son ganinka, tom gani nan Baba
Haka ya tafi, maganar akayi, nan da nan ya amince yace ai dama yanaso yayima Alhaji magana, (lokacin da Abba zaizo saida akaje gidan boka yanada sa'a)
Ai Abba baibar gidan ba, sai da aka saka biki, wata biyu
Tunda akace magana taxama babba, shi kenan yake jinsa wani iri, hakalinsa a tashe, shi yarasa meyasa ya amsa
Tun Zainab na tambayar sa yana mata k'arya, haryazo ya fad'a mata komai, sosai tashiga shock no wonder shiyasa Chuchu tadena zuwa
Nuna masa tayi ba, komai kunsan larabawa da kishi, amma Zainab ko a fuska, saima rarrashinsa tayi ganin yana neman sa damuwa
Biki kuma sai matsowa yake, Maman Futha batasa komai arantaba, tabarwa Allah komai, tunda batada dangi ko d'aya a Nigeria🇳🇬 sai abokanan arziqi, dasuka zama tamkar 'yan uwanta
Sai kuma Aunty Maijidda data zamar mata uwa, sai kuma abokanan aikinta, irinsu Nafeesa Anker, Afreen, Jidda ja'o data zamar mata tamkar k'anwa, batada abin cewa sai San barka
sune ke bata shawara, akan komai, kuma da addu'oi da suke bata, Alhamdulillah yanda tazaci komai sai abin ya xomata da sauqi
Dan Abdul ko d'aya bai ragamata da abinda yake mata ada ba, danginsa, dai aka shanye dashi ta wani b'angaren, amma wajan kulawa da 'yarsa da ita, basu sami galaba
A yau aka d'aura Aure, bayan shagalin da aka d'auki lokaci anayi, Amarya part d'inta daban
Anqawata mata shi, da kayan alatu, amma ko kad'an bai kama qafar koda kayan kitchen d'in Xainab ba, kada kumanta itafa 'yar gidan vice President CE ta qasar
[23/09 7:38 pm] @ut@r h@jiy@💅🏻✍🏻🌹🍇💖🌷: Libiya, kuma yayunta manyane a manyan ma'aikatu, duk wannan badak'alar da ake, ko d'aya bata tab'a bugawa gida ba, akan wai tanada matsala
Ankawo Amarya, kuma kowa a dangi sai murna yake, tunda sunga Hajiyan ta canja hali
Haka kowa ya watse aka barta daga ita sai halinta. Ango tun wajan, k'arfe bakwai ya dawo gida, amma ko d'aya baiyi gigin shiga ba'arin kowacce ba, dan baya cikin hankali sa
Ita Zainab tana can tunanin yana wajan, Amarya, ita kuma Chuchu tana tunanin yana shashin Zainab
Haka kowacce ta kwana da haushin kowacce, saida safe Chuchu ta shigo take cewa uwar gida, kin kanainaye komai, mijin ma ba'a aramin shiba, Zainab cewa tayi banganeba? ai a wajanki ya kwana
Ban kwana wajan ko wacce ba, dole ne? Kinga fice kibawa mutane waje, kinyi nasarar aurata amma bazakiyi nasarara samun jikina ba, insha Allah
Jikina, kinga ya nuna Zainab natane ita kad'ai, yana gama fad'a ya juya ya koma hanyar dayabiyo
Lallai bokanki yabaki sa'a, amma kisani wallahi sai kinzama abin tausayi, dama bason Allah na nuna miki ba, kingaje komai saike d'aya mu xuba ni dake aga mai nasara
Haka taqaraci maganarta ta fice, tana fita ita kuma tayi d'akin sa, kusan fad'a sukayi akan hakan amma yace itama idan tagaji dashi to tafita, ba yadda ta iya haka ta daure
Haka xaman yayi ta tafiya, wataran dad'i wataran mad'aci, mad'acin daga b'angaren dangin Abdul ne wad'anda ayanxu suka juyamata baya, ko Futha dasuke d'auka yanxu sun daina
Dad'in ta dasamun sauqinta mijinta babu abinda ya canja mata, saima k'ara kula da ita
Haka aka d'ebi shekara biyu, har yanzu Chuchu bata samu kan Abdul ba, duk yanda tayi, abin yaci tura
Lokacin FUTHA nada shekara 6 yarinya kamar ita tayi kanta
Muje zuwa dai
By
@ut@r h@jiy@
[11/10, 8:13 PM] +234 809 308 3613: [24/09 9:23 am] @ut@r h@jiy@💅🏻💦✍🏻🌹🍇💦💖: *FUTUHATUL KHAIR*
*®NWA*
*©Zainab Y Hussain*
*Dedicated to FUTHA LUV*
_Page 63-64_
Har a wannan lokacin Allah bai qara bawa Zainab ciki ba, kuma bata saka damuwa arantaba, tasan cewa Allah shine mai komai, yanda yaso haka za'ayi
Tunda yabasu FUTHA ma, yaba su abu mai daraja, saboda 'yarta mai nutsuwa ce, duk da qarancin shekarunta
Yausu Chuchu an qudiri aniyar cewa kota halin qaqa sai tasamu zuciyar Abdul, koda hakan na nufin zatayi yawo tsirara
Dama ai tsirarar kike, tunda da auren ki kike kai, kanki wa miji Wanda bana kiba
Haka tunsafe tafice daga gidan, dama ai ba maganar tambaya, tunda ko kallon inda take bayayi
Iyayen sa kullum cikin fad'a suke masa, akan ya zab'i bare ya bar 'yar uwarsa, shiyasa yanxu kwata kwata basa shiga shirgin ta, itama data fuskanci haka, bata shiga nasu, sai dai duk qarshen sati zataje ta gaidasu
Ada can, yini take agidan, sai dare take tafiya, amma yanzu ko awa biyu bata iyawa
*Birnin gwari* shine garin da aka tafi, aka wuce tsaunuka, da bishiyu, sannan aka haura bukkar *Boka Nargas*, wanda idan ka ganshi, kai kace irin tsofin *gorilla* ne saboda bak'i da munu, gashi gajere
Haka suka tamfatsa cikin bukkar, yasan da zuwan su, tunda wata qawartace tayimasu hanyarsa, kuma shi bucking akeyi, bawai kaxo da ka ba
Suna shiga kafin yace komai, sukaga wani qullin abu cikin bakin wani qaton kifi, sosai suka razana saboda basu tab'a ganin kifi mai girma haka ba
Kud'auka yace, angayan komai, basai kun fad'a ba
wannan kullin, shi zaki d'auka tareda wan nan kan kifin, kisamu k'aton dutse ki d'oramasa, kinga bakinsa zai rufe, idansa zai rife, kunnansa zai rife, bazaiga kowa ba saike
kuma guri da kikasan idan aka ajiye babu mai zuwa balantana ya gani
Abu mafi sauqi, ki samu qasan gadonki, ko kid'ora dutsan, ko kisamu turmi na qarfe ki d'ora, tunda babu mai shiga cikin d'akin ki
Wannan shawarar uwarta mahaifiya, itane tace haka, dariya yai yace kinyi dai dai, Ku zube Ku tafi, wannan kuma layar ki tabbata kinsata gurin d'umi, inda sanyi bazai shi gaba
Ma'anarta, bazai qara kusan tar taba, harsai randa layan sanyi ta ta b'ata
Haka suka ajiye masa kud'i, suka fito
Basu tsaya komai ba, a hanya, gida suka tawo, sunata sheqa dariya irinta arna
*Wannan shine mafari*
Zuwansu gida ba jimawa, suka fara aiwatar da qudirunsu, saida suka gama, tas sannan sukaje cikin kitchen, bayan gas cooker suka ajiye layar, amma saida suka cire one tile na gurin saboda sunsan zai iya d'aukan sanyi
Abdul yana office operation yagama, yana hutawa, yaji kansa yayi wani irin juyaeay, idansa ma haka, bakinsa yafi komai yimasa nauyi
Haka dai ya zauna, jin xaman ba dad'i yasaka shi fara tattara kayansa, zai koma gida
Tundaga gate yakejin wani feeling akan Chuchu, ko kallon part d'in Zainab baiyi ba, ya yi part d'in Chuchu
Yana shiga tana zaune, akan kujera, tana ganin sa tafara washe baki, zuwa yayi wajan ta, hannunta Yakama yace I'm sorry Chuchu for evrthin na zalunceki, na kuma tauyemiki haqqinki amatsayinki na mata waje na, saboda haka kiyiwa mijinki afuwa
Yanxu bashida lokacin kowa sai naki, dana babyna FUTHA
Sosai taji dad'in haka
Duniya sabuwa, ita kuma jin har anyi isha'i bai dawo ba, yasaka takira shi, lokacin yana tare da Chuchu
"Hello" Abban Futha shiru ina katsaya?
Wajan matar sa, mai qaunarsa, mai tattalinsa, ya tsaya, ko kinada abin cewa?
Babu tace, sosai tayi dauriya, saboda dama tayi mafarki akan haka, bata ce komai ba, saima addu'a datake ciga ba dayi
A haka aka d'auki lokaci ko leqe saidai taganshi ya dawo, Futha ce dai, xa'a turo a d'auketa
Iyayen sa basu damu da rashin saba, tunda suma basuda bakin magana, an kulle, kud'i kuwa kamar ruwa haka take maidasu wajan tambayar sa
Amma duk da wannan samun data yi masa, bata sami jikin saba, dan kuwa ko tab'ashi baya son tayi, haka tayi haquri tunda tana samun masu gidan rana
*Bayan shekara biyu*
A haka aka shafe wannan lokacin Abdul bai tab'a koda kallon b'arin Xainab ba, komai nasa kacokan yakoma gun ChuchChuchu
By
@ut@r h@jiy@
[11/10, 8:13 PM] +234 809 308 3613: [24/09 10:51 am] @ut@r h@jiy@💅🏻💦✍🏻🌹🍇💦💖: *FUTUHATUL KHAIR*
*®NWA*
*©Zainab Y Hussain*
*Dedicated to FUTHA Luv*
_Page 65-66_
Iyayen sa a wannan lokacin da ita kanta Meena yayarsa, hankali yafara zuwar musu, tunda ayanzu suna d'an hirar sa, kuma har suna yunqurin zuwa wajan sa
Chuchu yau bata nan, shiyasa 'yar aikin ta, yau take gyara kitchen harta wuce saita dawo taga wata Leda, lah aunty ko mancewa tayi da ita?
D'aukanta tayi, tasa a saman cabinet
Lokacin da Abdul ya shigo gidan lokacin yaji babu abinda yake so irin yajishi gashi ga Zainab
Haka ya shiga wajan ta, sosai taga abin kamar almara, baiyi wata magana da itaba, illa nuna mata yayi ta taimake shi, bata tsaya Jan ajiba, tunda itama tanada buqatar sa
Haka suka farantawa junan su, magana yake son, yimata amma ya kasa, ta lura da hakan shiyasa koda zai fita saidatayi tofi, a ruwa ta bashi qin karb'a yayi saida kyar
Inda suka tafi, badan komai sukaje ba, saidan 'yarsa, suna son itama ya mantata, nan da nan aka yimusu aikin, suka dawo
Haka xaman ya kasance Indai bata nan to Abdul yini yakeyi tareda Zainab, wani abin mamaki kuma yanxu tsakanin sa da FUTHA sai harara da duka, ko yaya tazo kusa dashi
Ita kuma Zainab takasa fad'a a gida, duk da batasaka damuwa ba, amma dai kowa ya ganta saiya CE kin rame sai dai tayi dariya
Matsalar FUTHA da babanta, yasa ta yanke shawarar kaita gidan su Abdul
Haka akayi maidata gidan tayi, anan ma bata tsira ba, saboda har yanzu akwai ragowar asiri jikinsu
Lokacin data fuskanci bata gidan, takanas taje gidansu Abdul dan fad'awa Maman sa, sai ta ganta agidan
Gaisawa sukayi, anan ta yini lokacin da zata tafi batayi shawara da kowa ba, ta d'auketa, haka ta maidata wajanta makaranta ma, tadena zuwa, saiya kasance aikin komai itace lokacin tanada shekara 11, amma tasan me Kishiya take ciki
Itama tsareta akayi, ko gigin zuwa gurin uwar ta batayi
Rabo shine yakai Abdul wajan Zainab, dan yanzu cikine da ita wajan watansa 5 lokacin kuma yafara fitowa, yau ta dawo daga gun aiki tabiya dan ganin FUTHA, amma wayam tambaya tayi, a daqike Hajiya tace ai tana gidan Ku, wajan Chuchu
Bata qarasa ba, ta fita da sauri, sai gidan, FUTHA sunanta ta shiga kira, jin ana karanta yasa tafito da gudu muryan Umman ta tajiyo
A sukwane ta fito, me kikazo yimun a gida?, 'yata nazo d'auka mitsiyaciya Allah ya kusa tona asirin ki, mai raba mata da miji, d'a da uwar sa
Kinsan badan abinda kika yi ba, kebaki isan Abdul ya kalle kiba, Hajiyan sa ma haka, 'yata tafi k'arfinki, ko shine yabaki bai isaba, kiyi d'an kanki
Juyawar da zatayi sai ganin ciki tayi, kut ke Zainab iskanci kika koma? cikin waye wannan?, cikin mai gidan ne, ko shima sai ya nemi izininki? shashasha wahalalliya, haka ta janyo hannun 'yarta suka fice
Bata tsaya wata wata ba, ma'ajiyar ta, ta duba? wayam, Munay kina ina dan uwarki ina kika ajiyen ledar da kika gani?, lah asama na ajiye mantata kika yi ta fad'a baya, ai jibgarta tafata yi, ganin dai ta cuceta kuma tsayawar b'ata lokaci ne, yasaka tayi maza ta ajiye shi inda yake
Abdul koda yadawo, bai qara bi ta kan part d'in Zainab ba, masifa yashata kamar d'anta, hak'uri yafara bata, amma ko kallo bai isheta ba
Safiya nayi, aka tafi wajan boka, magani yabata ta tabata ta tsallake, haka akayi kuwa, tana xuwa ba sanya, haka ta xuba maganin
Lokacin da take zubawa, babu kowa, haka tagama ta koma part d'inta
lokacin ne FUTHA tana ta wasanta da ball suna hira itada Mamanta akan school nasu, wadda tace ta dad'e bata jeba, ball d'in data buga sai tayi hanyar waje, tana zuwa akaci sa'a ta tsalleke maganin da uwarta yakamata ace ta tasalleke, dan cikin jikinta ya zube
Amma akasin haka, yasa ta taka
Haka ta dawo, uwar tana magana amma bakinta yaqi ya bud'e dan tayi magana, tai tai takasa, kuka sukasaka baki d'ayan su
Asibiti ta kaita, akace komai normal, batada zab'in daya wuce addu'a, ita kuma tasaka agaba
Kwanaki na tafiya, FUTHA harta saba, da maganar kurame, daga ita har Mamanta, ciki kuma yanata girma abin sa
Ganin cikin yana nan, tayi tayi amma bai fita ba, sai tayanke shawarar sace FUTHA, shine ta d'auketa tabawa wani mutum akan ya taimaketa yakai wannan yarinyar wani gari nesa da Sokoto
Maqudan kud'i ta bashi, shikuma bai duba k'ank'antar taba, ya sunkuceta sai NIGER, anan ya ajiye ta agarin Duffa
Tafi tafi, harta kai Numeiy, anan ne Kaber ya tsinceta ya kaiwa Matarsa MEIMiE ita
*A dawo labari*
By
@ut@r h@jiy@
[11/10, 8:13 PM] +234 809 308 3613: *FUTUHATUL KHAIR*
*®NWA*
*©Zainab Y Hussain*
*Dedicated to FUTHA LUV*
_page 67-68_
*Cigaban Labari*
Haka itada wannan yaran sukayi ta tafiya, har sukakai inda Mama Anker take sana'ar saida abinci cikin kasuwar sokoto
A nan yar bukkarta take, wajena babba, dan harda kujeru da tables a wajan, saiya kasance kamar wani k'aramin Hotel
Anan take kwana, itada yaranta, ma'ana masu yimata aiki, tanada kirki a wajan bawa mutum hakkinsa indai kana k'arakashinta zakasha masifa, amma kuma batada bak'in ciki ko tauyewa yaro hakkinsa, itane da kanta take sayamusu bankin k'asa, indai antashi tabasu sallama bazata bari mutum ya kashe ba, zata sashi yasaka cikin bankin
Takance, kwad'ayi shike kawo yunwa, kuma babu yunwa cikin Ku
Mama Anker dai kowa yasanta, tanada nasibi cikin harkarta, kuma dai dai batada tsada
A haka suka k'ara sa, cikin kasuwar
Cikin shagon nata suka shiga, yana zuwa kowa yayo Kansu, Kabeeru ina kaje anata nemanka, munzata ka mutu? Shafa jikinsa 'yan uwansa suke
Haka dai suka k'arasa ciki, suka zauna, labarin komai yabasu, da labarin itama yanda akayi suka kasance tare
Sosai kowa wajan ya tausayamata, jin wanda suke tare ya mutu, ko kuma yana nan itad'ince data b'ata bai ganta ba, kuma gashi bata san garin da zasu ba, wata sabuwa dasukaji bata magana
Haka dai aka gama jajantawa, har Mama Anker duk jarabarta saida ta zubar mata da hawaye
Kama hannunta tayi, tace zaki zauna a wajena?, kai ta kad'a, yauwa kinga ba wani abu zakiringa yi ba, gyaran d'akina zakimun, idan kika gyara sai kiyi zaman ki aciki, kinga kasuwa ce nan, ta maza bata mata ba
Kai ta kad'a mata, d'akin suka shiga, katifa ce, da kujera guda biyu, ga carpet da labulaye mai kyau mai kyau
D'aki guda ne, sai band'aki aciki, kan kujera ta zauna, a'a 'yata zauna akan gado, kafin haka ma, tashi kiyi wanka, tunda magari ba tayi sai kiyi sallah
Kici abinci sai, saiki kwanta, kisaki jiki dani, kamar uwa nake wajan ki, indai kinbi yanda kike so, kuma insha Allah muna tare zakiga 'yan uwanki
Ki kama kanki, ki rik'e mutuncinki, nidai ina k'ara fad'a miki nan kasuwa ce, duk da ni maza nake sawa aiki, kuma da inada wani gidan wallahi da can zan kaiki
Amma bandashi, banason munafurci, kuma banason fad'a, ki rik'e darajarki ta d'iya mace
Mama Anker, anyi magana a hankali batare da masifa ba, lallai FUTHA taciri tuta, wajan Mama masifa
Zaman ta wajan Mama Anker, zamane na kwanciyar hankali, ci sha komai tanai mata dai dai gwargwado, suttura kanta saida tayimata kala biyar
Daga dare zuwa Safiya take walwala, amma daga ance mutane sunfara fitowa, zata koma ciki, kallo take zamanyi, tunda solar ce a wajan
Mama bata yarda, da ko ragowar ma aikatanta ne, suna yiwa FUTHA magana ba
Kuma tundaga ranar da FUTHA tazo wajanta, ta harantawa mazan shiga d'akinta
Tafi tafi FUTHA ta d'auki kimanin wata uku, wajanta, batare da ta fuskanci wata matsala daga kowa ba, kuma tana kiyaye maganar mama Anker, shiyasa ba'a tab'a jin kansu ba
Amma sautari zata jiyo masifar ta, daga waje, koda customer, koda yaranta
Ganin hankali da nutsuwa irinta FUTHA, yasaka mama nemomata cigaban makaranta, tunda takardunta acikin jakar hannunta ta zubo, lokacin dazasu tawo, kuma koda accident yazo, jakar na hannunta
Shiyasa dataga takardunta, bataji kyiwar kaita makaranta ba
GGC Sokoto nan ta kaita, alhamdulillah tafara zuwa asa'a, tunda dama tanajin komai, mayarwa ne bata iyawa
~@ut@r h@jiy@~
[11/10, 8:14 PM] +234 809 308 3613: [28/09 7:06 pm] African girl 🇳🇬: *FUTUHATUL KHAIR*
*®NWA*
*©Zainab Y Hussain*
*Dedicated to FUTHA Luv*
Page 69-70
Haka rayuwarta tayi ta tafiya, har takai SS2 lokacin tazama budurwa, wani irin sirrin kyau, takeda shi, bata kula kowa tunda tasan ita d'in ba wata bace, face 'yar aikin maisaida abinci a kasuwa
Mama akullum shinkafa da Miya, sai roman kansa, da wainar shinkafa kwano goma take dafawa, kuma insha Allah kafin dare ta k'are
Yau Mama antambayi lafiyarta, ko d'aga kanta bata iyawa, sai rawar sanyi, ahaka kaberu yazo ya ganta, Asibiti a kasamo mota aka kaita
FUTHA ita ta zauna, ganin har lokacin da mama ke d'ora ke abinci yakusa, basu dawo ba, yasaka tafito da kanta, hijab tasaka har k'asa, tafara aikin had'a murhu, tana gamawa shinkafa bata san kwano nawa ake dafawa ba
Haka tahad'a murhu biyu, shinkafa kwano bakwai bakwai haka ta d'ora, kafin wani lokaci har sunyi, sammuy a hankali itada Musa sukayi parboiled nata, 20 minute suka bata, sannan suka fara kwashewa
Tukunyar bata kama ba, haka suka maida ruwan, taliya, nan ma, mama nadafa kwali d'aya, su kuma suka dafa kwali da rabi, Omar shine mai soya waina , kuma dama anrigada anyi markad'enta, da miyar, shiyasa aikin yayi musu sauk'i, kafin 1pm har sun gama
Wanke wanke, sukai, tunda sauran yaran taredasu aka tafi Asibitin, haka suka gama komai, sannan suka fara saka cokula kan table d'in
Wanka tashiga tayi, doguwan riga tasa, sannan ra zauna kan kujerar da mama ke zama, dayake Musa duk yad'an nuna mata yadda zatayi hakan yasa tafara zubawa mutane masu siya
Lokaci kad'an sai yazama abinci kamar rububinsa ake, wad'an da basa siya, saigasu, daga wainar har shinkafa kafin la'asar sai kwano
Ganin irin yadda abincin yayi saurin k'arewa da wuri sai kawai tak'ara d'ora wata, itama tanayi ta siyar duka
Dayake ansan halin mama da masifa, babu wanda ya tsaya wani maganar banza, amma kowa saiya tafi da santin kyau na FUTHA, ga kuma abincin kowa yaji testing nasa yayi dad'i
Wajan 6 idan kazo wajan bazaka ce, anyi wani abu ba, yanda suka gyara wajan, suka kayi k'alk'al dashi, komai suka mai dashi mmazauninsa
Kud'i tacira yabawa, Musa tace yasiyo sub'o, kai aiba'a lemo, ko ita tace ayi?, kai ta kad'a masa, alamar a'a, tanason gwadawa ko za'a siya, haka aka siyo kwano biyu, suger rabin kwano, sai flavour, da sweetener dasu tiara, komai dai haka ta rubuta masa yaje yasiyo kuwa.
Motar taxi, ita ta ajiye su mama Anker, dakanta take tafiya, kuma kamar ba mara lafiya ba,sab'anin da safe da idan kaganta, bazakace zata k'ara koda second bane
D'akin suka shiga, itada kabeeru, FUTHA da sauri ta miqe ta tareta, kan gado ta ajiye ta, sannan tafara jeramata sannu, amsawa take, ruwan zafi ta kaimata toilet tace Mama dazakiyi wanka zakiji dad'i? Kai ta kad'a alamar eh
Haka ta shiga, tana fitowa ga flask na ruwan zafi da wainar shinkafa a jiye, bata tsaya tambayar Ina aka sami wainar ba, shi tayi ba miya tareda ruwan Lipton, gyatsa tayi, sannan tasha magani ta kashin gid'e
Sallama su kabeeru sukaiwa FUTHA, suma tabasu abincin su, kowa Yakama gaban sa
Wajan k'arfe 4 ta tashi, dayake ta rigada ta had'a komai, k'ulli da zuba kayan k'amshi sune suka rage, haka ta zauna ita d'aya tafara k"ulli a leda, ahaka harta gama, lokacin har anyi assalatu haka dai ta daure tagama
Cool dream, ta Mama wadda take saida qanqara, ita ta bud'e tazuba a k'asa sannan ta zuba wasu cikin cooler, tana gamawa adaren ta wanke komai, bata koma ba saidatayi alwala tana cikin nafeela mama ta fito
Itama alwala tayi, lokacin ana tada iqama, haka suka bi liman, ana idarwa, harzata koma bacci, saitayi tunanin bara tayiwa mama bayani akan abincin jiya, gani tayi tafita, kuma itama bacci takeji sosai, shiyasa ta kyaleta, tace koda safe ta gayamata, haka FUTHA ta koma baccin ta
Mama kuma, d'an kayan tafara had'a wa, kafin safiya
Tunda ta kwanta, bata farka, sai da wani wawan kira da taji Mama tayi mata
Ke, kina ina, alokacin buhari, da shinkafa ke tsada, ke ko garine shima yazama kud'i yanzu, balantana shinkafa, ina aka kaimun shinkafa, kwano goma sha hud'u taliya cartan biyu, nifa gadai markad'ena nagani, wato saboda banda lafiya,kina zatan mutuwa zanyi shine kika had'a baki da wani a cuceni, aka d'ibi shinkafa ta aka siyar, to wallahi afitomin da ita, kuma ki tabbata kin b'acemun da gani
Saidata bari takai aya, sannan ta janyo hannunta, Musa yana wajan shima haka ta kira shi, littafi ta d'akko tanuna mata
Sosai Mama zatayi masifa, Musa yace mama abinda kike tunani wallahi bashi bane, amma ki karanta kafin kici gaba, da yanke hukuncin
D'ai d'ai da d'ai d'ai, tabi tana karantawa, bata gama ba, ta d'akko mata, damin kud'i, kafin kace me sai ga mama na washe baki, balantana data fara irga kud'i, ai sai murnar tafi haka
Musa shiyayi mata bayanin komai, aikuwa sai rawa, abinda ya nunku akud'in kashi uku bisa ribar da akeci da
Kuma gashi ta nuna mata lemon datayi, sosai taji dad'in sa, lokacin data sha, saiga mama nashima FUTHA albarka
A tak'aice dai, mama saidata k'arar da buhun shinkafa aranar, lemo harda masu siyayya, ashago, siya suka fara
Tundaga lokacin komai na mama ya canja, duk abinda take ada, yanxu ukunsa, takeyi, FUTHA wataran ranar daba makaranta, tana zama
Lemon dai, ita takeyi saboda ta iya sosai, kullum tafara had'a lemon, saita yiwa Aunty Meemi addu'a, saboda ita ta koyamata komai
Haka rayuwa taci gaba, ci gaba, yazowa Mama Anker, saboda yanzu har gida take k'ok'arin siya tabar kasuwa, idan yaso taringa zuwa kasa kayan
Yau tana gama komai, haka ta shirya ta tafi makaranta, lokacin suna extra lesson saboda gabatowar qualifying nasu, sai wajan k'arfe 4 ake tashi
Lokacin da aka tashi, itada wata k'awarta Khadeeja Taheer, ita tana magana, amma kuma tanada kirki sosai
Suna kan hanya, dai dai inda zasu rabu, da khadeeja, zata tsallaka kenan, bata lura da tawowar mota ba, sai jin keeeeeeeeeeeee tayi, duk yanda yaso yakaucemata mai motar Allah bai nufaba, saida motar tayi kanta
Keeeeee, saijin k'arar ta Deeja Taheer tayi, tana juyowa sai ganin jini tayi, ga FUTHA yashe a k'asa
@ut@r h@jiy@
[11/10, 8:14 PM] +234 809 308 3613: [29/09 8:21 am] @ut@r h@jj@ju✍🏻💅🏻🌹: *FUTUHATUL KHAIR*
*®NWA*
*©Zainab Y Hussain*
*In dedicated to FUTHA Luv*
_Page 71-72_
Wata mata nagani ta fito daga cikin motar, da sauri tazo tana tab'a jikin FUTHA, inalillahi "
"Yanzu malam idi sai da nace katafi a hankali, amma kaqi, gashi kajamana wahala"
Bansan ya zanyi ba, haka dai suka d'auke ta, cikin sauri sai mota
Lokacin da Deeja zata tsallako, itama mota ta tawo, shiyasa ta tsaya, kafin ta wuce ita kuma tazo, motar wannan hajiyar taja, sai Asibiti
Treatment na gaggawa aka yimata, saboda taji rauni, kuma badan tanacin protein da vitamin ba, da sai ank'aramata jini, saboda tanaci shiyasa ba'a samata
Amma dai, ansamata drip, haka Hajiyan ta zauna, wajanta, tunaninta d'aya 'yar waye? tunda ba taga wani sign wanda zai nuna, yarinyar badaga gidan manya ta fito ba
Hankalin ta, duk ya tashi, burinta ta farfad'o, taji inane gidansu, dan magareeb takawo kai, kuma duk iyaye nagari, bazaso d'ansu ya kai dare a wajeba, especialy ita da, daga makaranta ta tawo
Acan kuma, Deeja bata tsaya ko ina ba, sai runfar Mama Anker, tana zuwa da hakinta, tace Mama FUTHA tayi, hatsari kuma wad'anda suka kad'eta, suntafi da ita
Wayyo nashiga uku, abinda take cewa kenan, ya zanyi? wannan yarinya kamar amana take wajena, daga makaranta, ba zama, kai Musa, Isah, kabeeru, saleh kutawo sai nema
Haka suka bazama government hsptl amma komai kama da FUTHA babu
Hankali ya tashi, FUTHA ta b'ata
Acan, bayan k'arewar ruwan da 'yan allurorin da akayi FUTHA, shine yabata damar farkawa, da salati a zuciyarta ta farka, sai ganinta tayi cikin wani d'aki daban, sosai ta watstsake, ta mik'e tafara kallon ko ina, cikin d'akin
Turo k'ofar da akayine yasa ta juya, da sauri Hajiyan ta matso kusa da ita, ya jiki tace mata, kai ta kad'a da s'auki, hamdan tace, doctor ne yazo dubatayi yayi yace komai fine, zaku iya tafiya
Kafin su fito, daga d'akin, tafara tambayar ta inane gidansu, sosai takemata kwatance da hannu, kenan bebiya ce, wannan kome? tanaji amma bata magana, ikon Allah gata kyakyawa, Amma Allah ya tauyeta tawani part d'in
Haka suka tafi, har cikin kasuwa, Mama ansha kuka, idon nan nata yayi ja, kabeeru wanda shi ya kawota shima kuka yake, basu san ina zasu ganta ba, sai ganin tsayuwar mota sukayi kusa da d'akin mama
Da saurin su suka tawo, FUTHA ce da bandages a goshinta, da hannunta, taba d'an d'ingisa k'afa
Mama ce, ta tawo tace alhamdulillah FUTHA ina kika shiga?, babu inda bamu duba ba, bamu ganki ba, dariya