Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 2
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels This Document is compiled by Shuraihu Usman - 08140419490 YEAR of compilation - 2023; Published to Taskarnovels.com.ng 01. HIKAYAR TUFFA UKU Allah shi ne Sarki ma fi daukaka daga dukkan Sarakuna, shi ne ma fi tsarki daga dukkan abubuwa. Wata rana da dare, daga cikin ranaku, a cikin birnin Bagadada, lokacin da Halifa Harun Al'Rashid da Wazirinsa Ja'afarul Barmakiyi ke mulki, Halifa ya aika cikin dare aka kira masa waziri Ja'afaru da sarkin fada Masruru. Ya ce musu, "Ina so a cikin wannan dare mu canja kama, irin ta fatake, mu shiga cikin birni, mu tambayi talakawa a kan yadda suke ganin mulkinmu a kansu, duk wani hakimi, ko wakili ko mai unguwa da muka ji talakawa na kuka da shi, sai mu tube shi." Ja'afaru da Masruru suka ce, "Mun ji, mun dauka!" Suka yi shiga irin ta fatake, suka shiga cikin birni. Suna cikin tafiya cikin wani kwararo, sai suka ga wani tsoho, shekaru sun yawaita a kansa, yana dauke da wata tsohuwar koma ta kamun kifi, yana tafe yana wake-wake. A cikin wake-waken nasa sai suka ji yana cewa: "Koyaushe mutum ya kai kara zuwa gare su, sai su wulakanta shi, koda shi yake da gaskiya. Idan haka ne kuwa, kasancewar ran talaka a cikin kabari shi ne ma fi kyawon zama." Yayin da Halifa ya ji wannan waka ta dattijo, ya dubi Ja'afaru ya ce, "Dubi wannan talaka, ka ji wannan waka tasa? Lalle akwai abin da ke damun sa a cikin zuciyarsa." Halifa ya gabata a gaban tsoho ya ce, "Ya kai wannan tsoho, mene ne sana'arka?" Tsoho ya ce, "Ya shugabana, su ce sana'ata. Ni talaka ne, na fita daga gidana tunda tsakar rana na nufi kogi kamun kifi, har zuwa wannan lokaci da na dawo, Allah bai nufa na kama wani abu da zan ci ni da iyalina ba, domin bakin cikin wannan abu, nake gurin mutuwata." Halifa ya ce da shi, "Ko za ka koma tare da mu zuwa ga kogin Dujillati, ka jefa komarka a ciki, bisa ga arzikina, komai komarka ta debo a cikin kogin zan saye shi dinari dari, ka sami abin da za ka ci da iyalinka?" Tsoho yayi farin ciki da jin wannan magana ta wannan farke. Baisan sarkinsa bane' Ya ce, "Na yarda, ya shugabana." Suka dunguma suka nufi kogin Dujillati, da suka isa, tsoho ya warware komarsa, ya jefa bisa ruwa, ta nutse kasa, ya jirkita ta, sannan ya jawo ta. Koma ta fito da akwati dake sarki me cika alkawarin saiya biya' kudin wannan akwati babba mai nauyi. Yayin da Halifa ya gan shi, ya dubashi shi, ya same shi nannauya. Ya ba masunci dinari dari, ya tafi yana murna. Masruru ya dauki akwati tare da Ja'afaru suka nufi gidan Halifa. Da suka isa, suka kunna fitila, aka ajiye akwati saiya ciro mab'alli Halifa. Ja'afaru da Masruru suka karye murfin akwati suka tarar da kubba a ciki, an rufe ta da jan gashi. Suka yaye gashin, suka tarar da mayafi karkashinsa, suka yaye mayafin, suka tarar da shimfida karkashinsa, suka yaye shinfidar, sai ga yarinya a kwance, kai ka ce narkakkiyar azurfa ce don kyau. An yanka ta gunduwa-gunduwa, ta kasance matacciya. Yayin da Halifa ya ga wannan yarinya da irin kisan da aka yi mata, sai hankalinsa ya tashi, hawaye ya karyo masa yana gudana a kan kundukukinsa. Ya waiwaya zuwa ga Ja'afaru cikin fushi mai tsanani, fushin da bai taba yin irinsa ba, ya ce da shi, "Ya karen wazirai, Wallahi ka cancanta da na kashe ka a cikin wannan lokaci. Kana wazirina har a kashe mutum, a saka a cikin akwati a jefa cikin kogi cikin zamanin mulkina. Kuna so wannan laifin kisa ya ratayu a kaina? Wallahi! Babu makawa in bincika al'amarin wannan yarinya, duk wanda aka samu ya kashe ta, in kashe shi, in saka mata hakkinta." Hankalin Ja'afaru ya tashi, domin bai taba ganin fushin Halifa kamar irin wannan ba. Halifa ya dube shi ya ci gaba da cewa, "Da girman saduwata ga dangin Halifofi na daga Banu Abbas, idan ba ka zo mini da wanda ya kashe wannan yarinya ba, in saka mata gare shi, Wallahi sai na rataye ka a kofar gidana, kai da mutum arba'in na daga 'yan uwanka!" Ja'afaru ya ce, "Ka jinkirta mini zuwa kwana uku, ya Sarkin Musulmi!" Halifa ya ce ya jinkirta masa. Ja'afaru ya fita daga gidan Halifa, ya nufi cikin birni yana mai bakin ciki, yana cewa a cikin ransa: Ina zan san wanda ya kashe wannan yarinya, har in hallara shi gaban Halifa? In na hallara masa wani wanda ba shi ya aikata laifin ba, aka kashe shi, alhakinsa ya ratayu ga wuyana ke nan, ni yanzu ban san abin da zan aikata ba. Ya nufi gidansa. Ja'afaru ya yi zaune gidansa har kwana uku suka wuce. Rana ta hudu Halifa ya aika zuwa gare shi, yana nemansa. Yayin da ya zo gaban Halifa, sai ya tambaye shi, "Ina wanda ya kashe yarinya?" Ja'afaru ya ce, "Ya Sarkin Musulmi, ni na san abin boye ne, ballantana na san wanda ya kashe yarinya?" MUHADU GOBE DOMIN CIGABA02. HIKAYAR TUFFA UKU (TALE OF THE THREE APPLES) Halifa ya juya wurin dogarawa ya ba su umurni su rataye Ja'afaru da 'yan uwansa. Tausayi ya kama mutane, wasu suka fara kuka. Dogarawa kuwa suka zabura domin cika umurnin Sarkin Musulmi Daga nan sai ga wani saurayi kyakkyawa, mai kyawawan tufafi, ya keto daga cikin mutane da gaggawa, ya zo ya durkusa a gaban Halifa. Ya ce, "Ya Sarkin Musulmi, ni ne na kashe wannan yarinya da kuka gani a cikin sunduki. Kashe ni a madadinta, domin daukar mata fansa." Yayin da Waziri Ja'afaru ya ji zancen wannan saurayi, da abin da ya bayyana daga zancensa, ya yi farin ciki da kubutar ransa da na 'yan uwansa, sannan kuma ya yi bakin ciki da hukuncin da za a yi wa wannan saurayi. Halifa ya yi umurni da a rataye wannan saurayi tunda ya yi ikirari. Dogarawa suka cafe saurayi za su rataye shi. Daga nan sai ga wani tsoho mai yawan shekaru, ya ratso ta cikin mutane yana kuka. Ya zo ya durkusa a gaban Halifa ya ce, "Ya Sarkin Musulmi, kada ka kashe wannan saurayi ba da alhakinsa ba. Ni ne wanda ya kashe yarinya, a kashe ni maimakonta." Saurayi ya ce, "Ya Halifa wannan tsoho ya tsufa da yawa,rudewar tsufa ce ta sa shi yin wannan magana. Ni ne na kashe yarinya, a kashe ni maimakonta, ku biya alhakinta da ni." Tsoho ya ce da saurayi, "Ya dana, kai yaro ne kankane, yanzu ka fara sha'awar duniya. Ni na girma na koshi da duniya, na fanshe ka na fanshi Waziri Ja'afaru da 'yan uwansa, babu wanda ya kashe yarinya sai ni. Domin Allah na roke ku, ku gaggauta kisasi da ni." Halifa ya dubi saurayi da tsoho ya ce, "Wanene daga cikinku ya kashe yarinya?" Saurayi ya ce, "Babu wanda ya kashe ta sai ni, don haka a kashe ni." Tsoho ya ce, "A'a, ni ne na kashe ta, don haka ni ne ya kamata a kashe." Da Halifa ya ji haka, sai ya ce a rataye su duka su biyun. Waziri Ja'afaru ya ce a'a, mutum daya ya yi kisan kai kuma a rataye biyu, wannan zalunci ne ya Halifa. Saurayi ya ce, "Da girman wanda ya daukak sama, ya shimfida kasa, ni ne na kashe yarinya, na sanya ta a cikin sunduki, na jefa sundukin a cikin kogin Dujillati." Ya siffanta abin da aka samu a cikinsundukin majeranta. Halifa ya gasgata saurayi, ya kuma tabbata shi ne ya kashe yarinya. Halifa ya yi al'ajabi a kan wannan al'amari, ya tambayi saurayi dalilin kisan yarinya. Saurayi ya ce, "Ka sani ya Sarkin Musulmi, cewa wannan yarinya matata ce, 'yar baffana. Wannan tsoho shi ne ubanta kuma baffana ne. Na aure ta tana budurwa, na sami zuri'a da ita 'ya'ya uku, dukkansu maza. Ta kasance tana so na, matsanancin so, tana yi mini biyayya iyakar biyayya, da dai ba ta taba bata mini rai ba. Ranar farko ta wannan wata, sai ta kwanta rasahin lafiya mai tsanani. Na nemo masu magani kala daban-daban, suna ba ta magunguna har ta fara samun sauki. Ran nan na shiga dakinta, sai ta ce da ni, tana son wani abu, domin tana marmarinsa. Na tambaye ta menene shi? Ta ce da ni, tana marmarin cin tuffa. Na ce zan siyo mata. Da fita ta daga dakinta, ban zame ko'ina ba sai kasuwa wurin neman tuffa. Na zagaye kasuwa duka amma ban samu ko daya ba. Na dawo cikin gari ina cigiyar tuffa koda daya ta kasance dinari daya in siya, amma ban samu ba. Na kwana cikin wannan dare ina mai tunani. Da gari ya waye na kara fita cigiyar inda zan sami tuffa. Na hadu da mai sayar da 'ya'yan itace, na tambaye shi tuffa, ya ce mini, tuffa ta yi karanci yanzu, ba lokacinta ba ne, ba a samunta ko'ina sai a cikin gonar Sarkin Musulmi ta Basara. Da na dawo gida, na shiga wurin matata, sonta ya daukaka a gare ni. Na yi nufin tafiya Basara wajen neman tuffa, daga nan Bagadada kuwa tafiyar kwana goma sha biyar ne, amma ban gaya wa matata ba, sai dai na fada mata zanyi tafiya ta kwana talatin. Muka yi bankwana da ita. Na shirya na kama hanya, ina ta tafiya ba dare ba rana, har kwana goma sha biyar, na isa Basara. Na tafi wurin mai kula da gonar Sarkin Musulmi, na siyo tuffa guda uku, kowace daya a kan dinari daya. Na juyo zuwa gida, na yi wasu kwanaki goma sha biyar kafin na iso. Bayan na iso gida, na shiga dakin matata na ba ta tuffar guda uku, na fada mata inda na samo su, da kuma kudin da na siyo su. Ba ta nuna alamun farin ciki ba ko kadan da wannan kokari da na yi. Ta karba ta ajiye su yashe a kasa. Bayan 'yan kwanaki kadan ta warke sarai daga rashin lafiyarta. Ran nan na fita kasuwa, ina zaune a cikin rumfata ina cininki. Daga nesa, sai na hango wani bakin mutum a cikin rana, da tuffa a hannunsa. Da ya zo ta gaban rumfata zai wuce, sai na ce a zuciyata, ina wannan bakin mutum ya sami tuffa a cikin wannan gari wanda na zagaye ko'ina ban samu ba? Bari in tafi ya fada mini inda ya siyo, idan na tashi saye nan gaba ba sai na sha wahala ba. Da ya zo dab da rumfata, sai na yi sauri na fito na tare shi, na ce abokina ina ka siyo wadannan tuffa, idan na tashi siya in tafi can in siyo? Sai bakin mutumin nan ya yi dariya ya ce mini, "Masoyiyata abar begena ce ta kai mini su har gida. Ta ce mini lokacin da ba ta da lafiya, sakaran mijinta ya tafi har Basara ya siyo mata su, guda ukun nan a kan kudi dinari uku." Lokacin da na ji zancen wannan bakin mutum, ya Sarkin Musulmi, duniya ta yi mini baki kirin, na ji babu wanda na tsana a raina kamar wannan mutum da matata, maciya amana. Amma ita ce mai babban laifi tunda har gida take isko shi. Nan take na rufe shagona, na nufi gida a fusace. Da zuwana na tambayi matata, "Ina tuffar da na siyo miki guda uku?" Ta ce da ni, ba ta sani ba, ba ta kuma san inda suke ba. Tun daga nan na gasgata zancen bakin mutumin nan, bana tsaya na yi wani dogon bincike ba. Idanuna suka rufe da tsananin fushi da kiyayya. Na tashi na dauki wuka, na hau bisa ga kirjinta, na yanka ta da wukar. Na yanke kanta da gabobinta, na yi mata gunduwa-gunduwa. Na yi gaggawa na rufe ta da mayafi, na kunsheta a cikin shimfida, na sa ta cikin kubba na rufe, na sa kubbar a cikin sunduki. Da dare ya yi na dauki sundukin na dora shi a kan alfadarata, na tafi na jefa shi a cikin Bahrul Dujillati, babu wanda ya sani, domin lokacin 'ya'yanmu sun tafi gidan baffana. Bayan na jefa sundukin a cikin kogi na dawo gida,sai na tarar da a cikin 'ya'yana daya ya dawo gida yana kuka. Na tabbata bai san abin da na yi wa mahaifiyarsa ba, sai na tambaye shi, me yake yi wa kuka? Ya ce mini, "Na dauki tuffar da ka siyo wa mama, lokacin da ta shiga wanka, na fita ina wasa da su a hannuna zan je gidan kaka, sai na hadu da wani bakin mutum ya kwace su daga hannuna ya ce ina na same su? Na fada masa babana ne ya siyo wa mamata su lokacin da ba ta da lafiya, duk daya a kan dinari daya, kuma har Basara ya tafi neman su saboda sonta da yake yi. Ya mangare ni, ya tafi da su. Ina jin tsoro kada mama ta gane ni ne na dauke su ta buge ni." Yayin da na ji zancen dana, sai na tabbata lalle bakin mutumin nan shi ne ya yanka zancen karya game da matata. Na kashe ta a kan zalunci, ba tare da ta yi mini wani laifi ba. Na yi kuka, kuka mai yawa. Ina cikin wannan hali, sai ga wannan tsoho, mahaifin matata, ya rako sauran 'ya'yanmu. Na labarta masa ga abin da ya kasance ga 'yarsa, ya zauna a gefena yana kuka, ba mu gushe ba muna kuka har tsakar dare. Muka yi zaman makoki a wannan dare. Bayan kwana hudu sai muka ji ana shelar ratayewar Waziri Ja'afaru da 'yan uwansa, shi ne muka zo, sai muka samu wannan labari. Ina hada ka da girman Allah, ya Halifa, ka gaggauta sa a rataye ni, domin biyan kisasi ga matata, ni ina jin tsoron yin shari'a da ita ranar lahira." Koda saurayi ya gama labarinsa, gaba dayan jama'ar dake wurin idonsu ya cika da hawaye, hatta Halifa sai da ya zubar da hawaye. Halifa ya ce, "Na rantse da Allah ba ni kashe kowa face wannan bakin mutum, funafuki, annamimi." Halifa ya juya ga Ja'afaru ya ce, "Na ba ka kwana uku, ka kawo mini bakin mutumin nan, idan ba haka ba zan rataye ka, da 'yan uwanka mutum arba'in." Jama'a duk suka watse. Waziri Ja'afaru ya koma gida yana mai bakin ciki, yana cewa a ransa, "Ta yaya zan iya nemo wannan bakin mutum cikin dubban mutanen da ke wannan birni? Na rantse da Allah ba zan fita daga gida na neman kowa ba, Allah da ya kare ni daga halaka yanzu shi nake roko ya kara yi mini mafita." Ya yi zamansa gida har tsawon kwana uku bai fita ba. Zanci gaba03. HIKAYAR TUFFA UKU (TALE OF THE THREE APPLES) Koda saurayi ya gama labarinsa, gaba dayan jama'ar dake wurin idonsu ya cika da hawaye, hatta Halifa sai da ya zubar da hawaye. Halifa ya ce, "Na rantse da Allah ba ni kashe kowa face wannan bakin mutum, funafuki, annamimi." Halifa ya juya ga Ja'afaru ya ce, "Na ba ka kwana uku, ka kawo mini bakin mutumin nan, idan ba haka ba zan rataye ka, da 'yan uwanka mutum arba'in." Jama'a duk suka watse. Waziri Ja'afaru ya koma gida yana mai bakin ciki, yana cewa a ransa, " Ta yaya zan iya nemo wannan bakin mutum cikin dubban mutanen da ke wannan birni? Na rantse da Allah ba zan fita daga gida na neman kowa ba, Allah da ya kare ni daga halaka yanzu shi nake roko ya kara yi mini mafita." Ya yi zamansa gida har tsawon kwana uku bai fita ba. A cikin kwana na hudu, Waziri ya kira alkalai da shaidu, ya yi wasiyya ga 'ya'yansa da iyalansa, ya yi bankwana da su, yana kuka suna kuka. Daga nan sai ga manzon Halifa ya zo da sakon Halifa na nemansa yanzu-yanzu. Manzon ya ce da shi, " Halifa ya yi fushi mai tsanani, kuma ya rantse wannan rana ba za ta wuce ba face kana ratayayye, kai da 'yan uwanka arba'in, muddin ba ka zo masa da bakin mutumin nan ba." Yayin da Waziri ya ji wannan sako na manzon Halifa, sai ya sake fashewa da kuka, 'ya'yansa ma suka fashe da kuka. Da ya gama bankwana da su, sai ya gabata a gaban 'yarsa karama, 'yar autarsa mai kimanin shekaru shida, domin ya yi bankwana da ita. Ya kasance Waziri na son 'yar nan tasa fiye da sauran 'ya'yansa. Ya jawo ta zuwa ga kirjinsa domin ya rungume ta, sai ya ji wani abu mai tudu a cikin aljihun rigarta. Ya sa hannu cikin aljihunta ya fito da abin da ke ciki, sai ya ga tuffa ce. Nan take kamannun Waziri suka canja, ya tambayi 'yarsa ina ta sami tuffa? Ta ce da shi, "Bakin bawan nan ne namu Raihanu ya ba ni ita tun kwana hudu da suka wuce. Tuffa uku ce, na cinye biyu saura wannan daya, ita ma yau zan cinye ta." Lokacin da Waziri Ja'afaru ya ji ambaton bakin bawa da tuffa uku, ya yi farin ciki ya ce, "Ya mai kusata farin ciki, ubangijin sammai da kassai, ina kara godiya a gare ka, da ka kubutar da ni da 'yan uwana daga halaka kashi na biyu." Ya yi umurni da a kira masa bawa Raihanu. Da aka hallaro da bawa Raihanu, Ja'afaru ya tambaye shi ina ya sami tuffa uku? Bawa ya ce, "Ya shugabana, tun kwana takwas da suka wuce, ina tafiya cikin wani kwararo na wannan birni, na ga wani yaro yana wasa da tuffa guda uku, na kwace su a hannunsa, bayan ya fada mini cewa na mahaifiyarsa ne da mahaifinsa ya tafi har birnin Basara ya siyo mata, lokacin da ba ta da lafiya, ya fada mini duk daya an siyo ta a kan dinari daya. Na tafi suna rike a hannuna, har na shiga cikin kasuwa. Wani saurayi ya gan su a hannuna ya tambaye ni inda na same su, ni kuwa na yi masa karya na ce, masoyiyata ce ta kai mini su har gida, na tafi ina masa dariya. Bayan kwana hudu sai shugabata ta gan su a hannuna ta ce tana so, ni kuwa na ba ta su duka." Yayin da Ja'afaru ya ji wannan labari na bawa Raihanu, ya yi al'ajabi domin duk wannan fitina ta kashe yarinya da aka saka cikin sunduki, aka jefa a kogi, ta faru ta sanadiyyar wannan bakin bawa nasa. Ya yi umurni da a daure bawa. Ya kara yi wa Allah godiya da ya kubutar da shi. Sannan ya rera wadannan baitoci, ya ce: "Wanda masifarsa ta kasance manisanciya, Rai ba ya da ikon sa shi fansarta, Kai mutum za ka sami bayi da yawa, Amma ranka ba ka samun waninsa." Ja'afaru ya umurci wasu bayinsa da manzon Halifa su tafi da bawa Raihanu wurin Sarkin Musulmi, yana isowa yanzu. Suka tafi da bakin bawa yana daurarre. Amma 'yar Ja'afaru da ba ta san abin da ke faruwa ba, da ta ga an fita da bawa Raihanu a daure, sai ta fashe da kuka tana cewa a dawo musu da bawansu. Ja'afaru ya lallashe ta, ta yi shiru, ya yi mata alkawarin za a dawo da shi. Bayan Waziri Ja'afaru ya shirya, sai ya nufi fadar Halifa. Da ya isa, ya kwashe duk abin da ya faru ya fadawa Halifa. Halifa ya sa aka kira masa saurayi wanda ya kashe yarinya, da dattijo uban yarinya. Bayan sun zauna ya nuna wa saurayi bakin bawa ya ce, "Wannan shi ne bakin mutumin da ka gani da tuffa a hannunsa?" Saurayi ya ce shakka babu, shi ne. Waziri ya bayyana musu yadda aka sami tuffa a hannu 'yarsa wadda ita kuma ta ce bawa Raihanu ne ya ba ta su. Shi kuwa bawa Raihanu sai a lokacin ma ya san abin da ke faruwa na kisan yarinya sanadiyyar karyar da ya yi. Ya durkusa a gaban saurayi da tsoho, yana kuka yana tumurmuza fuskarsa a kasa, yana ba su hakuri a kan karyar da ya yi wa saurayi, yana cewa, " Ya shugabana, ka gafarce ni, wallahi ban fada maka waccan maganar ba domin in hada ka fada da matarka, ban taba sanin ta ba, kai ma ban san ka ba, sai ranar da muka hadu da kai a kasuwa. Wannan maganar na fade ta ne kawai domin in yi dariya. Ina neman gafararku." Halifa ya yi mamaki a kan wannan al'amari da ya faru matukar mamaki. Ya ce, "Da dai ban taba jin labari mai al'ajabi da mamaki ba kamar wannan." Ya juya wurin bawa ya ce babu makawa sai an rataye ka a kan wannan karya da ka yi." Sannan ya ba da umurni a rubuta wannan labari a ajiye shi a dakin ajiye littattafai domin na baya su karanta su karu da darussan da ke ciki. Waziri Ja'afaru ya ce, " Hakika wannan labari abin mamaki ne, amma ko kusa, ko alama, bai kai labarin Waziri Nuruddin da dan uwansa Shamsuddin ban mamaki da tausayi ba. Amma ba zan fada wa Halifa wannan labari ba sai idan ya yi alkawri labarin zai zama fansar rayuwar wannan bawa nawa." Halifa ya amince da haka, amma da sharadin idan labarin bai kai wannan ban mamaki ba, to za a kashe bawa Raihanu. Waziri Ja'afaru ya yarda da haka. Ya gyara zama ya fara bayar da labarin Waziri Nuruddin da dan uwansa Shamsuddin. This Document is compiled by Shuraihu Usman - 08140419490 YEAR of compilation - 2023; Published to Taskarnovels.com.ng An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money

Chapter 1 of 2