Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ta dace da kayan.  Tunda idanunsa suka sauka akanta, ya kasa daukesu, daskarewa ya yi a wajen kawai don  ya yi kamar zuciyartasa ma tsayuwar ta yi. Haka har ta k'araso wajenshi ta tsaya gefe tana wasa da jelar mayafin. Yasa hannu ya dago ha6anta, idanunsu cikin juna sannan ya kauda hannunsa.   "Kinyi kyau matuk'a."   Ta lumshe ido gami da kauda kanta cikin bugun zuciya mai sauri. To Faruk ina wani kyau a wajenta idan aka had'asu? Gaba daya ganinta ta keyi wani tsami akansa, ta k'ara raina ajinta kwata-kwata, har ta hangowa kanta irin kyamar da za'a nunamata yau. Watakil ma su Ihsan su yi mata dariya. Idanunta ya yi kwal-kwal. Hannu ta ji yasa ya janyo mayafinta ya dan rufe kusan rabin fuskarta da shi.   "Muje." Ya yi maganar cikin dusashshiyar murya. A hankali suka soma takawa, Faruk shi kansa dakewa yakeyi don ba shi da yak'inin samun goyon baya, yana dai ji a jikinsa kawai zai yi nasara idan Allah Ya so.   Haka har suka shigo falon Hajiya, babu kowa, daman hakan yafi buk'ata, yasan a wannan lokacin Hajiya na sashen Daddy, kai tsaye kofar zuwa sashen Daddy ya shige. Anan kofar falon ya dakata gami da umartar Ummi da tsayawa anan. Ba musu ta tsaya, ta bishi da kallo har ya shiga da sallamarsa, kirjinta ta dafe jin irin yanda ya ke bugu fiye da baya, addu'o'i kawai ta ke karantowa.    Daddy da Hajija suka amsa sallamar dan nasu fuska a sake.      Ya karasa yana taku a kasaitance ya zauna a gefen kafafun Daddy ya gaishesu. Suka amsa suna k'are mishi kallo. Daddy ya kasa hak'uri ya tofa.   "Wai ni kodai wajen surukartawa za ka tafi ne? Wannan ado haka?"   Ya shafi k'eyarsa da murmushi saman fuskarsa, Hajiya na dariya.   "Daddy na je na dawo, kuma tare muke da ita ma yau za ku ganta."   Sai Hajiya ta hau salati. "Kai Sadaukina, haka kuma akeyi babu sanarwa? Maimakon ka fad'amin a shirya?"   "To yanzu dai ai magana ta k'are tunda daman ya sanarmana a satinnan zai kawota, kinsan halin d'annaki komai nashi daban ne."   Cewar Daddy yana duban matarsa kafin ya maida dubansa ga Faruk.   "Tana ina ne?" Faruk ya dubesu, su dinma shi suke kallo fuskokinsu a sake. Hakan ya k'ara mishi wani k'arfin gwuiwa, ya mik'e tsaye ya nufi hanyar waje.    Ya dubi Ummi wacce ya tabbata a rud'e ta ke.    "Addu'a zakiyi, Allah na tare da mu." Ya fada cikin muryar rad'a. Ta gyada mishi kyau kafin ya bata hanya. "Bismillah."   Dagowa ta yi ta dan bude fuskarta ta dubeshi kamar zata yi kuka, ya jefeta da kallo mai sanyaya jiki, dole ta maida ta rufe fuskarta sannan ta saka k'afa da sallama, shima ya biyo bayanta. Iyayen suka amsa fuskarnan a sake, suka zuba mata ido har ta k'araso ta zauna, Hajiya dai gani ta ke kamar muryar da kuma tafiyar ba yau ta soma ganin irinta ba. Ta dai danne, ta amsa gaisuwar surukarta ta wacce ke ta bad'ad'a k'amshi. Kafin su kai ga tambayar wani abu, Dakta Ridwan ya yi sallama ya zo gaida iyayensa.    Ya dubi Ummi sannan ya dubi Faruk yana 'yar dariya.   "Ikon Allah, ashe na zo a daidai, da rabon ayi da ni." Sukayi dariya iyayen, shi kuwa gogan murmushi kawai ya yi.     Dakta ya gaisar da su Daddy sannan aka zauna yana fadin shi fa sai ya ga fuskar surukarsu.    Ikram ce ta shigo rik'e da hannun yaron Dakta, Ma'aruf, wanda ke faman rigimar zuwa wajen ubansa. Nan itama ta yi sararo tana duban Ummi.   "K'araso mana, yau fa babbar bak'uwa mukayi, matar Sadaukin Hajiya."   Ikram ta dubi Hajiya, Hajiya ta kauda kanta, to me za ta ce? Idan Faruk ya ce ga wacce ya ke so ya zata yi? Batun Ihsan ne sai yanda sukayi da shi.    "Mene sunanta ne?" Daddy ya tambaya. "Hasiya." Cewar Faruk, Ummi ta lumshe ido jikinta na rawa, tana gudun ace za'a bud'e fuskarta.    Ikram ta saki hannun Ma'aruf sannan ta karaso tana yar dariya na dole. "Nidai sai naga fuskar Antina."   Kafin Ummi ta yi wani yunk'uri, ta d'an bud'e mayafin ta lek'a. Zaro ido ta yi gami da bud'e mayafin gaba daya tana salati.    "Me..." Kowannensu ya mak'ale tambayar da ya yi niyya sakamakon fuskar Ummi da ta bayyana agaresu. Daddy yana mata kallon sani don tabbas yana ganinta jefi-jefi a gidan, saidai baisanta a suna ba ko matsayi.    Hajiya ta ji jikinta ya yi mata nauyi ta dubi Faruk, shi dinma ita ya ke kallo, gaba daya alamun tausayi, tsoro da kuma firgici sun bayyana saman fuskarsa. Ta maida kallonta ga Ummi wacce ta ke kuka sosai ga jikinta da ke kad'awa kamar mazari.    "Meke faruwa ne?" Fadin Daddy yana dubansu. Hajiya ta kasa kwakkwarar magana, karshe ma ta mik'e ta nufi dakin Daddy. Ikram da ta ke duban Ummi duba na tsana ta nunata da yatsa.   "Daddy wannan ba kowa bace face 'yar aiki, a gidan Mami ta ke a Kano shi ne ta dan zo nan, ita Yaya Faruk ke son kawomuku matsayin suruka alhalin ita din ba..." Wani kyakkyawan mari ne ta ziyarci kuncinta daga uban gayya, ta rike kuncinta wanda ba karya ta ji marin matuk'a. Ya nunata da yatsansa mai rawa, idanunsa sun kad'a ainun.   "Koda wasa, koda wasa ki ka k'ara wannan kuskuren sai kin raina kanki! Yaushe raini ya shiga tsakanina da ke?!"   Dakta cikin 6acin rai ya ke dubansa. "Ba ka da hankali Faruk! Akwai wani abu a kwakwalwarka, ina kai ina wannan? Akanta har ka d'aga hannu ka mari k'anwarka?!! Haba Faruk!! Wannan zubda k'ima har ina?!!!"          Faruk ransa ya yi mugun 6aci, ya girgiza kai yana duban Dakta.   "Na yarda k'ima da komai nawa su zube, sannan don Allah ba kai na kawowa Ummi ba, da ta yi maka da bata yi maka ba, wannan ruwanka."  Tsananin mamakinsa ne ya kama su, tunda suke da shi basu ta6a ganin kalar tashin hankali har haka akan fuskarsa ba sai a yau d'in, haka koda wasa bai ta6a yiwa wani cikin yayyunsa rashin kunya ba ko dai mayar musu da magana.  Daddy kallonshi ya ke yi yana nazari, shi yasan waye Faruk, mutum ne mai tsananin hakuri, kusan duk a yaransa daga Usman(Babban Yaya) sai shi a fannin hakuri, yakan hakura da abu duk son da ya ke mishi matukar wani cikin yayyunsa ya nuna baiyi ba saboda tsantsar kauna ta jini d'aya da ke gudana tsakaninsu.    Ya maida dubansa ga Ummi yana nazari, can kuma ya dubi Ridwan.   "Wuce gidanka." DAN ADAM @RUFAIDA OMAR    69Ya bud'e dakinta, saidai Binta ya gani wacce ke yawo a tsakar dakin tana jiran dawowarta, ganin Yalla6ai da kansa yasa ta russunawa ta gaisheshi, batare da ya amsa ba ya jefomata tambaya. "Ina Ummi?" Ta girgiza kai. "Bata shigo ba tun bayan fitarta." Ya juya kai tsaye wajen garden ya nufa, acan kuwa ya ganota durkushe k'asan bishiyar mangwaro tana faman kuka sosai. A gigice ya isa gareta ya durkusa kusa da ita. Jin motsi ne yasa ta dago kanta da sauri, ganin shine yasa ta numfasawa. "Kaga abinda muka janyo ko? Ni nasan wannan lamari ba mai yiwuwa bane." Baisan sadda ya rik'o hannunta ba. "Wa ya gayamaki bazai yiwu ba? Kada ki damu da abinda ya faru domin na zo miki da kyakkyawan albishir, iyayena sun amince da aurenmu." Ta yi sakato tana kallonsa, babu alamun wasa ya ke yi, ganin ta yi shiru ya girgiza hannunta. "Ba mafarki ki ke ba fa Ummi, dagaske sun amince da zancen aurenmu. Godiya ya kamata muyi ga Ubangiji." Ta lumshe ido, ta rasa irin yanayin da ta ke ji a jikinta, ji ta yi yana kokarin mik'ar da ita, a kunyace ta zare hannunta daga nasa ta mik'e, jerawa sukayi suka soma tafiya tamkar basu so, kallo daya idan kayi musu, zaka so kayita kallonsu tsabar dacewa da sukayi da juna. Ya dubeta. "Ummina shiru fa, kiyi magana please." Ta share ruwan hawayen da suka k'i tsayuwa. "Yaya Faruk." Ya tsaya a gefen kujera mai lilo ya zauna, sannan ya yi mata nuni da gefensa. "Zauna nan." Ba musu ta zauna jikinta a sanyaye. Ya juyo yana fuskantarta yana ji tamkar ya had'iyeta don so da tsantsar kauna. "Ina sauraronki." Ya fada cikin kankan da murya tamkar wanda baya son magana. "Kamar fa 'yan uwanka ba..." "Shiii.." Yasa yatsa a saman le66anta, ta kauda kai tana mai takaicin yanda bayason ta kawomishi zancen abinda ya kasance gaskiya kuma shima ya sani. "Ya dace ka bani dama ka ji abinda zan fada Yaya Faruk, akwai babbar matsala da kai ka ke mata kallon sassauk'a. Yaya Faruk kana da labarin Ihsan na sonka?" Ta karashe tana kallonsa, shima ita ya ke kallo, kenan dai shi 6oyon ma da ya ke mata ta sani? Abu daya ne bazai iya sanarmata ba, batun auren da Hajiya ta ce zaiyi da Ihsan don bai dauki hakan mai yiwuwa ba, kuma ba wai don Hajiyartasa bata isa ba, aa, sai don kokusa ba shi da tsarin had'a mata biyu a gidansa. Saidai abinda ya ba shi mamaki, bai wuce ta yacce akayi tasan da cewa Ihsan na kaunarsa ba. Ya kauda fuskarsa yana mai dan hade gira. "Ya akayi kika sani?" Ta yi murmushi mai ciwo itama ta maida dubanta ga wata shuka a wajen. "Shi so ba'a 6oyonsa, itama nata ya fito fili, k'alilan ne basu san tana sonka ba a gidan..." "Kinga ya isa haka please, ya isa. Ke bakya kishina ne? Bakya jin wani abu a ranki idan kina had'ani da wata bayan ke? Bazan iya rayuwa da kowace mace ba bayan ke. Ummi wai kinsan waye Umar Faruk kuwa?" Ya k'arashe yana mai tsuramata ido da wani murmushi. Daman ba kallonshi ta ke yi ba, wasa kawai ta ke yi da yatsunta. Ya girgiza kai. "Shikenan dai. Ban labari game da farin cikin da zaki yi ranar da aka shafa fatiha?" Maganar ma sai ta bata dariya, ta rufe fuskarta tana murmusawa. Karaf akan idanun Ihsan wacce ta fito don bawa wani mai wankin gidan ya siyo mata kati don kiran Maminta, ta jima tsaye tana kallonsu basu sani ba, hawaye kawai ke zuba daga idanunta. Ta k'arewa Ummi kallo, ta yi wani kyau a suturar dake jikinta, sannan ta dubi Faruk wanda ya bawa inda ta ke baya, ya wani duk'ar da kai a gaban Ummi yana lek'en fuskarta kamar mai shirin kai mata sumba. Nan duniya ta ji ta k'ara tsanar Ummi, ta k'ara tsanar Faruk da wai suke takara a sonsa da ita. Ina ita ina had'a masoyi da wacce tasan ta fi? Faruk ya cuceta, inama bai soma son Ummi ba ita ya so? Katin da bata bada an siyomata kenan ba, da gudu ta koam ciki tana rusa kuka, a kicin ta yada zango ta yi mai isarta sannan ta fito ta fada bandakin dake falon ta wanke fuskarta ta koma sama zuciyarta na wani irin zafi. Daddy ya cigaba da yiwa Hajiya nasiha mai ratsa jiki gami da nunamata shi fa lamari na aure ba'a dole, ya amince da bukatarta na aurawa Faruk duk su biyun saidai su dage da mik'a lamarin ga Allah kafin komai, a karshe ya ce su bar maganar nan zuwa kwanaki uku. Hajiya ta aminta da hakan, ta kuma sanarmishi cewar a gobe Ummi zata koma Kano. "Badai don maganarnan ba?" Ta girgiza kai tana dan murmushi duk don ta kwantarwa da mijinya hankali. "Ko kusa, saidai Madina ta buk'aci hakan tun ba yau ba, daman ina shirin sanarmaka sai wannan al'amari ya 6ullo." Ya jinjina kai alamun gamsuwa. "Shikenan ai, Allah Ya nunamana. Shima Ridwan zan ganshi gobe, banason abinda zai kawo rikici tsakaninsu." "Hakane." Hajiya ta amsa kafin ta mike don kawomishi ruwan lipton wanda ya saba sha duk dare. *** *** *** RINGIM Abu kamar wasa, k'aramar magana ta zama babba, don kuwa tuni Deen ya damk'awa Dija mak'udan kudi ta had'o lefenta. Tare da Saude da Baba Habiba suka shigo kasuwar Kano, nan suka shek'o kayayyaki masu dan karen kyau da tsada don har saida Deen ya k'aramusu kud'i. Yan uwa daidaiku ne kawai suka halarci ganin lefen don kuwa acewarsu abin kunya ne da abin tirr irin wannan cin amana da suka yi ga Munira. Kuma tabbas Allah bazai barsu ba, to ance wanda ya yi nisa ba ya jin kira, ko a jikinsu wai an tsikari kakkausa, Malam Yahuza abin na damunsa a kasan zuciya saidai babu abinda zai iya cewa, haka zai zauna tare da Balarabe mahaifi ga Ummi ya yi ta gayamishi bayason auren, shima kasancewar ba wani kata6us ne da shi a gidansa ba, saidai ya ce "To ya zaayi banda hakuri da addua? Matar mutum babu makawa sai ya aureta indai Allah Ya kaddaro tasa din ce." Haka suna gani matansu suka shiga shirye- shirye, an kai Dija wajen bokanya yafi sau biyar ana mata tsafe-tsafe don ta mallaki zuciyar Deen. Aikam sai haukacewa ya ke k'ara yi akanta, Munira dai yanzu abin ma ya ca6emata don hatta Yaransu ba shiga harkarsu ya ke ba, idan ka gansu kasan suna cikin tashin hankali marar misaltuwa. Har ana washegari Asabar daurin aure, Deen bai samu wata fuska daga yan uwansa ba, Munira kuwa a ranar ta juma'a ta iso Ringim din suna k'ara jajanta lamarin da yan uwanta, iyayenta kuwa nasiha kawai sukai ta binta da shi akan ta yi hakuri ta rungumi kaddara. DAN ADAM @RUFAIDA OMAR    68 Dakta daman a fusacen yake, hannun dansa ya rik'e ya bar falon bayan ya jefi Ummi da mugun kallo wanda batasan ma yana yi ba don kanta a sunkuye ya ke tana faman kuka da sheshshek'a. Itama Ikram mara mishi baya ta yi a guje tana kukan marin da ta sha. Daddy ya dubi Ummi. "Tashi ki je Hasiya." Ummi ta mik'e tana had'a hanya ta fita, tasan daman lamarin ba mai yiwuwa ba ne sam, tun yanzu ta soma fuskantar tashin hankali ina kuma ga idan ta koma Kano? Daddy ya zauna sannan ya dubi Faruk wanda ke tsaye yana duban hanyar da Ummi ta bi cike da matsanacin 6acin rai, har lokacin bai daina jin dacin maganganun yan uwansa ba ga matar da yafi so duk duniya. "Zo ka zauna." Cewar Daddy cikin kwantar da murya yana mai mishi nuni da gefensa. A hankali ya taka ya zauna a k'asa rai a jagule. Shiru na yan mintuna ya biyo baya kafin Daddy ya soma magana....Ihsan tsaye a falon Hajiya Babba ta yi tana jin yanda 'yar hatsaniya ke tashi a sashen Daddy, ji takeyi kamar ta je ta ga abinda ke faruwa. Tana nan tsaye Dakta ya fito a fusace, ko lura da ita baiyi ba haka ya fice, bata kai ga cewa komai ba Ikram ma ta sanyo kai, hawaye sha6e-sha6e saman fuskarta, a guje ta yi saman Hajiya, baki sake ta dubi saman, tana shirin maramata baya Ummi ta fito itama cikin shigar da ta mugun kad'a hanjin cikin Ihsan, gabanta ya hau duka da sauri-sauri. Suka dubi juna ido cikin ido kafin kuma a sanyaye Ummi ta soma tafiya, har ta bar wajen bata iya ce mata uffan ba, ta dafe kirji wanda ta ke ji kamar zai fad'o. "Me Ummi kuma ta ke yi a sashen Daddy, da kuma shiga irin haka?" Ganin babu mai amsamata ne yasa a karshe ta yanke shawarar bin bayan 'yar uwata tasan ko menene zata ji. Daddy ya dubi Faruk cikin kwantar da murya ya soma magana. "Tun tashinka ban ta6a kamaka da laifi na k'arya ko yaudara da makamancinsa ba Faruk, hakazalika ka kasance mutum wanda bai 6oye abinda zuciyarsa ke so." Daddy ya danyi shiru sannan ya cigaba da magana. "Ni ba k'aramin mutum bane, ba alfahari ba, Allah Ya azurtani da yara masu d'abi'u kyawawa hakazalika masu iyakar kokari wajen kiyaye dukkan wasu dokoki na Ubangijinsu, wannan karon sai aka samu akasi, zuciyata ta kasa nutsuwa da za6inka na matar aure, ina ganin kamar da wata manufa ta daban ka ke son auren wannan baiwar Allah da idan a batu na dukiya ne da jin dadin rayuwa, to kai din kana sama da ita, ina so ka gayamin tsakani da Allah, wane irin so ka ke ji ga yarinyar nan? Bazan lamunci tozarta DAN ADAM ba, don kowanne akwai darajarsa ta musamman, bazan lamunci ka aureta daga baya azo a samu matsala ba. Ka fadamin gaskiyar abinda ka ke ji game da ita." Faruk ji ya yi kamar ya d'aga Daddy ya cillashi sama yana ca6e don dad'i. Ya dan saki fuska. "Tsakani da Allah nake sonta Daddy, asalima kaunarta ta samo asali ne daga tausayinta da nake ji, wallahi ba ni da haramtacciyar nufi akanta." Daddy ya yi murmushi gami da dafa kan Faruk. "Tun da kake a rayuwa, ka ta6a zuwar min da wata buk'ata na k'i?" Hakoransa a bayyane yana murmushi ya girgiza kai. "Aa Daddy." "To wannan ma bazan k'i ba, matuk'ar na yi bincike akan yarinyar na samu kyakkyawan magana, baka da matsala. Ni mai aura maka Hasiya ne." "Da SHARADI.!" Suka tsinci muryar Hajiya daga bayansu, Faruk a rud'e ya ke dubanta, ta karaso idanunta na zubda ruwan hawaye ta zauna saman kujera. "Ki ka ce me?" Daddy ya fada da mamaki yana kallonta. Ihsan ta iske Ikram a daki tana kuka da sheshshek'a, wai yau Yayansu Faruk mai hakuri shine ya mareta akan wata banza yar aiki Ummi? Wannan abu da cin rai ya ke. "Ke wai meke faruwa? Tashi ko sanardani don Allah, ni gaba daya na shiga rud'ani wallahi, naga Ummi da wani shiga mai ban mamaki." Ikram ta mik'e zaune tana dubanta cikin dacin rai. "Za ki ganta da fin wannan ma wallahi muddin ba ki bud'e baki kin fayyacewa iyayenmu yanda ki ke ji game da Yaya Faruk ba, a yau Yaya Faruk ya kawo Ummi gaban su Daddy matsayin wacce ya ke so da aure. Har akanta ya mareni." Ihsan daskarewa ta yi tana duban Ikram, ji take kamar jinin jikinta baya gudana yanda ya dace, kamar wata sokuwa ta bude baki ta na kallonta. Ikram ta fayyacemata duk yanda akayi tun daga farko har zuwa marin da akayimata da rikicin Dakta da Faruk. Hawaye ne kawai ke kwararowa daga saman fuskar Ihsan ta kasa kata6us. Abin ne ta ke masa kallon mafarki. Ummi dai 'yar aiki, Ummin da ta ke ganin ta fita a komai na rayuwa, ta fita kudi da ilimi kai harma da yawan dangi kuma wadatattu da sauransu. Faruk matashi abin so da shaawa ga duk wata mace mai lafiya, matashi irinsa da ko 'yar shugaban k'asa ko wani basaraken, bata isa ta yi mishi kallo daya ta kauda kai batare da ta yabawa tsarin halittarsa ba, mata nawa ne ke son dace da samunsa? Su nawa ke rububi da fatan inama ace suna da damar da zaisa ya kasance a matsayin mijin aurensu? Ta girgiza kai tana sheshshek'a tana mai cigaba da sak'e- sak'en zuci. Abin kaico, ya buge a auren 'yar aikin gidansu, wacce zai iya samun dubu da suka fita komai ya aura. Abin kunya ne da takaici ace wai suna takara akan namiji daya tilo ita da'yar aikin gidansu, wannan kam raini ne da kaskanci agareta, wannan zubewar k'ima da ajinta ne a idanun kawayenta da duk wanda yasan irin mutuwar son da ta ke yiwa Faruk. Ikram kasa zaman dakin ta yi ta fito falo don ta ji da nata zuciyar dake mata wani irin daci, ga kuma tausayin Ihsan din da ta ke ji. Wasu lokutan so baima san kan wanda ya dace ya fad'a ba, ba don zargi babu kyau ba da sai ta ce anya kuwa ba wani siddabarun Ummi ta yi ga yayannata ba? Idan ba haka ba, ina shi ina wata Ummi? Ko diri da kyawun fuskarta ne ya d'ebeshi? Ta jefawa zuciyarta tambayar, sai kuma ta girgiza kai. Kayya da kamar wuya, idan don hakan ne kadai akwai wadanda suka ketare Ummin masu kaunarsa amman bai za6esu ba. Hajiya ta share hawayenta don daga daki ta ji dukka abinda ke gudana, hankalinta ya tashi jin wai yau yaranta sun samu sa6ani akan zancen auren Faruk. Ga kuma a gefe da ta ke tsoron abinda zai rushen k'akk'arfan zumuncinsu da kanwarta Madina. Ba zata ta6a amincewa hakan ya afku ba, don Ummi kuwa, kwarai yarinya ce mai hankali, ta cancanci zama matar d'anta don a halayya bata ta6a kamata da wani dabi'a mai muni ba, hakanan bata ta6a cin amanarta ba, daidai da Madina ta sha yaba hankalin yarinyar. Ta dubi mijinta kafin ta maida dubanta ga Faruk wanda ya sunkuyar da kansa cike da jin wani mugun tashin hankali. Yana fargabar abinda zai fito daga bakin Mahaifiyartasa. Baya fatan ace itama bata goyi baya ba, to amma a maganarta, ta nuna goyon bayanta saidai ta ce da sharad'i. "Kwarai kuwa Abban Ridwan, akwai sharad'i. Na amince ya auri Ummi, amma ina so itama Ihsan ya aureta!" Gaban Faruk ya bada sauti mai k'arfi, ya juyo a razane yana duban Hajiya, fuskarta a daure wanda hakan ya nuna babu alamun wasa a zancenta. "Ita Ihsan din ce ta ce tana sona?" "Na tabbatar kasan tana sonka Sadauki." Daddy ya yi shiru. Faruk ya girgiza kai a gigice. "Ni bana son..." "Kaga, tashi ka tafi zan nemeka." Cewar Daddy, Faruk ya mik'e ransa babu dadi ya fita, bai ta6a sha'awar zama da mata biyu ba, ta ya ya Hajiya za ta k'ak'aba mishi Ihsan alhalin tasan bai ta6a sonta ba? Asalima bai ta6a soyayya da wata diya mace ba sai Ummi. Hankalinsa ya koma ga Ummi, a wane ta ke ciki ne? Kai tsaye ya nufi wajenta don bincikawa.   DAN ADAM @RUFAIDA OMAR 71       "Ummi " Ya kira sunanta wanda ya yi sanadin katsewar aikinta da baya sauri don kusan rabinsa tunani ne ja gaba da zubda hawaye. Ta d'ago a sanyaye ta dubeshi, ya zauna gefenta duk jikinsa a sanyaye, ganin haka yasa ta yi kokarin maida kanta ga aikinta, saidai bai bata dama ba don kuwa da sauri yasa hannu ya taro ha6anta. Gefen fuskarta na hagu ya zubawa ido ganin yanda shatin yatsu ya fito 6aro-6aro, hakazalika wajen ya yi jawur, ya dubi tsakar idaninta da nasa idanun wadanda har sun soma kad'awa don 6acin rai.   "Wa ya mareki?" Shi ne tambayar da ya jefamata cikin kakkausar murya. Ta girgiza kai tana sheshshek'a.   "I'm asking you, who slap you?!!" Ya yi maganar cikin tsawa batare da ya ko tuna cewar wacce ya ke yiwa bata jin yaren ba.  Ta runtse ido don a zatonta ma duka zai kawomata.   "Ka yi hakuri don Allah." Ta yi maganar cikin muryar kuka, ya sauke hannunsa gami da yamutsa sumar kansa idanunsa a runtse, baya son jin kukanta ko kadan. A tausashe ya kara fadin.    "Naji, gayamin wa ya mareki?" Ina, ba fa zata fad'a ba, batason tashin hankali ya k'aru a gidan sanadiyyarta.     "Idan kana kaunar Allah da Manzonsa (S.a.w) abar maganar, ni ba wanda ya mareni ma." Yanda ta ke maganar gwanin ban tausayi yasa shi saukowa. "Shikenan tunda kin 6oyemin, share hawayen fuskarki."   Ba musu ta sa hannu ta sharesu. "Meyasa ba ki sanardani yau ake shirin tura ki Kano ba?"   Ta sunkuyar da kanta, dagaske ba kaunar Kanon nan take ba don ta tsorata da kalaman Ihsan.  "Kin dauka bazan sani ba? To babu inda za ki k'ara takawa da sunan aikatau in sha Allah, idan kinga kin bar nan to fa sai da niyyar tafiya gidanku." Jin haka yasa ta dubansa, ya gyada mata kai. "Dagaske." Kawai sai ta tsinci kanta da murmusawa, ta tuna Ihsan da alwashin da ta ci akanta, kenan dai Allah Ya yi nufin ku6utar da ita?   "Tunanin me kike? Kin ma karya kuwa?"   Kai ta gyada.  "To yanzu wannan ruwan da ki ke faman tsoma yatsunki ciki, zai iya sanyaki mura, kinga tashi mu shiga ciki. Bala!" Ya juya ya soma kwalawa mai kula da shukoki kira, mintuna k'alilan sai ga Bala ya iso, ya russina a ladabce. "Ranka ya dad'e." "Matse ka shanya wadannan." "To." Ya dubi Ummi da wani kallo wanda ta kasa jurewa. "Muje ko?" Ta kauda kanta ta soma tafiya. Bala ya soma wanki yana binsu da kallo cike da tunane-tunane a ransa da kuma mamaki, to me ya had'a kashi da fura?   "Ikon Allah." Ya fad'a a fili sannan ya cigaba da abinda ke gabansa.                       ***  ***  ***                         KANO       Ta kama baki cike da mamaki sadda ta ke fitowa daga d'aki sai kuma ta saki fuska tana 'yar dariya-dariya.   "Ikon Allah, ashe dai yaronnan da gaske ya ke, to, halan dai yau 6atan kai kikayi?"   Hajiya Mama ta ja guntun tsaki tana dariya alokacin da ta cire takalmanta ta k'arasa har falon Mami na biyu tana fadin. "Jimin ke da wata magana? Sai kace wacce ta kwashi shekaru bata lek'o ba."   "Aa, ba zancen shekaru, saidai idan ban manta ba rabon da ki zo gidannan tun kafin bikin Baraka, saidai fa a waya ko kuma idan na je."   Ta dan dara. "To naji marar mantuwa, ai gani yau na lek'o."    Mami ta zauna tana dariya. "Na ganki kam."   Hajiya Mama ta bi Mami da kallo cikin shak'iyanci ta ce. "To wannan k'ibar kuma fa? Anya Fahad bai kusa samun k'anwa ko k'ani ba?"   "Um, haka fa shima Abbannasu ke fad'i, wai duk na chanja kodai juna biyu gareni."   Hajiya Mama ta gyada kai. "Da alamu dai wallahi, amman ki je asibiti ki ji tunda ba kiyi girman da za ki tantance ko kina da ciki ko babu ba." Ta k'arashe tana 'yar harararta, sai ma ta bawa Mamin dariya, suka dara. Sun dan ta6a hira sai kuma Mamin ke sanarmata cewar yau Ihsan zata dawo tare da Ummi. Alokacin ne Hajiya Mama ta taso da maganar da ya kawota.    "Ke, ni wata magana ma na zo miki da shi, aikoni Hajiya Babba ta yi wajenki."   Cikin rashin

Chapter 19 of 40