Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuma ga jaruntaka. Ko katta dari suka taram masa, ba shakka zai watsa su.

Ana kamar gobe Iliya zai tashi, sai ya tafi babban masallacin garin, ya yi addu'a, ya roki Allah ya ba shi sa'a. Ya dauri niyyar lalle zai tafi Birnin Kib ta hanyan nan da ce ba ta biyuwa ba kuwa zai fasa ba. Ya kuma yi alkawari har ya isa Birnin Kib ba zai yi amfani da makami ba, komai tananin wahalar da ta same shi. Ya koma masauki ya yi ta shiri Asuba na yi ya hau dokinsa, ya kama hanya ya yi ta tafiya. Ya yi kwana da kwanaki yana tafiya babu gida kusa balle gari, sai daji. Yana tafiya har ya kai ga wani tsauni wanda aka ba shi labarin yawansa, ya kuwa ga lalle haka ne. Ya dai dubi bisansa, ya kuma dubi tsawonsa, baiga iyakarsa ba. Ya yi ta zaga shi, ko ya ga wani wuri mai sauki yaketare, ya rasa. Sai da ya kwana biyar, sa'annan ya sami wani dan wuri ya sa takobinsa ya gyara, sa'an nan ya haye, ya yi ta tafiya.

Bayan kamar mako biyu yana tafiya, sai ya taras da wani katon kogi da aka ba shi labari. Ya sauka, ya duba wuri mai kyau ya daure dokinsa, ya sari ya yi bukka, ya kwance wa dokinsa sirdi. ya sa kayansa cikin bukka, ya kwanta. Da gari ya waye, ya sami wani katon itace ya sare, ya shiga sassakar jirgi. Ya yi kamar wata guda a dajin, ba abin da ya ke yi sai aikin jirgi. Da ya kare, ya sa dokinsa, da kayansa ciki, ya ketare ya nufi BIRNIN KIB .

Daga kogin, bayan ya sake yin tafiyar kamar kwana ashirin, rannan sai ya karaci wani gari wai shi KANIFU. Tun kafin ya isa bakin garin, ya hangi rundunar 'yan yaki sun yi wa garin zobe, ba mai shiga, ba mai fita. Suna jira mutanen garin ne kawai su galabaita, su da kansu su bude kofar, su kuwa su shiga. In kuwa mayakan nan ba su sami haka ba, to, niyyarsu su karya Kofar da karfi su shiga garin, su ci shi da yaki. Mayakan nan suna da yawa. Komai jaruntakar mutum, idan ya ga yawansu da irin shirinsu, lalle ba zai iya fada musu ba.

Manyan garin kuwa duk sun taru a babban masallacin garin suna ta addu'a, Allah ya saukake musu wannan masifa. An rurrufe kofofin garin duk..

Allah maji roko. Kwaram sai ga Iliya ya tunkaro sansanin mayakan nan ta baya, bisa dokinsa Kwalele. Shi bai san abin da su ke ciki ba. Ya tasam musu zai shige ta cikinsu. Suka kuwa yiwo masa kukan kura, daga mai takobi sai mai mashi, sai mai kulki, sai mai kibiya. Iliya ya tuna da alkawarin da ya dauko cewa ba zai yi fada da makami ba har ya isa Birnin Kib Sai kawai ya zare dantsensa, ya yi wa Kwalele kaimi, ya zabura ya shiga cikinsu, ya ce, "Arna, maza bisa kanku!" Suna bugunsa, yana bugunsu da hannu, suką yi ta dauki-ba-dadi, shi daya tak. Kafin a jima ya watsa su ko. Ya karkashe wadansu, ya yi wa wadansu rauni. Da dai suka ga ba dama, sai sauran suka yi ta kansu, suka gudu. Ba a bar kowa ba sai matattu, da wadanda ba su iya gudu. Sansani ya fashe.

Wannan ita ce ranar farko da Iliya ya fara jarraba karfinsa da jaruntakarsa. Ya wuce zuwa kofar gari, ya tarar duk suna kulle. Sai ya koma da baya, yayi wa Kwalele kaimi, ya zabure shi, ya daka tsalle, sai ga su cikin gari. Ya tafi fadar garin, ya tarar ba kowa, duk suna masallaci wurin addu'a. Bai tsaya ba, sai ya tafi masallacin. Ya tambaye su dalilin taruwarsu a wurin. Liman ya ba shi labarin mayakan nan duka. Iliya ya ce, "To, yau Allah ya amshi addu'arku. Babu sauran mayakan nan, duk na kore su Ku saki jikinku." Jama'a suka dubi Iliya, suna mamakin maganarsa kawai, amma ba su yarda ba.

Da Iliya ya ga alamar ba su yarda da zancensa ba, sai ya ce su aika a leko ta kan ganuwa a gani. Wadansu manya suka ce a jarraba a gani. Nan da nan aka tashi wadansu jarumai suka hau ganuwa suka hanga Ba su ga kowa ba sai matattu da masu rauni kawai kwance hululu. Tun daga can suka fara kururuwar cin nasarar yaki Suka kawo labari wurin Sarki. Gari duk ya kaure da murna, nan da nan suka fara kade-kade da bushe-bushe. Sarki da dukan manyan gari suka taru suna ta kallon Iliya suna mamaki, suna kuma yi masa godiya. Shi kuma ya ba su labarin yadda abin ya faru.

Da dare ya yi, manyan gari duka suka taru suka yi shawara suke ce wa Iliya ya tsaya idan Sarkin garin yamutu, su yi masa Sarauta. Suka kuma tara zinari mudu dubu, da tarin azurfa mai yawa, da sauran kaya masu tsada, suka ba shi. Shi kuwa ya ce ba ya bukatar kome nasu. Abin da ya ke so kawai su nuna masa hanyar Birnin Kib. Da mutanen nan suka ji inda za shi, sai duk suka katse, suka yi ajiyar zuciya, wadansu suka yi salati. Sarkin garin da liman da sauran manyan gari suka taru suka yi ta rarrashin Iliya don ya hakura da zuwa Kib. Don kuwa sun tabbata zai halaka ne. Suka fada masa duk labarin dajin da ke hanyar, wanda rabon da wani mahaluki ya bi, tun wajen shekara hamsin. Ba komai a dajin daga giwaye sai miyagun namun daji, da kuma dodon nan Gogaji, dan fashi. Jarumai fiye da dari sun tafi don su kashe shi, amma ya gagara, ya kashe su.ILYA ƊAN MAI KARFI-04

ILIYA YA GAMU DA GOGAJI

Duk irin wadannan labarai na ban tsoro, ba su firgita iliya ba sai ma suka kara masa karfin tafiya Ya ce, "Ni dai ku nuna mini hanya kawai. Idan na halaka, Allah ya hada mu da alheri a ranar kiyama. In kuma na kubuta, to, Allah ya sa ina da halin dawowa garinku in sake taimakonku fiye da wanda na yi muku a yanzu."

Suka hakura dai suka kyale lliya, suka sa shi a hanyar Birnin Kib, suka yi masa rakiya, suka yi ban kwana ya tafi. Ya yi kwana da kwanaki cikin kungurmin daji, babu kome, daga tsaunuka sai duwatsu, sai kwazazzabai da koramu Wani lokaci ma ruwan sama ya ba shi kashi. A wadansu wuraren ma kamar Allah bai taba sa wata halitta tabi ta wurin ba. Kwanci tashi, ran nan sai Iliya ya shiga dajin da Gogaji ya ke. Yana ta tafiya har ya kai ainihin inda aka ce yana zama.
Tun daga nesa Gogaji ya hangi Iliya tafe. Abin da ya rabu da gani shekara da shekaru Sai ya yi maza ya zaro kulkinsa, ya shiga shiri, yana lashe-lashen baki. Ya nufi wajen Iliya, yana tafe yana kuwwa, hayaki na fita daga bakinsa. Saboda tsananin gaza da kururuwa, har Kwalele ya firgita, ya yi sassarfa, ya durkushe. Iliya ya husata, ya buge shi, sa'an nan ya mike. Gogaji ya taso wa Iliya haikan zai kashe shi. Amma Iliya ya tuna da alkawarinsa, na ba zai yi fada da makami ba. Sai ya Ballo wani itace ya gyara, ya dana a bakansa maimakon kibiya. Ya auni Gogaji da kyau, a kahon zuci, ya sakar masa. Maimakon ya same shi a kirji, sai ya same shi cikin kunnen hagu, ya bulle ta kunnen dama. Gogaji ya yi sama ya fado, ya tashi ya yi wata irin kara, ya sake faduwa rim! Sai ka ce giwa ce ta fadi.

Nan da nan Iliya ya sauka ya kukunce Gogaji, ya daure shi da asalwayin dokinsa, ya kada shi gaba suka nufi wurin kwanansa, watau wurin da 'ya'yansa su ke.

Suna tafiya, har suka ketare wani kwazazzabo, suka isa wata korama mai kurmi, a tsakanin duwatsu, Wurin kuwa wani katon lambu-lambu ne, an shafe tsakiyarsa da duwatsu kamar sumunti. An kakkafa wadansu manyan karafa kamar azaru, an yi babban daki.
Da 'ya'yan Gogaji suka hango su Iliya tafe, tun daga nesa suka fara murna suna tsalle, suna cewa, "Alo, ga baba can tafe, ya kawo mana nama. Ashe yau muna da shagali Wannan ya ce ni ke da kai, wannan ya ce shi ke da ido. Sai Malele, wadda ta iya shirin nan ta ce musu, "Kai sakarkaru, ku duba sosai, yau ubammu ne aka kamo, ba shi ne ya kamo ba." Sai suka yi kuri da ido, suna jiran su Iliya su iso. Tun daga nesa Gogaji ya ce wa 'ya'yansa kada su sake su taɓa Iliya. Amma duk da haka sai da Malele ta ciro daya daga cikin azaruna nan na karfe, ta kwada wa Iliya a kai. Iliya ko dubanta bai yi ba. Ta sake dagawa za ta kara, sai Iliya ya husata, ya sa hannu ya fizgo ta, ya jefa ta sama, ta fado, ta ragwargwaje. Gogaji ya ce, "Ai na fada muku. Ga irinta nan !" Ya ce wa 'ya'yan su kawo birgamin zinariya dari, da birgamin azurfa metan, da na lu'ulu'u hamsin, su ba illiya, don ya sake shi. Iliya ya ce, "Bari kayanka, ba ni son ko anini. Bukatata in tafi da kai Birnin Kib." Ya tura keyar Gogaji, suka kama hanyar Birnin Kib. Ya bar 'ya'yan Gogaji suna ta kuka.

Ana nan kwance tashi, suna tafiya, har rannan suka kai Birnin Kib. Iliya bai nufi ko ina ba, sai ya tafi masallacin garin. Ya daure dokinsa, ya kuma daure Gogaji, ya ce masa kada ya sake ya ce zai gudu. Gogaji ya ce wane shi da zai iya gudu. Nan da nan Iliya ya tafi fada, ya aika a fada wa WALDIMA, Sarkin garin cewa, ga shi ya sauka. Ya fito daga Kanifo ne, ya biyo kuwa ta hanyan nan da ba ta biyuwa. Waldima ya yi mamaki kwarai, har bai yarda da dan sakon ba. Ya sa aka isa da Iliya wurinsa. Ya tambayi lliya garinsu, da labarinsa. Iliya ya fadi duk abin da ya gudana tun daga farko har karshe. Amma duk da haka Waldima bai gaskata shi ba sosai cewa ya biyo ta wannan hanya. Wadansu a nan wurin ma sai suka rika ce wa Iliya, "Karya ka ke yi. Hanyar da manyan barade da dakaru suka kasa bi, sai kai za ka ce ka biyo ta kai kadai !" Daga nan ran Iliya ya baci, ya ce, "Ku tashi mu tafi babban masallaci, zan gwada muku shaida."

Sarki da Sarauniya, da mutanen gari, suka dungum sai masallci. Kowa ya yi arba da Gogaji daure, sai ya yi baya kamar ɓera ya ga kyanwa. Duk wuri ya rude, sai mutane ke ta gudu suna komawa gida. Da Iliya ya ga haka sai ya dakawa mutane tsawa, suka Kara razanafiye da ganin Gogaji, suka rasa inde zasu nufa Duk suka yi dabur dabur. Wadansu suka fadi kwance, wadansu suka shiga cikin kwaruruka suka buya. Waldima shi da kansa ya firgita, ya ce wa Iliya, "Mun yarda, lalle ta wannan hanya ka biyo, don kuwa mun ga shaida ta sosai. Yanzu sai mu tafi gidana ka huta ka ci abinci sa'an nan da marece, mutane za su taru, mu sake zuwa kallon Gogaji. Muna so ka sa ya yi irin gazan nan da ya kan yi wa taron mutane, idan ya tare su." Iya ya ce, "To, yanzu yana jin yunwa, sai a kai masa abinci, da giya, don ya cika cikinsa, ya ji dadin yin gazar." Waldima ya sa akai masa tulunan giya wajen metan, da kabukan abinci masu yawa. Gogaji ya ci ya koshi.

Kafin marece, duk labari ya watsu cikin gari, kowa ya kosa lokaci ya yi, ya zo kallo. Sarki da Sarauniya suka ci ado, suka fito suka iske fada ta cika makil da jama'a, suka wuce gaba jama'a ta bi su, tuu, sai wurin Gogaji, Iliya ya ce, "Kai Gogaji Sarki Waldima yana so ya ji irin gazan nan da ka ke yi wa mutane idan ka tare su a hanya."

Gogaji ya bude ido ya ga mutane jingim. Ya yi dan murmushi, sa'an nan ya kafa bakinsa kasa, ya tattake ya yi wani irin ruri, wanda bai taba yin irinsa ba. Kamar aradu goma suka fadi gaba daya. Kasa dai kamar za ta tsage a lokacin. Mutane don tsananin firgita har suka kasa gudu, suna zato duk inda suka nufa za su hadu da shi ne. Wadansu suke sume a nan, wadansu suka fadi kwance wai suna jiran mutuwa ta zo ta dauke su. Mukarrabai don razane har suna kade Sarki da Sarauniya, ba su sani ba don firgita. Daga nan Iliya ya daka wa Gogaji tsawa don ya yi shiru. Wohoho ILIYA-DAM-MAI-KARFI Tsawar da ya yi harta fi gazar Gogaji ban tsoro. Mutanen da ke da dan sauran motsi sai suka katse sosai suna zato ko Gogaji ne ya taso zai halaka su. Gogaji shi ma kuma can ya firgita ya rasa wajen da zai nufa. Ya fadi gaban Iliya a gigice, yana hurwa, yana jewa, "Na ba ka dukan dukiyar da ke gidana, ni dai kada ka halaka ni Iliya ya ce wa Gogaji "Ba ni son kome naka. Kashe ka zan yi, wannan shi ne sakamakon abin da ka yi wa mutane shekara da shekaru

To, alkawarin da Iliya ya yi ya cika, tun da ya kawo Birnin Kib bai zubad da jini ba. Daga nan ya tafi da Gogaji bayan gari, ya ciro kibiyarsa guda ya dana ya sakam masa a makogwaro. Gogaji ya yi tsalle sama, ya fadi matacce. Iliya ya koma fada, ya fada wa Sarki. Jama'a duk suka yi ta murna. Shi kuma Sarki don ya nuna farin cikinsa ga Iliya, sai ya tara dukan manyan garin da attajirai, ya shirya biki kasaitacce. Bayan Iliya ya huta kwana kadan, sai yayi ban kwana da Sarki, ya ce zaici gaba.

ILIYA YA SAKE SHIGA DUNIYA

CIKIN yawace-yawacen da Iliya ke yi, ran nan sai ya je wani babban gari, wanda ya shahara ga yaki. Garin kuwa Sarauniya ce ke mulkinsa. Yarinya ce Karama, 'yar shekara ashirin. Ga ta kyakkyawar gaske, kuma ga ta jaruma. Ba a dade ba Iliya ya daura aure da ita. Suka zauna kamar wata uku tare cikin jin dadin duniya, da annashuwa. Rannan suna zaune, sai kawai Iliya ya tuna da yake-yake. Nan da nan sai fuskarsa ta sake, ya shiga tunani. Ya ce wa Sarauniya, "Ina so in shiga duniya kadan, in ga irin abin da ta ke ciki. Na dade ban motsa jikina ba." Hankalin Sarauniya ya! tashi. Ta yi rarrashin duniyan nan Iliya ya hakura, yaki. Har ta ce ta ba shi sarautarta. Amma bai yarda ba. Ta fashe da kuka, ta rungume shi, tana ba sa magana. Iliya ya ce, "Da ma kin daina kuka, don tafiya kam ba shakka zan yi ta. Yi fatan Allah ya sa muna da rabon ganawa da juna. In kuma babu, ina fata Allah ya hada fuskokimmu a Darassalamu."

Asuba na yi Iliya ya jefa wa Kwalele sirdi, ya taka ya hau, daga shi sai mashi da takobi, da kulki rataye. Ya mika abinsa cikin duniya, ya yi ta yake-yake. Duk inda ya ji ana hargitsi, sai ya nufi wurin, ya yake shi ya kafa salama, kana ya wuce.

Ashe lokacin da Iliya ya bar Sarauniyan nan ta sami ciki. Bayan watanni kadan ta haifi da namiji. Aka sa masa suna FALALU. Ana nan yaro ya fara girma. Da ganinsa ka ga ubansa. Duk irin halin Iliya, ubansa, Falalu bai bar ko daya ba. Har ran nan dai ya isa misalin mutane, ya zama jarumin gaske, wanda ba kamarsa duk karkarar. Ran nan sai ya tambayi uwarsa ko wane ne ubansa. Ta ce ya mutu, tun ba a haife shi ba.

Tun daga ran nan Falalu ya ce shi ma zai shiga cikin duniya, ya yi ta yaki, har ya mutu kamar ubansa. Abin duniya ya dami uwarsa. Ta yi rarrashi, ta yi rarrashi, ya ce shi dai sai ya gaji ubansa. Da ta ga ba ta iya hana shi, sai ta ce masa, To, idan dai ka tafi wurin yake-yakenka, in ka gamu da wani ana kiransa ILIYA-DAN-MAI KARFI ka roke shi gafara ka wuce, kada ka yi yaki da shi. Ban da shi, ba mai iya samum nasara a kanka." Da jin haka, sai Falalu ya yi shiru lokaci mai tsawo, sa'an nan ya ce, to. Ya yi ban kwana ya tafi.

Falalu ya san uwarsa Sarauniya ce, kuma yana zato lalle ubansa ya kasance Sarki. Saboda haka uwar ta ji tsoron kada ta fada masa ubansa ba Sarki ne ba, wani mayaki ne, kuma talaka, ya yi fushi ya kashe kansa. Ya dai shiga duniya, ya yi ta yake yake. Ko ina kuwa sai nasara ya ke samu, har ya shahara warin, duk kasashen Birnin Kib da na Kanifo suka karni da shi, suna tsoronsa iyaka. Sai ya shiga ko ina cikin kasashen nan ya yi barna, ba mai iya tararsa.

A lokacin Iliya kuma yana can ya nutsa cikin duniya, yana ta karo da mazambata, masu cutar jama'a ba dalili. Shi ba ya zalunci, ba shi kuwa son mai zalunci. Don haka ba shi da abokin gaba sai azzalumi. Wata rana da maraice yana zaune yana shan iska, sai Birnin Kib ya fado masa a rai. Ya tuna Waldima Sarkin Kib, da irin hargitsin da ya sha da Gogaji dan fashi. Sai ya ce a ransa, "Lalle na dade rabona da wajejen nan ya kamata in je in ga irin halin da su ke ciki." Gari na wayewa ya shiga damaru, ya rike takobi da mashi da kulki, ya sakam ma Kwalele linzami, ya nufi Birnin Kib.ILYA ƊAN MAI KARFI-05

DINAR SARKI WALDIMA

A Ranar da Iliya ya isa garin, ya tarar Sarki ya yi kiran dina. Ya tara Sarakunan kasar, da 'ya'yan Sarki, da malamai, da attajirai, da jarumai wadanda suka yi wata bajinta. Ko wadanne an shirya musu rankin wurin zamansu daban. Kowa ya shiga kayan ado masu tsada. Sarki da Sarauniya kuma suna zaune bisa kujera a gefe guda, sai barori ke raba abinci iri iri.

Da zuwan Iliya bai jira an yi masa iso ba, sai ya fada cikin dakin dina. Bai zame ko ina ba sai wurin Sarki, ya dan sunkuyar da kansa kadan, kana ya zauna gab da shi. Waldima bai gane shi ba. Ya dube sh kawai a maras hankali, ya ce, "Na yi murna da ka sami dama ka zo wurin wannan biki da na shirya, don manyan mutane, da jarumai, da attajirai. Zan sa a ba ka daga can gefe guda. Za ka ci, ka sha kyauta, ko da ya ke ba ka daya daga cikin irin mutanen da aka shirya dinar dominsu. Amma kuma kai daga ina ka ke? Mutumin wane gari ne? A halin wace zuriya ce kai?"

Jin haka sai Iliya ya yi fushi. Ya dai tabbata babu jarumi kamarsa duk cikin taron. Sa'an nan bai kamata Sarki ya manta da shi ba. Kuma kamarsa a ce a ware shi waje daya, ya kuma ci abinci kyauta! Sai ya ce "Kai Waldima, ni ne zan ci abincinka kyauta ! Ni za a fada wa haka a cikin mata!" Da fa jaruman nan suka ji an ce musu mata, sai duk suka dubi Iliya da fushi. Daya daga cikinsu ya mike ya ce, "Kai, Sarki ka ke fada wa wannan magana? Karya kake yi. Ina ka ga mata a nan, sai fa in kana hauka ne!" Zuciyar Sarki ta harzuka, ya kira jarumai shida, ya ce su fitar da Iliya waje. Suna matsawa, Iliya ya zubar da su matattu duka. Sarki ya sake ce wa jarumai goma su kama shi. Su kuma an take Iliya ya kai su lahira.Wuri fa ya yamutse, kura ta yi sama, sai rikici a keyi. Aka tattaka wadansu suka mutu, wadansu suka gudu. Iliya ya fita abinsa, ya hau dokinsa ya tafi kasuwar garin, ya sayi abinci, ya tara mutanen garin, ya ce su yi ta ci. Wadansu suka ce suna tsoro kada Sarki ya ji labari, ya aiko a kama su. Iliya ya ce musu. "Ku yi ta ci ba kome. Gobe war haka ni ne Sarki Birnin Kib. Zan kuwa nada muku Sarautu." Saboda tsoro, tilas suka ci abincin. Sai da aka dade, sa'an nan suka saki jiki sosai, suka yi ta kwasar gara. Amma shi Iliya bai ci abincin ba, sai ya tafi wani gida da ake yin abincin sayarwa, da shaye-shaye iri iri, masu tsada, ya yi tasa dinar a can.

Abin duniya fa ya shawa Waldima kai. Ga dai gawar mutane hululu am bari a gidansa, ga shi yana jin yunwa bai ci abinci ba, an kashe kuku da su boyi duka. Sai Waldima ya leko, ya tambayi wadansu mutane, ko sun san mutumin nan da ya yi musu wannan aiki. Sai wani mutum ya ce, "Allah ya ba ka nasara, ai Iliya ne, wanda ya taba zuwa nan da gagararren dan fashin nan Gogaji." Sarki ya ce, "Haba, sai haka. Na san ba mai iya yin haka sai shi!" Sa'an nan ya tambaya ko wani zai iya zuwa ya rarraso shi ya zo da shi. Duk fadawa sai kowa ya yi shiru, suna tsoron ransu. Can sai wani ya ce zai tafi. Da ya kusa da Iliya, sai ya lababa ta bayansa har ya kai kusa da shi, ya ce, "Ka zo Sarki na kira." Sai ya juya da gudu. Iliya ya yi shiru yana jiran ya ga wanda aka aiko ya kewayo ya fada masa, amma bai ga kowa ba. Ya waiga bai ga kowa ba, sai ya ce, "Haka na ke zato. Wane yaro, wane sunansa! Da ya tsaya da bai kai labari ba."

Iliya ya aika lwa Waldima cewa yana tafe, amma yasa a yi shela tukuna birni da kauye duk kowa ya taru a kofar fadarsa shi ma zai yi tasa dinar. Masu yin abincin sayarwa su kuma a fada musu duk su yi mai kyau, mai tsada, shi zai saye duk ya ba mutane. Aka fada wa Sarki. Nan da nan da rawar jiki, ya sa aka yi shela, aka sanar da kowa da kowa abin da Iliya ke so ya yi. Har wadanda ba su taba yin abincin sayarwa ba, rannan sun yi. Mutane kuma har wadanda suka dade rabonsu da zuwa birni, sun zo. Filin fada dai ya cika makil. Iliya da kansa ya nuna wa kowa inda zai zauna. Ya rarraba mutane kungiya kungiya, ya sa Sarki daga can gefe, kamar wani almajiri. Sa'an nan ya shiga raba kayan dina. Da aka kare, Iliya ya ce wa Sarki, "To, yanzu fa na huce."

Tun kafin mutane su watse, sai Sarki ya mike ya ce a fada wa mutane, ya yi murna da wannan dina ta Iliya, amma yana so gobe a sake taruwa zai yi wata dinar saboda murnar zuwan wannan bako.

Kashegari mutane suka sake taro fiye da jiya. Sarki ya sa aka shirya dinar da ba a taba yin kamarta ba a kasar. Aka shiryawa kowace kungiya wurin zamanta dabam. Sarki da Saranniya da Iliya kuma a ran nan warin zamansu guda. Aka ci aka sha aka yi ta shagali. Can da Iliya ya ga giya ta buge kowa a taron, har da Sarki, sai ya tashi tsam, ya sulale ya fita, ba wanda ya san inda ya nufa. Don kada ma a gane shi sai ya shiga irin ta alhazai, ya nufi wani kauye kusa da Birnin Kib. Da giya ta saki Sarki, ya duba bai ga Iliya ba, ya sa aka dudduba ba a gan shi ba. Aka dai bi sawu har hanyar dan kauyen nan, amma ba a ga kowa ba sai wani alhaji. Aka komo aka fada wa Sarki. Abin duniya ya rude wa Sarki, ya yi zato ko Iliya bai huce ba ne iliya bai tsaya ko ina ba sai wani gida inda a ke sayar da da wata irin giya mai tsada. Wadda sai Sarakuna ke iya sayenta, Ya ce da mai giyar yana so zai saya. Mai giya ya dube shi ya gan shi tsofai tsofai, ba alamar anini tare da shi, sai ya daka masa tsawa, "Kai, dattijo, taf inda za ka tunda wuri, ai ba irinku na ke sayar wa da giya

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment