Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 2
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels This Document is compiled by Shuraihu Usman - 08140419490 YEAR of compilation - 2023; Published to Taskarnovels.com.ng HIK’AYAR ALIYUL MASIRIYI D’AN HASANUL BAGADADIYU An bada labarin cewa akwai wani attajiri a birnin Masar, ya kasance ya mallaki dukiya mai yawa da kadarori na daga jirage da bayi da gidaje wad’anda sun fi gaba k’idaya.Sunansa Hassan mai Jauhari, asalin mutumin Bagadaza ne. Haka kuma Allah ya albarkace shi da wani d’a mafi kyau daga mutanen wannan zamaninsa. Ya kasance mai kyawon fuska, madaidacin tsayuwa, mai santsin kundukuki, ma’abocin kwarjini da cikar kama da k’oshi. Ana kiran wannan yaro Aliyul Masiriyi. Yana da ilmin Alk’ur’ani mai girma da sauran ilmai na fasaha da dabarun zaman duniya. Bayan ya samu ilmin da ake buk’ata sai ya zauna wajen mahaifinsa yana koyon kasuwanci har zuwa wani lokaci mai tsawo sa’adda cuta ta kama mahaifin nasa, ya zamana kullum ciwo na dad’a yin gaba gaba, har dai ya sakankance da mutuwa. Ya kira d’an nasa ya ce da shi. “ya d’ana hak’ik’a duniya k’ararriya ce, lahira ce madauwamiya. Duk abin da ke wannan duniya tilas wata rana ya k’are. Ka sani kwanakina na wannan gida sun zo k’arshe, zan tafi zuwa ga Ubangijina. Zan yi maka nasiha, idan ka rik’e ta ka yi aiki da ita ba za ka talauce ba har ka koma ga ubangijinka. Amma idan ka yi watsi da ita ka k’i aiki da ita za ka had’u da wahala da talauci da wulak’ani a rayuwar ka ta duniya.” Ali Masriyi ya ce, “ Ya mahaifina, ta yaya zan ji umarninka daga kalaman bakinka na aikata sab’anin haka alhali kuwa doka ta wajabta min yi maka biyayya sau da k’afa?” Ya ce, “ka sani ya d’ana na bar maka gidaje da kadarori da dukiya mai yawa ta fi gaban k’idaya. A ciki kullum ka fitar da dinari d’ari biyar ka yi sadaka, ba za ka tab’a samun raguwa ba. Ina yi maka nasihar ka ji tsoron Allah, ka yi biyayya ga umarnin fiyayyen halittu Annabi Muhammadu mai tsira da amincin Allah su tabbata gare shi. Ka yi aiki da umarninsa, ka hanu da haninsa na daga hadisansa, ka zama mai koyi da sunna tasa bisa ga aikata alheri da ba da nagarta da abotaka da mutanen kirki. Ka zama mai sulhu tsakanin wad’anda suka b’ata. Ka rungumi ma’abota ilmi sannan ka yi huld’a da talakawa, ka rik’a yalwatawa miskinai da mabuk’ata. Ka guji huld’a da miyagun mutane. Kada ka yi ciniki cikin shubhu, ka rik’a duba ayyuka na k’asa da kai kana kyautata musu. Sannan ka lura da matarka da kyau, domin ita d’iyar manyan mutane ce, na zab’o maka ita domin kwad’ayin Allah ya azurta ku da haihuwa ku haifi ‘ya’ya nagari.” Ya cigaba da yi masa nasiha da wa’azi shi kuwa Aliyu na kuka yana amsawa. Ya ce, “ya d’ana, ni ina rok’on maka Allah mad’aukakin Sarki, Buwayi Gagara misali, Ubangijin sama da k’asa da al’arshi mai girma da ya kub’utar da kai daga dukkan wani bala’i da zai same ka.” Aliyu ya sake fashewa da kuka mai tsanani yana cewa, “ya Abbana, ni kam na narke daga zantukanka, domin wad’annan kalamai ne irin na wanda ke bankwana da duniya.” Uban ya amsa ya ce, “haka ne, ni kam tawa ta k’are.” Ya yi ajiyar zuciya yana mai fad’in kalmar shahada yana ambaton wasu surori na Alkur'ani mai girma har zuwa lokacin da ransa ya kusa fita. Ya ce da d’ansa, “matso kusa da ni.” Ya matsa kusa, ya sumbace shi. Ransa ya fita daga gangar jikinsa ya tafi ga rahamar Allah. Ali Masiriyi ya zauna yana cikin bak’in ciki. Ya durkusa bisa gwiyoyinsa yana kuka, abokanen mahaifinsa suka shigo suka kewaye gawar suna addu’a. Daga nan aka shirya shi aka yi masa sallah aka kai mak’abarta aka binne. Bayan an binned gawar mutane suka kewaye kabarin suna addu’a tare da karanto wasu surorin na Alkur'ani mai girma. Daga nan suka juyo zuwa gida suka yi wa d’an marigayin ta’aziyya sannan kowa ya kama gabansa. Ali kuwa ya tafi masallacin Juma’a ya yi wa mahaifinsa addu’a ta musamman, sannan ya rik’a yi masa addu’a duk dare har zuwa kwana arba’in, a wannan tsakanin kuwa ba ya fita ko’ina sai masallaci. Duk juma’a kuma yana zuwa kabarin mahaifinsa yana yi masa addu’a. Ya cigaba da wannan d’abi’a har zuwa lokacin da ‘ya’yan fatake suka d’unguma zuwa gare shi, suka gaishe shi sannan suka ce da shi, “har yaushe za ka zama cikin makoki ka yi watsi da sha’anin kasuwancinka da abokanka da sauran jama’a? Hak’ik’a wannan abu ba zai k’are ka da komai ba face ya raunana maka jiki ya sa ka wahala matuk’a gaya.” A lokacin da suka shiga gare shi Iblis na tare da su la’ananne yana gyara musu magana yana k’awata masa batunsu, har ya rud’u da maganarsu. Iblis ya ingiza, ya lamunta da su, ya tashi daga wajen zamansa ya fita tare da su. Zanci gaba02 HIKAYAR ALIYI MASIRIYYI DAN HASANUL BAGADADU A lokacin da suka shiga gare shi Iblis na tare da su la’ananne yana gyara musu magana yana k’awata masa batunsu, har ya rud’u da maganarsu. Iblis ya ingiza, ya lamunta da su, ya tashi daga wajen zamansa ya fita tare da su. , ‘Ya’yan fatake suka yi ta rarrashin Ali Misiriyi cewa ya bi su zuwa ga shagalinsu har ya amince cikin hukuncin Allah da ya yi nufin tabbata. Ya tashi ya daga gidan da yake makoki ya bi su. Suka ce da shi “ka hau alfadararka mana mu tafi zuwa lambun waje kaza inda za mu yi nishad’i, bak’in cikinka ya yaye.” Ya sa bawansa ya kawo masa alfadara ya bi su. Yayin da suka shiga wani daga cikin su ya kawo musu abinci da abinsha suka ci suka sha sannan suka zauna suna hira har zuwa fad’uwar rana, sannan suka watse, ya dawo gida. Da gari ya waye suka dawo suka ce, “ka taho tare da mu.” Ya ce, “ina za mu je?” suka ce, “lambun wane da ke waje kaza, ya fi na jiya kyau da k’ayatarwa.” Ya tashi ya bi su zuwa lambun da suka fad’a masa. Wani daga cikin su ya kawo abinci da abinsha sannan ya taho da giya mai k’arfin sa maye. Bayan sun ci abinci aka kawo giyar ya ce musu, “menene wannan?” suka ce, “wannan shi ne sinadarin gusar da bak’in ciki da b’acin zuciya, kuma yana jawo farin ciki.” Suka yi ta rud’arsa har ya amince ya sha wannan giyar, sannan suka zauna suna ta hira har zuwa fad’uwar rana sannan kowa ya watse. Amma shi Ali Masiriyi tun da ya sha giyar nan hankalinsa ya fita daga gare shi, ya rik’a fad’uwa yana tashi, ya tafi gida da jirkitaccen hali, matarsa ta gan shi ba yadda ta san shi ba ta ce, “me ya same ka ne a wannan ranar duk ka sauya haka?” Ya ce, “yau mun kasance cikin ni’ima ni da abokaina, mun je wani lambu suka kawo mana abinci da wani abinsha, kowa ya sha har da ni sai na rik’a fad’uwa ina tashi kamar yadda kika ganni.” Ta ce, “haba shugabana, yanzu har ka manta da nasihar mahaifinka cewar ka guji huld’a da miyagun mutane?” Ya ce, “ai wad’annan ba wasu miyagu ba ne, ‘ya’yan fatake ne, ba su da wani aibu tare da su. Kawai dai suna son wartsakewa ne da nishad’i.” Ya cigaba da biyewa abokansa suna zuwa kullum lambu na yau daban da na gobe suna nishad’i suna shaye – shaye har zuwa lokacin da suka ce masa, “to mu mun kammala namu saura kai.” Ya ce, “wannan babu laifi, gobe kowa ya zo gidana mu yi walima a can.” Washegari kowa ya zo, ya sa aka kawo gasasshen rago da dukkan abin da ake buk’ata na wajen ci da sha ninki biyun yadda suka saba yi masa. Ya d’auki masu dahuwa da shimfid’a da sauran kaya suka tafi zuwa ga lambunsa. Ya zauna a nan wata guda cikakke suna nishad’i suna cin abinci da sauraren kuyangi suna musu kid’a da wak’a. Bayan watan ya k’are Ali ya lura ya ga ya kashe kud’i masu yawan gaske, amma bai damu ba saboda gamsuwar da ya samu kuma yana da dukiyar kamar ba za ta k’are ba. Shaid’an kuwa ya sake ingiza shi yana riya masa a ransa cewa, “ko ka kashe fiye da haka babu komai saboda ka mallaki dubunsu. Ina ruwanka ma da wani lissafi tunda babu wani abu da ya ragu daga mallakinka?” Sai kuwa ya hau ya zauna. Ya cigaba da shagalinsa da abokansa har shekara uku. Matarsa a kullum na tuna masa nasihar mahaifinsa amma baya kula da ita ba har ya wayi gari tsabar kud’i ya k’are gaba d’aya babu ko dirhami d’aya. Ya zamana yana d’aukar jauhari yana siyarwa yana musayar tamaninsu har su ma suka k’are gaba d’aya. Sannan ya shiga cikin kadarorinsa na daga gidaje da filaye da gonaki da lambuna har ya kasance d’aya bai ragu ba sai gidan da yake zaune tare da iyalinsa. Ya kwshe kayan adon gidan ya sayar. Sannan ya sa aka b’amb’are dutsen adon ya sayar ya sha shagali da kud’in. Da kud’in suka k’are ya wayi gari bai mallaki komai ba sai kangon gida, shi ma ya sa shi a kasuwa ya sayar ya karb’e kud’in. Bayan wani lokaci wanda ya sayi gidan ya zo ya ce masa, “yau nake so ka ba ni gidana.” Ya fita zuwa ga wani abokinsa ya yi aron d’aki, ya kasance bai mallaki komai ba daga shi sai matarsa sai ‘ya’yansa biyu, mace da namiji. Ya sayar da dukkan bayin da ya mallaka. Ya zama yana fita wajen dilallai yana musu k’wadago suna biyan sa abin da bai kai ya kawo ba, domin ba ya isar sa biyan buk’atunsa na yau da kullum. Matarsa ta ce, “na sha yi maka gargad’i kan nasihar da mahaifinka ya yi maka amma ba ka ji ba, to yanzu kam abin ya zama lahaula wala k’uwwata. Ka tafi wajen abokanka ko za ka samu wani abu daga gare su domin mu samu abin da za mu ci.” Ya tashi ya tafi gidajensu d’aya bayan d’aya, duk wanda ya je ya yi masa sallama sai ya b’oye fuskarsa daga gare shi. Bai samu d’aya da ya amsa masa ba balle ya biya masa buk’atarsa. Ya dawo wajen matarsa ya ce, “babu wanda ya ba ni komai.” Da ta ji haka sai ta tashi ta tafi wajen danginta ta shaida wa wata mace halin da suke ciki. wadda a baya ta san suna cikin wadata. Da ta gan ta a wani mawuyacin hali sai matar ta ce mata,”me ya faru gare ku haka?” Matar ta kwashe dukkan zance ta shaida mata. Ta yi kuka mai yawa sannan ta ce, “kada ki damu, zauna ki yi farin ciki, zan ba ku abin da zai ishe ku ba tare da neman biya daga gun ku ba.” Ta ba su kayan masarufi da zai ishe su wata guda suna amfani da shi. Da ta isa gida mijin ya ga wad’annan kaya sai ya ce, “daga ina kika samo wannan?” Ta ce, “daga wajen wance na samo bayan na shaida mata abin da ya same mu.” Mijin ya yi kuka mai yawa sannan ya ce, “tun da ke kin yi wannan k’ok’arin, ni ma zan fita domin na je wani wurin watak’ila Allah ya bud’a min a can.” Ya sumbace ta sannan ya yi mata sallama da ‘ya’yansa ya fita bai san inda yake tafiya ba har ya gangaro yankin Bulak’u wajen kogi ya ga jirgin matafiya, yana shirin tafiya zuwa Dimyad’a ya shiga. A ciki ya tarar da wani mutum tsohon abokin mahaifinsa, ya gaishe shi sannan mutumin ya ce masa, “ina za ka je ne haka?” ya ce, “za ni Dimyad’a ina da wasu abokai a can za ni mu gaisa na dawo.” Mutumin ya d’auke shi ya girmama a hanya kuma ya mutunta shi, ya ba shi wata jaka mai k’unshe da dinarai. Yayin da suka isa Ali ya sauka bai san inda zai nufa ba, ya yi ta yawo cikin kwararon garin. Wani bafatake ya gan shi, ya ji tausayinsa, ya kai shi gidansa ya zaunar da shi zuwa wani lokaci. Ali ya ce cikin ransa bayan ya jima a wannan gidan, ‘har yaushe wannan zaman zai k’are a gidan mutane?’ ya fita daga gidan yana yawo har ya zo mashigar jirage ya tambayi inda jirgi mai tashi ya nufa aka ce masa zai tafi zuwa Sham. Ya shiga aka tafi da shi. Tafiya ta yi musu kyau suka isa lafiya sannan ya sauka ya cigaba da tafiya har ya isa birnin Dimashk’a. Yana tafiya shi kad’ai sai wani mutum ya gan shi, wanda zuciyarsa ke cike da alheri ya kama hannunsa ya kai shi gidansa ya zaunar da shi yana kula da shi har zuwa wani lokaci. Wata rana ya fito yana yawo sai ya ga karauka na shirin tafiya zuwa birnin Bagadaza, sai ya ji sha’awar shiga cikin su a tafi tare da shi. Ya koma ya shaida wa maigidansa, ya shaida masa sannan ya yi masa bankwana. Ya komo cikin karauka aka tafi da shi. Allah da ikonsa sai madugun tafiya ya jawo shi kusa da shi yana kyautata masa yana ciyar da shi gami da ba shi kyautuka har suka kusato da birnin Bagadaza. ‘Yan fashi suka tare su suka k’wace musu duk abin da suke da shi na daga kud’i sannan suka hallaka wasu. Allah ya kub’utar da Ali Misriyi ya tafi shi kad’ai zuwa birnin Bagadaza. Lokacin da ya isa rana ta riga ta fad’i daidai lokacin da masu tsaron k’ofa ke shirin rufe k’ofar ya isa da gaggawa yana mai cewa, “bari na shiga kafin ku rufe!” Suka bar shi ya shiga, sannan suka ce da shi, “daga ina kake kuma ina ka dosa?” Ya ce musu, “ni mutumin Misira ne daga birnin Alk’ahira, akwai tare da ni dukiya mai yawa da bayi da hadimai. Na rigaye su zuwa ne kafin su iso domin na shirya wurin da zan sauke kayana na shiga kasuwanci. Ina cikin tahowa a kan alfadarata na iske gungun ‘yan fashi suka tare ni suka k’wace min komai, amma na tsira da raina. ZANCI GABA03 HIKAYAR ALIYUL MASIRIYYU DAN HASANUL BAGADADU Masu tsaron k’ofa suka yi masa karamci sannan suka ji tausayin labarin da ya ba su, suka ce masa, “zauna nan wajenmu har gari ya waye za mu kai ka wurin da ya kamace ka.” Ya zauna nan tare da su, ya fito da kud’i daga wad’anda bafatake ya ba shi ya mik’a wa d’aya daga masu tsaron ya ce, “karb’i wannan ka samo mana abin da za mu ci.” Bayan an jima kad’an mai tsaron k’ofa ya dawo d’auke da sha’ir da nama. Suka zauna suka ci gaba d’aya sannan ya kwanta barci a wurin da suka tanadar masa. Da gari ya waye suka kai shi wajen wani attajiri, suka shaida masa cewa bak’on falke ne wanda ke jiran zuwan kayansa, amma ya gamu da tsautsayi a hanya. Kayansa na nan zuwa ba da jimawa ba. Attajiri ya aminta da wannan labarin, ya marabce shi da kyau, ya aika gida aka taho da kayan sawa na alfarma daga cikin nasa sannan ya ce da Ali, “mu je na raka ka gidan wanka.” Suka tafi tare, Ali ya yi wanka, ya gyara jikinsa ya sanya wad’annnan tufafin da attajiri ya kawo masa. Sannan suka dawo suka yi kalaci na abinci mai rai da lafiya. Attajiri ya ce da wani bak’in bawansa, “kai Mas’udu tafi da shi gidajen nan nawa guda biyu ya zab’i duk wanda ya yi masa ya zauna a ciki.” Ali ya bi bayan bawa har zuwa wani kwararo inda wasu sababbin gidaje uku suke gefe da gefe duk suna rufe babu kowa a ciki. Aka bud’e gida na farko, ya shiga ya dudduba sannan ya fito ya shiga na biyu ma ya dudduba. Bayan sun fito sai bawan ya ce masa, “wanne kake son zama a cikin su?” Ali Misiriyi ya ce, “wancan na ukun mallakin wanene?” Bawa ya ce, “shi ma na maigidanmu ne.” “Bud’e min shi ma na gan shi.” “Wannan bai shafe ka ba.” “Saboda me?” “Saboda duk wanda ya shiga ciki da dare, idan gari ya waye da safe sai dai a tsinci gawarsa. Mu kuma ba ma iya bud’e k’ofa idan za mu kawar da gawar sai dai mu shiga ta rufin d’aki daga d’aya daga gidajenmu mu fitar da shi. Saboda haka maigidanmu ya yi watsi da gidan yana mai cewa shaid’anu ne a ciki. Ba za a sake saukar da bak’i a ciki ba.” Ali Misiriyi ya ce a ran sa, “wannan ce damar da nake nema. Gara na shiga ciki kurum na mutu na huta.” Ya ce da bawa, “bud’e min na gan shi duk da haka.” Bawa ya bud’e masa ya shiga. Ya tarar da kayan alatu fiye da abin da ke cikin na baya. Ya fito ya ce da bawa, “wannan gidan shi ya yi min, ba ni mukullansa.” Bawa ya ce. “ba zan aikata haka ba sai na shaida wa maigidina tukunna.” Ya juya ya tafi wajen maigidan. Yayin da attajiri ya ji haka sai ya taso da kansa ya taho wajen Ali ya yi masa magana ya ce, “ya shugabana, hak’ik’a ba ka buk’atar kwana a wannan gidan domin kuwa kana buk’atar shan ruwa a gaba.” Ali ya ce, “babu makawa na kwana cikinsa domin ya fi ragowar kyau, ban kula da wannan camfin naku ba.” Attajiri ya ce, “to sai ka rubuta mini takardar cewar kai ne bisa ra’ayin kanka ka zab’i kwana a wannan gida, duk abin da ya same ka ba ka da kaito.” Ali ya ce, “na amince a rubuta.” Aka kirawo alk’ali da shaidu suka tabbatar da haka, sannan attajiri ya tafi ya aiko masa da shimfid’a, bawan ya kawo masa shimfid’ar sai ya ajiye daga waje saboda tsoron kada wani abu ya same shi idan ya shiga gidan. Ali ya shiga da shimfid’ar, sannan ya sake zagaya cikin gidan yana masa kallon tsanaki. Ya ga rijiya a ciki da guga. Ya d’ebo ruwa ya yi alwalla ya yi sallah. Ya zauna yana jan carbi sai bawan nan ya dawo d’auke da fitila da abinci da tasa da kuma shantali, duka ya ajiye su a k’ofar gida ya tafi. Ali ya d’ebo kaya duka ya shigo da su, ya kunna sannan ya gabatar da sallar dare, ya ci abinci ya yi shirin barci. Ya soma barci kenan sai wata zuciyar ta ce masa gara ya koma daga sama ya yi barcin a can. Ya kwashe shimfid’arsa ya hau zuwa d’akin da ke saman bene, ya ga d’akin k’awatacce fiye da adon d’akin k’asa. An shafe bangayensa da launin ruwan zinariya, ya d’aga kansa yana mamakin adon da aka yi masa. Sannan ya baza shimfid’arsa ya kwanta. Ya soma karanta ayoyin neman tsari daga Alk’urani mai girma sai ya ji wata murya tana ce masa, “Ya Aliyu d’an Hassan, yalla kana buk’atar na yi maka ruwan dinari?” Ya amsa ya ce, “daga wanne bigire za ka aiko mini da dinarin?” Tun kafin ya rufe bakinsa sai ga dinarai na zuba kamar ruwan sama, sai ka ce dutsen da aka harbo suna fad’owa da k’arfi wasu na dukan jikinsa. Ba su gushe suna zubowa ba har wannan bigiren ya cika mak’il da dinari. ZANCI GABA04 HIKYAR ALIYYI MASIRIYIL DAN HASANUL BAGADADIYU Ba su gushe suna zubowa ba har wannan bigiren ya cika mak’il da dinari. Daga nan muryar ta ci gaba da cewa, “yanzu ka ‘yanta ni na kama gabana tunda na kammala abin da aka umarce ni, na sadar da wannan ajiyar gare ka.” Ali ya ce, “na had’a ka da girman Allah ka fad’a mini musabbabin wannan ruwan dinarin.” Muryar ta ce, “wannan dukiya ce da aka yi siddabaru a jikinta lokaci mai tsawo ga dukkan wanda ya shiga wannan gida muna ambatonsa da Ali d’an Hassan domin shi aka ce mu dank’a wa duk ranar da ya shigo nan. Idan muka yi wa mutum wannan tambayar muka ga ya razana ya shiga yin kururuwa, sai mu sauka bisa gare shi mu karya masa wuya, amma kai da muka yi maka wannan tambayar sai ba ka rud’e ba, sai ma ka k’ara da cewa ta ina za a samu wannan dukiyar. Da haka muka gane cewa kai ne wanda aka nufa da ita muka kawo maka. Bayan wannan kuma akwai dukiya mai yawa da ke jibge a birnin Yamal, sai ka tafi ka je ka d’auko kayanka. Ni dai yanzu ina so ka sallame ni na kama gabana” Ali Misiriyi ya ce, “wallahi ba zan sallame ka ba sai ka kawo min dukiyar Yamal d’in nan wurina.” Muryar ta ce, “idan na kawo maka ita za ka sallame ni?” “K’warai kuwa zan sallame ka.” Ali ya ce da muryar. “Ina so ka rantse mini kan haka.” Ali ya rantse sannan ya ce, “ina da buk’ata d’aya gare ka bayan wannan.” “Wacce buk’ata ce?” “Ina mata da ‘ya’ya biyu suna birnin Masar a waje kaza. Ina so ka je ka taho mini da su cikin dad’in rai ba da cutarwa ba.” Ya ce, “zan zo maka da su cikin darbuka tare da bayi da hadimansu gaba d’aya da dukiyar nan ta Yamal da yardar Allah.” Daga nan ya nemi ya ba shi kwana uku zai je ya taho da dukkansu ya tafi. Aliyu ya kwana a wannan waje, yayin da gari ya waye ya tashi ya zagaya cikin gidan ya ga ko’ina ya cike da dinari. Ya ga wata ‘yar k’ofa daga k’asa da aka rufe ta wani murfi ya d’aga ya shiga ya tarar da wajen da ake ajiye tufafi ne babu komai sai kyankyandi ne a jejjere. Ya d’ebo kyankyandai ya rik’a cika su da dinaran har ya cika su baki d’aya ya kawo su wurin ya adana. Ya maida marufin ya rufe kamar ba a tab’a bud’ewa a kusa ba. Ya koma ya zauna babu jimawa ya ji ana k’wank’wasa k’ofar gida, ya bud’e sai ya ga bawan nan a tsaye. Yayin da bawan ya gan shi cikin k’oshin lafiya da ransa sai ya cika da mamaki ya juya da gaggawa zuwa ga maigidansa. domin ya kai wa maigidansa labari, yana zuwa sai ya ce da shi, “ya shugabana, hak’ik’a wannan attajirin nan da ya kwana cikin gidan nan yana da alak’a da aljanu. Na same shi cikin k’oshin lafiya da alheri yana zaune bisa kujera da ke bayan k’ofa a wurin da ake samun gawar duk wanda ya kwana a gidan.” Attajiri ya tashi cikin farin ciki da murna ya tafi gidan yana d’auke da kayan karin kumallo. Yayin da suka had’a ido sai ya rungume shi yana mai nuna farin cikinsa da haka. Ya tambaye shi, “yaya lamarin Allah ya kasance a kanka?” Ali ya ce, “na yi barci na a d’akin sama wanda aka yi wa ado da ruham.” “Wani abu bai zo gare ka ba na daga ban tsoro?” “Ban ga komai ba saboda lokacin da zan kwanta na yi addu’a daga surorin Alk’ur’ani mai girma. Da na farka na yi alwalla na yi sallah sannan na dawo bayan k’ofa na zauna.” “Mun gode wa Allah ubangijin Musulunci da ya tsare ka!” In ji attajiri yana mai nuna farin cikinsa da wannan abu. Ya tafi ya aiko masa da bayi da kuyangi da hadimai. Suka share gidan gaba d’aya suka yi shimfid’a a d’akunan sama da na k’asa. Sannan suka tafi suka bar bayi uku da hadimai biyu da kuma kuyangi hud’u domin su hidimta masa. Yayin da attajirai ‘yan kasuwa suka samu labarinsa sai suka rik’a aika masa da kyautuka daga zab’ab’b’un abubuwa na daga abinci da abinsha da tufafi. Suka zo wurinsa suka ce masa, “yaushe kayanka zai iso?” Ya ce, “ina sa ran nan da kwanaki uku za su iso.” Yayin da kwanakin suka cika sai wannan mai tsaron taskar ya zo gare shi ya ce masa, “je ka bayan gari ka samu dukiyarka da ke Yamal da iyalinka duk na taho maka da su. Amma dukkan bayin da hadimai da dabbobin da ke tawagar aljannu ne.” To a lokacin da aljanin nan ya yi

Chapter 1 of 2