Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

haɗa a second c.a da exams kawai."



"To shikenan tunda kince haka kinga Dr ba shigowa yayi ba captain ya kira Allah ya sa ba fixing zai yi mana ba, "Amin."



Haka suka gama zamansu babu abunda suka yi suka koma gida, washe gari suka dawo suka yi lecture din Hakim..



Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, dan tsakanin Hakima da Hakim abun nasu sai Allah dan ba kaunar junansu suke ba..


Karatu yayi nisa sosai dan 300lvel ba abun wasa bace shiyasa Hakima take karatu ba kama hannun yaro, duk da Hakim yace ya zama dole sai ta zo office dinshi dan ta bashi hakuri, kamar yanda duk wanda baiyi ma attendance suka zo har office bashi hakuri, ita kuma tace bata zuwa sai wannan abun ya zama sillar caryover dinta..



Yau da wuri ta shirya ta wuce school saboda Dr Moha zai yi masu test shiyasa ta fito tun eight duk da sai ten zaiyi masu test din, tunda taje karatu take dan ta lura course din Dr shima ba laifi yana da wahala shiyasa ta dage mashi, sai wajen nine thirty Maryam ta shigo itama..


"Hakima tun yaushe kika zo?, "tun eight mana, sannu da zuwa late comer, "Yauwa dan Allah Hakima idan kika fito test din nan kije ki ba Yaya Hakim hakuri ai malaminki ne karki biye ma zuciya."



"Maryam ban daukar wulakancin Hakim shiyasa, na gaji da abunda Hakim yake yi man na gaji am tired wallahi."



"To mai yayi saura keda kin kusa gama baki daya baki sake ganin shi tunda ba garinku daya ba, "to naji zan je kinga ga Dr nan yazo Allah ya bamu sa'a baki daya, "Amin."




Bayan Dr Moha ya shigo yayi masu test ba laifi dan sunyi mamaki saboda ba haka suka ran test din zata yi masu ba amman tayi dadi sosai , dan question yayi masu masu sauki sosai, bayan sun fito Maryam ta raka Hakima Office din Hakim amman bata shiga ba sai ta tsaya bakin office din..



Nocking tayi sannan ta shiga, bata damu da yace ta zauna ba ta samu wani sit ta zauna ta jiran ya gama waya dan ta lura waya yake mai mahinmanci shiyasa..




Bayan Hakim ya gama waya ya juyo ya kyaleta sanann yace, "what Wrong with you? Kin zo ki sani gaba sai kallo kike kamar tsohuwar maiya."



"Lafiyarce ta kawo haka, dakata Hakim komai kake karka kuma ceman Maiya, kuma inni maiyace nafi karfin na cinyeka kuma kasan office dinka kallo bai isheni balle har na cinyeka."



"Shut up, stupid girl, wai Hakima sai yaushe zakiyi hankali dan Allah dan Annabi? ace mutun kamar ciwon ciki, ki kiyayeni Hakima, to wata tsiyar ta shigo dake."?




"Ni ba tsiya ta shigo dani office din ka ba, daman zuwa nayi akan attendance din da kayi first week din dawowa, nazo ka sa suna kamar yanda kasa na su tunda mu ba garinku muke ba shiyasa bamu shigo week din farko ba."



Tunda Hakima ta fara magana Hakim ke kallon dan karamin bakinta dan ba karamin burgeshi tayi sai yaji ina kartayi shiru ta cigaba da maganar, shidai bai san reason ba amman yana san yaga Hakima na magana ba tun yau ba, amman shi dai baya daukar raini duba da yanda take magana kamar tana bashi comment..



"Ta shi ki barman Office Hakima ba wani sanyaki da zanyi tunda na fahimci baki iya magani ba."



"Bangane ban iya magani Malam duk maganar nayi ita maicece?shikenan zan tafi Allah yana sane da Hakima."



Nan Hakima ta fita office din Hakim cikin fushi wai ita Hakim zaice ma bata Iya magana ba ga kuma yace mata maiya.







_By Jameelah Jameey ✍🏻_





#JameelarhSadiq
#Share
#Comment
#Vote
#Like
#Please





👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
*GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻



*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻```
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
________________________________



_STORY AND WRITING_ _BY_

_Jameelah jameey 🖋_

*(Yar mutan kankia👸🏻)*






*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*


_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

```NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍```




55&56



"Hakima ya naga kin fito cikin fushi ba dai bai yi maki ba."?


"Kyaleshi Maryam shiyasa nace maki bani zuwa dan nasan ko naje wallahi sai Hakim ya bata man rai, wai ni Hakim yake cema Maiya."




"Maiya kuma Hakima.''?


"Haka kika ji nace, wallahi na tsani Hakim ban san Hakim dan haka in dan ya gadama ya bani C. O, nidai nasan Allah yana tare dani."



"Aiko bai kyauta ba, bari na dawo, "ina zakije Maryam."?



"Kedai ki jirani kawai am coming."


Nan Maryam ta shiga office din Hakim, dan bata ji dadin abunda yayi ma Hakima, dan ji take kamar ita yace ma Maiya ba Hakima ba..



"Yaya Hakim sannu da aiki, "Yauwa Maryam, lafiya mai ya samaiki naganki haka."?


*🥶🥶Hakim na kusa fa to Team Hakima kunji Hakim mai kanwa ko? Duk ya shiga damuwa amman yanzun ya gama wulakanta Hakima cikin office din shi bai damuba🙄.*



"Yaya Hakim why? Maiyasa kace ma Hakima Maiya."?


"Ke tashi ki barman office tun kafin na taitaikaki, ke har ni zaki sa gaba kina yi ma silly questions kamar wani abokinki."?



Cikin kuka Maryam ta fara magana dan baki daya ta fara gajiya da abunda suke kamar kananun yara..


"Haba Yaya Hakim wai sai yaushe zaku fara rage tsanar da kuke yi ma junanku kai da Hakima."?


"Yaya Hakim bai kamata ba wallahi totally is round ace kaine kake kallar wannan abun ka biye ma Hakima, koda Hakima bata gaya man ba nasan ni kaina na girme Hakima Yaya Hakim maiyasa."?




"Dan Allah Yaya Hakim mai Hakima tayi maka har haka da wannan bakar tsanar ta shiga tsakanin ku."?



"Ya isa Maryam is enough."


Hakim yace ma Maryam cikin fushi dan yaga Maryam nason raina mashi wayau..


"Get out of my office useless girl, kin biye ma wancan useless girl din ta bata maki rayuwa kin fara rashin Kunya wawiya kawai zaki fita ko sai nayi ball dake."?



Haka Maryam ta fita duk ba dadi dan ita gaskiya ta gaji da wannan abun, dan ta gaji iyakar gaskiya..



"Maryam yi hakuri wuce mu tafi, kibar Hakim da halinshi."

"Dan Allah Hakima ki kara hakuri da halin Yaya Hakim nasan kina hakuri ki kara yin wani insha Allah komai ya kusa zuwa karshe."



"Naji ni zan wuce gida thank you, "ok bye."



Tunda Maryam ta fita office din Hakim, Hakim yake tunanin maganganun da Maryam tayi mashi, "wai daman Hakima ta tsaneshin kenan."?



Abunda Hakim yake maimaitawa kenan, "oooo! Ni Hakim maiye abun damuwa dan Hakima ta tsane, nima da man na tsaneta to mai aciki dan Hakima ta tsanani."


Tambayar da Hakim yayi ma kanshi kenan sannan ya cigaba da aikin gabanshi..



Tun bayan wannan cases din da Hakim yayi da Hakima, Hakima bata sake yarda wani abu ya hada ta da Hakima ba dan ta gaji da halin Hakim shiyasa ta kama mutuncinta ta cigaba da karatunta dan har ta fidda rai da course din Hakim..
_____________________________



Rayuwa na tafiya komai faruwa yake cikin gidan su Hakim dan Gimbiya Kilishi ta zage wajen bin bokaye dan yanzun ba wajen Turmurturs kawai take zuwa ba.


ita kuma Gimbiya Zulaha bata damu da zuwa wajen ko wani boka ba, dan tasa ma ranta shekara biyar nayi zataga gawar Hakim, amman daga baya tana yi ma Kilishi zagon kasa wajen Maimartaba dan so take kafin shekara biyar Maimartaba ya saki Kilishi, saboda bata shirya zama da Kilishi ba.


(Kuma kai su Gimbiya Zulaha ba Amana tsakanin ki da Gimbiya Kilishi ko wananku yi ma dan uwanshi yake daga boye😝.)



Ita ko Gimbiya Fulani Kubrah bata damu da abunda suke ba duk da tana sane da dun wani tungu da kulle-kullen da suke cikin gidan amman bata damu ba ta barma Allah lamarinta baki daya..


_________________________

Rayuwa ma tafiya dan Hakima yanzun an shiga 400lvl yanzun haka second semester take final year, Allah yaso Hakima ba Hakim ke mata project supervisor ba, shiyasa hankalin ya kwanta ta cigaba da hidimar gabanta dan yanzun bata da damuwar komai sai ta karatunta..



yau Hakima suke fara exams shiyasa ta cika zaman gida, ba dan so take ta gama fresh ba tare da spell over ba shiyasa bata tsayawa baye ma kowa duk da Samari sunyi ma Hakima ca, amman basu gabanta.




Exams sai dai ace Alhmdulh yau Hakima ke gama Exam kuma take gama *AHAMADU BELLO UNIVERDITY ZARIA* bayan sun fito final exmas ba karamin murna suka yi ba nan sukayi exchagings numbers da kawayenta sannan ta wuce gida tana zuwa gida suka dauki hanyar Kano daman already su Azima sun shirya masu kayan su jiran fitowarta suke su kama gabansu dan suma murna suke zasu zauna waje daya, amman da basu kano basu zaria karatun ne kawai basu yi ba amman suma sun sha wuya..




Tafiya suke dan sosai Bala yake ba mota wuta cikin ikon Allah suka iso gida lafiya..


Direct shashen Gimbiya Yakumbo a ka wuto da ita dan yau shima Yarima Annas ya dawo gida shima dan shi da safe ya dawo da shi yayi niyar zuwa ɗauko ƙanwar tashi Maimartaba ya hanashi yace itama zuwa anjima zata iso sai gashi ta shigo itama..



"Momy Momy Momy! Alhmdulillahi Momy yau nayi degree."



"Oyoyo! Daughter am so happy today, Daughter kinga komi yayi farko yana karshe ko."?



"Hakane Momy, ina Yaya Annas?, "yana shashen Fulani kin sani."


"Na tafi naga Yayana, "to nima da man yanzun zan tafi shashen ta Baffanku nacan shima, "to Momy mu tafi."


Nan suka tafi tare shashen Gimbiya Fulani ko wacansu fuskarta dauke da murmushin farinciki..



Suna shiga Hakima ta ruga da gudu ta fada jikin Annas tana cewa, "Yaya Annas am so happy to see you yau, congrats Yaya angama phd lafiya Allah yasa angama a sa'a."



"Congrats tooo,, ƙanwa kema ina taya ki murnar gama degree ɗinki, "thank you Yaya."



Bayan sun gama murnarsu Maimartaba yake shida masu gobe za'a yi masu walima a bakin kogin masarautar haka suka gama sanann kowa ya wuce shashen shi cikin farinciki..




Tana zuwa shashenta bayi suka fara yi mata Allah yasa alkhari, yasa ta gama karatun nan nata a sa'a..




Amin kawai take ce mashi bayan ta shiga wanka ta fito ta shirya hutawa tayi sannan ta kira Maryam waya nan take gaya mata Annas ya dawo gida shima ya gama karatun shi bayan sun gama waya ta kwanta bacci..




Shima Annas bayan ya gama gaisaPlease




bayin shi yayi wanka ya kira Hakim waya yake gaya mashi ya dawo gida shima bayan sun gama waya shima ya kwanta dan yana san ya tashi da wuri gobe insha Allah...







_By Jameelah Jameey✍🏻_







#JameelarhSadiq
#Share
#Comment
#Like
#Please



👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
*GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻



*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻```
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
________________________________



_STORY AND WRITING_ _BY_

_Jameelah jameey 🖋_

*(Yar mutan kankia👸🏻)*






*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*


_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

```NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍```



57&58


"Allah ya taimakeki angama haɗa ruwan wankan yana jiran ki."


"Azima ki fiddo man kaya masu sauki dan kwaliya kawai zamu tafi sai gyaran jiki cikin gari kafin lokacin walimar yayi."



"Angama uwar marayu a fito lafiya, "Uhmmm."


Bayan Gimbiya Hakima ta shiga wanka Azima ta fido mata wani material wanda ya ansa sunan shi material, dan Azima ba daga baya ba wajen iya zaɓen kaya shiyasa Gimbiya Hakima take san duk inda zata ta tafi da Azima dan tana da kallar waye wa..



Sai da tayi kusan awa biyu sanann ta fito daga wanka, nan su duka ukku suka haɗu wajen shirya ta, bayan sun gama shirya ta ita da Azima suka ɗauki hanya sai salon dan Gimbiya Hakima ba daga baya ba wajen tsata ba..



Shiri akeyi naga ni na faɗa dan sai mutun yayi tunanin biki ake ko suna amman ba ko ɗaya kawai walimar gama karatun su Hakima Sarki Abdulhadi ya shirya dan ba ƙaramin san yaran nashi biyu yake ba dan su kawai Allah ya bashi kuma gashi Allah yasa yana da rabon ganin kammala karatunsu lafiya dole ya haɗa liyafar da ba'a taɓa yin kamarta ba a masarautar kano.



Niko nace ina da zaiyi masu aure ai abun mai faɗuwa sai dai.. Ba ruwa 🤭.




Shima Yarima Annas ba'a barshi a baya ba wajen shiri duk da ba wani aboki ga gareshi ba a cikin masarautar hakan bai hanashi yayi abunda ya ga ya dace ba, shida Hakim abokaine a makaranta suka haɗu lokacin shi yarima Hakim yana Phd ɗinshi shi kuma Yarima Annas yazo yin masters degree nansu haɗu sai tasu tazo ɗaya duk da Hakim ya dan girmi Annas amman ba wani girma yayi mashi sosai ba kuma halin su yazo ɗaya shiyasa freindship ɗinsu yazo dai-dai.



Sai da Yarima Annas ya gaiyyaci Hakim yazo walimarsu amman Hakim yace yayi hakuri bai da lokaci comitement sunyi mashi yawa amman insha Allah ya samu time zai zo yayi mashi congrats ya gama karatu lafiya..



Bangaren sarki kuwa ya gaiyaci ko wani sarki da yake Nigeria suzo su taya shi murnar kammala karatunsu Hakima, su ma su Gimbiya Yakumbo ta gaiyyaci ko wace matar sarki da matan yan siyasa dan tayata murnar gama karatun su Hakima.



______________________________


*× ZARIA×*


"Hakim cikinku ku ukun nan ɗaya ya shirya insha Allah zamu masarautar kano , domin taya Sarki Abdulhadi murnar kanmalawar karatun yaronshi da ya dawo daga dubai."



"Ba sai na gaya maku ba waye Sarki Abdulhadi ba a wajena ba, don Sarki Abdulhadi Aminane na hannun dama tare mukayi karatu da shi masarautar su na zauna da nayi karatu B. U. K Kano, dan haka hallatar walimar ta zamai mana dole koda muna da uziri mu ajiyeshi gefe muje."




"Allah ya taimaki adalin Sarki Abdulmatalak, ai ba wanda ya dace da ya baka zaria inba Hamad ba tunda shine babba."



"Zulaha wa ya baki izinin magana ?, "Ina neman afuwa, "ni ban damu da babba ba kuma in ta girma zan bi ai da Hakim zan tafi kenan tunda kinsan ya girmi Hamad kowa ma ya sani cikin masarautar nan ban san tashin hankali Zulaha dan haka akiyaye."



"Cikin ku wa kuka fidda mu tafi tare."?


'Allah ya taimakeka, nidai na hakura cikinsu sai ka tafi da ɗaya."


"Ina ai ba zai yuyuba idan har za'a tafi da Hamad sai dai a tafi da Humad dan shima Humad ɗin ba wani girmanshi a kayi sosai ba da za'a ringa nuna mana banbanci."



"Kilishi kema ko? To tunda abun ya zama haka ku tashi ku ban waje ban zuwa da kowa baki ɗayansu daga ni sai waziri zamu tafi."


"Allah ya huci. "Ya isa haka ku tashi ku ban waje."


Haka suka fita ana hararar juna tsakanin Gimbiya Kilishi da Gimbiya Zulaha, ita dai Gimbiya Fulani Kubrah bata tanka ba nata ido duk abunda akace shi zatayi..




Bayan ta fiyarsu Sarki ya shirya ya sa aka kira mashi Hamad suka tafi tare ba dan yaso ba, amman ba yanda zaiyi dan shi da Hakim yaso zuwa amman haka Allah ya so.



Haka suka ɗauki hanyar kano, shi ko Hakim direct shashen shi ya wuce dan ya lura kwana biyu bai da aiki sai tunanin Hakima gashi ta tafi shi ko garinta bai sani ba, "maiye amfanin tunaninta!?? Wai mai ke damuna ni Hakim, ina no gaskiya ba haka bane ni Hakim zan so wannnan useless girl ɗin Allah ya tsari kakana da asara, kawai dai dan mun saba faɗa da ita shiyasa banjin daɗin gamawar da suka yi."


Haka Hakim ya kama yan surutanshi har ya samu ya ɗauro alwallar wal'ha ya fara sallolinshi yana neman tsarin ubangiji Allah dan ya lura maƙiyanshi ba kyaleshi suke ba, shiyasa ya miƙama Allah lamarinshi shida ƙannanshi da kuma mahaifiyarshi.




Bayan ya gama sallahrshi ya tafiyarshi school ya fara marking ɗin papers din su Hakima..




Ko da yazo wajen paper ɗin Hakima yayi mamaki sosai dan yanda yaga waje ɗaya ta faɗi shima wajen final answer ne ta rubuta ba dai -dai ba.


"Uhmmm! Gaskiya yarinyar nan tana da koƙari shiyasa wani time ɗin take bugerni."



Hakim ya faɗa yana ajiye paper ɗin Hakima wajen da yayi marking sai da yayi da yawa ba laifi sannan ya ɗauki hanyar Join domin yana bukatar refresh ɗin brain ɗin shi, saboda hayaniyar da su Gimbiya Zulaha su kayi ɗazun ba ƙaramin ciwon kai take sa shi ba.




Anya Hakim hayaniyar su Gimbiya Kilishi ta saka ciwon kai🤔, nidai babu ruwa na 🤭, Team Hakima ina jiran ansarku.






_A gaskiya masoyana bani da bakin da zani yi maku godiya sai dai nace Allah ya bar kauna masoyana❤️💃🏼_




```Tabbas naga masoya, da wanda nasani da wanda ma ban sani ba, ina ganin ruwan comments da ma fatan alkhari da masoyana suke yi man duk suna isowa gareni dan haka ba abunda zance sai Allah ya barman ku my Fans much love❤️💯```





*Yan wattapad kuma ba'a barku a baya ba, kuna nuna man iyakar kaunarku kuma inayin ku over and over kudia ku cigaba da comments and vote ni kuma na cigaba da surbudu mako da zafafan litaitafai da litafin na suna hanya very soon kudai cigaplease



biyoni 💃🏼💃🏼💃🏼*


_Yan facebook ban san mai Zance ba aiku sai dai kwando godiya da miko zuwa ga duk wani masoyana da suke facebook inajin dadin ganin comments ɗin ku kuma😍_



_By Jameelah Jameey_✍🏻





#JameelarhSadiq
#Share
#Comments
#Vote
#Like
#please


👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
*GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻



*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻```
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
________________________________



_STORY AND WRITING_ _BY_

_Jameelah jameey 🖋_

*(Yar mutan kankia👸🏻)*






*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*


_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

```NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍```



59&60



"Ranki ya daɗ'e, asa maki eyeshadow ne."?

"Azima kyalenni sosai kinga ya nayi idan ya dace a saman eyeshadow ɗin sai ta saman."


"To Allah ya taimakeki."

Masha Allah ba ƙaramin kyau Gimbiya Hakima tayi ba abunka da farar fata sai abun ya wuce masali, dan tsayawa na gaya maku irin kyaun da Hakima tayi ɓata lokacine dan haka Team Hakima wanan aikin naku ne sai ku gaya man kalar kyaun da Hakima tayi 😍.



"Allah ya taimakeki gskiya ko ba'asa eyeshadow ba kinyi kyau a haka, amman a sanya maki dan ƙara ma kwaliyar armashi."


"Uhmmm."


Abunda Gimbiya Hakima tace kenan, sannan mai make-up ta cigaba da aikin ta bayan ta gama yi mata kwaliya wata arniyar atamface black and red a Hakima tasa sanann aka murza mata ɗaurin dankwali mai kyau da aji bayan angama ɗaura dan-kwalin ta ɗaura alkaibarta bisa kayan sanann tasa takalimin viccin half-shop tasa sai ta sake fitowa Hakimarta yar'shekara 22,bayan sun gama shirya ta dubu ɗari hudu ta ba masu gyaran sannan suka wuto gida.

Bayan sun koma gida direct shashen Fulani ta wuce nan ta sake gyara idan ta ga ya dace ta gyara sannan ta wuce shashen Yarima Annas su Lantana na take mata baya.


Bayan ta isa bakin shashen shi aka yi mata iso ta shiga su kuma su Lantana suka tsaya bakin shashen suna gaisawa da sauran bayi yan uwansu.


"Yaya sannu da hutawa."

"Yauwa Hakima, masha Allah gaskiya ƙanwar nan tawa tayi kyau sai kace wanda zataje kasar kyau."


"Haba Yaya Annas karka fasa man kai fa, "Hakima ai gaskiya na faɗi amamn sirikin nawa zai hallaci wannan walimar ko."?


"Rufan asiri Yayana ina Hakima ina kula saurayi? Kaganni nan bani da wani saurayi kawai dai kwaliya akayi man saboda wannan walimar."


"Hakima kina aikin mai baki tsada miji ba? Bayan kin san Baffah aure zai yi maki tunda kin gama karatu."



"Yaya Annas am still young fa, duka duka yanzun nike da 22yrs ban isa na fara kula samari ba."



"Shut up Hakima, ke ɗince baki isa kula samari ba dan sakarci irin naki na banza."?


"Yaya Annas, haba maiyasa ni ba'a sona cikin gidan nan inba ba'a sona ba taya za'a yiman aure inada wannan shekaru."?



"Hakima kisa ranki anyi maki auren dole angama, dan wallahi nasan Baffah aure zai yi maki kuma laifin kine, kinga ni da man nasan Baffah zai fidda man mata shiyasa ban kula ko wace yarinyaba, amman ke dai Baffah ya baki chain ke kika yi wasa damarki tashi mu tafi naga am fara taruwa."


"To shikenan, nasan insha Allah Baffah ba zai yi man haka ba, "kina da wanda ki fidda a matsayin miji."?



"Aa babu, "kinga baki da magana ƙanwata tashi mu tafi naji ance Sarki Abdulmatalak da Sarki Abubakar Sadiq sun fara isowa."



"Saraukunan ina ne su?, "da Sarkin Zaria da Sarkin Katsina, "ok shikenan mu tafi."



suna fitowa waje kunyangen suka take masu baya suna kirari suna cewa, "takawarku lafiya ya'yan sarki jikokin sarki, Allah ya taimakeka Yarima Annas sarki mai jiran gado, Allah ya taimakeki Gimbiya Hakima, Gimbiya uwar'sarki da yarda Allah, kunyi gaba maƙiyanku suna bayan ku ba mai ganin bayan ba dai maƙiyi ba".



Haka suka kama kirari har suka isa wajen da aka tanadarnasu domin zamansu, tunda suka taho Yarima Hamad yake kyallon Gimbiya Hakima take ya ji shi duniya ba wanda yake sha'awar aure inba ita ba dan bai san da yace Masha Allah ba saboda da kyaun da tayi mashi son Gimbiya Hakima ya shiga cikin zuciyar Yarima Hamad ba tare da ya fargaba.



Tunda ake yi masu wanna kirari har suka zauna sannan suka tashi suka fara miƙa gaisuwa wajen sarakunar da su ka hallaci taron da ma wanda basu samu damar zuwa ba suka aiko da Waziransu, tafiya suke cikin natsuwa da man Gimbiya Hakima ba daga baya ba wajen iya tafiya shima Yarima Annas ba'a barshi a baya ba.



Sunje gun ko wani sarki sun kai gaisuwa, ki wani sarki da kyautar da yake basu har suka zo wajen Sarki Abdulmatalak shine ya ba Gimbiya Hakima kyautar Mota shi kuma Yarima Annas ya bashi kyautar mota da gida.



Tunda Sarki Abdulmatalak ya ga Gimbiya Hakima ya ji yana san ya haɗata aure da Yarima Hakim, dan ya yaba da tarbiyarta da hankalinta yana yi ma Hakim sha'awar auren ta, dan haka ya gudurinma kanshi zai nema ma Hakim auren Hakima bayan an gama taro.



Bayan sun gama gaida manyan da ke wajen suka koma suka zauna, nan Sarki Abdulhadi ya tashi yayi bayanin ya kuma miƙa godiya ga manya baƙin da su hallaci taron.



Anci ansha an koshi sanann ko wani sarki ya kama gabanshi yana yi masu fatan alkhari, bayan ko ya watsa Sarki Abdulmatalak ya bukaci san yin magana da sarki Abdulhadi.



Bayan sun ƙara gaisawa nan Sarki Abdulmatalak ya fara magana kamar haka, "Abokina gaskiya ina mai ƙara taya ka murnan sosai, Allah yasa karatun da sukayi ya anfani al'ummar musulmai baki ɗaya."




"Amin ya Allah, nagode sosai Abokina dan kunyi man kara kuma naji dadi sosai, "haba ai yi ma kaine, ai wannan abun na taya murna ne, in tambayeka mana Abokina."?




"Sosai ma ina saurarenka yi man ko wace tambaya ce Allah yasa inada answer ɗinta."




"Da man ina san naji ko ka fidda ma Gimbiya Hakima miji, idan baka fidda mata ba muna bisa ga so dan zanso mu haɗa jini da kai, ina nemama ɗ'ana *YARIMA HAKIM* auren *GIMBIYA HAKIMA* amman idan ba'a rigamu ba."




Wani kallar farin cikine ya mamaye Sarki Abdulhadi dan daman yana da niyar yi ma Sarki Abdulmatalak maganar Hakima

Please Login or Register in order to submit comment