Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

K'ara mata lafiya.



"Hydar najika shuru game da zancan da nayi maka kwanaki akan Khairat ko baka amince bane?".





"Fatima ba amincewa ce banyi ba a'a inason kisani ko wanne namiji yana da irin kalar macen da ya keso wlh Inna b'oye miki bazan b'oyewa Allah ba Khairat bata d'aya daga cikin irin matan dana keso ya kamata ki fahimceni".



"Hydar zama na kusanci tsakanin ma'aurata yana sawa su shak'u da juna musamman in d'aya yana son d'aya, Khairat na sonka matuk'a Hydar meyasa bakason farin cikina?, bayan na shaida maka Khairat itace farin cikina".





"Fatima me nayi miki haka da yasa kika sadaukar da soyayyata da rayuwata domin farin cikin y'ar uwarki?, meyasa ni ba kya son nawa farin cikin?,meyasa kika amshi soyayyata bayan kinsan a k'arshe yaudara ta zakiyi?, meyasa Fatima?".



"Kai me bada labarine game da irin son da nake maka,wanda kasani ko da wasa bazan so na rasa ka ba ka d'auki haka a matsayin k'addara Hydar kamar yadda nima na jima da d'auka,ka amshi y'ar uwata a matsayin masoyiyar ka, faruwar hakan ba yaudara bace Hydar illah wani abu dana barma cikina,Hydar na had'aka da girman Allah kafito a d'aura muku aure da Khairat in har da gaske kake son farin cikina".





"Naji zancanki Fatima kuma na gamsu da bayananki Allah yasa haka shi yafi alkha'iri,amman ki sani wlh banason Khairat zan aure ta ne don faranta miki rai koba komai zanji a raina nayi miki abinda yasaki farinciki,auranta dazanyi baze hana nan gaba innaga wacce nakeso ko a ina bane na kasa auranta,sabida don farin cikin ki na aureta nan gaba zan auro farin cikina,na amince da auran Khairat Fatima domin farin cikinki".





"nagode Hydar Allah yasa hakan yazama silar d'orewar zumun cinmu har abada nagode sosai".





"yaushe kike so nafito ayi auran".



"In so samu ne nanda sati biyu nakeso sabida iyayenmu sun matsa kafito d'in dan a had'a da nawa auran".



maganar jinta Hydar yayi kamar durar aradu akansa daurewa kawai yayi yace.





"To shikenan Fatima zanyi yadda kikeso Allah yabaki zaman lfy keda mijinki Allah yasa yabaki kulawar da nake mafarkin baki,se anjima yanzu ina Abuja ne gobe week-end zanzo dan mu gaisa dasu Abba nagode".



Godiya Fatima tayi mishi sosai sannan suka yi sallama.





Khairat kuka tasa sabida duk maganar da sukayi a kunnenta domin hands-free Fatima tasa,rarrashinta Fatima tayi tace.





Ki dage da addu'a Sis k'iyayyar Namiji is not easy In sha Allahu zaki ci nasara a kanshi tunda kina sonshi zakiyi hak'urin zama dashi kibarwa Allah lamuranki.



Godiya Khairat tayiwa Fatima sosai, maganar k'inta da Hydar yace yanayi tasan data aure shi zata koya masa sonta ita wannan be dameta ba, ita de burinta ya amince ze aureta tunda ko ya amince komai me sauk'i ne.





Haka ko akayi washe gari Hydar yazo suka gaisa da iyayen su Fatima, har gidan Grany aka kaishi ya gaishe ta,ya kuma basu tabbacin gobe wakilanshi zasuzo nema masa auran Khairat.



Fatima tafi kowa murna da Hydar ya cika mata alk'awarin da ya d'aukar mata.



Khairat ko ay baki yak'i rufuwa don murna,Hydar ko da Fatima kad'ai ya gaisa yawuce abinsa ko ta kan Khairat be biba.



washe gari iyayen Hydar suka zo neman auran Khairat, aka basu batare da b'ata lokaci ba sabida ba wani bincike da zasuyi akan Hydar,duk wani halinshi bawanda jama'a basu sani ba sabida shi ba b'oyayye bane,a take aka yanke musu sadaki dubu d'ari suka biya inda aka tsaidar ranar auran nan da sati biyu masu zuwa.



wayyo Khairat har ruwa ta zuba a k'asa tasha domin cikar burinta.



Umman Khairat gyara Fatima takeyi da magunguna masu kyau na mata ko takan Khairat batayi,har tausayin Khairat Fatima takeji,ga me gyaran jiki da ta d'auko mata tana gyarata kullum.



Umman Fatima lura tayi ba'a yiwa Khairat gyaran se ta d'auka kara ce Umman Khairat d'in takeyi shiyasa itama ta fara gyara Khairat d'in bada wasa ba, har me gyaran jikin itama ta d'auko mata tana yi mata,hakan yama Khairat dad'i da ko har kuka takeyi.





lokacin biki se k'aratowa yakeyi kamal kamar ze lashe Fatima dan kulawa,ita ko Khairat angon na Abuja ko awaya be tab'a nemanta ba.



Ana saura sati d'aya biki aka kawo lefen Khairat kaya na gani na fad'a,akwati goma sha biyu aka yi mata babu ce kawai babu acikin kayan.



Fatima akwati shida Kamal ya mata da kansa dan ya hana iyayensu suyi masa dan ganin hidimar dake gabansu,ba laifi yana da rufin asirinsa daidai gwargwado k'aramin ma'aykaci ne a nufanari dake kaduna.



Sadakinta shima dubu d'arin ya biya iyayensu se albarka suke sa masa.





Maman yusuf.

[4/26, 10:10] Zahra Surbajo: 📓📓📓📓📓📓📓📓📓

*CIN AMANA KO FANSA*

📓📓📓📓📓📓📓📓📓





Zahra Muhammad mahmud





*Please mosoyana kuyimin afuwa abisa rashin jina da kukeyi akan kari kuyimin uzuri.*





*Dedicated to all writers of pure moment of life writers group,loves you all from the bottom of my inner heart,thanks for the care and support am really appreciate.*



*pure moment of life is group*

*pml*





*page 15-16*







Cike da matsanancin mamaki Fatima take kallon Yaya Kamal har ya samu guri yazauna.



"Nasan zakiyi mamakin jin Kalamaina,ba abin mamaki bane My Sister Umma tasanar dani duk abinda Khairat tamiki wanda kaf family bawanda yasani daga ni se ita,banji dad'in abunba sam Khairat ta b'ata wayonta amman ba komai kanta tawa,ni na rok'i alfarmar Umma tasa su Abba su aura minke a matsayin Matata ta aure,najima da sonki a zuciyata Fatima nak'i bayyana miki ne gudun kar kije ki fad'awa Khairat ku taru ku raina ni,amman wlh ni me k'aunar kine nayi alk'awarin kulawa dake zuci da fili pls ki amince da Yayanki amatsayin wanda yafi kowa sonki",ya fad'i har yana durk'usawa a gabanta.



Fatima ba baki ta sakiba harda ido da hanci sabida tsananin mamakin abinda ke faruwa yanzu a gabanta,inde ba mantawa tayi ba to zata iya k'irga maganar data tab'a shiga tsakaninta da Yaya Kamal sabida shi mutumne miskili ga son girma kamar tsiya sam baya shiga harkar da bata shafeshi ba mutumne shi me aji wanda ko kad'an baya son raini.



shiyasa abin yay matuk'ar bata mamaki ganinshi tsugunne a gabanta yana rok'on soyayyarta,jikinta na rawa ta tsuguna itama a gabanshi tace.





"Yaya inajin kamar mafarki nakeyi nagaza gasgata wannan al-amari pls in wasa Kake min don Allah kadena".



hannunta ya riko yana murmushi yace.



"Sister ya kamata kisan irin wasan da Yayanki ze iya yimiki da wanda baze iyaba,koda ace wasa zanmiki bazanyi a gaban Mahaifiyarmu ba sabida sanin darajarta, iya gaskiyata na sanar dake".



Kukane ya kubce mata tashiga yinshi me tsuma zuciya,kamal runtse idonshi yayi yanajin kukannata yana tab'a mishi zuciya,rarrashinta suka shiga yi shida Umman har seda tayi shuru sannan ta iya bashi amsa.



"Yaya nagode da wannan karramawar da kamin na Zab'ata da kayi nazamo abokiyar rayuwarka, nayi farinciki da kasancewar hakan koba komai kai jinina ne na amince da wannan soyayya Allah yasa ace gwanda da akayi,yabamu zaman lafiya da kwanciyar hankali nagode sosai".



"Alhamdulillahi nagodewa Allah da ya nunamin wannan lokacin, ba tun yauba nake sha'awar aure a tsakaninku to Allah be kawo lokacin ba se yanzu, Allah ya baku hak'urin zama da Juna nagode muku a bisa wannan farinciki dakuka sani wanda nasan kaf dangi zasuyi irinsa,ku tashi kuje Allah yayi muku albarka",Umma ta fad'a fuskarta na nuna tsantsar farin cikin datake ciki.



Mik'ewa sukayi suka mata sallama suka fice a d'akin har d'akinsu na nan gidan kamal ya raka Fatima sannan yace mata.



"Oya shiga ki kwanta ki huta banason kiyi tunanin kowa se nawa inkuma kikayi wuta balbal anjima da yamma zanzo muyi hira kinji Baby na",yafad'i cikin salon jan hankali da tsantar nuna kulawa.



Abin dariya yaba Fatima jin kalmar wuta balbal d'in da yace shi yafi komai bata dariya bata iya bashi amsaba domin nauyinshi takeji shigewa d'akin tayi da gudunta,murmushi Kamal yayi ya wuce shima.



Fatima tana shiga d'akin kan gado ta haye ta rushe da wani kuka me tsuma zuciya,"meyasa Khairat zaki tarwatsa farin cikina?, me nayi miki me zafi har haka dakikaga Ta hakane kawai zaki rama?,kinsan inason Hydar irin son da Uwa takewa D'anta amman lokaci guda kika wargaza wannan soyayyar why Khairat?",sune kalaman da Fatima ke furtawa cikin kuka.



Tana son Hydar amman yanzu yazamar mata dole tacire sonshi a ranta tasa na Yayanta me burin faranta zuciyarta,da wannan tunanin bacci yay awon gaba da ita.



Umma ko Abba nadawo wa taje ta sameshi da zancan auran Kamal da Fatima,ba k'aramin farincikine ya kama Abban ba, dan haka mik'ewa yayi yanufi gidan Abban Fatima yayi masa albishir,sabida dad'in da zancan yayiwa Abban Fatima rungume yayannasa yayi yana me jin dad'i, daganan gidan Grany suka nufa itama taji dad'in faruwar hakan inda tabasu shawarar to ayiwa me neman Khairat magana ya fito ayi rana d'aya.



A wunin ranar gaba d'aya zancan auran Fatima da Kamal yagama zagaya dangi kowa se fatan alkha'iri yake musu.



Umman Fatima da taji zancan har kuka tayi na nuna farincikin ta,dan tasan tabbas Fatima tayi dace da miji nagari na nunawa mutane sabida kamal yarone me tsananin tsaron Allah,tayi imani tsoronshi ga Allah baze bari ya cutar da Fatima ba,har gida tasamu Umman Khairat tayimata Allah yasanya alkha'iri.



Khairat sanda labarin yasameta kasa zaune tayi,ranta yay matuk'ar b'aci ba taso hakanba,tasone ace seta riga Fatima aure har seta haihu sannan Fatima ta yi amman se gashi Yayantama uwa d'aya Uba d'aya zata aura.



Se k'arfe biyar na yamma Fatima ta tashi daga baccin, wanka tayi tayi sallah sannan ta zauna a gaban mirror tana kwalliya.



Kamal ne yay sallama ya shigo d'akin dan beyi zaton ganinta a haka ba, daga ita se tawul da gudu ta Mik'e ta haye kan gado ta k'udundune acikin bargo jikinta se rawa yakeyi.



murmushi yayi yace,"oh am sorry Baby bansanibane in kin shirya kisameni a falo ina jiranki".



da kyar ta bud'e baki daga cikin bargon tace, "to".





Maman Yusuf

[4/26, 10:10] Zahra Surbajo: 📓📓📓📓📓📓📓📓📓

*CIN AMANA KO FANSA*

📓📓📓📓📓📓📓📓📓





Zahra Muhammad mahmud





*pure moment of life writers*

*pml*





*page 21-22*





Tafe suke bame cewa kowa komai,se y'ar satar kallo sukeyiwa juna.



Carab Hydar ya kamata tana kallonshi duk kunya tabi ta kamata,muryarshice ta dawo da ita seti.



"Allah de yasa baki da maita bayan kwacen masoyi",ya fad'i batare da ya kallo inda take ba.



Ranta ya b'aci dajin zancannashi amman tasan dole dama zata fuskanci irin hakan daga gurinshi,dan haka dole seta zama me hak'uri kamin taci riba murmushi tayi tace.



"Ay sede kar a kuma amman inde maita ce tonice shugaba a wannan fannin kuma duk Wanda na kama sena tabbatar dana lasheshi nake k'yaleshi",ta fad'i cikin muryarta me d'aukar hankali duk wani me sauraronta.



Waigowa Hydar yayi yana kallonta ayko ta haskeshi da fararan idanuwanta datayi fari dasu,kan motar ne yakusa kwacewa a hannunshi da sauri yamaida kallonsa kan titi sannan yace.



"Ashe ko kin had'a kanki da wahala dan inde Hydar ne ba maita ba kukar bulukiya ma taci ubanta, sede ki ganni ki k'yale wlh,ni nafi k'arfin wannan maitar taki".



"Honey kenan ay ba'asan maci tuwo ba se miya ta k'are,kuma bakasan inda rana zata fad'i ba".



"Karki sake kirana honey d'inki sunana Hydar in baki iya fad'a ba ma kice Aliyu,Rana kuma ta gabas take fitowa ta fad'i ta yamma,kuma banajin akwai wata rana da Kare yake da ita data wuce ta haushi kamar yadda kikeyi yanzu".





maganganun sun doketa shiyasa bata sake cewa komai ba har suka k'araso gidan.



kyau da tsarin gidan shi ya k'ara rikita Khairat aranta tace, "wai wai wai dank'ari wai gidan iyayensa kenanma inaga gidanshi kuma".



k'arasawa falon gidan sukayi,Hajiyar na zaune ita dasu Haisam suna kallo,da gudu yaran suka nufi daddyn su suna kiranshi rungumesu yayi ita kuma Hajiya tasowa tayi ta rungumi Khairat tana fad'in, "sannu da zuwa y'a ta".



Khairat ko se rurrufe fuska takeyi alamar jin kunya,tsugunawa tayi ta gaida Hajiyar,yaran Hydar d'in suma suka gaisheta,nan Hajiya tasa aka cika mata gabanta da kayan lashe-lashe,kasa cin komai tayi se nonnok'ewa takeyi wai kunya.



Hydar ji yayi kamar ya doketa dan takaici,yanzufa suka taho tana mishi rashin kunya amman shine dan munafunci wai yanzu kunya takeji,k'wafa yayi yawatsa mata harara a fakaice gudun kar Hajiya ta gani amman ita wacce akayi dominta ta gani.



Y'an uwansu ne suka shigo falon da yake suma nan y'an bikin sun taru,nanfa suka shiga tsokanarta da yake yawancinsu abokan wasan Hydar d'inne,Khairat rasa inda zatasa kanta tayi, Hajiya kwab'arsu take amman ina kamar ta zugasu kowa se son cusa kansa yakeyi a gurinta.



Hydar Hajiya tacewa.



"Wlh Hydara ka d'auke matarka a gurinnan kamin su kurmanta maka ita, irin wannan hayaniya haka ay se kunne yasamu matsala".



Da k'yar ya samu ya isa inda take d'agota yayi,ayko nanfa suka fara yimusu gud'a,khairat ko k'ank'ame Hydar d'in tayi gudun karsu ruk'ota a haka har ya fice da ita b'angaren Hajiyar,part d'inshi na gidan ya kaita suna shiga ya k'wace jikinshi anata,itako se ware ido takeyi sabida tunda take bata tab'a jin hayaniya irin ta yau ba kamar zasu cinyeta,ita abun har haushi yabata duk sun gama dak'una mata jiki.



"Jita don Allah kamar tsohuwar munafuka se wani zare ido kikeyi to wlh karki sake inji wani acikinsu yayi ciwon kai, dan yadda kike zare idanuwannan alamu ne na maitar ki tafara motsawa to wlh kul".



Hawaye ne suka zubo mata na takaici da k'yar tace.



"Don Allah kamai dani gida ay mungaisa da Hajiyar pls"





"Ba yanzu zan maidakeba sekun gaisa da Alhaji dan ya kusa dawowa,keda kika fito yawon maita menene naki nason komawa gida da wuri?".



Bata bashi amsaba illah samun guri da tayi ta zauna.shima ficewa yayi daga d'akin,part d'in Hajiya yanufa yasamu wata acikin y'an uwan nashi yace ta kwashi kayan abincin da aka kawowa Khairat takai mata part d'inshi, ayko nanda nan takwasa takaimata.



Hajiya ko bin Hydar tayi da kallo fuskarta d'auke da murmushi tace, "wlh Hydara na ka iya zab'en mata Allah yasa yadda take Da kyau na zahiri yasa har bad'ini haka take, Allah yabaku zaman Lafiya da hak'uri da juna".



murmushi kawai yayi bece mata komai ba, sema kawar da zancan da yayi da cewa,"zuwa anjima zan maida ita gida sabida muna jiran Alhaji ne yadawo su gaisa".



"Gaskiya ka kyauta, yanzu kaje kasa ta taci abincin inta gama seka dawo da ita nan tunda nasamu na kad'asu cikin gida masu hayaniyar".



"To Hajiya bari naje",ya mik'e yafice daga falon,part d'inshi yanufa inda yasamu Khairat se share k'walla takeyi.



K'arasawa yayi inda take yaga bata ci komai ba acikin abincin,be cemata komai ba yad'ebo abincin yanufo bakinta dashi,da sauri ta d'ago ido tana kallonshi gyad'a mata kai yayi ba musu ta amshi abincin,haka yadunga bata har taji ta k'oshi sannan ta kawar da kai.



Bakomai yasa Hydar yayi mata haka ba, illah shi mutum ne da baya son ganin mace na kuka yanzu hankalinshi ze tashi musammam ma ace shi yasata kukan, shiyasa yanzu ya rarrashi Khairat ta wannan sigar,duk da ranshi besoba amman de ya daure.



iyayensa sun had'a mata shatara ta arzik'i sannan ya d'auko ta ya dawo da ita gida.



suna zuwa tun kamin ya gama parking tasoma k'ok'arin bud'e k'ofar motar amman se taji a kulle take,har seda yayi parking Ya kashe motar ya waigo yana kallonta itama shi take kallo,yace.





"Na b'ata miki rai ko? am sorry bada son raina nai miki hakan ba, dan ba halina bane sa mutum b'acin rai laifinki ne da kika tursasa y'ar uwarki wajen ganin ta bar miki ni wanda kinsani ita nakeso itama kuma ni takeso, amman sabida biyan buk'atarki ke kad'ai kinsa mun haramta ga juna, duk abinda namiki ki kuka da kanki ba Hydar ba".





zatayi magana ya dakatar da ita ta hanyar d'aga mata hannu sannan yace.



"get out from my car I need to go".



Jiki a sanyaye ta fito daga motar bayan ya mik'a mata tsarabar da aka bata a gidansu,yaja motar yabar gurin.





Da murna Fatima ta tarbeta itama Khairat d'in haka dan b'oye abinda ya mata tayi nan suka d'unguma d'akin Maman Fatima anan aka bud'e tsarabar.





*RANAR BIKIN*





Ko ta ina in ka duba jama'a ne birjik wa'inda suka halaccin d'aurin auran.



Y'an majalisu, sanatoci, ministoci, da tawagar shugaban k'asa kowa yazo d'aurin auran.



Inda aka d'aura aure lafiya jama'a se fatan alkaha'iri akewa angwaye da amare.





Taro yayi taro inda k'arfe hud'u aka wuce dinner amare sunyi kyau har sun gaji haka suma angwayen anci ansha anyi godiyar Allah inda k'arfe takwas na dare taro ya watse.



Tara daidai aka Kawo motocin d'aukar amarya Fatima sabida ita kad'ai za'a kai ranar,ita Khairat da yake Abuja ne se gobe da safe za'a tafi da ita.



kuka Fatima da Khairat sukeyi kamar anmusu mutuwa, kowa a y'an biki seda ya tausaya musu sanda aka kai Fatima gurin umman Khairat taimata fad'a bayan tagama yimata fad'anne Fatima ta rik'e k'afarta tana kuka take nemarwa Khairat yafiya, sosai take kuka da yake su biyu aka bari a d'akin sauran mutanen suna waje seda Fatima tajima tana rok'on Umman, tausayin Fatiman ne yasa Umman tace ta yafewa Khairat d'in,Allah ya musu albarka duka.



Da kyar aka b'anb'are Khairat a jikin Fatima,se yanzu Khairat take danasani na gasken gaske,se yanzune soyayyar Fatima ta gasken gaske ta kamata,kuka take kamar ranta ze fita tana sake neman gafarar Fatima a haka har aka wuce da Fatima gidanta dake unguwar dosa GRA dake kaduna tana kukan rabuwa da gida.





Maman Yusuf.

[4/26, 10:10] Zahra Surbajo: 📓📓📓📓📓📓📓📓📓

*CIN AMANA KO FANSA*

📓📓📓📓📓📓📓📓📓





Zahra Muhammad mahmud





*pure moment of life writers*

*pml*







*page 19-20*









Lokacin bikin se matsowa yakeyi,ta kowanne b'angare shiri suke bana wasaba.



Mahaifiyar Hydar ko kiranshi tayi awaya tana ta fad'a akan be kawo mata surukar tata sun gaisaba,hak'uri ya dunga bata akan insha Allahu gobe ze kawo mata ita.



Suna gama wayar ranshine yay mugun b'aci akan umarnin mahaifiyar tashi duk abinda ze had'ashi da Khairat gudun shi yake gashi yanzu tace ya kawo mata ita.

Fatima yakira a waya bayan sungaisa yace.



"Don Allah kisa k'anwarki ta shirya gobe da k'arfe biyar na yamma zanzo muje da ita gurin Hajiyata,ta matsamin se na kawota sun gaisa".



Dariya Fatima tayi sabida yadda Hydar yake maganar kamar zeyi kuka,da kyar tace.



"To Hydar ay ita zaka kira ka fad'amata,ko in kunyi auranma nice y'ar sak'onku?, nide wlh bazan fad'a mata ba,ka kirata da kanka mana".





"Oh my God,Fatima bazaki ganeba wlh hakan dana keyima dauriya kawai nakeyi domin naga nasaki farin ciki,kinfi kowa sanin ko number d'inta bani dashi taya zan kirata?".





"wannan me sauk'ine Hydar nagode da irin wannan k'auna da kakemin,kaci gaba dayin dauriya wata rana se labari,zancan rashin number d'inta kuma zan turo maka yanzu seka sanar da ita".



Sallama sukayi,sannan tayi masa text d'in number Khairat.





Koda yaga text d'in number ji yayi Ranshi ya sake b'aci don gani yake kamar Khairat d'in yake gani,be kirata ba text yatura mata kamar haka.





_"gobe da k'arfe biyar na yamma ki shirya za muje gidan hajiyata zaku gaisa,y'ar wahala Kawai"._



Sanda sak'on ya samu Khairat mamakine ya kamata tarasa waye ya turo mata wannan sak'on don bata da number,gurin Fatima taje ta nuna mata sak'on,Fatima bataji dad'in kalmar Hydar ta k'arshe ba amman yata iya, duk wanda yasai rariya dole yasan zata zub da ruwa,jiki a sanyaye ta fad'awa Khairat sak'on daga Hydar ne.



Murmushin takaici Khairat tayi sannan tace,"yanzu shine baze iya kirana ba sede yamin text sabida bayason jin muryata?".



"hak'uri zakiyi kita addu'a Allah ya tausasa zuciyarsa ku zauna lafiya".





Haka Fatima taci gaba da tausasa Khairat har ta mance da b'acin ranta amman ji take a zuciyarta ko kullum da naman jikinta za'a dunga miya a gidanshi zata jure zama dashi tunda tana sonshi uwa uba ga hatimin nasara, itama tasha alwashin yin hak'urin da kowacce mace takeyi domin samun nasara.





Washe gari da wani farin ciki Khairat ta tashi sabida yau zata sa Hydar a idonta bama hakaba yau har anguwa zasuje tare wannan ya haifar mata da farinciki mara misaltuwa dan yanzu ne tak'ara yarda tafi Fatima agurinsa Tunda be tab'a fita da Fatima ba se ita.



More than one hours ta kwashe gurin kwalliya,shafa wancan goga wancan,har seda Umman Fatima tace ta barshi haka,haka gurin zab'ar kayan sawa ma ruwan ido ta zauna yi harde Umman Fatima ta gaji ta zab'o mata wata doguwar riga sky color and'an yimata ado da pink d'in flowers,d'inki ya zauna mata kasancewar ta kyakkyawa, takalmi da jaka da gyale duk pink ne haka d'ankwalin data d'aura akantama pink ne,b'arin turare Umman Fatima taimata.



wayyo duniyar kyau.



Kyan da Khairat tayi wlh duk k'iyayyarka da ita seta burgeka kuma dole ka fad'i tayi kyan ko baka fad'i a fili ba zaka fad'i a zuciyarka.



Fatima ma datazo taganta kirari tashiga yimata,da zuzuta irin kyan da tayi,to dama Khairat ba baya bace gurin kwalliya ta iya kwalliya kamar wata makeup artist.



Hotuna Fatima tashiga d'aukar ta a wayarta kala-kala,har zuwa sanda Hydar ya iso.



Cikin gidan kamal ya shigo dashi ya sake gaisawa da mutane,da yake y'an biki sunfara zuwa nan aka shiga tsokanarsa ana ga Ango shide Hydar yak'e kawai ya keyi dan gefen kumatunshi har sunfara yimishi ciwo, da kyar ya samu ya fice daga gidan sannan Kamal yaje yace ma Khairat ta fito su tafi,jan kunne sosai Umman Fatima tai mata akan ta tsare mutuncinta,itako Umman Khairat sanda taje yimata sallama ko kallon inda take batayiba jiki a sanyaye ta baro gurinta tazo tasa Fatima a gaba wai tarakata gurin motar,itako Fatima dariya ta keyi sosai duk da a zuciyarta wani d'acine ke tasowa na kishi amman koda wasa bata bari ya bayyana akan fuskarta ba,duk yadda Khairat taso Fatima ta rakata k'i tayi dole ta hak'ura ta tafi ita kad'ai.



Tunda ya hangota tana tahowa ya shagalta da kallonta,tabbas Khairat me kyau ce irin kyan da duk k'iyayyarka da ita inka kalleta seka k'ara.Ga ta akwai iya taku don in tana tafiya tamkar me tausayin k'asa.





Tana k'arasowa ta bud'e gidan gaba ta shiga,wani ni'imtaccen k'amshine ya bugi hancin kowannensu,ba abinda yafi basu mamaki irin shigarsu domin shima shaddace me ruwan sky color a jikinshi har hula da takalmi agogon shine kawai silver.sosai abun yabasu mamaki amman shi Hydar haushin hakan yaji itako Khairat wani dad'i ne ya ziyarci zuciyarta.





tana zama ko gama rufe k'ofar bata yiba yaja motar suka bar harabar gurin.







Maman Yusuf.

[4/26, 10:10] Zahra Surbajo: 📓📓📓📓📓📓📓📓📓

*CIN AMANA KO FANSA*

📓📓📓📓📓📓📓📓📓





Zahra Muhammad mahmud







*pure moment of life writers*

*pml*





*page 23-24*





Ankai amarya gidanta lafiya kuma y'an kai amaryar basu jimaba suka juyo,suka barta ita kad'ai se kuka takeyi abin tausayi fuska da idanunta duk sun kumbura sabida kuka.



Tawagar ango ne da abokanshi suka shigo gidan se barkwanci sukeyi.



A falo suka zauna sannan Kamal yanufi d'akinta domin kiranta su gaisa da abokansa.



A kwance ya sameta ta k'udundune jikinta acikin lafayar da aka nad'eta aciki,se sautin kukanta yake ji kad'an kad'an.

Da saurinsa yak'arasa kan gadon ya d'agota a hankali ya rungume be cemata komai ba itama batayi k'ok'arin kwace jikinta ba,shafa bayanta yashigayi alamar rarrashi yana hura mata iska a kunne.



Tun tana kukan har wani baccine yaso kwasheta dan tuni ta manta kuka take, a hankali ya rad'a mata akunne.





"Wake up baby is too early, kizo muje kugaisa da friends d'ina kinji,inmuka dawo sekiyi baccin pls".



Da kyar ta yarda ta sakko akan gado shida kanshi ya k'ara gyara mata lafayar sannan yaja hannunta suka nufi falon.



Kamar de yadda kuka sani,shegan taka da akeyi gurin siyan baki itace ta faru suma anasu daga bisani sukayi musu addu'ar samun dawwamamman zaman lafiya tare da zuri'a d'ayyiba.Rakiya ya musu daganan ya rufe gidan sannan ya dawo,k'ofar falonma rufewa yayi dayake gidan two bedrooms plat ne.



A d'aki ya sameta duk tayi wani tsuru tsuru abin yakusa bashi dariya amman ya maze,sata yayi tayo alwala shima yayo yajasu Jam'i, raka'a biyu domin nuna godiyarsu ga Allah daya nuna musu wannan rana.



Bayan sun idar ledar kajin dasuka shigo da ita yajawo musu gamida fresh milk me sanyi da ruwan faro,kitchen taje ta d'auko musu plate da kofuna sannan ta dawo shi ya juye kajin a plate d'in sannan ya tsiyaya musu fresh milk d'in.



Sam ta kasa sakin jikinta taci dan haka jawota yayi jikinshi yashiga bata da kanshi yana mata kalamai masu dad'i a haka har ta k'oshi sannan shima ya maida hankali yaci, d'aukar sauran yayi yakai kitchen da kanshi sannan yadawo yajata zuwa toilet sukayi brush.

Bayan sun fito kyaleta yayi ya nufi d'akinshi domin yayi wanka ya sauya kaya.



Itama yana fita gudu gudu sauri sauri ta cire kayan jikinta ta fad'a toilet domin tayi wanka,dan tana ganin har ta fitoma be dawoba dan ta d'auka irin masu shekara a toilet

Please Login or Register in order to submit comment