Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dan Ba'ana mugun babarbarene mai baƙar zuciya.

Haka dai aka tashi wannan taron da yake dama sun gama tattauna yadda zasuyi farmakin.


Washe gari ranar wata Tuesday 21 November 2017 itace ranar da har abada al'ummar Rugar Bani bazasu mance da itaba a tarihin rayuwarsu, itace ranar da duk motsin da numfarfashi Shatu zatayi sai ta tunashi ranace data girgiza, zukatan al'ummar musulmai, ranace da tasa duk wani bafulatani makiyayi jin ƙuna da tafasar zuciya.
Ranace da tada hankalin al'ummar ƙasarmu nan dama maƙotanmu.

Tunda safiyar ranar, dattawan garin suka gama shirinsu cikin shigarsu ta al'farma, Malam Liman (Bappa) Arɗo bani Jauronsu, Ahaji Horo da Ahaji Umaru, kana Malam Yero, da kuma Alhaji Sa'idu.
su rai takwas dai suka shirya cikin kamala da mutunci. Junaidu ne yake cikin Shikan ya samo musu mota kirar siyana wacce suka ɗauki shatarta, domin zai kaisu har cikin fadar masarautar Joɗa kuma zai jirasu. Su dawo tare.


Nan suka shiga Mota gaba ɗayansu, suka tafi.

Kai tsaye har bakin masarautar suka tsaya dan an hanasu shiga,
sai da ɗaya daga cikin hadiman dake tsaron ƙofar, yaga duk manyan daddatawa ne yasa yaje ya samesu bayan sun gaisane sukayi mishi bayanin abinda ke tafe dasu.
Jin abin babbane yasa yaje yayiwa sarkin ƙofa bayanin.
Nan shima yaje suka gaisa suka ƙara jaddada mishi, zancen abinda ke tafe dasu, sannan
sukayi musu izini suka shigo cikin asalin farfajiyar mashigar masarautar.
Kan kujerun dake jere a wurin suka nuna musu su zauna.
Bayan sun zaunane sarkin kofa yaje, wurin sarkin fada ya sanar mishi, to nan sarkin fada ke cewa.
"To ai babu abinda zamu iya musu, tunda shi GARKUWAN FULANI, baya ƙasar waye zai saurari kukansu, suje sai ya dawo su sake zuwa".
Cikin rauni sarkin ƙofa yace.
"Ranka ya daɗe sarkin fada, da dai an nema musu izinin ganin mai martaba, domin bazaiji daɗi ba in yaji sunzo kuma an medasu".
Cikin isa da izaya sarkin fada yace.
"A kul sarkin ƙofa ka tsaya iya matsayinka, kaje kace suyi maza su bar nan domin GARKUWANSU baya nan".
Cikin sanyi da mutuwar jiki sarkin ƙofa ya juya ya fita, koda yaje ya sanar musu, abinda sarkin fada ya faɗa hankalinsu yayi masifar tashi.
Cikin tashin hankali Arɗo Yabani yace.
"Shikenan danmu fulanine makiyaya mazauna daji, sai ya zama matsalarmu ba abar dubawa bace, wa al'ummar birane, duk inda muka kai kukanmu sai a koramu".
Cikin sanyi sarkin ƙofa yace.
"Kuyi haƙuri ba korarku akayiba, in sha Allah za'abi kadunku, wlh shi kanshi mai martaba in zaiji abinda sarkin fada yayi to zai barranta dashi, kuma haka nan shima GARKUWAN FULANI in da zaiji abinda sarkin fada yayi wallahi zai haɗu da fushinsa mai tsauri, domin shi zuciyar Sheykh zuciyace mai cike da imani da tausayi".
Cikin rauni Alhaji Haron yace.
"Ana binmu ana kashemu, ana sace yaranmu ana kora dabbobinmu.
Munje Police station an koramu, da mukaƙi tafiya suka watsa mata tiyagas, muje masarautar Numan akaci mana zarafi, sannan yanzu mun gudo gareku da yaƙinin zakubi kadunmu sannan kuma zaku koramu, so kuke mu ɗauki makami domin ramuwa ne?".
Da sauri suka juyo gaba ɗayansu jin muryar Jamil da yanzu ya iso wurin da hadimanshi, cikin sanyi yace.
"A a Baba kada ku ɗauki makami domin ramuwa zuwanku nan shine babban abinda ya dace".
Cikin jin daɗi suke kallonsa, murmushi sarkin ƙofa da sauran hadiman sukayi dan sun san yanzu dai sarkin fada bai isa ya hanasu ganin Maimartaba. Domin yanzu bai fito fada bama tukun so zasu ganshi a kebantaccen wuri na musamman.
Cikin kulawa da sakin fuska Jamil yace.
"Baba ku biyoni".
Cikin jin daɗi sukace mishi to, kana suka bishi a baya.
Ta gaban shashin Sarkin fada suka shiga, kai tsaye har cikin fada ya shiga dasu,
shida kanshi yasa hadimai suka kawo musu ruwa.
Sannan a nitse yace.
"Baba ku zauna a nan zanje in sanarwa mai martaba, duk sanda ya fito daku zai fara, tattaunawa
In da masu buƙatan zagawa gacan wancan kusurwar in kumbi cikinta zata sadaku da bayi".
Cikin jin daɗi sukace.
"Mun gode yaro Allah yayi maka al'barka".
Amin Amin yace kana ya sallamesu ya fita.
su kuma sukaci gaba da zaman jiran fitowan sarki.


A can kasa mai tsarki kuma,
Sheykh ne zaune a gaban Sitti, kana Haroon da Jannart na gefenshi Sheykh Aliyu Abdulkareem, kuma da Sheykh Jabeer Aliyu da wasu manyan malamai na zuriyar tasu duk suna zaune a cikin falon.
Jazrah kuma na gabanshi da wani tray mai masifar kyau da tsada.
Madara da zuma take zuba mishi a cikin wasu ƴan kananun kofuna masu masifar kyau da ɗaukan hankali.

Wannan ya kasance al'adarsuce ta baiyana nuna yarda da soyayya ko akasinshi, indan ana son a haɗa yara aure, to za'a tattauna tsakanin manya, bayan sun gama dai-dai-ta magana tsakaninsu kamar yadda yanzu su Mai alfarma Jalaluddin da Sarki Nuruddeen, da kuma su Sheykh Jabeer Aliyu da babban babansu Sheykh Aliyu Abdulkareem da kuma Sitti suka gama haɗa zancen auren Jazrah da Sheykh Jabeer, to yanzu ta zuba mishi madara da zuma a gaban kowa, ta ajiye mishi, idan ya ɗauki kofin madara to yana nufin yana sonta ya kuma amince da ita da aurenta.
In kuma ya ɗauki kofin zuma, to yana nufin ya tsaneta baya kuma sonta bazai kuma auretaba bare ya zauna da ita.
Za'ayi komai a gaban manya ne, don suga zahiri kuma a tsarin ko ɗan uwanka zai iya yi maka zaɓin da kuma in dai am zaɓa maka sai ka aura.

Shiru sukayi baki ɗayansu falon, kowa da tunanin da yakeyi.

Sheykh Jabeer dake zaune a tsakiyarsu cikin shiga ta al'farma sai sheƙi al'kyabbar sa keyi, ga tattausan hirami a kanshi, ido ya lumshe daya gane manufarsu.
"Domin shi basu gaya mishi cewa, zasuyi wannan abun bane daya sani wallahi da yasan duk yadda zaiyi ya gudu, ya tafi harami, har sai sun gaji sun watse.
A hankali ya kalli Sitti dake kallonshi cikin rauni da alamun.
"Dan Allah kada kace, a a yar ɗan uwanane, kada ka bamu kunya nida kakanninka maza yar uwarkace kasan tarbiyarta".
Kauda idonshi yayi daga kallon Sitti, wani irin kallo yayiwa Haroon daketa yi mishi, murmushin muguntan yau dai an titseka baka da hanyar tsira.
Cikin ranshi yake mgnar zuciya.
"Ta yaya zan amince ince zan aureta? Dame zan zauna da ita?".
Sai kuma ya ɗan fidda nannauyan numfashi.
"To idan ban amince da aurentaba me zamcewa, waɗanannan bayin Allah'n da sukayi min dukkan gatan duniya, na zauna a gidansu tsawon shekaru masu yawa nayi karatuna har na gama, sukemin komai na rayuwa, suna nuna min soyayyar da mahaifinama baya nuna min, da wanne idon zan kallesu inna ɗauki zuma alamar na tsani yarsu?".
A hankali ya buɗe idonsa, jin muryar. Sheykh Aliyu Abdulkareem kakan Mamanshi kenan, baban kakarshi Sitti dottijon daya yake sonshi tamkar ranshi yana cewa.
"Sheykh Jabeer Habeebullah Nuruddeen Bubayero Joɗa, kayi zaɓin da ranka keso, bamu da nufin yi maka dole, sai dai ina da burin aurar maka jikata Jazrah ɗiyar mai sunanka. Ina so da fatan ganin nasabarka ta cika, cikar nasabarka kuwa, shene aure."
Wani irin sassanyan numfashi ya shaƙa a hankali, wasu irin zafafan tunanuka ne ke zirya a zuciyarshi".
Cikin harshen hausar katsinawa, Haroon yayi mgna can ƙasa yadda ko Sitti bazata jisuba.
"Sheykh kafa, shanyamu, nifa zan ɗaukar maka Madara".
Ido ya lumshe tare da ɗan jingina da jikin kujerar da yake zaune, wanda yake kusa da Sheykh Abdulkareem.
Sitti ce ta ɗan kalli Haroon tare da mishi alamun ya taɓo Sheykh.
cikin harshen larabci Haroon ya kalli kakar tasu, tare da cewa.
"Sitti ai nasan zaɓinsa, bari ki gani in nuna miki".
Ya ƙarishe mgnar yana kai hannunshi kan kofunan.
da sauri Sheykh Jabeer ya buɗe kekkyawar ƙwayar idanunshi da wasu ke kiransu da zaiba, wato kamar idon mage, idon ya ɗan zaro ganin Haroon yasa hannunshi kan kofin M...!




😂😂😂😂😂

Masu cewa na kulle musu kai kada ku damu zan kuce kawunanne, lokaci ne😂🙏🏻🤝🏻

By
*GARKUWAR FULANI*
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

🐄🕊️🌈🦚🐍🤴🏻💘

*GARKUWA*

PAGE 12

NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

📝🍇🐄🌈🦚🤴🏻💘



Littafin GARKUWA na kuɗine turo katin mtn na ɗari uku ta wannan number 09097853276. KO kiyi min TRANSFER ɗin 1k ta asusuna na Jaiz domin samun shiga Special Group, wanda cikin kwanaki ƙalilan za'a gama littafin da izinin ubangiji. Ga asusun kamar haka 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa, 1k ne SPG sai ki turo min shaidar biyan
ki ta wannan number 09097853276.


Gareku iyayen ƴan mata da za'a aurar, akwai sittin amare mai kyau na gyaran jiki, bisa farashi mai sauƙin, akwai na manyan robobi akwai na ƙananan robobi, akwai haɗin masu jego, da na maida tsohuwa yarinya, sayan na gari meda kuɗi gida, in kayan gyaran kikeso ki fara min text message ta inbox ta wannan number 09097853276 sai ki gaya min kaya kikeso, kana sai ki kirani to nan zan ɗaga kirankin sai muyi mgn zaki turo kuɗi ta ACCOUNT number ni kuma zan tura miki kaya ta mota, duk garin da kike a Nigeria ina aikawa, in dai ba lungu yayi sosaiba. Kana mutanenmu mazauna ƙasashen ƙetare kamarsu Saudia, India, Gabon, Ghana, Niger, Cameroon, da dai sauransu in kinada dalili kayana na zuwa can cikin salama. Ina saida kaɗan-kaɗan ina kuma bada sari.



A dai-dai kan kofin madarar ya sa hannunsa, alamum zai mishi zaɓi kenan, murmushi yayi dan ya samu damar, da zai tserewa tsarinsu. Cikin ihima da sanin makaman kariyar kai daga jin kunya ko yin abinda zai ɓata ran wani, ƙafarshi ta dama dake kusa da hannun Haroon yasa cikin hikima ya bugi hannun Haroon da ke gab da ɗaukar kofin.
ture hannun yayi da babbar yatsarsa, wanda, hakan yasa hannun Haroon ya bugi kofunan da ɗan karfi, sai gashi duk sun tuntsure a tsakiyar tiren madarar da zumar kab suka malale cikin tray ɗin.
A tare suka zubawa tray idanu gaba ɗayansu.
Sitti kuwa wani irin kallo tabi Madarar dashi.
Shi kuwa Sheykh Jabeer, cikin iya taku da kamalarsa murya a mutunce ya kalli Haroon daya kafeshi da idon tuhuma, cikin harshen larabci da kamala yace.
"Harooon meyasa baka da nitsuwa?".
Cikin tarin mamaki Haroon ya gwalo ido tare da cewa.
"Haaahh".
sai kuma ya kalli Sitti da ta kwaɓe fuska tamkar zata kurma ihun takaici.
Shi kuwa Sheykh Jazrah ya zubawa ido, ganin yadda ta zuba mishi kekkyawan idanunta, wanda suke sheƙin hawayen dake nuni da zazzafan son da takeyi mishi.
Kauda kwayar idanunshi yayi, da sauri.
Jannart kuwa hannun Sitti ta kamo ganin zata jawo tray.
A hankali Sheykh Khalillullah wanda yake ƙanin Sitti ya gyara zama cikin sakin fuska da murmushi ya kalli jikan nasu, nitse yace.
"Laaba'as". Dib-dib haka ƙirjin Sheykh Jabeer Habeebullah ya fara bada sauti, fahimtar kakanun nashi zasu ɗaura zabin kan, fahimtar lafazin Haroon.
Shi kuwa Haroon, wani irin murmushi jin daɗi yayi.
Shi kuwa dottijon nan, ido ya zubawa ƴaƴanshi da jikokin ƴaƴan nashi, da wasu jikokinshi. Kallonsu yake yana nazartansu.

A hankali wayar Sheykh Jabeer ta fara bada wani sauti mai masifar sanyi da daɗin sauraro, sautin gwauraye yake da kukan sassanyan tsuntsaye.
da sauri ya zaro wayar a al'jihun tattausan al'kyabbar tasa.
Ganin sunan Maimartaba Nuruddeen ne, ya sashi sakin wata sassanyan ajiyan, cikin ladab ya kalli Sitti, kana a hankali ya kalli Sheykh Abdulkareem, cikin sanyi da nitsuwa yace.
"Mai martaba Nuruddee ke kirana, bisa alamu da babbar mgna domin baya kirana haka banza".
Murmushi dottijon yayi, domin ya fahimci hanyar fecewa, Sheykh yake nema, hakan yasa ya mishi izinin tafiya.
Cikin sauri Sitti ta yunƙuro da niyar yin mgna, sai kuma tayi shiru, sabida nuni da tayi shirun da mahaifinta yayi mata.
Shi kuwa Sheykh Jabeer, a hankali ya yunƙara, ya miƙe ya nufi hanyar fita bayan yayi musu, su huta gajiya.

Kai tsaye Side ɗinsu ya wuce.
Yana shiga kai tsaye bedroom ya wuce, gyara al'kyabbar jikinshi yayi kana, ya zauna bisa wata tattausar doguwar kujera.


A nan ƙasar kuma, cikin faɗar masarautar maiartaba Sarki Nuruddeen.

Bayan Jamil ya fita, wurin da yayiwa su Bappa Masauki,
kai tsaye, sashin kakanin nashi ya nufa.
Bayan an mishi isone, ya shiga, ya gaisa da kakan nashi kana ya ƙara da cewa.
"Mai martaba, akwai baƙi ma buƙatar kulawarka, suna tsumayinka".
Murmushi mai cike da kamala farin dottijon bafulatanin yayi, cikin ratsin sarauta yace.
"Yau ka zama, sarkin fada kenan, kaine mai yiwa baƙi iso ko?, ko dai matane baƙin dan nasan ta nan kafi ƙarfi". Ya ƙarishe mgnar da yanayin tuhuma.

Kanshi ya ɗan shafa, kana a hankali ya girgiza kansa tare da cewa.
"A,a mazane dattawan Fulanin dajine,".
Ido ya ɗan zuba mishi kana yace.
"Kaje kace a kula dasu, gani nan zuwa yanzu".
Kanshi ya ɗan rusunar tare da cewa.
"Nasa an basu dukkan kulawar da zasu, buƙata, zuwa yanzu sunfi buƙatar ganinka fiye da komai".
Kai ya ɗan jinjina alamar to.
Yunƙurawa yayi tare da cewa.
"A fito lfy".

"Allah yasa".

"Amin Amin". Yace kana ya fita.

Shi kuwa Sarkin ya fara shirin, fitowa fada.


A can sashin Sheykh Jalal ne, zaune da Ya Jafar, Aunty Juwairiyya na gefenshi.
karatu yakeyi kamar koda yaushe, tun jiya yaƙi barin sashin Sheykh, koda aka kira Sheykh Jabeer video call, ya ganshi sai yayi ta kuka.
Wannan abun shiya ƙara tada hankali Sheykh Jabeer.

Yana yawan, bin Jalal, wanda mutane ke zaton ko dan tsananin kamannin da Jalaluddin keyi da Sheykh Jabeer ɗinne yasa, yake ganin kamar shine, to sai dai sam Jalal baya iya mu'amalantar Babban yayan nasu, kamar yadda Sheykh keyi har yake sama mishi nitsuwa, sai dai shima yana iya yinshi.


Shigowan Hajia Mama da hadimanta ne, yasa Juwairiyya, jin rauni, a take hawaye ya cika mata idanu. A duniya bata da babbar matsala sama da larurar mijinta.
Ita kuwa Mama, gefenshi ta zauna, cikin sanyi ta kalli, Jalal da fuskarshi ke murtuƙe kamar ko yaushe,
cikin baiyanar damuwa tace.
"Ya za'ayi ya samu gamsuwa da kulawarka, a yadda kake haɗe fuskarnan tamkar wanda aka sanarwar labarin mutuwar uwarshi, ba haka Sheykh ke mushiba, yana kula dashi, da tausayawa da sakin fuska tunda yasan larurar haukace dashi, amman kai ko yaushe kana nan kamar boss".
Sai ta kuma kalli Jakadiyarsu Kana, ta kalli Jamil dake waya da alamun da budurwarshi yake mgna, hararanshi tayi tare da cewa.
"A haka kuke samawa kanku tabon nunawa a rayuwarku, shi wannan ya zama, mahaukaci, shi Jalal ya zama tantiri ɗan shaye-shaye, kai baka da aiki sai bin matan banza. Kuna samin ciwo a raina, shima kanshi Sheykh duniya ta zata fara zargin cewa mazinacine shiyasa yaƙi yin aure ya zauna, sinƙitin fakitin. Shi kuwa Affan in banda shashanci da tarin ƙuruciya babu abinda yasa a gaba.
Ya kukeso inyi, ya kuke son mahaifinku yayi? Yana da yaya maza har ku shida, amman ku biyar manyan duk kun zama, ababe masu taɓo a idon duniya, ya za'ayi yayi mararin gadar mulki a hannun mahaifinshi, tunda yasan shi bashi da masu gadarsa, a kusa,ku duba, Imran da yake uwarsa ta tambaɗaku, ta nesan taku da mahaifinku, sai ta kusanta ɗanta da mahaifin naku.
Shiyasa mahaifinku keta ƙin amsar sarautar har sai randa Imran ya mallaki hankalinshi, ku kuwa kun zama ababen kyarata. Yaya zanyi da raina.
Shiru sukayi gaba ɗayansu,
Shi kuwa Ya Jafar sai ƙara sautin karatun yayi. Yanayi yana zubda hawaye.


Shi kuwa Jalal, shiru yayi yana riƙe da hannun Jafar ɗin.
Jamil kuwa katse kiran yayi.
Affan kuma wanda dama tare suka shigo, fuska ya ɗan kele, cikin irin matsayin da ƴan auta kedashi a wurin iyayensu yace.
"Mama, shifa zato zunubine koda ya kasance gsky. Ki dena jifar Mommy da batun wai ita ta tambaɗamu, ya za'ayi keda kanki ki rinƙa suffantamu da marasa nagarta mu dai gsky ba a tamɓaɗe mukeba,
Menene a cikin mulki da sarauta, Mama akwai wani mulkine matabbaci a duniya banda mulkin mahaliccin mu, in ma Imran ya gaji sarauta menene a ciki ɗan uwanmu nefa".
Cikin sanyi ta girgiza kanta a hankali tace.
"Ɗan uba dai ba ɗan uwaba".
A tare suka zuba mata ido baki ɗayansu.
Aunty Juwairiyya kuwa, ruggume yarta kawai tayi, tana jin ranta na suya.

A cikin fada kuwa, tun tuni Maimartaba ya fito, yana shigowa suka gaisa dasu Bappa ya amshesu a mutunce, cikin kulawa, da mutuntaka, bayan sun gaisa ɗinne suka koro mishi jawabin abinda ke tafe dasu.
Shiru mutanen fadar sukayi baki ɗayansu, sai muryar Ardo Bani, da yake ƙare zancensa da cewa.
"Babban tashin hankalinmu, kullum ɗauki ɗaɗɗayan da akeyima yaranmu da tsoffinmu.
Kana a sace dabobbin mu, in mun kai kukanmu ga hukuma ko masarauta sai ayi burus damu, koma a ƙara mana da cin zarafi ko ƙazafi. To gashi yanzu ankai matakin ana sace mana yara, ko gawarwakinsu ba'a bar mana, shiyasa mukayi tattakin isowa gareka adalin shugaba, ka duba lamarinmu."

Wani irin zafi da ƙuna ne ya cika zuciyar, Maimartaba Lamido, zalumci yayi yawa.
Gyara zaman babbar Al'kebbar sarautar dake jikinsa ya ɗan yi, yana maijin ƙuna da tafasa a zuciyarshi, fargaba da tsoron, haƙin bayin Allah'n da aketa kashewa ya cika mishi zuciya, sabida sanin shine sarki kuma shugaba, ga duk wani mutun dake yankin.
Wani nannauyan numfashi yaja mai ƙarfi.
Juyawa yayi ya fuskanci maga takardar fadar tashi, cikin bada umarni yace.
"A rubuta takarda a aikawa Haman-Ɓachama cewar ina bukatar ganinshi, da gaggawa.
Kana ya tabbatar kafin ya isoni yankin da yake mulka babu sauran zalumci, ko ƙabilanci!".
Cikin cika umarnin da maga takardar ya ɗan rusuna, tare da cewa.
"An gama ya Mai alfarma Sarki Adalin Sarki."
Waziri, Galadima, Wambai, Sarkin fada, kana da sarkin dogarai, duk, shiru sukayi sabida a zahiri ake iya hanƙo tsantsar tashin hankali da ɓacin rai a fuskar adalin shugaban nasu.

Su kuwa su Bappa sosai sukaji sanyi, a zuƙatansu, sabida nuna kulawarshi garesu,
cikin iya sarrafa harshe da tausasan laffuza mai martaba sarkin Nuruddeen Bubayero Joɗa yace.
"Kuyi haƙuri, ku gafarceni, bani da labarin dukkan abinda ke faruwa daku, sai yanzu, naji daɗi da kuka nemeni, da matsalarku, In sha Allah ni kuwa zan ɗauki mataki, da izinin ubangiji koda belbelun dake cikin shanunku baza'a sake kashesuba, bare dabobbin ku, bare a kai ga rayukanku. Zan kirayi GARKUWAN FULANI, yanzu, zan sashi maza ya taho ya dawo ƙasar sa,
Domin shiga lamuranku nauyin a kanshi yake."
Sai kuma ya ɗan numfasa kana ya kalli wani bafadensa dake tsaye bayanshi yanayi mishi fifita da maficin da akayishi da gashin kekkyawan ɗawisu.
Cikin bada umarni ya umarceshi daya koma gefe,
Da sauri ya rusana ya koma gefen.
Shi kuwa Sarki Nuruddeen, wani ɗan kekyawan matashi dake gefen damanshi ya kalla tare da cewa.
"Imrana, kiramin Sheykh Jabeer."
Kai ya ɗan rusunar kana yasa hannu ya amshi wayar da Kakan nashi ke miƙa mishi.
Amsa yayi, kana ya kira Sheykh Jabeer, wanda shi kuma a dai-dai lokacin yana gaban Sheykh Aliyu, Abdulkareem, Jabeer, Sitti, Jazrah, Haroon. Da dai sauran ahlin nasu.

Wanda kiran ne yasa ya samu ya fece daga tarkon da ake naɗa mishi.

Jin wayar tayi ringing har ta katse ba'a ɗaga bane, yasa Imran ɗan rusunar da kanshi tare da cewa.
"Wata ƙil baya kusa da wayar."
Kai ya jinjina mishi tare da cewa.
"A a zai kira, bayan amsa kirana yanzu zai kira".
Kai ya gyaɗa alamar gamsuwa.
Suko su Bappa duk suna zaune cikin kamala.

Shi kuwa Sheykh kamar yadda ya saba, hakane baya amsa kiran kakan nashi, sai dai ya bari in tayi ta katse sai ya kira, shiyasa, yanzuma ya bari saida ta katsen sannan ya kira.


Gyara zamansa yayi tare da kara wayar a kunnensa na dama.

Imran kuwa yana ganin kiranshi yayi maza ya amsa,
cikin tarin girmamawa yace.
"Barka da hantsi, Hamma Jabeer".
A can gefen Sheykh Jabeer ɗin kuwa, ido ya lumshe cikin yanayinshi da sun rigaya sun saba yayi shiru.
Da sauri Imran ya kuma ɗan rusunar da kanshi yace.
"Afwan Sheykh Assalamu alaikum ".
Murya can ƙasa yace.
"Wa alaikassalam".
Cikin ɗan tura baki Imran ya kuma maimaita mgnarsa ta forko.
"Barka da safiya, Hamma Jabeer ya, Sitti?".
A taƙaice yace.
"Alhamdulillah".
Da sauri Imrana yace.
"Masha Allah, ga Lamiɗo".
"Na'am". Yace a takaice.
Shi kuwa Imran miƙawa kakansu wayar yayi.
A hankali Sheykh ya ɗan buɗa laɓɓansa cikin zazzaƙan sautin muryarsa yace.
"Assalamu alaikum".
Murmushi mai cike da so da ƙaunar jikan, nasa yayi tare da amsa sallamar tasa. Gaisawa sukayi, bayan sun gaisa ya tambayi labarin su Sitti da ƙanennenta da kuma mahaifinta, sai kuma ya kora mishi jawabin abinda ke faruwa a jihar tasu.
Kana, ya ɗoro da cewa.
"Ka dawo, kayiwa lamarin tubkar hanci". Cikin sanyi yace.
"In sha Allah. Ina nan tafe, nanda kwanaki uku. Ina jajanta musu, abinda ya faru, kuma in sha Allah.
hakan bazai kuma faruwa ba.

Da haka sukayi sallama.

A can garin Numan kuwa cikin Rugar Kikan.

Gaba ɗaya garin shiru yayi, dan wannan abunda ya faru yayi masifar shiga jikinsu.
Da dama maza matasanmu sun tafi kiwo, kamar yadda suka saba, rayuwar yau da kullum.
Saura sai irin dattawan da aka bari, da mata da yara maza da mata.


Cikin garin Bonon kuwa, gaba ɗaya, matasan garin dama ƙauyuka gefensu na ƙabulun Ɓachamawa, duk sun hallara wuri ɗaya, suna cike gaban dodon tsafinsu, wato Bonon ɗin, giyar burkutu mai ɗan karen tsami da wari, suketa sha, tamkar zasu fasa cikkunansu.
Yayinda gefe guda kuma, maƙerar dake gefe wasu matasa su ne maƙera keta wasa ababen faɗansu, kamarsu wuƙaƙe, Adda, sitaka, barandami, mashi, kibau, da dai sauran mugayen makamai, sai sheƙi sukeyi.

Suna cike a wurin, Ba'ana ya iso, cikin wata shigar rigar saƙi.
Hanya suka rinƙa buɗa mishi, hardai ya isa ga sarkinsu, dake zaune gefen dodo sun. Zama yayi kusa da sarkin nasu ya sasu a gaba,
Cikin harshen ɓacamancin yace.
"Ku hanzarta, ku shiga, duk matasansu majiya ƙarfi, sun tafi kiwo. Dottijan su kuma sun tafi, kai gulmarku, ga Sarkin su wannan karon basu tsaya ga sarkinku na nanba, ina da yaƙinin kuma za'a sauraresu a can.
Yanzu matansu da ƴaƴansu, ƙanana mata da mazane suka rage a garin.
Sai wasu dattawansu dake, dakon dawowar magulmatan can.
Kuyi maza, kushiha kafin su dawo, ku share garin kab.
Ku kashesu gaba ɗaya babba da yaro mace dana miji."
Da sauri wani daga cikin su yace.
"Harda gidansu Shatu?".
Cikin izaya yace.
"Harda su, domin Mata, bata nan, ku kashe kowa nata, ta hakane zata dogara dani kaɗai tunda bata da kowa nata a duniya, dole Ni zan zama mijinta ubanta yayunta ƙannenta uwarta, in zama Garkuwarta in zame mata duniyarta ta hakane zata yarda nine ɗaya gatanta kuma duniyarta, ba tare da ta zargeniba, a hankali wata rana in sata tayi ridda, musha giya, muyi tsafi tare da ita, bazatayi min musuba, mu haifi ɗanmu na forko mu bawa dodonmu yasha jininshi yasa mana al'barka a aurenmu".
Wani irin ihu da sowa na tsantsar jin daɗin bayaninshi sukayi baki ɗayansu.
Hakama dodonsun, saida ihunshi ya firgitasu baki ɗayansu.
Dariya mai amo mara daɗin ji. Sarkin nasu yayi, kana ya busa ƙahon dodonsun, alamun ya basu izinin tafiya.

Nan fa duk suka rinƙa shiga, cikin maƙerarnan suna ɗaukan makamai, suna nufar garin Rugar Kikan (Rugar Bani) kenan a guje...


Cikin garin Shikan kuwa, Bani rana ta fara tasawa, mata masu zuwa tallan nono cikin garin Numan, suka fara ɗaukar ƙorarensu, suna fita garin.
Yara maza da mata kuwa, wasu na wasa wasu na ɗebo ruwa, wasu na ɗebo kayan lamɓu.
Yayinda wasu kuma suka dawo break dan tara tayi.

Cikinsu kuwa harda Junainah.

Tafe take da saurinta da ɗan tsalle-tsallenta tana rataye da yar jakarta,
da sauri ta tsaya ganin Junaidu a gabanta rike da kwanɗon zabari wanda yake cike da ƴaƴan itatuwa.
Murmushi ta ɗanyi tare da sunkuyar da kanta cikin surutunta tace.
"Har naji tsoro!".
ta ƙarishe mgnar tana kallonshi,
Murmushi yayi mata shima cikin son ƴarinyar yace.
"Haba dai, tsoron me kuma zakiji, tunda gani, babu abinda zai sameki muddin ina raye, zan zame miki Garkuwa".
Da sauri tasa hannu ta rufe bakinta tare da cewa.
"Kai! Kai! Ya Junaidu, sunan Babanmufa ka kira".
Murmushi mai kama da dariya yayi kana yace.
"Au na manta ashe sunan surki nane".
Kai ta gyaɗa mishi kana tasa hannu ta amshi, nonon inabin da yake miƙa mata,
baki ta buɗe da nufin sawa a baki,
sai kuma ta tsaya tare da tura baki jin yana ce mata.
"No kada kici ba'a wonke bafa."
Sai kuma ya ajiye kondon, ya amshi inabin ya ɗan

2 Comments On GARKUWA
avatar
nafisa-9-6

1 year ago

Reply

Masha Allah

avatar
nafisa-9-6

1 year ago

Reply

Masha Allah

Please Login or Register in order to submit comment