Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 2
daukakani da ka tako ka zo gidana, kar allah ya rabamu da irin wannan bullowar da karramwa taku. Sannan sai ta zaunar dashi kan wannan shimfida tace : ranka ya dade ! yakamata ka tube babbar rigan na da rawaninka ka saka karamin rigar. Sai ya tube babbar ragarsa mai tsada irin ta gwamna. Sannan sai ta bashi karamin riga (singlet) da kyalle. Sannan sai tace masa : ranka ya dade ! Ai wannan babban riga da kasa na wazirai yanzu ba lokacinsa bane, kabari idan lokacinsu yayi sai ka dauka kasaka, amma yanzu wannan lokacin Ai lokacin kananan kaya ne kayan bacci, . Da waziri ya karbi kayan bacci ya saka sai suka zauna a kan shimfida, jim kadan sai waziri ya yi yunkurin matsowa saboda ya biya bukatarsa, ita kuma tana kokarin hana sa. Tana ce masa : ranka ya dade ! ai akoi sauran lokaci kar kadamu. To suna cikin haka, sai kawai Aka kwankosa kofa, komai ya wargaje, waziri ya tsorata ya firgita ya tamabayi matar yace mata : waye ? sai tace : mijina ne ya dawo, sai waziri yace : to yanzu me dabara ? sai tace masa : ka tashi in shigar da kai cikin wannan drowan sannan in je in komar da mijina, sai in dawo wurinka in bude, kar kaji tsoro. Sai ta shigar dashi cikin drowa ta sa shi a hawa na 3 ta kulle kirip da kwado. Bayan matar ta kulle waziri a cikin hawa na 3 na wannan drowa. Sai ta je ta bude kofa. Kawai sai ga mai alaframa mai marataba sarkin gari ya bayyana a tseye a bakin kofa. Da matar ta ganshi atake sai ta zube a kasa ta durkusa tayi gaisuwa ta bada girma. Sanna sai ta kama hannunsa ta shigar da shi ciki ta zaunar dashi kan shimfidar. Sai tace masa" - cikin murmushi da fara'a da annashawa - ya mai martaba yau dinnan ka karramamu ka daukakamu, da zamu dauko duniya gabadaya da abunda ke cikinta muka kawo maka To abunda mukayi bai kai ko kadan daga cikin takowar da ka yi ka karramamu ka zo wajenmu ba…. Ranar juma,a insha Allahu zan dora daga yarda na tsaya". Yusuf abdullahi A jibaga, ke kawo muku wannan labari" Whatsapp only 080710511 3803 KAIDI Bayan sarkin wannan gari ya iso gidan wannan mata, sai ya kwankosa kofa, matar ta bude, ta durkusa ta yi gaisuwa ta yi masa marhaba da zuwa. Sanna sai ta kama hannunsa ta shigar da shi ciki ta zaunar dashi kan shimfidar. Sai tace masa : ya mai martaba yau dinnan ka karramamu, zuwarka ta daukakamu, da zamu dauko duniya gabadaya da abunda ke cikinta muka kawo maka, To bai kai ko kadan daga cikin takowar da ka yi ka karramamu ka zo wajenmu ba ( wato halacci da kayi mana ba zamu iya biyanka ba ) Da mai martaba sarki ya zauna akan shimfida sai tacemasa : ya mai martaba ka bani izini inaso in yi maka wata magana, sai yace : kiyi maganarki yadda kikeso na amince miki, sai tace masa : ya shugabana ! yau dinnan ka zauna a nan ka huta kayanka, kuma katube wannan babar riga da rawanin nan naka ka kawo in ajiye maka su...... kuma shima sarkin rigar da ya saka yazo da ita rigace mai tsadar gaske, tafi ta sauran tsada, kimarta ya kai DINARI 1000. To bayan wannan mata ta karbe rigar sarki da rawaninsa, sai ta bashi karamin riga – na bacci – (singlet) wanda kimarsa baiwuce DINARI 10 ba. Bayan haka sai, matar ta soma debe masa kewa tana dauke hankalisa. Kuma wannan duka yana faruwane – wato hirar da ake – alkali da mai girma gwamna da kuma waziri suna kulle a cikn drowa suna sauraron duk abunda ke gudana – hira- tsakanin mai martaba sarki da wannan mata. Amma saidai babu wanda zai iya magana daga cikinsu. A lokacin da sarki ya yunkuro ya miko hannunsa zai daura akan wuyar matar saboda biyan bukatarsa, sai tacemasa : ranka ya dade Ai da sauran lokaci, wannan ranar takace kai dadai, bazata kubuce maka ba, Idan baka manta ba ranka yadade Ai kafin wannan lokacin na maka alkawarin cewar zanbaka irin wannan damar, saboda haka kar ka damu ! zaka samu abunda zai faranta maka rai awurina…. suna cikin haka suna hirai, kawai sai aka kwankosa kofa. Sai sarki yace : – cikin takama da nuna isa – waye wannan ? sai tace : mijinane, sai yacemata : ki je ki komar mana dashi cikin ruwan sanyi ( wato ya koma da son ranshi ) ko kuma in fito ni da kaina in tilasta masa komawa ko bayaso. Sai tacewa sarkin : A’A ranaka ya dade baza’ayi haka ba, kawai kaidai kayi hakuri zanje in yi masa dabara irin tamu ta mata in komar da shi. Sai yace mata : To ni kuma yanzu yaya zanyi ? kawai sai ta kama hannunsa ta daukeshi ta shigar da shi cikin hawa na 4 na wannan drowa ta kulle krip da kwado, sannan sai ta je ta bude kofa, sai ga kafinta a tseye a bakin kofa. Batareda bata lokaci ba, kafinta ya yi sallama ya kutsa ya shiga. ita kuma Batareda ta amasa sallamar ba tacemasa – fuskarat a daure - : wannan wani irin drowa ne ka kera mini ? sai yace mata : ranki ya dade ! me ya samu drowar ? sai tace masa : Ai wannan drowar da ka kera tayi matsi sosai, sai yace mata : ranki ya dade ! Ai wannan drowan yana da fadi, kamar yadda kika fada haka na yi, sai tace masa : ka shiga kai da kanka ka duba ka gani bazata isheka ba, zata maka matsi, sai yace mata : A’A ai wannan zata iya daukan mutum hudu ma… sannan sai ya shiga cikin hawa na 5 saboda ya goda ya gani ko tayi matsi ko batayi ba. Shigarsa keda wuya kawai sai wannan mata ta kulle shi a ciki krip ta dannan kwado. To Bayan wannan mata ta kulle kafinta a cikin hawa na 5 na wannan drowa, sai ta kwashe wadannan riguna masu tsada na wadannan shuwagabanni dattawan gari. Sannan sai ta dauki wannan takarda da mai girma gwamna ya rubata, na kubutar da wannan saurayi (masoyinta) da aka kulle agidana yari ( prison ) kuma atake batareda bata lokaci ba ta fita ta nufi gidan mai girma gwamna, ta shiga ofishinsa ta samu sakatarensa ta bashi wannan takarda. Da sakatare ya karbi takarda ya karanta ya fahimata, batreda wani bincike ko bata lokaci ba atake ya bada umurni aka bude wannan saurayi aka fito da shi daga gidan yari. Sannan bayan wannan saurayi ya fito, sai matar ta bashi labarin yadda ta yi ta kubutar dashi da gidan yarin, sai saurayin yace mata to yanzu me yakamata muyi ? sai tace masa : Ai fita zamuyi mu gudu ma bar garin nan kawai, saboda wannan danyen Aiki da muka aikata, zama a wannan gari ba zaiyu mana. Sannan sai suka shirya kayansu gabadaya, har dawadannan riguna masu tsada, suka daura akan doki suka fice suka bar gari babu wanda ya san abunda ke faru a gari. … To wannan mata a nan nata ya kare, ta kwashi rabonta. Amma su kuma wadannan shuwagabanni da kuma kafinta, basu gushe ba suna cikin wannan drowa har tsawon kwana 3, batarda ci ko sha ba, suka samu kansu cikin matsi da kunci, saboda kwana 3 basuyi fitsariba. To (da tura ta kai bango … ruwa kuma ya karewa dan kada) sai kafinta ya yi fitsari, fitsarin ya tsiyayo kan mai martaba sarki Da sarki ya matsu abun ya dameshi sai shima yayi fitsari akan wazirinsa, haka shima waziri ya fitsari akan mai girma gwamna, sai shima mai girma gwamna yayi fitsa fitsarin ya koraro kan alkali wanda kuma shine na karshe. Da alkali yaga fisari – kala kala – ya koraro kansa, sai ya daka tsawa yace : kaai !! wannan wani irin rashin mutunci ne ? wani irin kazanta da najasa kuke turomini ne ? shin wannan hali da muke ciki na matsi bai ishemu ba har sai kunyi mana fitsari a nan ? sai mai girma gwamna ya daga muriyarsa yace : ya kai ! alkali ALLAH ya saka maka da alkhairi, . Da alkali yaji wannan muriya, sai cewa mai girma gwamna ne da kanshi a nan. Sannan sai gwamnan ya daga muriyarsa yace". wannan wani irin kazanta ne (najasa) ? To sai wazirima ya daga muriyarsa yace : wannan wani irin kazantane ? sai sarki yaji muriyar waziri yace : ALLAH ya sakawa wazirin sarki da ALKHAIRI. Sannan da sarkin ya gane muriyar waziri sai ya ja baki yayi shiru. Da waziri yaji anfadi haka kuma baisan cewa mai martaba sarki bane, sai yace : wannan abu da wannan matar tayi mana UBANGIJIN ALLAH ya tsine mata albarka, ta tara manyan dattawan garin nan gabadaya a cikin wannan drowa ta kulle saura sarkine kawai ya rage bata kawoshiba, sai gwamnaa da alkali suka cewa waziri : hakane kayi gaskiya. Da mai martaba sarki yaji haka sai daka tsawa yace : (shut up ) kuyi min shiru gabadaya, Ai nine farkon wanda ya fada cikin tarkon wannan la’ananniyar mata. Da kafinta yaji abunda wadannan dattawa suka fada sai yace : To nikuma me nawa a ciki ? wani laifi na yiwa wannan matar da zata yimin haka ? tace mini in kera mata drowa zata biyani DINARY 4, ? gashi yanzu na gama na zo karba kudin Aikina, kawai sai tayi min dabara ta kulleni a cin wannan wuri !! ?. Sannan sai suka cigaba da hira a cikin wannan drowa, suka debewa sarki kewa, suka kawarmasa da kunci da muwa dake taredashi Ana cikin wannan yanayi, sai makwabtan wannan gida – gidan matar – suka zo suka samu gidan babu kowa a ciki, kuma matar bata nan. Sai suka gayawa junansu " shekaranjiya wannan makociyar tamu matar wane tana cikin wannan gida, amma yanzu kuma babu kowa a cikin wannan gida, bamu jin muriyar kowa. Sai suka balla kofofin gidan saboda su tabbatar da gaskiyan al’amarin. Sai sukace : ya kamata mu bude mutabbatar saboda kar mai girma gwamna ko sarki yaji labari ya kullemu, daga baya muyi nadama muce mesa bamu balla kofar mun tabbatarba ? . sannan sai suka balla kofar wannan gida suka shiga suka samu drowa ta katako, kuma suka ji sautin garada a ciki suna nishi saboda tsananin ishruwa da yunwa. Sai mutanen suka soma maganganu a tsakaninsu suna shawara, sukace : shin aljanine a cikin wannan drowa ? sai daya daga cikinsu yace : kawai mutara itatuwa mu kette ashana mu kona wannan drowan. Da Alkali yaji haka sai ya daka masu tsawa yace musu : kaai ! ! kar ku Aikata haka …. Bayan da makwota suka yanke shawarar cewa zasu tara itatuwa su kona wannan drowa da suke tsammani kamar aljanu a ciki,,, atake sai alkali ya musu tsawa yace : kaai ! kar ku aikata haka. Da mutane ( makwota ) sukaji muriyar mutum ‘DAN ADAM yana tsawa a cikin drowa sai sukace : babu shakka wannan aljanine yake kamanta irin muriyar ‘YAN ADAM. Da alkali yaji maganar da suka fada, atake sai ya gyara muriyasa ya karanta wasu ‘A’YOYI daga cikin ALKUR’ANI mai girma saboda ya tabbatar musu cewar ba aljanu bane a cikin drowar, sannan bayan ya gama karatun sai yacemusu : kumatso kusa da wannan drowa da muke ciki, su kuma basu ji tsoro ba sai suka matso. Bayan sun matso sai alkalin yacemusu : nine wane ( ya fadi sunansa ) ku kuma kune su wane da wane ( ya kira sunansu gabadaya ). Kuma ya cigaba da cemusu : a cikin wannan drowa akoi su wane da wane. Da makwotan sukaji haka sai suka tambayi alkalin suka cemasa : wayene ya kawoka wannan warin ? kabamu labari ? sai alkali ya warwaremusu labarin yadda lamarin ya faru daga farko zuwa karshe. To Bayan alkali ya bawa wadannan mutane (makwota) labarin abunda ya faru, sai su kuma suka je suka kawo wani kafintan -daban - ya balla wannan drowa, Farkon wanda aka bude ya fito shine alkali, sannan mai girma gwamna, sai waziri, sannan sarki, kafinta shine a karshe. Kuma kowannensu ya fito da rigar da ke jikinsa – wanda wannan mata bashi - . Bayan sun fito daga cikin wannan drowa sun tsaya da kafafunsu, sai ko wa daga cikinsu ya soma kallon dan uwansa, suka soma yiwa junansu dariya. Sannan - jim kadan - sai suka soma bincike suna neman wannan mata a cikin gidan, amma basu ganta ba, basu ga alamunta ba, ita kuma ta riga da ta kwashe rigunansu – masu tsada – ta yi gaba da su. To Sai kowa daga cikinsu ya aika gida aka kawo masa wata rigar daban ya saka. sai suka fice daga wannan gida aboye saboda kar wani ya gansu, sukabi ta cikn lungu – lungo, sako sako, har suka isa gida. Saboda haka yakamata ka duba kayi nazari sosai kaga irin wannan makici da kadi da wannnan mata shirwa wadannan dattawa shuwagabanni, kar kayi gaggawar aiwatar da hukuncin kisa akan wannan yaro ‘(DANKA) saboda maganar da matarka ta gayamaka. ( waziri na 6 ya ke gayawa sarkin ) Bayan da sarkin yaji wannan labari sai ya huuce, ya kuma sauya ra’ayinsa gameda aiwatar da hukuncin kisa akan (‘DANSA) Bayan haka, washegari sai matar taji labari, cewar sarki ya sauya ra’ayinsa, atake ta shiga ta zugashi tayi ta kuka tace sai ta kashe kanta idan sarki bai karba mata hakkinta ba. To sai ta bawa sarkin labari da ke kunshe da makircin maza, da sarkin yaji labarin sai ya rikide hankalinsa ya tashi, atake sai ya canza ra’ayi, ya bada umurni a kashe wannan yaro. Da waziran suka ji labarin irin matakin da sarkin ya dauka gameda '(DANSA) sai suka turo waziri na 7 yazo ya rarrashi sarkin, kuma ya bashi wani labarin daban gameda makircin mata… haka sukayi tayi har zuwa karshe labarin. TO WANNAN LABARI DA KUKA KARANTA, DAYA NE DAGA CIKIN LABARU FIYE DA 20 DA SUKE KUNSHE DA MAKIRCE - MAKIRCE DA KAIDI NA MATA DA NA MAZA… KAMAR YADDA MUKA SANAR DA KU - A BAYA - CEWA WADANNAN WAZIRAI ADADINSU YAKAI 7, KUMA WANNE DAGA CIKINSU IDAN YA SHIGA WURIN SARKI SAI YA KAWO LABARI FIYE DA 1 .. DAGA BAYA ITAMA MATAR TA SHIGA TA KAWO LABARI FIYE 1.. TO ANAN ZAN TSAYA Yusuf abdullahi A jibaga' ke kawo muku wannam labari This Document is compiled by Shuraihu Usman - 08140419490 YEAR of compilation - 2023; Published to Taskarnovels.com.ng An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 2 of 2