Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 2
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels This Document is compiled by Shuraihu Usman - 08140419490 YEAR of compilation - 2023; Published to Taskarnovels.com.ng 01 KAIDI! Allah shi ne Sarki mafi daukaka daga dukkan sarakuna. Shi ne mafi tsarki daga dukkan abubuwa. Tsira da aminci su tabbata ga Manzonsa kuma Annabinsa, Muhammadu dan Amina (SAW). akwai wani sarki ne da ya kasance yana da masaruta mai giman gaske.. - a takaice dai - wannan sarki babu abunda ya rasa a duniya, sai dai kawai matsalar itace : .. bashida (‘DA) na miji da zai gajesa. To sai wannan abun ya damesa sosai, sai ya yi ta rokon ALLAH.. sai ALLAH ya arzuqtashi da (‘DA) na miji kyakkyawa kamar farin wata. To bayan wannan yaro ya girma , sai mahaifin nasa ya hadasa da malamai masu hikima su koyar dashi. To ana nan sai wata rana daya daga cikin matan wannan sarki ( mahaifin wannan yaro ) ta nemi tayi lalalta da ( 'Dan) sarkin.. sai dan sarkin ya ki amincwa, kuma yace sai ya sanar da mahafinsa ya kasheta. Da wannan mata taji haka sai tayi sauri ta garzaya zuwa wurin sarkin, ta riga yaron zuwa wajen wurin mahafin nasa, tayi ta kuka tana I’hu. Da sarki ya tambayeta me ke faruwa ? sai tacemasa : Ai ‘Danka ne ya so yayi lalata dani, ni kuma sai na ki amincewa, sai yace sai ya kasheni, ni kuma sai na gudu na zo wurinka ka ceceni kuma ka dauka mini fansa. Da sarkin ya ji wannan magana sai yayi fushi sosai, ransa ya baci atake ya tara waziransa ya umurcesu da su kashe wannan yaro (‘Dan nasa).. To sai waziran sukayi shawara a tsakaninsu sukace : yanzu sarki ya samu mu kashe wannan yaro nasa , idan har muka bari aka kashe wannan yaro, to babu shakka sarki zai yi nadama dagabaya, saboda yanzu yana cikin tsananin fushi ne shi yasa ya dauki wannan mataki.kuma Bayan wani dan lokaci Idan sarki ya huce daga fushinsa yayi nadama, to mu zai zarga, zai ce : me yasa muka kyalesa ya dauki wannan mataki ? me yasa bamu bashi shawara ba ? me yasa bamu bullo da wata dabara da zata hana shi kashe wannan yaro ba ?.. To sai wadannan wazirai suka yi shawara a tsakaninsu gameda wannan al-amari, ra’ayinsu ya zo daya, suka amince cewar zasu bullo da wata dabara da zata hana wannan sarki aiwatar da wannan danyen hukunci akan (‘DAN) nasa. Kuma zasu sa sarkin ya canza ra’ayinsa. To sai daya daga cikin waziran ya gabato yace : A yau ni dinnan zan kareku daga sharrin wannan sarki, zan canza masa ra’ayi. Sai wannan wazir ya nufi fadar sarki, ya shiga ya tseya a gabansa ya nemi izinin yin maga, sai yace masa : - ya mai martaba : yanzu – misali - da ace kana da ‘YA’YA 1000, to bai kamata ka yiwa zuciyarka da’a ka kashe daya daga cikinsu ba kawai saboda maganar da matarka tafada akan wannan yaro. Abu daya cikin biyu ne : ko ya zamanto wannan matar taka ta fadi gaskiya, ko kuma kariya da sharri ta masa, watakila wannan makircine ta shiryamasa ! Da sarkin yaji wannan magana daga bakin wazirin sai yacemasa : shin akoi wani labari da ka taba ji – ya iso maka - gameda makircin mata ne ??? To a nan sai wannan waziri ya bawa sarkin wani labari mai ban al-aljabi wanda yake kunshe da makircin mata. Bayan sarkin ya ji wannan labari sai ya huce ya sauya ra’ayinsa gameda kashe wannan (‘DA) nasa. bayan wazirin ya fita daga fadar sarki, sai wannan mata ta ji labarin cewar sarki ya huce ya canza ra'ayinsa gameda kashe wannan yaro, sai ta garzaya ta shiga wurin sarki ta yi ta kuka tana I’hu, ta tayarwa da saki hankali, tacemasa : idan bai daukar mata hakkinta daga wurin dansa ba, to zata kashe kanta, zata kona kanta, kuma zata mutu ta bar hakkin a rataye kan wannan sarki,, kuma sai tace masa : shin baka san halin maza bane ? baka san makircinsu da kadin ba ? da irin zalunci da suke yiwa mata ? To a nan sai wannan mata ta bawa sarkin wani labari da yake kunse da makircin maza da zaluncisu a kan mata, kuma a karshe sai matar tanemi sarkin da ya ya kashe wannan yaro saboda ya tabbatar mata da hakkinta. Da sarkin yaji maganar wannan mata da kuma labarin da ta bashi, sai ya rikide hankalinsa ya tashi ransa yabaci sosai, atake sai ya bada umurnin akashe wannan (‘DA) nasa . To bayan haka, labari ya iso wa waziran sarki cewar sarki ya bada umurnin a kashe wannan yaro. To a nan sai waziri na biyu ya shigo ya tseya a gaban sarki ya rarrashi sarki ya lallabesa ya gayamasa irin abunda dayan wazirn ya fada masa, kuma ya bashi labarin makircin mata. To da sarkin yaji wannan labari sai ya canza ra’ayinasa gameda kashe ‘(DAN) nasa. Washe gari sai matar taji labari, sai ta kara garzayawa zuwa wurin sarki tayi kuka ta maimaita maganra da tayi a baya, ta zuga sarki akan sai ya kashe wannan yaro, kuma ta bashi wani labarin daban gameda makircin maza. Da sarkin yaji maganar wannan mata sai ransa ya baci hankalinsa ya tashi atake ya kara canza ra’ayinsa kuma ya bada umurnin a kashe wannan yaro. To haka aka yi ta yi, idan matar ta fita sai waziri ya shiga ya bawa sarki labarin makircin mata sai sarki ya huce ya canza ra’ayi, washe gari sai matar ma tashiga ta zuga sarki ta bashi labari gameda makircin maza, ta canza masa ra’ayi… haka akayi tayi,, akayi ta zama cikin wannan hali, har sai da wazirai 7 suka shiga wurin sarki suka bashi labarin makirci da kaidi na mata. Kuma kowannensu bayan ya fita, sai itama matar ta shiga ta bada nata labarin gameda makircin maza, ta zuga sarkin.... LABARIN YANA DA YAWAN GASKE, AMMA ZAMU KAWO MUKU CIKEKKEN LABARIN GABADAYA A CIKIN LITTAFIN MU MAI FITOWA, WATO DARE DUBU DA DAYA. WANDA KE KAN HANYAR FITOWA.. yanzu dai ga daya daga cikin makircin mata ku karanta ga labarin da waziri na shida ya baiwa sarki. Yanzu labari dai fara" da waziri na 6 ya shigo sai yacewa sarkin ya mai martaba ! ya kamata ka jinkirta aiwatar da wannan dayen hukunci na kisa akan danka, saboda ita batacciyar hanya kamar hayaqi take, shi kuma gaskiya kamar gida ne wanda rukunanasa (ginshikinsa) a tabbace yake , kuma ita gaskiya tana da haske, haskenta yana kawar da duhu na bata,kuma kasani fa kaidin mata yana da girma sosai, makircinsu yana da yawan gaske, shi yasa ubangijin ALLAH ya fada a cikin littafinsa : ﺇﻥ ﻛﻴﺪ ﻛﻦ ﻋﻈﻴﻢ ( wato kaidin ku yana da girama) .. hakika na taba jin labarin wata mata da ta yi wa wasu dattawa kuma shuwagabanni wata kasa makirci mai girma wanda ba’a taba yin irinsa ba a baya , sai sarkin yace : yaya haka ya kasance ? kabani labarin wannan makircin mana in ji ? sai wazirin yace : ya mai martaba labari ya iso mini cewar : akoi wata mata da ta kasance daya daga cikin ‘ya’yan wani hamshakin attajiri, kuma mijin wannan mata ya kasance mai yawan tafiye tafiye ne, To sai wata rana mijin wannan mata ya yi wata tafiya mai tsawo kamar yadda ya saba, ya dauki lakaci mai tsawo bai dawo ba, To sai wannan mata ta kasance ckin tasananin kewar rashin mijinta, a dalilin haka sai hankalin wannan mata ya karkata zuwa ga daya daga cikin samarin da suke aiki a gidan mijin nata, sai ta kaunace shi ta so shi so mai tsanani… To ana nan,, wata rana sai aka wayi gari wannan saurayi ya shiga cikin gari, ya yi chachar baki da wani mutum sukayi fada suka tayar da tarzoma da hayaniya a tsakaninsu, To sai wannan mutumi ya kai karan saurayin zuwa wajen gwamnan (governor) na wannan gari, atake sai gwamnan ya sa aka kulle wannan sauri a gidan yari, bayan haka sai labari ya iso wa wannan mata, cewar an kulle wannan saurayi - masoyinta -, sai hankalinta ya tashi ta rikide.. To bayan wannan mata ta ji labarin kulle masoyinta, kawai sai tayi kwalliya ta sanya mafi kyawun tufafinta ta nufi gidan gwamna, (governor) da isarta gidan sai ta yi sallama ta shiga ta samu gwamna yana a cikin ofishinsa, sai ta mika masa takarda wanda yake kunshe da bayani cewar wannan saurayi mai kamanni ..kaza.. da aka kulle ( 'Dan Uwanta) ne, kuma wannan mutumi da sukayi hayaniya sukayi fada da wannan saurayi har yasa aka kullesa ba shi bane da gaskiya, kuma mutanene da suke wurin lokacin da aka yi wannan rikici basu bada shaidar gaskiya ba, yanzu gashi an kulle wannan 'Dan Uwan nawa ( saurayin ) a gidan yari a karkashin ikon ka, kuma zaluntarsa aka yi, gashi ni kuma bani da kowa, bani da wanda zai ke lura dani a gida, mijina yayi tafiya, shi yasa nake neman alfarma a wurin mai girma gwamna ya taimaka ya bada umurni a saki wannan ‘Dan Uwan nawa ( wannan shine abunda takardar wannan mata ya ke kunshe da shi ) Da gwamna ya karanta takardan wannan mata kuma ya fahimci abun da ke ciki. Sai ya daga kansa ya kalli wannan mata, kuma yaga tana da matukar kyau, to sai hankalinsa ya karkata zuwa ga wannan mata ya ji yana son ta da lalata, sai yacemata : yanzu ki tashi ki shiga gidana ki zauna ki jirani, zan je in kawo miki ‘DAN Uwanki ba tare da bata lokaci ba, yanzu zaki daukeshi ki tafi da shi.. sai tace masa" ranka ya dade gwamna ! ni fa bani da kowa a garin nan in ba ALLAH ba, kuma ni bakuwa ce bazan iya shiga gidan wani ba, sai mai girma gwamnan yacemata : To bazan sake shi ba har sai kin shiga cikin gida, na biya bukatana da gare ki, sai matar tacemasa : idan kanaso ka biya bukatarka ne, to ya zama dole kai ka zo gidana ka zauna ka huta kayi bacci ka babu wanda zai sani.. To sai mai girma gwamnan ya tambayeta yacemata. gidan naki yana ina ne ? sai tace : gidana yana wuri kaza … (sai tayi masa kwatance ) ta bashi lokaci da zai zo.. daga nan sai ta fita abunta ta bar gwamna cikin tunani, zuciyarsa tana tamasa raye raye, shaidan na tunzurasa. bayan wannan mata ta fita daga ofishin mai girma gwamna, sai ta nufi ofishin shugaban alkalain wannan gari. Bayan ta isa ofishin sai ta shiga ta same shi tace masa : ranka ya dade shugaban alkalai ! . sai alkali yace : NA’AM Ina sauraronki kifadi bukatarki, sai tace : ya mai girma inso ka yi min alfarma ka duba wannan lamari nawa kayi A’dalci ALLAH zai yi maka sakayya.. sai mai girma alkalin yace mata" wanene ya zalunceki ? sai tace : ranka ya dade akoi ‘Dan Uwana da aka kulle, kuma bani da wani a garin nan in ba shi ba, a dalilinsa ne na fito na zo wurinka ka taimaka ka kubutar da shi, saboda mai girma gwamna shine ya kulle shi, kuma wasu mutane ne suka masa shaidar kariya sukace shine azzalumi mai laifi.. saboda haka nazo wurinka ka taimaka ka je wurin mai girma gwamna ka nema mini alfarma saboda a kubutar da ‘Dan Uwana. Da Alkalin ya ji wannan magana sai ya daga ido ya kalli wannan mata, sai shima hankalinsa ya karkata zuwa gareta ya sota da lalata, To sai yacemata : ki shiga cikin gida ki zauna tare da kuyangu zuwa dan wani lokaci, ni kuma zan aika wa maigirma gwamna saboda ya kubutar da ‘Dan Uwanki.. kuma ai da nasan kudin da za’a biya a kubutar da shi da zan biya saboda nima in samu biyan bukatata daga wurinki, saboda gaskiya kyawawan kalamanki sun burgeni sosai.. sai tacemasa : - cikin fushi - ashe duk kanwar ja ce,, idan har ya kasance kai da kanka – al kali - kana aikata haka To ai bazan zargi wani ba idan ya ai kata haka,,, sai alkalin – cikin fushi – yacemata : idan baza ki shiga cikin gidana ba to ki tashi ki kama hanya ki tafi kiyi gaba.. sai tacemasa : A’A ranka ya dade, ai ba haka bane ! idan har kana so ka biya bukatarka ne Ai gidana yakamata ka zo, saboda hakan ya fi kyau ya fi rufin asiri, akan da hakan ya faru a gidanka, saboda a gidanka akoi ‘yan mata kuyangu da masu aiki (hidima) da masu shige da fice, saboda ni mace ce wanda bata saba da irin wannan harka ba (lalata) amma yanzu bukata da matsuwa ta sani cikin harkar.. sai alkalin ya tambayeta inda gidanta yake, sai tacemasa : gidana yana wuri kaza..( ta yi masa kwatance.) Sai ta bashi lokaci da zai zo, kuma lokacin daidai yake da lokacin da ta bawa mai girma gwamna. Daga nan sai ta kama hanya ta fita abunta ta tafi. Bayan wannan mata ta fita daga ofishin alkali, sai ta nufi gidan waziri (minister).. da isarta ta yi sallama ta shiga ofishin mai girma wazirin sarki, bayan ta yi gaisuwa, ba tare da bata lokaci ba ta gabatar da bukatarta ga mai girma waziri, ta bashi labari daga farko zuwa karshe, ta koka masa matsalar da ‘Dan Uwan ta – saurayin - ke ci, kuma ta sanar da shi cewar mai girma gwamna ne ya kulleshi.. To a nan sai shima waziri hankalinsa ya karkata zawa ga wannan mata yaji ta kwanta a ransa ya sota da lalata. Sai yacemata : zamu biya bukatar zuciyarmu daga gereki sannan sai mu kubutar da ‘Dan Uwan ki.. sai tacemasa : idan haka kake to Ai yakamata kazo gidana, saboda hakan yafi mana rufin asiri dani da kai gabadaya, saboda gidanan bashi da nisa daga nan, kuma ka san muna bukatan tsabtataccen wuri mai kyau. Sai ya tambayeta yace mata : A ina gidan naki yake ? tacemasa : A wuri kaza .. - ta yi masa kwatance - sai ta bashi lokaci daidai da lokacin da ta bawa gwamna da alkali. Daga nan sai ta fice abunta daga gidan waziri. To Da wannan mata ta fita daga gidan waziri sai ta nufi gidan mai martaba mai alfarma sarkin wannan gari, bayan ta isa ta sumu shiga fadar mai al farma batare da bata lokaciba, ta gabatar da kokenta zuwa ga mai martaba sarki, ta bashi labarin abunda ya faru daga farko zuwa karshe, kuma ta roki taimako da alfarman a kubutar da ‘Dan Uwanta.. sai sarkin ya tambayeta yacemata : wayene ya kulle ‘Dan uwan naki ? sai tacemasa : mai girma gwamna ne ya kullesa. Da mai alfarma yaji dadin kalaman wannan mata, sai harsashin soyayya ta harba cikin zuciyarsa. Sai ya umurceta da ta shigo cikin fada tare da shi, zai aika wa mai girma gwamna da umurni da a fito ‘Dan Uwan ta da aka kulle. Da wannan ta fahimci abunda sarkin ke so - yanaso yayi lalata daita -, sai tacemasa : ya mai martaba ! wannan Ai abune mai sauki a gareka, saboda ko ina so ko bana so idan sarki ya bukaci abu a wurina Ai wannan abun al faharine agareni. Amma kuma da zaifi kyau ace mai martaba sarki ya zo gidana, saboda hakan zai daukakani idan ya tako da kafafunsa masu al barka ya zo gidana. Sai ta yabe shi da wannan baiti na kasida kamar haka. ya ku Abokanaina shin kun taba gani ko kunji ziyarar mutumin da karamcinsa ya yi yawa a gareni Sai mai martaba sarki yacemata : Ai ba zamu ki bin umurninki ba . sai shima ta bashi lokaci daidai da lokacin da ta bawa mai girma gwamna da al kali da waziri. Kuma ta kwatanta masa inda gidanta yake. To Da ga nan sai wannan mata ta wuce wurin kafinta… RANAR LARABA INSHA ALLAHU , Zan dora daga yarda na tsaya misalin 9 pm02 KAIDI! bayan wannan mata ta kwatanta sarkin inda gidanta yake. Da ga nan sai ta wuce wurin kafinta ta samesa tace masa : inaso ka kera mini drowa (drewer) mai hawa 4 ajere daya bayan daya, kuma ka sa masa wurin makulli da kwado a kowanne bangaer (hawa) daga ciki ta yadda zai yu a kulle, sannan ka gaya mini nawane kudin aikinka in biyaka.. sai kafintan yace : kudin aikna DINARI 4 ne.. amma ranki ya yade da zaki yi mini alfarma ki bani dama in samu ganawa da ke in biya bukata (lalata) maimakon kudin aiki na DINARI 4 da zaki biyani, da haka zai fi min dadi, bazan karbi kudinki ba.. Da matar ta fahimci manufarsa sai tace masa : to idan haka kake so Ai babu matsala, Amma yanzu na canja shawara inaso ka kara girman wannan drowa (drewer) ka yi mai hawa 5 maimakon 4 da na gayamaka da farko, kuma kar ka manta ka sa wurin makulli da kwado a kowanna bangare.. sai kafintan yace mata : an yi anga ranki ya dade. To sai ta yi masa kwatancen inda gidanta yake, ta bashi lokaci da zai kawo mata drowan idan ya gama, kuma lokata bashi daidai yake da lakacin da ta bawa mai girma gwamna da mai martab sarki da alkali da kuma waziri.. To bayan matar ta umurci kafinta da ya kaimata wannan drowa idan ya gama, sai shi kuma kafintan yace mata : ranki ya dade ! Ai kawai ki tseya ki zauna ki jira in gama ki tafi da kayanki, yazunnan zan gama aikin batare da bata lokaci ba, sannan ni kuma daga baya zan zo gidanki hankalin a kwance.. To sai ta zauna ta jirashi har saida ya gama kera drowa mai hawa 5 ta dauka ta tafi dashi gida ta ajiye a cikin daki. Bayan wannan mata ta kawo drowan cikin dakinta, sai ta samo wasu riguna (singlet) guda 4 ta kaisu wajen mai rini, tasa mai rini ya rina mata su kala daban daban har kala 4. Sannan bayan haka sai ta dawo gida ta soma shirya kayan shakatawa da liyafa, kamar, kayan ciye ciye, da na shaye shaye, da kayan marmari, da suransu.. ta shinfide wannan wuri da shinfida – kala kala -, ta saka turaren wuta ta shirya wajen tsap, Da lokaci yayi sai ta yi kolliya ta sanya mafi kyawun tufafin ta, sannan ta zauna tana jira wanda zai zo da farko daga cikin wadannan dattawan baza. Ba a jima ba, sai mai girma Alkali ya bude kofa ya shigo, yariga sauran dattawan isowo. Da wannan mata ta ga alkali ya shigo sai ta mike tseye da kafafunta, ta durkusa ta gaida alkali ta girmamashi, sannan sai ta kama hannunsa ta zaunarda akan shinfida, sannan sai suka zauna suka soma hira, jim kadan sai alkali ya yi yunkurin soma yin lalata da ita, ita kuma sai tace masa : ranka ya dade ! yakamata katube wannan babbar rigan naka da kuma rawaninka, ka saka wannan dan karamin rigan nan yafi dadin sha’ani, sai ta bashi daya daga cikin kananan rigunan (singlet) da ta kai wajen mai rini ya rina, (mai shudin launi).. Kuma daama rigar da alkalin ya saka yazo da ita tana da tsadar gaske, rigar manyan mutane ce, kimarta – kudint – ya kai DINARI 700. Kuma rigar da ta bashi ya saka kimar baiwuce DINARI 5 ba. To bayan wannan mata ta karbi babbar rigar alkali sai ta bashi wannan karamin riga (singlet) da ta rina, kuma ta hada masa da wani dan karamin kyalle tace masa : ka daura wannan kyallen a kanka maimakon wannan babban rawani naka, ni kuma zanje in kawo maka abinci da abun sha, sannan idan ka ci abinci ka gama sai ka biya bukatarka ko ? alkali yace : hakane. To sai ta dauki wannan riga nasa da rawanin ta ajiye a gefe, shikuma sai ya dauki wannan karamin riga (singlet) da kyalle ya saka. To suna cikin wannan yanayi, Jim kadan sai ga wani daga waje yana kwankwasa kofa, sai alkali ya firgita yacewa matar : waye wannan yake kwankosa kofa ? sai tace masa : Ai mijina ne ya dawo. Da alkali yaji haka sai ya kara razana yace : To yanzu me dabara ? ina zan shiga ? sai tace masa : kar ka damu kar ka tsorata ! zan shigar da kai cikin wannan drowan ( drewer). Sai yace mata : kiyi duk abunda kikaga ya dace. To sai ta kama hannunsa ta shigar da shi a cikin wannan drowa ( drewer) ta saka shi a hawa na 1 ( matakin farko - first Floor ) ta kulle da kwado kirip. Sannan sai ta je ta bude kafa sai ga mai girma gwamna ya bayyana a bakin kofa. Da wannan mata daga gwamna na tsayae a bakin kofa sai ta durkusa a gabansa tayi gaisu ta bada girma, sannan sai ta kama hannunsa ta shigo da shi ciki, ta zaunar da shi kan shimfida, sai tace masa -cikin murmushi - : ranka ya dade mai girma gwamna shugabana ! wannan gidan gidankane, kuma shimfidannan nakane, Ni kuma kuyangarka ce, ina daya daga cikin masu maka hidima, kuma yau a nan zaka zauna a wurina ka huta kayanka, saboda haka ka tube wannan babban riga naka, kasa wannan dan karamin riga na bacci (JAN singlet) saboda shine rigan bacci.. Sannan sai ta hada masa da karamin kyalle ta daura masa a kansa, sai ta kwashe kayan nasa ta ajiye a gefe. kuma shima rigar da ya saka ya zo da ita mai tsadace, harma tafi ta alakali tsada, kuma karamar riga da aka bashi ya saka (singlet) bata wuce DINARI 5 ba. To bayan wannan mata ta kwashe kayan mai girma gwamna, sai ta zo ta zauna a kusa da shi, jim kadan sai gwamnan yayi yunkurin miko hannunsa zuwa ga wannan mata, sai ita kuma tace masa : - cikin murmushi - ranka ya dade shugabana ! Ai wannan ranar ranarka ce kai kadai, babu wanda zai yi chudanya da kai a ciki, amma ranka ya dade dan darajarka da kyautatawarka inaso ka rubuta mini takardar kubutar da ‘Dan Uwana daga gidan yari ( prison ) ka bani saboda hankalina ya kwanta. Sai yace mata : wannan ai mai saukine, ki kwantarda hankalinki. Kamar yadda kikeso haka za’ayi. Sannan sai ya dauko takarda ya rubuwa sakatarensa yana mai bashi umurni, a ciki yace : ( A cikin takardar) A lokacinda wannan takardan yake isowa wurinka to kar ka yi wata wata ka saki wane … mai suna kaza… ba tareda jinkiri ko bata lokaciba, kuma kar ka binciki wanda ya kawo wannan tarkada. Sannan sai ya buga tambarinsa (stamp) a cikin wannan takarda ya bawa matar, sai ta karba ta ajiye a wurinta. Bayan haka sai ta zo ta zauna a kusa dashi, shi kuma sai ya yi yunkurin miko hannunsa saboda ya biya bukatarsa, kawai sai aka kwankosa kofa. Sai mai girma gwamna ya firgita hankalinsa ya tashi, ya tambayi matar yace mata : wayene yake kwankosa kofa ? sai tace masa : mijina ne ya dawo. Sai yace mata : to me abun yi ? sai tace : kawai ka shiga wannan drowan (drewer) ni kuma zan yi dabara in mayar dashi waje, sannan sai in zo in budeka. Sai ta shigar da gwamna cikin wannan drowa ta sa shi a hawa na 2 ta kulle da kwado. Kuma wannan abunda ya faru gabadaya – tun shigowar gwamna – alkali yana kulle a cikin drowa ya jin abunda suke yi. Amma saboda tsoron kar asirinsa ya tonu yaji kunya sai yayi shiru kamar kamar macecce. To Bayan wannan mata ta shigar gwamna cikin drowa hawa na 2, sai ta je ta bude kofa, sai ga waziri (minister) na na tseye a bakin kofar, sai ta durkusa ta yi gaisuwa ta bada girma, ta yi masa marhaba da zuwa, ta yi masa hidima, sannan sai tace masa : - cikin murmushi - ranka ya dade yau dinnan ka karramani ka

Chapter 1 of 2