Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 7
d'an uwana kai nake so ada gashi yanzu ina jin abubuwa game da kai da dama alokacin da wasu ke neman yi mana sha maki da juna". Yasar shima a gunsa abun haka yake baran shida tun haihuwar Yasira ya ke tsananin sonta matsalar d'aya ce abunda ta aikatawa". Bai san lokacin da ya saki ajiyar zuciya ba kafin ya sake duba Yasirah ta b'ace ba labarinta shi yanzu abun ma tsoro ya fara bashi sai da ya 'yan waige-waige bai ga kowa ba da gudu ya tayar da mota ya bar gun ko da ya isa gida yamma tayi sosai abincin ma kasa ci yayi tunanine kala-kala a zuciyarshi sai da aka kira sallah ya fita sai bayan isha'i ya nufo gida zuciyarsa cike da tsoro da ikon yau yashigo lafiya ba abunda ya gani har kusan tara na dare hakan yasa yayi shirin kwanciya ya kwanta. Cikin wani surkukin daji, babu gida gaba babu gida baya Yasar ya tsinci kansa.Take garin ya juya masa, sama tai jajjur a kasa kuwa wasu irin macizaine nannade da kafaffunsa ya kasa katabus wani nannauyan naushi aka kaiwa kuncinsa a sukwane ya kauce dukan yafi iska. Wata muguwar bahaguwar murya ta ziyarci dodon kunnuwansa, cikin rashin zato. "Yasar ka fita hanyar Yasiraht, domin ita din mallakin shugabanmu ce kuma dokar kungiyarmu babu aure". "Bazan fita ba domin Yasiraht rayuwata ce". Ya fada da kakkausar murya mai amo, take wata irin dariya ta soma karade kunnuwansu.Cikin tashin hankali ya sa hannu ya toshe kunnuwansa, bai auneba aka soma jansa wani wawwakekken rami ya na ji yana gani ya kasa kubuta.Cikin bazata ta bayyana a wajan cikin sakan guda ta warceshi suna hadda ido ta watsa masa harara cikin fushi tace. "Mudin kana sakaci da addu'a kana tare da gaggarin rayuwa". Firgiggit ya tashi, zufa, zazzabi tashin hankali sukai masa rufdugu lokaci guda.Ya daga kai ya kali agogo, karfe biyun dare cike da tsoro ya dire ya dauro alwala ya soma gabatar da nafilfili. Sai goshin asuba ya dakata ya dora da karatun alkur'ani mai girma, ana kiran asuba yai raka'atul fijir yai sallah ya dan kwanta. Washegari ya tashi da karfin zuciya yana jin nishadi a ransa sossai, karfe takwas ya fito cikin shirin fita.A daining sukai clash da Yasiraht suna hada ido wani abu nannauya ya daki zukatansu Yasiraht ta lumshe ido batare da ta sani ba.Cikin zuciyarta tace "Allah ya yi hallita" tai saurin dauke idonta daga kansa tace"morning broth" bai tanka ba ya wuce abinsa.Tai murmushi tana jinjina yadda ya shareta. Yana fita yaje ya gaida su Abba nan Abba yake tambayansa “ya shirye-shiryen biki?". Cike da jin kunya Yasar ya amsa da “Alhamdulilah! Abba mu kai". Abba ya ce“madallah! Allah yayi albarka a kara kula katashi ka tafi aiki kar ka makara". Cikin ladabi ya mik'e ya fita motarsa ya shiga ya nufi office cike da jin ni shad'i. aiki yayi sosai sai da lokacin sallah yayi ya fita yaje masallaci bayan ya idar da sallah ya nufi office kenan suka had'u da Nawas cikin zolaya Nawas ya ce“Ango! Ango!! Kai tun ba'ayi bikin bama naga kasha mai sai wani shek'i kake yi dan Allah miye sirri?". Cikin sigar zolaya da raha yayi maganan. Yasar ya ce“ sirrin da ka gani Amarya na kusa dani ya bazanyi mai k'o ba". Shima cikin sigar wasa ya mayar masa da amsa. Nawas ya ce“maganar gaskiya ya kamata mu tsaya mu tsara biki yau saura sati uku biki amma banga kana wani shiri ba?". Yasar ya ce“shiri ai nakune kune manyan abokai nawa akai min ne kawai". Nawas ya ce“ai baka isa ba dole mumaka 'yan jike-jike sabida ka dawo tuzuru kaga kar kaje ka....“. Yasar ya ce“kai ka sani ni lafiyata lau aha zam- zam nake". Haka suka yita raha daga k'arshe Yasar ya ce“ka bar magan bikin nan inaga sai a weekend sai mu tsara komai in Allah ya kai mu". Nauwas ya ce“ba matsala Angon Yasirah kuma 'Ya'yan Abba". Da haka kowa ya nufi office d'insa basu fita ba sai yamma da'aka tashi daga aiki kowa ya nufi gida. Yasar ya na zuwa gidan Abba ya wuce don haka kurum yaji yana son ganin Amaryansan yana zuwa ya ajiye mota ya shiga gida da salalmansa ba kowa a falo hakan yasa ya wuce d'akinta. K'ofan ya tura ya ganta tana bacci sai murmushi take yi a hankali ya tako har zuwa bakin gadon ya zauna a d'an k'aramin kujeran da ke bakin gadon kalon ta yakeyi cikin so da k'auna bai san lokacin da bakinsa ya fara furta “Yasirah ina tsananin k'aunarki gan-gan jikina mallakin kine a duk lokacin dana kalli kyakyawan fuskanki nakan tsinci kaina cikin nishad'i wansa bazai misaltu ba". A hankali ya sauk'e numfashi tare da lumshe idonsa ya bud'e ya cigaba da cewa“ban san mai yasa baki sona ba kuma kika fad'a wani irin hali wanda nagasa a hak'uri akanki ina matuk'ar kaunanki Yasirah". Hannuta ya kama ya mata kiss ya fita abunsa. Rash Kwanci tashi babu wuya wajan ubangiji biki ya rage saura sati daya,duk kauce kaucan Yasiraht saida ta tsaya ta saurari Yasar suka shirya lamarin bikin.Duk ta rame ta fita hayyacinta, ga yawan barazanar Samar da kungiya da take samu.Ga rama Najwa ta lafaffa mata ganin zata auri wani ta barmata Samar.Sai dai a wani fannin tana taya Samar kishi domin samun shiga wajansa, tare suke yakin.Rana bata karya sai dai uwar diya taji kunya, cikin hukuncin ubangiji aka soma shirye-shiryan biki gadan-gadan babu kama hannun yaro. Ranar Alhamis sukai kamu, a babban dakin taro na Hajiya Rash dake Bauchi.An shirya wajan ya kawatu sossai, yara matasa aka samu sukai shigar yoruba kowace tasha murjani ta tamke kugu tamkar ahlin emeka su goma shabiyu ne suka saka amarya a tsakiya suna tafe suna watsa mata wani hadin turare mai hade da furani sunai mata kirari.Har zuwa tsakiyar dakin taron wanda ya kawatu da shimfidu kilisai da tum-tum tamkar diyar sarauta.Yasiraht sanye take cikin wani rantsatsan swice kalar blue light, an mata head pink kafarta flate shoe shima pink sai mayafi da aka lulluba mata kalar azurfa mai ratsin golden.Fuskarta ta kawatu matuka,sai sheki take tana zama ta dago kai dam! Gabanta ya fadi saboda hango Najwa da Samar cikin tawagar biki tai saurin dauke kanta tana mamaki.Batai auneba yara matasa kimanin mutum sha biyu suma suka sako ango gaba, tamkar yadda akai mata. Dukkansu suma suna sanye da kayan yoruba da izga da murjani nan fa waje ya dauki tafi ni kaina sun burgemu har Rash ta dubeni tace. "Cwt Sanah nima haka zan yi da bikina amma shigar Larabawa". Na saki murmushi nace "ni kau shigar Fulfulde ko Kanuri zan yi". Mukasa dariya muka maida hankali kansu, a hankali Malama Husnah Muhammad Inuwa ta bud'e taro da addu'a ta soma lacture kan biyayyar aure. _"Bisimillahir-rahmanir rahim yake kawata yata yayyata kakkata, da duk wata mace dake wannan waje. Inaso ki bude kunnuwanki ki ssurarreni,shin kina cikin sahun mata nagari? Idan ma bakya ciki saurarreni domin zama abar alfaharin mijinki in kuma kina ciki kikara kaimi. WACECE MACE TAGARI?.Mace tagari itace takan yi kokaarin tazamar wa mijinta aljannarsa ce, batason taga gazawarta a idanunsa,don haka takan yi farin ciki idan taga murmushinsa takan damu matuka in taga fushinsa koda badaita yake ba.Bata jinkiri a wajen abinci, kuma ta iya dafawa batare da almubazzaranci ba, itace amintacciyar abokin shawararsa, mai iya rike masa sirri, bata yarda wani yasani ko waye kuwa, sannan ga taimako._ _Mace a kullum mai sanyaya raice ba mai jiran a sanyaya mata ba, farin cikin maigidanta shi ne nata, komai yabata takan gode, ga fadin yi haquri kamar nunfashinta.Tana fama da baqin ciki amma tayi dariya,tanajin zafin abin da mijin yayi mata amma tayi tunanin yadda zata faranta masa rai._ _Aure sunna ce da Annabawan Allah duk sukayi,ya kamata mugaya matansu suka zauna dasu ???Bai dace ba kowane mutum ya riqa jin matsolinki da mijinki, sai in abin yafi qarfinki.Mace tagari mijinta shine komai, koda bai iya soyayya ba.Bata zama a gabansa ko gefensa saida yardarsa,takan cika da ladabi aduk inda yake, takan nuna masa qauna sosai ta gaskiya ce ko qirqira ce kawai.Idan zai fita qafarsa qafarta, idan taji ya shigo ta tarbo shi cikin fara'a da annushuwa, nan da nan tafesa turare ta shafawa lallenta mai yafito sosai ta danyi kwaskwarima, ta canja murya tareda yawan murmushi da fari.Idan zai fita addu'a, in yadawo godiya da murna dafarin ciki._ _Asma'u bnt Kharijatul Furaziy take cewa 'yarta ranar budar kanta cewa:ke cewa 'yarta ranar budar kanta cewa:"Yanzu fa kinfita daga sheqar da aka kyankkyashe zuwa shimfidar da baki santa ba, da abokin tare da baki san shiba, ki zamar masa qasa sai ya zamar miki sama, kizamar masa shimfida zai zama miki turaku, ki zamar masa baiwa, zai zama miki bawa, kar ki nace wajen neman abubuwa domin karya gujeki, kar kiyi nisa dashi domin karya manta dake, idan ya matso, ki kusance shi, idan yaja jiki, kema ki dan ja da baya, amma ki kiyaye hancinsa da kunnensa da idonsa, karya shinshini komai a wurinki sai qamshi, kar yaji komai sai kyakkyawan abu, kar yaga komai sai wanda zai burge shi.Girki, mahalin kwanciyya girmama danginsa mahaifiyarsa haka abokansa.Tattalin kayansa tare da kilace masa su, kula da damuwarsa insha Allahu zai yi farin ciki dake".Dan uwana maigidanta shawara zan baka, ga amana zamu baka a cikin hannunka.Ci da shanta da tufafi suna hannunku,kyautattamata ka rike amana insha Allah ka zamo mai kauna zatai zaman lafiya_ Bayan an gama aka soma rabon abubuwan kayatarwa, lalle turare littafan addu'o.Mazan suka watse aka soma rawar gada.Yasiraht ta saki ajiyar zuciya ganin an kare lafiya su Najwa basu tada rigimar komai ba. Washegari aka daura aure da safe da yamma akai dinner zuwa dare aka soma haramar sadata da dakinta. Sanah Rash. Tunda aka soma shirye shiryan kai amarya Yasiraht ta rasa nutsuwarta ga wata faduwar gaba da take mai tsananni. Da magarba aka soma yimata mitar taki shiryawa tilas ta soma niyyar shiga wanka lokacin data fito babu kowa dakinta ta lumshe ido tana tuna kalaman Yasmin. "Aunty Yasiraht nima inaso ayi biki a gidanmu,ayi taro musha shagali". Hawaye mai zafi ya zubo mata, tai murmushi tana furta. "Yasmin saina dauki fansa jininki yantacene'. Shigowar kanwar mahaifiyarta yasa tai saurin gogge hawayan ta hau shafa mai. Kafin mintuna goma ta shirya aka wuce sashin mahaifinta da ita. Nasiha sossai mai ratsa jiki yai mata haka ma mahaifiyarta, daga nan aka nufi wajen mota da ita wani gunjin kuka Yasiraht take musamman dataga dagaske nisa zatai da gida. Haka aka sakata a mota zuwa gidanta dake unguwar nassaraea law cost. Yan kai amarya kowa ya watse sai ita da kadai,kamar almara bangon dakinta ya soma darewa suka dunga biyo layi a shirye a shirye harsu ashirin da hudu cif. Kowannansu sanye cikin jajjayan kaya da bakin dankwali, hannunsu rike da kokkouna cike jini suna kallonta.Najwace kan gaba tana murmushin mugunta.Samar na gefe a tsakiyarsu yaci kunu yana dubanta,ya tsuke girar sama da kasa yana muzurai ya dubeta da kakkausar murya. "Yasiraht kin bata mana tsari kin cutar da zukatan yan kungiya, yau bandan inasonki ba saina hallakaki amma zamu dauki fansa kan mijinki kwatankwacin kuntatta mana" Bat suka bacce saboda shigowar Yasar da abokansa, nan akaita barkwanci Nawas yai musu nasiha sukai salama ya ta Yasar ya je musu rakiya yana cike da farin ciki yake hawar matakalan har da d'an gudunsa. Yana isa falo ya tarar tashiga d'akinta kasancewar lokacin k'arfe goma da kusan rabi a hankali ya taka har zuwa d'akin ya saka hannu zai bud'e k'ofa sai yaji kamar ana kwan kwasa gareji ya share zai bud'e d'aki sai yaji yanda ake buga garejin kaman za'a cire a jiyeshi a gefe. Cikin b'acin rai da fushi ya nufi fita ya waye haka mai buga k'ofan don shi ya gama tanadin bazai fita ba ya shigo kenan ya sanya k'afarsa a step na farko a kattt! Wutan gidan gaba d'aya ya d'auke tare da wani irin k'ara mai shiga kunne a hankali uuuuuwu! Irin karannan wanda zakana jinsa cikin yana yin abun tsoro. Duhu sosai yake gani baya iya ganin hannuda bare fararen kayan da ke jikinsa duk sun zama baki. Cikin dauriya ya sauk'a zuwa gate yana fitow haraban gidan yaji bugun k'ofan ya tsananta, sauri ya k'ara abun mamaki yana zuwa aka daina kuma ba mai gadi a gun k'aramin k'ofar ya bud'e ya leka waje amma ba kowa a ciki da sauri ya dawo ya mayar da gate d'in ya rufe. Har lokacin da ya dawo gun d'akin mai gadi baya nan a hankali yasoma tafiya yazo dai-dai zai shiga cikin falo sai hango wani yayi da fararen kaya yana tafiya zai nufi garden kuma wannan yana yin jikin bana mai gadi bane don yayi tsayi da yawa ga shi ko fiskansa baya gani fararen kaya sun b'oye shi. Da sauri ya ce“Baba Mai Gadi yaji bai amsa ba kuma ya ci gaba da tafiya ganin haka ya soma binsa da sauri kafin ya cimmasa har ya b'ace sai da ya duba gurin bai ga kowa ya juyo sai ya sake ganinsa ya nufi cikin gida mai fararen kayan da sauri ya sake binsa. Har yanzu wannan k'aran yana jinsa da sauri ya fara haurawa mata kalan yana bin mai farin kayan ha hau matakala sai yaji an rike masa k'afa cikin sauri yasaka hannu agun sai jin hannu yayi amma ba alamar mutum da sauri ya feta k'afarsa sai yaji an sake sa da gudu ya haura sama ya shiga falo. Yana zuwa hakki yasoma yi ya d'an jin gina da k'ofar gashi da duhu gun ga wayarsa ya manta a motarsa ba kuma toci bare ya haska, sai yaji ihun mai gadi da k'arfi yana kiransa yazo ya tai maka masa. Cikin tsoro ya soma bud'e tagan don ya lek'a ya ga miye amma yaki bud'uwa gashi ihun sai k'ara yawa yake yi, da sauri ya soma sauk'owa don ya tai maka masa bakin Yasar ya kasa furta ko da kalma d'ayabna addu'a. Yana isa bakin gate yaji ba kukan kuma ba mai gad'i a gun yana 'yan dube-dube sai yasake jin ihunsa a cikin gida da sauri ya haura saman ya zo dai-dai k'ofar shiga falonsu ya yi k'aro da wani abu kamar katako amma dogo ne da tsayi sun kuyawa yayi ya fara lalub'e cikin zuciyarshi ya ce“wannan kaman ```Makara``` ne cikin ```Makaran``` ya taba yadi ko da ya d'ago yadine fari kal kaman likkafani ko ince likkafanin ma. Tsoro ne ya fara kamasa ya soma ja dabaya gani yayi ```Makaran``` yana binsa ga yadin likafanin sai k'ara haskawa yake yi a hannusa. Cikin wata irin murya mai firgitarwa ya ji ana cewa“ ```Yasar``` kayi gan-ganci shiga hurumin da bana ka ba kasani yau kwananka ya k'are nine nan zani ```ALAJALINKA".``` ido ya zaro sai Cikin rawan murya Yasar ya ce“ waye kai dan Allah?". Sai da akayi wani dariya mai amo sanan ya ce“nine nan ```ALJALINKA! AJALAINKA!! ALAJALINKA NE!!.``` hahaha!!!!". A ka ci gaba da dariya Yasar na ganin haka bai san lokacin da yayi wani tsalle ya tsallake makaran ya nufi cikin falo da gudu. 'Dakin da ke farkon shiga falon ya shiga yana shiga sai yaga an kawo wuta nan yaga abu a lulub'e da farin kyalle wanda zamu iya kiranshi ```likkafani``` an rufe abu dashi ga jini ya b'ata shi da sauri cikin tsoro ya je ya bud'e wa zai gani Baba mai gadi ne wance matatce a cikin jini da baya yasoma ja jikin tsoro dun ya gama razana. Samar ya kalli Najwa ya ce“ki je gun Yasirah kiyi ta janta ban yarda ki cutar da ita ba kin san ina matuk'ar sonta ni zanje na gama da Yasar". Yana gama fad'in haka ya b'ace bat kamar ba shi a gun. Samar ne ya bayyana a gabansa yana dariya ya ce“kad'an da ga aiki na". Ya nuna kansa da d'an yatsa ya ce“kai ma yanzu zamu gama da kai". Yasar ya soma bashi a hak'uri batare da b'ata lokaci ba Samar ya ce“da ka bar b'ata bakinka ko ka manta irin jan kunne da mukayi ta maka da tsoratarwa kala-kalq amma ka share don haka yau ba sassauci. Wani sanda ya soma nuna Yasar dashi take wata irin iska mai k'arfj tayi sama dashi tasoma jujuya shi a saman d'akin tana buga kanshi da bango take jini ya fara zubowa tamkar an kunna famfo. *33* Samar na b'acewa Najwa ta kece da dariyan mugunta ta ce“daman wannan ranan nake jira tazo ranan d'aukar fansa ta d'aure fiska ta ce“ni Najwa ```Bana yafiya bana manta ranan d'aukar fansa".``` tabbas Samar kayi gan-ganci barina da Yasira a ranan ta yau". Tana gama fad'in haka ta b'ace bata bayyana ko ina ba sai d'akin Yasirah. Amarya Yasirah ganin ango ya fita rakiya nan ta soma rage kayan kyale-kyalen dake jikinta zoben gwal ta cire sannan tashiga bayi ta watsa ruwa tana fitowa ta shafa mai tasaka kayan bacci riga da wando masu d'an kauri bayida shara-shara sosai sabida yanayin huturu da ake ciki. Najwa ne ta bayyana gaban Yasira nan ta kalleta ta ce“kee Yasirah ina mai farin cikin sanar da ke ranan dana ke jira tazo ki sani ina tare da Mijinki Yasar Yanzu haka kuma yana gab da mutuwa". Tana fad'in haka ta b'ace. Yasirah na jin haka itama tayi siddabaru ta b'ace nan ta hango Najwa ta nufi wani jeji cikin hanzari ta bita da kyar ta isota tana zuwa taha bata gun sai can ta hango wani k'aton maciji yana kawo mata hari nan ta gane Najwa ne itama ta rikid'a ta dawo wani k'aton kububuwan maciji nan suka fara fafatawa cikin salon tsafi dankwarewa. Sun d'au kusan awa d'aya da kyar Najwa tayi nasaran cire wannan babban Zoben sihirin da ke hannu Yasirah wanda dashi ne yake sarrafa mayan siddabaru da tsafin da takeyi. Najwa tana saka zoben a hannuta ta kece da dariya ta ce“tababs yau buri na ya cika yau zan b'atar dake a doron k'asa sannan kuma Yasar yana gun Samar ya gama dashi". Nan ta bayyana mata hotonsu Yasirah na ganin haka ta saki k'ara ranta ya b'aci gashi ba halin yin wani yink'uri. Najwa ta nuna Yasirah da wannan zobe tasoma wasu surkulle. Kuma in har wannan surkulen ya kama Yasirah to narkewa zatayi ta k'one q gun ta zama tarihi. Shin masu karatu Samar yana nasaran kashe Yase kuwa?. Shin Najwa na cimma burinta akan Yasirah kuwa?. Don jin wannan amsoshin sai ku biyo mu. Take Najwa ta soma wani irin surkule tana karanta wasu dalamusan tsafi batai aune ba ta nemi Yasiraht ta rasa.Nan ta soma yunkurin nemanta amma babu alamunta hankalinta yai mugun tashi ta bace saboda yadda tsafin ya soma cin jikinta. Yasiraht bata bayyana ko inaba sai gidanta, nan ta riski Yasar kwance shabe-shabe cikin jini.Hankalinta yai mugun tashi nan ta dauki waya tana kuka ta kira mahaifansu a rikice suka karaso gidan.Sai dai tun kafin karasowarsu hankalinta yai mummunan tashi kan ya zatai da gawa maigadi.Ana haka Samar ya bayyana ya dauke gawar ya tafi da ita,tana kallonsa ya fice taji dadi sabida batasan mizata cewa police ba kuma dole ta zamo abar tuhuma. Cikin tashin hankali aka dauki Yasar zuwa asubiti,babuma lokacin tambayarta ya hakan ta faru.Dr yaita fada sabida yaga yamusu matsalarsa, to harzuwa wayewar gari baima farfadoba hankalinta ya tashi sossai duk tayi zuru-zuru. Can Dr ya fito duk ya hada gumi, da sauri Yasiraht ta tare shi"Dr lafiya jikin nasa ya farfado?".Tausayinta ya kamashi yai murmushi, "i'am sorry to say Yasiraht bai farfadoba kawai da bugawar kirjinsa muke gane yana da rai kansa ya bugu sossai". Abu daya ta ayyana Yasar ya rasa tunaninsa wanu giggitacan ihu ta saki ta zube sumammiyya a rikice iyayan sukai kanta bata ko motsi Najwa na gefe tana dariya bata an karaba Samar ya bayyyana ya shaki wuyanta yai sama da ita. Bai dire ko'inaba sai cikin wasu mugayan tsaunuka, take yai nuni da hannunsa wani dutse ya fashe wasu sarkoki suka bayyana ya daureta a jiki tamau tamkar daurin goro.Yai nuni kujera ta bayyana ya hau kai ya dora daya kan daya yana murmushin mugunta. "Baki da mutunci Najwa, zanyi maganinki". "Kayi kuskuren bani amanar Yasiraht walahi saina illatata". Bai tanka ba ya wuce, ya bari ana azabtar da ita.Kwanan Yasiraht uku a gadon asibiti bata magana sai kuka Yasar kuma kwanansa hudu bai farfadoba hankalin kowa ya tashi musamman da likitoci suka bada tabbacin in ya kai kwana biyar komai zai iya faruwa.. ... Take Najwa ta soma wani irin surkule tana karanta wasu dalamusan tsafi batai aune ba ta nemi Yasiraht ta rasa. Nan ta soma yunkurin nemanta amma babu alamunta hankalinta yai mugun tashi ta bace saboda yadda tsafin ya soma cin jikinta. Yasirah na hango a hannu wata Tsohuwa mai shiga ta kamala ko da na kalli k'afar matan kwafato ne orin na doki gashin kanta fari k'al kamar auduga. Cikin ke keb'antacan daji mai cike da ni'ima, take tafiya da yafira a kafad'arta sai da tayi tafiya mai nisa naga ta tsaya a wani gili wanda namun daji irin su Kura, Damisa, Zaki, B'auna su suke mata gadin gidanta. Katangan gida na alfarma da gani kasan ginin aljanu ne saboda bene ne hawa uku komai akwai a ciki. Tsohuwan ne ta kai Yasirah wani d'aki ta kwantar da ita gashi ko motsi bata yi da alamar kamar ba numfashi a tare da ita. Washegari da safe aka aiko a kawo musu abinci, dan 'yar aika tana shigowa ta haura sama shuru taji kamar alaman bakowa haka kurum taji gabanta na fad'uwa, da sallamanta nan tayi karo da Yasar kwance cikin jini ko motsi ba yayi. Cikin tashin hankali ta fita da gudu ta sanar ma driver tare suka shigo ganin halin da Yasar ke ciki ya d'aga waya ya kira Abba ya sanar masa cikin tashin hankali ba tare da b'ata lokaci ba sula iso. Aka dauki Yasar zuwa asubiti, babuma lokacin tambayar ya hakan ta faru.Dr yai ta fada sabida yaga yamusu matsalarsa, to harzuwa wayewar gari baima farfadoba hankalin Hajiya Nafisa ya tashi sossai duk tayi zuru-zuru.Sai lokacin suka soma bincikar ina Yasiraht asibitin suka baro Yasar kwance suka nufi gidan. Samar ne ya bayyana gaban Najwa yana huci bai saurareta ba ya sureta. Bai dire ko'inaba sai cikin wasu mugayan tsaunuka, take yai nuni da hannunsa wani dutse ya fashe wasu sarkoki suka bayyana ya daureta a jiki tamau tamkar daurin goro.Yai nuni kujera ta bayyana ya hau kai ya dora daya kan daya yana murmushin mugunta. "Baki da mutunci Najwa, zanyi maganinki". "Kayi kuskuren bani amanar Yasiraht walahi saina illatata". Bai tanka ba ya wuce, ya bari ana azabtar da ita. Kwanan Yasar hud'ua gadon asibiti bai san inda kansa ba kuma kwanansa hudu bai farfadoba hankalin kowa ya tashi musamman da likitoci suka bada tabbacin in ya kai kwana biyar komai zai iya faruwa.. Take Najwa ta soma wani irin surkule tana karanta wasu dalamusan tsafi batai aune ba ta nemi Yasiraht ta rasa. Nan ta soma yunkurin nemanta amma babu alamunta hankalinta yai mugun tashi ta bace saboda yadda tsafin ya soma cin jikinta. Yasirah na hango a hannu wata Tsohuwa mai shiga ta kamala ko da na kalli k'afar matan kwafato ne orin na doki gashin kanta fari k'al kamar auduga. Cikin ke keb'antacan daji mai cike da ni'ima, take tafiya da yafira a kafad'arta sai da tayi tafiya mai nisa naga ta tsaya a wani gili wanda namun daji irin su Kura, Damisa, Zaki, B'auna su suke mata gadin gidanta. Katangan gida na alfarma da gani kasan ginin aljanu ne saboda bene ne hawa uku komai akwai a ciki. Tsohuwan ne ta kai Yasirah wani d'aki ta kwantar da ita gashi ko motsi bata yi da alamar kamar ba numfashi a tare da ita. Washegari da safe aka aiko a kawo musu abinci, dan 'yar aika tana shigowa ta haura sama shuru taji kamar alaman bakowa haka kurum taji gabanta na fad'uwa, da sallamanta nan tayi karo da Yasar kwance cikin jini ko motsi ba yayi. Cikin tashin hankali ta fita da gudu ta sanar ma driver tare suka shigo ganin halin da Yasar ke ciki ya d'aga waya ya kira Abba ya sanar masa cikin tashin hankali ba tare da b'ata lokaci ba sula iso. Aka dauki Yasar zuwa asubiti, babuma lokacin tambayar ya hakan ta faru.Dr yai ta fada sabida yaga yamusu matsalarsa, to harzuwa wayewar gari baima farfadoba hankalin Hajiya Nafisa ya tashi sossai duk tayi zuru-zuru.Sai lokacin suka soma bincikar ina Yasiraht asibitin suka baro Yasar kwance suka nufi gidan. Samar ne ya bayyana gaban Najwa yana huci bai saurareta ba ya sureta. Bai dire ko'inaba sai cikin wasu mugayan tsaunuka, take yai nuni da hannunsa wani dutse ya fashe wasu sarkoki suka bayyana ya daureta a jiki tamau tamkar daurin goro.Yai nuni kujera ta bayyana ya hau kai ya dora daya kan daya yana murmushin mugunta. "Baki da mutunci Najwa, zanyi maganinki". "Kayi kuskuren bani amanar Yasiraht walahi saina illatata". Bai tanka ba ya wuce, ya bari ana azabtar da ita. Kwanan Yasar hud'ua gadon asibiti bai san inda kansa ba kuma kwanansa hudu bai farfadoba hankalin kowa ya tashi musamman da likitoci suka bada tabbacin in ya kai kwana biyar komai zai iya faruwa.. Sai can dare Hajiya ta soma tambayar ina Yasiraht lamarin daya haifar da kace nace ita ta zauna mahaifinta ya nufi gidan.Tunda suka shiga shi da Nawas gabansu ke faduwa harzuwa cikin falon nan suka

Chapter 4 of 7