Shima haka.

Tana fita zee da Zeemah ta hango suna tsaye, ta nufi in da suke, zee ne ta rungumi Khalfana Tace "My Habibty am so happy For you, kinga yadda Allah yake lamarin sa ko"?

Zeemah ita rungumar Khalfana tayi Tace "mahakurci mawadaci" dukkan su hawaye ne faal a idanun su, Khaleel karasowa yayi inda suke hannayen sa a aljihu yace "in Kun Gama rungume rungumen na ku sai mu shiga ko"?

Kunya suka ji, a Hankali suke tafiya har suka shiga ciki, order sukayi ba b'ata lokaci aka kawo musu duk abubuwan da suke bukata, bayan sun Gama suka Koma cikin makaranta, zee da Zeemah sukayi musu bankwana da fatan Alhairi.

Bayan su zee sun tafi sai yace "Mi Amor gida Zaki koma yanzu na maida ke"?

"Eh gida Zan Koma,Amma Ina da mota ta, nagode"

"Kash Amma ban so hakan ba"

Murmushi tayi Tace "Kar ka damu"

Rakota yayi har inda tayi parking, sai da shiga ya bar wajen, Khalfana na tuki tana murmushi ita kad'ai, tana Isa gida ta Sanarwa Aunty Fatee abubuwan da ya faru aunty Fatee tayi murna sosai tayi Mata fatan Alhairi, tana shiga d'akin ta wanka tayi sanan tayi sallah Jakarta ta shiga nema don zatayi karatu Amma Bata gani ba,defe kanta tayi tace "ohhhh jakan na gun Zee, gashi anyi magrib, dole naje gidan su na karb'o"

Fita tayi ta Sanarwa Aunty Fatee, Tace Mata "Toh sai kin dawo karfa ki dad'e kin San uncle d'inki Baya so kina yin dare a waje" "Toh Aunty yanxu Zan dawo"

Abaya ce bak'a a jikanta, Rolling kawaii tayi ta d'auki wayarta ta fice, har ta tada motan sai Tace "kashh Amma ban kyauta ba"
Dialing Numb Mr Unknown tayi dialing duka 2 ya d'aga yace "Ai na d'auka baza a Kiran aji ya nake ba" murmushi tayi tace
"Toh ka aje an Kira ka" murmushi yayi sun d'au lokaci suna Hira sai Tace Masa "sai anjima" "Lafiya me zakiyi"?
"Zan fita ne" "fita Kuma Ina Zaki"?
"Gidan su Zee"
"Yin me"?
Dariya tayi Tace "irin wannan tambaya haka sai kace d'an jarida"?

"Jiman bani amsar tambayar da nake Miki"

"Jakata na Manta a gunta, zanje na karb'o na dawo"
"Bari kawai nazo na kaiki"
"A'a Kar ka damu kagarawal ne fa ba nisa ai yanxu Zan dawo"
"Amma kinsan unguwar ba kyau ko"?
"Eh na Sani bazan b'ata lokaci ba"
"Toh kina dawo wa ki Sanar Dani"
"Toh yallab'ai"
Ta katse wayar.

Ba b'ata lokaci ta Isa gidan su zee, horn tayi Mai gadi ya fito yana ganin motar ya gane Khalfana ce, da sauri ya bud'e kofar , tana shiga sauke glass na motar tayi ta gaishe shi, ya amsa sai ta wuce, parking area ta nufa tayi parking motar ta sai ta fito, tana shiga parlor da Sallama Kannen Ya Maan ta gani suna Hira a Parlor, suka gaishe ta, sai Tace musu "Ina hajiya"?
Ummi Tace Mata "Tana part d'inta " "okay Zainab fa"? "Tana d'akin ta" Tace "nagode" cikin nutsuwa take tafiya har ta Fara Hawa matakala, Kai tsaye ta shiga d'akin , zee ta gani da Azeemah suna zaune a kan gado suna karatu, Tace "Toh munafukai wato Kuna Nan Kuna karatu, kun Manta Dani Koh"? zee kallon agogon Dake d'akin ta takeyi sannan Tace "Khalfana daga ina kike"? "Daga gida Mana"
Azeemah Tace "Amma Lafiya dai ko"?
"Lafiyar ce ta kawo haka Ina jakata"?
"Oh Yana cikin mota, bari na d'auko Miki"
Zee Tashi tayi ta d'auki makullin motarta ta fita Bata dad'e ba ta shigo da jakan.
Khalfana na karb'a ta nufi kofar fita tana fad'in "sai da safen ku"
Zee Tace "yawwa Khalfana tsaya Dan Allah akwai wani calculation da nake so ki nuna min please"
Khalfana Tace "zee ki bari muyi gobe man dare yayi fa"
"Please Khalfana gobe 7 Zan yi test d'in course d'in"
"Zee dad'i na Dake naci wallahi, ki bani hijab nayi sallar isha tukunna."

Bayan ta idar da sallah ta Fara nunawa zee, Basu Ankara ba har karfe 11 ya wuce, wayar Khalfana ya Fara ringing tana dubawa taga aunty Fatee ce, tana picking Aunty Fatee Tace "sannu Khalfana aikin ki Yana kyau" sai ta katse wayar.

Khalfana Tace "Na shiga Uku , zee sai da safen ku, Zeemah anan Zaki kwana ne, ko zanyi dropping d'inki"?

Zee tayi charap Tace " ji mugunta anan zata kwana"

"Chan muku kunga tafiyata" fita tayi ta samu babu kowa a parlor, tab'e baki tayi ta fita, Mai gadi na ganinta yace "anfito Kenan"?
Murmushi tayi Tace "Allah yayi" yace to "mukwana Lafiya"
"Allah yasa" ta jaa motar ta ta fita.

Tana tuki tasa kira'an Sheik Ahmed Suleiman,tana bin Bakinsa, har ta wuce sai taga kamar taga mace a tsaye, sauke glass d'in motar tayi ta leka sai taga dagaske mace Ce tsaye wurin reverse tayi, sannan ta fito tana kalle kalle ta a ranta Tace "me Kuma babbar mace kamar wannan take yi anan" karasa wa tayi Tace "Assalamu alaikum" a tsorace Matar Tace "Wa alaikissalam"
"Mama me kike yi anan cikin dare Haka Lafiya Kuwa"?
"Yar Nan wallahi da Yan iskan gari na had'u na fito daga unguwa suka tare ni, suka kwace mota ta abin takaicin ma har da wayata da komai na"

"Subhannallah Basu tab'a ki bako"
"Eh Basu min komai ba"
"Masha Allah ki shigo mota ta mu karasa maganar kinga tsayuwar mu anan ma matsala ce"

"Haka ne, Nagode sosai, Allah ya Miki Albarka"

"Amiin"
Bud'e Mata kofar tayi ta shiga sannan ta zaga ta shiga, ta jaaa motar sai tace "Mama a wani unguwa kike"?
"GRA"
"Okay ni Kuma gidan mu na Nan Tudun Wada, yanxu mu biya ta chan tukunna ko"?

"Toh Shikenan ba matsala"
Suna Isa horn ta farayi baba Mai gadi yazo ya bud'e Mata gate, suna shiga parlor uncle ta gani Yana ta safa da marwa , Sallama tayi chaaan ciki, Rai a b'ace ya juyo yace "Khalfana wannan wani irin rashin...." Kasa karasa maganar yayi ganin ba ita kad'ai bace sai yace "Khalfana wace ce wannan"?

Labarin yadda suka had'u ta bashi , "Allah sarki sannu bismillah ki zauna" zama Mama tayi , Aunty Fatee Jin muryar uncle yasa ta sauko Rai a b'ace, tun daga stairs take Cewa "Ai Daddyn Aayan Khalfana ta Raina mu in ba haka ba takai dare haka waje"?

Uncle yace "gata ki tambaye ta"
"Khalfana baza ki amsa ba"

Khalfana hawaye ne ya Fara sauko Mata tana shasshekar kuka "Aunty wallahi gidan su Zainab naje, na tsaya koya Mata wani calculation ne, in baku yadda ba ki kirata kuji"

Mama a karo na farko Tace "Haba kubi ta a Hankali yaro ai ba a Masa tsanani haka musamman ma mace" aunty Fatee kallon Mama take cikin mamaki don ita Sam Bata Lura da mutum a wurin ba, gaishe ta tayi ta amsa.

Aunty Fatee Tace "kiyi hakuri Khalfana ba Wai bamu yarda Dake bane, kinsan garin Nan fa ba kyau, in wani Abu ya same ki me zamu fad'a wa su Daddy"?

"Kuyi hakuri Dan Allah bazan sake ba"
Uncle yace "Amma Zaki kwana anan ko"? Yana kallon Mama, Tace "a'a Zan Koma gida"
Aunty Fatee Tace "kiyi hakuri ki kwana kinga Sha biyu ya wuce"

"Toh Shikenan tunda kun dage sai na kwana d'in gobe da safe sai na Koma gida"
Khalfana Tace "Mama Tashi mu shiga ki watsa ruwa ko"?

Tashi sukayi ko wannen su ya shiga d'akin su, Khalfana film ta kunna ta zauna a kushin a yayin da Mama Kuma na kwance a kan gado, Khalfana wayar ta, ta d'auko ta shiga Kiran Layin Khaleel, Yana picking yace "sai yanxu"?
Tace "eh wallahi"
"Hmm shine yanxu ko"?
"Wata Yar matsala aka samu"
"Khalfana zamuyi waya gobe yanxu bana hayyacina, kinji"?
"Lafiya me ya faru"?
"Zan fad'a Miki gobe Insha Allah"
Toh "Allah ya Kai mu" jiki a sanyaye ta katse wayar karatun ma tayi, ta Tashi ta kashe kayan kallon, Mama Kam har tayi bacci, Khalfana a kushin ta kwana.

*Washe gari*


Kamar kullum bayan tayi sallah ta had'a musu breakfast tayi wanka, har yanxu mama na bacci, Khalfana tashinta ta shiga yi a Hankali dakyar ta samu ta bud'e Idon ta, "Mama ki Tashi kiyi sallah" "Khalfana Dan Allah ki bani magani Kai na ciwo yake sosai" "ayya sannu Mama akwai bari na kawo Miki, gashi jiya kin kwana da yunwa, duk na sha'afa" murmushi Mama tayi Tace "ai a koshe nake shiyasa" Mika Mata maganin tayi,tasha sannan ta shiga tayi wanka sannan tayi alwala, bayan ta fito taga ba kowa a d'akin wani abaya ta gani jaa da Farin hijab a aje a kan gado, murmushi tayi Tace "Allah sarki Yar kirki" sa kayan tayi ta Fara salla, idar da sallan ta yayi dai dai da shigowar Khalfana.
"Mama Ina kwana" "Lafiya kalau Khalfana, kin Tashi Lafiya"?
"Lafiya kalau ya ciwon kan"?
"Da sauki Alhamdulillah"
"Mama an Gama breakfast ke kad'ai muke jira"
Ta ce "To"

Suna Isa dinning room, uncle da Aunty Fatee da Aayan da Ayyan a na zaune, bayan sun gaisa suka fara cin abinci, suna gamawa Mama tayi musu godiya Tace "Ni Zan Koma gida nasan hankalin su a tashe yake yanxu" uncle yace "haka ne bari na shirya na Kai ki" Khalfana Tace "A'a uncle Ni Zan kaita dama lectures d'ina sai karfe 4"

Mama tace "Yawwa kinga sai ki d'an Taya Ni Hira ko"?
Murmushi kawaii Khalfana tayi, aunty Fatee tasan halin Khalfana Sarai zata ce a'a sai ta yi saurin fad'in
"Ba komai ai Mama sai kuyi hiran" ta karasa maganar tana hararan Khalfana, Khalfana kauda kan ta tayi.

Tashi Khalfana tayi ta shirya tsaf, farin Atamfa tasa an Masa flowers da ruwan bula, d'inki borno style aka yi, tasa gyalle ruwan bula hka ma takalmin ta.


Bayan ta Gama suka nufi mota da Mama aunty Fatee ta rako su, suna fita basu nufi ko Ina ba sai GRA,
Gidan ya Had'u don duk kyawun gidan su Khalfana gidan Mama yafi nasu nesa ba kusa ba.

Suna shiga Kai tsaye suka shiga parlor, gidan Shiru, Mama Tace "to Ina suka shiga ne, Khalfana zauna bari na dubo su" Khalfana zama tayi tana bawa Idon ta abinci, Idon ta ne ya fad'a a kan wani hoto da aka Manna a bangon d'akin a fili Tace "kamar Khaleel me Kuma hoton saa yake yi anan"? Wani hoto ta sake gani, wani babban mutum ne ya rike Mama, sai Khaleel da Wata Wacce zasu yi sa'a da Khalfana, kana gani kasan family picture ne.

Jin murya kamar na Khaleel yasa tayi saurin duba wa taga tabbas shi d'in ne Yana fad'in "Momy kin tsorata mu wallahi jiya kasa bacci nayi,Amma Allah yayi wa yarinyar Nan Albarka" ya rike Momy a kafad'a, Momy Tace" ai tare muke da ita, itace ta kawoni" "Muje na ganta" suna saukowa daga matakala, Khaleel na d'aga Kai ganin Khalfana a zaune a cikin gidan su ya sa shi suman tsaye.
Mama tace "Yadai meyasa kake kallon ta haka ka Santa ne"?

Shiru ba amsa Mama ganin Khalfana ita ma kallon Khaleel d'in take ta karaso inda Khalfana take ta dafe ta a kafad'an ta " 'Yata Lafiya me kike kallo haka" Khalfana baki a bud'e so take tayi magana Amma ta kasa.
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Mu had'u a page na gaba

Please Comment and share🙏🏻🙏🏻🙏🏻

Milhaat ce🥰

💜💜💜💜💜💜💜💜
*MATAR AURE NAH*
💜💜💜💜💜💜💜💜

_*(A love and sympetic story)_*

```Story and written by Fadeelah Yakubu (Milhaat)```🖊️

*Matar Aure Nah, labarine Wanda ya kunshi soyayya tausayi fad'akarwa Nishad'antar wa gami da ilmantar*

*Note_* ```bamu yarda Wani ko wata su juya mana labariba ba tare da izininmu ba```


*Daga Alkalamin*
*Fadeelah* *(Milhaat)*✍️✍️


🌎 *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da aikida da ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da masoyan ta.```🥰
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*PAGE* 1️⃣6️⃣5️⃣↔️1️⃣7️⃣5️⃣
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
"Khaleel Kai don gidan ku Ina maka magana baza ka amsa min ba"?

Tsotsa keya ya fari yace "Momy na santa ai, mun tab'a Had'uwa a wani shopping complex a Abuja"

"Uhmnn sai aka yi Yaya" dariya ya shiga yace "Momy ki tambaye ta da sauri ya bar parlor Momy na Kiran sa "Khaleel Khaleel" Amma Ina har ya fice.

Momy Tace "yaron Nan ya maida Ni kakar sa, Khalfana Ina fatan ba wata matsala ko"?
"Eh Mama, Ni Zan tafi" "a'a ai baki Isa ba yau anan Zaki wuni har sai Lokacin zuwa makaranta yayi, kinji ko"?
"Toh Momy"

Wata budurwa na gani tana saukowa daga matakala,tana waya, kamannin su sak da Khaleel kamannin har ya b'aci tana karasowa ta zauna Tace "Sannu da zuwa bakuwa" cikin fara'a Khalfana ta amsa "Yawwa sannu" tana murmushi
Mama tace "Khausar kinga na kawo Miki Qawa sunan ta Khalfana" Tashi tayi ta zauna kusa da Khalfana Tace "Momy Nagode gata kyakkyawa wallahi" "Kyakkyawa son Mai so kin Wanda bai samu ba, haka ma halinta, itace ta taimake Ni jiya" "Khalfana mun gode sosai, Allah ya saka da Alhairi" "Ameen, ai ba komai Amma Dan Allah godiyan ya Isa haka, tun jiya Momy take ta min godiya kema kin Fara naki"

Dariya Khausar ta Fara yi Tace "Amma kina da abun dariya waya ce Miki godiya Yana yawa"

Momy Tace "Kila a garin su ana haka"

Duk sukayi dariya, sun dad'e suna Hira, har kusan karfe 1 Mai aikin gidan ta shigo da Sallama ta durkusa Tace "Hajiya angama abincin" Momy Tace "Har kin shirya a dining"?
"Eh na shirya komai da komai" "Toh sannu da aiki, ki samu kiyi wanka, ayi sallah kiyi bacci Kan zuwa anjima, Zan nemi ki ko"?
"Toh hajiya Nagode"
Ta tashi ta fita

Momy tace "Khalfana Tashi muje muci abinci ko"?

"Toh momy "

Dinining suka nufa duk suka zauna, Khausar ce tayi serving d'insu, suna ci suna Hira, Khalfana tunda ta gane Mama itace Mahaifiyar Khaleel duk ta kasa sake jikin ta, Khaleel ne rike da Jaka a hannun sa yana biye da wani mutumin, yasa babban Riga suna tafiya suna Hira har suka karaso dinining d'in suna zama Momy tayi serving d'insu, Sai wannan mutumin yace "Hajiya itace wannan"? Yana nuna Khalfana, "Eh itace"
"Masha Allah ya sunan ki"?
"mujeedat"
"Masha Allah, mun gode sosai Allah ya Miki Albarka" "amiin nagode"
Khaleel tun da ya zauna kallon Khalfana yake da ke ya zauna a kujeran da ke kallon nata. Khausar ta Lura da kallon da Yayanta yake yiwa Khalfana sai ta ce

"Ya Khaleel kaga bakuwar mu sunanta Mujeedat, had'in Nan fa yazo

Please Login or Register in order to submit comment