Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

haɗe da bayan shi, idanunsa ya buɗe ai ko ya yi arba da ƴar Teddy ta rungume shi a jikinta..

"Ku kuke ganinmu ba mu muke ganinku ba, Mama fatalwa ki mini rai z.. Bai ƙarasa fa aka zafga masa mari, magana ƴar Teddyn ta fara magana cikin wani irin amo marar daɗin saurari..

"Dama kai kasan Allah ne kake kiransa? Mugu azzalume mai son ɓata rayuwar bayin Allah, to saina aikaka lahira inyaso sai kaje can ka yi tijarar da kake yi anan duniya..

Tun da aka mari Sudas ya sume..

Wata sanda ce ta bayyana daga saman ɗakin, kallon sandar ƴar Teddyn ta yi idanunta sun yi jajur suna zubar da hawayen jini ta ce" Ku lallasa mini ɗan iska."

Dukkan Sudas aka shiga yi tako ina ita kuma Teddy ta ɓace daga kan gadon ta dawo samar ɗakin tana kyakyata dariya marar ɗakin ji..

Dukan Sudas ake ba kakkautawa, tun yana cikin suma dukan ya farfaɗo dashi ya shiga kwara ihu yana kiran Daddy da Fadila da Sauban.. Sai da aka masa lilis kana yaji an dena dukansa, a daddafe ya miƙe ya sauko daga kan gadon yana nufar ƙofar fita daga ɗakin, har ya kai hannu zai buɗe ya yi wani tsalle ya dawo baya yana mayar da numfashi tare da ja da baya..

Ƙatuwar macijiya ya gani a jikin ƙofar ta kwanta ta yi luf, idanunta fari ƙal babu ko ɗugon baƙi da cikinsa, kanta guda biyu ne jikinta ma haka fari sol, ƙurawa Sudas idanu Macijiyar ta yi tana fito da harshe tare da fasa kanta tana huci. .

"Shi kenan na mutu na lalace don girman Allah ki yi mini rai fatalwa duk abin da kike so zan miki z... Maganar shi ce ta katse jin ana buga ƙofar da ƙarfi, yana son isa ya buɗe amma ba hali macijiya na jikin ƙofar.

"Yaya Sudas! Yaya Sudas! Ka buɗe mini ƙofa zan ɗauke Teddyna na kasa bacci da ban ganta ba.

Waro idanu ya yi jin muryar Auta sai kuma yaji ta Daddy da Sauban, ihu ya kurma yana faɗin" Daddy ku taimakeni fatalwa a ɗakina za ta kasheni" Ya faɗa yana jan majina."

Da ƙarfi Sauban ya buga ƙofar ta ɓalle, duhu ne ya mamaye ɗakin Sauban ya ce" Kai ɗan rainin hankali ka kunna wutar ɗakin mana tun ɗazu nake jin ihunka." Sudas dake manne a jikin bango yana zare idanu ya ce" Don Allah ku kunna ƙafafuwana sun karye." Dariyar Fadila yaji tana ce masa matsoraci wai ya damesu da ihu a gida, bai ce mata komai ba burin shi bai wuce ya buɗe idanu ya gansa a kusa da su ba. Sama aka yi dashi zai yo ihu yaji an rufe mata baki, a kan kujera aka dire shi idanunsa a rintse.

"Kai dalla can banza ka damu mutane da ihu kana kan kujera a zau ne, ashe ma ba komai kawai dan ka tashi hankalin mu ne, yanzu da Mommy tana nan sai ta wanka maka mari" Fadila ta faɗa tana ƙarasowa bakin gadon tana za ma..

A hankali ya buɗe idanun shi, yana gama buɗewa yaga komai tsam-tsam, tsananin al'ajabi da tsoro ya sa Sudas sakin baki yana kallon su Fadila. Auta ta iso ta hau kan gadon ta ɗauki Teddynta ta rungume tana cewa" Yaya Sudas me ya sa baka kai mini Teddy na ba da ka zo? Ihun ka naji sai na tuna Teddyna a gurinka na ce bari na zo na amsa, ina nufo ƙofar na haɗu da su Daddy lafiya kake ihu a cikin daren nan?" Dariya Sauban ya yi ya ce" Amma kai dai Sudas mugun ɗan iska ne duk ka ishi mutane, yanzu saboda Allah me aka maka kake wannan ihun?" Shi dai Sudas kasa magana ya yi ɗago kai ya yi yana kallon Auta da ta rungume Teddynta tana shafa kanta, gani ya yi Teddy ta juyo kanta tana aiko masa da harara idanunta sun kara za ma manya-manya. "Waiyo! Daddy Wallahi wannan Teddyn ta Auta fatalwa ce ita ce take tsoratani tun ɗazu" Ya faɗa yana faɗowa daga kan kujera..

Dariya suka sa har Daddy , Auta kuwa kuka tasa tana ƙara rungume Teddynta ta ce" Wallahi ni dai babyna ba fatalwa ba ce, haka kawai kaje ka kalli horror film ɗin ka ko kasha giyarka ka ce wai Teddyna faltawa ce akan me?" Ta faɗa tana murguda baki.."

Kowa ya tashi zai bar ɗakin Sudas ya yi saurin binsu ya ce ba fa zai kwana a ɗakin shi ba , haka dai suka tafi ɗakin Sauban yana manne da shi kamar wani baby..


Yau ta kasance Saturday babu makaranta hakan ya sa Auta ta shirya ta shiga ɗakin Daddy ta same shi yana waya, za ma ta yi tana jiran ya gama ,sai da ya gama kana ya dawo gareta fuskar shi dauke da murmushi ya ce" Auta ya dai?" Murmishi ta masa kana ta ce" Daddy ina so zanje gidan su Ƙawata Amra, to bani da kuɗin da zan saya ɗan wani abun na kai mata so nake ka bani dubu goma dan bana so wata ta fini a cikin ƙawayena, inaso nafi kowacce yarinyar a cikin ƙawayenmu" Ta faɗa tana wani cin magani ba alamar wasa."

Wani ƙayataccen murmishi Daddy ya yi najin daɗin kalaman Auta, hannunta ya riƙe cikin nasa ya ce" Da kyau Auta haka nakeso naga kin kere duk wata yarinya a cikin ƙawayenki, yanzu dubun goma ta isa ki saya mata abin da za ki kai mata?"

Dariyar jin daɗi ta yi a ranta tana cewa" Yes Daddy plain ɗina ya tafi yadda nakeso." Miƙewa ta yi tsaye ta ce" E ka bani ya isa inaso zan je direba ya kaini ba zan daɗe sosai ba, yawwa Daddy Mommy ta ce gobe za ta zo ko?"

"Kwarai ma kuwa yanzu ma muke waya da ita gobe za ta iso..

"Kuma Daddy gobe birthday Anty Fadila ni dai ba zan je ko ina ba in ba a hol za ta yi, haba ina dalili mutum sai son kaɗe kaɗe kamar shedani" Ta faɗa tana cuno baki gaba.."

Murmishi kawai Daddy ya yi ya ciro kuɗin ya bata, godiya ta masa kana ta wuce zuwa palo. A hanya suka ci karo da Fadila tasha adon riga da wando jins sun matseta sosai, rigar hannunta ɗaya bakin kafaɗa ne ɗaya kuma dogon hannu ne har gwiwar hannunta.. Riƙe baki Auta ta yi ta ce" Wai wannan ɗiyar Musulmai ce kuma Musulma? An ji kunya dai Wallahi Allah ya sa wani ya miki dukan tsiya a samarin naki, kuma gobe Mommy za ta zo na huta da zalincin ki muguwa."

Mutumelesy! Ni kike zagi? " Fadila ta faɗa a fusace ta miƙa hannu za ta ɗamko Auta. Ke! Da sauri ta juyo suka yi ido hudu da Sauban da yake ƙasa yana kallonsu, Auta na ganin haka ta soma ƙoƙarin sauka Fadila ta biyota suka sauko ƙasa tare..

Da gudu ta iso gurin Sauban ta ɓoye a bayan shi tana cewa" Yaya gata nan karka bari ta dakeni babu abin da da na mata fa."

Fadila na huci ta nemi kamo hannun Auta, da sauri Sauban ya daka mata tsawa taja da baya tana zagin Auta, ita kuwa Auta na mata gwalo tana mata dariya, hakan ba ƙaramin ɓata mata rai ya yi ba fuuu ta wuce sama da gudu tana cewa za su haɗu an jima...

"Na gode Yaya" Cewar Auta tana barin shi ta nufo ledar dake kan kujera ta ɗauka ta wuce zuwa waje, shi ko da idanu ya rakata har ta fita ya saka eapis ɗinsa yaci gaba da jin waƙar shi yana gyaɗa kai ya zau na akan kujera...

Auta na fita Direba ya buɗe mota ta shiga suka bar gidan..

A inda suka saba haɗuwa Direba ya sauketa, kallon shi ta yi ta ce" Direba ka tafi idan Yamma ta yi ka dawo nan ka ɗaukeni." Cike da girmamawa ya ce" To Madam amma yanzu ita Ƙawar taki ina gidansu yake?" Ɗan murmishi ta yi sannan ta ce" Gidansu na can bayan dutsen can sai an jima ka tafi." To ya ce sannan ya shiga motar yabar wajan..

"Ƙawata sannu da zuwa.

Juyowa Auta ta yi da sauri suka yi ido hudu da Amra dake tsaye a baya, sanye take da wata doguwar riga ta yage daga gefe, kanta ta wani ɗan kwalli irin mai sulɓin nan shi ma duk ya yi dauɗa. Turo baki Auta ta yi ta saki kayan hannunta tare da buɗe hannayenta tana kallon Amra dake mata murmushi, ganin haka ya sa Amra ta iso gareta suka rungume juna cikin farin ciki.

"Amra na yi kewarki sosai ya jikin Inna?

Ɗagowa ta yi daga jikinta ta ce" Lafiya lau ni ma na yi kewarki Inna tana nan lafiya zo muje." Binta ta yi suka jera suna ta hira cikin nishaɗi, suna zuwa saitin wata bishiya Auta ta tsaya ta ce" Inuwar nan akwai daɗi." Murmishi Amra ta yi ɗago kan da za ta yi,ta yi arba da wani ƙaton Zaki a samar bishiyar, waro idanu Amra ta yi cikin ƙaraji ta ce" Auta maza ki dawo bayana! Ta faɗa da ƙarfi hakan ya sa Auta sakin kayan hannunta ta kwasa a guje ta dawo bayan Amra jikinta na rawa, sai da ta ɗaga kanta sama taga abin da Amra ta gani ai ko ta ɗauke salati tare da sakin kuka ta ce" Amra mu gudu don Allah kar Zakin nan ya sauko ƙasa, waiyo Allah! Yanzu ya za mu yi Amra? Ta faɗa a firgice..

Amra dake tsaye bata ko motsa ba ta rufe idanunta..

Dirowa zakin ya yi a gabansu yana wage baki, tuni Auta ta yi baya luuu ta zube a ƙasa sumammiya..

Cikin tsananin ɓacin rai Amra ta ce" Ka tafi na ce! Mai ya kawo ka nan? Za ka tafi ko saina canja maka halitta yanzun nan? Ta ƙarashe maganar tana buɗe idanunta wanda ya yi jajur. Suna haɗa idanu da Zakin ya yi wata irin kururuwa ya yo kanta gadan-gadan.....




_*Taku har kullum Maman Nusaiba ce*_
[30/11, 14:41] Umma Amjad: _*🧟‍♀️ALJANAR GIDANMU 🧟‍♀️*_



Daga Alƙalamin

_Sarat Alƙasum (Maman Nusaiba)_


_🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_


_Masu son littafin *ABBA NE* complete N500 ne ku tuntubeni ta WhatsApp number na👇🏻_


*بسم الله الرحمن الرحيم*

0️⃣5️⃣


Hannu Amra ta ɗaga sama sai ga wata takobi ta bayyana a hannunta, cake takobin ta yi a ƙasa har sai da ƙasar gurin ta yi wani irin girgiza. Ja baya Zakin ya shiga yi tana binsa riƙe da takobin, cikin kakkausar murya ta ce" Ni har zan baka umarni kaƙi bi? Yaushe ka soma taurin kai ban sani ba Aliyu? Mai wannan yarinyar ta maka da ka firgitata haka? Kasan kalar hukuncin da nake yiwa mutane idan suka taɓa Auta? Babu ruwana da tsakanina da kai tsam zan iya aikaka lahira indai ka ce za ka taɓa mini Ƙawata" Ta ƙarashe maganar tana ɗamko wuyan Zakin."

Ƙoƙarin kwace kanshi ya shiga yi amma ina ta masa ƙwaƙƙwaran ruƙo, sai da taga ya galabaita kana ta sakeshi ya faɗo ƙasa tim. "Ka kula bana son shiga abin da bai shafeka ba..

Cikin fushi Zakin ya soma rikidewa ya dawo wani kyakyawan saurayi matashi mai tsananin kyau, jikin shi sanye da ƙananan kaya, kallon Amra ya yi data saɓa Auta a kafaɗa ya yi, cikin shashekar kuka ya ce" Haba Yaya Amra yanzu ke kina ganin abin da kike yi daidai ne? Ko kin manta da abin ahalin yarinyar nan suka mana ne? Gaskiya ki canja tunanin dan ta taimakeki dhi kenan sai ki zubar da makaman yaƙinki ki ce ba za ki iya rama cutar da aka mana ba? Kina nufin sunci banza kenan? Wallahi ba zai yiyuba da Yaya Amina tana nan ai kin san ba ki isa ki fara wannan alaƙar da yarinyar nan ba, ko kuwa dan kinga ba ɗaki ɗaya muka girma ba shi ya sa kike abin da kikeso? K..

Ya isa Haidar! Ta faɗa a tsawace tana kallom shi, a kufule ta ɗamko hannun shi suka iso bakin duntsen ta shafa a fusace ta ce" Banza mai manta alkhairi kalli nan ka gani" Ta ƙarashe maganar tana nuna masa inda ta shafar..

Auta ya gani a cikin yara tana raba musu abinci sai murmushi take saki, wani makaho ta hango zia tsallaka hanya da sauri ta aje hular abincin ta nufi inda yake da gudu, taimaka masa ta yi ya tsallaka hanyar kana ta dawo ta ɗauko abincin dayawa ta kawo masa..

Murya makahon suka ji yana cewa" Yarinya kina da kirki Allah ya kareki daha dukkan sharri, in sha ba za ki wulaƙanta ba a idon Duniya." Amin ta faɗa tana murmishi kana ta wuce.

Amra ta shafa jikin dutsen ta kuma cewa" Kalli nan ɗan rainin hankali." Autar ce dai ta fito daga ciki jin hayaniyar Babanta, Maigadi ne durƙushe Daddy na masa faɗa hakan, tana gefe sai da ya gama ya fice ta iso ta tashi Maigadi tana ba shi haƙuri, tambayarsa ta shiga yi akan me Daddy ke masa faɗa haka baiga girman shi ba?

"Auta albashina nakeso wata biyu kenan bai bani ba, kuma Ƴata ake yiwa aure idan har bai bani ba ban san da mai zan fita kunya ba" Ya ƙarashe maganar yana zubar da hawaye..

Ranta ne ya yi matuƙar ɓaci ta bashi ta juya ta ce tana zuwa yanzu za ta dawo, daret ɗakin Daddy ta nufa ta buɗe lokar gefen gadonsa, kuɗi ne ɗauri-ɗauri a ciki daga kan naira zuwa dollars, hannu tasa ta ɗauko ɗaurin 'yan rafa gida biyar ta zuba a cikin rigarta ta fito da gudu gudu, a palo ta haɗu da Fadila tana aika mata ruwan ashariya amma bata kula ta ba ta wuce ta dawo gurin Maigadi ta kama hannunsa suka shiga ɗakinsa, kuɗin ya aje a gabansa ta dubesa ta ce" Baba ka rabu da Daddy bashi da tausayin na ƙasa da shi, ka ɗauki wannan kuɗin kaje ka sayawa ƴarka kayan ɗaki zan cewa Mommy kana yiwa ƴarka aure sai muje ranar ɗaurin aure.."

Baba Maigadi ya tsorata da ganin kuɗin da yake gabansa, ya ce ba zai dauka ba ya yi yawa, sai da ta ɓata rai kana ya ɗauka ya mata godiya sosai tare da mata addu'a, sannan ya haɗa kayansa tana tsaye ya fito ya yiwa sauran abokan aikinsa sallama ya tafi, sai da taga bayar layin kana ta dawo ciki ta shige ɗakinta...

Juyowa Amra ta yi ta dubi Aliyu ta ce" Yanzu wannan kake so ka kashe Yarinyar da take taimakon al'umma? To wannan kaɗan daga cikin alkhairanta. "

Ajiyar zuciya Aliyu ya sauke ya ce" Yo haƙuri Yaya Amra na ɗauka itama haka take amma daga yau na dena bibiyar rayuwarta, kin san kuwa shekarar data wuce na firgita Yarinyar nan amma ta dake ta dinga yin addu'a, ganin haka sai na rabu da ita dan ta nemi tsari a wajan Allah ya kare ta daga duk abin da zai cutar da ita kana ta kwanta, amma kuma Yaya Amra haka za mu rabu da wannan ahalin bamu ɗauki fansa ba?"

Dafa kafaɗarsa ta yi tana kallonsa cikin saisaita murya ta ce" Wa ya ce maka kyalesu za mu yi?Ai dole mu rama abin da suka mana ba fashi, ita ɗin ce dai ba za mu taɓa cutar da ita ba.."

Jinjina kai ya yi cike da gamsuwa da maganarta ya yi gaba ta bisa a baya..

Fadila ta samu Daddy zaune a palo, zama ta yi tare da zamewa ta ɗaura kanta a cinyarshi cikin shagwaɓarta ta ce" Daddy kasan dai gobe ake yin birthday na ko?"

Shafa kanta ya yi yana murmishi ya ce" Na sani sosai to kike so ki yi a taron naki?"

"Daddy nifa a gida nake so mu yi shagalin birthday bana son zuwa hôtel wannan karon..

"Ok to shi kenan kinga gobe Mommyn ku za ta iso Ƙasar sai ku tarbeta ayi shagali sosai, amma ni zan ɗan je wani meeting da aka gayyaceni ƙarshe goma zna fita, idan na dawo da dare sai mu yi koda hirar dare ne." Tashi ta yi daga kanshi ta kai masa runguma tana dariya ta ce" Godiya nake Daddy naga ka mini transfer ɗin kuɗi zanje nida su Mufy mu sayo duk abin da ya kamata.." Murmishi kawai ya mata ta miƙe tabar wajan, babu jimawa ta fito cikin shigarta na riga da sket kayan sunbi jikinta da ƙyar take tafiya tana wani ɗaga hanci sama ta wuce...
*************************
Babu inda su Amra suka nufa sai cikin wannan dutsen, wani babban gida ne ginin laka, wata ƙofa suka nufa sai gasu a wani babban palo daret wani ɗaki suka nufa, akan gado Amra ta aje Auta tana sauke numfashi ta juyo ta kalli Aliyu idanunta sun yi jajur ta ce" Aliyu je ka kawo mini ruwa."

Da mamaki yake kallonta wai ruwa to me kuma Yaya Amra za ta yi da ruwa?" Ya faɗa a cikin ranshi. Tsam ta gano abin da yake tunani ta saki murmushi ta ce" Kaga ka fita ka yi abin da na umarce ka." Jinjina kai kawai ya yi ya fice daga cikin ɗakin..

Za ma ta yi tare da kai hannu ta soma shafa fuskar Auta tana kiran sunanta, a hankali ta fara buɗe idanunta har ta gama buɗe su akan Amra dake mata murmushi. Da sauri ta zabura ta tashi ta kama hannun Amra cikin nuna tsoro ta ce" Amra ba dai abin da ya sameki dai ko? Ina Zakin nan yake da na gansa a sama?" Ta ƙarashe maganar da tambaya tana shafa jikin Amra."

"Ai na kore shi ki dena jin tsoro Ƙawata yanzu dai gamu a gidanmu na kawo ki. Da sauri ta ɗago tana kallon ɗakin wanda ba shi da komai sai gadon ƙarfe wanda take kai, gefe ta kalla inda taga langogi an jerasu ƙasar ɗakin rairayi ne ja a shara tass babu wani datti, ajiyar zuciya ta sauke ta ce" Ashe nan ne gidanku to ina Innar take?" "Inna ai bata nan taje Unguwa daga ni sai Aliyu ƙanena gashi nan a bakin ƙofa zai shigo" Ta faɗa tana mata nuni da ƙofar ɗakin..

Kallon ƙofar ta yi inda ta yi arba da Aliyu tsaye yana mata murmushi, itama murmishin ta mayar masa ta ce" Ya sunanka?" "Aliyu sanana" Ya bata amsa yana ƙarasowa hannun shi dauke da langa babba da ƙarama, yana isowa ya aje a gefe ya zau na..

Buɗewa Amra ta yi ta miƙawa Auta ba muso ta amsa tana kallon abin da yake ciki, koko ne a ciki ɗayar langar kuma ƙosai ne yana turiri, cikin zumuɗi ta sauko ƙasa ta zau na tare da yin bismillah ta soma cin ƙosan tana korawa da kokon. Sai da ta ci ta ƙoshi kana ta janye tana hamdala, murmishi ta yi mu su ta ce" Ban taɓa cin ƙosai mai daɗi irin wannan ba wa ya yi shi?"

Aliyu ne ya yi saurin cewa" Yaya Amra ce ta yi ai."

"Au kuwa kin iya Ƙawata.

"Na gode.

Hira suka soma cikin nishaɗi, suna a haka sai ga Amina ta shigo bakinta dauke da sallama. Kallonta Amra ta yi da mamakin ganinta, itama Amina kallon nata take tana sakin murmishi, a nutse ta ce" Yaya Amra wai mamakin ganina kike?"

"E sosai ma ina fatan dai lafiya dai ko?

"Gaskiya akwai magana Yaya Amra zp muje kiji. Da sauri Amra ta suka fita ta cewa Auta tana dawowa suka fita, can bayan ɗakin suka nufa su ukun, Amina ta ruƙo hannun Amra ta ce" Yaya Amra akwai matsala yanzu nan naje yankin su Amsar ya ce yana nan zuwa gurinki ki tayashi yaƙin ɗaukan fansa akan wani mutum, ke kuma nasan bakwa shiri dake sun tsara yadda za su tsaraki ki yarda da su yanzu haka nan da sati ɗaya za su iso can inda muke..

Jinjina kai Amra ta yi sai kuma ta yi murmishi ta ce" Amina karki damu zan ji da duk wani daɗin bakinsu, ki kwantar da hankalinki babu abin da zai faru sai alkhairi.."

Aliyu ya ce" Nifa ina tunanin Amsar akwai abin da yake nufi damu."

"Karka damu Aliyu babu abin da zai faru mu koma Yamma ta yi inaso na kai Auta gida..

Juyawa suka yi duk suka nufi ɗakin inda suka samu Auta tana gyanyadi , tadata Amra ta yi, kallonta Auta ta yi cikin muryar bacci ta ce" zan tafi gida Amra bari na kira Direba ya zo ta ɗaukeni." "A a ni zan kaiki da kaina tashi maza muje na rakaki har gida" Cewar Aliyu yana murmishi." Ƴar dariya ta yi ta ce" Kai Aliyu a ina kasan gidanmu? Kaga ko Amra bata taɓa zuwa gidanmu ba." "Da gaske fa kedai ki tashi mu kaiki gida kuma kar ki mana kwatance daret gida za mu kaiki. To shi kenan kace dai ku 'yan baiwa ne da alama ko? Miƙewa ta yi tsaye Amra ta kama hannunta tana dariya ta ce" Auta rufe idanunki." Cike da mamaki ta rufe idanun nata tana cewa" Kai yau dai zanga baiwar Aliyu inaso yanzu na ganni a gida indai da gaske kasan gidanmu" Ta ƙarashe maganar tana ƙara riƙe hannun Amra..

"Buɗe idanunki Auta mun kawoki har bakin ƙofar gidanku..

A hankali ta buɗe idanunta, tana gama buɗe su ta ganta a bakin get ɗin gidansu, cike da mamaki take kallon su da kuma al'ajabi ta ce" Amra taya ku ka san gidanmu?"

"Hmm ba dai kin ce bamu sani ba to gashi mun kawoki, yanzu sai an jima mu za mu koma gida" Cewar Amra tana rungumar Auta...

"Na gode Ƙawata sai mun haɗu zuwa jibi gobe Islamiya ba tabbas ba ne muga juna, amma jibin zamu haɗu..

Sai da suka ga tafiyarta kana suka ɓace daga ƙofar gidan..


Tana shigowa gaishe da Maigadi ta yi kana ta wuce ciki, tin kafin ta shiga sautin kiɗa ya fara ziyartar kunnenta, tsaki taja tana haɗe tasa Kai ta shiga cikin palon...

Ko kula kowa bata yi ba ta kawar da kanta gefe zata wuce, har ta hau kan stap taji muryar Mufy kawar Fadila na cewa" Ke Auta dawo nan na ce miki ko ba ki gansu ba ne" Ta ƙarashe maganar tana aiko mata harara..

Ba juyo ta kallesu ba ta yi saurin wucewa sama..

"Kan uban can! Wai Fadila yaushe wannan Ƙanwar taki ta raina mutane ne? Nifa da ni Ƙanwata ta yiwa Ƙawata Wallahi sai na kusa karya ƴar iska" Ta ƙarashe maganar hura hanci..

"Hmmm ki rabu da ita ɓakin ciki ne yake damunta dan taga Daddy ya sakar mini kuɗi ba iyaka ina shagalina, ki rabu da ita dama da safe ta zageni ta tafi, so nake na gama komai zan waiwaye ta ai...

"To gara dai dan naga alama Yarinyar nan gaba sai ta soma dukanki..

*Washe gari*

Tun da sassafe ƙawayen Fadila suka sauka gidan su, duk wanda ya zo sai an cika palon da ihun murna har duk suka gama zuwa saura saurayinta ya rage bai zo ba, a ɓangaren Auta kuma murna take Mommy za ta zo gida itama ta huta da hantaran da Fadila take mata, ko ba komai Mommy ba za ta bari ta daketa ba..

Cikin sauri ta yi wanka ta saka riga da sket ta sauko ƙasa fuskarta ɗauke da murmishi mai ƙayatarwa, dukkansu 'yan palon zubawa Auta idanu suka yi suna binta da kallo musamman ma mazan, wani friend Fadila ya kasa daurewa ya ce" Wow cute girl Fadila wannan Ƙanwar mu ce ko?"

Cikin iyayi Fadila ta ɗaura kafa ɗaya kan ɗaya tana shan ƙamshi kana ta ce" Yes this is my sister, ko ta birgeka ne?"

"Kai sosai sai dai kamar yarinyar yanzu ta soma girma ma, idan

1 Comments On ALJANAR GIDANMU
avatar
taskar

2 years ago

Reply

Good

Please Login or Register in order to submit comment