Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 1
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels This Document is compiled by Shuraihu Usman - 08140419490 YEAR of compilation - 2023; Published to Taskarnovels.com.ng MUTUNCI KO SO Cikin hanzari na fito daga dakina, na doshi mahaifiyata, bayan na durkusa na gaisheta nace mata zan tafi wurin aiki, tace yau ba zaka tsaya ka karya ba? nace mata Wallahi na makara ne sauri nake, tace to Allah ya kiyaye hanya. Kai tsaye wurin babur dina na nufa, na tadashi kenan zan fita naji mahaifiyata ta kwalamin kira, na sauko na isa wurinta tace dama na manta jiya Safina ta zo nemanka bata sameka ba, shine ta bayar da wannan tace a baka, ta mikomin wata leda. Saboda saurin da nake, ban ko tsaya duba ledar ba, aljihu na sakata na kara gaba. Koda na isa ofis na tarar aiki ya tarar min saboda haka ban tsaya komai ba aiki kawai na fara. Ban tuna da ban karya ba sai misalin 11:00 sannan na bukaci abinci, bayan naje na siyo abinci naci, sannan fa na tuna da ledar da Safina ta bayar a bani, hannu na saka a aljihuna na dauko ledar na kwanceta, alewa ce na gani tare da katin gayyata, gefe daya kuma wata gajeruwar wasika ce. Kai tsaye wasikar na fara karantawa kamar haka:salam yusuf ya ka ke? nayi ta nemanka a waya, ban samu kuma naje gida ban sameka ba, dama katin daurin aurena ne nake so na baka, kuma kayi hakuri kar ka ga ban sanar da kai da wuri ba, Wallahi daurin aure ba zata yai min, sai na jika.. Hankalina ba karamin tashi yayi ba da na karanta wasikar, zuciyata kasa gasgata abinda idanuwana suka karanta a jikin wasikar ta yi. Katin na dauko na karanta. Sunan Safina na gani baro-baro a matsayin amaryar da za'a daurawa aure, nan da sati, nafi sama da rabin sa'a gangar jikina tana kokowa da hankalina kafin daga bisani su samu yin sulhu a tsakaninsu, kai tsaye wayata na dauko na kira lambarta said dai nayi rashin sa'a wayar a kashe take. Mantawa nayi gaba daya da aikin da ke gabana na shiga karanta wasikar jaki (tunani), ya za'a yi Safina tayi min haka? Me nayi mata? Ashe dama ba sona ne take ba yaudarata ne ta ke? In kuwa haka ne tabbas Safina ta kai makura a yaudara, gefe daya kuma sai na fara ganin wautar kaina, ya aka yi na amince da cewar tana so? Ya aka yi na sakankance cewar ita ce matar da zan aura, ya aka yi na saka tunanin gina tubalin rayuwata da ita a zuciya, lallai na zama sakarai na karshe da na hakikance cewar Safina ba ta da wani a zuciyarta bayan ni. Da wadannan sake-saken na bata sauran lokacin da nake da shi a ofis. Tashina daga ofis kai tsaye gidansu Safina na wuce, na sami yaro na aika yai kiranta, sai ga ta ta fito da fara'arta, dama yusuf kai ne? Shi ne ka tsaya a waje ka ki shigowa, mu shiga ciki mana, tana yin maganar ne ba tare da ta dubi yanayin fuskata ba, lokacin da idanuwanta suka kai kan fuskata sai ta sha jinin jikinta, lokaci guda fuskarta ta juye zuwa damuwa, ta shiga tambayata lafiya? Gaskiya ce ta yimin yawa lallai yarinyar nan 'yar rainin hankali ce ta yaya zata tambayeni lafiya, bayan tafi kowa sanin dalilin shiga yanayin da nake ciki, hasalima ita ce ta sakani ciki, a zahiri kuma sai na ce mata kina so ki ce dani baki san dalilin shigata damuwa ba kenan? Gaskiya Safina kin bani mamaki ban yi zaton zaki iya yimin haka ba. Cikin firgici da rashin sanin laifin da tayi ta jehomin tambaya, me nayi ma yusuf? Haba Safina kar ki mayar dani karamin yaro mana, yanzu don Allah Safina ko kunya baki ji? Ki tunkareni da katin daurin aurenki? haba yusuf meye abin jin kunya?, a ganina ai abin farin ciki ne a gareni, abin farin ciki kuwa duk wani makusanci fada masa ake yi, to meye laifi don na gaya maka, kina so ki ce min dama ba sona kike yi ba yaudarata ne kike yi kenan? Idan kuwa haka ne tabbas kin cika mayaudariya, haba Safina ina kika kai soyayyar da muka shafe shekaru muna yi? Ina kika jingine wannan doguwar alakar da ke tsakaninmu? Wace makoma kika tanadar wa wannan alaka, da kuma ni kaina? A'a yusuf kar ka ce haka, ban yaudareka ba, ni Wallahi ban yi tsammanin Mutuncin da ke tsakaninmu a wajenka ya rikide ya koma soyayya ba, da na san haka da tuni na fatattaki wannan tunani daga ranka, ni Wallahi a matsayin dan uwa, Yayana na daukeka kuma abokin shawarata, ban taba daukarka a matsayin masoyi ba, kuma ni kaina na dauka a hakan ka daukeni, haba yusuf yaushe wani abu wai shi So ya taba shiga tsakaninmu? Idan har kallona ka ke yi a matsayin masoyiya, tabbas kai ne ka yaudari kanka. Ku biyoni don jin ya ya wannan alakar ta ke, shin soyayya ce ko kuwa zanci gaba gobeMUTUNCI KO SO 2 Tun lokacin da na baro gidansu Safina na sami kaina cikin damuwa mutuka, na shiga tunane-tunane, in saka wannan, in kwance wancan, lokaci daya sai kwakwalwata ta shiga tariyo min abubuwan da suka faru shekaru uku da suka wuce. Haduwata da Safina kenan. A makaranta mu ka hadu, ba zan taba manta wata ranar talata ina zaune a barifikeshin bulok (verification block) ina jira malaman da ke yin barifikeshin su fito domin a yi min barifikeshin din. Tun daga nesa idanuwa suka haskomin wata kyakkwar sura, suturce cikin jar atamfa. A zahirin gaskiya ban taba ganin halittar da ta yi kyanta ba, jar atamfar ta yi mutukar fito da kyawun surarta, wankan tarwada ce, siririya sai dai ba sosai ba, mai matsakaicin tsawo ce, tana da dara-daran idanuwa, mamallakiyar doguwar fuska ce, dauke da madaidaicin baki, hade da dogon hanci, a takaice dai ko ita ce ta halicci kanta iyaka kenan, duk na fahimci wannan ne a kallon da nayi mata wanda bai wuce na dakika biyar ba. Ga mamakina sai naga ta tunkaroni, kai tsaye sallama ta fara yi min tare da gaisuwa, daga bisa ta jehomin tambaya, don Allah ina ne barifikeshin bulok? Nan ne, na bata amsa a takaice, za'a yi maki barifikeshin din ne? Na tambayeta, eh! Ta bani amsa, ni kaina shi zan yi, ina jira su fito ne, me zai hana ki zauna mu jirasu, bata musamin ba ta samu wuri kusa dani ta zauna, hala a wane difatimen (depertment) ki ke? Na ci gaba da jan ta da hira, Computer Science, ta amsa min, amma yau kika fara zuwa ko? Me yasa kai min wannan tambayar? A can nake kuma ban taba ganinki ba sai yau, shi yasa na tambayeki, eh haka ne gaskiya yau na fara zuwa, ko ina ma ban sani ba a makarantar nan, ko wurin da zamu dauki lakca ma ban sani ba. Wani farin ciki na ji ya kamani, saboda ganin na samu damar da zan cusa kaina a wurinta. Haka dai muka ci gaba da hira har lokacin da masu barifikeshin suka fito, ta shiga layin mata, ni kuwa na shiga na maza. An riga kare mata da kusan minti biyar sannan a ka karemin, ko da na sauko na sameta tana jirana, difatimen muka nufa, bayan na nuna mata duk wasu wurare da ya kamata ta sani. Washe gari ko da na shiga makaranta na sameta a aji, rakube ita kadai, kasancewar kowa bata sani ba a ajin, sai fa ni da muka hadu jiya, kai tsaye wurinta na nufa, bayan mun gaisa na sami wuri na zauna muka fara hira bayan mun dan taba hira ta bukaci da na rakata a saka mata hannu a difatimental dinta (depertmental). Daga ranar kyakkyawar alaka ta kullu tsakanina da Safina, har ya zama cewa idan har ta shigo makaranta bata ganni ba, ba ta jin dadi, hakan kuwa ya faru ne kasancewar ni na ke taimaka mata wajen karatu, kasancewar na fita ganewa. A bangarena kuwa sai na fara tunanin cewar tauraro na ya haska, ko ba komai abin alfahari ne a gareni a ce ina tare da Safina, zamana da Safina ta tallafawa karatuna mutuka ta gefen kudi, domin kuwa duk wasu kudade da za'a bukata, ita ce take biyamin su, kama daga kudin handi awut (hand out) da sauran abubuwan da ake bukata, kasancewar iyayenta masu hali ne, nawa kuwa talakawa ne, wannan ne ya sani tunanin cewa tuni na samu muhalli a zuciyarta, lokuta da yawa sai nayi yunkurin bijiro mata da soyayyata, sai wani sashe na zuciyata yace min, me zaka wahalar da kanka fada mata kana sonta, bayan ka tabbata ta dade da fada wa cikin tarkon sonka. Ku dai biyoni. MUTUNCI KO SO...3 Lokuta da yawa na sha rubuta mata sakon kar ta kwana a wayata (text) dauke da ajandar soyayyata, amma sai wani sashe na zuciyata ya gargadeni, kul! Kar ka kuskura ka tura mata wannan sako, idan har ka tura wannan sako ko shakka babu sai ta ga wautarka, ai irin wannan sako na masu yakin neman zabe ne, kai da tuni kayi zaben kuma ka lashe. Me zaka yi wa kamfe. Idan zuciyata ta yi min wannan gargadi sai na fasa tura sakon, haka ma duk lokacin da na kirata a waya sai nayi kudurin fayyace mata sirrin zuciyata, amma da zarar na tuno da waccan hudubar da daya sashen zuciyata ke yi min, sai in yi sauri in sauya akalar zancena zuwa wani zance dabam. Akwai lokacin da muna zaune muna hira, na sha alwashin fada mata ko da kuwa zata ga wautar tawa, na ke ce mata dama akwai maganar da na ke so gayamaki . Ina shirin fada mata sai na tuno da wannan hudubar da zuciyata ke yawaita yimin a kanta, sai fasawa nayi, na ce mata ta dai bar maganar, ta yi juyin duniya a kan in sanar da ita, na ki fada mata, karshe da naga ta nuna damuwarta, wata karyar daban na samu na fada mata. Abokanaina da yawa a makaranta sun sha fadamin cewa Safina ba karamin so ta ke yi min ba, su kan bugamin misali da irin kulawar da ta ke yi min, da irin dawainiyar da ta ke yi min, duk lokacin da suka yi min wannan maganar, na kan tuno da wani mawaki wai shi Aminu Dumbulu a cikin wakarsa ta Soyayya Sauda'ï, wani baiti da ya ke cewa "dama kula ne soyayya, kula da ni na san da ka na sona" idan na tuna wannan baitin, na kan tambayi kaina, in ce wace kulawa ce Safina ba ta yi min? Na kan yi murmushi in bai wa kaina amsa da cewar tabbas Safina sonka take. Wace mace ce zata yi min irin kulawar da Safina ke yi min? Ni dai ba kudi gareni ba, balle in ce ko don kudina ta ke kulani, hasalima sai dai ta bani kudin. Abu daya ne na ke dashi wanda nake tunanin zata iya kulani don shi, shine basirar da Allah ya bani, sai dai kuma duk lokacin da zuciya ta kawo min wannan tunanin na kan yi gaggawar fatattakarsa a zuciya, bisa la'akari da nayi cewa matan yanzu babu ruwansu da hazakarka wurin karatu in baka da kudi. A shekaru biyun da maka yi na karatun diploma, gidansu Safina sai da ya koma kamar gidanmu, domin kuwa ba wanda bai sanni ba a gidansu, a duk lokacin da na je gidan bani da sanke, kai tsaye na ke wucewa. Ni ma kuwa babu wanda bai san Safina ba a gidanmu, in takaice muku zance dai zumunci mai karfi ya kullu a tsakin gidanmu da gidansu. Hatta aikin da nake tutiya da shi ita ce Sanadiyar na sameshi. Wata biyar da suka wuce ne, ta kirani ta waya take ce min idan na samu dama in sameta gida akwai maganar da take so mu yi. Haka kuwa aka yi, yamma nayi na sameta gidansu, bayan mun gaisa, ta ke gayamin cewa dama dady ne yace in yima magana ka kawo takardunka ya sama maka aiki, wai wani abokinsa ne yai masa magana cewa ya kawo takardun yaronsa ya samar masa aiki, to shi bai son na fara aiki mijin da zan aura daga baya yace bai son aikin, yafi son idan ina gidan mijina, mijin ya ga damar samar mani aiki ya samar mani, to shine yaga bari ya bada takardunka. Hmm! Kar dai ku kosa, ku kara biyoni, don ku fayyace wa kanku me ya kamata a kira wannan alakar tamu, Mutunci ko kuwa So?MUTUNCI KO SO 3 Kwarai mahaifin Safina yai min kokari wurin samar min aikin nan, tsaye yai tsayin daka har sai da ya ga na samu aikin, hakika kokarin da yai min ba zan taba mantawa da shi ba. Wannan kokari da mahaifin Safina yai min shi yasa ni kara hakikancewa a zuciyata cewa Safina tana mutukar sona a zuciyarta, kuma a shirye take da tayi duk wani abu da zai kara kusanci a tsakaninmu. A duk lokacin da nayi tunanin me yasa ba ma musayar kalaman Soyayya kamar yadda nake gani a fina-finai ko a labaran soyayya, sai wani sashe na zuciyata yace min, ai wannan shiririta ce kurum irinta masu fina- finai da kuma sakarci hadi da rashin kunya...... Shigowar abokina waziri aku cikin dakina shi ya katse tunani daga doguwar tariyar baya da yake. Sallama yaimin, Shiru nayi ba amsa, a sannan ne ya fahimci damuwar da nake ciki, tasa ni a gaba yayi da tambaya, akan sai na fada masa Me ye damuwata? Ganin ya matsa yasa ni fada masa abinda ke tsakanina daSafina ban boye masa komai ba. Ajiyar zuciyarsa ce ta kawar da shirun dakin bayan da na gama bashi labarin, sannan yace hakika abokina kayi babban kuskure, a yanda ka bani labari bana ji akwai wata soyayya a tsakinku da Safina, mutunci ne kawai da kuma shakuwa. Hakika yusuf mutunci da shakuwa babu irin kyautatawar da basa sawa. Mutane da yawa suna fama da kwatankwacin matsalar da ka tsinci kanka ciki, yusuf wai me yasa mutane ire-irenku suke kasa fahimtar menene So? Tsakanin saurayi da budurwa, mene ne kuma Mutunci? Ai soyayya yarjejeniya ce tsakanin zukata biyu da kuma mamallakan zukatan, ta yaya Soyayya zata kasance ba tare da ka tallata hajarka gareta ba, ita kuma ta amince maka? Dakata waziri idan na fahimceka so kake kace dani bata yaudareni ba, kana so kace ban san mene ne so ba kenan?haba kamar baka san mata ba, kawai dai taga ni talaka ne, shi yasa da mai kudi yazo sai tayi watsi dani ta daukeshi, ganin ni ba zan iya wadatata da kyale-kyalen duniya ba, kar kace haka abokina, ka daina gasgata zargin zuciyarka, macen da tayi dawainya da kai kamar yanda ka fadamin, idan har sonka take bana tunanin zata iya barinka ta dau dukiya,in tambayeka mana yusuf? Waye mijin nata? Gaskiya ban san shi ba, amma ga katin gayyatar da ta kawomin ka duba ko ka san shi, na mike tsaye na dauko masa katin ya amsa ya duba, Au! Wai dama itace Safinar da Abubukar zai aura? Ka san mijin nata kenan? Eh unguwarmu daya, in dai Abubakar ne bana ji ya mallaki rabin Dukiyar da ka mallaka Abokina, Abubakar malamin Firamare ne, ko gidan da zai zauna haya ya kamashi. Saboda haka ka daina zarginta kawai dai kai ne baka fahimceta ba. Watakila da kayi saurin sanar da ita kafin haduwarta da Abubakar ta karbi tayinka, amma yanzu kam ka makara, sai ka dau hakuri ka kuma roke Allah da Ya musanya maka da wace tafita. Ban gasgata cewa Safina ta kubucemin ba sai da naji ana shafa Fatiha a wurin daurin aurenta, sannan na tabbatar da cewar Safina tayi min nisa, irin kuma nisan da baza ta tabo dawowa gareni ba. Wannan ne Dalilin da yasani garzayowa Shafin sada Zumunta (facebook) domin tallata muku wannan labari nawa, don neman shawararku. Watakila kuma nayi gamo da wacce zata mayemin Gubin Safinata. Lol toyanzu kanma nasamu gawata can tace zata iya. meye shawararku? This Document is compiled by Shuraihu Usman - 08140419490 YEAR of compilation - 2023; Published to Taskarnovels.com.ng An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 1 of 1