Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 2
sharad’i da Aliyu Misiriyi sai ya soma tafiya Misira ya samu iyalin Alin a cikin fatara da yunwa da tsiraici, sai ya d’auke su ya tafi da su Yaman ya ba su tufafin alfarma daga dukiyar nan suka sanya sannan ya taho da su nan. Yayin da Ali ya ji maganar zuwan iyalinsa sai ya tashi ya tafi wurin attajirai ya fad’a musu labarin zuwan kayansa yana cewa, “ku zo ku raka ni wajen taren kayana, kuma ku taimaka da iyalanku domin su tarbi nawa iyalin domin na san yanzu a gajiye suke.” Suka ce, “mun ji, mun bi.” Suka fita gaba d’aya zuwa bayan gari suka zauna suna hira suna tattaunawa sai ga k’ura ta turnuk’e sararin samaniya. Kowa ya maida hankalinsa zuwa ga wannan k’ura, yayin da ta yaye jama’a suka ga abin da ke musabbabin k’urar. Alfadarai ne da rak’uma birjik da dawaki da mahaya da ‘yan mata suna ta wak’a har suka iso kusa da jama’ar nan. Shugabansu ya matso kusa da Ali ya sumbaci hannunsa ya ce, “ya shugabana mun samu jinkirin isowa domin jiya muka so mu shigo amma saboda tsoron ‘yan fashi muka jira sai yau, shi ya sa muka yi kwana hud’u bayan shigowar ka, Allah ya kiyaye mu da su.” Daga nan attajirai suka hau alfadaransu suka yi gaba, karauka na biye da su sai kuma tawagar mata da yara da masu tsaronsu na biye da su. Matar Ali da ‘ya’yansa na cikin su suna sanye da kayan masu daraja na alfarma. Mata na kallon su suna sha’awar kayan, suna cewa, ‘hak’ik’a wad’annan kayan ko ga sarakunan Bagadaza ba za su samu ba balle wani wuri daban. Attajirai kuma suna ta mamakin irin wad’annan alfadarai da dawaki fird’a – fird’a. Haka suka yi ta tafiya, Ali na cikin jerin manyan attajirai, matarsa da ‘ya’yansa na cikin manyan matan attajirai har suka isa masaukinsa. Zanci gaba05 HIKAYAR ALIYYUL MASIRIYI DAN HASANUL suka yi ta tafiya, Ali na cikin jerin manyan attajirai, matarsa da ‘ya’yansa na cikin manyan matan attajirai har suka isa masaukinsa, suka sauka Shiga cikin gidan har zuwa tsakiyarsa aka sauke labtu tare da dukkan abubuwan da ke d’auke da dabbobin nan. Matan fatake suka tafi tare da matarsa da ‘ya’yansa zuwa wajen wanka, wajen ya kasance mai yawan itatuwa da shimfid’u masu kyawun launi da tsuntsaye na ta kuka mai dad’in saurare. Yayin da ta fito sai wajen duk ya haskake ta zama ita kad’ai ake kallo. Suka zauna suna cin abinci suna hira tsakaninsu ana ta dariya da shewa. Bayan nan suka dawo zuwa gidan mijinsu sannan da attajirai suka bar wajensa sai suka aiko masa da kyautuka da yawa, matayensu ma suka aikawa da matarsa irin tasu kyautar abin da ya danganci gari, da sukari da ruwan wardi da turare da sauransu masu yawa da suka fi gaban k’idayawa. Ali ya zauna tare da attajiri mai masaukinsa suka yi ta hira suna tattaunawa game da harkar ciniki da sauransu. Attajiri ya ce masa, “ka bar bayi da hadimai da babanni da sauran dabbobi su je gidana da ke bayan gari su huta anan. Ali ya ce, “yau za su tafi domin na aike su zuwa wani wuri.” Suka tafi zuwa bayan gari, bayan sun b’ace daga idanun mutane sai duk suka b’ace zuwa wurin sabgoginsu. Su ba su kasance sun yarda an sallame su ba, sai da suka tabbatar sun yi nisa tukunna suka cika da murna da farin ciki. Ali da mai masaukinsa suka yi ta hira har zuwa sulusin dare sannan suka yi sallama da juna, Ali ya shiga wajen matarsa suka dasa wata sabuwar hira. Ya tambaye ta game da halin kasancewarsu tun lokacin da ya tafi ya bar ta shekaru masu yawa. Ta fad’a masa irin wahalun da suka shiga na k’uncin rayuwa da talauci da fatara da yunwa da tsiraici har sai da ta kai kowa ya guje su. Ya ce, “godiya ta tabbata ga Allah da ya kub’utar da ku. Fad’a min yadda kuka zo nan wurina.” Ta ce, “muna kwance ni da yarana sai kwatsam muka ji an yi sama da mu muna tafiya tsakanin sararin samaniya, ya kai mu wani waje inda muka ga tawagar larabawa ya sauke mu ba tare da wani lahani ba. Bayan ya sauke mu muka ga gungun alfadarai da bayi maza da mata yara da manya da yara. Na ce da su, “su wanene ku, kayan wanene wannan kuma ina za ku da mu?” suka amsa suka ce, “mu bayin Aliyul Misiriyi ne d’an Hasan mai jauhari na Bagadaza, ya aiko mu domin mu d’auke ku zuwa gare shi a Bagadaza.” Na ce da su, “ku fad’a min daga nan zuwa Bagadaza kwanaki nawa ne?” Suka ce, “ranki ya dad’e tsakaninki da birnin Bagadaza tafiya ce kurum cikin duhun wannnan daren.” Daga nan suka shigar da mu cikin darbuka muka ci gaba da tafiya. Da gari ya waye muka tsinci kanmu anan wajen babu ciwo babu lahani.” Ya ce, “to wa ya baku wad’annan kayan alfarmar?” Ta ce, “madugun fataken ne ya ba ni, ya bud’e d’aya daga akwatin da ke bisa alfadari ya fito daga wad’annan tufafi ya ba mu ni da yarana muka sanya, sannan ya kulle ya bani mukullai ya ce ki kula da su idan kin sadu da mijinki ki ba shi.’ To ga mukullan a hannuna.” Ya ce, “za ki iya gane akwatin daga ciki?” Ta ce, “eh zan gane shi.” Ya kai ta zuwa taskar nan ta k’ark’ashin k’asa, ta duba akwatunan nan ta gane wanda aka fito da shi daga ciki. Ya sa mukullin ya bud’e ya ga yana d’auke da mukullan ragowar akwatunan. Ya rik’a bud’e akwatunan ya tarar da tufafin alfarma masu daraja da wasu nau’in zinariya da jauharai da lu’ulu’ wad’ana ba a samun tamkar su sai wajen sarakuna, ya kwashe dukkan wad’annan ya kai waccan taskar ya had’a da wad’ancan na farko. Ya ce da ita, “kin ga wannan falala ce daga ubangiji mai girma!” Ya fad d’imbin dukiya haka. “wannan falala ce daga ubangiji mai girma mad’aukakin sarki.” Ta ce, “ya shugabana wannan duka ya kasance daga addu’ar da mahaifinka ya yi maka gabanin mutuwarsa inda yake cewa, “Ya Allah kada ka sa d’ana ya abku cikin wahala, ka riskar da shi cikin sauk’i a kusa.” Na godewa Allah da ya k’addara kub’utar ka daga mawuyacin hali kuma ya yi maka sakayya mafificiya tun daga nan duniya. Na rok’e ka don girman Allah kada ka sake komawa cikin halinka na baya inda ka ke mu’amala da miyagu. Ka ji tsoron Allah bisa dukkan abin da za ka aiwatar a fili ko a b’oye.” Ta ci gaba yi masa nasiha tana tausasar zuciyarsa. Tana jan hankalinsa kan ya bi sunnar ma’aiki mai tsira da aminci su tabbata a gare shi. Ali da matarsa da ‘ya’yansa suka cigaba da rayuwa cikin yalwar arziki da wadata. An ba shi rumfa cikin kasuwa inda ya jera kayan jauhari da lu’ulu’u masu tsada, ‘ya’yansa da bayinsa da barorinsa na taimakonsa wajen saye da sayarwa. Ana nan sarkin Bagadaza ya samu labarinsa ya aika masa da ya je fada domin ya ganshi. Ya d’auki manyan farantai na jan zinare ya cika su da kyautauka na daga dukiya mai daraja da tsada ya tafi wajen sarki. Ya fad’i gabansa yana mai gaisuwa. Sarki ya ce, “ya kai tajiri hak’ik’a mun yi murna da zuwanka wannan gari namu.” Ali ya rusuna cikin girmamawa ya ce, “Allah ya taimaki sarki, ga wata ‘yar kyauta daga bawanka na kawo maka gaisuwa.” Sarki ya karb’i farantan ya duba ya ga dukiya mai tsadar gaske wadda biyanta zai kwashe adadin kud’in da ke babbar taska guda. Sarki ya cika da mamaki, domin irin wannan dukiya ko wajen sarakuna ba wurin kowa za a samu ba. Sarki ya ce, “mun karb’i gaisuwarka, kuma za mu sakanta maka da misalinta da yardar Allah.” Ali ya sake rusunawa ya yi gaisuwa ya tafi. Sarki ya tara manyan majalisarsa ya ce da su, “sarakuna nawa ne daga sarakunan duniya suka nemi auren d’iyata?” Suka ce, “suna da yawa k’warai.” “To a cikinsu wanene ya kawo min kyauta kamar wannan?” Suka ce, “babu ko d’aya, domin babu ya mallaki kwatankwacinta!” “To zan rok’i Allah mad’aukakin sarki domin neman dacewarsa na aurar da d’iyata ga wannan attajirin. Me kuka gani game da haka?” Suka ce, “wannan al’amari daidai ne kamar yadda ka yi nufi.” Ya sa bayi suka shiga da farantan dukiyar cikin gida aka nunawa matarsa. Ta duba su d’aya bayan d’aya ta ga ba ta tab’a ganin abu mai kyau da daraja irin su ba. Ta ce “daga wanne sarki wannan abu yake? Da fatan yana d’aya daga cikin manema ‘yata.” Sarki ya ce ba ya ciki amma saboda ganin irin wannan kyautar mai girma gare mu na ga dacewar na aura masa ita. Kuma na shawarci mutanen fada sun lamunce min. Yanzu kuma ina son ji daga gare ki. Yaya kika gani?” Matar ta ce, “wannan kam babu laifi, domin ya cancanci fiye da haka ma.” Ta k’ara da cewa, “wannan al’amari ne daga wajen Allah, idan ya k’addara haka babu mai ikon hanawa.” Sarki ya ce, “idan haka ne kuwa babu wanda zan aurawa d’iyata sai wannan saurayin.” Da gari ya waye ya aika aka kirawo Ali tare da dukkan fatake suka hallara gaba gare shi yana kishingid’e bisa kujerar sarauta. Suka kwashi gaisuwa sannan ya umarce su da su zauna, ya sa aka hallara da alk’ali da shaidu. Ya ce da alk’ali, “ka rubuta cewa na aurarwa da d’iyata Ali Misiriyi.” Ali ya yi farat ya ce, “ya sarki ina neman afuwarka, kama ta da bai wuce bafatake ba, na yi kad’an ya had’a surutaka da kai.” Sarki ya ce, “nufina ne na yi maka ni’ima kuma na jawo ka jikina, don haka na nad’a ka sarautar wazirina.” Ya sa aka kawo kayan sarauta ya sanya masa sannan aka rubuta masa takardar nad’i aka ba shi. Sarki ya yi umarnin ya zauna akan kujerar wazirci, bayan ya zauna ya godewa sarki bisa wannan nad’i sannan ya ce, “ya sarkin zamani, ina mai matuk’ar jinjina da godiya gare ka bisa wannan karamci da ka yi min, amma ina da magana d’aya da nake so ka ji.” Sarki ya ce, ‘fad’i maganar ka kada ka ji shakkar komai.” “Ran sarki ya dad’e, tunda mai martaba ya yi nufin aurar min da d’iyarsa tun farko, ina rok’on wannan karimci ya karkata zuwa ga d’ana a d’aura masa ita aure.” Sarki ya ce, “kana da babban d’a ne?” Ya amsa, “eh ina da shi.” “A kawo shi mu ganshi.” Ya sa aka kirawo d’ansa wanda a lokacin ya kai shekaru goma sha hud’u. Sarki ya dube shi ya gan shi cikakke ne wajen kyau da nishad’i da ban sha’awa. Babu makusa a tare da shi, har ya fi ‘yarsa kyawu ma. Yaro ya durkusa cikin ladabi da biyayya da harshe mai fasaha. Sarki ya gamsu da nutsuwarsa da hankalinsa. Ya ce masa, “d’ana yaya sunanka?” “Sunana Hasan.” Alk’ali ya juya wajen alk’ali ya ce, “ka rubuta takardar aure tsakanin Hasan d’an Aliyu Misriyi da ‘yata Husunul Wujud.” Aka rubuta takardar aure tsakaninsu, daga nan fada ta watse kowa na cike da farin ciki saboda alherin da sarki da waziri suka yi musu. Waziri ya samu rakiyar manyan fadawa da sauran jama’a har zuwa gidansa. Sannan duk suka watse kowa ya shiga sha’anin gabansa. Ya shiga wajen matarsa ta ganshi cikin tufafi irin na wazirai ta tambaye shi yadda abin yake ya bayyana mata komai, ta yi farin ciki mai yawa. Aliyu ya kwanta barci har zuwa wayewar gari sannan ya kintsa ya tafi fada. Ya durk’usa gaban sarki ya kwashi gaisuwa. Sarki ya karb’e shi da murna ya jawo shi kusa da shi domin su k’ulla shawara. Ya ce da shi, “ya waziri, ina so a shirya bikin yaran nan da wuri domin su tare mu huta.” Waziri ya ce, “haka nan ne Allah ya baka nasara.” Sarki ya sa aka rubuta wasiku zuwa k’asashe sarakuna, ya sa aka k’awata gari aka shiga shagali har kwana talatin cif sannan aka daina. Hasan ya shiga wajen amaryarsa. Yayin da ‘yar sarki ta ganshi da irin kyawunsa sai ta cika da tsananin begensa, ta so shi fiye da yadda yake sonta. Kamar haka kuma mahaifiyarsa ta nunawa amarya k’auna. Sarki ya sa aka gina turaka nan kusa da turakarsa, aka kammala aikin cikin hanzari da gaggawa. Ya sa ango da amarya ciki bayan an k’awata gidan da kayan alatu. Mahaifiyarsa ta kasance kullum tana gidan tare da d’anta da surukarta. Idan ta yi ‘yan kwanaki sai ta koma wajen mijinta. Saboda haka matar sarki ta ce masa, “Ya sarkin zamani, matar Waziri Aliyu kuma uwar mijin ‘yar mu ba za ta iya barin d’anta ba kuma ba zata iya barin mijinta ba. Ta kasance kullum tana zirga – zirga, a san abin da ya kamata a yi.” Sarki ya ce, ‘wannan zancen gaskiya ne.” Ya sa aka d’ebi wani babban fili a kusa da shi aka gina turaka ta uku cikin hanzari. Ya umarci waziri Aliyu ya dawo nan gidan ya zauna. Wajen ya kasance da turaka uku kenan. Duk lokacin da sarki ke son hira da waziri sai ya taso ya zo wajensa su yi ta hira abinsu, ko kuwa ya aika a kirawo shi wajensa. Wani lokaci kuma ya kana tara dukkan iyali a zauna ana ta hira. Da haka suka zauna cikin farin ciki da jin dad’in rayuwa. GOBE ZAMU KARASA SANNAN MUSHIGA WATA SABUWAR HIKAYAR06 HIKAYAR ALIYYUL MASIRIYYI DAN HASANUL GADADIYU Sarki da Waziri suka zauna cikin farin ciki da jin dad’in rayuwa har zuwa lokacin da Sarki ya kwanta rashin lafiya, kullum ciwo ya zamana ya hauhawa. Da ya ga haka sai ya aika aka kirawo masa manya fada tare da sauran masu fad’a a ji duka suka hallara gabansa. Ya ce musu, “kun ga yadda cuta ta k’i warkewa, na hak’ik’ance wannan ciwon ba mai warkewa ba ne, domin duk d’an Adam sai ya d’and’ani mutuwa. Don haka na kira ku a kan sha’anin sarauta bayan na mutu, ina so ku duba lamarin da kyau.” Suka ce, “wacce nasiha za ka yi mana game da haka ya Sarki?” Ya ce, “ni yanzu na tsufa, ga ba ni da lafiya. Ina tsoron bayan mutuwata wannan masarauta ta fad’a hannun mak’iyanta ko kuwa ku yi ta fad’a a kan sarautar har abokan gaba su rinjaye ku. Don haka nake so ku zab’i wanda zai gaje ni a cikin raina domin zan fi samun nutsuwa.” Suka ce gaba d’ayansu, “mun zab’i mijin matarka, Hassan d’an Waziri Aliyu Misiriyi. Domin kuwa mun yaba da hankalinsa gami da hangensa nesansa da ladabinsa ga manya. Sannan yana girmama dukkan babba da k’arami a cikin mutane.” Sarki ya ce, “kun amince da hakan ku da kanku?” Suka ce, “k’warai da gaske mun amince.” Ya ce, “ta yiwu kun fad’i haka ne a gabana domin ku faranta mini rai. Ku je ku yi tunani kada kuma daga baya ku sauya ra’ayi.” Jama’a suka ce, “wallahi ba da gangan muke ba, shi ne zab’inmu a fili da b’oye, mun amince da shi da zuciya d’aya da iya kk ya wa ur niyya.” Sarki ya ce, “tunda kun amince da haka, ina so ku kirawo alk’ali tare da ragowar dukkan manyan fadawa da masu sarauta wad’anda ba su hallara nan ba, domin a tabbatar da wannan shawara.” Mutane suka tafi suka hallara da dukkan malamai da masana da sauran sarakuna duka suka hallara washegari a k’ofar fada. Bayan sun samu iznin shiga wajen Sarki suka gaishe shi sannan suka ce, “ga mu gaba d’aya a gabanka domin cika umarninka.” Ya d’aga kai ya dube su sannan ya ce, “ya ku sarakunan Bagadaza, wa kuka zab’a a cikinku domin ya sarauce ku bayan raina.” Suka ce gaba d’ayansu, “mun zab’i Hassan d’an Waziri Aliyu surukinka.” Ya ce, “tunda gaba d’ayanku kun amince bisa wanan matsaya, to a je a kirawo shi nan gabanmu.” Aka tafi zuwa gidansa aka kirawo shi. Ya zo gaban Sarki ya fad’i yana mai gaisuwa. Sarki ya ce masa, “zauna nan kusa da ni ya d’ana.” Ya matsa kusa ya zauna, Sarki ya cigaba da magana yana cewa, “ya kai Hassan, sarakunan wannan daula tamu sun amince gaba d’aya da kasancewar ka Sarki bayana. Saboda haka na yi nufin na tabbatar da wannan al’amari a lokacin rayuwata, domin zance ya zo k’arshe tun yanzu.” Hassan ya mik’e ya sumbaci k’asa gaban Sarki sannan ya ce, “ya Sarki babana, ka sani a cikin sarakunan nan akwai wad’anda ya fi ni cancanta da dacewar ya zama Sarki fiye da ni.” Dukkan sarakunan suka ce, “mu ba mu da wani zab’i sai kai. Mun amince ka sarauce mu.” Hassan ya ce, “to ga mahaifina nan a ba shi a maimakon ni.” Waziri Ali ya ce, “a’a, wallahi ba za a yi haka ba, dukkan abin da ‘yan uwana suka amince da shi ni ma na amince da haka. Kada ka sab’a umarnin Sarki da na iyayenka.” Hassan ya sunkuyar da kansa saboda jin kunyar Sarki da mahaifinsa. Sarki ya dubi jama’a duka ya ce, “kun amince da ya zama sarkinku?” Suka amsa gaba d’aya, “mun amince bisa ga ya zama sarkinmu!” ya dubi alk’ali ya ce, “ya alk’ali a rubuta takarda cewa dukkan sarakuna sun amince da Hassan d’an Waziri Aliyu Misriyi ya zama sarkinsu bayan raina.” Alk’ali ya rubuta haka, kowa ya rattaba hannu, ya zama doka. Daga nan Hassan ya shimfid’a hannunsa, dukkan sarakuna suka yi masa mubayi’a, Sarki ma ya yi masa haka. Ya umarce shi da ya zauna a kan karagar mulki. Gaba d’aya sarakuna suka mik’e suka yi gaisuwar ban girma gare shi, suka sumbaci hannunsa. Sannan suka yi rantsuwar biyayya a gare shi. Sabon Sarki ya yi mulki a tsakanin mutane a wannan yinin, ya ba da umarni, ya yi hani ya yi ta kyauta da sadaka ga mutane daidai gwargwadon ikonsa. Da yamma da fada ta watse ya je gaban surukinsa ya gaishe shi sannan ya sumbaci hannunsa. Tsohon Sarki ya ce masa, “ya d’ana, ina maka nasihar ka ji tsoron Allah a zuci da bayyane. Ya amsa ya ce, “ya babana, da addu’arka gami da fatan alherinka gare ni zan samu cimma dukkan abin da nake buk’ata.” Ya yi masa sallama ya shiga turakarsa, ya tarar da matarsa da mahaifiyarta, suka tashi suka tarbe shi da murna da farin ciki. Suka sumbaci hannayensa. Sannan ya shige wajen iyayensa su ma suka yi masa addu’a da fatar alheri. Mahaifinsa ya yi masa nasihar ya ji tsoron Allah wajen tafiyar da mulkinsa kuma ya yi adalci tsakanin talakawa. Ya kwana a wannan daren cikin farin ciki da godiya ga Allah. Yayin da gari ya waye ya yi sallar asuba sai ya tafi wajen surukinsa ya gaishe shi, sannan ya dawo wurin iyayensa ya gaishe su. Daga nan ya kintsa ya tafi fada. Ya wuni a wannan ranar yana hukunci tsakanin jama’a cikin adalci, kowa yana farin ciki da wannan sarautar tasa. Da yamma bayan tashin fada ya shiga wajen surukinsa ya same shi ciwonsa ya sake tsananta, ya durk’usa yana masa addu’ar samun sauk’i. Sarki ya bud’e ido ya kira sunansa, “Hassan!” “Labbaika ya sayyadi.” Hassan ya amsa cikin girmamawa. “Ka sani ni lokacina ya k’arato, na hore ka da ka zama mai adalci ga matarka da mahaifiyarta da kuma iyayenka. Ka ji tsoron Allah bisa dukkan abin da za ka aiwatar a rayuwarka. Ka zama mai adalci a cikin mulkinka kada ka zalunci mara k’arfi ko ka hana talakawa zuwa kusa da kai.” Hassan ya ce, “na ji wannan nasiha kuma zan yi aiki da ita da yardar Allah.” Daga nan Sarki ya cigaba da jinya tsawon kwana uku ya ce, ‘ga garinku nan.’ Aka yi masa lifafa aka yi masa sallah sannan aka binne shi. Aka samu wasu suka tsaya akan kabarinsa suna karanta Alk’ur’ani mai girma. A gida ma aka cigaba da addu’oi gare shi har kwana arba’in. Sarki Hassan d’an Waziri Aliyu ya cigaba da mulki a madadinsa. Ya shimfid’a adalci tsakanin talakawa na birni da na k’auye, ko’ina aka rik’a sonsa. Mahaifinsa ya zama babban wazirinsa na hannun dama sannan aka nad’a wani wazirin na hannun hagu. Mulkinsa ya zamana mai cike da adalci a duk tsawon zamaninsa cikin Bagadaza. Allah ya azurta shi da haihuwar ‘ya’ya uku duka maza tare da ‘yar Sarki wad’anda suka gaje shi. Haka suka cigaba da zama cikin farin ciki da annashuwa har mai rusa jin dad’i, mai rarraba jama’a ta zaike musu. Tsarki ya tabbata ga wanzajje wanda ba ya mutuwa har abada. INSHA ALLAH GOBE ZAMU SHIGA WATA SABUWAR HIKAYAR This Document is compiled by Shuraihu Usman - 08140419490 YEAR of compilation - 2023; Published to Taskarnovels.com.ng An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 2 of 2