Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 4
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels AWA 48 A ZIRIN GAZA Ibrahim Ahmad Daurawa Made:- Shuraih Usman Domin download na wasu kayatattun hausaebooks namu sai ku ziyarcemu a shafin yanar gizo gizon mu akan wannan adireshi http://shuraih.waphall.com Kuna iya ziyartarmu a shafinmu na facebook kuyi like http://fb.com/hausaebooks AWA 48 A ZIRIN GAZA Na Ibrahim akhatibi daurawa Littafi na daya 1 Page 1 Typing:- shuraih Usman Post shuraih 99% JAFFA . Allah daya gari ban ban nace a zuciyata bayan da iska mai zafi ta bugi fuskata a lokacin dana leko waje. Na tsaya karewa wajen kallo , tutar kasar izra'ila na fara hangowa tana filfilawa akan husumiyar filin jirgin saman , inda nan ake gudawar da zirga zirgar jiragen sama . Jama'a suna kaiwa da komowa a filin sannan na fara tako matakalar sauka daga jirgin , wani abu da bana mantawa da shi ne duk san da na dubi tutar izra'ila sai naji gabana ya yanke ya fadi ras . Da haka jakata a rataye a kafada ta muka yi dan tattaki zuwa falon karbar baki , wasu yan uwan su ko abokan harkansu sun zo tarar su cikin murna da annushwa . . Na kuma lura dda wasu ba taryar kowa suka zo ba babu wata walwala ko fara'a tare da su, idanunsu na kan kowa, kamar yadda kyanwa ke tare nutstuwa idan taji motsin bera. Ko ban fada ba kasan ko su waye su JAMI'AN TSARO NE . Wajen karban baki nan ne kuma ake duba fasgo da sauran takardun tafiye tafiye , gurin a tsare yake akwai kayan binciken muhimman takardu na zamani kamarsu inji mai kwalkwalwa da fitilun siddabaru wanda suke bayyana rubutun boye sirri . Kaman misali irin na takardar kudi, na bude baki ina kallon abubuwa har layi yazo kaina wani bayahude ya kalleni sama da kasa alokacin dana mika masa fasgodina a lokaci guda kuma gabana yaba da ras. Daga nan ya fara jeho tambayoyi barkatai iri iri kamar ruwa, kai ka cebai karanta fasgodina ba. . Abin dayai ba shi muhimmancin shine "me ya kai ka bosniya Hasgobina har tsahon wata biyar " don ya lura kan sarkin dayake jikin fasgon da kuma sabon da aka buga akwai tsahon kusan wata biyar a tsakani. . Azuciyar tana ce wannan bai shafe ka ba. Ina tunanin amsar da zan bashi yace "me ya kaika sayarebo" kai tsaye na bashi amsa "neman labari ya kaini" ya dubeni sosai kamar lokacin ya fara gani na "me ya zaunar da kai har tsahon wannan lokaci " ya bude ta ya kuma dubeni sosai " na so dawowa amma babu hanya saboda filin jirgin saman sayarebo yasha wata majalisar dinkin duniya ne ta rufeshi" yayi mini kallon ban gamsu ba . Ya gyada kansa cikin dabara hannunsa yanakan tebur ya gusa da shi gefen teburin ya danna wani dan kulltu wanda aka rufe gefensa da takardu, cikin ya aikata amma na lura da komai, don haka nasan cewa wani abu zai faru . Na kalleshi ido da ido yana shirin sake tambayata a cikin dakin dayake ciki kofa ta bude daga bayansa wani dogo kakkarfan bayahude ya fito ko'ina jikinsa an rubuce shi da jami'an tsaro ba sai ka tambaya ba duk da babu wata alama ko ta kayan sarki ,kallo daya kawai zaka yi masa ka tabbata jami'in tsaro ne ajin farkon babu wata tantama . Ya karbi fasgodina ya duba sukayi yaren yahudanci ya danna na'urar mai kwalkwalwa, yayi nazarin wasu bayanai cikin sauri "daga wacce kasa kazo nan" ya jeho min tambayarsa a lokaci guda kuma ya kura mini ido "daga Bosniya nake" na maida masa kai tsaye nima na kura masa ido " kai dan wacce kasa ce" ya sake tambaya ta . "Nijeria" na fada ba tare da na dauke idona daga kansa ba "Me ya kawo ka nan?" Nayi tunnani cikin sauri kafin na bashi amsa don na fara fahimta makircin da suke shirin kulla min kuma na san kasar izra'ila basa maraba da yan jarida kasan wanda yake da abin fada kum yason a afada bazai taba maraba da dan jarida mai kishin ba, sai dai yan abi yarima asha kida . Ni HADI sam ba irinsu bane ni dan jarida ne na hakika mai kishi, ina cikin wannan sake sake ne yace meye sana'arka na amsa "rubuce rubuce da neman labari" ya matso kusa dani "kana da sheda" na ciro katina daga aljihun rigata na mika masa ya duba ya kalleni ya sake kallona ya dauki kan talho yayi magana . . Ya ajjiye shi a hankali naga kamar yana tuna wani abu "me kazo yi nan" cikin sauri nace "yawon bude ido" ya tsira mini ido yasa hannunsa daya a aljihun wando ya kuma nuna ni da hannunsa na dama "bana son yan jarida a kasarmu sam bana maraba da ungulaye" . Yana rufe bakinsa wasu majiya karfi suka nufoni sun fito daga kofar kudu da inda nake ,kai tsaye suka nufo ni kamar kibiya,cikin sauri suka kewayeni daga nan suka ce na bisu inda suka fito na bisu ban yi wata gardamaba suka kai ni wani dakin bincike kwkkwara duk kayan jikina ba ain da basu duba ba hatta dunduniyar takalmina sai da aka kusa ballata bayan an gama bincike da wata yar na'ura mai kwalkwalwa da ake kira metal detector kwalar rigata ma bata tsira ba, babu inda ba'a bincike ba na share sama da sa'o'I ana yimin tambayoyi kala kala kamar mutumin daya fado daga duniyar wata . Daga karshe aka shige dani wani ofis inda na iske wani bayahude kato zaune akan kujera mai juyawa yana da kasumba da saje da gemu da kumatu luhu luhu yan idanunsa sun nutse ciki , akan teburin akwai talho zai kai biyar daya ajjiye wannan sai ya dauki wannan, ban ga sunan sa ba kamar yadda ake ajiye sunan mutum akan tebur ajikin dan katako ko roba , yana zaune yana busa tabar hanavana katuwa ahannunsa kamar yankan rake, muna shiga firgigit ya juyo da kujerar ya zuramin ido tamkar yana kallon wani dan kwaron da yake neman fada masa cikin shanyinsa ya gummtsi hayaki ya fesa sama, kumatunsa sukayi sama da kasa sai naji wani dan sauti kamar na kuya "Vulture are not welcome here and we think you have a hidden mission not tourism, even though we have nothing to incriminate you" Ma'ana ba a maraba da da ungulaye ,kuma muna tsammanin kana da wani boyayyen shiri ba yawon bude ido ka zo ba, ya sake busa sigarinsa na dube shi kawai cikin tsana da bacin rai don duk na gama galabaita da tambayoyi da bincike na wulakanci ga kallon kaskanci iri iri ya kalleni sosai "you are to deported back to where you come from" bansa dana yi subul da baka ba nace " tafi nono fari" ya dubi jami'an tsaron dake baya. Nan da nan suka bukaci dana fassara abin da na fada ya nace "shi kenan na gode" Toh anan zan dakata Tambayata anan shine MAI NE NE SUNAN MARUBUCIN LITTAFINNAN . AWANI SHEKARA YA WALLAFA WANNAN LITTAFI Bazan ga masu cika bakin cewa wai su suna karanta tsoffin littatafan hausa Daga naku shuraih 99% AWA 48 A ZIRIN GAZA Na Ibrahim akhatibi Daurawa Littafi na daya 1 Page 2 Typing:- shuraih Usman Post shuraih 99% . [kar ku manta dai kuna tare da shuraih 99% ne] Lokacin daya juya na naji yayi tsaki yace "we don't know who give you this pucking visas....." Na dan tsaya don naji karashen maganar jami'in tsaron ya rike kafada ya hankadani gaba "you are not welcome here" Turanci irin na amurka . Hankalina ya tashi gaba daya yayin da muka fito muka shiga dakin da akayi min bin cikie na zauna ina jiransu su tattaro min kayana . Raina ya gama baci matuka ainun don ba irin wulakancin da ban gani ba wajen binciken nan tambaya kamar wanda aka kama da laifin kisan kai . Aka garomin fasgo din akan tebur ya fado kan cinyata na yunkura na dauki jakata , don haushi ko budawa banyi ba na saka a ljihu, na figi jakata na saba a kafada nayi waje fuskata a daure rai na abace .inajin takun sahun mutun yana biye dan yana kokarin kwantar min da hankali wai ba sun yi min hakan don wulakanci ko kin bako bane sunyi ne don matakan tsaro .[kar ku manta dai kuna tare da shuraih 99% ne] Ni dai ko sauraransa ban yi ba da haka ya rakoni har tsakiyar filin jirgin saman abin dauya dameni kawai in rabu da wadannan yan wulakancin in dawo sayarebo wajen kausar ko hankalinta ya kwanta ni kuma inji sanyi a raina saboda ganin masoyiyata . Mutumin yayi min rakia zuwa kofar wani jirgin saman "swiss air" ina kokarin mika "boarding pass" dina na shige jirgin sai naji an rike min hannu ta baya , na juya a hankali na dube shi tsaf, dogo ne fatar jikinsa jajaja alamar ya zauna a kasa mai zafi , . Idonsa kanana masu launin toka toka , gashin kansa ruwan gitsawa yana da gashin baki ba gemu .[kar ku manta dai kuna tare da shuraih 99% ne] Ya mika mini hannu nine mr Ros ina son ganinka a ofis dina Wannan kalaman sun bata mini rai kwarai sai naji kamar ya kwaro min ruwan zafi, cikin sauri na nuna masa bodin pas "bana bukatar ganawa da kowa ba kun koreni ba na jefa masa maganar cikin gadara . Alokaci guda nayi kokarin shigewa ya rikeni gam " haryanzu kana cikin kasar izra'ila don haka dole ka mutunta dokokin karsa, ka biyoni kada kaji komai" . Naso nayi gardama koda na lura jami'an tsaro suna yimin muzurai kuma na san cewa ban shiga cikin jirgin ba dana shiga to nabar izra'ila kenan, ina cikin inuwar swizland" dole subarni ganin haka dole na rufawa kaina asiri na bishi duk jama'a suna kallona sun kuma san cewa da walakin goro amiya wannan shima ba karamin wulakanci bane , ace cikin dubbai an tasa ka gaba kamar barawo kowa na kallonka . mintina biyar a tsakanin ya miko min takardar iznin yawon bude ido a izra'ila amma banda wasu wurare daya kira "security zone" na duba takardun na ga babu iznin zama a telaviv da kewayanta sannan kuma an rubuta baro baro kada na shige kwana uku a kasar [kar ku manta dai kuna tare da shuraih 99% ne]. Na nutsu sosai wata tambaya tazo min me yasa yanzu aka bani izini bayan angama wulakantani an galabaitar dani an koreni kuma meyasa aka bani izni bayan da an mini cikakken bincike an gano ni hatsari ne ga tsaron izra'ila har an koreni don a huta da kaya sannan kuma a kirayoni a bani iznin ba wani kace na ce , lai lai da sake wai mai kaza ya tashi da kai, don haka nace dole nayi taka tsantsan da mutanen nan sai maganar shugaban hizbulla a sarayebo ta fado min "zasu iya binka su halaka ka" ************************************** Rana ta raba sama gari ya dauki zafi sosai na duba agogona na ga shabiyu da rabi na rana , na shafe a sama da awa biyar kenan a filin jirgin saman ana yimin tambayoyi da binciken bin kwakwaf . Na fito harabar filin jirgin tare da dan rakiyata inda jama'a suke zirga zirga a wajen akwai wajen ajiye motoci masu zuwa filin jirgin. Akwai kuma wajen ajiye motocin haya da bas bas na alfarma sunyi layi , sai ka fadi inda zaka kuyi tsada da direba [kar ku manta dai kuna tare da shuraih 99% ne]. Kai tsaye ko kuma kaje ofis dinsu idan kana da kudi da yawa ka cashe musu kudinsu su baka direna ya kai ka duk inda kake son zuwa iya tsahon zaman ka a kasar, idan kuma kai sananne ka iya hayar motar har iya zamanka. . Na dauki hayar mota ajin masu kudi duk kuwa da cewa ba matsala bane a guna amma ina da wani abu araina . Muna shige shigen karge na jami'an tsaron filin jirgin sama na faa fahimtar halin kuncin da falasdinawa suke ciki. . Duk ina da naga ana aikin kaskanci ko aikin wahala idan na tambayi direna sai yace falasdinawa ne. Ina son tambayar dalilin daya sa falasdinawa ne kawai suke aikin kaskanci sai naji gabana ya fadi Ras. Don haka na kanne nace na bincika da kaina . Yayin da yake shigowa yakin cikin birnin telaviv lokacin na kuma ga wani abu daban wato taruwan jami'an tsaro da sojoji dauke da makamai kamar ana yaki, motocin yan sandan tarzoma suna zirga zirga ko'ina rike da bindigogi da rediyon walis a kugunsu suna lura da kowa suna muzurai kai kace jiya jiya ne akaci garin da yaki. . Gaba daya yanayin garin ya sauya ya koma irin yanayin filin daga , a gaskiya har yasa tunanin tuzla ya fado mini arai, naji na kasa jurea har zuciyata ta fara bugawa da karfi, na dubi wanda yake gefena wanda shine dan rakiyata "tourist guide " na kalleshi sosai "wannan jami'an tsaron haka lafiya kuwa?" Na tambayeshi tun daya shigo baice komai ba sai a lokacin "Sune dakarun zaman lafiya" ya dauke kansa yana kallon waje a daidai lokacin wata mota ta gifta mu na lura da ita ganin yadda ya kalleta, sabuwa ce mutum biyu ne acikinta daya yana magana ta rediyon walis dake cikin motar babu fallen rubutun lamba, bayanta kuma wata ta shigemu an rubuta "first class citizen" dan kasa mai daraja ta daya. Ba a jima ba kuma wata ta shige da lambar "third class" da fari dai banyi niyyar tambaya ba saboda yadda naga na kusa dani yana kallona amma cikin dabara sai na jeho tambayar"mai daraja ta daya" meye kuma haka ya dubeni zaiyi magana sai mukayi burki a shigen jami'an tsaro [kar ku manta dai kuna tare da shuraih 99% ne]. A gabanu jerin gwanon motoci suna tafiya a hankali zuwa kofar shingen sojoji da yan danda wasu dauke da bindigogi suna muzurai, wasu kuwa suna rike da na'urorin bincike irinsu na'urar sansanar bomb data binciken bindiga wasu kuma suna takardun mutane sunayensu da kuma gurin da zaus da lambar motar da matsayin mai motar wato bako ne ko dan gida ne, shi din ma wacce daraja yake da ita kuma wanne jinsi ne bayahude ne ko balarabe "kai wadannan mutane da rashin yarda suke" bansan lokacin da wannan furucin ya fito daga bakina ba sai dai nayi sa'a da harshen hausa nayi shi . Mutumin dake kusa dani ya kura mini ido ya kalleni sosai, adai dai lokacin kuma motarmu cikin sanda ta kai ga kofar shingen wani soja rike da bindigarsa kirar amurka m16 ya iso cikin sauri ya sunkuya tun kafin yayi magana direban ya bashi takardunsa sukayi magana, ga alama dai sun saba da shi na lura lokacin daya mika takardunsa sinyi musanyar alama ta cikin dabara cikin na lura da su ta wutsiyar idona . Wani ya karaso dauke da wani dogon karfe mai fadi daga karshen sa kamar shebur ya karasashe a karkashin motar sannan ya umarcemu mu fito ya kara mana na'urar binciken bindiga, ya bukaci fasgo dina na mika masa ya buda ya dubeni sama da kasa [kar ku manta dai kuna tare da shuraih 99% ne]. Yayi magana sojoji cikin sauri suka baibayeni kafin kace kwabo har wani ya doramin bindiga a wuya , sunyi mamaki da suka ga ko gezau banyi ba ni mamaki kawai suke bani ba tsoro ba, Na dubesu daidai cikin natsuwa "ka keta dokar kasar izra'ila "wata murya ta fada a bayana nayi kokari na waiwaya don yin tozali da mai maganai suka hanani motsawa "what is the hell with you" na fada cikin fushi "you are deported" murya ta mayar mini duk jami'an tsaro dake wajen suka juyo guri na cikin sauri suna jiran cika aiki kamar kare ya hango muzuru . Toh anan zan tsaya don na gaji Sai mun hadu ranar friday Daga shuraih Usman Inkiya shuraih 99% AWA 48 A ZIRIN GAZA Na Ibrahim akhatibi Daurawa Littafi na daya 1 Page 3 Typing:- shuraih Usman Post shuraih 99% . [kar ku manta dai kuna tare da shuraih 99% ne] Cikin hanzari na fisge fasgona daga hannunsa na buda wani shafin na nuna musu inda aka buga mini iznin shiga kasar kuma na cire "tourist visit permit" na nuna musu a daidai wannan lokacin wata mota jif patrol ta soja tayi birki a gabanmu akwai eriya doguwa a jikin motar . Wani manjo janar din soja ya dirgo kato ne mai katon ciki kamar tulu da walis a hannunsa fuskarsa kamar an aiko masa da mala'ikan mutuwa a turbune babu wani annuri Idanunsa irin na kyanwa kumatunsa kamar an sassaka, mai zagayyar fuska yana da saje da gemu buyya wanda ya maida shi tamka dattijon biri . Kafafunsa shafta shafta kamar dirka, kafarsa daya tafi daya tsawo abinda yasa tilas yake tafiya irin na kaguwa ya na dinkisawa a birkice . A kowane gefensa wasu matasa madaka kare suna biye da shi, kowane da karamar mashigan rike a hannunsa sun gama shirin tsaf suna shirin bude wuta jiransa kawai suke yace ket su cika aiki. Duk suna sanye da kayan soja mai rodi rodi , sauran kuma cikin motarsu suke suna masa rakiyta duk sunyi shirin kota kwana , yana karisowa gurin sauran sojojin a sauran jami'an tsaro suka sara masa sukayi cirko cirko wani kurtu ya fara masa bayani da yahudanci, ya dubi ne yayi musu magana da amon sautin jemage [kar ku manta dai kuna tare da shuraih 99% ne]. Nan take suka janye bindigoginsu daga saman sukayi sororo da su suna sauraransa cikin tsoro da girmamawa kai kace mala'ika neshi . Wannan girmama ta bani mamaki . Ya karen kallo tsaf ya karbi takarduna ya duba su a hankali cikin takama, kasaita da nuna isa ya gama ya sake kallona yayi magana daga cikin motar sai naga wal hasken fitilar daukan hoto na tabbata hoto na aka dauka , kawai sai naji sautin jemagen yana furta kalmomin turanci "be careful don't do anything wrong like gathering information or tres-passing into security zone or any no go area" yayi murmushin mugunta ya girgiza kansa "I will teach you a lesson that you will never forget throughout your life " Ya kalleni ya nuna ni da dan yatsansa cikin wani sauti mai tsoratarwa yace " kada ka tara ko ka rubuta mummunan rahoto akan kasar izra'ila kada ka kuskura ka aika da labarai a ciki ko a wajen izra'ila idan ka saba wannan ka'idodin yan yatsunka zasu baka amsa" . "I will cut this into pieces if you write mischief against us Mr goyim remember I am major dayin robert" ya kalleni sosai ya kada kai ya juya yana dingisawa ya shige motarsa suka rankaya a guje suka barni anan ina gumi ina yarfewa, sautin maganarsa yana kararawa acikin kwakkwalwata .[kar ku manta dai kuna tare da shuraih 99% ne] Mun karaso birnin telaviv da la'asar, yunwa da gajiya da zulmin major doyin yasa abun duniya ya dameni Na lura lallai nan ba wurrin da yan jarida suke da yanci bane , banayi binciken abubuwan da suke raina . Ko'ina jami'an tsaro da sojoji ne birjik kamar wani sansanin yaki, irin shingayen da na gani a hanya tamkar wani filin daga ne daya fada hannun abokan gaba , irin yadda ake binciken mutane daga inda suka fito da inda zasu da kuma abin daya fito da su sai ya tuna mini kasar afirka ta kudu alokacin wariyar launin fata inda bakin mutum bashi da iznin zuwa wani gari sai da takardar izni idan turawa sun amince da dalilin zuwansa a bashi kayadadden lokaci idan kuma lokaci yayi ya fice ko ya yabawa aya zakinta . Direba ya dauke hanya yaki shiga dani cikin birnin ya zarce dani wani gari a bayan telaviv JAFFA inda larabawa ne suke zaune a cikinsa . Dana nemi dalili yace wai ba bashi iznin kaini cikin birnin tel-aviv ba "doka ta hana shiga da bako sai da izni na musamman" . dana ji haka nace ya kaini otal mai saukin kudi ba wai don babu kudi isassu ne aguna ba , ina da kudi masu yawa wanda na samu daga wajen kaosar dalar amurka cinkus a jakata kuma duk binciken da akayimin ba wanda ya damu da kudina ina dauke da "america express card" don gudun sata ko shiga halin kaka ni kayi naso zama a otal mau saukin kudine don na samu cudanya da talakawa da sauran mutanen da ake samun labarai barkatai a gunsu . Sabo da yar gogayyar dana samu a aikin jarida , na lura mutane masu kudi ko fada aji basu cika fadar labaran rayuwansu ba, ko abinda jama'a suke da sha'awa akansa na halin zamantakewa ko halin musgunawa daga hukuma , su kullum suna boye labaransu suna kuma kaffa kaffa da abinda zasu fada a ko'ina suke, sannan kuma hukuma bata cika musguna musu ba, don haka basa sukarta , Bihasali ma ra'ayinsu shine ra'ayin hukuma amma ta zama cikin talakwa kuma larabawa zai kai ni na samu na kai ga bin da na zo nema ba tare da katsalandan din jami'an tsaro ba Matsala ta itace wannan dan rakiyar dole nasan yadda nayi na yarda shi cikin dabara .[kar ku manta dai kuna tare da shuraih 99% ne] Tafiyar kamar mil shida daga tel-aviv muka yi kwana zuwa dan gari mai girma da ake kira jaffa, abubuwan danagani sun bani mamaki kwarai , gidajen larabwa falasdinawa wasu sun rushe wasu kuwa sun dade da zama kango, wasu kuma ga suna ,rabi a rushe rabo a tsaye , babu wani gyara kamar wani sansanin bayi , Jami'an tsaro da suke safa da marwa sun maida garin kamar garin da aka fafatawani yaki . Abinda zaka fara fahimta shien talauci yayiwa mutanen farin kanta na tambayi direba dalilin da gidajen wasu suke a rushe "basu da iznin gyara gidaje" ya fada mini . Wannan amsar ta bani mamaki mutum da gidansa wai sai ya sami iznin gyarasa, zan sake tambayar naga dan rakiyata yana kallona sai kawai na kanne dana tuna da maganar mr doyin , muna dada ratsa garin jami'an tsaro suna kara yawa suna tsaida abin hawa suna bincikawa suna buda kaya sannan su caje mutum tsaf . Da kayi wata gardama sai su kama mutum su garkame shi acikin wata shiga ba biya. Wannan abubuwan din bani mamaki da tsoro da haushi alokaci guda, domin wannan babu wata maraba da mai mutane fursononi a garinsu ko daurin talala mai kamar sake .[kar ku manta dai kuna tare da shuraih 99% ne] Mun isa babbar kasuwar garin karfe biyu da rabi na yamma munje don nayi saye saye sannan ya wuce dani gidan saukar baki Tun kafin na fito daga motar naga matan larabawa suna saye da sayarwa cikin fara'a wasu suna sai da kayan marmari da yayan itace . . Alokacin guda kuma wani abu ya bata mini rai matasa sanye da wandon kaki rin na soja da fara singileti sanye da wata hula yar karama mai kama da yar madina shudaye mai ratsin fari suna rike da mashigan suna bi layi layi , rumfa rumfa kamar duba gari kasancewar su agun sun mai da kasuwar kamar kurkuku [kar ku manta dai kuna tare da

Chapter 1 of 4