sanye da alqabba a jikin ta ta rufe kwalliyar ta,gaisawa sukayi sannan ta kawo masu kayan motsa baki.
"Wai ina yaran namu?"
Cewar Huzaifa.
Murmushi tayi tace.
"Ankaisu zumunci wajen su Ummu."
Jinjna kai yayi yace.
"Allah ya maidosu lfy."
Ameen ta amsa sannan takoma bedroom ɗinta.
*RUNO*
Jama'ar annabi ne tamkam kamar ba gobe inda aka gama ɗaura auren Huzaifa Abdullatib da Amaryar shi Hafsat Abu-Jalal haka aka gama ɗaurin auren Sarki Abu-Jalal ne keta hidima da manyan bakin su kowa najin daɗi musamman su Sarki MalikusSaif dake tsokar Ango Huzaifa shiko baki har kunne yakasa rufe shi.
da misalin karfe sha biyu na rana aka bada amarya gimbiya Hafsat ba karamar nasiha bace iyayenta sukai mata ba musamman Sarki Abu-Jalal da haka suka ɗunguma zuwa Masarautar Daborah,da misalin karfe ɗaya da rabi suka isa sashen gimbiya Salsabila aka kai amayar tasu inda gimbiya Zahara'u itama tasha ado ana jiran a ɗaura aure,suko anguma canza kaya sukayi inda Sarki MalikusSaif da Yarima Huzaifa suka saka kaya iri ɗaya blue black din yard ne sai Yarima Yazid da Yarima Lurwan su kuma sukasa Brown ɗin Yard ba karamin kyau sukayi ba direct wajen ɗaurin auren suka wuce lokacin kuwa angama haɗuwa ba tareda bata lokaci ba aka gabatar da ɗaurin auren Yarima Yazid da amaryar sa gimbiya Zahara'u sai kuma Yarima Lurwan da gimbiya Bilkisu, ba karamin murna sukayi ba da farin ciki ana ida ɗaurin auren suka ɗunguma sai wani kayataccen hall nan sukayi walimar farin ciki kowa yai sambarka dasa albarka, haka angunan suka wuce sashen Sarki Abdulmalik sukai tasu walimar ranar ko Huzaifa yasha zolaya da haka marece yayi sallar magrib sukaje sukayi,suko amaren anma kowa huɗuba dai dai gwalgwado sannan akai kai kowa ce amarya sashen mijin ta,cikin aminci.
Shiko Sarki Malik abokin anguna saida ya tabbatar da yakai kowane ango ɗakin amaryar shi,sannan shima ya tafi wajen sahibar shi.
Washe gari da safe kuwa komai yataima amaren yanda ya kamata kowace sai sambarka domin sun kai ƙimar su ɗakunan mijin su cikin aminci,haka akai masu kyautuka kamar yanda al'adar Masarautar take kowa sai farin ciki yakeyi.
Bayan sati ukku Yarima Yazid ne da amaryar shi gimbiya Zahara'u sai Yarima Huzaifa da gimbiya Hafsat sai Yarima Lurwan da amaryar shi gimbiya Bilkisu suka tafi sashen Sarki MalikusSaif suna shiga suka iske shi tareda iyalin nashi,cikeda farin ciki ya tarbi abokan nashi suka zauna aka hau fira ta abokai hakama matan nasu suma waje suka samu cikin falon Gimbiya Bahijja suka wuce bayan sun gaisa aka hau fira cikin jin daɗi da kaunar junan su,kai kace ba wata matsala data taba shiga tsakanin su,musamman Bahijja da gimbiya Zahara'u sai fira suke tamkar yan uwan juna dan kan matan su a haɗe yake kowa nasan ɗan uwan shi cikin aminci.
Hakama wajen mazajen nasu sai fira suke suna nishaɗi,daga bisani matayen nasu suka gyara masu wajen cin abinci, haka sukaci suka sha kowa na farin ciki,basu sukabar gidan Sarki Malik ba saida akayi isha'i sannan sukayi sallama kowa ya koma sashen shi cikin farin ciki.
Haka rayuwa ta kasance a cikin Daborah cikin aminci komai yana tafiya dai dai yanda ya kamata.
Bayan Shekara biyar zuwa lokacin ya'yan Sarki MalikusSaif sun girma sunyi wayau sosai,danko gimbiya Fatima sashen kakarta Binta can take rayuwar ta, tayau da kullin saidai takaima iyayen ta da kakarta ziyara danko itada ɗan uwanta Yarima Abduljabbar ba karamin shakuwa ce ta shiga tsakanin su,kansu a haɗe yake.
Yau kamar kullin gimbiya Fatima ce a sashen kakarta Sarauniya Zulaiƙa sai zuba take mata tana shagwaba itako Sarauniya sai ririta yar lelen tata takeyi sallamar Yarima Hassan suka tsinkaya ya shigo hannun rike da Zainab yar Yarima Yazid gudan hannun shi kuma Jalal ne ɗan Yarima Huzaifa atare suka zauna wajen kakar tasu suka fara fira, itako Sarauniya Zulaiƙa sai farin ciki takeyi tana ganin jikokin nata, hadiman Sarauniya ne suka kawo masu kayan marmari suka aje agaban su, haka sukaita yima Sarauniya fira,tana ta biye su suna cikin firar sai ga Saifulislam ya shigo shima zama yayi akaci gaba da firar dashi,cikin aminci.
Haka rayuwa tai ta wanzuwa a cikin Daborah komai yana tafiya yanda yaka mata ta kowa ne fanni komai ya daidai ta musamman rayuwar bayi da suka gama yarda cewa Bayima 'Ya'yane zuwa yanzun sun samu cikakken ƴanci a cikin Masarautar dan ba kaɗan sukejin daɗin mulkin Sarki MalikusSaif da adalar matar shi Gimbiya Bahijja wadda tazama fitila mai haskawa a cikin zukatan bayin Daborah da sauran talakawa harma da masu mulki.
_*END✍🏻*_
_*Tammat Billahi,Alhmdullh nima Jameey na amince cewa*_ _**Bayima*_ _*Ya'yane**_ 🥰
_Laifin daɗi karewa anan na dasama wannnan labarin aya na *Bayima* *Ya'yane* _inafatan Allah ya gafarta mana da iyayen mu da dukkkan ɗaukakin al'ummar musulmai Allah yasa mucika da imani_ 🙏
*_Fatan alkhairi masoyana abin alalfaharina_* 🥰
*Kardai ku manta* 👇
_Yar Mutan Kankia ce❣️_
Share
Comment
And
Vote
❣️
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 46 Chapter of 46