Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 2
ashe ta kikkira su babu adadi. Anas ne ya zabura ya tashi da sauri ya ce "bari in sauka kasa in kira ta." Ya na sauka ya kira Mama ya fara yi ma ta bayani. Sharifah ta yi murmushin karfin hali ta ce " dole hankalin Mama fa ya tashi, kun zo gidan fatalwoyi ta ji shiru, ku ce ina gaishe ta kuma zan kawo ma ta ziyara." Sai su dukka suka kwashe da dariya har da Sharifah. Yayin da Samha da Aliyu kowannensu nauyinta ya kama su. Anas dai ya na ta faman yiwa Mama bayanin cewar ga su ga Sharifah da iyalanta mutane ne ba fatalwa ba, ta fayyace musu komai ashe duk rashin fahimta ne ya sa ake yi ma ta kallon fatalwa. Mama ta ji bayanansa banbarakwai zuciyarta ba ta yarda ba. Ta hau shi da fada ta ce "babu irin sigar da shu'umar yarainyar nan bata iya biyowa ba, dan ta yaudare ku, ta halakar da ku. In ga fatalwa da idanuwana har sau biyu. Daya da yamma a gidana daya a asibiti da tsakar dare a sigar gurguwa yanzu ka yi min musu ka ce ta gyaru ta dawo mutum. Ka fadawa Samha da Aliyu ku gaggauta barin gidan nan ko in yi muku baki." Anas ya zabura ya ce "Ah Mama me ya yi zafi haka? Allah Ya baki hakuri bari in kira su mu taho. Menene abin yi mana baki kuma? Tunda ba ki fahimta ba shi kenan ai." Anas ya ji nauyin yadda zai shiga ya fada musu wannan sako na Mama a gaban Sharifah, ga labari ya kwaranyo dadi. Anan ya tsaya ya tuttura musu text massages ta waya ya ce lallai-lallai su taso su tafi, ran Mama ya baci ta ce su taso." Kowannensu ya karanta sai suka hada ido su ka yi shiru, can da aka jima kadan sai Anas ya shigo ya sami waje ya zauna. Sharifah ta duba agogo ta ce "ya kamata ku tafi Mama na kira nima.kuma ina da ganawa da zan yi da Matar gwamna akan wasu harkoki. In sha Allah za mu hadu wataran ma karasa labarin." Daga dukkan alamu ta fahimci abinda Mama ta ce da sakonni da Anas ya turo mu su a waya. Sharifah ta raka su har kofar gida bakin get inda suka ajiye motarsu suka shiga su ka tafi. Kowannensu zuciyarsu cika da mamaki su na ganinsu kamar a mafarki, ga su tare da Sharifah da ake gudun famfalaqi idan an ganta, yau gata ga su har ta yi musu rakiya. Tabbas su na cike da mamaki gami da samun nutsuwa da kwanciyar hankali da Allah Ya sa suka gane ba fatalwa ba ce, sannan kuma dan cikin Samha mutum ne. Gidan Mama aka wuce kai tsaye aka same ta a farfajiyar get ta na ta kai kawo ta kasa zama a waje daya dan fargaba. Ta na ganinsu sai ta ji hankalinta ya kwanta bayan sun gaishe ta, aka dunguma zuwa cikin gida. Bayani suka yi mata tsaf akan tabbacin Sharifah mutum ce ga dalilan abubuwan da suka faru har ake zaton ba mutum ba ce. Wasu dalilan Mama ta aminta wasu ne basu kwanta ma ta ba, ita dai koma menene ayi baya-baya da Sharifah kawai. Samha da Aliyu suka sauke Anas a gidansa, kamar yadda suka dauko shi sannan suka wuce gidansu suma. Samha na shiga gida ta bugawa kawayenta su Nana Ahmad waya ta basu labarin Sharifah cewa mutum ce ba fatalwa ba ce. Ta fada musu dalilan da ya jawo suke tunanin ba mutum ba ce. Su ka tambaye ta ko ta bata labarin abubuwan da suka faru da rayuwarta ya jawo har kamanninta suka canja kuma menene maqasudin shariar ta a kotu? Samha ta tabbatar musu Sharifah ta shirya bata labarin rayuwarta bayan rabuwarsu sai kuma Mama ta kira su ta tubure ta ce su bar gidan. Amma za ta samu ta lallaba Mama ta bar ta su sake haduwa da Sharifah don jin ci gaban labarin. Sai dai ba ta sani ba ko sirri ne tsakaninta da ita, ko ita kadai ta fadawa ko kuma zata so kowa ya ji. Idan sirri ne toh ba za ta fada musu ba amma idan Sharifah ta amince kowa ya ji toh za ta sanar musu. Su Nana suka nemi da ta samo musu lokaci su hadu su dukka su je gidan Sharifah su ba ta hakuri akan gudun ta da suka yi, a lokacin da ta kawo musu ziyara gidajensu. Samha ta tabbatar musu cewa zata fada mata. Aliyu ya kula da matarsa ta dawo yadda take ada, ga hira da girken-girken da aka saba yi masa ana yi yanzu, bayan kwalliya da kalaman soyayya wanda dukka ya rasa su a baya. Sai ya ji dadi sosai kuma sai a lokacin ya sanarwa da 'yan gidansu labarin bayyanar cikin Samha. Dan duk tsawon lokacin nan bai fadawa kowa ba dan ana tunanin fatalwa ce ta yi ajiya. Amma yanzu komai yayi daidai dan haka ya daki kirji ya fada. Jamila Umar Tanko: JUT Haqqin mallaka:Jamila Umar tanko Copyright: Jamila umar tanko Wannan littafi mai suna HIRa DA MATATTU na 2 na kudi ne. 300 ne kacal Zaa biya 0112240731 Gt bank Jamila umar tanko Idan an biya a turo shaidar biya ta wannan lambar: 08061225337 Na gode An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 2 of 2