Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya yi yace"Hajja ina son sunan ne kawai"Kwanci tashi gashi har sun share wata d'aya a asibiti kasancewar batai k'wari ba saboda k'a'idar zamansu a kwalba wasu na sati biyu wasu har wata suke in dai basu yi k'wari ba.Sannan idan an dawo da su gida, ba'a fita dasu, suna nad'e cikin d'aki da rigar sanyi da bargo. Sai sun yi wata biyar kafin a fara fita da su,haka kuma ba'asan yawan jagwalggwala su. Abinci kuma abu mai gina jiki ake basu bayan nono daga wata shida.Dangin madara ta yara, frisco cream, custard da sauransu.
Har girman su ma zuwa 3 years(shekara uku) abinci mai gina jiki suke ci.

Bayan sallamarsu asibiti da sati biyu, Baana ya shiga primary five (aji biyar) sossai karatu yake baya wasa.Benazirahtu na samun kulawa sossai,Kwanci tashi zama ya mik'a Marwanahtu da Benazirahtu suka cika watanni takwas tubarkallah yaran b'ul-b'ul dasu baya Benazirahtu kunsan bakwaini inya samu kulawa bai iya girma ba.Shekarsu d'aya da rabi babu inda basa yawo, hakan yasa aka yayye su.Yakura ta d'auko Marwanahtu tun daga yayye tak'i maida ita Yagana ta hak'ura ta bammata.



Shekarunsu biyu Hamza ya samu k'arin matsayi, dai-dai lokacin Baana ya kammala makarantar primary tare da hadda izuf ashirin.Walima sossai aka had'amasa don taya murna,Yakura ta d'auki tsanar duniya ta d'orawa Benahzirahtu har bata iya kiran sunanta kai tsaye sai ta hada da inkiyar *'YAR KURMA* hakan na ciwa Baana tuwo a k'warya sossai tun yana kawaici harya kai ga yin magana,ai kuwa yasha duka ranar harda fasa baki.Suna shekaru uku aka saka su makarantar nursery su da Marwanahtu lokacin Baana yan form two (aji biyun makarantar gaba da primary).


Bakura yaso a saka Baana a bording school(makarantar kwana) amma Hamza ya dage kan bayasan ya samu nakasu a karatunsa na islamiyya gara yayi day school.

Benazirahtu ta taso da farin jini, gata kyakkyawa da ita akwai surutu da saurin dauke abu hatta saka da Faanah take a gabanta k'ok'arin gwadawa take yi fahimtar yawan surutunta yasa Hamza ya sata makaranta da wuri kuma kullum ya dawo aiki sai ya had'asu su duka ukun yai musu lesson.Baana yana sonta sossai, shi dai ransa na son mace mai saurin fahimar abu sai dai inda suka b'atawa akwai ta da tsokana ta inda suka sha bam-bam kenan. Bai cika son dukanta ba hakan yasa duk lokacin da tai masa laifi yake had'a yatsunsa ya murza su bada sauti alamun gargad'i.Benazirahtu kuwa ta d'auki wannan d'abi'a ta rik'e ram sai ma ya zamo abin tsokanarta.Duk inda ta ganshi sai tayi masa wannan inkiya, wani lokacin ya biyota da gudunta zata nufi wajan Hajja yana hucci Hajja zata tare shi tana fad'in"kai da matarka kuma Baana? ".Yakan zub'uri baki yace "Hajjanmu me zan yi da me majina kawai k'azama".Ai kuwa ihu take sawa tana birgima,Marwanatu na gefe tana dariya shi da ya yi laifin har sai ya dawo yana lallashi.Tana mik'ewa kuwa zata huce kan Marwahnatu.Da kuka take korata gida, duk duniya hakan yafi komai batawa Yakura rai sai dai tai ta masifa wani lokacin har rama mata take.Da farko Yakura tana barin Marwanatu taje lesson daga baya saita hanata.Babu yadda Baana bai yi ba kan tabarta amma tak'i,sai ya hak'ura ya tattara ya rabu da ita.Baana ya taso da tsanin son karatu boko da addini hakan yasa Hamza yake alfahari da shi tare da tsaya masa sossai kan hidimar karatu.

Shekarun su Benazirahtu biyar a duniya,Baana yana aji hudu na makaranta yana da shekaru goma sha hud'u zuwa lokacin ya mallaki haddar alk'ur'ani na izzuf arba'in Benazirahtu na da izzuf biyar Marwanahtu ce kwantan baya a shekarar suna aji uku-uku na primary.


Tun Benahzirahtu bata fahimci kalmar *'YAR KURMA* ba harta fahimta, idan Yakura ta gayamata sai tak'i amsawa ko tai gun-guni ta wuce abinta,sunan ya soma tasiri saboda yadda Yakura ta ingiza Marwanahtu take kiran Benahzirahtu da sunan.Bale wata kalma da Benahzirahtu take yiwa kallon iyayi ne kawai wanda Baana ya gadar dashi inda yake kiranta da sunan Benah kanwarsa kuwa Marwa.Ita nan duniya ta tsani sunan Marwah kuwa sossai take son nata sunan shi a fadarsa yai masa tsayi ita kuma tana adawa da Benazirahtu ya fi dad'i.
Sanin tsanar sunan yasa Marwa ta tsaya tsayin daka wajan bin hud'ubar Yakura, saboda ta tsani yadda Mallamai ke nan-nan da Benah ko speech za'ayi sunanta ne a farko.Sossai ta dage da kira
Sunan Benah 'yar kurma ya karad'e ko'ina,hakan yasa kullum Baana cikin rabon fad'a yake Hajja kanta abun ya dameta.Data ga babu sarki sai Allah, suna son haukata mata jika zaunar da ita tayi tai mata nasiha.Cikin muryar kuka tace"Hajja duk fa Hajjan su Marwah ce ta samun sunan"jin-jina kai kawai Hajja ta yi tana bata hak'uri.Iyakar kulawar data dace Faanah na bawa Benah,duk da tana matsayin kurma a hakan tare suke komai da 'yarta kama daga girki zuwa hidimar gida uwa uba sak'a Benah akwai fikra wani lokacin har mamakinta iyayanta suke yi saboda da kanta sata zauna ta fitar da (style) na sak'a mai kyau sab'anin irin na Faanah.

Kwanci tashi babu wuya wajan ubangiji,Benah suka shiga aji hud'u Baana aji biyar.Kwatsam Benah ta kamu da wata irin rashin lafiya mai tsananin zafi, zazzab'i na rana d'aya bayan sun dawo makaranta kafin kafe kwabo ta soma suma.Sai kakkafewa take,hankalinsu ya tashi sossai a kid'ime Baana ya sureta sukai waje cikin ikon Allah ya samu abin hawa suka nufi asibiti.Jikinsa na rawa suka shiga, kai tsaye (office) d'in Dr Hamza ya nufa yana kiran sunanta.Kici6us sukai da Dr.Alanguburo cikin hanzari ya amsheta suka wuce (emergency) wajan taimakon gaggawa.


Likitoci sun duk'ufa a kanta har zuwa lokacin babu wani takaimaiman zance, iya kad'uwa ahalinta sun kad'u Hajja kuwa kuka kawai take Faanah ce ma mai dauriyar cikin su.An samu ta dawo hayyacinta, zuwan Dr,.Hamza likita ya ja shi office yana yi masa bayyanin sank'arau ne ya kamata,hankalinsa ya tashi sossai ya dinga kwantar masa da hankali.Sai da suka shafe sati biyu a asibiti sannan Benah ta samu lafiya.Sai dai me kowar su gida da kwana uku,suka fahimci kwata-kwata Benah bata ji in a kai mata magana sai an yi da k'arfi sossai sannan take ji.

Iya tashin hankali Hajja da Faanah da kuma Baana sun shiga, Bakura yai ta k'ok'arin kwantar musu da hankali Yakuwa kuwa shewa take tana k'arawa hada habaici wai dama ya za'ai kurma ta haifi abin kirki? tayo gadon hallita(genetic).Bakura ya fito ya nunawa Yakura b'acin ransa sossai,har ta kaisu ga sa'insa lamarin da ya jawo yai mata saki d'aya da k'yar Hamza ya je ya dawo da'ita.


Tsayin wata d'aya ana bawa Benah magani, sai dai babu wani canji hakan yasa Dr.Hamza ya yanke shawarar tunkarar Dr.Hannafi kan lamarin ranar yai nasarar samunsa a (office) bayan sun zauna ya mik'a masa hannu suka gaisa yace.

"Dr. Nazo ne kan matsalar Benah, har yanzu babu wani canji sai an yi magana da k'arfi take iya jin abinda aka furta.Ni shawarar dana yanke ko fita za'ayi da ita mugwada ko za'a dace?".

Dr. Hannafi ya numfasa"ban tari hanzarinka ba Dr. Matsayinka na likitan kunne ya kamata kai ho66asa a kai".Murmushi ya yi ya shafi kansa yace"tunanin hakan ya hanani sukuni, amma akwai maganin da zan d'orata akai insha Allahu za'a dace sossai kobata dawo dai-dai(normal) ba za asamu sauk'in rashin jin sossai.Kasan shi Sank'arau matsalarsa yana iya jawo abubuwa da dama".
"Kasan dake ba fannina bane ban san abinda yake haifarwa ba".Cewar Hannafi kenan yana murmushi.

"Eh! To hakane Dr. Amma yana da kyau kasan hakan dan bawa iyali kariyar data dace".
"Ok! Amma fa ka kawo shawara, in babu damuwa yimin bayani yadda zan fahimta".

Murmushi ya sub'uce masa yace"Dr.Kenan nima saboda yana tab'o kunnene in ya yi tsanani shiya sa ya shigo fannin mu. Kamar yada kaji ana fad'a".

_"Ciwon sank'arau wani nau’in ciwo ne da k'wayoyin cuta ke mamaye mayafin da ke lullu6e k'wak'walwa da lakar wuya da gadon baya wato (meninges) a turance.Akwai nau’o’in ciwon sank'arau daban-daban wanda k'wayoyin cuta iri-iri ke kawowa.K'wayoyin cutar bacteria ne da ake kira (Neisseria meningitidis)ke kawo nau’in sank'arau d'in da muka fi sani.Su wad'annan k'wayoyin cuta suna nan a cikin iskar da muke shak'a mai zafi.Hasali ma kashi daya cikin biyar a cikinmu masu lafiya na dauke da wad'annan k'wayoyin a hancinmu da mak'ogwaronmu bamu sani ba.Ta haka ake yad'asu in anyi kaki an tofar ko kuma ta iska a wuri mai cinkoso.K'wayoyin cutar mutuwa suke da sun ji sanyi.Don haka da wuya ayi sank'arau lokacin sanyi.Idan aka shak'esu ta hanci k'wayoyin na samun shiga jiki har jini ya kwashesu ya kai mayafin kwakwalwa. Nan da nan alamomin cutar suke bayyana"._

Cikin murmushi Dr.Hannafi yace"to ya alamomin ciwon suke? ".Shi ma martanin murmushi ya yi ya cigaba.

_"Alamomin ciwon sank'arau yafi kama yara ‘yan shekara 5-10, amma a lokaci na annoba zai iya kama kowa.Alamomin ciwon sank'arau suna da yawa. Da farko dai akan ji ciwon kai mai tsanani.Zazza6i, sai sank'arewar wuya.Wasu lokutan kuma akwa amai rashin son ganin rana ko haske.Wasu kuma sukan suma tare,d'aukewar numfashi akai-akai wanda yakan sa a rasa mutum._
_A tabbatar dakin barci na da tagogi bud'e a kalla biyu masu kallon juna. Idan taga daya ce abar kofa bude musamman idanmutane fiye da biyu ne a dak'in.A je cibiyoyin alluran riga kafi domin a karb'i allurar riga kafin ciwon sank'arau.Sai face majina inda ya dace ba a cikin mutane ba.Idan wani na kusa a gida ko wurin aiki ya kamu da ciwon to duk mutanen wurin ko da basu yi ciwon ba,su je su karb'i magani a asibiti.A yi saurin kai wanda ya kamu da wannan ciwon asibiti don gudun yad'a cutar ko ya galabaita.Cin abinci mai gina jiki da shan kayan itatuwa na marmari masu tsabta musamman ga yara don kara k'arfin garkuwar jiki masu iya kashe k'wayoyin cutar tun kafin su isa k'wak'walwa. Sank'arau yana haifar da d'aukewar ji na tsayin lokaci, ko kuma daukewar muryar mai ciwon ya zama ta shak'e matuka har ba'a iya jin sautin mai magana.Wannan kad'an kenan daga bayani kan sank'arau."_

Murmushi ya yi yace"sannu Dr.Ubangiji ya ba Benazirahtu lafiya"suka amsa da "amin" gaba d'ayan su. Kwanci tashi haka Benah take rayuwarta, Baana yana takaicin nakasar kunnanta sai dai in ya tuna haka ubangiji ya tsara mata sai dai ya yi mata kyakkyawan fata.Matsalar kunnanta yasa in akai karatu a makaranta bata samun fahimta sossai.Hakan ya ja ta soma fuskantar matsala a karatunta nan da nan ta tashi hankalinta sossai.Da kukanta ta samu Baana tana fad'amasa,sossai ya zauna yana lallashinta daga ranar kullum ya ta dawo makaranta yakan zauna ya duba aikin da akai musu ya k'ara yi mata bayani zuwa dare kuma Dr.Yana k'aramata.Nan da nan ta ware ta dawo (normal) dai-dai.

Kwanci tashi Baana ya kammala makarantarsa, result ya yi kyau lokacin su Benah na aji na shida a makaranta.Zaman wata biyar ya yi a gida a wannan zaman Dr.Ya dage sossai wajan koya masa kiwon kifi da noma,nan da nan ya maida hankali sossai cikin ikon Allah sakammakonsa ya yi kyau Dr. Ya nema masa addimission a b'angare biyu Kano da Maiduguri sai dai kash ba'a samu Maiduri ba sai Kano ya samu jami'ar B. U. K.



Bakura ya ji dad'in yadda d'an'uwansa yake kulawa da d'ansa hakama Hajja.'Bangara Yakura sai addu'a kwata-kwata ta tsani ganin Benah da Faanah har gobe tana da mummunan k'udirinta a kansu.Cikin ikon Allah Baana ya tafi Kano ranar Benah tasha kuka sossai da k'yar suka rabu,farkon zuwansa makaranta kewar 'yan uwansa ta dameshi daga baya ya ware sosai yake rayuwara.Lokaci zuwa lokaci yakan zo hutu in sun samu hutun makaranta, in yazo ya dinga nan nan da Benah wannan na hassala Yakura ta dinga fad'a tun Bakura na zuba ido yana kyaleta har ya soma tsawatar mata.Hajja tsufa yaja sossai,Benah kullum tana tare da'ita suna barkwanci tana koya mata al'ammuran rayuwa tana yiwa Hajja wanki da shara da sauransu.Marwanatu sarkin tsiwa,tayi d'are-d'are kan hud'ubsr Yakura duk inda suka je sai ta yiwa Benah gorin kurumta Benah sarkin rashin hak'uri ta kamata ta loda san ranta.Kullum suna hanyar kawowa Hajja k'ara sai an zauna sulhu amsar dai daya ce "cemin take 'yar kurma" dan haka ita Hajja take bawa rashin gaskiya,Dr.Ya kashe setroom na gidansa ya fitowa da Baana shi waje duk lokacin da yazo hutu nan yske sauka,Benah sarkin son tsafta duk sati saita bud'e ta gyara masa koda bai zo hutu ba, yanzu yana level two Beenah da Marwah na form one a secondary school.

AN DAWO LABARIN ......
Tsayin kwanaki biyu Baana yana jujjuya lamarin
Yakura cikin ransa, sai dai zuwa lokacin ya kasa
samawa kanta mafitar data dace ga Benah
kwata-kwata a kwanakin ta k'auracewa zuwa
gidan ko makarantar ma ta daina biyowa
Marwa.Kamar ko yaushe yana zaune kan dakali
yana duba wani lillafi kan couse d'insa,kamar
ance dubi nan ya daga idanunsa cikin nutsuwa
take tafiya.A hankali ya saki ajiyar zuciya, kwana
biyun da bai ganta ba duk ta rame kad'an cikin
nutsuwa ta gifta shi ko kallonsa batai ba ta shige
gidansu kai tsaye fanin Hajja (kakarsu) ta
nufa.Baana ya yi jim lamarin ya tsinka masa
zuciya, maida kai ya yi ya cigaba da abinda yake
sai dai kash! Zuciyarsa ta kasa karb'ar lamarin
rufe littafin ya yi tsam! Ya mik'e ya shiga gidan.
Turus ya tsaya ganinta tana yi wa Hajja wanki,
hakan yai matuk'ar birgeshi sossai k'arasawa ya
yi ya soma d'auraye wanda ta ajiye ko kallonsa
ba taiba har ta gama sab'awa ya d'auraye.Hajja
ce ta fito daga d'akinta, cikin murmushi tace.
"Sannu Benazirahtu 'yar albarka" cikin murmushi
Baana yace"wannan d'in Hajja?".
'Dagowa ta yi ta jefeshi da wani kallo,ta mugud'a
baki ya guntse dariyarsa yace"kinga zahiri ko
Hajjanmu"sakin tsintsiyar hannunta tayi ta ruga
d'akin Hajja da gudu tana kuka.Hajja ta kafe shi
da ido"Mai sunan manya me ya had'aku? " ya
shafi k'eyarsa yana murmushi ya sadda kai k'asa
yace"Hajja mu shiga ciki ki ji komai".Juyawa ta
yi bata tanka masa ba,a sanyayye ya rufa mata
baya.Suna shiga ya hango Benah tana gyaran
gadon Hajja, ya kad'a kai ya yi murmushi
yace"kayan rigima" bata juyo ba.Ya zauna a
hankali ya warwarewa Hajja komai,ta jin-jina kai
tai murmushi bata tanka ba ta ja fasali
tace"Allah ya kyauta".
Tana fad'in hakan ta bar d'akin, murmushi ya yi
ya kira sunanta ta d'ago ta kalleshi ba tare data
amsa ba.Yanayin kallonta ya tsinka masa
zuciya,ya kanne tare da danne abinda ke cin
zuciyarsa ya cigaba"Benah bakya kyautawa,
saboda abinda ya faru shi ne kike son yanke
zumunci ko?Kin kyauta kenan?".Idonta ya kawo
ruwa k'wal-k'wal ta sunkuyar da kai k'asa ta
share tausayinta ya ziyarci zuciyarsa cikin
bazata,muryarta na rawa tace"Yah Baana ba
yanke zumunci zan yi ba domin ba abune mai
kyau ba amma dole in yi nisa da kusantarku
Hajjan ku bata so ta tsaneni ta tsani Hajja
na.Kullum naje sai tamun gori Hajjana kurma
ce,ta kirani 'yar kurma bani na hallici kaina
ba.Ina duba kusancinmu daku ko dan Abbanku
shi yasa bana tankawa", ta had'iyi miyau ta
d'ago tai masa kallon cikin ido ta cigaba. "Bana
kawaici kan duk wanda ya tab'amun Hajja na
mahaifiyata ce ina sonta a duk yadda take zan
jura komai banda wulak'antata.Ba zan yanke
zumunci daku ba,domin babu kyau cikin addini.
_Daga Jubairu d'an Mud'im, yaji Manzon Allah
(s.a.w) yana cewa: "Mai yanke Zumunci bazai
shiga Aljannah ba._Kaga kuwa bazan so in shiga
cikin wad'anda baza su shiga aljanna ba".Cikin
murmushi Baana ya saki ajiyar zuciya,yana jin-
jina maganganun Benah zahiri yasan gaskiya ta
fad'a ko kad'an bai ji zafin ta ba ya dubeta yace.
" Benah kiyi hak'uri komai nada lokaci".
Murmushi ta yi tace"babu komai Yaya insha Allah
zan dinga kiyayyewa".Kamar an jehota ta fad'o
d'akin babu ko salama tana taunar cingum cikin
gatsali tace"Baana kazo in ji Hajja" a zafaffe ya
d'ago ransa na suya ya dubeta"ke mahaukaciya
ce? Zaki shigowa mutane babu salama yaka aka
koya miki?.Turo baki ta yi tana gunguni ai kuwa
ya shak'a ya kawo mata cafka da gudu ta yi
waje Benah ta kwashe da dariya"kana nuna
k'wanji kan mace?".Harara ya wurga mata ya yi
waje, ta gimtse dariyarta tare da lumshe ido.
Haka Baana ya kammala hutunsa ya koma
makaranta,cike da kewar 'yan uwa da iyaye.Cikin
ikon Allah karatu yake sossai, ya maida hankali
gefe d'aya kuma wani al'amari na mintsinar
zuciyarsa.
"Benazirahtu ya kamata ki hak'ura da sak'ar yau, tunda weak end ne mu zauna mui hira."Cewar Dr.Hamza,ta d'ago kai tana murmushi"Abbuna ina so ne in sak'a kayan yara, amma in kana so in zauna zan zauna mui hira".Cikin jin dad'i yace"Beenah wai me yasa kike son sak'a?".Tai jim alamun tunani,ta d'an b'ata fuska"Abbuna bana son Beenah, sarkin iyayi ne yake fad'a fa"."wakenan Benazirahtu? ".
"Yah Baana mana wai wani Benah ko Marwa.Dan kawai yaje Kano ya kama ya aro yaran wasu naga al'adarsu ma ta soma zame masa jiki shiyasa yanzu ba sossai muke shiri ba"."Ke Benazirahtu banda ke ai Beenah ma akwai dad'i, dan bakya so ne".
"Eh! Abbuna bana so","to an daina yarinyar kirki".
"Yauwa Abbuna na ji dad'i, ina son sak'a ne saboda inason in zamo mai dogaro da kai a duk inda na kasance, saboda Hajja tana gayamun irin yadda dogaro da kai yake da muhimmanci cikin rayuwa musamman matasa. Abbuna akwai hadisan da suke nuna cewa musulmi ya kamata ya zama mai sana’a, babba ko k'arama ba tare da ya raina ba kuma ya guji zaman kashe wando da maula.
_Hadisi na farko a wannan b'angare;An tambayi manzon Allah a cikin arziki, wanne yafi. Sai yace:“Dukkan sana’ar da mutum yayi da hannunsa itace arziki kuma tafi kusa da zama halal (indai ba’a yi ha’inci a ciki ba).” (Imam Hakim ne ya rawaito.)Akwai hadisin Zubairu Ibn Awwam, Manzon Allah yace:“Dayanku ya dibi igiyoyi ya tafi daji ya yiwo itace ya d'oro a gadan bayansa, yazo ya sayar domin ya kare k'imar fuskarsa,wannan shi yafi alheri gare shi fiye da ya roki mutane, ko sun bashi ko basu bashi ba(Bukhari ya rawaito shi.)_
_An karb'o daga Ka’ab Ibn Ujurah yace:“Wata rana manzon Allah na tare da sahabbansa sai wani mutum yazo ya wuce, wanda a jikinsa akwai alamar karsashi da k'uruciya,sai sahabbai suka ce: ‘ina ma wannan yana fagen jihadi fisabilillah (Musulunci ya fa’idanta da kuzarinsa).Sai Annabi yace: “Fitowar nan da yayi daga gida,idan dai har ya fito ne domin neman abinda zai ciyar da kananan yara, to daidai yake da fisabilillahi.Haka kuma, idan ya fito ne domin ya nemo abinda zai ciyar da iyayensa guda biyu tsofaffi da suka gajiya, to daidai yake da yaki fisabiliilah.Haka kuma idan ya fito ne domin zai kare mutuncinsa daga rokon mutane, to dai-dai yake da yak'i fisabilillah."_
_(Dabarani ya rawaito)Saboda haka, dole ne mu dage wajen sana’a babba ko k'arama, tare da dagewa wajen ingantata,da bata muhimmanci,musamman ga mata mazauna cikin gida"._

Tak'arasa furucin tana murmushi, shi ma murmushin ya yi yana dubanta zuciyarsa k'war cike da farin cikin samun yarinya kamarta.
"Aikuwa Benazirahtu zan k'ara bud'add'amiki wajan daga yau, tunda manufarki kyakkyawa ce"."A'a Abbuna yara nake so wanda na girma kad'an in dinga koya musu suma su dogara da kawunansu a nan gaba".


"Amma fa kin kawo shawara d'iyar kirki, ni burina ina so ki karatu mai zurfi Benah"sunkuyar da kai ta yi bata tanka ba.Cikin ranta tana jin-jina k'udirin mahaifinta,mik'ewa ta yi ta d'auko jakar islamiyyarta tana murmushi"Abbu jiye mun haddata tunda yau ba fita".

Cikin zazzak'ar muryarta take rai-rairo karatun,mahaifinta yai tsai da ransa yana saurara harta dire.A hankali ya saki ajiyar zuciya harta k'arasa izzuf d'in suratul ankabut.Cikin jin dad'i tace "Abbuna saurana izzuf ashirin hadda" cikin sanyin murya a hankali yace"Allah yai miki albarka Benazirahtu"bakinsa kawai ta kalla ta gane abinda ya fad'a."Amin Abbuna".

Cikin wata d'aya Dr.Ya gyarawa Faanah da Benah shagonsu sossai, aka zuba kayan aiki tare da zare akaiwa shagon docoration.Gida-gida ya bi da kansa ya nemi yardar iyayyan yara tashin farko aka d'ibi d'alibai ashirin nan da nan aka soma gudanar da koyo ga matasan 'yan mata.Kafin sati sun iya dashin sak'a.

"Hajja nifa gaskiya na tsani ganin yadda Baana yake yiwa Benah, kamar bani ce tilashinsa ba sai yai ta yi mata abu bandani.Kuma kin san halin masifarsa yanzu ina yin magana,zai hauni da bala'i gashi gaba d'aya ya daina mun dariya wai bana son karatu."

"Ke! Ni tashi ki bani waje sakarya, ai nagaya miki ki dinga yin abinda yake so kink'i ya zan miki?".Turo baki ta yi ta tashi fuu! Tabar wajan, Yakura tai ajiyar zuciya"oh! Ni Yakura yadda Kurma ta zamemin bala'i haka 'yar kurma take neman zamemin masifa, gaskiya ba zai sab'u ba dole in d'auki mataki".Ta furta hakan a zahiri.Cikin sauri aka d'auketa aka yi clinic da ita ko motsi k'wak'wara bata yi.Allah ya taimaka ta dawo hayyacinta,akai treat d'in goshinta inda ta fashe.Tambayar duniya an mata kan waya ji mata ciwo, babu amsa sai sharar hawaye take tana batasan waye ba haka aka hak'ura aka dawo da ita zuwa aji.Malam na fita ta jawo jakarta da niyyar copyn aikin da akai musu,kwatsam tai karo da abinda ya d'aga mata hankali tama manta da ciwon goshinta ta daddage ta k'wala k'ara ta fitar hankali hakan yai sanadiyar dagawar ciwonta.Ba komai yasata hakan ba face karo da tayi da littafin biology d'inta an yi gutsi-gutsi da shi.Gashi Uncle Tunde ya basu aiki yau zai karb'a hankalinta yai mummunan tashi.

Cikin muryar kuka ta dubi mak'ociyarta,nan da nan yan ajin suka baibayeta suna tambayar dalili.Ta kasa magana sai nuni take musu da hannu, Falmat ce ta finciki jakar ganin littafi gutsi-gutsi a kacaccale yasa tai saurin zazzage jakar tana fad'in "kungani".Gaba d'aya suka had'a baki"la! Garin ya Benah? ".Idonta ya yi k'wal da hawaye tace"nima bansani ba".Jikinsu ya yi sanyi sossai nan da nan sukai tai mata jajje tare da bata hak'uri Falmata ce taja hannuta suka je sukaiwa Uncle Tunde bayani dake akwai shi da fahimta bai ja ba yai mata lamuni. 'Yan ajinsu sunji dad'i sossai, nan da nan akasamu saban littafi wasu suka soma tayata kwafi.

Dole suka koma clinic aka sake gyara ciwonta.Ana tashi ta nufi gida tana tsananin ciwon kai.A k'ofar gida ta had'u da mahaifinta da Bakura gefansu Baanah ta saki ajiyar zuciya,cikin girmamawa ta risina tana gaishesu da kulawa Bakura yace."Benah ciwo kika ji? "Eh Abbu ciwo na ji".Ta fad'a tana sharar k'wala,"garin ya Sis Benah kukan kuma na menene? ".Muryar Baana ta daki dodon kunnanta, cikin amo a hankali ta kaleshi suka had'a ido yarrr! Tsigar jikinsa ta zuba ya kauda kai yana jadadda tambayarsa"faduwa na yi".Bata sake magana ba ta shige gida, ya kad'a kai kawai take ya gimtse fuska sakammakon hango Marwa ta jero gefanta namiji tsakiya ita daya gefan namiji ganin su yasa jikinta ya d'auki rawa tai saurin sallamar su ta nufi gida.

"Ke! Marwa zo nan" y fad'a da sautin murya,jiki na rawa ta sunkuya ta gaida su Dr. Tana kame-kame "daga ina kike? Su waye wad'anan da kuka jero tare?"."Yaya da... ga da.... ga makaranta nake, 'yan ajinmu ne" kyakkyawan mari ya wanka mata "baki da kunya baki da mutunci ko Marwa ni kike kallo kice wa 'yan ajinku ne? ".Dr ne ya kamo shi ya dubi Marwa" baki kyauta ba Marwa wannan ba tarbiya bace, haka kika ga 'yar uwarki nayi? Kar in sake gani".Kai ta daga ya sallameta ta wuce gida tana k'un-kuni.Ya juyo kan Baana "na dawo gareka na fahimci kana da zafin zufiya Baana, ka dinga bin komai a hankali mace ce ba'a nuna kwanji a kanta ka ji ko.Sannan ka dinga sanyayya zuciyarka akwai abubbuwan da basu canccanci daukar zafi ba.
_Kamar yadda yazo a hadisi daga Manzon Allah yace.“A cikin jiki akwai wata tsoka idan ta gyaru dukkan jiki ya gyaru,idan tab'aci dukkan jiki yab'aci,wannan itace zuciya.”Wannan hadisi ya nuna mana idan zuciya ta gyaru wato ta tsarkaka,dukkan sauran gururruwa na jiki misali harshe,ido,kunne da dai sauran su suma zasu gyaru wato zasu tsarkaka._

_Zuciya ma’anarta shi ne jujjuyawa, anace mata haka saboda jujjuyawar ta a tunani,amma a isdilahance tana da ma’anoni guda biyu tana da ma’ana ta zahiri wato jis-miy,da kuma ma’ana ta bad'ini wato ma’anawiy.To ma’anar ta ta bad'ini shi ne Malaman Irfan suke bayani akai,shi kuma ma’anar ta zahiri shi ne likitoci suke bayani da kuma kula dashi,tun da ya shafi bangaren gangar jiki ne.Saboda haka idan mutum yaga ambaton zuciya anan,ba ana nufin ma’anar ta ta zahiri ba wato tsoka wanda aka sani tana jikin dan Adam,a bangaren jikin sa na hagu,wato a kirjinsa.A’a ana nufin ma’anarta ta badini,wanda akan wannan asasi ta ma’anarta ta bad'ini zuciya itace mahallin imani,tsoron Allah,son Allah,da dai sauran matakai suluki zuwa ga Allah kuma a irin wannan ma’anar ta badini ake nufin inta gyaru dukkan jiki ya gyaru,inta bacci dukkan jiki ya baci._

Dan haka sai kayi da gaske wajan yakarta,kan aikata alkhairi da sabaninsa".
"Na gode Abbagana" sallama

Please Login or Register in order to submit comment