inda har ƙungiya ta taimaka ma marayu da marasa shi na buɗe, inda ni da Ya Ameen muke zuba abunda ya sauwaƙa, muna bi lunguna da saƙuna muna taimakon al'umma, har cen Adamawar ma bamu barta a baya ba.
Su Wazeeri dai an yanke masu hukuncin kisa ta hanyar zama gidan yari har ƙarshen rayuwar su, haka ita ma Maree da ɗan ta'addan ta. Su kuwa su Hajiya Laila da Hajiya Sa'a da Alhaji Yaro, zaman gidan yari na shekara goma goma na cin amana, tare kuma da tarar kuɗi manya.
Zan iya cewa yanzu hankalin mu ya kwanta sosai, tunda Ya Ameen ya ce ba zanyi aiki ba, bam matsa ba, dan ina gida irin nasu, ba abunda zanyi da wani aiki, duk da dai shi aiki security ne dashi.
Ƙungiyar mu mai suna *Needies are all human being* sai gashi yanxu ta karɓu tayi suna, har kwantaragi gwamnati ke bamu, tunda ta san ba ƙwange ba coge, zai kai hannun masu buƙata, sannan wasu ƙungiyoyi masu zaman kansu ma suna tallafawa, kai har ma da turawa, masu yaƙi da fatara da kuma talauci, ba inda bama taɓawa mu, hatta da yara ƴaƴan masu ƙaramin galihu muna sakawa makaranta, tare da ba iyayen su jari, ta yanda zasu tallafa ma ƴaƴan su yayin karatun.
Wani lokaci na kan ɗan leƙa shago na, dayake wani amintaccen yaron Ya Ameen ke kula man dashi, Amman dayake ban cika zama ba, ina yawan zuwa seminer, da kuma taron ƙara ma juna sani, Jaana ma saidai mu kaita wajen Mom, har ta saba da ita ma, tun ban yaye ta ba, har na yaye ta. Zaman ta yafi yawa ma wajen Mom, amman ana kawo ta indai ina gari. Ya Ameen bai damu ba, mutum ne ɗan boko mai aƙidar boko, ya san amfanin nema na, ko domin gaba, bai taɓa nuna man damuwa ba, watarana ma, shi ke zama da kanshi ya koya man abunda ban iya ba.
Zama ne muke na so da ƙaunar juna, tare da mutunta juna, duk inda na shiga sha'awa ta ake, hutu da natsuwa sun ratsa ni.
**************
Ranar Asabar ya kasance ranar hutun ƙarshen mako, aiki ne ya kacame man sosai, dan ma Mom ta sama man ƴar matashiyar yarinya dake taya ni kula da Jaana, ganin irin yanayin da nake ciki, na shigar wani sabon cikin. Yanzu mukayi waya dashi yake sanar mani ya sauka a ƙasar tashi ta haihuwa, in bam manta ba, yau watan Ya Ameen biyu baya ƙasar, wani aiki ya riƙe shi mai muhimmanci, inda suke ta ƙoƙarin dawo da dukkan wasu harkokin su ƙasar tasu ta haihuwa gabaki ɗaya, basu samu nasarar kammala wannan aikin ba sai yanzu.
A gurguje na shiga wanka, dama naci sa'a Aliya mai kula da ita, wanda ba zata wuce shekara sha uku ba, itama na saka ta makaranta ɗaya da Jaana, yanda ko acen zata dinga kula da ita, yarinya ce mai ƙwazo, ban saka ta komai, in banda wasa da Jaana, ita ke ɗauke mata hankali suyi ta wasannin su a lambu ko ɗakin su. Ta shirya ta sosai ta mata kwalliya, sannan na saka mata kaya masu kyau sosai, yau zata haɗu da cucu Abbin ta, kaman yanda take kiran shi.
Shirya kaina nayi cikin wata jar jallabiya ƙirar ta larabawa mai haɗe da wando, rigar iyakar ta guiwa daga gaba, sai daga baya ne har tana jan ƙasa, tana da kyau sosai, gami da babban baƙin ɗakwali. Dan haka dashi nayi amfani na yane kaina, takalma masu tsawo nayi amfani dasu baƙaƙe suma, ƴan kamfanin bineina fesa turare ne naji dirin motar shi, inda Mudi Driver ya ɗauko shi, shi da Bilal, amman sun biya sun ajiye Bilal a gida.
Kafin ma'in fita, Jaana tayo but ta fita da ɗan gudun ta, tana ɗaga hannuwa take faɗi "My Cucu Abbi welcome dear" caraf yayi da ita zuwa sama, sannan a hankali a hankali ya fara juyi da ita sosai, wara hannuwa tayi sosai tana ƙyalƙyala dariya, gashin ta na danyi mata calaber dashi, sannan na saka mata bids yana ta faman reto shima.
Har saida ya gaji ya tsagaita da ita, yana mai sakin nishi tare da ɗan ƙaramin haki, sannan ya rungume ta tsam cikin ƙirjin shi, yana sakin wani irin murmushi mai ƙayatarwa. Luf tayi sosai a ƙirjin nashi, tana sakin ajiyar zuciya.
Daga bakin ƙofa da nake tsaye, saidai na saki murmushi, ina mai relaxing a jikin ƙofar harɗe da hannuwa na, cikin so da ƙauna nake kallon su.
A hankali na shiga takawa zuwa inda suke, ganin hankalin shi ma bai kai kaina ba. Ta baya na rungume su su duka, ina mai cewa "Ban yi fushi ba Habibi na, idanun ka sun kulle kan ɗiyar ka ko? Ka manta da ɗiyar Mom ko?"
Dariya ya saki sosai, yana mai juyowa ya rungume ni tsam ni da Jaana ɗin, "Am really sorry dear, kinsan nayi missing naku ku duka, taya zan manta da hasken zuciya ta?" ɗan ɗagowa nayi ina kallon shi, cikin murmushi da ɗan farfar da ido na lakace mashi hanci, ina mai cewa "Ba wani nan, yanzu dai ka ajiye ta ka huta, muje" na faɗa ina mai nuni da hanya..
Hannu ma ya kamo, har yanzu Jaana na kwance a ƙirjin nashi, abun gwanin ban sha'awa. Bayan yayi wanka ne muka zauna dining table. Wasa yake ma Jaana, yana bata abinci, rabi da kwatan hankalin shi na kanta.
Ɗan ƙwarewa nayi da gangan.. Saurin tasowa yayi zuwa inda nake, yana mai tallafo ni sosai zuwa jikin shi, luf nayi, yana shafa man baya a hankali. Ganin Jaana tana kallon mu, ya sanya na ƙwace kaina daga gareshi, yarinyar ta fara wayau, tana iya fahimtar wani abu.
Saida muka kammala komai ne, sannan muka yi niyyar fita siyayya, daganan zamu je mu gaida Mom.
Ko da muka je cewa tayi Aliya da Jaana ba zasu bimu mu koma ba, tayi hakan ne domin na sake da miji na, mun fahimce ta, shiyasa sai bamu ja ba, muka tattara muka koma gida, bayan mun ajiye mata nata siyayyar, tana ta shi mana Albarka sosai, kaman ta goya ni. Hakan yana yi ma Ya Ameen daɗi, shiyasa yanzu yake bin Mom sau da ƙafa, yanzu har cewa take ya rage wannan shegen kafiya da taurin kan nashi, gami da miakilanci Wai taga amfanin aure na dashi.
Kwana biyun da ya Ameen yayi a gida, ya sangarta ni, hatta da girki wanke wanke da shara hada mopping shi yake yi iyaka dai a fita dani a siyo man shawarma da ice cream.
Haka kuwa akayi yau, fitowar mu kenan daga shagon ice cream, ina daga gaba jingine da mota, yayin da yake fitowa hannun shi ɗauke da ƴar ledar ice cream.
Gaban shi ta sha cikin yanga da kwarkwasa, "Hey Handsome Ameen" ta faɗa, tana mai far-far da idanu. Ɗan kallon ta yayi a fizge, fara ce sosai, saidai ƴar fingila ce bata da jiki sosai kaman bulala, amman da gani hutu ya ratsa ta. Zagaye ta yayi niyyar yi, ta saka hannun ta tana mai ɗan ja mashi hannu haka. A zuciye ya dawo baya yana mai zare farin glass ɗin idanun shi ya kalle ta. Sauke kai ƙasa tayi, saboda kwarjini da yayi, mata, ɗan tsoki yayi, yana mai zagaye ta ya wuce. Duk akan idanun Suhan, ɗan dariya ta saki, bata san yana kallon ta ba, amman ita kanta ta yarda da Ya Ameen ɗin, koda wata ya gani ya ce yana so a yanzu, zata ji kishi, amman ba tare da tayi na hauka ba. Saida ya buɗe mata gaban motar, sannan ya ja motar suka fice daga wajen.
Tsantsar ƙaunar juna cikin zukatan su, shafo ɗan cikin ta yayi cikin ƙauna, yana mai cewa "Janaa Lil sis ya hutu?" murmuahi na saki, ina mai ɗora hannu na saman nashi, ƙwaunar shi ne ke kwarara a zuciya ta zuwa ƙalbi na. Kamo hannun nashi nayi ina mai sakar mashi kiss sosai, tare da rungumi shi, da kwanciya bisa kafaɗar shi, yana mai ƙarama motar tashi gudu zuwa gida....
Riri ta ni yake, haɗi da lallaɓa ni, saboda cikin dake jiki na, yana tausay man, baya mance wahalar da nasha a lokacin na Jaana, tabbas ya sani Allah ne ya jarabce ahi da so na, ahi kansho ya san *BAIFI ƘARFI NA BA* kaman yanda wasu ke faɗa ada. Matar tashi ɗaya ce cikin dubu, duk tunanin wani abu baya yi idan yana tare da ita. Ni kaina ririta abu na nakeyi sosai, ni kaina nasan Ya Ameen miji ne, a koda yaushe zuciyar shi a wanke take fes, koda yaushe baka raba shi da masu neman taimako, kuma daidai ƙarfin shi yana yi masu, gashi nima har na koya zama tare dashi.
Babu abunda yake son ji da gani a yanzu sai ganin matar tashi ta sauka lafiya, dan haka duk wani abu na wahala ya hana ta. Da kanshi yake raka ni har zuwa bayan layi inyi exercise, kowa ya ganmu sai yayi sha'awar mu, masalan da kowa ya san cewa Ya Ameen ɗin matashi ne mai jini a jika.
Hankalin ya Ameen ya kwanta sosai, yayi ƙiba shima ya murje gwanin ban sha'wa, ga wata ƙasumba ya ajiye, dariya nake yi mashi, ya zama wani alhaji cikin lokaci, amanar shi da Bilal har yanzu tana nan, Umme ta sake haihuwa ta haifi wani namijin aka saka mashi Khalil, Afnan ma ta haihu har munje suna an samu *Asiya* Sunan ƙanwar Salim ɗin, haka ma Saudat ta haihu itama. Fanuky namu ya cika da yara fa, gwanin ban sha'awa maslaan idan aka zauna meeting na wata shida shida da akeyi wanda ya Ameen yake jagoranta, dukda ba shine babba ba, saidai ba zance ya fi kowa kirki ba, aman mutum da matashi kaman Ya Ameen samun kaman shi sai an tona.
_Alhamdulillahi, na gode ma Allah daya bani ikon kammala wannan littafi, kuskuren da nake ciki Allah ya yafe mani, Allah kuma ya baku ikon yin amfani da dukkan abubuwa na alkhairi da ƙaruwa dake ciki Ameen._
~Oum-Deedat ce~
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 100 Chapter of 100